Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wata biyu sai su dawo, Kin san manager gun nan sonta ya ke shiyasa ta ke abinda taga dama, ita kuma hankalinta nakan Oga Habib". Hassana shiru kawai ta yi, amma tasan zata sha wahala ace aikin da wasu sukeyi su biyu suka kasa abata shi ita kad'ai.staff d'in nan kallan Hassana ya yi, ya ce, "Tom ni dai Sunana kabiru, amma mutane na kidana da barber for ladies,ki fa ya sunan ki? ". murmushi Hassana ta yi mai sannan ta ce, "Sunana Hassana". kabiru kallan Hassana ya yi, ya ce, "kai amma gaskiya kinada suna mai dad'i , bari in je in yi abinda zanyi, sai anjima in munhad'u". Kabiru ta fiya ya yi yabar Hassana gun tsaye tana kallan yadda ma aikatan ke ta aikin d'ura yughurt d'in da akai cikin robobi. Hassana na nan tsaye tana kallan aiki ga wani irin k'amshin swtrovery da ke tashi agun. Hassana na nan tsaye ta ji, andafa ta. Da sauri Hassana ta waigo tana kallan wadda ta da fata.matashiyar budurwar ce, zasu iya zama sa'a da Hassana, kallan Hassana ta yi, ta ce, "Amma dai ke new worker ce anan ko? ". Kai Hassana ta d'aga mata. "Ai dama tunda naga kina sauraran kabiru na san ke sabuwar ma'aikaciya ce nan, abinda zan fad'amiki ki rabu da Kabiru dan daga ganinki kina da mutunci da kamun kai, kabiru ko d'an iskan mai rai ne, biki ji sunan shi ba, barber for ladies,sannan idan supervisor tazo ta ganki tsaye ahaka, zaki samu matsala. B'angaran me ye aka d'auke ki". Hassana kallanta ta yi, ta ce, "shara da goge- goge". "Tom kinga ga rack can d'akko shi zaki yi, duk abinda ya zube kina gogewa, ki tafa bata yadda ta ganka a tsaye ba". Hassana godiya ta yi mata, sannan ta zo gusa da su, da morpper d'inta duk abinda ya zube tana gogewa. Kafin lokacin tashi ya yi Hassana ta share duk inda ya ke ak'ark'ashin ai kinta. K'arfe 8:00pm Hassana ta fito domin ta fiya gida, sai a lokacin Hassana ta tuna bata da ko sisi, gashi tun d'azu taga fitar manager bare ta fad'a mai inda taga alamar yana da kirki sosai. Hassana wajan parking space ta shiga tana zuwa ta motar Oga Habib agun, azuciyar ta tace bai tafiba kenan, Ya Allah banda yadda zan yi kuma bazan gane gidan ba, Allah ka bashi ikon d'aukata. Hassana guri ta samu ta zauna tana tunanin yadda zata iya yima Oga Habib magana ya d'auketa. Wata zuciyar ta ce, kai Wallahi bazan iya ba, dan ko nayi ma ba d'aukata zai yi ba, wata zuciyar ta ce mata, tom idan baki mai magana ba, ai kin kwana a titi. Hassana na zaune tana wannan tunanin ga tunwa duk ta da meta, tun tea d'in da Jimmai ta bata da safe tasha har yanzu shi kad'ai ne a cikinta, d'azu tana gani staff d'in gunna fita cin abinci amma ita bata da kud'i sai dai ta hakura. Hassana na nan zaune, ta ga fitowar Oga Habib, yana zuwa ya fad'a motar shi. Hassana da sauri ta tashi ta nufi gun motar Oga Habib...............





TOFA IDAN OGA HABIB BAI D'AUKI HASSANA BA, YA ZATA YI????? 🙆‍♀️🙆‍♀️


ANYA KO KUNA GANIN OGA HABIB ZAI IYA D'AUKAR HASSANA?????





COMMENT &
SHERE
PLEASE
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

TSARAWA
DA
RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy Baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

My Facebook group:Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

MATSALOLINMU A YAU GUDA BIYU NE:MU YI AIKI KAFIN MU YI NAZARI, KO MU YI TA NAZARI BA AIKI. ALLAH KASA MU RIK'A AMFANI DA LOKUTAN MU.


SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.



Shafi na 12&13.




Hassana cikin fargaba ta k'arasa gun motar Oga Habib. Sai dai Hassana na k'arasawa gun shi kuma yana sama motar shi key ya bar gurin. Hassana d'agama Habib hannu ta ke amma Habib na lure da ita, ya yi tafiyar shi, yana maganar zuci, ba dai yarinyar nan tana nufin in d'auketa bane a motata ko. K'wafa Habib ya yi yaja motar shi ya tafi.
Hassana ko rasa yadda zata yi ta yi, hanya ta kama takama tafiya a k'asa dan tana ganin zata Kane gidan. Tafiya sosai Hassana ta yi sannan ta isa gidansu Oga Habib. Lokacin 11:30 pm.Hassana na zuwa ta iske anrufe get d'in gidan, tom dama daga Habib ya dawo ake rufe gidan.Hassana cikin fargaba ta fara bubbuga get d'in gidan. Hassana ta dad'e atsaye tana bubbugawa sannan d'aya daga cikin get man's d'in gidan yazo yana tambayar waye. Hassana cikin tsoro da jin yadda ya yi mata magana ta ce, "Hassana ce sabuwar ma aikaciyar da Oga Habib ya d'auka jiya". Tom a k'a'idar gidan su Oga Habib duk 'yar Aikin da aka d'auka sai an nuna ma masu gadin gidan gaba d'aya ita dan su shaida fuskarta. Wannan umarnine daga Hajiya turai. Hakan yasa ya koma ya tambayi sauran masu gadin, akan ko sun san da d'aukar sabuwar mai aiki a gidan. Nan suka ce mai a'a. Jennies dawowa ya yi, ya ce, ma Hassana, su babu wata mai aiki da aka d'auka jiya, dan haka tabar gun kafin ya fito.
Hassana cikin kuka da da nasanin barin gidansu da ta yi, ta ce, "Wallahi da gaske na ke, ka tambayi Oga Habib, ni ce wadda Oga Bilya drivern Oga Habib ya kawo, tom jiya suka d'aukan aiki, ko yau ta get d'in nan na wuce". Shiru ya yi dan ya ji maganar ta kamar da k'amshin gaskiya, hakan yasa ya ce, "Ok, bari in kira Oga Habib tukun, idan yace abarki ki shigo tom zan bud'e miki, amma idan yak'i sai dai ki yi hak'uri". Jennies number Habib ya kira. Lokacin Habib ya yi nisa sosai a bacci, ringing d'in wayar shine ya ta da Habib daga bacci. Habib cikin murya bacci ya d'aga wayar batare da ganin Number ko waye ba, ya sa akunne. Jennies naji Habib ya d'aga wayar ya ce, "Oga Habib dama wata Yarinya ce ta zu yanzu tana nocking get wai jiya aka d'auketa aiki a gidannan". Habib najin haka ya yi tunanin yarinyar nan ce, acewar shi. Habib ce mai ya yi karka bud'e mata. Yana cewa haka ya kashewar. Jennies buga get d'in ya yi, ya ce, ma Hassana "knji ko, Oga Habib ya ce bai sanki ba, dan haka ki bar nan yanzun nan! ". Hassana matsawa ta yi daga jikin get d'in. D'annesa da get d'in, Hassana zuk'unna ta yi tana kuka.Habib ko tashi ya yi, ya zira jallabiyar shi ya nufi wajan get yana jan tsaki. Habib na zuwa ya yi ma d'aya daga cikin ma'aikatan magana, ya ce, "kubud'e min get ". Bayan an bud'e ma Habib get d'in fita ya yi, can nesa da gidansu yahangi Hassana zaune ta tura kanta tsakankanin cinyoyinta tana kuka. Habib daga idan ya ke tsaye, ya kira Hassana ya ce, "keee!! ". Hassana cikin tsoro tata shi zata gudu. Sai ji ta yi, Habib ya kuma cewa, "kee bakya jine". Hassana da katawa ta yi daga gudun da za ta yi, ta k'arasa in da Habib ya ke tsaye. Habib kuma yana ganin Hassana ta taho ya shiga cikin gidan. Hassana shiga ta yi ita ma, Hassana nashiga ta iske Habib tsaye kamar ita ya je jira. Hassana k'arasawa in da Habib ya ke ta yi. Habib wani irin kallo ya yi ma Hassana mai cike da ma'anoni da dama, sannan ya ce, "Daga yau in dai kika wuce 7:00pm baki dawo ba, tom karki kuma buga ma mutane get, idan ba haka ba kuma Habib ya nunata da hannu, ya ce, "Sai dai ki nai mi gurin zama, amma ba dai gidannan ba". Habib na fad'in haka ya tafi yabar Hassana nan tsaye k'irjinta na dukan uku-uku.Hassana cikin sauri ta je site d'in su, har sun rufema ta buga masu, suka bud'e mata. Jimmai ce ta tashi ta bud'e ma Hassana k'ofar, dama tun da zu ta ke tunanin lafiya, jin Hassana shirun da ta yi.Jimmai na bud'ewa ta kalli Hassana ta ce, "Hassana lafiya dai ko?, na jiki shiru tun d'azu". "Kud'in napep ne banda shi, a k'asa na dawo shiya sa". Jimmai sosai ta tausayama Hassana sannan ta d'akko ma Hassana abincin da ta d'ibar mata ta bata". Hassana nagama cin abincin ta kwanta ta kama bacci, dan sosai ta gaji.
Washe gari da wuri Hassana ta tashi ta yi wanka, ta sa kayan Jimmai kamar yadda jimmai ta ce ta rik'a sawa, Sannan Jimmai ta ranci kud'in napep gurin karima, taba Hassana. Hassana sosai ta yi ma Jimmai godiya sannan ta ta fi. Hassana na isa ta ta cigaba da sharar b'angaran ta. Kafin wani lokacin Hassana ta gama share gurin ta goge".



BAYAN SATI D'AYA.
Yau sati d'aya kenan da fara aikin Hassana a sanat yoghurt. Kullum Jimmai ke rantar kud'in napep tana ba Hassana, da sunan idan wata ya yi, anyi albashi Hassana ta biya su. Yau ma Hassana da wuri tata shi domin tafiya sanat yoghurt Company. Hassana sai da tama shirinta, ta tambayi Jimmai kud'in napep. Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, "Hassana Wallahi yau sai dai ki yi hak'uri , kin san ni dama daga wata ya yi an bani salary na na ke kaiwa gidanmu, tom wadda na ke rantar mi ki kud'i gurinta kuma, Wallahi ita ma kud'inta sun k'are". Hassana shiru ta yi tana tunanin mafita , dan tasan sai dai ta je ak'asa, kuma idan har ta je a k'asa tom tabbas baza ta iya sharar da ta ke ba, dan yanzu haka ciwan baya ta ke, dan gurin nada girma kuma ita kad'ai ke aikin sharesa da gogesa. Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Jimmai ya zanyi?, dan Wallahi supervisor d'in mu bata da kirki ko ka d'an,bata karb'ar uzirin mutum in dai bai je aiki ba". Jimmai dafa Hassana ta yi, ta ce, "K'awata ni gani na ke yi ki yi hak'uri da zuwa yau inda ya za ki yi, ba ki da kud'in napep ". Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Jimmai zata fa iya korata aiki akan haka, nace miki bata da kirki".Shiru Jimmai ta yi, sai zuwa can ta ce, "Yauwa k'awata ko zaki je wajan get ki jira idan Oga Habib zai tafi sai ki fad'a mai baki da kud'in napep yau ba za ki samu zuwa aiki ba"Hassana da fe k'irji ta yi ta kalli Jimmai, ta ce, "Jimmai rufa min asiri, kin san ko waye Oga Habib!?". Dariya Jimmai ta yi, ganin yadda Hassana ta dafe k'irji, ta ce, "Hmm Hassana ke nan, ni ko nasan waye Oga Habib, bashi da d'igon kirki ko kad'an, dama dan naji kin ce shiya d'auke ki aiki ne,shi yasa. kuma tunda har ya barki ki ke zaune anan ai ke da dama-dama, ni da ko hanya bana so ta had'ani da shi, dan ni Wallahi tsoran shima na ke ji". Hassana kallan Jimmai ta yi da mamaki, ta ce, "Ki ce ba ni ka d'ai ke tsoransa ba, amma shine ki ka ce in rok'ai kud'in napep, bacin kin san ba ban zai ba, sai dai ma k'ila ya yi min wulak'anci". "Hakane k'awata ki yi hak'urin zuwa yau, zuwa gobe insha Allah zamu san yadda za ai". Hassan tom kawai ta ce ma Jimmai dan bata da yadda zatai. Amma tana tunanin yadda zasu kaya da supervisor d'in".


Can sanat yoghurt ko,haka akai aiki gun batare da anshare ba, ko angoge.
Yau kwana uku kenan Hassana na zaune gida bata da kud'in zuwa company. Tom kuma dama Hassana ce kad'ai mai sharar b'angaran, Billy duk ta ba sauran masu sharar suspension.
Yaune kuma abokan Habib wa inda su kai karatu tare suka kawo mai ziyarar bazata. Habib na zaune a office d'in shi ba zato ba tsammani, ya ji nocking. Izinin shiga Habib ya basu. Sai dai Habib sumar tsaye ya yi, da mamaki ke kallansu, rungume su su duka biyu Habib ya yi, ya ce, "Faruq, Nasir, zan rama, nima duk sanda zan yi visiting naku, sai dai ku ganni, ba bu Anousing". Habib zama ya yi yana nuna masu gurin zama. Wanda Habib ya kira da faruq, kallan Habib ya yi, ya yi murmushi ya ce, "Habib Allah ba zuwan siri bane mu kai, yanzu dai babu lokaci, mu shiga ciki Nasir yaga factory naka". Habib jagora ya yi masu yana kaisu kona suna gani. Wanda aka kira da Nasir ko sai yaba girman gurin ya ke, da tsaruwa irin ta gurin ya ke. Faruq, kallan Habib ya yi, ya ce, "Habib kasan Allah ina jin dad'in Yoghurt d'in ku sosai,dan gaskiya mutanan Taraba, suna son yughurt d'in ku sosai, dan manyan-manyan restaurant d'in Taraba duk inda kaje zaka samu sanat yoghurt". Murmushi Habib ya yi mai, ya ce, "Kasan ko kwanannan na ke son juwa Taraba dan bud'e sabon Company acan". "kai Habib, wai yanzu state nawa ke da branch a can". "Kano, Kaduna, sai nan Abuja". Habib suna tafiya suna tattauna da abokansa har suka isa, site d'in da ake Yoghurt d'in. Duk company babu inda ya kai gun girma, kuma site d'in ne Hassana ke aikin sharewa da gogewawa. Gashi yau har kwana uku kenan Hassana bata zoba, gun ya yi datti sosai dan har k'udaje ke ke waye gun saboda yadda ya yi. manager ko yau satin shi d'aya kenan da yin tafiya, yabar komai a hannun supervisor. Habib sosai ya ji kunyar yadda friend's d'in sa suka ga gurin. Hakan yasa Habib ya ja su suka koma Office d'in shi. Habib na kai su Office ya dawo gun ranshi ab'ace yana kallan ma'aikatan gun, Habib cikin daka tsawa da b'acin rai, ya kalli ma'aikatan gun ya ce, "Aikin waye wannan!? ". Yafad'i maganar ya na nuna gurin da hannu shi. Dukkan su shiru su kai dan ba sanin sunan Hassana su kai ba. Hakan yasa Habib ya kalli d'aya daga cikin staff d'in ya ce, "ki ramin supervisor ". Wanda Habib ya aika da saurinsa yabar gun ya nufi office d'in, Bill.
Billy na zaune da waya rik'e a hannunta tana charting ta ji ana mata nocking. Billy izinin shigowa ta bata. Staff d'in da Habib ya aika, kallan Billy ya yi, ya ce, "Sister Billy Oga Habib na kira". Billy kallan staff d'in ta yi, ta ce, ka ce mai ganinan zuwa, yana office d'in shi ne? ". "A, a yana site d'in mu". Yana fad'in haka ya juya ya tafi.
Billy kuwa jin Habib na kiranta powder ta k'ara shafawa da lipstick abakinta, sannan ta fita.
Habib na tsaye ranshi ab'ace, ga shi shi a ganinshi Billy ta b'ata mai lokaci. Habib na nan tsaye yana huci Billy ta tahu tana yauk'i ita Allah dole ga wadda Oga Habib ke kira. Billy na zuwa gaban Habib ta tsaya kamar zata shige jikinsa, ta ce, "Oga Habib ga ni". Habib ko, kallan k'askanci ya yi ma Billy sannan, ya ce, "Yama sunan ki? ". Billy cikin mamaki wai ita Habib ke ce ma ya sunanta. Billy kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib yanzu kamant.... ". Habib hannu ya d'agama Billy sannan ya ce,"Daga nan zuwa minti shafiyar idan har ba agyara gurin nan ba, tom ki gama aiki a sanat yoghurt, sannan wannan ya zamana na farko da na k'arshe, aiki kika zo yi ko shirme?, in dai baki gyara ba tom zamu da katar da ke! ". Habib na fad'in haka ya juya ya bar gun ranshi b'ace ya bar gun.
Billy kuka ne kawai ba tai ba , dan a cewarta Habib ya tozartata gaban staff. Hakan yasa Billy ranta b'ace ta ce, "Wata idiot d'in ce ke kula da site d'in nan". Wata daga cikin sttaf d'in ce ta ce, "supervisor new worker d'in nan ce, kuma yau kwana uku kenan bata zo ba, ina jin bata da lafiy.... ". Tsawar da Billy tai mata ce yasa tai shiru, ta ce"Allah yasa ubanta ne ya mutu tabar aiki amasana'artannan, kuma sai naci mutuncinta fiye da wanda Oga Habib ya ci min............





COMMENT
&,
SHERE
PLEASE 🙏
📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Fabby baby).


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

Facebook group :Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

IDAN KA MUTU AN RUFE LABARINKA, AMMA ABUBUWA UKU SUNA RAYUWA A BAYANKA:
☝🏻ILIMI DA
✌️HAIHUWA SAI
AIKIN ALHERIN DA KA SHUKA. ALLAH KA SA MU DACE👏.


SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN 👇🏻
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT 👇🏻
08142904255.


Shafi na 14&15.




B'angaran friend's d'in Habib, Habib na koma wa Office d'in su kai mai sallah su kace tafiya za su yi. Habib godiya ya yi masu sosai, sannan yasa aka cika masu bayan But d'in su da yoghurt.
B'angaran Hassana ko, Yau ta tashi da niyyar ko ak'asa ne sai ta je aiki dan zaman ya isheta, ga tsoran supervisor d'in su da ta ke yi, dan ana yawan fad'a mata rashin mutuncinta. Hassana da wuri ta shirya kamar yadda ta saba shiryawa ta kama hanya ak'asa ta tafi. Hassana ba ita ta isa sanat yoghurt ba, sai 9:30Am. Ita da ke zuwa tun seven o'clock. Tom dama Billy ta bada sak'o ta ce idan Hassana tazo aiki ace mata tana nai manta a office d'in ta. Hakan ce ta kasan ce, Hassana na zuwa wata daga cikin staff d'in ta sanar da ita sak'on supervisor d'in. Hassana cikin fargaba ta tura Office d'in supervisor ta shiga. Lokacin Billy na zaune tana aikin danna waya. Hassana cikin girmama ta ce, "Barka da aiki supervisor". Da kai Billy ta amsa ma Hassana. Hassana kuma ci gaba da tsayuwa ta yi, tana jiran hukuncinta. Ita ko Billy tama manta da wata Hassana, hakan yasa ta kalleta ta ce, "Lafiya za ki zo ki tsamin akai? ". Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "Supervisor dama wata staff ce ta ce kince idan nazo aiki nazo kina kirana". Hassana ta ci gaba da cewa, "Supervisor Wallahi rashin kud'in napep ne ya hanani zuwa aiki, kwana uku da banzo ba, ko yauma ak'asa nazo". Billy bar abinda ta ke yi awaya ta yi, ta d'aga kai tana kallan Hassana, ta ce, "Ki ce mai sharar site d'in da ake yoghurt ko? ". "Eh ni ce". Cewar Hassana. "Billy kallan Hassana ta yi da b'acin rai dan sai abinda Habib ya yi mata yadowo mata farko, hakan yasa cikin d'aga murya ta ce, "Hassana ki ke ko me!?, mun da katar da ke aiki a k'ark'ashin sanat yoghurt Company ". Hassana cikin tsoro da fargaba jin abinda Billy ta ce mata, ta ce, "Supervisor dan Allah ki yi hak'uri insha Allah daga yau haka bazai kuma faruwa ba". Billy ko inda Hassana ta ke bata kalla ba ta ce, "Nariga na gama magana, ki kalli time kigani ko yanzu k'arfe nawa kikazo aiki?, bama aiki da wanda bashi da experience, fitar min daga Office! ". Hassana fita ta yi batare da ta k'ara cewa ko mai ba, Hassana na fita ta nufi Office d'in Manager ".manager na zaune Hassana tai mai nocrking. Izinin shiga manager ya ba Hassana. Hassana shiga ta yi,Hassana cikin girmamawa ta gaida manager. Manager cikin sakin fuska ya amsa ma Hassana, ya ce, "Hassana lafiya dai ko? ". Hassana kamar zata yi kuka ta ce, "Manager supervisor ta dakatar da ni aiki". Manager cikin tsoro ya d'aga kai yana kallan Hassana. Shiru manager ya yi na d'an wani lokaci sannan ya kalli Hassana ya ce, "me kika yi mata? ". Hassana cikin sanyin muryarta, ta ce, "Banzo aiki ba kwana uku, bani da kud'in napep, ko yauwa ak'asa nazo". Shiru manager ya yi, sannan ya ciro kud'i yaba Hassana ya ce, "Hassana amshi kud'innan kinji sai ki amfani da su, ki yi hak'uri kinji naso kiyi aiki anan, tom amma inda haka ya faru sai dai hak'uri ". Hassana amsa ta yi taima manager godiya jin abinda ya ce, ta fita daga Office d'in. Hassana na ta fito daga Office d'in manager ta had'u da staff d'in da ta bata sak'on supervisor na kiranta. Staff d'in cikin tausayama Hassana ta k'araso inda Hassana ta ke, ta ce, ta koreki ko? ". Kai Hassana ta d'aga mata ta ce, " Ta kore ni, na yi ma manager ma magana ma ko zai sa baki, amma ya ce min inyi hak'uri ". staff d'in kallan Hassana ta yi ranta ad'an bace, ta ce, "Ni da nasan zaki gurinsama da na hanaki, ai indai supervisor ta yanke hukunci bai iya yin komai, sai dai ya baka hak'uri bai iya sab'a maganarta". Hassana sallama ta yi ma staff d'in ta tafi dan maganar ma da kyar ta ke yinta. Cikin kud'in da manager ya ba Hassana ta hau napep ta koma gidansu Oga Habib, duk da zuciyarta cike ta je da bargabar komawa gidan, in da yanzu tabar aiki ak'ark'ashin su, haka nan Hassana ta koma inda bata da yadda zata yi.Jimmai cikin mamaki ta ke kallan Hassana ganin Hassana ta dawo gida yanzu.Jimmai k'arasawa inda Hassana ta ke ta yi, ta ce, "Hassana lafiya kuwa naganki kin dawo? ". "Supervisor ta koran aiki". Jimmai ta fe k'irji ta yi tana salati, ta ce, "manager kuma ya sani? ". "Eh ya sani, wai budurwarsa ce ba ya musu da abinda ta ce, inji wata staff". Jimmai shiru ta yi, tana jimamin abinda ya faru. Hassana kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Jimmai tom kina ganin babu damuwa inci gaba da jama gidannan yanzu bana aiki ak'ark'ashin su? ". Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, "Tom nima dai ban sani ba, amma dai yau Hajiya turai zata dawo ai, shiyasama kikaga ko ina

Please Login or Register in order to submit comment