Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

katse kiran.
Bilya ko lokacin da Habib ya kira shi tashinshi a bacci kenan, hakan yasa Cikin sauri Bilya ya shirya yaja motar shi yafita. Da safe da kuma dare Habib tea kawai ya ke iya sha, sai wainar k'wai. Bilya na shiga Sanat yughurt , ana sauke Hassana ita kuma a napep. Bilya kallan Hassana ya yi, ya ce "Yauwa Hassana dan Allah amshi break fast d'in nan ki kai Office d'in Oga Habib. Hassana tsayawa ta yi tana kallan Bilya ta ce, "Oga Bilya dan Allah ka kaimai da kanka Allah bana son shiga office d'in Oga Habib. Bilya mik'ama Hassana ya yi, ya ce, "Hassana haka nan zakiyi Hak'uri ki amsa, tun d'azu Farida ke kirana in zo in kawota Sanat yughurt, Wallahi na manta sham sai yanzu na tuna, tom shine ke so inje in d'akkota, yanzu idan na shiga office d'in Oga Habib zai iya sani wani abun, ba zai barni in fito yanzu ba, dan Allah ki amsa ki kai mai". Hassana amsa ta yi ta ce, "Haba Oga Bilya, ai Umarni zaka bani na aikata ba sai ka rok'eniba". Dariya Bilya ya yi ya ce, "Bakomai Hassana girmanki ne, bari in je in dawo dama Wallahi ina son wata magana mai mahimmanci da ke". Hassana itama murmushin ta yi tace, "Tom Oga Bilya sai kadawo". Bilya tafiya ya yi Hassana kuma tana rik'e da break fast d'in Habib ta nufi office d'in shi".


Hassana nocking ta yi. Tad'an dad'e atsaye tana nocking sannan Habib ya bata izinin shiga. Hassana na zuwa Cikin girmama ta ce, "Barka da safiya Oga Habib ga shi inji Oga Bilya, ya ce yanzu zai dawo". Habib batare da ya amsa gaisuwar Hassana ba, dan zuwa yanzu sosai ya ke jin ciwo acikin jikin shi. Habib kallan Hassana ya yi, sai zuwa can ya tashi kamar zai amshi jug d'in hannun Hassana, sai kuma ya fasa, ya dafe kanshi da hannun shi guda d'aya ya mik'ama Hassana d'ayan hannun nashi, yana rin tse ido, ya ce da k'arfi dan har wanda ke waje sai da yaji. "Ahhhh rik'e min hannunaaaa!!? Habib ya fad'i maganar da k'arfi yana mik'ama Hassana hannun shi. Hassana sosai ta tsorata, Hakan yasa ta saki jug d'in hannunta ta bud'e k'ofar Office d'in zata fita. Sai dai ina ta makara kafin ta bud'e kofar sai dai taji anjawo hannunta da k'arfi.....................



A'A, WAI ME KE FARUWA NE?, NI FA BANGANEBA.


NASAN WASINKU DA DAMA ZASU CE HAKA.


KARKU DAMU ZAKU GANE.


LABARIN YANZUN YAFARAπŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»πŸ’ƒπŸ»


BANDA LAFIYA DAN ALLAH INA BUK'ATAR ADDU'ARKU.


COMMENT
&
SHERE
PLEASE πŸ™

πŸ“š OGA HABIB πŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI ( Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

My Facebook group :Fadila Sani.
https://m.facebook.com/groups/565235401564189/
πŸƒ Ibnul-Qayyim (Allah Yayi masa Rahama) yana cewa: *"Lalle damuwa, baΖ™in ciki da qunci suna faruwa ne ta dalilai guda biyu: _Daya daga cikinsu shine son duniya da nemanta (ta kowace hanya), na biyu kuma rashin aikata ayyukan kwarai da (kyautata) ibada"_*
πŸ“’ [Iddatus-Saabireen - P. 265].
Allah kasa mu dace.


SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN πŸ‘‡πŸ»
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA ZA A FARA POSTING.
KI GARZA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT πŸ‘‡πŸ»
08142904255.


Shafi na 18&19.



Hassana sosai ta tsorata, hakan yasa ta saki jug d'in hannunta ta bud'e k'ofar Office d'in zata fita, sai dai ina ta makara kafin ta bud'e k'ofar sai dai taji anjawo hannunta da k'arfi, an dawo da ita baya. Hassana cikin tsoro ta d'aga kai tana kallan Habib".

Habib ko rik'e hannun Hassana ya yi da k'arfi da d'ayan hannunsa, d'ayan hannun kuma ya dafe kan shi da shi.
Hassana da Habib kusan atare suka yi k'ara wadda duk kusan wanda ke cikin Sanat Company babu wanda bai ji k'ararnan ba".

Ita Hassana k'arar tsoran yanayin da taga Habib ne ta yi, shi kuma Habib ta sabon yanayin da yatsinci kan shi cike ce. Hassana cikin tsoro ta kalli Habib tana cewa, "Wayyo hannuna Oga Habib dan Allah ka yi hak'uri kasakanmin hannu". Hassana ganin Habib kamar ba cikin hanyyacin shi ya ke ba, kuma ya rik'e hannunta katakam, ga zafin rik'on da ya yi mata take ji. Hakan yasa Hassana ta dage sai ihu ta ke".

Dai-dai likacin ne kuma Bilya da Farida suka shigo Sanat company. Bilya da Farida da saurinsa suka k'arasa shiga cikin Sanat company. Inda suke jiyo ihun suka nufa. Dai-dai lokacin shima Manager ya fito daga Office d'in shi da sauri ya nufi na Oga Habib dan anan ya ke jiyo sautin k'arar. Atak'aice dai duk wani ma'aikacin da ke cikin Sanat yughurt, da saurinsa ya ke nufa inda ya ke jin alamun k'arar mutum".

Manager da Bilya kusan atare suka turo k'ofar office d'in Oga Habib, inda Farida da Billy suka mara masu baya. Bilya cikin tashin hankali ya nufi inda Habib ya ke, ganin yarik'e hannun Hassana kata kam, yak'i saki, sai wasu magan-ganu da yake yi kad'an-kad'an, bazaka iya jin me yake cewa ba, kodan ihun da Hassana ta ke yine".

Bilya cikin girmama da fargabar ganin yanayin da yaga Habib, ya ce, "Oga Habib lafiya karik'e mata hannu?, idan laifi taima dan Allah ka yi hak'uri ". Habib kallan Bilya ya yi yana zazzare ido. Bilya kallan Habib ya kuma yi da kyau, dan sosai abinda Habib ya yi ya ke naiman d'aure mai kai, dan asanin Bilya mata ma masu aji Habib bai kulaba bare kuma Hassana da ke a k'ark'ashinshi. Sannan idan ya lura da kyau kamar Habib bacikin hayyacin shi ya ke ba. Hakan yasa Bilya kama hannun Habib da niyyar fusge hannun Hassana.
Wani duka Habib ya ke ma Bilya a wuya, wanda sai da Bilya ya yi k'ara. Bilya da sauri ya matsa yana kallan Habib. Bilya manager ya kalla yana dafe gefan wuyan shi inda Habib ya nusai, yace, "Manager lafiyar Oga Habib k'alau kuwa? ". Manager kallan Bilya ya yi, ya ce, "Nima abinda nake tunani kenan, amma bari mugani".

Manager matsawa ya yi kusa da Habib ya ce, "M. D, dan Allah ka yi hak'uri idan laifi taima, kasakar mata hannu yau zamu koreta daga ma'aikatar nan baki d'aya ". manager ganin Habib ya yi banza da shi yana kallan shi, hakan yasa ya kama hannun Habib da niyyar b'amb'are na Hassana".

Habib duka ya kawo ma manager.
Allah ya tai maki manager ya kauce da sauri. Tun daga nan fa kowa ya fara baya-baya.
Hassana ko ganin haka suna nai man fita subarta daga ita sai Habib, ya sa ta fasa kuka tana cewa, "Wayyo Allah Oga Bilya dan Allah karku tafi, manager dan Allah kuzo ku taimaka min".

Bilya kallan manager ya yi dadamuwa yace, manager akwai damuwafa, Wallahi Oga Habib baida Lafiya, dan kai kasan wannan abinda da yake yi ba halinsa bane, idan zaka kalli idon shima kamar baya cikin hayyacinsa". Manager numfasawa ya yi sannan ya ce, "Wallahi maganarka hakane, nima abinda nake tunani kenan, yanzu ya kake ganin za ai? ". Shiru Bilya ya yi, Sannan ya ce, "Ni gani nake kawai mu kwaci yarinyar nan daga hannun shi, mu kai shi gida, ala bashi sai a kira likitan k'wak'walwa ya duba shi". "Eh haka za ayi". Cewar manager. Manager wasu k'arfafan samari da ke aiki gurin guda biyu yasa su tai maka masu".

Bilya da manager ne suka yi jarimtar rik'e Oga Habib, sannan sauran staff d'in guda biyu suka k'wace hannun Hassana daga hannun Oga Habib da kyar. Sosai su manager suka sha wahala wajan sa Oga Habib a mota. Sannan Bilya ya shiga ya tuk'a motar da manager da Faruq kuma suka rik'e Oga Habib. Ahaka dai suka samu suka k'arasa gidansu Oga Habib".

Hassana ko bayan ta samu an kwaceta da kyar daga hannun Oga Habib guri ta zamu tazauna tana sare hawayanta, da kuma al'ajabin abinda yasa mu Habib. Hassana na nan zaune supervisor tazo tana mata wani irin kallo mai ma'anoni da dama. Billy kallan Hassana ta yi tace, "Hassana ki ke ko?, sannu Hassana gaskiya kinyi k'okari, sai dai ina baki shawar duk abinda ki kaima Oga Habib kafin Hajiyarsa ta dawo ki yi gaggawar warware shi". Billy na fad'in haka ta juya ta tafi, tabar Hassana nan tsaye da baki sake tana kallanta".

Hassana maganar zuci tafara, "Tom wai me supervisor ta ke nufi da duk abinda ta yi ma Oga Habib, tom ita mai tai me?, me zata yi gaggawar warware wa?". Nan dai Hassana ta gama tunaninta bata gane takan zancan Billy ba ta tashi".

Can gidan su Oga Habib ko, da kyar su manager su kama Oga Habib suka shigar dashi d'aki, sai dai suna sashi suka rufe d'akin.
Bilya hankalin shi ta she ya ke kallan manager ya ce, "Manager karfa ace Oga Habib hauka ya ke, dan abin ya tadamin hankali, kalli yadda ya ke bige-bige! "."tom Wallahi nima haka ne tunani, dan bisaga alamu wannan abinda ya ke kamar hauka ne, tom yanzu in ma munkira likita taya zai duba shi ayarda ya ke haka d'innan? ". Cewar manager.
Shiru Bilya yi yi sannan ya ce, "Gasakiya na fara tunanin kiran Hajiyarsa in fad'i mata halinda Oga Habib ya ke ciki, kasan hausawa sun ce da zafi-zafi ake dukan k'arfe, gara ai gaggawar fad'a mata, in dai Hajiya ce a yauma zaka iya ganinta, ko gobe da wuri".

Haka ko akai, Bilya kiran Hajiya Turai ya yi yi, Bayan sun gaisa ne ya ce," Hajiya a kwai damuwa fa, Oga Habib bashi da lafiya, kuma gaskiya yana yin ciwan yana buk'atar ki zo kusa da sauri". Hajiya Turai shiru ta yi , sannan cikin damuwa ta ce, "Bakomai Bilya ganinan zuwa, idan na sauka idan nasamu ticket zan juyo yau". Hajiya kamar yadda ta ce haka akai, tana sauka jirgi ta nemi ticket d'in Nigeria Allah ya te maketa ta kuma samu".

K'arfe sha biyu na dare, jirginsu Hajiya Turai ya sauka. Bilya ne ya je d'akko Hajiya Turai. Hajiya Turai na issowa ta kalli Bilya cikin tsantsar damuwa, ta ce, "Bilya kai ni in ganshi". Bilya cikin lallashi ya kalli Hajiya Turai ya ce, "ki yi hak'uri Hajiya yanzu nasan k'ila ya samu bacci zuwa gobe sai ki ganshi". Hajiya Turai cikin d'aga murya ta ce, "Bilya kana nufin in kwanta in yi bacci banga halinda Habib ya ke ba, kai yanzu kana ganin zan iya bacci batare da na duba jikin Habib ba? ". Shiru Billy ya yi, sannan ya ce, "Hajiya ki yi hak'uri, Wallahi bazai yuwuba ne ki ganshi, ki dai bari sai goban"."You are very stupid, Bilya ko kana hauka ne!, ko-ko wani abinne ya sa mai kuke b'oyemin!!? ". Hajiya Turai ta idasa maganar kamar zata yi kuka. Sannan ta ci gaba da cewa, "Bilya wai baku kira Family doctor mu bane ya duba shi? ".Bilya ganin Hajiya Turai tana nai man rud'ewa ya sa, Bilya cikin sanyin murya mai kwantar da hankali, ya ce, "Hajiya ki yi hak'uri, ina mai bak'in cikin sanar da ke halin da Oga Habib ya ke ayanzu haka, Hajiya Wallahi da kyar muka samu daga Sanat Company muka kawo shi gida, ayanzu haka maganar da na ke miki babu mai iya shiga inda Oga Habib ya ke, amma ban sani ba ko inda ke Mahaifiya ce zaki iya ganin shi". Hajiya Turai kuka ta fasa, ta ce, "Innalilahi'wa inna'ilaihirraji'un , Bilya muje inga Halinda ya ke, dan Allah Bilya muje ka kaini". Hajiya Turai hanyar part d'in Habib ta yi cikin tashin hankali ta na goge hawan da ke zubar mata".

Bilya tsayawa ya yi yana jiran Hajiya Turai ta shiga.
Hajiya Turai ko na zuwa ta bud'e kofar ta afka. Sai dai kwance ta iske Habib yana bacci ya yi kaca-kaca da d'akin. Hajiya Turai zuk'unnawa ta yi tana kuka kad'an-kad'an gudin karta tada Habib daga bacci.
Bilya jin Hajiya Turai shiru, ya sa ya shiga d'akin, cikin damuwa Bilya ya kalli Hajiya Turai dan sosai ta bashi tausai, hakan yasa Bilya cikin damuwa ya kamo hannun Hajiya Turai, ya ce, "Ki yi hak'uri Hajiya kizo muje ki kwanta ki huta karki tada shi".

Hajiya Turai tashi ta yi tabi bayan Bilya tana goge hawayanta, bayan sun fita ne, Hajiya Turai ta kalli Bilya ta ce, "Bilya dan Allah ko zaka koma ka kwana da shi? ". Shiru Billy ya yi sannan ya kalli Hajiya Turai, cikin taushin murya ya ce, "Hajiya Wallahi ko ke dan Oga Habib na bacci ne kika samu ganinshi, amma Wallahi idan idon shii biyu bazaki tab'a iya shiga inda ya ke ba, kwana wajan shi da akwai had'ari". Hajiya Turai tana kuka ta kalli Bilya ta ce, "Bilya kana nufin Habib duka yake?, idan haka ne kana son cemin Habib hauka ya ke kenan? ". "Tom Hajiya bandai sani ba , amma dai tabbas Oga Habib duka ya ke". Hajiya Turai ta fiya tayi tana Kuka tashiga site d'inta".

Hajiya Turai adaran kusan zaune ta kwana, tsabar fargabar abinda ke damun Habib. Bayan Hajiya Turai ta Idar da Sallar asuba ne ta tashi ta shiga room d'in da Farida ta ke kwana, dan taga alamar Farida bata san ta dawo ba. Sai dai maganar da Hajiya Turai ta ji Farida na yi ne yasa ta tsaya.
Hajiya Turai tsayawa ta yi cikin furgici da gigin jin abinda Farida ta ke cewa, "Mommy Wallahi na so zuwa Office d'in nashi kafin ciwan ya riskeshi, amma sai drivern gidan ya yi min shiririta, ni yanzu abinda ke damuna shikenan yanzu babu yadda za ai yarinyar da yafarka ya gani shikenan da ita zai rik'a yadda ke nan? ". Daga can b'angaran na ji tace, "Haba Farida me yasa tun da kika tabbata ya sha tea d'in ka yadda kika rik'a nesa da shi?, bacin kinajin abinda malam mai buzu ya ce miki, ko ajiyan Farida sai da nakiraki nace miki karki yadda ki nesa da Habib, tahakanne zamu zasu abinda muke nema cikin sauki". Farida shiru ta yi sannan ta ce, "Mommy ya zanyi dan Allah? ". Daga can b'angaran aka ce, "Farida kina jina ko? "? "Eh Mommy inaji". "Yanzu Hajiya Turai ta dawo gidanne? ". Farida cikin tabbarwa inda batasan da dawowar Hajiya Turai ba, ta ce, "A'a Mommy ina tunanin yau zata dawo". "Ok, yasunan yarinyar da kika ce alokacinda ciwan ya same itace kusa da ita? ". Shiru Farida ta yi dan ita batatab'a ganin Hassana ba ma sai jiya da abin yafaru, hakan yasa, ta ce, "Mommy bansan sunan yarinyar ba, amma ina tunani a Company nin shi yarinyar ta ke aiki". "Shikenan ki yi k'ok'ari ki samomin sunan yarinyar". Nan Farida taima Mahaifiyarta sallama ta kashe kiran".

Hajiya Turai ko mutuwar tsaye ta yi, da ta gama jin duk abinda Farida ke cewa ita da Mahaifiyar. Daya ke Farida a Hans free ta sa wayar shi yasa Hajiya Turai taji duk abinda suka ce..........




TOfA WAI meke faruwa ne, nifa har yanzu bangane ba?????.


Karki damu ke dai kibini ahankali zaki gane😘😘😘😘😘



Dan Allah ayi hak'urin jina da akayi kwana biyu shiru, ina ba duk wani mai bibiyar littafin Oga Habib hak'uri, na jina shiru da aka yi kwana biyu, Allah Aimin uziri insha Allah haka bazai k'ara faruwa ba.

Masoya wa inda suka nuna min kulawa ta hanyar ganin text messsage d'in su nagodee, da masu kiran waya duk ina godiya sosaiπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»



COMMENT
&
SHERE
PLEASE πŸ™

πŸ“š OGA HABIB πŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy babuy).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

*☘️ADDU'A DAGA BAKIN ANNABI S.A.W.☘️*

_🩸Ya Allah Ina Neman Tsarinka Daga Sharrin Jina Da Ganina, Da Sharrin Harshe na, Da Sharrin Zucuya ta, Da Kuma Sharrin Sha'awa ta... Yana Nufin Tsiraicinsa.🩸_

Abu Dawud,Tirmizy Da Nasa'i Suka Rawaito Shi.

SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!
YAUNE NAKE FARIN CIKIN SANAR DA KU, MASHIYAR HAZIK'R MARUBUCIYAR NAN TAKU, WADDA TA SABA NISHA D'AN TARKU DA HAZIK'AN LITATTAFAN, IRINSU, :RAYUWAR GIDAN MU,JALILAH , SHAIRIN SO.TOM
YAU GATA TAFE DA WANI SABON LABARI WANDA YASHA BAMMA DA SAURAN, NASAN WASUN KU ZASU CE MIN HARDA SU JALILAH, DA SHAIRIN SO, TOM HADDA SU.TOM KUDUBI HAD'UWA DA TSARAWA NA LITTAFINTA MAI SUNA K'AWAYE, AMMA ARADU WANNAN LITTAFIN YA DOK'E SHI.
NA SAN MASOYAN LITTAFIN AUTAR MAMA, DAMA WA IN DA SUKE JIN LABARIN LITTAFANTA SUN K'OSA SUN MATSU DAN JIN SUNAN LITTAFIN.TOM GA SU NAN NAN πŸ‘‡πŸ»
K'ABILA CE! K'ABILA CE!! K'ABILA CE!!!
KU DAGA JIN SUNAN KUN SAN YAZO DA SABON SALO MAITAFIYA DA ZAMANI.
K'ABILA CE! :SABON LITTAFINE DA AKE POSTING.
KI GARZAYA KI RUGA DA GUDU DAN KI ZAMA D'AYA DAGA CIKIN MASU KARANTA K'ABILA CE!
WHATSAPP CONTACT πŸ‘‡πŸ»
08142904255.


Shafi na 20&21


Hajiya Turai zufa ce ke keto mata ko ta'ina , dan sosai abinda ta ji Farida na fad'a ya tada mata hankali, ya rud'ata, Hajiya Turai maganar zuciya ta fara, tana cewa, "Yanzu abinda kunnena suka jimin hakane kuwa?, Kai ina bazai yuwuba ace Hajiya Murja zata iya had'a baki da 'yarta su juya brain d'in Habib? ". Hajiya Turai zuciyarta ce ta bata amsa, da cewa, "Tom idan kince k'arya ne, abinda da kunnanki su ka jimiki fa? ". Shiru Hajiya Turai ta yi, sai zuwa can ta ce, "Tabbas abinda kunnena suka ji min hakane, tom amma meyasa Hajiya Murja zata juya k'wak'walwar Habib?, me Habib ya yi mata?, Sannan me Farida ta ke nufi da taso ace lokacinda lallurar ta samu Habib tana kusa dashi?, tasan da da'ita zai rik'a yarda?, me suke nufi da haka?, Sannan wata yarinya ce suke maganar lokacinda Habib ya farka da ita yayi tozali ?". Hajiya Turai dafe kanta tayi kamar zata sa kuka tace, "Wayyo Allah wa zai amsa min wa'innan tambayoyin?, Yallah ga Habib nan kai kasan dalilin shigar wannan lallura jikinshi Ya Allah kakawo mai sauk'i". Hajiya Turai fasa shiga d'akin Farida ta yi ta juya tana mai goge hawayan dake ambaliya cikin fuskarta. Hajiya Turai Bilya ta kira awaya, dan duk ma aikatan gidan mutum biyu ne Hajiya Turai ta yadda da su wa inda har ta ke naiman shawara agunsu, wato Bilya da Baba Lami.

Bilya na kwance tunanin halinda Habib ya ke Shikanshi kusan ya hana shi sakat. Bilya na awannan halinne kiran Hajiya Turai ya shigo wayar shi. Bilya cikin hanzari ya d'aga wayar, banji mai Hajiya Turai ta ce ba, sai dai naji Bilya ya ce, "Ok, Hajiya ganinan zuwa".

Bilya tashi ya yi ya nufi part d'in Hajiya Turai. Bilya zaune ya iske Hajiya Turai tana kuka. Cikin damuwa Bilya ya samu gu ya zauna, sannan cikin sanyi murya mai cike da rauni ya kalli Hajiya Turai ya ce,"Hajiya tabbas na san dole kishiga damuwa, tom amma ita damuwar ce babu maganin abinda zatayi mana, ki yi hak'uri kima Oga Habib addu'a, dan ayanzu addu'arki ya ke buk'ata , nasan zata taimaka mai sosai wajan rage mai halinda ya ke ciki".
Hajiya Turai da katawa ta yi daga kukan da ta keyi, ta d'ago tana kallan Bilya, Hajiya Turai cikin raunin murya mai kama da kuka ta ce, "Bilya ayanzu ba halinda Habib ya ke ciki ba nake ma kuka"HajiyaTurai shiru ta yi ta da kata nad'an wani lokaci, sannan ta ce, "Bilya d'akin Farida nayi sammakon shiga da niyyar in sanar da ita dawowata, amma sai kunnuwana suka ji min wasu zantuka da ta ke yi, tabbas Bilya da ace wanine ya fad'a min abinda kunnena yaji min yau Farida na fad'a Wallahi da bazan yarda ba".Hajiya Turai shiru ta yi sannan ta ce, "Bilya alokacinda lallurannan ta samu Habib wata yarinya ce kusa da shi? ". Bilya cikin mamaki ya kalli Hajiya Turai jin abinda ta ce, amma sai ya waske kawai, ya ce, "Hajiya Hassana ce yarinyar da ke aiki Sanat company ta ke kwana gidannan". "Me ya shigar da ita Office d'in Habib?. "
" Eh tom gaskiya ban sani ba". Hajiya Turai kallan Bilya ta yi ta ce, "Kaje yanzu ka tahomin da yarinyar ina son ganinta". Bilya kallan Hajiya Turai ya yi zai yi magana ta d'aga mai hannu. Hakan yasa Bilya ya juya ya tafi yana tunanin lafiya Hajiya Turai ke son ganin Hassana, can wata zuciyar ta ce mai, "Tom ko dai maganar da tace taji, cemata akai ana zargin Hassana ne, ita taima Oga Habib wani abun".Haka dai Bilya ya idasa b'angaran masu aikin gidan yana tunani kala-kala, shi dai addu'ar shi d'aya in ma wani sharinne aka k'ullama Hassana Allah ya kub'utar da ita. Bilya Jimmai ya gani tana shara. Kallanta ya yi, ya ce, "Hassana fa? ". "Tana ciki Oga Bilya". "Ki ce mata Hajiyar naiman ta yanzu, tazo yanzu". Bilya na fad'in haka ya juya ya tafi".

Jimmai kuma barin sharar ta yi ta shiga ta kira Hassana. Lokacin Hassana na kwance tana bacci, Jimmai ta bubbuga ta ta ce, "Hassana ki tashi Hajiyar Oga Habib na son ganinki yanzu". Hassana tashi ta yi tana kallan Jimmai ta ce, "Jimmai lafiya dai ko? ". "Tom nima dai bansani ba amma ki je kiji". Hassana tashi ta yi ta sa Hijab d'in Jimmai ta tafi kiran da Hajiya ke mata, zuciyarta na cike da fargaban kiran".

Hassana sallama ta yi, tana jiran abata izinin shiga.
Daga cikin falon Bilya ya ce, "Hassana ki shigo mana". Hassana shiga ta yi, ta zuk'unna can gefa ta gaida Hajiyar Habib. HajiyaTurai ba tare da ta amsa gaisuwar da Hassana tai mata ba, ta kalli Hassana ta ce, "Hassana tambayarki na ke son yi, kuma ina so kifad'amin gaskiya? ". Hassana kallan Hajiya Turai ta yi gabanta na fad'uwa ta ce, "Inaji Hajiya, kuma insha Allah zan fad'amiki gaskiya". Hajiya Turai, kallan Hassana ta yi na second's sanan ta ce, "Watanki nawa da fara aiki a Sanat yughurt? ". "Wata na biyu na ke Hajiya". Cewar Hassanan. "Ok, alokacinda lallurar nan ta samu Habib ance min kina Office d'in shi, hakane? ". Wata irin fad'uwar gabace ta samu Hassana dan sai maganar Billy ta dawo mata farko da ta ce mata, "Hassana ki yi gaggawar warware duk abinda ki kaima Oga Habib tun kafin Hajiyarsa ta dawo".

Bilya ne ya kalli Hassana ganin ta fad'a kogon tunani, ya ce, "Hassana ke fa Hajiya ke saurare".
Hassana kallan Hajiya Turai ta yi, sannan cikin sanyin murya ta ce, "Eh Hajiya inanan". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Me yashigar da ke Office d'in shi alokacin?". Hassana Bilya ta nuna ma Hajiya Turai ta ce, "Hajiya Oga Bilya ne yaban ruwan tea in kaime". shiru Hajiya Turai ta yi, dan tabbas idan bata mantaba taji Hajiya Murja

Please Login or Register in order to submit comment