Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin sanyin murya ta ce, "laa Mommy ki ce, bari in bud'e miki". Hajiya Turai da katar da Hassana ta yi ta ce, "A'a my daughter bari basai na shigoba, nazo ne in ganku, inji ya kuka tashi". Hassana cikin girmama Hajiya Turai ta ce, "A'a Mommy dan Allah ki shigo". Hajiya Turai murmushi ta yi tace, "My daughter so kike yau in kasa bacci, dan wujijjigawar da yayi min rannan har yanzu ina jinta ajikina, dan haka barni kawai ba saina shigoba". "Mommy Allah naga kamar ya rage, dan ko yau da Baba Lami ta shigo kawo abin breakfast naga bai ce zai bita ba, ki shigo ai ina nan". Hajiya Turai shahada ta yi ta ce ma Hassana tom bud'emin". Hassana bud'ema Hajiya Turai ta yi".


Habib ko da yake tsaye kusa da Hassana yana rik'e da hannunta yana ganin Hajiya Turai ta shigo ya yi kanta. Hassana da sauri ta jawo Habib ta ce, "Oga Habib Mommy ce fa?, kamanta ta ne, kabarta kaji? ". Habib mak'e kafad'a ya yi".


Hajiya Turai ko naganin haka ta ce, "My daughter rabu da shi bari in fita ". Hajiya Turai ta yi maganar kamar za tai kuka".

Hassana kai ta girgizama Hajiya Turai ta ce, "A'a Mommy dan Allah ki zauna babu abinda zai miki insha Allah ".

Hajiya Turai d'annesa da su Hassana ta zauna kan 1 seater. Hassana ma zama ta yi, kan 3 seater, Habib ma ya zauna kusa da Hassana".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Daughter ya jikin nashi kike gani tsakanin jiya da yau? ". "Tom da sauk'i inda naga kamar yanzu yarage cewa zai bugu duk wanda ya shigo sai dai hargagin zai bugun, inda kinga ko d'azu da Baba Lami ta shigo sai dai har gagin ya yi". Hajiya Turai cikin jin dad'i ta ce, "Alhamdulillah Allah ya kawo sauk'i gaba d'aya ". "Ameen ya Allah ". Cewar Hassana. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "My daughter inda naga alamun sauk'i yafara zuwa, inda gani har kusa da Habib bai min komai ba, abinda da bahaka ba, yanzu insha Allah nan da sati idan naga yanayin jikin zan je London, wajan aiki sun daman da kira, zan je ko sati d'aya inyi in dawo, yanzu baki da wata matsala ko? ". "Eh Mommy babu"."Ok, yau zanba Bilya kud'i ya sayo miii waya idanma kina buk'atar wani abun sai kikirani awaya, inda naga mutumin naki babarinki fita zai yi ba". Murmushi Hassana ta yi ta ce, "Tom Mommy nagode".


Hajiya Turai fita tayi tabar Hassana da Habib.Hassana na nan zaune tana tunanin yadda za tai tai wanka sai ta ji nocking d'in k'ofa, da yake tunda Hajiya Turai ta fita Hassana bata tashi ta rufe ba, yasa ta ce, "Shigo". Duk da bata san kowaye ba".

Jimmai ko da mamaki jin ance ta shigo ta shiga, tana mamakin wai yau ita ce zata shiga falon Oga Habib, Lallai wani abu sai ciwo, ammma in bahakaba waneni acewar Jimmai".


Jimmai ko ko da ta shiga d'annesa da Hassana ta tsaya tana k'arema falon kalo da jinjina had'uwa irin ta falon Habib".


Hassana ganin hankalin Jimmai gaba d'aya ya tafi a kallon falon ya sa, ta ce, "Barka da safiya sister Jimmai". Jimmai cikin jin kunya ta ce, "Hassana kingani kamar wata sakarya ko?, ina nan ina kallan tsaruwa ta falon Oga Habib, dama kayan da mukai da ke jiya zan siyo miki ne, na kawo miki".

Hassana cikin mamaki ta kalli Jimmai ta ce, "Kai dan Allah har kin sayo, amma gaskiya kinyi sauri". Jimmai mik'ama Hassana ledar kayan ta yi".


Hassana amsa ta yi ta bud'e tana gani, dogayan rigunane kala masu kyau, kala shida, sai riga da siket kala uku, sai da wando suma kala uku. Hassana kallan Jimmai ta yi tana jin dad'in kayan dan sosai su kai mata kyau, ta ce"Kai sister Jimmai amma gaskiya kayan sunyi min kyau sosai, nagode Allah ya saka da alkairi". Ameen Jimmai ta ce, sannan ta mik'ama Hassana sauran kud'in ta ce, "Ga sauran kud'in kirik'e a hannun ki". "A'a, ki bari kirik'e a hannunki". Jimmai tafiya ta yi da kud'in kamar yadda Hassana ta buk'ata".

Hassana ko har yamma tana nan zaune bata yi wanka ba,abin har ya fara damunta. Dan bawai a gidan ba, tun kan Hassana ta zo gidan su Oga Habib ta saba wankan safe, hakan ne yasa yau take jinta duk ba dad'i. Hassana kallan Habib ta yi da ya ke kusa da ita rik'e da hannunta yana wasa da shi ta ce, "Ayyah Oga Habib kaga ban iya daurewa in banyi wanka ba, dan Allah zaka zauna nan kajirani inyi wanka da sauri in dawo? ".Habib mak'ema Hassana kafad'a ya yi.Hassana kamar za tai kuka ta kuma cewa, "Dan Allah Oga Habib, inje zaka jirani? ". Yanzu Habib banza ya yi da Hassana ya kalleta kawai".

Hassana kuma ganin bai kuma d'aga mata kafad'a ba tashi ta yi, ta nufi toilet. Kusan tare da Habib suka isa toilet d'in. Hassana cikin jin haushin Habib d'in ta ke kallan shi, sannan ta ce, "Tom yi haka". Hassana ta rufe idonta tana numa Habib shima ya rufe".

Habib rufe idon shi ya yi kamar yadda yaga Hassana ta rufe".

Hassana ko naganin Habib ya rufe idon shi ta yi saurin cire doguwar rigar da je jikinta da bra da pant d'inta. Tana yi tana kallan Habib gudun karya bud'e idon shi. Hassama matsawa ta yi inda Shower ta ke ta kuna".


Habib ko najin sud'in fitar ruwa ya yi saurin bud'e idon shi".

Hassana ko ta juyama Habib baya, tana wanke jikinta da sauri da soso gudun kar Habib ya bud'e ido. Sai jin mutum ta yi bayanta yana k'ok'arin fusge sosan da take hannunta".

Hassana cikin rud'ewa ta juyo tana kallan Habib. Kafin ta yi wani abuma ya fusge sosan dake hannunta yana wanke jikinshi shima kamar yadda yaga tana yi".

Hassana lokaci d'aya dariya ta kamata ga b'akincin bud'e idon shi da ya yi ga kuma dariyar yadda ya ke wanke kayan jikinshi da soso shi ala dole wanka ya ke yi. Hassana baya ta kuma juyama Habib ta ci gaba da wankanta da soap ka d'ai ba soso".


Habib ma aje sosan ya yi , ya dawo d'aukar soap d'in yana gogawa a kayan shi kamar yadda yaga Hassana na gogawa ajikinta".


Hassana ko ganin Habib ya aje sosan d'auka ta yi ta ci gaba da wanke jikinta da shi"


Habib ganin ta d'auki sosan, shima aje soap d'in ya yi ya fusge sosan daga hannunta". Hassana wanke jikinta ta yi da ruwa ta d'aura towel d'in da ta gani agun an rataye".


Habib ma towel d'in ya d'akko shima ya d'aura akan kayan shi kamar yadda yaga Hassana ta yi".


Hassana ko kallan Habib ka wai ta yi tai murmushi ta barshi ta fita daga toilet d'in. Habib ma bayan Hassana ya bi shima".


Hassana dressing mirror d'in Habib ta je ta d'auki lotion d'in shi tana shafawa, Hassana jin k'amshin man ya yi yawa yasa ta kuma dubawa dan ta gani kodai turare ne bata sani ba. Dubawa ta yi taga mai ne".


Habib shima tatsa ya rik'ayi yana shafawa, kamar yadda yaga Hassana na yi".


Hassana d'aya daga cikin doguwar rigar da Jimmai ta siyo mata sata. Bayan Hassana ta gama shiryawa Habib ta kalla da ya ke tsaye yana kallanta kayan shi duk sun jik'e har d'iga suke. Hassana wajan kayan Habib ta je ta d'akko mai k'ana marasa nauyi ta kawo mai ta ce, "Oga Habib ga kayanka ka sa".


Habib kallan Hassana ya yi. Hassana tunanin Habib ba amsa zai yi ba da ta yi, yasa ta kama hannun Habib d'in ta zaunar da shi kan lover chair d'in bedroom d'in. Hassana rigar Habib da ke jik'e ta cire mai ta sa mai wata, sannan ta rufe idonta ta kama wandonma ta zare mai, ahaka dai da rintse ido Hassana ta sa ma Habib kaya ".


Hassana nagama shirya Habib aka kira sallar magriba. Toilet d'in ta koma ita da mak'ake mata d'inta suka yi alwallah, tazo ta shimfid'a sallahya ta tada sallah. Nan dai duk yadda tai Habib ya yi ahaka tai sallar. Tana idarwa Baba Lami ta kawo masu abincin dare. Hassana sai da tayi sallar Ishsha'i sannan ta tashi daga kan abin sallar".

Tuwan semo miyar kuka ta ji naman rago. Hassana hannu tasa tasa ma Habib ma nashi suka ci tare. Suna gamawa ta wankema Habib hannu itama ta wanke nata".


Dama Hassana ta sa da baccin wuri, suna gama cin abinci ba dad'ewa ta tashi ta nufi bedroom d'in Habib ta kwanta. Inda shima oganta ya mara mata baya, ya kwanta kusa da ita, 12:59Am Allah ya tai maki Hassana ta tashi ta ba Habib rubutun shi".


Washe gari Hassana bayan ankawo masu abin kari sun karya. Tashi ta yi takama rigar jikinta ta cire ta d'ora towel. Habib ma naganin haka shima ya kama tashi ya cire kamar yadda yaga Hassana ta yi. Tom da yake ita Hassana ba dogon wando gareta ba bare Habib yaga ta cire shima ya cire. Hassana toilet ta shiga Habib ya fita".


Wanka Hassana ta yi duk yadda ta yi Habib na yi kamar jiya ahaka dai suka gama wankan".


Wajan shama haka sukai duk yadda Hassana ta yi Habib na yi ahaka ya shafa mai, Hassana ta ciroma Habib kayan shi ta samai kamar jiya, itama ta sa cikin wa inda Jimmai ta siyo mata".


Hassana bayan ta shirya ta shirya Habib. Kallan Habib ta yi ta ce, "Tom Oga Habib yau Mommy za mu je mu gaida ". Hassana fita ta yi ta ja k'ofar ta rufe. Habib kuma kama hannun Hassana ya yi katam ya rik'e".


Ahaka Habib da Hassana suka jera suka nufi part d'in Hajiya Turai. Duk 'yan aikin gida da mamaki suke kallan Hassana, dan duk cikinsu ba kowa bane yasan Hassana na kula da Habib, bare kuma magar auran su banda Jimmai babu wanda yasan da maganar auran Hassana da Habib ba".


Hassana dai-dai zasu shiga site d'in Hajiya Turai sai ga Farida da zuwanta kenan gidan".

Farida cikin tashin hankali da damuwa ta ke kallan Hassana da hannunta ke cikin na Habib......



Idan kin karanta d'aure ki yi Comment Sister ๐Ÿค



Share
&
Comment please ๐Ÿ™.

๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA NA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Ayi hak'uri da wrong typing ina ciwan ido ne๐Ÿ‘๏ธ๐Ÿ‘๏ธ.



Shafi na 40 & 41.



Farida cikin tashin hankali da damuwa ta ke kallan Hassana da hannun ke cikin na Habib amak'ale.
Hassana ko da bata lura da Farida ba ta gaban Farida ta wuce, batare da ta lura da ita ba. Farida ko cikin jin zafi da haushi ta da kama Hassana tsawa, ta ce, "Ke wata irin sakarya ce!, kuma ubanwa yasa ki ki fito da Oga Habib!? ".

Hassana da kwatakwata bata lura da Farida ba, sai tsawarata ta ji, cikin tsoro ta juyo tana kallan Faridar, ta ce, "Ayyah Aunty Farida dan Allah ki yi hak'uri, Wallahi ban lura da ke bane". "Dama taya zaki lura dani, kanki narawa ke ga Amaryar Oga Habib ko?, Tom bari kiji Wallahi daga yau har uzuwa ranar da auran nan zai zo k'arshe karki yadda karki kuskura kik'ara fitowa da Oga Habib, idan kuma ba haka ba zan nuna miki ainihin kalata, dan haka ki mai dashi inda kika fito da shi sakarya kawai! ".

Hassana harga garanta bataji dad'in yadda Farida ke zaginta ba. Hassana kama hannun Habib ta yi suka juya".

Hajiya Turai ko da hayaniyar Farida ta sa ta fito, kallan Farida ta yi, tana kuma kallan bayan Hassana ta ke tafiya, ganin kamar gunta suka zo kuma ta ga sun juya, tabbas ko ba a fad'a mata ba tasan Farida ce ta koreta, inda taji yo hayaniyar fad'an Farida. Hajiya Turai kallan Farida ta yi, ta ce, "Farida ke da wa kike hayaniya haka? ". Farida cikin alamun ta ji haushin abinda Hassana tai ta ce, "Mommy wannan 'yar iyayin yarinyar ce mana, ta wani kama ta fito da Oga Habib ,kowa wama yasata". "Ok kiramin ita ". Cewar Hajiya Turai ".

Farida ko cikin b'acin ciki dajin haushi ta je kiran Hassana, dan ita a ganinta rainine kamarta ta je kiran Hassana. Farida tun kan tak'arasa inda Hassana ta ke ta ce, "Ke! ". Hassana tsayawa ta yi amma bata waigoba".

Farida k'arasowa inda Hassana ta ke ta yi, ta ce, "Lallai, kin isa, tom Mommy na kiranki, kuma Wallahi Kin dai ji kashai din da nai miki, kar in kuma ganin kin fito da Oga Habib , idan kuma ba haka ba, zaki gani! ".

Ita dai Hassana bata ce ma Farida ko mai ba, kama hannun Habib ta yi suka k'arasa inda Hajiya Turai ke tsaye".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter lafiya kika fito ke da Habib? ". Hassana cikin sanyin muryata ta ce, "Mommy munzo gaida ke ne? ". Hajiya Turai cikin nuna jin dad'in ta ta ce, "Kai, ka ce yau inada manyan bak'i tom ku shigo ciki".

Hassama ta na rike da hannun Habib suka Shiga tan k'ameman Falon Hajiya Turai.
Bayan Hassana ta zauna ne, ta gaida Hajiya Turai cikin grimamawa kamar yadda ta saba".

Hajiya Turai da sakin fuska ta amsa ma Hassana ta ce, "Lafiya lau daughter ya kike?, ya Habib da jikin da fatan ana ganin sauk'i ? ". "Eh Mommy da sauk'i, inda kinga yafara sakewa da mutane bakamar da ba". Hajiya Turai cikin jin dad'i ta ce, "Alhamdulillah Allah yak'aro sauk'i". "Ameen ya Allah ". Cewar Hassana".

Hajiya Turai shuru ta yi na 'yan second's, sannan ta kalli Hassana ta ce, "Daughter mai ya had'aki da Farida? ". Hassana cikin sanyin muryarta ta fara ba Hajiya Turai amsa kamar haka"fad'ata tai min wai kar in sake fitowa da Oga Habib ". Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ita ta sa kika koma da shi ko? ". "Eh Mommy ita ce". K'wafa Hajiya Turai ta yi, ta ce, "zata sani dan taga ina barinta ne".

Hajiya Turai kiran Maimuna ta yi ta ce ad'ora girgi yanzu, kuma tana buk'atar abinci mai dad'i dan acewarta tana da manyan bak'i ".

Hassana dai murmushi ta yi, jin Hajiya Turai na kiransu da manyan bak'i ".

B'angan Farida ko, cikin damuwa ta shiga d'akinta. Waya ta ciro ta kira Mahaifiyarta. Hajiya Murja na d'agawa Farida ta sa mata kuka. Hajiya Murja cikin damuwa ta ke tambayar Farida abinda ke damunta. Farida ko cikin kuka ta ce, "Haba Mommy taya zaki tambayan meke damuna bayan kinsan damuwata, yanzun haka fa, yarinyar nan na Falon Mommy ita da Oga Habib, bikiga yadda Mommy ke nan-nan da ita ba, har da sawa wai ai mata girki mai dad'i wai tana da manyan bak'i ". Daga can b'angaran Hajiya Murja ta ce, "Yauwa Farida kina jina ko?, ai abun yazo da sauk'i yanzu ki je kiba Balaraba maganin da Malam ya baki, ki ce nace ta zuba shi a girgin da za tai ma su". "Mommy ba fa Balaraba ta sa girkinba, Maimuna ta sa, amma ki bari duk yadda zanyi yanzi, yau d'in nan na bazasu k'etarema maganin nan ba, ke dai Mommy ki taya ni addu'a, Allah yaban nasara akansu". Daga can b'angaran Hajiya Murja ta ce, "Farida ai ke ke da nasara akansu, ke dai kamar yadda kika ce duk yadda zaki yi ki yi ki zuba masu maganin komai yazo k'arshe in samu hankalinkina ya kwanta". Nan dai su kai Sallama Farida tana mai k'ara tabbatarma Mahaifiyarta yau sai sunci maganin".


B'angaran su Hajiya Turai ko, Hajiya Turai sai jan Hassana da fira ta ke, cikin wayo kuma tana jin shirrin Hassana da wacece ita. Suna ahaka ne aka kira Sallar azahar ".

Hajiya Turai tashi ta yi taje tai alwallah, bayan ta yi alwallah ne ta kalli Hassana ta ce, "Daughter ki je kiyi alwallah ki zo ki yi sallah".

Hassana tashi ta yi Habib ya tashi shima zai fita". Hassana koma ta yi ta zauna ta kalli Habib ta ce, kamar mai yima k'aramin yaro wayau ta ce, "Oga Habib ka zauna nan kaji rani, in yi alwallah yanzu zan fito kaji? ". Habib mak'ema Hassana kafad'a ya yi".

Hajiya Turai ko abin dariya ma ya bata ganin Hassana wai ita wayo zata tai ma Habib. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter ku je tare, danni tsoro nake ma kibarni daga ni sai shi, ya wijijjigani".

Hassana kama hannun Habib ta yi suka nufi bedroom d'in Hajiya Turai, inda acan toilet d'in ya ke".

Hassana duk yadda ta yi haka Habib ke yi, ahaka dai asiririta suka gama alwallar. Hassana kwata-kwata bata luraba sai da suka gama alwallar taga yadda hannun rigar Habib ya jik'e sosai. Hassana kallan shi ta yi ta ce, "Oga Habib haka ka jik'e rigarka gashi ba yanzu zamu tafi ba". Hassana jan hannun shi ta yi suka fito".

Hajiya Turai ko da tun d'azu ta idarar da sallar ta, kallan Hassana ta yi tana murmushi ta ce, "Daughter hala Habib wasa ya yi da ruwa? ". Hassana sosa k'eya ta yi, ta ce, "Mommy Allah ban lura ba, kuma shi sai yace duk yadda nayi sai ya yi".

Murmushi Hajiya Turai ta yi, ta ba Hassana gu ta ce, "Tom zoki tada sallar ".

Hassana tada sallah ta yi, Habib ma yazo ya tsaya kusa da ita duk yadda ta yi ya yi, ahaka aka idar da salar".

Hassana na idarwa ya yi dai-dai da zuwan Maimuna ta sanar da Hajiya Turai ta gama girkin ta jera koma a darnin space".

Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana kin zoma Habib da maganin shi? ". "Mommy da yake banyi tunanin zamu dad'e ba, shiyasa amma bari in d'akko mai yanzu in dawo". Hassana tashi ta yi zata tafi Habib ma ya tashi ya bi bayanta. Hassana kallan shi ta yi ta juya zata tafi, ya rik'o hannunta shima ya bita".

Farida ko da ke alab'e tana son samun damar zuba maganin, tana ganin Hassana ta je site d'in Habib ta yi saurin nufar derning space d'in".

Farida cikin kwanciyar hankali ta san har ta gama Hassana baza dawo ba. Farida maganin ta d'akko da ke d'aure a zaninta ta zuba a abincin sosai,Sannan ta goge gurin yadda babu wata alama da zata nuna alamun barbad'an wani abu. Farida na gamawa ta yi sauri ta bargun, tana mai jin dad'in yau target d'in ta zai kama su Hassana".


Hassana maganin Habib ta d'akko ta canja mai riga inda tashi ta jik'e. Sanna ta kamo hannun Habib suka dawo Falon Hajiya Turai ".

Suna dawowa Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, "Daughter mu je kuci abinci".

Hasssana kama hannun Habib ta yi, suka tafi site d'in derning space. Sosai Hassana ta rud'e da tsaruwa irin ta gurin cin abinci. Zama ta yi , mutu minta ya zauna kusa da ta, dan sai da Hassana ta matso da chair d'in kusa da ita, dan tasan in ba haka ba zai iya cewa zai zona kanta".

Hajiya Turai wani abin ya bata mamaki wani ya bata dariya. Dan ko wajan cin abincin Hajiya Turai da ta zuba ma Habib nashi a plate ta mik'a mai, ko kallan shi bai yi ba , na Hassana da yaga tana ci yasa hannu shima ya kama ci".


Allah sarki haka su Hassana suka ci abincin da Farida ta zuba magani sosai batare da sanin su ba".

Farida da ke lab'e tana ganin sun fara cin abincin, ta fita tana rawa tana jin dad'in burinta ya gama cika gobe iwar haka.......... โœ๏ธ



Wayyo Hassana ta ci magani a abinci, Habib ma ya ci๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ.


Idan kin karanta d'aure ki yi Comment sister ๐Ÿค


Idan Allah yaban lafiya zaku ga posting gobe insha Allah, ayi managa da wannan.

Kwana biyu anji ni shiru, a yi haku ri banda lafiya ne.

Ina barar addu'a dan Allah idona ciwo ya ke๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ.


Comment
&
Share please ๐Ÿ™.

๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Ina ba duk wani mai bibiyar littafin Oga Habib hak'uri, naji na shiru da akayi kwana biyu, haka ya faru ne saka makon ciwan ido da nayi. Masu text massage da masu kiran waya nagode da nuna kulawarku gareni, nagode da kulawa sosai๐Ÿ‘๐Ÿป, Allah yabar zuminci๐Ÿค.

Masu comment na last page na gani kuma nagode sosai, a yi hak'urin rashin replying da ban samu yi ba๐Ÿ‘.



Shafi na 42&43.



Farida da ke lab'e tana ganin sun fara cin abincin ta fita, tana rawa tana jin dad'in burinta ya gama cika gobe iwar haka".

Hassana ko na aje spoon d'inta Habib ma ya cire hannunshi. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter ba dai kin k'oshi ba? ". Hassana kanta k'asa tana wasa da finger's d'in ta, ta ce, "Eh Mommy na k'oshi". Girgiza kai Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Garama Habib naga yaci sosai, amma ke cinnaki shiririta ne, dan haka yau kina nan har dare, yanzu dai nabarki k'ila wannan bai miki dad'i bane, daddare zan ga d'an abinda zaki kuma ci". Ita dai Hassana bata ce komai ba, murmushi tai ma Hajiya Turai ".

Hajiya Turai tashi ta yi, ta ce, "Tom ku tashi mu koma Falo".
Hassana tashi ta yi, Habib na rik'e da hannunta suka koma falon Hajiya Turai. Bayan sun zauna ne, Hajiya Turai ta kalli Hassana ta ce, "Daughter bari inyi baccin 30 min's in fito ko? ". "Tom Mommy, afito lafiya ".

Bayan shigar Hajiya Turai bedroom d'in ta bai fi da 20 min's ba, Hassana da hankakinta duk kusan ya tafi a american film d'in da ta ke kallo, duk da tun d'azu tana jin jikinta wani iri, tana shashsharewa ne kawai, da kuma film d'in ya kuma tai ma ka mata wajan kaudar da hankakinta a abinda ta ke ji. Hassana babu zato sai ji tai Habib ya jawota ta fad'o kan shi. Da sauri ta yunku'ura jata tashi daga kan shi, ya rik'e ta kata kam ya kwantar da kanshi cima kanta yana wani irin nishi kad'an-kad'an alamun magani ya fara aiki".

Hassana fara kokwawar k'wacewa daga ruk'un da Habib ya yi mata ta yi, amma ta kasa".

Habib ko da maganin boka keta k'ara ta siri ajikinsa, rigar jikinsa, ya cire ya wurgar gefe yana k'ok'arin yage taji kin Hassana".

Hassana ganin ciwan Habib d'in kamar irin na rannan, kuma a d'akin Hajiya Turai da rana, Hassana cikin ammafani da k'arfin da Allah ya bata ta yunk'ura ta tashi zata gudu, cikin rashin sa'a ta fad'i agurin. Tana ta fud'uwa Habib ya bita k'asan, ya jawo rigarta da k'arfi ya yaga wanda sai da rigar ta dire har k'asa".


Hassana cikin tashin hankali ta yi k'arar da bata san ta yi taba, tana kiran sunan Hajiya Turai, tana cewa, "Wayyo Mommy ki fito dan Allahhhhh!!! ".

Hajiya Turai cikin daddad'an baccin da ya kwasheta, ta jiyo ihun Hassana tana kiran ta. Hajiya Turai da sauri cikin tashin hankali yadda ta ji Hassana na ihu tana kiran ta ta nufo falon".


Hajiya Turai da bata san meke faruwa, ita dai atunaninta dukan mutane

Please Login or Register in order to submit comment