Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ya kamata Hassana su je, sun je, k'arfe 10:00Am Habib ya kalli Hassana ya ce, "Sanat ki shirya yan zu zamu wuce? ". Hassana dafa Habib ta yi kamar za tai kuka ta ce, "Dan Allah Oga Habib ka bari sai gobe mana". Habib da sosai ya daurema ya yi kwana d'a yan da ya yi, kallan Hassana ya yi, ya ce, " Dama nayi tunanin mu tafi da su Umma ne da Usaina suga in da kike, Allah basshi sai su zauna wajan Mommy har uzuwa lokacin da zaki haihu". Hassana da itama ta yi tunanin hakan, amma kuma ta kasa fad'ama Habib, Hassana cikin jin dad'i ta rungume Habib ta ce, "Sweetheart kamar ka shiga zuciyata nima nayi tunanin haka". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "tom muje asanar da su sai su shirya mu tai da wuri".


Habib zaune gaban Umma, ya ce, "Umma dama cewa nayi keda Usaina ko zaku shirya mu tafi tare kuga inda Hassana ta ke". Allah sarki itama dama ta yi tunanin hakan, hakan yasa batare da ja ba tace, "Tom ai shikenan sai mu shirya ".



Cikin k'ank'anin lokaci su Umma suka shirya, in da Hassana ta hana Usaina d'aukar kayan sawa ko d'aya ta ce ta bari ta rik'a sa nata, haka ko akai Usaina ban da kayan jikinta bata d'au ko d'aya ba".



K'arfe Biyar na yamma suka sauka. Wato su Umma mutuwar tsaye su kayi lokacin da suka ga gidan da Habib ya shigar da su".



Haka suka shiga Falon Hassana,Habib kuma ya shige ciki. Usaina da ta kasa daurewa kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana dama a irin gidan nan kike rayuwa?, gaskiya Hassana kin ji dad'i, kin ga ni son zuciya ya ja min na zama k'aramar bazawara". "Kibar tuna abin da ya wuce Usaina haka Allah ya k'addara". Cewar Hassana".


Habib hajiyar sa ya kira ya ce ta turomai Maimuna tai masu girki dan Hassana bata iyawa ta gaji. Aiko haka akai Maimuna ce ta zo tai masu girki. Suna nan zaune suna hira Maimuna ta zo ta Sanar da Hassana ta gama. Hassana kallan Umma ta yi, ta ce, "Umma muje muci abinci".


Haka suka ci abincin su suka gama. Koda lokacin kwanciya ya yi Hassana side d'in ta ta bar masu ta tafi wajan Habib ta kwana".


Yau kwana nan su Umma uku kenan da zuwa. Habib ya zo zai gaida Umma, bayan sun gama gaisawa Umma ta kallai ta ce, "Yau she zamu tafi ne? ". Habib cikin girmama Umma dan shi ya na mata Kallan mahaifiyar Hassana ne, inda ita ta shayar da Hassana, ya ce, "Umma dama yau Mahaifiyata zata dawo, idan ta dawo zaki koma wajan ta da zama ne, idan Hassana ta haihu sai ku tafi".
Umma k'in yarda da haka tai da kyar dai Habib ya samu ta yarda, dama Umma tana ma Hassana kallan kamar mai ciki, ashe ko haka ne".


Hajiya Turai na dawowa Habib ya d'auki Umma da su Hassana ma baki d'aya suka je. Wajan dawowa ne suka dawo suka bar Umma, inda suka dawo da Usaina, dan Hassana ta ce bata yarda ba sai dai Usaina ta dawo wajanta".


Billy ko tare da Manager suka zo har gidan Habib kawo ma Hassana invitation na biki. Hassana sosai ta yi mamakin ganin Billy amma kuma sai ta wuske, bayan manager ya ba Hassana Invitation card d'in, ya ce, "Madam dan Allah karfa kik'i zuwa". Hassana murmushi ta yi, ta ce, "insha Allah zan zo ".Billy kuma cikin kunya ta ce, "Dan Allah amaryar Oga Habib duk abin da ya faru ki yi hak'uri ki yafe min, Wallahi har da zigar Farida abubuwa da dama da nai miki". Hassana cikin nuna ba komai ta ce, "laa ni har nama manta karki ji koma Babu komai Wallahi".
Billy Sallama su kaima Hassana suka tafi".


Akwana atashi babu wuya awajan Allah cikin Hassana ya shiga watan haihu, amma cikin babu wani girman kirki. Yau tunda Hassana ta tashi ta ke jin ciwo ka d'an -kad'an tun tana daurewa har tasa Usaina ta kira mata Hajiya Turai".


Hajiya Turai ko najin kira wai Hassana bata da lafiya, suka tafi ita da Umma in sa suka biya ta wata private hospital suka tafi da wata nursing".


Cikin k'ank'anin lokaci Allah ya sauki Hassana ya bata yarinyar mace. Duk abin da ake Habib bai sani ba, har sai da Hassana ta haihu aka gyarata aka gyara jaririyar, sannan Hajiya Turai ta kira shi, yana d'agawa ta ce, "Habib gani agidan ka kazo yan zu, zamu yi magana".


Habib ko batare da tunanin ko mai ba, ya taho, yana zuwa Hajiya Turai ta tare da Baby a hannun ta, ta mik'a Habib, Habib ko kamar sakare ya amshi Baby yana kallanta yana kallan Hajiya Turai ya ce, "Mommy dan Allah ki min bayani ban gane ba, ina kika samu Baby? ". Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Nima ban santa ba". Habib da tunanin shi ya bashi Babyn shi ce, barin Hajiya Turai ya yi ya nufi bedroom d'in Hassana ".


Habib zau ne ya iske Hassana tana shan tea, ga Usaina kusa da ita. Habib kallan Usaina ya yi ya ce, "Usaina Mun samu Baby kenan? ". Usaina dariya ta yi, ta ce, Aikam dai Na samu Baby". Habib zama ya yi kusa da Hassana ya na kallanta ya ce, "Sanu ". Hassana turo baki ta yi ta ce, "ka yi lattin zuwa". Habib murmushi ya yi ya ce, "Ban sani na Wallahi Mommy ce ta kirani wai za muyi magana, ashe Baby na samu Mommy ta b'oye min". Hassana Murmushi ta yi sannan ta lek'a tana kallan fuskar Baby'n. Dan sai yan zu taga yarinyar".



Kwana atashi babu wuya yau kwana nan Hassana hud'u kenan da haihuwa. Billy ko tuni an amarce dan har tazo Barka, duk masu aiki Sanat Yoghurt babu wanda bai zo barka ba".


Hassana tana zaune fitowarta daga wanka kenan, Umma ce ke mata wanka. Hassana na nan zaune tana ba yarinyar mama Habib ya shigo. Habib zama ya yi yana amsar Yarinyar, kuka yarinyar ta yi jin ancire bakinta Maman. Habib mai da ta ya yi yana zare ido, ya ce"ki ce Baby'n ci gareta kamar Mommy'n ta". Hassana harara Habib ta yi, sannan ta mik'a mai yarinyar. Habib kallan Hassana ya yi ya ce, "Sanat dama cewa nayi ina son in sa ma Baby sunan Farida, amma kuma ban san yadda zaki d'auki abin ba". Hassana da ita burinta asama yarinyar sunan mamanta shiru ta yi, bata ce komai ba, Habib jin tayi shiru yasan hakan bai mata dad'i ba, hakan yasa ya ce, "Kin yi shiru Sanat? ". "Kasa mata". Hassana ta ba Habib amsa".


Habib tashi ya yi, ya bar Hassana nan".


Akwana atashi babu wuya yau ne suna. Duk su Hajiya Turai babu wanda ya san sunan da Habib ya sama yarinyar, kuma Habib ya hana su Bilya su gad'a dan sai da ya jama Bilya ma kunne ya ce, "Saura ka fad'i ma Usaina, dan yanzu Usaina da Bilya soyayya ake sosai dan babu wanda bai sani ba, har anyi ko mai ma, yan zu haka k'arshen watan nan ne bikin, Umma ko Habib ya bata side d'in shi na ki gidan Hajiya Turai ya ce taci gaba da zama anan. Hassana na haihuwa Umma da kanta taje kano ta fad'a ma 'Yan'uwan Hassana, hakan yasa yau gidan yake cike, dan duk kusan sun zo sunan".


Hassana ko dama tasan Farida Habib zai sa hakan yasa bata matsu da ta ji ba. Su Hajiya Turai na zaune har da Hassana Habib ya shigo. Hajiya Turai harara shi ta yi ta ce, "shine ka hana kowa ya fad'i sunan Baby ko, tom kai da kake son fad'a da kanka ai sai ka fad'a d'in".


Habib kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Mommy nasa ma Baby Hassana, Saboda dalili uku, na farko saboda sunan late Hassana Sister na, na biyu sabo da sunan Company'na, na uku Sabo da Sanat". Habib ya nuna Hassana da ke gefan Hajiya Turai".


Hajiya Turai cikin jin dad'in sunan da Habib ya sa ma Baby, ta ce, "Habib ka sama Baby nan sunan da nima shi nake buri in ce kasa". "Mommy na san burinki kenan shi yasa banyi tunanin shawara dake ba, nasan kema shine zab'in ki". Cewar Habib".


Hajiya Turai cikin jin dad'i ta d'aga hannunta sama ta ce, "Ya Allah ka albarkaci auran Habib da Hassana, Allah ka raya masu Hassana ka k'aro mu zuri'a masu albarka, Ya Allah ka k'aro mai bud'i mai yawa mai albarka, Ya Allah ka albarkaci Company shi SANAT YOGHURT".

Dukan su da "Ameen ". suka amsa. Hajiya Turai wayarta ta ciro tai ta masu pics kala-kala, tun Umma najin kunya har ta daure ta tsaya itama aka ci gaba da d'auka da ita. Hajiya Turai Habib da Hassana da Baby ta shiga tsakiyar su ta sa Usaina ta d'auke su✍️.




ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!!

Ya Allah nagode maka da kaban iko na gama Oga Habib lafiya. Ya Allah kuraran da ke cikin wannan littafi ya hurarrahman ya Allah ka yafe min ba dan halina ba, dan alfarmar anbi Muhammad (S. A. W).


Masu Comment's akan Oga Habib na gani kuma Wallahi naji dad'i, nagode sosai Allah yabar zuminci. Comment d'in ku ke k'aramin k'warin gwiywa. Kuna da yawa lissafo sunan ku ba zai yuwu ba, amma Wallahi duk wanda ya yi nagani nagode na kuma ji dad'i sosa.


Masu taya ni sharing na Oga Habib, nagani na kuma godee, kuma kuna da yawa sunan ku ba zai lissafu ba, amma ku sani nasan kunyi nakuma ji dad'i sosai Allah, nagode sosai Allah ya bar zuminci.



Sai mun had'u asabon book d'ina mai sun RAYUWAR HAIDAR. Ku nuna min k'auna ta hanyar shiyan RAYUWAR HAIDAR.


Dan Allah duk wanda na fad'ama rai ta hanyar rubuta Oga Habib ya yafe min. na yafe ma kowa.


Ina alfahari da ku masoyana aduk inda kuke, Allah kairin Allah ya isa GAREKU ✍️ . Fadila Sani Bakori ce
08063830828

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment