Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalinki, sai kin auri Habib koda ko abinda na mallaka zai k'are Wallahi sai kin aurai". Farida kwanciya ta yi jikin Mahaifiyarta cikin raunin murya ta ce, "Mommy kina ganin Hajiyar Oga Habib zata bari kuwa in auri Oga Habib? , ni fa 'yan kwanakin nan naga d'auke min kai ta ke, tabar zama dani ta yi fira kamar da, Wallahi mommy yanzu Hajiyar Oga Habib tafi ji da 'yar iskar yarinyar nan akaina". Farida ta idasa maganar tana kuka".


Hajiya Murja cikin damuwa ta kama Farida ta ce, "Yi hak'uri My sweet daughter kibar zubar da hawayanki kinji, Hajiya Turai kuma nina san tana sonki, kawai dai tashin hankalin ciwan Habib ne yasa kike ganin kamar tana shashshareki, ita kuma Hassana sunan ta kome?, tana janta ajikine ganin yadda ta ke kula mata da Habib, amma karki damu, auran ki da Habib babu bashi Wallahi, tashi mu tafi gun Malam kinga dare nak'arayi, danma babu wani nisa".


Hajiya Murja da Farida zaune agaban Malam mai biyan buk'ata dole. Bayan su Hajiya Murja sun gaida shine, Hajiya Murja ta ce, "Tom Malam ni dai ina d'aya daga cikin wa inda zasu yaba k'warewarka a aiki, dan kai min aiki ba d'aya ba, ba biyu ba, kuma duk naga biyan buk'ata, amma Malam wannan karan aikin yazu da matsala, dan har yanzu Yaron nan bai kusanci yarinyar nan ba, kuma gashi kace dole sai ya kusanceta shine makarin amintarshi da ita, tom amma Malam kaga yadda abin ya ke ta faruwa".
Tun da Hajiya Murja ta fara bayani Malam mai biyan buk'ata dole ya ke ta zane-zane a kaskon da ke gaban shi, har ta kai bayanin ta, sannan shima ya tsaya daga zane-zanan da ya ke yi, sannan zuwa can cikin kausassar murya ya ce, "Wannan karan bada gunkuba aka samu matsala, daga Mahaifiyar yaron ce, ita ta taimakama yarinyar , ta tai maketa, ta kub'utar da ita daga hannun shi, amma bacin haka babu abinda zai hana bai kusan ceta ba". Hajiya Murja cikin sanyayyar murya irin ta masu rok'o ta ce, "Malam dan Allah atai maka aimana wani abun dan Allah ".
Wani farin abu mai laushi ya mik'ama Hajiya Murja ya ce, "Ki barb'ata masu wannan a hanyar da zasu bi, ana so ne suk'etarashi, ke da kanki zaki ban labarin abinda ya faru".

Hajiya Murja amsar maganin ta yi, tai ma malam godiya sosai sannan suka tafi".

Bayan sun isa gida ne, Farida ta kalli Mahaifiyarta ta ce, "Mommy kin matsamin mun sake komawa gurin Malam mai biyan buk'ata dole na je, tom amma fa ki sani daga wannan Wallahi idan har Oga Habib bai kusanci yarinyar nan ba cikin wannan ritsin, tom tafiya Nigar fa ta kamamu, dan gobe zan yi abinda Malam ya ce, idan bai ba, jibi zamu tafi nijar dan haka kima fara shiri". "Karki damu Farida ai bana son Hajiya Turai ta zo ta iske yarinyar , kodan haka nima na dage, dan haka ba fata muke ba, idan har wannan karan ko ba ayi as'a ba shima, tom ashirye nake ki zo mu tafi Nijar d'in ".


Washe gari Farida da wuri ta yi sammakon komawa gidan Hajiya Turai dan zuwa ta ida aikinta, tana zuwa direct ta nufi part d'in Habib, dan acewarta gudin kar Hassana ta ki fitowa har falon zata shiga ta barbad'a masu, inda taga yanzu Habib ya bar duka".


Lokacinda Farida ta isa bakin k'ofar falon, dai-dai lokacin Hassana suka fito wanka ita da Habib, daga ita sai d'an k'aramin towel iya cinya, tana cikin tsane jikinta ta ji nocking, Hassana tunani ta fara tom waye, dan jiya Bilya ya tafi zaria, Hassana ta fiya ta yi ta ji waye dan tana tunanin ko Jimmmai ce. Hassana na zuwa bakin k'ofar ta tsaya ta ce, "Wacece..............โœ๏ธ.


Idan kin karanta d'aure ki yi Comment sister ๐Ÿค.



Share
&
Comment please ๐Ÿ™.

๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

*ISTIGHFARI TANA SANYA NUTSUWA A ZUCIYA TANA KAWO BIYAN BUKATU WAJEN UBANGIJI UWA UBA KUMA ISTIGHFARI TANA BADA TICKET NA ALJANNA DIRECT. ALLAH KASA MU DACE*




Shafi na 46&47.



Farida da ke tsaye bakin k'ofa sosai ta ji zafin maganar Hassana, wai ita ta ke cema wacece. Farida danne zuciyarta ta yi, dan cikar burinta ta ce, "Hassana bud'e nice". Hassana ta gane muryar Farida sarai, amma sai ta nuna ma Farida bata gane ba, ta ce, "Bangane kice ba?, kece wa? ". Farida da ranta yagama b'aci cikin zafin rai ta ce, "Farida ce ki bud'emin zaki wani tsaya kina min shirman tambayoyi Saboda kina ganin kamar kin isa! ". Hassana daga can ciki, ta ce, "Ayyah Aunty Farida wai ke ce?". Farida cikin jin haushi ta ce, "Ke ki bud'emin mana, ko bikiji abinda nace ba ne?". Shiru Hassana ta yi, tana tunanin ma fita, sannan ta ce, "Ayyah dan Allah ki yi hak'uri duk da bangane mai magana ba, amma Hajiya kafin ta tafi ta hana komawaye yashigo inda Oga Habib ya ke, amma idan kanji haushi ki yi hak'uri dan Allah, ba laifina bane". Farida da ke tsaye tana sauraran Hassana tsabar al'ajabi ne yahana ta magana, zuciyarta ce ta bata amsa da cewa, "ki yi hak'uri ki fad'a mata kece mana, wata k'ila bata gane ki bane". Farida maganar zuciyarta ta bi, ta za wani uban tsaki sannan ta ce, "Ke da Allah can sakarya kawai 'yar k'auye wadda bata gane mutane, tom Farida ce ta gidannan". Hassana sosai ta ji zafin zaginta da Farida ta yi, amma sai ta shareta ta juya takoma ciki ta barta agun tsaye, dan tasan ba alkairi bane zai kawo ta, dama kuma Hajiya Turai kafin ta tafi ta jama Hassana kunne koda wasa karta ce zata bud'ema Farida ta shiga part d'in Habib, idanma tai magana ta ji ita ce, karta amsa mata. Dama kuma itama Hassana ko da taji Farida ce ba niyyar bud'ewa tai ba, kuma sai Faridar ma ta b'ata mata rai".


Farida ko da ke tsaye tana jiran Hassana ta bud'e mata k'ofa ta ji shiru, Farida cikin d'aga murya ta bugi k'ofar ta ce"Ke wai bakya jine!? ". Nanma Farida shiru ta ji, hakan ya tabbatar mata da Hassana tama dad'e da tafiya ta barta tsaye tuntuni. Shiru Farida ta yi tana tunanin yadda zata shiga part d'in Habib ta barbad'a maganin. Farida matsawa ta yi daga jikin k'ofar kad'an ta kira Mahaifiyarta, Hajiya Murja a waya".


Farida cikin k'asa da Murya gudin kar wani ya ji, ta ce, "Hello Mommy kina jina? ". Daga can b'angaran, Hajiya Murja ta ce, "Eh Farida inajinki, ya akai kin barbad'a musu maganin ne? ". Daga b'angaran Farida ta ce, "A'a Mommy Yarinyar nan ta fara rainani wai na yi nocking d'in door d'in part d'in Oga Habib yanzu, shine da tazo take ce min wai Hajiya ta ce karta bud'ema koma waye, shine yanzu nake tunanin yadda zan yi in shiga , dan bisa ga alamuma yarinyar kamar bata fitowa yanzu tunda Hajiya ta tafi, bale in zuba mata maganin ak'ofar d'aki, shine Mommy naki raki ki fad'a min yadda zanyi".


Shiru Hajiya Murya ta yi, sannan ta ce, "ki kira Hajiya turan sai ki ce mata kin zone kina son gaida Habib, amma kinkira Hassana ta ke kome?, ta ce wai kin hana, ke kuma kina son ganin Habib kiga ya jikinshi ". Farida cikin jin dad'in shawarar da Mahaifiyarta ta bata, ta ce, "Yauwa Mommy bari in kashe in kira".


Farida katse kiran Mahaifiyarta ta yi, ta kira Hajiya Turai, amma bata d'aga ba. Farida sai da taima Hajiya Turai kira goma amma ko d'aya ba tai picking ba".

Hajiya Turai ko tana ganin kiran Farida da gangan tak'i d'agawa, dan ta tsani Farida Sosai, kawai dai ita Allah ya yo ta mai kawai cice sai kai ta cutarta ta. Hajiya Turai ganin Farida tak'i daina kiranta, kashe wayar ta yi gaba d'aya ".


Farida ko koda ta k'ara kiran Hajiya Turai ta ji wayar kashe ba tai tunanin komai ba, dan atunaninta suna wani programs d'in ne, kamar yadda ta tab'a fad'a mata, in dai kakira kaga bata d'aga ba tom suna bakin aiki ne. Hakan yasa Farida ba tai tunanin komai ba, tunaninta ya bata kawai Hajiya Turai na bakin aiki ne".


Farida Mahaifiyarta ta sake kira ta shaida mata ta kira Hajiya Turai bata d'aga ba, dan haka ta bata wata shawar". Hajiya Murya cema Farida ta yi,"Farida ki yi hak'uri zuwa anjima sai ki kuma kiran Hajiya Turai awaya, kin san in tana kan aiki bata amsa kira".


Farida tom kawai ta ce ma Mahaifiyarya ta kashe kiran, Farida d'akinta ta shiga ta kwanta tana ta malele kuwa , dan jinta ta ke indai ba Hassana ta bar gidan ba, tom bata da sauran na tsuwa, bakamar yau ba da Hassana ta kuma in gizata, dan ta yi ran tsuwar sai ta nuna ma Hassana ruwa ba tsaran kwando bane. Farida da ke kwance da sauri ta ta shi Saboda wani tunanin da yazo mata, hakan yasa ta tashi da sauri ta nufi site d'in worker's d'in gidan"..


Farida tsaye ta yi tana Waige-waige, tana nai man wadda tazo gani, cikin sa'a Farida ta hangota tana shanya. Farida da sauri ta k'arasa inda ta ke, cikin sakin fuska, Farida ta kalleta ta ce, Sannu ko? ". "Yauwa Aunty Farida Sannu". Farida cikin sakin fuska ba irin yadda ta saba yima worker's d'in magana ba, ta ce, "Yauwa dan Allah ya sunan ki". Jimmai da mamaki ya cika ta, tun zuwan Farida gurinta, ta ce, "Sunana Jummai". Farida cikin yaudara irin na wayayyun mata ta ce, "Wow nice name, tom dan Allah Jimmai wani tai mako zaki min, zan biyaki konawa ne, na zab'eki kimin wannan aikin ne, Saboda na lura duk gidan nan babu wadda ta fi kusanci da Hassana kamar ke, tom dan Allah Jimmai zaki min wani taimako ne, ba mai wani wuya ba ne".Farida maganin da ke jikin zaninta ta ciro ta mik'ama Jimmai ta ce, "Jimmai dan Allah zaki barbad'amin maganin nan ne, a part d'in Oga Habib". Jimmai ta ke tsoro ya kamata ta ja da baya tana mai mak'e hannunta ta k'i amsar maganin, dan sosai ta tsorata da jin abinda Farida ta ce".


Farida ko ganin Jimmai ta tsorata da maganin da ta ke mik'o mata, murmushi ta yi, ta ce, "Malama Jimmai karkiji komai ba maganin cutarwa bane, na san dai kin san ina son Oga Habib, dan nasan duk wanda yake agidan nan yasani, tom maganin nan da kike gani Jimmai bana cutarwa bane, idan ma k'awarki kike ji, itama ba cutar da ita maganin zai yi ba, ni nai miki alk'awari babu abinda zai samu k'awarki, na naimi kimin hakane dan nasan ke kad'ai ce agidan nan ayanzu zaki iya shiga part d'in Oga Habib kai tsaye, dan Allah ki tai makamin ki amsa".


Jimmai da ke tsaye al'ajabi ya isheta, amsar maganin ta yi tana ma jin tsoran karna cutarwa ne ya fara aiki akanta".


Dubu goma Farida taba Jimmai , ta ce, "Wannan ba biyanki nai ba, sai kin cika aiki sannan nima zan cika ki da abin arzik'i kala-kala".


Jimmai godiya taima Farida, ta amshi kud'in , Farida kuma ta wuce tana mai jin dad'in burinta ya kusa cika".


Jimmai ko tana ganin Farida ta wuce ta yi sauri ta shiga toilet ta jefa maganin, dan acewarta idan na zutarwa ne k'ilama ita zai fara cutarwa ita da take rik'e da shi. Jimmai sai da ta jefar da maganin sannan ta ji hankalinta ya kwanta. Murmushi ta yi, ta ce, "Aunty Farida baki da arzik'in da zaki ban kisa in zutar da Oga Habib bare kuma Hassana, ya Allah na godema da ka ba ma wannan baiwar taka zuwa guna, bata je inda zata bata ba burinta ya cika, Allah kaika san mai take nema da yarinyar nan, Allah kakareta daga shairinta, duk abinda zata mata Allah ka mai da mata aniyarta". Jimmai zama ta yi gun tana sake yima Hassana addu'a, akan Allah ya kareta daga shairin Farida."


WASHE GARI:
Farida da wuri ta yi sammakon zuwa gun Jimmai jin shiru bata ga Hassana ba, dan acewar in dai magani ya yi Habib ya kusanci Hassana ai ya isa ace ta ji alamun motsin Hassana. In da in dai akan yadda Malam mai biyan buk'ata dole ya ce musu ne, Hassana da kanta zata bar gidan, wata zuciyar kuma sai ta ce mata" tom koma Hassana ta bar gidan baki sani ba ne bama". Hakan yasa Farida zuwa ta tambayi Jimmai. Farida har cikin d'akin su Jimmai ta shiga ta kira Jimmai".


Farida kallan Jimmai ta yi, ta ce, "Jimmai na ce kin ko zubamusu maganin? ". "Eh Aunty Farida na zuba". Farida cikin jin dad'i ta juya ta nufi part d'in Habib, Farida na zuwa ta yi nocking d'in k'ofar, ta ji shiru ta kuma yi nan ma shiru".


Hassana ko lokacin ko tashi basu yi ba, dan takan dad'e tana addu'ar in ta idar da sallar asuba, hakan yasa idan ta koma baccin safe ta ke jimawa. Hassana cikin bacci ta ji bugun k'ofa, da saurinta ta tazo dan jin waye. Hassana na zuwa cikin murya mai kama da ta bacci ta ce, "Waye? ". Farida sumar tsaye ta yi, tana tunanin tom idan rannan ance Mommy ta ce ci Hassana yau kuma fa, yau dai daga ita sai Oga Habib, "anya ko maganin mutumin nan nayi?".Farida ta tambayi kanta, dan acewarta ba zai yuwu ba, ace haka na faruwa, sai dai in ko Malamin k'arya ne". Farida shiru ta yi bata amsa ma Hassana ba tabar gurin, tana zuwa ta kira Mahaifiyarta awaya ta ce, ta shirya gata nan zuwa kuma Wallahi yau babu abinda zai hanata zuwa Nijar, dama tun farko Mommy na ce miki bana son aiki irin wannan k'ila wa k'ala, tom gashi nan dai Oga Habib bai kusanci 'yar iskar yarinyar nan ba, dan haka gani nan yanzu ki shirya Wallahi bazan bari Hajiya ta dawo ta isketa a gidan nan ba". Hajiya Murja ko da bata da abin cewa wanda ya wuce ta yi biyayya da abinda Farida ta ce , ta ce, "Shikenan Farida ki zo tom dan nasan kona ce miki ki bari sai gobe ba bari zaki ba".


Farida na zuwa ta iske Hajiya Murja ta shirya ita taje jira, direct suka nufi airport sai dai inda suka je sai dai jirgin da zai kai su Katsina suka samu. Cikin isshan lokaci suka isa katsina, tun a airport d'in Katsina suka samu maimotar da zata kai su Nijar ".


Kasan cewar ba cancikin Nijar za su shiga ba , farko-farko ne yasa k'arfe hud'u na yamma suka isa gidan friend d'in Hajiya Murja wanda zata tai masu jagora zuwa gun bokan da zasu, in da dama ita ce ta tab'a yima Hajiya Murja hanyar shi".


Kasan cewar friend d'in Hajiya Murja ta sanda zuwan su Hajiya Murja yasa a ready ta ke, suna isa babu hutawa babu komai, danma sunci abinci akan hanya"..


Hajiya Bilki k'awar Hajiya Murja a motarta ta d'auki su Hajiya Murja ta kaisu har k'auyan da bokan ya ke".


Koda suka isa sun iske layi dan har sai da suka jira, sannan suka shiga. suna zuwa ya dakatar dasu ya ce, cikin muryar shi mara dad'in sauraro, "mai buk'ata kad'ai muke son gani, bama son 'yan rakiya, ku jirata a waje".


Hajiya Murja da Hajiya Bilki komawa sukai suka bar Farida kad'ai."..


K'urama Farida ido ya yi yana kallanta, dan har sai da Farida ta fara tsorata da kallan da bokan ya ke mata, sai zuwa wani d'an lokaci, ya ce, " me kike so ai miki, auran za'araba?, koko yarinyar ce kike so a kora daga gidan baki d'aya? ". Farida cikin zuciyarta ta ce, "Alhamdulillah kaji aiki". Sannan ta yi sauri cikin jin dad'i ta ce, "So nake araba auran kuma a kori yarinyar daga gidan baki d'aya, sannan ina son a dawo mai da hankalin shi ad'ora mai sona mu yi aure yana cikin hankalin shi ". Batare da bokan ya kuma cewa komai ba, wani magani ya d'akko yaba Farida, ya ce, "wannan zaki tauna shine ahaka zaki cinye shi, wannan kuma zaki wanke fuskarki da shi, wannan kuma zaki yarfa mai ajikine , ai dama ke ce kika haukata shi". Shiru bokan ya yi sannan ya ci gaba da cewa, "Magani na farko da nace miki zaki tauna, duk abinda kika ce, kina so agurinsa zai yi, zai ji maganarki fiye da ta Uwar da ta haifaima, a haka ne zaki bashi umarnin ya kuri ita yarinyar kuma ya saketa, magani na biyu da nace zaki wanke fuska da shi, shi kuma duk wani abun k'i da yake gani wanda ya hana shi sonki tom kamar shine kika wanke, magani na uku kuma wanda nace ki yayyafame, shine wanda zai dawo da shi hayyacinsa". Yana kaiwa nan ya ce, "mungama miki aiki, saura kud'in aiki zaki biya".


Farida kud'i ta ciro masuyawa ta ajema bokan, sannan ta ce, "Amma abinda yake ban tsoro ta yadda zanga Oga Habib d'in, dan yarinyar bata barina shiga wajan shi? ". Wani magani ya d'akko ya ce, kikira sunanta sau uku, sannan ki sha wannan, harta bar gidan sai abinda kika ce zata rik'a yi, dan haka daga kince ta ta bud'e miki da sauri zata bud'e". Farida da d'i ya ishsheta , kud'i ta kuma d'ebowa ta ba bokan, sannan ta tafi tana mai farincin nasara"..


Farida a cikin mota ta samu su Hajiya Murja suka tafi, gidan Hajiya Bilki. Inda suna tafiya Farida na basu labarin yadda su kai da bokan. Hajiya Bilki ce ta ce, "Ai Farida karki damu tunda kikazo gun kafin gobe..., ai aikinki yagama biya, tun-tuni da muntab'a wannan hirar da Hajiya Murja ai da tuni kin auri Habib angama, nan dai suka ta hirarsu har suka isa gidan Hajiya Bilki inda a nan za su kwana sai gobe zasu wuce".


Haka ko akai, washe gari da wuri su Farida suka kama hanyar Katsina, dan daga inda suka je zuwa airport akwai nisa".


Su Hajiya Murja sai dare suka shigo Abuja, Hajiya Murja ganin dare ya yi , ta tsare Farida ta kwana awajanta".


Washer gari da sassafe Farida ta yi sammakon zuwa gidansu Habib.


B'angaran Hassana ko, tun jiya ta kasa gane kan mutuminta, sai wani irin bacci ya ke, duk yau kuma tun safe yak'i cin komai, tayi- tayi yak'i ci, yana cikin baccin ita kuma lokacin tana kitchen tana k'ok'arin had'a musu dinner ta ji wani irin k'ara wadda sai da k'arra ta firgitata, hakan yasa ta rigo da gudu daga kitchen d'in, ta nufi bedroom d'in Habib, tana zuwa zaune ta iske Habib tsayiyar gado yana dafe da kanshi da hannun wanshi guda biyu, yana jijjuya kan yana rirrintse ido. Hassana na zuwa ta hau kan gadon cikin rud'u da yanayin da taga Habib d'in, Hassana na zuwa ta rik'o Habib d'in tana tofa mai duk addu'ar da tazo bakinta. Can Hassana ta ji Habib ya yi wata uwar gyatsa da k'arfi. Can kuma sai taga ya saki kanshi da hannu wanshi da yasa ya daddafe kai d'in ".

Habib d'ago da kanshi ya yi yana kallan Hassana. Hassana kuma cikin jin dad'in ganin Habib ya bar abinda ya ke, da alamu ya ji sauk'i, ta rungumo shi, ta ce, "Ayyah Oga Habib Sannu ko, tsakanin jiya da yau kana shan wahal...... ".

Hassana tsawar da ta ji ce tare ta turota k'asan da Habib ya yi yasa bata k'arasa abinda ta ke fad'aba".


Allah sarki Hassana bata damu da abinda Habib ya yi mata ba, ta shi ta kuma yi zata hau gadon, Habib ya kuma daka mata tsawa , wadda tafi waccan, ya ce, "Ke ! , wacece ke!?, kuma me kike yi anan? ". Hassana cikin tsoro da al'ajabi ta ke kallan Habib, dan idan taji da kyau sai taji kamar Habib ne yake magana, kuma kamar yadawo hankalinshi abisa ga yadda ya ke maganar............ โœ๏ธ



Tofa wai meke faruwa ne, Habib kamar yadawo hankalin shi nake gani๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค.


Ga kuma su Hajiya Farida da tarin Magunguna ko ya abin zai kaya???.


Idan kin karanta daure ki yi Comment sister, Comment ke k'aramin kwarin gwiwar update da wuri.



Share
&
Comment please ๐Ÿ™.

๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI.

https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Lale watan alkairi, watan da ummulkairi, Amina zatil fatahi ta haifi d'a al sugaba, lale watan da duka aljanu suke ta ce wa sun bani dan basu k'ara ci gaba.
Yau ne sha biyu ga watan rabu Auwal, wata mai girma mai daraja, watan da fitayyan halitta yazo duniya, Allah kak'ara mana k'aunar annabi Muhammadu (S, A, W).
Happy maulud.





Shafi na 48&49.



Hassana cikin murna da manta waye Habib, ta kalli Habib, tana mai k'okarin k'ara hawa gadon, ta ce, "Wayyo Oga Habib ka warkene ko ko magana ce ta samu? ". Hassana ta fad'i maganar tana mai saurin rik'o hannun Habib d'in. Habib ko da al'ajabi ya bi Hassana da kallo".

Hassana ganin haka, yasa ta d'an girgiga Habib ta ce, "Wayyo Oga Habib kafara magana ko? , dan Allah ka ce wani abu, ko zanji dad'i".
Habib da ke zaune yana jin maganganun Hassana mamaki ne sosai ya cika shi, wanda yasa ya kasa cewa komai, hakan yasa yafara tunanin wai lafiya ko dai mafarki ya ke, idan kuma mafarki ne tom wacece haka tazo mai da siffar da bai sani ba".


Hassana ko ganin Habib ya yi mata shiru yana kallanta, yasa ta kuma kai hannu da niyyar ta girgiza shi. Wani ma haukacin mari Habib ya wanke Hassana dashi yana mai sake turota k'asa, ya ce, "Wacece ke?, kuma me ya shigo da ke nan? ". A hankali sosai Habib ya ke maganar.
Hassana da marin Habib ya farkar da ita ta dawo hayyacinta, da fe inda Habib ya fareta ta yi, tana kallan shi da idonta da ya kad'a ya yi ja".

Habib ko cikin d'an d'aga murya ya kuma cewa, "Fita ki bar nan kafin inyi k'asa-k'asa da ke! ". Still Hassana na tsaye dan ko motsawa bata yi ba, daga inda ta ke. Take Hassana ta shiga wani hali mai wuyar fita, dan indai dai-dai ta ke gani, kuma jinta ma dai-dai ya ke, tom tabbas Habib ya samu lafiya, dan ko daga kalar kallan da yake mata, hakan ya tabbatar mata Habib ya dawo hayyacinsa".


Habib ko ganin Hassana kamar bajin abinda ya ke cewa ta ke ba, sakkowa ya yi daga kan gadon, ya na kallan Hassana cikin ido, ya ce, "Wacece ke?, kuma me yakawo ki nan?, nace ki fita ko! ". Hassana cikin rawar murya ta fara magana, da cewa, "uhm ba komai". "Ba komai ".Habib ya mai-mai ta. Hassana d'aga ma Habib kai ta yi, ta ce, "Eh".

Kasan cewar rashin k'arfin da Habib ba ya ji ajikin shi koka d'an, dan ji yake kamar zai fad'i, dan ko maganar da yake ma Hassana da kyar yake mata ita, hakan yasa batare da Habib ya kuma cewa komai ba, ya nuna ma Hassana k'ofar fita da hannu, shi kuma ya koma bakin gadon ya zauna yana mai dafe kan shi".


Hassana juyawa ta yi ta kama hanyar fita bedroom d'in Habib, har ta kai bakin k'ofa ta juyo ta kalli Habib d'in da yake

Please Login or Register in order to submit comment