Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi tashiga bedroom d'in Habib ta gyara mai komai, sannan ta shiga toilet d'in ta wanke mai".


Bayan Hassana ta gama aikin komai ne, dama ta samo gyad'arta da shinkafar tuwo. Dan yau kunun gyad'a ta ke son yi ma Habib. Hassana sai da ta had'a koma na kunun, sannan ta bari, dan tafi son ta dama shi gaf da Habib d'in zai dawo. Kiran Sallar magriba da akayi Hassana ta je tai sallah, bayan ta idar ne tashiga wanka. Sosai Hassana ta shafe jikinta da oil oud aribian perfume. Sannan ta sa wasu riga da siket cikin wa inda Jimmai ta sai mata da bata saba. Sosai kayan suka amshi Hassana tai kyau na bugawa ajarida sister. Hassana sai da ta yi sallar issha'i sannan ta je ta had'a kunun tasa a flasks. Hassana kan caution d'in Falon ta kwanta tana jiran shigowar Habib amma shiru".



Abu kamar wasa Habib har 10:00 Pm Habib bai dawo ba. Wani tunani ne yazo ma Hassana, ta ce, "ko dai tun d'azu ya dawo ina bedroom d'ina ko kuma ina kitchen". Wannan tunanin da Hassana ta yi yasa ta nufi bedroom d'in Habib".



Habib na zaune bakin gado da laptop akan cinyar shi, Hassana ta turo k'ofar ta shigo ". Duk lokacinda Hassana zata keb'e da Habib ta kan manta shak'uwar da su kai ada baya cikin hayyacinsa, sai ta rik'a ganin kamar da. Hakan yasa Hassana take abubuwan ta kai tsaye gaban Habib".



Hassana d'an d'aure fuska ta yi, ta ce, "Oga Habib dama kadawo?, amma tun d'azu ina falo ina jiran dawowarka, ashema kadawo". Habib d'ago kai kawai ya yi ya kalli Hassana. Hassana kuma zuwa ta yi ta zauna gefan Habib tana lek'a laptop d'in da ke kan cinyar shi, ta ce, "Oga Habib yau ko naima wani abu, kuma nasan zaima dad'i, dan ko Mommy ta ce in nayi yana mata dad'i ". Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "In kawo ma kagani? ". Habib a halinda ya ke ciki yanzu Idan son samu ne baya son hayaniya, saboda lissafi yake, hakan yasa ya kalli Hassana ya ce, "Je ki ina abune". Hassana kamar za tai kuka ta ce, "Oga Habib kunu fa nada ma ma baka sone, kuma fa ni dan kai nadama, amma da bazan yi ba, dama lokacin da muna gida ne da nake damama nima na koyi sha, amma shine zanyi wahala indama kace sai anjima kana lissafi ne". Habib kamar yace wayyo da magan-ganun Hassana dan ko yanzu dauriya kawai ya ke yi, amma surutunta yafara b'atar da shi. Habib aje laptop d'in ya yi ya tashi, ya kamo hannun Hassana, ya ce, "wai ke baki da hankali ne bikiji ba nace miki, Ina lissafi ne". Habib tura Hassana ya yi waje, ya ce, "innagama kin kawo min". Hassana fita ta yi kamar za tai ihu, ta ce, "Ni Wallahi ba zan iya ba Sister Jimmai ni bazan iya ba, kina gani ma yanzu turoni waje ya yi wai na Isheshi". Hassana koma wa ta yi kan caution d'in ta kwanta".



Hassana bacci ne ya kwasheta, ba ita ta farka ba, sai 11:30 Pm. Tana tashi kamar wata zautata ta d'auki flasks d'in kunun ta nufi bedroom d'in Habib da shi".



Habib ko har ya gama abinda ya ke yi ya kwanta, dan bacci ma har ya kwashe shi. Hassana ta turo k'ofar ta shigo, da d'an haskan da ke d'akin Hassana ke kallan Habib. Hassana aje cup d'in kunun ta yi taje ta hau kan gadon, tana bubbuga Habib ta ce, "Oga Habib kai fa kace in kawoma in nagama, amma shine kai bacci". Habib ko da yake yanada nau yin bacci in ya kwanta, kodan baya samun yin narana ne. Hakan yasa bai ji bugun da Hassana ta ke mai ba, duk da kad'an-kad'an ta ke bugun shi".



Hassana ko dagewa ta yi, tana bubbuga Habib tana jan abun rufar shi. Can bak'in cikin hawalar dama kunun da tayi, gashi yanzu sai dai tai asara hakan yasa ta fara kuka, tana mai kuma bubbuga Habib".



Habib da cikin bacci yaji kukan Mutum, kuma ana bubbuganshi. Tashi ya yi zaune, Habib da mamaki yake kallan Hassana, sannan ya ce, cikin irin muryar wanda ya farka daga bacci. "Lafiya, me yasa me ki? "."kunun da nace ma na damama na kawo ma". Cewar Hassana ".



Habib ranshi ne ya b'ace, akan me zata tada shi yana bacci wai ta kawo mai kunu, gashi shi indai ya yi bacci aka tada shi da kyar yake samu wani baccin ya d'aukai. Hakan yasa Habib ya daka ma Hassana tsawa yana masifa, ya ce, "Wallahi ki gaggawar bari nan, dama akan kunu ne zaki tasheni, gashi nan har kin samin ciwan kai, bazan sa kunun ba, tashi kiban guri Kafin in daddakaki a nan gun!". Hassana da sauri hajjikanta na rawa ta tashi ta fita".


Washe gari Hassana da wuri ta tashi taima kan ta kad'ai abin breakfast, sannan ta shiga wanka, dan 8:00Am ne time d'in zuwanta, su tashi 2:00 pm. Hakan yasa Hassana nagama shiryawa cikin doguwar rigar shaddar da Hajiya Turai ta kawo mata, ta d'auki jakarta ta tafi".




Can Sanat yughurt ko su Billy na ta zuba idon ganin Hassana, amma shiru. Hassana ba ita taje sanat ba sai da ta tashi daga caktrea school, sannan".


Su Billy tsab sun lura da lokacinda Hassana tazo Sanat. Hassana na zuwa side d'in su Amina taje tana taya su aikinsu, a haka aka tashi Billy bata tankama Hassana ba, dan acewarta barta sai ta aikata sau uku saboda k'ar Habib ya yi masu kallan masu yawan kan k'ara".



K'arfe biyar nayi Hassana ta fito ta tafi gida, dan so take ta je tai aiki, dan ba tai akin komai ba ta fito, kuma tana son ta damama Habib kunu, inda Jimmai ta ce ta yi hak'uri katta gaji".



Billy da Farida na lure da Hassana lokacinda ta tafi. Hassana ko na zuwa gida ta shiga bedroom d'in Habib ta gyara ta wanke mai toilet, sanna ta gyara falon ma, ta d'ora mai kunun gyad'an. Hassana na gamawa ta shiga wanka, tai adonta mai kyau. Tana nan zaune a falo Habib ya shigo yau da wuri ya dawo. Hassana cikin nuna kula ta ce, "Barka da dawowa Oga Habib ". "Yauwa". Habib ya ce, ya shige ciki". Hassana sai da ta bari Habib ya isa ace Habib ya gama duk abinda ya ke sannan ta d'auki flasks d'in kunun ta shiga da shi bedroom d'in shi. Lokacin Habib ya gama shiryawa ya na zone yana tunanin kiran Bilya ya kawo mai wani abun dan yunwa yaje ji. Hassana da sallama tashi ga bedroom d'in, zaunawa ta yi kan lover chair d'in bedroom d'in, sannan ta bud'e flasks d'in ta zuba kunun ta mik'ama Habib, ta ce, "Oga Habib dan Allah gashi kasha kaga jiyama sai dai nai wahala baka shaba, kuma yafi wanda Farida ke kawo ma dad'i duk da shima nike yi". Habib amsar kunun ya yi daga hannun Hassana. Ya rik'e yana kallan Hassana. Hassana ma kallan shi ta yi, ta ce, "Tom Oga Habib kasha". "Infa nasha naji badad'i?". Cewar Habib". "Uhm ai Wallahi nasan ma zai ma dad'i, dan ko Mommy da ta tab'a zuwa lokacin nayi mana tasha, tace nafi su Maimuna iyawa". Cewar Hassana".



Habib kad'an ya kurb'i kunun, dan jin tasting d'in shi ". Hassana ko ganin Habib ya d'and'ana kunun, kallan shi ta yi, ta ce, "Tom ya, ya kaji kunun, baka tab'a shan irin shi ba ko? ". Habib tab'e baki ya yi, ya ce, "Bai min dad'i ba, kawai dai zan shane saboda kar azubar ayi almubazzaranci". Hassana shiru ta yi, dan tana tunanin Habib da gaske ya ke , yadda yi Maganar, hakan yasa ta kallai ta ce, "Dan Allah dagaske nai bai ma dad'i ba". Habib kai ya d'aga ma Hassana".Hassana hunnu ta mik'ama Habib ta ce, "Ban kunu na inda bai ma dad'i ba". "Yess ba tasting kunun, kawai dai inasha ne sabo da kar ai albazaranci". Hassana mamar Habib ta yi dai-dai zai kai cup d'in kunun bakin shi ta yi, wuf zata amshe, by mistake kunun ya b'arema Habib ajiki". Hassana cikin damuwa da rud'ewa ganin yadda tai ma Habib wanka da kunun".


Hassana b'alema Habib mab'alin rigar ta fara, tana cewa, "Ayyah yi hak'uri Oga Habib Allah bada sanina bane". Habib bige Hanun Hassana ya yi, ya ce, "Da Allah ni rabu dani, inda kin zubar da kunun ki tashi ki tafi". "Akwai fa saura, Allah bada sanina bane,". Habib hannun Hassana ya kama ya fitar da ita daga bedroom d'in, sannan ya rufe k'ofar shi.Cire kayan da Hassana ta b'ata mai ya yi, sannan ya shiga ya kuma wani wankan, ya dawo ya zuba kunun yasha. Sosai kunun ya yi ma Habib dad'i, dan ya yadda da Maganar Hassana da tace yafi wanda Farida ta ke sata tai mai dad'i. Sosai Habib yasha kunun Hassana ya kwanta, yana jinjina rawar kai irin na Hassana".



Washe gari da wuri Hassana ta tashi tai abin breakfast da Habib, tana gama wa ta shiga wanka, tana cikin shiryawa taji alamun fitar Habib. Hassana da sauri taya fa mayafinta ta fita, dan Habib har ya fita daga falon. Hassana da d'an k'arfi ta kira Habib ta ce, "Oga Habib! ".



Habib juyowa ya yi yana kallan Hassana. Hassana kuma da d'an gudu ta k'arasa inda Habib ya ke. Cikin nishin gudun da tayi, ta ce, "Oga Habib ga fa abin breakfast nayi da kai, kuma naga zaka tafi". Habib juyawa ya yi yaci gaba da tafiyar Shi, ya ce, "ni bana break fast da wuri". Hassana da sauri ta sha gaban Habib ta ce, "Uhm amma ai lokacin da na zauna part d'in ka dawuri nake mana, kuma kana sha, kuma kamanta jiya kace zaka shane saboda baka son albazaranci, tom Idan baka shafa sai dai in zubar, kuma kaga anyi albazzaranci inda ni bazan iya shanyewa ba". " ki aje anjima kisha , idan kika yadda kika zibar zaki ga abinda zan miki , waya ce ki yi dani bak'i tambayan ba? ". Habib yana tafiya yana fad'in haka".


Bilya yana cikin mota cikin mamaki ya ke kallan Hassana da Ogan nashi," dama sun fara magana haka? ". Bilya ya tambayi kanshi".



Hassana ko tana mai bin Habib ta ce, "Wallahi Oga Habib ni bana iya shanye shi ni kad'ai". Habib banza ya yi da Hassana ya shiga cikin motar. Hassana kallan Bilya ta yi, ta ce, "Oga Bilya ga kunu, in kawo ma". Aiko Bilya cikin jin dad'i dan yana son kunun ya ce, "Eh zan sha". Hassana da sauri ta shiga ta kawo ma Bilya kunun, sannan ya ja motar su ka tafi".




Yau kwanan Hassana Uku kenan da fara zuwa koyan girki da take yi. Yau Hassana ta riga Habib fita dan yana Falo tazo ta gaida shi ta wuce da sauri".



Yaune kuma Billy ta yi shirin kai k'arar Hassana gurin Habib na rashin aikin da bata zuwa sai 2:00pm, wata rana ma har 3 tana kaiwa sannan tazo".


Habib na zaune a Office d'in shi. Billy ta yi mai nocking. Habib izinin shiga ya bata, ta shiga. Billy cikin salon muna firci ta gaida Habib, sannan ta ci gaba da cewa, "Oga Habib dama kan Hassana ne, tun rannan da kaimana shara'a da Hassana, tom tun ranar Hassana bata zuwa aiki sai k'arfe uku ko hud'u, sannan Idan tazo bata aikin komai, Idan tazoma bai fi tai awa d'aya ba ta tafi, yanzu haka maganar da nake ma bata zo aiki ba yau". Habib da mamaki ya kalli Billy dan yau ai Hassana ma ta riga shi fita, hakan yasa ya ce, "Ki duba tana nan tazo". Billy cikin tabbatar ma Habib ta ce, "Wallahi Oga Habib bata zo ba, kullum haka ta ke yi". Habib kallan Billy ya yi, ya ce, "Ok, zaki iya tafiya".



Habib Bilya ya kira awaya ya ce, "Hello Bilya kaje gida ka duba min wannan yarinyar nan".



Bilya zuwa ya yi ya duba ba Hassana gidan yaga Hassana bata nan. Kiran Habib ya yi ya sanar da shi bata nan".



Habib kiran Billy ya yi yace, "dan tazo kikiramin ita".



Hassana ko yau basu suka tashi ba, sai 4:15pm haka yasa tana tashi ta nufi gida bata biyo Company ba".



Habib anayin Ishsha'i ya koma gida, zaune ya iske Hassana a falo. Habib tsaye ya yi yana kallan Hassana sannan ya ce, "Me yasa yau biki je aiki ba? ".kaina ke ciwo". Hassana taba Habib amsa saboda bata yi tunanin ya aiko gidan an duba bata nan ba".



Habib sake mai-mai ta ma Hassana tamyar ya yi, me yasa yau biki je aiki ba.......... ✍️



Idan kin karanta daure ki comment sister 🤝.



Comment
&
Share Please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/postsBah/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).


https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7


https://www.facebook.com/groups/301023561618950/

Ina ma dukkan d'aukakin musulmi barka da juma'@t mubarak, Allah ka had'amu da alkairin da ke cikin wannan rana mai albarka.


Ina godiya da addu'a inku gareni, Alhamdulillah Allah yaban lafiya. Nagode 🤝.




Shafi na 68&69.




Habib sake mai-mai ta ma Hassana tambayar ya yi, "me yasa yau biki je aiki ba? ". "Oga Habib kaina ke ciwo shiyasa banje ba". Cewar Hassana. Habib shiru ya yi yana kallan Hassana, sannan ya ce, "Daga yau Idan kinje aiki kira shiga Office d'ina ina ganin zuwanki, sannan Idan zaki close shima ina son sani". Habib na fad'in haka ya bar Hassana gurin tsaye, ya shige side d'in shi".


Hassana Shiru ta yi, tana tunanin wannan duk yana cikin shairin su Billy.Hassana kunin da ta dama ma Habib ta d'auka ta shiga side d'in shi da kunun. Hassana gefan Habib ta zauna, ganin bai d'ago kai ya kalleta ba, ta ce, "Oga Habib ga kunun ka? ". Habib ba tare da ya kalli Hassana ba, ya ce, "Ok, aje anan". Hassana ganin yau Habib ya koma asalin Habib d'in da da ta sani, yasa ta aje inda ya nuna mata, ta tashi ta fita".


Washe gari Hassana da wuri ta tashi tai abinda za tai tai shirin ta fiya Sanat yughurt. Bayan ta gama shirinta na tafiya zama ta yi, tana jiran Habib ya rigata ta fiya sannan ta tafi daga baya. Hassana na nan zaune Habib ya fito cikin shirinsa. Hassana ta shi ta yi tana gaida Habib. Babu yabo ba fallasa haka Habib ya amsa ma Hassana ". Habib na tafiya, bai fi da minti goma ba Hassana ma ta tashi ta tafi".


Hassana na zuwa Sanat yughurt, Office d'in Habib ta shiga kamar yadda ya umarce ta akan in tazo ta fara shiga Office d'in shi sannan".


Habib na zaune da laptop agaban shi, Hassana ta yi nocking. Izinin shiga Habib ya bata. Hassana shiga ta yi, sannan ta kuma gaida Habib ta ce, "Oga Habib gani nazo". "Ok, in zaki close ma ki shigo".Habib ya ce ma Hassana.Hassana kum fita ta yi, dan yau taji haushin rashin zuwa caktrea school d'in ta da ba tai ba. Hakan yasa ta ce kuma aikin bata yi". Hassana side d'in su Amina ta shiga, tana taya su hira, dan aikin ma da da take kamamusu yau ta yi alk'awarin ba za tai ba".


Billy koda tazo gun ta iske Hassana, kallanta ta yi, ta ce, "Ke nan ne gurin aikinki?, ki tashi kije ki wanke toilet d'in gunnan, dan an sanar da ni yau babu inda kika share ko kika goge, ki tashi ki yi ba zai yuwu ba, ana aiki kizo ki hanasu aiki da surutu kuma ke biki naki aikin ba". Hassana kamar karta tankama Hassana, sannan ta ce mata, "Supervisor banda lafiya ne, yau bazan iya aiki ba". "Wallahi ko mutuwa zaki yau sai kin yi aiki". Billy na fad'in haka, ta nufi Office d'in Habib".


Habib kallan Billy ya yi, yana mai tambayarta "lafiya?". "Ogq Habib dama akan dai Hassana ne, Wallahi har na gaji da kawo report akanta, ni yanzu rashin aikinta ma baya damuna, amma yanzu tana can ta had'a staffs' sai surutu su ke, nai mata magana. Amma ko kallo na ba tai ba, shine nazo na fad'ama ko kai zata ji taka". Habib kallan Billy ya yi, ya ce"kije zanzo in sa meta". Billy fita ta yi tana mai jin dad'i Habib zai tozarta Hassana yau agaban kowa, dan yanzu abubuwan da ta ke yasa wasu sun fara zargin ita wata ce agun , tunanin Billy kenan".


Habib ya tashi kenan don zuwa gun Hassana ya ci mutuncinta kamar yadda Billy ta ke tunanin, ringing d'in wayar shi, yasa ya zauna. Habib da fara'arshi ya yi pic d'in call d'in, saboda sunan Faruq da ya gani".


Daga can b'angaran mai kiran, ya ce, "Hello Habib, gumu nan yanzu haka muna daf da shigowa Abuja, nida Usman, da Jameel". Daga b'angaran Habib ya ce, "Wannan tafiyar lafiya kuwa? ". Wata uwar dariya Faruq ya yi, sannan ya ce, "Habib zumud'i yasa dole in fad'ima, da dai naso mu mamaye ka ne, Munzo ganin amarya ne, Mommy ta fad'a min ka yi aure, Wallahi Habib na k'osa inzo inga Amarya". Faruq ya fad'i maganar yana tun tsirewa da dariya". Habib cikin d'aurewa da fad'uwar gaba, ya ce, "Eh ina fatan ai Mommy'n ta fad'a muku yadda abin ya faru, kai ka sani nafi k'arfin auran yarinyar da ta had'a ni da ita, dan haka bana fargabar komai, kun dad'e bikuzo kun ganta d'in ba, baza b'ina bace bare ku kushe zab'ina, ammma Faruq Wallahi duk lokacin da nai aure bana shayin kaga zab'ina, kai dai kasan ni kasan waye ni, k'ananun Baby's din da kuke kulawa, kai kasan basu isan kallo ba, wallahi, dan haka baka da bakin magana akai na, sai ka bari sai na yi zab'ina ba wai zab'in Mommy ba, auran da bansan anyi shi ba". Faruq dariya sosai ya k'ara yi, sannan ya ce, "Kai guy baka da bakin magana, kai dai gamu nan zuwa muga amarya, kuma yunwa muke ji, ai mana girki, bama son na siye na amarya muke so". Faruq na fad'in haka ya kashe wayar shi".


Habib ko zufa keto mai ta farayi, duk sanyin Office d'in, saboda idan ba zai manta ba, Su Faruq du kansu babu wanda bai kawo mai budurwa ba kyawawan gaske 'yan boko, 'ya'yan manya, amma yana kushesu, yana ce masu duk basu yi ba, shi first class baby zai aura. Habib zama ya yi, sai ya tuno sun ce mai sun kusa shigowa Abuja, Habib tashi ya yi yafita, inda Billy ta ce mai Hassana na nan ya nufa".


Habib daga nesa ya tsaya yana k'arema Hassana kallo, azuciyar shi, ya ce, "Wallahi nasan dole ma su rai nani, dan wannan tafi kwarewa a surutu da rashin kunya, kai ya Allah ka fidda ni kunya. Habib k'arasawa inda Hassana ta ke ya yi".


Billy kuma sai dad'i ta ke ji, ganin Habib da ta yi ya nufi wajan Hassana, dan dama tafi so ya tozarta gaban worker's d'in".


Habib kuma na zuwa, ya kamo hannun Hassana, ya ce, "zo". Habib matsawa ya yi d'an nesa da Staff's d'in.inda hankalin kowa, uwa uba su Billy ya koma kansu".


Habib ATM card d'in shi ya ciro ya mik'a ma Hassana, ya ce, "ki koma gida yanzu, friend's d'ina ne zasu zo, ki biya gidanmu ki taho da maimuna ta kamamiki, da akwai wani shago da ake makeup, ki je ai miki, ki yi komai da sauri". Hassana tsayawa ta yi tana kallan Habib, sannan ta ce, "Oga Habib ni ba saina kira Maimuna ba, nima zan iya, sannan kuma ni zan ma kaina kwalliya bazani ko ina ba". Habib nuna Hassana da hannu ya yi, cikin fad'a-fad'a ya ce, " ki yi duk abinda nace, idan kika bari naji kunya..... ". Kad'a kai ka wai Habib ya yi, sannan ya ce, "bari in kira Bilya ya kai ki, idan kina buk'atar wani abun kuma ya siyo miki ". Hassana amsar ATM card d'in ta yi tana turo baki, dan ita bata son irin kalliyar nan".


Habib kuma Bilya ya kira awaya ya ce, "Bilya kazo yanzu". Habib na nan tsaye da Hassana Bilya yazo. Habib kallan Bilya ya yi, ya ce, "Ka kaita gida, idan ta gama abinda ta ke ka kaita nan kusa da mu d'innan inda ake makeup ai mata". Bilya cikin girmamawa ya ce, "Tom Insha Allah Oga Habib ".


Sannan Bilya ya tafi Hassana ta bi bayan shi. Billy ko da mamaki ta bi su da kallo, baka mar abinya yafi d'aure mata kai ba, ganin Habib ya ba Hassana ATM card d'in shi".


Hassana ko a hanya ta sa Bilya ya tsaya ya cirar masu kud'i, sannan suka biya suka sai duk wani abu da suke buk'ata. Hassana na zuwa ta shiga kitchen ta fara girki, ta ce," coconut rice zan yi irin wadda mu kai practice jiya. Cikin k'ank'anin lokaci Hassana ta gama duk abinda ta ke yi, sannan ta had'a masu lemun kwakwa, masha Allah. Ta jera komai a derning space. Bayan Hassana ta gama ko mai ne, ta shiga wanka, ta sa doguwar rigar da Hajiya Turai tai mata ta shadda, sanna ta samu Bilya a waje, suka tafi wajan makeup d'in ".


Bilya da kanshi ya ya yi magana da su akan ai mata mai kyau. Wayyo sister haka suka zauna suka cancara ma Hassana kwalliya. Wajan sa eyelashes ne aka samu matsala, dan Hassana cewa tai bata so, da kyar dai ta bari aka sa mata.sannan zuka amshi d'an kwalin suka d'aura mata".



Wato had'uwa iya had'uwa Hassana ta had'u, dan shi kanshi Bilya da Hassana ta fito da kyar, ya samu ya kauda idon shi akanta, azuciyar shi kuma yana ganin sakarcin Habib, ya ce, "wai kawai kasa matarka tai ma abokanka kwalliya kawai dan kar a raina ka,Allah ya kyauta ".kiran Habib ne ya katsema Bilya zan can zucinsa".


Bayan Bilya ya d'aga, Habib ya ce, "Bilya sun fa iso kun koma gida ne". "Eh gamu a mota zamu koma". Habib datse kiran ya yi, dai-dai nan kuma su Faruq suka shigo Sanat yughurt ".



Habib da fara'a ya rirrin gume su, zai yi Office d'in shi da su, Faruq ya ce, "Kai Malam gidanka za ka kai mu". Habib murmushi ya yi, sannan yaja Office d'in ya rufe, dama tun Kafin su iso Habib yasa an kawo mai mota agida. Habib da kanshi ya tuk'a motar zuwa gidan shi".



B'angaran Hassana ma kusan zuwan su kenan taji alamun hayanir zuwan abokan Habib d'in. Hassana bedroom d'in ta ta ruga. Su Faruq ko da fara'arsu suka shigo falon".



Bayan sun zauna , Faruq ya kalli Habib ya ce, "Kasan nifa banda dauriya, ina amarya?, na zaci ita zata tarbemu, ko dai kasa ta gudune". Faruq ya fad'i maganar yana dariya. Dan yau ya shirya rama duk abinda Habib ke musu akan duk budurwar da suka kawo mai, yadda ya ke kyarar su, daga ya ce bata da kaza sai ya ce, bata iya kwalliya ba, abubuwa dai Kala-kala ".



Habib tsaki ya yi, ya ce ma, "Faruq, tom bari kaji ko kad'an bana fargabar ku ganta, saboda ita d'in ba zab'ina bace kamar yadda na cema, zab'in Mommy ce, dan haka sai ku taya ni fad'ima Mommy ba ta yi ba, dan na riga ku fad'a, ya idasa maganar yana yin hanyar bedroom d'in Hassana".



Hassana zaune kusa da mirro sai kallan kanta ta ke, dan in dai mudubin nan ba k'arya ya yi mata ba, ta yi ma kanta kyau sosai ".



Ta mirro Hassana ta hango Habib, aiko da sauri ta sa hannu ta rufe fuskar. Habib ma da sauri ya idasa gunta ya sa

Please Login or Register in order to submit comment