Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ci gaba da cewa, "Mommy banga Bilya ba, dan zuwa gobe nake son ya kaita gidansu, dan ya kamata ace ta koma gidandu haka nan". Sai yanzu Hajiya Turai ta d'ago kai tana kallan Habib, sannan ta ce, "Babu inda zata Habib ta na nan, nan zata ci gaba da zama, maganar kud'i kuma da kake cewa zaka biya Hassana abinda tai ma, Habib baka da abinda zaka biyata, amma kash kai baka sani... ".

Sallamar Hassana yasa Hajiya Turai tai shiru".


Hassana cikin girmamawa ta mik'ama Hajiya Turai wayar Habib. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Daughter bashi". Hassana mik'ama Habib wayar ta yi cikin girmawa. Habib ko ko kallan Hassana bai yi ba, ya amshi wayar shi, sanan ya tashi ya fita".


Habib part d'in shi ya koma yana tunanin yadda zai yi ya rabu da yarinyar nan, dan babban abin kunya ne kamar shi abokan shi su ji labarin yana auran staff d'in shi, ina ba zai yuwu ba, sttaf d'in ma mai mopping, nan dai Habib ya gama zan can zucinsa bai samo mafita ba".


Ana sallar magriba Bilya ya shigo gidan, da wowar shi kenan daga zaria. Bilya sai da ya yi sallar issha'i sannan ya shiga side d'in Habib. Bilya da murnar shi cikin girmamawa ya gaida Habib da jin dad'in ganin Habib d'in ya warware. Bayan sun gama gaisawa ne Habib ya ba Bilya kud'i ya siyo mai tea da wai nar kwai dan ba zai shiga side d'in Hajiya Turai ba, dan baya san ganin Hassana acewar shi".


Bilya cikin k'ank'anin lokaci ya yo ma Habib had'in tea d'in da ya saba siyo mai ya kawo mai. Habib zama ya yi sha tea d'in sanna ya kwanta dan da wuri ya ke son zuwa Sanad yoghurt".


Washe gari da wuri Habib ya tashi ya yi duk abinda zai yi, sanan ya yi shirinsa na alfarma kamar yadda ya saba yi, sannan ya kira Hajiya Turai a waya, bayan ya gaidata ne, ya ce, "Mommy dama karki ga ban shigo bane, ina sauri ne zani wajan aiki". Hajiya Turai cikin nunama Habib ba komai ta ce, "Bako mai sai ka dawo". Habib ka she kiran ya yi, sannan ya nufi wajan mota inda Bilya ke jiran shi".


Bilya cikin girmamawa kamar yadda ya saba, ya gaida Habib. Habib amsawa ya yi, sannan ya ce, "Bilya ka je ka ce ma yarinyar nan ta zo aiki". Bilya da mamaki ya kalli Habib ya ce, "Oga Habib wata ya rinyar? ". "Yarinyar da ke aiki a sanad ". Shiru Bilya ya yi sannan ya ce, "Oga Habib Hajiya ta warware auran ne? ". Cikin tsawa da hargagi Habib ya ce, "Bansani ba! , ka je ka yi abinda nace ma! ".


Bilya fita ya yi ya nufi side d'in Hajiya Turai, shi dai aganin shi yana ganin rashin da cewar hakan. Bilya sallama ya yi ya shiga falon, Hajiya Turai, in da ya iske Hassana kad'ai a falon zaune............ โœ๏ธ


Labarin yanzu aka fara dear๐Ÿ˜๐Ÿ˜.


Idan kin karanta daure ki yi Comment sister ๐Ÿค



Comment
&
Share please ๐Ÿ™.

๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

IDAN KA MUTU AN RUFE LABARIKA, AMMA ABUBUWA UKU SUNA RAYUWA A BAYANKA: ILIMI DA HAIHUWA SAI AIKIN ALHERIN DA KA SHUKA.
ALLAH KA SA BAMU IKON BARIN AIKIN ALKAIRI,BAYAN RANMU๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ๐Ÿคฒ.




Shafi na 52&53.



Bilya cikin fa'ara suka gaisa da Hassana kamar yadda suka saba gaisawa, sannan bilya ya kalli Hassana ya ce, yana mai kame-kame dan sosai ya ke ganin rashin da cewar hakan, ya ce, "Uhm dama Oga Habib ne ya aikoni ya ce wai kije aiki yau". Hassana cikin rashin damuwa da abinda Bilya ya ce mata, ta ce, "Tom Oga Bilya ganinan zuwa, bari in tashi in shirya".


Hassana tashi ta yi, dama ta yi wanka gyalan doguwar rigar da ta sane ta d'akko, sosai Hassana tai kyau, kwalliyar ta sake fito da haskenta, kasan cewar abayar lemon green ce ta ji adon tsones".


Hassana har bedroom d'in Hajiya Turai ta je , bayan ta gaida ta ne, ta ce, "Mommy sai na dawo ". Hajiya Turai da mamaki ta kalli Hassana ta ce, "Daughter sai kin dawo kuma?, ina zaki? ". "Mommy yau zan koma aiki". Cewar Hassana. Shiru Hajiya Turai ta yi dan bata yarda Hassana niyyar kanta bace zata je aiki, tafi tunanin daga Habib ne, hakan yasa Hajiya Turai kallan Hassana ta ce, "Daughter nasan Habib ne ya ce kije aiki ko?". "Eh Mommy, kuma nima ina son inje". Cewar Hassana".


Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter babu wani aikin da zaki". Hassana badan taso ba ta hak'ura, saboda bata son jayayya da Hajiya Turai, amma tana tsoran rashin mutincin Habib narashin zuwanta " .



B'angaran Habib ko, sosai ma'aikatan Sanat yughurt ke murna da ganin Ogan nasu yaji sauk'i. D'aya bayan d'aya staff d'in ke shiga suna gaida Habib. Hakan yasa Habib bai wani aiki ba".


6:00PM Bilya ya zo yi ma Habib magana jin ya ji shi shiru har yanzu bai fito ba, saboda Habib ya saba inda Hajiyar Oga Habib na gida, tom a gida Habib ke sallar magriba.Habib kallan Bilya ya yi, ya ce"Bilya sai 9 o'clock yau zan je gida". Bilya fita ya yi yana mamaki dan yasan indai Hajiya Turai na nan Habib da wuri ya ke komawa gida".


Habib sai 9 o'clock sanna ya koma gida kamar yadda ya ce, Habib kiran Hajiya Turai ya yi awaya, bayan sun gaisane, ya ce, "Mommy naso in shigo amma kuma ban dawo da wuri ba, sai gobe zan shigo"."Tom Allah shi kaimu". Cewar Hajiya Turai. Dan ta san abinda Habib kema kema guje-gujan".


Washe gari Habib da wuri ya yi shirinsa na tafiya Sanat yughurt, cikin blue d'in suit. Bayan Habib ya gama shirinsa ga ba d'aya ne, ya shiga part d'in Hajiya Turai".


Habib har bedroom d'in Hajiya Turai ya shiga, dan yawanci irin wannan lokacin yasan bata fitowa falo . Habib cikin girmamawa ya gaida Hajiya Turai, sannan ya tashi ya ce, "Mommy zan tafi, ina sauri ne sai in na dawo zan shigo". Habib tashi ya yi zai fita, Hajiya Turai ta kallai ta ce, "Habib koma ka zauna". Habib komawa ya yi ya zauna kamar yadda mahaifiyar shi ta umarce shi".


Hajiya Turai kallan Habib ta yi, sannan ta ce, "Habib ya maganar auranka da Hassana da nai ma?, ko akwai abinda baka gane bane abayanin nau? , in sake mai-mai ta ma? ". Habib zuk'unnar da kai ya yi, ya yi shiru.
Hajita Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib kai fa nake sauraro?". "Mommy naji kin min maganar aure da ki kai, amma Mommy ai kinsan wannan auran ba mai yuwuwa bane, na farko dai ni gaskiya babu aure a tsarina yanzu, na biyu kuma gaskiya abun kunya ne friend's d'ina suga ina auran staff d'ina, staff d'in ma cleaner , sannan yarinyar nan ma fa Mommy bamu san asalinta ba, ni Mommy ko bama komai kwata-kwata bana son yarinyar nan gaskiya!, sannan inajin nau yin aganta ace ita ce wadda nake aure, gaskiya Mommy kema ki duba ki gani, wannan ba abu bane mai yuwuwa..! ".


Hassana da shigowarta kenan dan gaida Hajiya Turai, taji maganar Habib ta k'arshe, Hassana na shigowa ta gaida Hajiya Turai cikin girmamawa kamar yadda ta saba,sai dai muryara na rawa sosai, Hassana kallan Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Mommy ke ki kai min alk'awari Oga Habib ba zai tab'a sanin da auran nan ba, amma Allah bai nufaba sai da ya sani". Shiru Hassana ta yi, sannan ta ci gaba da cewa, "Mommy dan Allah ina son yau ki cika min alk'awarin da kika d'aukar min yau, dan Allah ki warware auran nan yau ".Hassana ta idasa maganar kamar za tai kuka dan sosai ta ji zafin maganganun Habib, wai yana jin kunyar aganta ace ita yake aure".



Hajiya Turai shiru ta yi, dan tasan Hassana taji abinda Habib ya ce. Habib ko tashi ya yi, ya ce, "Mommy ni zan tafi, dama ba da yarda ta akai ba".Habib na fad'in haka ya juya ya tafi ".


Hajiya Turai ko shiru ta yi tarasa abinda ke mata dad'i, dan itama sosai maganganun Habib su kai mata zafi, sannan ya kuma daf kawa, wai shi zai tafi dama bada yardar shi akai ba".


Hajiya Turai kallan Hassama ta yi da ke zuk'unne kanta ak'asa. Hajiya Turai kamo hannun Hassana ta yi, sannan ta ce, "Daughter ki yi hak'uri, nasan kinji duk abinda Habib ya ce". "Babu ko mai Mommy, ai abinda ya fad'a haka ne ba asan asalina ba, ni yanzu Mommy abu d'aya zaki min dan Allah ki datse auran nan, insha Allah gobe zan tafi garinmu". cewar Hassana. Hajiya Turai cikin damuwa ta ke kallan Hassana jin abinda Hassanar ta ce. Sannan Hajiya Turai ta ce, "Daughter tafiya kuma? ".
"Eh Mommy tafiya nake son yi dan Allah karki hanani".
"Shikenan daughter share hawayanki, yau she kike son ki tafi? ". Cewar Hajiya Turai"."gobe". Hassana ta ba Hajiya Turai amsa a dak'ile".


Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta kalli Hassana ta ce, "daughter kije ki yi break fast, Allah ya kaimu goban ".


Hassana cikin sanyi ta tashi ta ta fita".


B'angaran Farida ko, yau ta shirya dan zuwa gidansu Hajiya Turai dan ganin lafiya, dan a yadda tai ma Habib magana akan sakin Hassana ya nuna ya amshi maganar, tom tunjiya taso zuwa, amma Hajiya Murja ta hanata ta ce, ta bari sai nan da kwana biyu tuk'un ta san kafin lokacin Habib ya rabu da Hassanar, Allah bashi sai su san ta yadda zasu b'ullo mai ya auri Farida, hakan yasa Farida yau ta yi shirinta ta na tafita gidandu Habib, in da yau ne Mahaifiyarta ta ce mata ya kamata ta je".


Farida k'arfe sha biyu na rana tazo gidansu Habib. Direct Farida part d'in Hajiya Turai ta nufa".


Hajiya Turai Farida ta iske zaune a falon ita kad'ai, Farida kamar yadda ta saba, haka ta je ta gaida Hajiya Turai. Hajiya Turai ko ta amsama Farida a dak'ile, babu yabo babu fallasa.
Farida d'an nesa da Hajiya Turai ta zauna, tana Waige-waige ko zata hango Hassana, dan ta k'osa ta ji har yanzu Hassana na gidan. Farida kallan Hajiya Turai ta yi, cikin sanyi ta ce, "Mommy Hassana fa?, banganta ba". "Tana ciki". Hajiya Turai ta kuma ba Farida amsa a da k'ile". Farida shiru ta yi tana tunanin tom Habib ya saki Hassana ne ko ko?".


Farida zama ta yi tana jiran Habib ya dawo ta kuma zuwa ta tunkarai da maganar ta ji abinda zai ce".


B'angaran Habib ko, dan karma ya dawo da wuri ya had'u da Hajita Turai, yauma k'in dawowa ya yi, sai 9:50Pm, kamar jiya. Yana dawowa ya kira Hajiya Turai a waya, bayan sun gaisane ya ke sanadar da ita, ya ce, "Mommy yauma bandawu da wuri ba, shigowata kenan yanzu, sai dafe na shigo". "Allah ya kaimu Hajiya Turai ta ce, ta yi rejecting call d'in ".

Farida ko ganin Habib bai dawo da wuri ba, yasa ta adana kala manta sai washe gari ta yi ma Habib ".



B'angaran Hassana ko yau haka ta wuni duk ba fara'a, dan ko abinci tsakura kawai ta ke. Ko da yaushe ko saurare ta ke, ta ji Hajiya Turai ta ce mata ta warware auranta da Habib, dan sosai ta ji hankalinta ya koma gida, mahaifarta kawai ta ke son tafiya, inda ga abin da barin gida ya jawo mata, har ana ik'irarin ba asan asalinta ba, tabbas bata tab'a, kawo ma ranta wata rana wani zai mata gori da hakan ba, hakan ne ya sa da akai mata ya tada mata hankali , taji gaba d'aya hankalinta ya koma ga mahaifarta.
Adaran dai haka Hassana ta yi bacci duk ba dad'i".


Washe gari. :washe gari bayan Hassana ta idar da sallar asuba gari ya fara aske, kamar yadda ta saba haka ta je gaida Hajiya Turai, sai dai Hassana koda ta tura bedroom d'in Hajiya Turai sai taji kamar ansa key, Hassana cikin mamaki ta juyo, ta koma d'akin ta. Hassana ta zauna babu dad'ewa Maimuna ta yi sallama ".


Hassana amsawa ta yi, sannan ta fito tana tambayr Maiamuna lafiya. Takardar da ke hannun maimuna ta mik'ama Hassana, ta ce, "Dama Hajiya ce ta ban ta ce in baki". Hassana amsa ta yi tana bin letter da Maimuna ta bata da kallo, sannan ta mai da kallanta gun Maimuna ta ce, "Ina Mommy fa?". "Hajiya ta yi sammakon tafiya". cewar Maimuna. Hasssana ba ta k'ara bin takan zancan Maimuna ba, ta bud'e letter tana karantawa kamar haka. :Assalamu akaikum. Da farko dai ina baki hak'uri daughter na sab'a alk'awarin da nai miki, hak'ik'a naso in raba auranki da Habib kamar yadda nai miki alk'awari, sai dai kash !, na kasa hakan. Daughter ba zan b'oye miki ba bazan iya raba auranki da Habib ba, sai dai idan Allah ya yi babu rabon zaman aure a tsakanin ku. ki yi hak'uri da rashin sallamr da ban miki ba. Daughter bana iya had'a ido da ke ne, dan ina jin kunyar abinda Habib ya yi miki. Dan Allah daughter ki lura yanzu akwai aure kanki, dan Allah ina rok'onki karki ce zaki tafi da aure kanki. Ki yi hak'uri insha Allah komai zai dai-dai ta tsakaninki da Habib.,ki yafemin daughter, bissalam ".


Hassana ko da ta kama karanta letter da Hajiya Turai ta bada a ba ta, gun ta zauna tana kuka. Cikin kukan tana cewa, "Haba Mommy biki ji abinda Oga Habib ya ce bane, koda ace ni 'yar asali ce, tom baya sona kwata-kwata azuciyar shi. me yasa zaki min haka!! ".


Haka Hassana tasha kukanta ta gaji ta lallashi kanta ta yi shiru".


Farida ko da kukan Hassana ya ta data, ta window ta lek'o tana kallan Hassana. Hassana ko nan ta tashi ta bar letter da Hajiya Turai ta bata agun".


Farida ko na ganin Hassana ta tashi ta zo da saurinta ta d'au letter tana karantawa ".


Farida ko da ta kagama karanta letter, kuka itama tasa, dan ta yi tunanin Hassana nakukan Habib ya saketa ne. Farida share hawanta ta yi sannan ta d'akko tan figigin mayafinta ta yafa, ta nufi gidan Mahaifiyarta, da letter a hannunta".


B'angaran Habib ko bayan ya gama shirinsa ya fito, ya nufi part d'in Hajiya Turai. Bilya ne ya yi saurin da katar da shi ta hanyar cewa, "Barka da safiya Oga Habib, ga shi inji Hajiya ta ce in baka".


Habib amsar letter da Bilya ya mik'a mai ya yi yana mamakin ta me ye. Habib bud'e letter ya yi ya fara karantawa kamar haka. :Habib raina b'ace na kema magana, hak'ika na ji zafin maganganunka na jiya akan Hassana, kuma ina son ya zama farko da k'arshe da zaka k'ara furta mata wata kallama mai muni irin haka. Habib na koma wajan aiki, hak'ika idan na kalli fuskarka ayanzu tana tuna min ne da kalmomin da ka fad'ama Hassana marasa dad'in ji. Daga k'arshe idan har ka saki Hassana koda ko ita ce ta naimi hakan Allah ya isa ban yafema ba Habib!!! ".



Wata irin zufa ce ke keto ma Habib lokacin da yagama karanta letter. Sosai ranshi ya b'ace da furicin Mahaifiyarshi akan shi, akan me za tai mai haka, koko ana zaman aure ba so ne, tom idan ma anayi gaskiya shi ba zai iya haka ba. Habib wayar shi ya ciro ya kira Hajita Turai, amma har ta gama ringing bata d'aga ba".


Habib ranshi b'ace ya kalli Bilya ya ce, "Bilya kiramin waccan yarinyar ". Bilya ko tunda yaga haka ya yi tunanin babu lafiya, dan lokaci guda idon Habib ya kad'a ya yi ja sosai".


Bilya kallan Habib ya yi, ya ce, "Oga Habib wata yarinyar? ". "Bansani ba Bilya!, ai kasan yarinyar da nake nufi".


Bilya ta fiya ya yi yana mai tunanin anya ko ba k'arya zai koma ya yi ma Habib ba, anya idan yaga Hassana ahalinda ya ke yanzu , ba zata ji da kyau ba, tom amma kuma nasan halinshi sare zai iya zuwa da kanshi kiranta. Bilya na wannan tunanin ya isa falon Hajiya Turai............ โœ๏ธ



Idan kin karanta daure ki Comment sister ๐Ÿค.


Idan naga Comment da yawa gobe insha Allah zaku ga Update da wuri Allah.

Idan na raina comment tom zafa kuji shiru๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค.



Share
&
Comment please ๐Ÿ™.

๐Ÿ“š OGA HABIB ๐Ÿ“š
๐Ÿ’ซ๐Ÿ’ซ
*๐Ÿ…™๏ธŽARUMAI ๐Ÿ…ฆ๏ธŽ WRITERS ๐Ÿ…๏ธŽSSOCIATION๐Ÿ“š๐Ÿ–Š๏ธ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa๐Ÿ’ช*_

*๐Ÿ’ซ(๐Ÿ…™๏ธŽ.๐Ÿ…ฆ๏ธŽ.๐Ÿ…๏ธŽ)๐Ÿ’ซ*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/



Shafi na 54&55.



Bilya ta fiya ya yi yana mai tunanin anya ko ba k'arya zai koma ya yi ma Habib ba, anya idan Habib yaga Hassana a halinda ya ke yanzu ba zata ji da kyau ba, tom amma kuma nasan halinshi sare zai iya zuwa da kanshi kiranta. Bilya na wannan tunanin ya isa falon Hajiya Turai. Sai dai ko da ya shiga ba kowa Falon, sallama Bilya ya yi da k'arfi, amma shiru. Bilya fita ya yi yana mai jin dad'in rashin ganin Hassana da bai ba , dan shi dama ba son isar da sak'on ya ke ba, aganin shi hakan bai kamata ba ".


Habib na tsaye inda Bilya ya barshi, Bilya ya dawo. Bilya kallan Habib ya yi ya ce, "Oga Habib inajin bata side d'in Hajiya, dan na yi magana naji shiru, babu alamun mutum".


Habib batare da ya tankama Bilya ba ya shiga mota. Bilya ma ya shigaya yaja motar suka tafi".


B'angaran Farida ko tana isa gidan Hajiya Murja, ta wurga ma Hajiya Murja letter da Hajiya Turai ta ba Hassana, ta ce, "Mommy nikam nagaji!, sai yaushe zan zama mai sa'ane, kince muje wajan wancan wai shi mai biyan buk'ata dole, ya ce sai Oga Habib ya yi hauka zan samu in aure hankali kwance, ya yi haukarshi ya gama k'arshe mai-mai kon a had'a auran da ni da wata aka had'a, yanzu munyi takakkiya munje gun wannan shima kinga shirman da yabamu, nifa nagaji zan yanke hukuncin da zai min dai-dai in huta da rayuwar bak'incikin nan da nake, Mommy koda yaushe ina fad'a miki Oga Habib shine cikar farincikina, duk wani farinciki indai ba ina tare da shiba tom jabu ne, dan haka ni yau d'in nan zan yanke hukuncina na k'arshe! ". Hajiya Murja sosai hankalinta ya tashi da furincin Farida dan ta san Farida babu wani hukuncin da zata yanke wanda ya wuce ta ce zata tafi ta barta".


Hajiya Murja hannun Farida ta kama ta ce, "Farida ki yi hak'uri kinji, bari in kira Hajiya Zaliha in mata bayanin halinda nake ciki nasan zata tai maka min da wani abun".


Hajiya Murja wayrta ta d'auka ta kira Hajiya Zaliha kamar yadda ta ce. Hajiya Zaliha na d'aga Kiran Hajiya Murja tai mata bayanin halinda ta ke ciki. Hajiya Zaliha cewa ta yi ta bari anjima zata shigo unguwar zata biyo".


Hajiya Murja kallan Farida ta yi ta ce, "Farida ki yi hak'uri kamar yadda kika ji nace miki, indai kika sa hak'uri aure zakaninki da Habib babu fashi, kinga ma dai shi Habib ba son yarinyar ya ke ba, son Hajiya Turai ko ai na banza ne inda ba ita zata zauna mai da ita ba, dan haka ke dai ki yi hak'uri ki ban nan da isowar Hajiya Zaliha". Hajiya Murja na nan sai aikin ba Farida baki take, sunanan zaune Hajiya Zaliha ta iso.
Bayan sun gaggaisa ne Hajiya Zaliha ta kalli Hajiya Murja ta ce, "Hajiya naji duk ba yaninki, amma yanzu zamu gwada da basirar da Allah ya bamu ne, dama ai k'issar baka tafi ta malam, dan haka inda Malaman sun kasa sai mu yi da k'isssar mu ta mata". Hajiya Zaliha kallan Farida ta yi, ta ce, " Haba Daughter kina so kiban kunya sai kace wata 'yar kyauye, yanzu ke baza ki iya yaudarar namiji da kalaman bakinki ba ya soki, sai kin had'ashi da Malam, Tom ni Wallahi a zamanina da kallo nake yaudarar d'a namiji, bare ke da kike da dama kina zaune gidansu. Yanzu dai ki bud'e kunnanki da kyau ji ji abinda zan fad'amiki, amma fa sai kin jure, dan shi dama mai nema sai ya jure indai kika sa juriya tom zakiga ribar abin. Yanzu dai da farko zakina yawan tusa kanki aduk abinda ya shafi Habib agidan, amma zaki yi abin a Sannu, dan karki kuskura kina nuna zak'ewa wajan tusa kanki,duk wani abu da ya dan ganci Habib ki yi k'ok'ari ya kasance ke zaki mai, ke idan zai yuwuma duk wani abu nashi ya dawo hannunki, ita kuma yarinyar dama kunce ba sonta ya ke ba, zakina nuna rashin iyawarta duk abinda tai a gabanshi, ko da ya yi kinuna mata ba haka ake ba. Shi kuma Habib d'in kina nuna mai kina jin tausan shi na had'a shi da yarinyar da akai , dan kwata-kwata ba ajinshi ba ce". Hajiya Zaliha kallan Farida ta yi ta ce, "Daughter ina fatan kina fahim tata?, yawan kwalliya ko ki dage da saka kayan da zaija hankalinshi, ita ko yarinyar in ma mai son kwalliya ce ki sanyadda zaki kina hanata".


Farida cikin jin dad'i ta rungume Hajiya Zaliha, ta ce, "Wayyo Mommy, dama nasan hakane ai da tuntuni gunki nazo da yanzu na auri Oga Habib anwuce gun".Dariya Hajiya Zaliha ta yi, ta ce, "Banni da shi daughter, k'aryar muskilanci yake. Sannan kina yawan kirana awaya ina k'ara miki wasu darisan".


Hajiya Zaliha ta dad'e tana kuma koyama Hassana dabarun da zata ja hankalin Habib, batare da ta had'a shi da boka ba ko malam".



Farida ko nagama jin k'issoshin da Hajiya Zaliha ta koya mata, ta tashi ta ce, "Ai tafiyama za tai".




B'angaran Habib ko bayan sun isa Sanat yughurt, kallan Bilya ya yi, ya ce, "Bilya ka tabbatar da yarinyar nan gobe tazo aiki! ". Magana Bilya ya ke son yima Habib amma baiga fuska ba, sai dai cewa ya yi, "Tom insha Allah Oga Habib".




B'angaran Hassana ko tsabar kukan da ta yi ne ya saukar mata da ciwan kai, hakan yasa ta kwanta, ba ita ta farka ba sai azahar, bayan ta yi sallah ne ta je derning space ta ci abinci, duk da bawani na kirki ta ci ba, danma yunwa ta ke ji inda tun jiya rabon ta da abinci".



Gaf da magriba Farida ta shigo gidan. Sai dai ko da tazo Falon bataga Hassana ba, hakan yasa ta zarce room d'in ta, wanka Farida ta yi sannan ta zauna ta rangad'a kwalliya kamar mai shirin zuwa gasar kyau. Falo Farida ta dawo ta zauna, duk da tana mai fargabar kar Habib yak'i ganin wannan wankan, inda in Hajiya Turai bata nan Habib ba ya dawowa da wuri. Farida na nan zaune Hassana ta fi to ta nufi kitchen tana son had'a tea dan shi kawai ta ke jin zata iya sha".


Hassana wucewa ta zo yi zata shiga kitchen, Farida ta ce, "Ke! ". Hassana juyowa ta yi tana kallan Farida, amma harga zuciyarta bata jin dad'in ke d'in da Farida ke ce mata ba".


Farida kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ki taho min da abinda zanci". "Tom". Hassana ta ce, ta juya ta

Please Login or Register in order to submit comment