Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bata matsayin ne ko-ko ? ". Ai Kafin Habib ya yi magana, Hassana ti yi wuf ta ce, "Manager ina tunanin koda ace k'arya nake bazan yi ba agaban Oga Habib, dan haka ina mai tabbatar maka shi yaban matsayin nan jiya, dan haka ina ganin zasu iya tafiya".


Manager da sosai ranshi ya b'ace ganin Habib ya yi mai Shiru, wannan k'aramar yarinyar na nai man rugaza soyayyar shi. Manager kallan Billy ya yi ya ce, "Supervisor ku saman a Office d'ina". Manager ya yi maganar daga gani kasan ranshi ya b'ace ya ke, da shirun da Habib ya yi mai"


Manager na fita su Billy ma suka bi bayan shi suka nufi Office d'in shi kamar yadda ya ce. Bayan duk sun gama fita ne Habib ya kalli Hassana ranshi b'ace, ya ce, "Dama kin rok'an in baki matsayine dan ki kore su?". Hassana Shiru ta yi tana mai wasa da hannunta, dan yadda ta ga Habib ya d'aure tasan ba wasa. Habib ko cikin daka ma Hassana tsawa ya ce, "Nace dama kin rok'an in baki matsayi ne dan ki kore su!? ". Hassana girgiza kai ta yi, ta ce, "A'a Oga Habib, amma kamar yadda kaji na fad'a Allah haka ne, Supervisor bata aiki, ita kuma Farida..... ". Tsawar da Habib ya yi ma Hassana ce yasa ta yi shiru. Habib hanyar fiya ya nuna ma Hassana da hannun shi, ya ce, "Barnan! ". Hassana fita ta yi, tana fita ta ta yi tafiyar ta caktrea school d'in ta, tana mai addu'ar Allah yasa Habib k'arya da wo da su Farida, idan ma zai dawo dasu, tom Banda Farida, dan tafi jin zafin Farida".


Manager ko a office d'in shi kallan su Billy ya yi, ya ce, "Supervisor ku yi hak'uri kuje gida koda na yau ne kad'ai, zan samu M, d, muyi magana zuwa anjima". Billy kallan manager ta yi, ta ce, "Idan har na bar gurinnan da sunan wai waccan bagidajiyar ce ta koran, tom kasani ba zan dawo ba". Manager cikin rashin sanin yadda zai yi ya ce, "Ki yi hak'uri Billy idan har kika tafi ni kuma nayi miki alk'awari zaji dawo da matsayinda take ta k'ama M, d ya bata, ki ce zaki koma kan matsayin". Billy cikin jin dad'i ta d'ago tana kallan manager, ta ce, "Manager ka tabbata? ". "Billy ba wai tabbata wa ba, alk'awari nayi miki, ke dai kin san yadda nake da M,D, ni ke tsara komai na gurin nan, dan haka nasan yadda zan mai , in ma ya bata mataimakiyar tawa da gaske , nasan yadda zanyi na dawo da shi kanki, amma yanzu ina so ki yi hak'uri ki je gida na yau kad'ai, zuwa gobe zaki dawo da matsayinta". Billy cikin jin dad'in kalaman manager, ta ce, "Godiya nake dearie". Sunan da ke kashe manager kenan, dan har Billy ta gano shi. Billy kallan Farida ta yi, ta ce, "Ya kika ji tsarin? ". Dariya Farida ta yi, ta ce, "reshe ya juye da mujiya". Dariya sosai sukai, sannan su kai ma manager sallama suka tafi ".


Hassana k'arfe 3 na rana bayan sun tashi ta biya ta Sanat dan ganin, su Billy suna nan ko sun tafi. Hassana babu inda bata duba ba, amma bata gansu ba, hakan yasa ta samu k'awarta Amina, ta tambayeta ko supervisor na nan".


Amina kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana Amma dai akwai releshanship tsakanin ki da Oga Habib ko? ". Hassana kai ta girgiza ta ce, "Babu komai tsakanin mu, malam ki ban amsa ta supervisor na nan ko ta tafi?, ita da Farida? ". "Eh naga tafiyar su, ita da Aunty Farida". Cewar Amina, tana kallan Hassana, dan bata yadda da cewar da Hassana ta yi ba babu dan gantakar komai tsakaninta da Habib".


Hassana kallan Amina ta yi, ta ce, "Nina wuce, sai gobe insha Allah ".


Habib yau da wuri ya koma gida. Hassana ko tana dawowa gida taima Habib kunun shi d'an kullun. Hassana ba ita ta shiga side d'in Habib ba sai da ta tabbatar ya gama komai sannan ta shiga, da kununta a hannu. Lokacin Habib yana waya da Hajiya Turai tana sanar dashi da wowarta gobe. Hassana guri ta samu ta zauna ta zauna tana jiran Habib ya gama wayar. Hajiya Turai ko, fad'a tai kema Habib ta ce yaba Hassana waya ya k'i tun da tazo basu yi waya ba, kuma tana kiran wayarta a kashe, dan haka yanzu ya bata. Habib mik'ama Hassana wayar ya yi. Hassana ko kallan Habib ta yi, tana tambayar shi waye Oga Habib? ". "Kisa a kunnanki kiji". Habib ya ba Hassana amsa".


Hassana sosai tayi murna jin Muryar Hajiya Turai da ta yi. Bayan sun gaisa ne, Hajiya Turai ke tambayar Hassana lafiya tana kiran wayarta bata zuwa? ". "Mommy ruwa ta fad'a nayi-nayi tak'i kawowa". Hassana taba Hajiya Turai amsa ".


"Zan kawo miki wata kinji daughter ". Hassana godiya ta yi ma Hajiya Turai dan tana son waya sosai. Bayan Hajiya Turai ta kashe ne, Hassana ta kalli Habib ta ce, "Ina wuni Oga Habib ". Habib banza ya yi da Hassana ya ci gaba da danna wayar shi. Hassana kuma cikin sanyin murya ganin Habib ya juya mata baya sosai, dan ko inda take yak'i kallo, kuma kwana biyu ba haka yake mata ba, hakan yasa Hassana cikin sanyin murya ta ce, "Oga Habib? ". Habib banza ya yi da Hassana. Hassana kuma bata gaji ba, ta kuma cewa, "Oga Habib! ". Nan ma Shiru ba amsa. Hassana kamar za tai kuka ta ce, "Oga Habib kaga ko hannuna inajin ya yi tsagewar k'ashi, bana iya d'aukar abu mai nauyi da shi, kuma bakaji ba yadda ya ke min zafi". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Muga hannun? ".Hassana da gaske hannun yana mata zafi amma ba sosai ba, mik'ama Habib hannun ta yi". Habib ko na amsar hannun ya rik'e ya na ja mata shi da k'arfi sosai, yana d'an bubbuga hannu".


Hassana da k'arya take hanun ba wani ciwan kuzo kugani hannunke mata ba, ai take ta fara kuka, tana cewa, "Wayyo Oga Habib basshi haka dan Allah ". Habib ko be bari ba cigaba da latsama Hassana hannun ya yi, ita kuma tana ihu, tana rirrik'e hannun Habib. Habib da katawa ya yi yana kallan Hassana, ya ce, "Kin sha maganinki? ". Kai Hassana ta d'agama Habib."banyar da ba, je ki d'akko in gani? ". Cewar Habib".


Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Nafa manta shi a Office d'inka". Habib shiru ya yi ya ci gaba da danna wayar shi. Hassana kuma so take taima Habib maganar su Billy ta rasa yadda za tai, sai zuwa can ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib dan Allah karka dawo da su Billy sai nan da sati, kaga nima ai kaji dad'i kace na fidda kai kunya ko?, dan Allah Oga Habib kabar su sai sun yi sati, dan Allah, kaji Oga Habib ". Habib ko kamar jiran Hassana ya ke, ya aje wayar hannun shi, ya kalli Hassana ya ce, "Wallahi! Wallahi!! Ida har aka kuma fad'a dake a Sanat... ". Habib kai ya girgiza. "Tom aini bani ke to nan su ba, suke to nona. Hassana kunun da ta damama Habib ta mik'ama mai ta ce, "Oga Habib ga kunun ka karya huce". "Bazan shafa".Habib yaba Hassana amsa".


Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib me yasa?". Kin b'ata min rai yau". Hassana dama tun a sanat da ta kori su Billy taga irin kallan da Habib yake mata, ita yanzu tashin hankalinta d'aya kar ya ce zai cireta a matsayinta".


Hassana kallan Habib ta yi, cikin sanyin murya, ta ce, "Oga Habib dan Allah ka yafe min, Allah bazan kuma ba, koma sun min zan rik'a banza da su, kuma dan Allah karka cireni a matsayina". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "da ga yau karki kuma fad'a da kowa!? ". Ya fad'i maganar cikin gargad'i ".
"Allah bazan kuma ba". Cewar Hassana, sanna ta d'akko kunun ta ce, tom gashi kashi".


Habib amsa ya yi, yana sha. da yake Habib kan 3 seater ya ke zaune,kafin Habib ya gama shan kunun Hassana da ke kusa da shi zaune, gafen kujerar ta kwanta, tana jiran Habib ya shanye kunun ta fita da Cup d'in. Sai dai Kafin Habib ya shanye kunun bacci ya kwashe Hassana. Habib ko yana gamawa ya ce, "Nagama tashi karki bacci, ki je ki kwanta". Abinda Habib ko bai sani ba, Hassana har ta yi baccinta".


Habib jin Hassana ta yi mai shiru, kallanta ya yi, abin mamaki sai yaga ashema baccin ta ke. Habib bubbuga Hassana ya yi, ya ce, "Ke tashi kije ki kwanta zan rufe k'ofana". "Hmmmm". Hassana da ke jin Habib sama-sama ta amsa mai".


Habib kuma buga k'afar Hassana ya yi. Hassana da bacci sosai ya kwasheta, ta ce, "Wayyo Allah na, tom ina zuwa". Habib tsaki ya yi ya tashi ya kashe wutar falon, ya nufi bedroom d'in shi, inda dama Hassana a falon shi ta sa mai".


Cikin dare Hassana ta farka fitsari, ta ganta cikin duhu, ai take ta fara ihu, dan ta mamanta kwata -kwata ba a bedroom d'in ta ta ke ba. Hakan yasa Hassana ta fara ihu tana laliban makunni amma bata gani ba, ita atunaninta wani ne ya shiga ya kashe mata wuta in da dai ita bata kashe wuta a haske ta ke kwana. Ai Hassana dagewa tai tana ihu ".

Habib ko da ya yi nisa sosai a bacci, cikin bacci ya ji yo ihun Hassana a falon shi, da sauri Habib ya tashi ya nufi falon, yana zuwa ya kunna wutar falon. Ko da ya kalli Hassana a furgice ya ga take. Tsaki Habib ya yi, ya ce, "Shikenan ke ako mai baki da hankali". Hassana baki ta turo tana cewa, "Oga Habib nifa na manta ba a bedroom d'ina nake ba, kuma ni bana kwana a duhu. Hassana da fitsari ya matseta, kallan Habib ta yi ta ce, "Oga Habib dan Allah inajin fitsari". "Kije naki toilet d'in ki yi mana". Cewar Habib".


Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib dan Allah fa, Wallahi ya matsan". Habib yana jan tsaki ya nuna ma Hassana bedroom d'in shi. Hassana da saurinta tashi ga. tana fitowa Ta nufi falon Habib. Habib koma ya koma bedroom d'in shi ya kwanta, Hassana zaune ta yi, a falon Habib, dan ita matsorarciya ce sosai. Sai da Hassana ta tabbatar ya isa ace Habib ya yi bacci sannan ta lallab'a ta shiga bedroom d'in shi ta kwanta can bayan shi, tana addu'ar karya tashi".


Habib ko bashi ya farka ba, sai asuba, ananne yaga Hassana kwance a bayanshi sai baccinta ta ke abinta. Habib da mamaki ya ke kallanta tom yaushe ma ta shigo ta kwanta bai ji ba. toilet d'in shi ya shiga ya yi alwallah ya zo ya tada sallah. Habib har ya idar da Sallah Hassana bata tashi ba, hakan yasa Habib ya ja bargon da ta rufe da shi da k'arfi. Hassana da sauri ta tashi tana sosa kai, ta ce, "Oga Habib... ". Habib hannu ya d'ora lips d'in shi alamun Hassana ta yi shiru. Hassana shiru ta yi ta tashi ta fita".


Habib wanka ya yi, ya yi shirinsa na tafiya aiki, ya tafi. Habib yana zuwa Office d'in shi babu dad'ewa, manager ya shigo. Bayan manager ya gaida Habib ne, manager ya ce, "M, d, dama game da tafiyar Supervisor gida ne, gaskiya m, d, gurin nan ace babu supervisor akwai fa damuwa, dan sanin kankane yarinyar na k'ok'ari sosai, tana kula da 'yan aiki sosai, ita Hassana ta dakatar da ita ne saboda bata yadda da rashin aikinta , ita sai take gani kamar ta tsaneta ne M, d, Supervisor tasan marketing sosai yarinyar, kuma tana da Experience sosai, Hassana ko bata san marketing ba, idan ake za'a d'auki matsayi irin wannan abata akwai matsala M, d, Dan haka ni idan har ka yarda inda na lura Hassana na son matsayi, tom sai a bata supervisor, ita kuma supervisor inda tafi ta Experience sai abata mataimakiyata. Yanzu idan har ka yarda anjima sai a had'a meeting aba kowa matsayinsa". Habib na yarda da duk wani tsarin da manager ya ke kawo, ba tun yau ba, hakan yasa ya ce, " Shikenan manager babu da damuwa, a had'a meeting d'in ".


Hassana da Billy kusan tare suka isa Sanat, inda Hassana ke mamakin ya akai Billy ta dawo aiki. Farida kuma daga baya ta zo".



Manager da kanshi ya bi kowana staff ya sanar da shi da akwai meeting k'arfe goma".


K'arfe goma nayi aka had'u a a inda aka tana da dan meeting. Kowa yana gurin hadda Habib. Manager ne ya tashi ya fara bayani kamar haka. "Tom kamar dai yadda muka saba yi a masana antar nan, duk wanda za'aba wani matsayi sai anyi meeting yau ma haka za muyi. A bisaga jajircewar Supervisor kamar yadda koma wa sani, mun k'ara mata matsayi abisaga jajircewarta na aiki, an k'ara mata matsayi izuwa ga mataimakiyata, inda ita ma Hassana zamu bata matsayin da Supervisor ta bari. ko akwai Wanda ke da magana? ".


Duka gurin suka amsa da babu, Hassana tashi ta yi, ta d'aga hannu , alamun tana da magana".

Manager kallanta ya yi, ya ce, " muna sauraranki. Hassana cikin hikima ta fara magana kamar haka...... ........ ✍️




Idan kin karanta daure ki Comment sister 🤝.




Share
&
Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚
💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7


https://www.facebook.com/groups/301023561618950/


Shafi na 74&74.



Hassana cikin hikima ta fara magana kamar haka, " Idan har a atsarin masana'antar nan mutum biyu zasu iya hawa matsayi d'aya, tom matsayin da manager ya ba Supervisor ya yi, amma idan har a tsarin masana'antar nan ba zai yuwu Mutum biyu su hau matsayi d'aya ba, tom ka barta a matsayin ta na supervisor, dan wannan matsayin da ka bata matsayina ne da Oga Habib ya ban, kuma ina nan akan matsayina, amma idan har naji daga bakin Oga Habib cewar ya saukeni matsayin ya ba Supervisor, tom nabar ma ta, amma ina nan a matsina da Oga Habib ya ban, na mataimakiyar manager ". Hassana na gama fad'in haka ta zauna. Duka gurin kowa shiru ya yi, idan wasu suka fara zargin kodai akwai releshanship ne tsakanin Hassana da Habib. Nan dai kowa da tunanin da yake. Inda shi kuma manager jira yake yaji abinda Habib zai ce, amma Habib shiru bai tanka ba, daga k'arshe ma tashi ya yi ya fita gurin, nan dai d'aya bayan d'aya aka fara fita gunan, inda manager shima yana ganin Habib ya tashi, shima ya bar gun. Nan dai a haka aka gama fita. Hassana tashi ta yi zata fita, su Billy suka yi saurin shan gabanta, Billy sai da ta gama yi ma Hassana kallan sama da k'asa, sanna ta yi dariya ta ce, "Hassana kike kome?, ina mai miki albishir gobe zan fara aiki a matsayina na mataimakiyar manager, dan Allah idan kin isa ke mai matsayi ce a gurin Oga Habib kisa ya dakatar da ni. Duk wanda ke Company a yau ya saida ni Billy an k'ara min matsayi daga Supervisor izuwa ga taimakiyar manager, inda ke kuma aka baki nau matsayin, kina b'ab'atun Oga Habib ya baki matsayi, amma kuma ko manager bai shaida hakan ba, kinga mu bamu san da maganar ba. Daga k'arshe ina mai jan kunnanki karki sake shiga gurimina idan ba haka ba, zanyi amfani da matsayina in wahalar da ke a Company'nan! ". Billy na kaiwa nan taja hannun Farida suka tafi suka bar Hassana nan tsaye".



Hassana taji zafin magan-ganun da Billy ta fad'a mata sosai, sai dai haka ne, ko manager bai shaida matsayin da Habib ya bata ba kamar yadda Billy ta ce, ita ko kowa ya shaida matsayinta. Hassana Office d'in Habib ta je, babu nai man izini ba komai, Hassana ta tura ta shiga . Dan Habib da ke zaune sai da ya d'ago kai yana kallanta".


Hassana nesa da Habib ta zauna ta tura kanta tsakanin cinyoyinta, tana kuka, dan sosai taji zafin maganganun da Billy ta fad'a mata".


Habib da mamaki ya ke kallan Hassana, banza ya yi da ita yaci gaba da abinda ya ke yi. Habib har ya gama abinda ya ke yi Hassana bata bar kukan da take ba, kuma ba wai ahankali ta ke kukan ba, ba kuma da k'arfi cancan ba. Habib da katawa ya yi da abinda ya ke yi, yana kallan Hassana, sannan ya ce, "Ke". Hassana ko dama ta tsani ke d'in da Habib ya ke ce mata, ci gaba da kukan ta ta yi, bata d'ago ba".


Habib da d'an k'arfi ya kuma cewa, "Ke!, bakya jine ina kiranki". Still Hassana banza ta yi da Habib, kuma bata da kata daga kukan da take ba".


Habib kallan Hassana ya yi, ganin yadda take kuka,amma sai magana ya ke mata ta yi mai shiru, ran shi ad'an b'ace ya ce, "Wai lafiya zaki shigo Office d'ina ki ta sani kina kuka, kuma ina miki magana kinyi banza dani, so kike kanki ya yi ciwo wannan kukan da kike yi". Hassana ko bata da kata da kukan da take ba, bare Habib yasa ran ta na ma sauraran shi, ci gaba da kukanta ta yi".


Habib tashi ya yi, ya je ya samu Hassana inda ta ke. Habib zama ya yi kusa da Hassana sannan ya d'ago kanta da ta tusa tsakankanin cinyoyinta, ya ce, "Shikenan ya isa haka, ki yi shiru kanki kar ya yi ciwo, yanzu fad'a min me ya faru? ". Habib ya fad'i maganar yana bubbuga bayan Hassana".


Hassana rage sautin kukanta ta yi, amma bawai ta yi shiru bane. Habib kallanta ya yi, ya ce, "Oh!, ki yi shiru ki fad'a min mana, kukan ya isa haka". Habib ya fad'i maganar yana jawo Hassana ajikin shi, alamun lallashi".



Hassana share hawanta ta yi, ta d'ago kai tana kallan Habib, Habib ma ita yake, kallo, ya ce, "Tom ina jinki? ". Hassana cikin murya irin ta wanda ya yi kuka, ta ce, "Oga Habib ba kai bane kaban matsayi, kuma yanzu manager ya maida matsayin kan Supervisor, bacin tun farko abinda na naimi kaban ke nan, abinda tun farko sai da nace ma kaban matsayin Supervisor kak'i, kace sai dai kaban mataimakiyar manager, shine kuma yanzu manager zai ba Billy, kuma ai kai ne kai min alk'awari kuma kasa min rai". Hassana ta idasa maganar hawaye na zubo mata".


Habib handkerchief d'in shi yasa ya goge ma Hassana hawayanta, sannan ya ce, "Tom shi Supervisor d'in da aka baki meye abun shi?, dama tun farko ai abinda kike so kenan, ki yi hak'uri kima wata rana zaki zo duk matsayin da kike so". Hassana mai da kanta ta yi tsakankanin cinyoyinta ta ci gaba da kukanta. Ana ahaka ne kiran Hajiya Turai ya shigo wayar Habib".


Habib na d'agawa Hajiya Turai ta ce, "Hello Habib nan da minti goma jirginmu zai sauka, kaje ka d'akko daughter kuzo ku tar ban tare". "Tom Mommy, gani nan". Cewar Habib, sanna ya kashe wayar. Habib kama hannun Hassana ya yi, ya ce, "Zomu je mu d'akko Mommy yanzu zata sauka". Habib handkerchief d'in shi yasa ya goge ma Hassana fuskarta, saboda ta nuna alamun kuka".


Hassana bayan Habib tabi suka shiga motarshi yaja suka nufi airport d'in. Hassana ko suna tafiya tana mai ci gaba da kukanta ka d'an ka d'an. Habib na lure Hassana har suka shiga airport d'in. Bayan ya yi parking ne ya kalli Hassana ya ce, "Ya Allah, wai har yanzu kukan nan kike yi, ki yi shiru kinga yanzu babu lokacin da za muyi magana, idan na kai Mommy sai muyi magana, yanzu goge hawayanki". Habib handkerchief d'in shi ya kuma mik'ama Hassana ta goge fuskanta. Ahana ahaka ne jirginsu Hajiya Turai ya sauka".


Habib fita ya yi, ya bud'e Hassana, ya kamo hannun ta, suka tsaya dai-dai saitin da zasu ga Hajiya Turai. Habib na hango ta ya za hannun Hassana suka k'arasa gun ta".


Hajiya Turai da fara'arta ta rungume Hassana tana Oyoyo daughter. Hajiya Turai na rik'e da hannun Hassana suka k'arasa inda Habib ya yi parking, suka shiga".


Bayan sun isa gidan Hajiya Turai ne, Hajiya Turai ta kalli Habib ta ce, "Habib me yasa mu daughter?, daga ganin idonta ta yi kuka ". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Me yasa me ki, ki kai kuka? ". Hassana turo ma Habib baki tayi. Hajiya Turai ta ce, "Zo nan daughter ki zauna, ki fad'a min abinda ya yi miki". Hassana tashi ta yi ta zauna kusa Hajiya Turai kamar yadda ta umar ce ta. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "daughter fad'amin me yasa ki kuka, dan da ga ganin idonki ya nuna kinyi kuka? ". "Mommy ba fa ko mai abu ne ya fad'a min a ido". Cewar Hassana. Hajiya Turai bar maganar kawai ta yi, badan ta yarda da abinda Hassana ta ce ba".



Hassana da Habib haddare suna gidan Hajiya Turai. Hassana ko tun d'azu da tai sallar magriba ta kwanta kan abin sallar saboda ciwan da kanta ya ke mata, dama in dai tai kuka sai tai ciwan kai. Habib zuwa ya yi ya yi ma Hajiya Turai sallama ya ce, "Mommy zan tafi sai gobe". "Tom daughter fa?, tun da tai sallar magriba bata fito ba, duba ta kagani ". Habib bedroom d'in Hajiya Turai ya shiga, Habib k'arasawa inda Hassana ta ke kwance ya yi, saboda jiyo sautin kukanta kad'an-kad'an da ya ji. Habib tado Hassana ya yi daga kwan can da ta ke, ya jingina ta da jikin shi, yana cewa, "yanzu dan Allah duk akan magana nan ce, ki ke kuka haka, ga kanki nan har ya d'au zafi, shikenan indai mataimakiyar manager ce na baki, shikenan kukan ya isa haka ". Hassana ko ita tama manta da wata mataimakiyar manager da ta ke so, kanta ke mata ciwo shi take ma kuka, ai ko tana jin abinda Habib ya ce, "d'ago kanta ta yi da yake mata ciwo sosai ta ce, "Oga Habib dan Allah da gaske? ". "Kai Habib ya d'agama Hassana, ya ce, "gobe zansa manager ya tabbatar da matsayin kowa ya sa ni". Hassana da ke zaune gefan Habib bata san sanda ta rungume Habib ba, tana cewa, "Dan Allah Oga Habib karka kuma can zawa, kuma kaima manager magana". "Tashi muje phamarcy d'in kusa da mu abaki magani sai mu wuce gida daga can". Cewar Habib".


Hassana tashi ta yi, suka fita da Habib. Zaune suka iske Hajiya Turai a falo. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Daughter lafiya ko? ". "Mommy kaina ke ciwo". Hassana taba Hajiya Turai amsa".


Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib ka biya da ita phamarcy ka amsar mata magani ". "Tom". Habib ya amsa ma hajiya Turai ".


Hajiya Turai waya ta mik'ama Hassana, ta ce, "daughter ka tsarabar ki ". Hassana da murnarta ta amsa tana ma Hajiya Turai godiya. Sanna suka tafi".


Habib sai da ya biya ta pharmacy ya saima Hassana magungunan ciwan kai sanna suka tafi. Kasan cewar sun ci abincin su gidan Hajiya Turai hakan yasa suna zuwa Habib ya zauna a falo, ya d'akko faro ya ba Hassana maganin ciwan kan. Hassana na gama shan maganin, ta kwanta. Habib kallanta ya yi ya ce, "ki tashi

Please Login or Register in order to submit comment