Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga kitchen ta had'a tea d'in ta, sanann ta d'iboma Farida abincin ta kai mata . Hassana mik'ama Farida abincin ta yi ta tafi, Farida kallan Hassana ta yi, ta ce, "Da hannunki zan ci? ". Hassana batare da ta tanta mata ba, ta koma kitchen ta d'akko mata spoon ta kawo mata".


Washe gari da wuri Bilya ya shigo falon Hajiya Turai yana sallama. Hassana da taji yo sallamar Bilya , fitowa ta yi, bayan sun gaisa ne Bilya ya kalli Hassana ya ce, "Dama Oga Habib ne ya aikoni ya ce, "Yau ki je aiki". Bilya na fad'ima Hassana haka ya juya ya fita".



Hassana dama ta yi wankanta, cikin kayan da Hajiya Turai ta sai mata, ta d'akko wata abaya da yake duk kusan dogayan riguma ne, tasa. Sannan ta d'auki ma yafin rigar da yake yana da girma ta yafa, takama hanya zata tafi.
Farida da fitowarta kenan, kallan Hassana ta yi damamaki ta ce, " Ke ina zaki? ". Hassana batare da ta kalli Farida ba ta ce, "Aiki". Hassana na fad'in haka ta juya ta tafi abinta. Tabar Farida gun tsaye, ko ba komai taji dad'in hakan dan hakan ya tabbatar mata Habib bai damu da Hassana ba".



Hassana ko kasan cewar babu kud'i a hannunta wajan Jimmai ta je. Jimmai da murnarta ta rungume Hassana ta ce, "Dama talaka irin mu na ganinki!, Wallahi bacin sanin da naimi ba d'an ka d'an bane da babu yadda za ai in gane ki. Hassana kinganki ko yadda kika dawo, kinyi fari kinyi k'iba.. ". Hassana murmushi ta yi, ta ce, "Uhm Sister Jimmai kenan, ni wata k'iba zan wani yi, ni dai yanzu sauri nake ban 1k a kud'innan,". Shiru Jimmai ta yi tana kallan Hassana, sannan ta kauda tunanin da ta ke yi, ta ce, "Wai Hassana ina zaki ne haka? ". "Aiki zani". Cewar Hassana ".


Jimmai kallan Hassana ta yi da alamun mamaki a tattare da ita, ta ce, "Aiki kuma?". "Sister Jimmai ban dan Allah, Allah akwai damuwa idan na je late". Cewar Hassana ".



Jimmai kallan Hassana ta yi da alamun tuhuma, ta ce, "Hassana ni na san jin sauk'in Oga Habib zaki fuskanci abubuwa da yawa agun Oga Habib, sannan zaki fuskanta agun Aunty Farida ma. Hassana ya auranki da Oga Habib yana nan ko ba ya nan?". "Bayanan". Hassana ta ba jimmai amsa. Jimmai kallan Hassana ta yi ta ce, "Bana son maganar wasa dan Allah, Hajiya ta raba auran ne koko? ".



Hassana shiru ta yi sannan ta kalli Jimmai ta ce, "Sister Jmmai dan Allah kiban in tafi, idan nadawo zanzo muyi magana". Jimmai shiga ta yi ta d'akkoma Hassana 1k kamar yadda ta ce, ta ba ta. Sannan Hassana ta tafi".



Hassana ba ita ta je Sanat yughurt ba sai 11:15PM. Abinda Hassana ko bata sani ba tuni Billy ta canza wata madadin Hassana. Hassana ko da ta je Sanat yughurt stuff's d'in gurin wa inda suka saba da da ita, da murnarsu suka tarbi Hassana suna tambayarta lafiya tabar zuwa shiru haka? ".

Duk wanda ya tambayi Hassana sai ta ce mai batada lafiya ne. Dariya sosai sukayi sannan Amina wadda tasu tafi zuwa d'aya da Hassana, ta kalli Hassana ta ce, "Sister ki canza wata k'aryar, amma wannan bata amsu ba, kallakki fa, yadda ki kai kyau, kika wani canza kamanni, da kyar muka iya gane ki, bacin ma wannan voice d'in taki da bazamu shaidaki ba, amma shine zaki wani ce mana kinyi ciwo ne ".ita dai Hassana murmushi kawai tai masu, sannan ta ce, "Ni yanzu tunanina d'aya yadda zamu k'arke da supervisor". Amina dariya ta yi, ta ce, "kuma kinsan rashin mutuncinta sai abinda ya yi gaba, dan Wallahi muna ganin mulkin mallaka".


Hassana kallan Amina ta yi, ta ce, "Sister Amina yanzu ya zanyi?, in da kince ta maida wata a mazaunina? ". "Zuwa zakiyi ki sa me ta sai ki mata bayanin rashin zuwaniki, amma fa karki ce mata ciwo kikai kamar yadda kika ce mana, dan Wallahi ba zata yarda ba, garama kice mata tafiya ce ta kamaki lokaci guda, k'ila idan kikaci sa'a ta yadda ki ci gaba da aiki".



Hassana da addu'a ta shiga office d'in supervisor. Hassana cikin girmamawa ta gaidata. Ita ko Billy bata gane Hassana ba, hakan yasa ta ce mata, "Lafiya?, kina son meye? ".dan ta zaci Hassana surpleaar ce. Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "Supervisor Hassana ce, wadda ta yi aiki wata Uku da suka wuce, ina b'angaran mopppiny, tom dama tafiya ce ta kamani lokaci guda shiyasa ban samu damar zuwa na sanar ba".


Kallan baki da hankali Billy tai ma Hassana, sannan ta ce, "Tom yanzu me kike so? ". "Na dawo aikina". Cewar Hassana. Kallan rainin hankali Billy taima Hassana, sannan ta ce, "Hassana ko da ace kin d'auki permission, tom mungama aiki da ke, bare kuma baki sanar ba, tuntuni mun maida wata ma zauninki, zaki iya tafiya".



Hassana a zaman da tai da Billy ta san halinta, hakan yasa bata kuma cewa ko mai ba, ta fita daga Office d'in. Hassana shiru ta yi tana tunanin komawa gida, tana kuma tsoran Habib, ga shi in tace zata gudu, bata son tafiya da aure kanta. Bilya ne ya fad'oma Hassana a rai, hakan yasa ta fita ta je side d'in da Bilya ya ke aiki ta sa mai".


Bilya cikin fara'a yace da girman kujerarki, amarya agidan Ogan mu, mai makon ki aiko akirani, sai kizo da kanki". Hassana b'ata fuska ta yi, ta ce, "Oga Bilya dan Allah bana son sunannan, dan Allah ". "Yauwa tom nima ki bar cemin Oga Bilya ". Cewar Bilya, dan shi yana ma Hassana yanzu kallan girma ne, dan ko ba komai, acewar shi akwai auran Ogan su akanta". Hassana kalla Bilya ta yi kamar za tai kuka ta ce, "Oga Bilya Allah ba zan iya fad'in sunan ka kai tsaye ba, kaine wanda ya taimaka min alokacinda banda yadda zanyi, kaine ka had'ani da manager, amma kuma in rik'a Kiran sunan ka kai tsaye, gaskiya bazan iya ba". "Shikenan nima zanci gaba da kiranki da amaryar Ogan mu". Hassana kauda maganar ta yi, dan tasan indai Bilya ne sai dai suyi ta ta yin ta , hakan yasa Hassana ta kauda maganar baki d'aya".


Hassana kallan Bilya ta yi, ta ce, "Oga Bilya Supervisor ta dakatar dani daga aiki, kasan ban sanar da itaba na daina zuwana". Shiru Bilya ya yi, dan ko ba adad'eba sai da Habib ya tambaye shi wai yarinyar nan tazo dai aiki ko.Dan haka yasan aikin Hassana dole ne, hakan yasa Bilya kallan Hassana ya ce, "Karki damu, bari in ma manager magana".


Bilya Office d'in manager ya shiga, bayan sun gaisane, Bilya ya kalli manager ya ce, "Manager dama Oga Habib ne ya ce Hassana ta dawo bakin aiki, tom ta dawo kuma supervisor wai ta kureta, shine nazo in ma magana kai mata magana".


Manager Kallan Bilya ya yi, ya ce, "Wai kana nufin yarinyar da Hajiyar M,D, ta had'a aure da shi, alokacin da yana ciwonnan? ". "Eh ita". Cewar Bilya. "A'a tom auran fa, ko kana nufin M. D, har ya warga tsa shi, dan nasan zaiyi wahala dama ya zauna da ita, dan gaskiya M. D, yana da damuwa, amma in ba hakaba ai yarinyar tana da kyau". Cewar manager yana kallan Bilya. "Tom abin na Oga Habib sai dai shiru". Cewar Bilya ".


Manager kallan Bilya ya yi, ya ce, "Babu damuwa bari in ma Billy magana ".

Manager tashi ya yi ya shiga office d'in Billy . Zama ya yi sannan ya kalli Billy, ya ce, "Sweetheart ki yi hak'uri dan Allah ki bar yarinyar nan ta dawo bakin aikinta". Billy kallan manager ta yi, sannan cikin fad'a-fad'a ta ce, "Na dai gama kula da son yarinyar nan kake, haka wancan karan da nakoreta akai ma kai min!, kuma banda ita babu wanda nake kora aiki kazo kai min magana sai akanta, dan haka Wallahi bazanyi magana biyu ba, sai dai ni in bar aikin! ". Manager kama hanun Billy ya yi ya zaunar da ita, sannan ya ce, "Sweetheart ki gane yarinyar nan bazata koru ba.. ". Billy saurin amshe zan can ta yi, da cewa, "Saboda me ba zata koru ba ?". "Saboda Oga Habib ke son ta yi aiki anan gun, kuma yanzu haka matar shi ce". Billy cikin firgita ta ce, "Matar Wa wai? ".


Manager cikin natsuwa ya ba Farida labarin yadda akai auran Hassana da Habib, daga k'arshe ya d'ora mata da cewa, " Habib yana son Hassana tai aiki anan ne dan kawai ya nuna mata shi ba sa'anta bane, nina san haka, dan nasan Oga Habib sosai".


Farida cikin zuciyarta ta ce, "Aiko zan taya shi nuna mata shi d'in ba sa'anta bane".


Wani murmushi Farida ta yi, sannan ta kalli Manager ta ce, "Ok, badamuwa zata iya ci gaba da aiki....... ✍️



Idan kin karanta, d'aure ki Comment dear🀝.



Share
&
Comment please πŸ™.
πŸ“š OGA HABIB πŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

MASU COMMENT NA LAST PAGE NAGANI NAGODE SOSAIπŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»πŸ‘πŸ»
A YI HAK'URI DA REPLY DA BAN SAMU YI BAπŸ™.

MARASA COMMENT 🀐🀐🀐🀐.

https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/



Shafi na 56 & 57.




Wani murmushi Farida ta yi, sannan ta kalli manager ta ce, "Ok, badamuwa zata iya ci gaba da aiki, idan ka fita ka turomin ita".
Manager cikin jin dad'in amincewer Farida ya tashi ya fita daga Office d'in ta".


Tsaye manager ya iske Hassana da bilya. Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, " Ki je Supervisor na kiranki". Hassana office d'in supervisor ta Shiga".


Hassana ta dad'e tsaye, kafin Billy ta d'ago tana kallanta, sannan ta ce, "tom kamar yadda nace miki mun dakatar da ke aiki, hakane, saboda mun maida wata a madadin ki , amma yanzu za kina wanke toilet d'in gunnan, safe da kuma dare, sannan sai 10:00PM zaki rik'a close". Manager kallan Hassana ta yi, da ta kai baya nan ta, ta ce, "Za ki iya tafiya". Shiru Hassana ta yi, dan gaskiya ita bazata iya wankin toilet ba, saboda tana da kyankyami sosai. Batare da Hassana ta ce ma Billy ko mai ba ta fita daga office d'in, direct Hassana gun Bilya ta koma. Hassana kallan Bilya ta yi, cikin damuwa ta ce, "Oga Bilya gaskiya bazan iya aikin da ta banba, badan komai ba, inada kyankyami sosai". "Wana side ta mai da ke? ". Cewar Bilya ".


"Wankin toilet, na wajan nan". "Wankin toilet kuma!?". Bilya ya fad'i maganar dak'arfi". "Eh Oga Bilya ".cewer Hassana ".



Shiru Bilya ya yi sannan ya ce, "kin gane ko, ki ci gaba da aikin da kike yi da, ki rabu da ita, amma Wallahi karki sake ki wankin toilet". Sosai Hassana ta gamsu da maganar Bilya, hakan yasa tai mai godiya ta tafi".



Kasan cewar Hassana bata je da wuri ba, hakan ya sa duk kusan aikin da ta ke yi, anyi. Ya zamana Hassana sai zamanta ta yi, kusa da Amina tana taya su nasu aikin, su suna side d'in da ake yoghurt ne".


Hassana na Sanat yughurt har yanzu 9:15PM, abu d'aya ke da munta yadda zata koma gida dan idan dare ya yi gun akwai wahalar samun abun hawa, Hassana na nan zaune ita kad'ai dan Amina tun 8:00PM tai close. Kuma dama kusan da ita ne su ka saba. Hassana na nan zaune sai ga Bilya".



Bilya kallan Hassana ya yi da murmushin shi, ya ce, "Idan kin gama abinda ki ke yi ke na dawo d'auka". Hassana da mamaki ta ke kallan Bilya, ta ce, "Oga Bilya ni kuma". "Eh mana, yanzu nake Oga Habib, shi yasa na dawo kai amaryar shi itama ". Cewar Bilya yana dariya, dan ya lura Hasssana bata son yana had'a ta da Habib ". Aiko d'aurewa ta yi, ta ce, "kai! Oga Bilya, dan Allah na cema bana son wannan sunan". Dariya Bilya ya yi, ya ce, "Tom in dai bakya son sunan, nima daga yau ki bar cemin Oga, mijinki shine ya can-canta da sunan". Hassana tafiya ta yi tabar Bilya gun tsaye, dan ya gama b'ata mata rai ".


Bilya da dariya ya bi bayan Hassana. Motar da Bilya ke d'aukar Habib da ita yazo ya d'au Hassana".


Can gida ko, Habib ji ya yi yau babu abinda zai iyaci da daddare in ba kunun gyad'a ba, hakan yasa Bilya na aje shi ya Shiga part d'in Hajiya Turai da niyyarshi ko zaiga Baba Lami ya sata tai mai kunun".


Sai dai Habib na Shiga da Farida ya ci karo, tana kwance kan 3 seater tana charting. Farida na ganin Habib amma sai ta yi kamar bata gan shi ba, hakan duk yana cin darisoshin Hajiya Zaliha".


Habib kallan Farida ya yi, yai tsaki, ganin bata ma wai ganshi ba, hakan yasa cikin d'an d'aga murya ya ce, "Ke ina Baba lami". Farida tashi ta yi, zaune, cikin sanyayyar murya irin ta masu son yaudara, ta ce, "Oga Habib ka manta?, ai Baba Lami bata cika zama ba, in Mommy bata nan, kana son wani abune? ". Habib shiru ya yi, yana danna wayar hannun shi, sannan ya ce, batare da ya kalli ko kusa da inda Farida ta ke ba,ya ce, " Kin iya kunun gyad'a? ". Farida kamar tace a'a, inda ba iyawa tai ba, sai kuma ta yi tunanin ai hakama da mace, gara ta kira Mommy'n ta awaya ta fad'a mata yadda akeyi. Hakan yasa Farida ta ce, "Eh na iya, Oga Habib kana so inma? ". Dai-dai lokacin Hassana ta yi sallam cikin cool Voice d'in ta".



Hassana ja tai ta tsaya, dan tana rasa na tsuwarta sosai, aduk lokacinda zata ga Habib, tarasa me haka d'in ke nufi, dan da ba haka ta ke ji ba. Hassana jarumta ta yi ta k'arasa shigowa falon, sannan ta ce, "Ina wani Oga Habib". Habib banza ya yi da Hassana yana mai ci gaba da danna wayar shi, sannan ya kalli Farida ya ce, "Ki damanin yanzu sai ki kawomin".


Farida ko cikin jin dad'in abinda Habib ya yi ma Hassana, ta ce, "Tom Oga Habib ". Habib kuma juyawa ya yi ya fita, ya bar Hassana da zan can zuci, ta ce, "Haka ma fa d'azu da na gaida shi bai amsa min ba, aiko daga yau insha Allah bazan k'ara gaida shiba". Hassana juyawa ta yi zata Shiga ciki. Farida ta kirata da cewa".



"Ke". Hassana tsayawa ta yi, tana mai sauraran abinda Farida zata ce mata". Farida kuma ganin Hassana bata juyowa, cikin fad'a-fad'a ta ce, "Ke da allacan bada ke nake magana ba!? ". Hassana juyowa ta yi tana kallan Farida alamun ina jinki? ". "Kin Iya kunun gyad'a? ". Farida ta tambayi Hassana. Shiru Hassana ta yi, dan tasan Habib ne yasa Farida shine ita kuma zata sata. "Eh". Hassana ta ce ma Farida".


"Yauwa tom zaki min yanzu nan, ina zuwa". Farida fita ta yi ma Maimuna magana, ta na son ta bata kamu zanyi kunun gyad'a yanzu. Farida kitchen ta shiga ta d'iboma Farida , da yake yana cikin freazier ta kawo mata".


Farida kuma Hassana ta kaimawa. Hassana amsa ta yi, ta shiga kitchen d'in falon Hajiya Tura".


Cikin minti 10 Hassana ta dama Kunun gyad'ar ta kaima Farida".


Farida ko sai da ta kuma shafa powder a fuskarta sannan ta d'auki kunun gyad'an ta yi side d'in Habib da shi".


Habib na kwance kan caution, dan yunwa ya ke ji sosai. Farida ta yi nocking. Habib izinin shiga ya bata".


Farida cikin yauk'i da kisisina ta isa inda Habib ya ke kwance, ta aje cup d'in kunun, ta ce, "Oga Habib ga kunun nan nagama". Habib kallanta ya yi, kamar Wanda baya son magana, ya ce, "Thanks". Farida har ta juya zata tafi ta dawo tana kallan Habib, ta ce, "Oga Habib idan kana buk'ata zan rik'ama kullum".aiko Habib sosai yaji dad'in hakan, dan babu abinda yake so yasha da daddare in son samu ne kamar kunu. Batare da Habib ya nuna ma Farida jin dad'in shi ba, ya ce, "Eh zaki iyayimin". Tom kawuta lafiya, sai da safe". Farida na kaiwa haka ta fita, tana mai murmushin ganin nasara kusa".



Hassana ko na nan zaune tana kallan Farida ta d'auki kunun gyad'an ta fita da shi, ko ba afad'a mata ba tasan side d'in Habib Farida ta nufa. Hakanan Hassana ta riski kanta cikin wani irin bak'in ciki da b'acin rai, haka dai Hassana ta kwanta cikin damuwar da ita kanta a yanzu bata san ta mecece ba, ahaka bacci b'arawo ya yi awan gaba da ita".


Washe gari Hassana da wuri ta shirta ta tafi aiki. Sai dai Billy na zuwa ta hana Hassana zama, daga tasata abu tagama sai ta bata wani. Haka dai tai ta kalato aiki tana sa Hassana. Aranar dai Hassana da gajiya sosai ta koma gida".


Yauma Bilya ne yazo ya d'auketa bayan ya kai Habib".



Hassana na isa gida kuma, ta iske Farida tana jiran ta dawo tai mata kunun ta kaima Habib".


Aiko haka akayi, Hassana ko zama bata yi ba, Farida ta ce mata tana son tai mata irin kunun jiya. Hassana haka ta daure ta shiga kitchen ta damoma Farida ta ka wo mata. Farida kuma ta ta d'auka kamar jiya ta nufi side d'in Habib da kunun".


Farida tana zuwa taima Habib nocking. Ya bata izinin shiga ta shiga ta kaima Habib kunun".


Yauma kamar jiya ba yan ta aje kunun ta kalli Habib ta ce, "Tom Oga Habib na barka lafiya sai da safe". "Yauwa Farida nagode ". Cewar Habib. Dan sosai yaji dad'in kunun, Allah yasa irin na jiya ne yace azuciyar shi".


Farida kuma har zata wuce ta fasa, ta ce, "Oga Habib ai kafi k'arfin haka awajena, abin harda godiya dan naima kunu, abinda zan iyama fiye da goma arana idan kana so, ni dai addu'a ta d'aya gareka, Allah ya baka mata ta nunama abokai, irin wadda ta iya f.... ". Tsawar da Habib ya yi ma Farida ce tasa tai shiru, ta fita da sauri".


Habib kuma ji yayi ranshi ya b'ace, dan yama manta da wata Hassana, amma wannan mahaukaciyar tana son tuna mai da abinda ya manta da shi".



BAYAN SATI D'AYA.

Hassana kullum ta je aiki da abinda Billy ke sata, in dai ta samu hutu tom Billy ta yi close ne , sannan Hassana ke samun hutu. Kuma har yau Billy bata san Hassana bata wankin toilet ba".



Kuma har yanzu kullum Bilya ke Kai Hassana gida. Daga taje kuma zata iske dama kunun Habib, wanda yake a matsayin Farida ta dama. Hassana har ta saba da dama kunun Habib".


Farida ko tun ranarda taima Habib ta tabar gazar zance, ya bar sakar mata fuska in ta kaimai kunun. Kuma kullum in Farida ta kaima Habib kunu ta fita, mai makon ta koma part d'in Hajiya Turai, sai ta zauna awaje ta gama danne-dannan wayarta sannan zata shiga ciki, duk dan Hassana ta d'auka awajan Habib d'in ta dad'e haka".



Hassana yauma ta yi kwalliyar ta cikin gayan da Hajiya Turai ta sai mata, ta yi kyau sosai, sai d'an fad'a wa da ta yi kad'an a fuska. Hassana na zuwa Billy ta sata aikin da tasaba sata, da ta gama kuma ta ce ta yi wancan. Bayan Hassana ta gama Mopping d'in Office d'in Billy, ta fi to zata fita Billy kuma zata shigo, suka ci karo da Billy, aiko Billy ta d'aga hannu ta wankama Hassana mari mai gigita k'wak'walwa".



Hassana dafe gurin ta yi ta d'ago tana kallan Billy da idonta da ya kad'a ya yi jajir lokaci d'aya ta ce, "Supervisor mari kuma!? ".Billy cikin gadara da ji da masifa ta kuma d'aga hannu ta wanke Hassana da mari, ta ce, "Na mareki!, ki yi abinda zaki y... ". Billy bata rufe baki ba Hassana ma ta wanka mata mari, ji kake fassss, ta kuma sake wanka mata wani ta d'a yan gefan".


Ai take danbe ya kaure tsakanin Hassana da Billy. Manager da ke Office da sauri ya fito Office d'in shi ya zo gun fad'an, ammma babu yadda manager bai yi ba ya kasa raba fad'an,Billy wata stick da ke kusa da ita ta d'akko zata bugama Hassana aka samu kuskure ta bugama Manager, kafin kace me duk staff's din suka taru gurin, sannan manager ya rik'e Billy Bilya kuma ya rik'e Hassana".


Amma duk da haka Billy fusgewa ta ke ita sai ta koma ta bigi Hassana, manager kuma na k'ara rik'e ta".


Habib kuma jin hayaniya ta yi yawa, da sauri ya fito daga office d'in shi. Cikin sauri yak'araso gurin da yaga taron staff's d'in shi agun. Habib yana k'arasowa ya fahimci abinda ke faruwa dan yaga manager na rik'e Billy tana fusgewa tana arabu da ita sai ta yima yarinyar nan hankali. Habib kallan manager ya yi ranshi b'ace ya ce, "Manager karabu da ita mana ta je ta bugeta d'in!, dawa suke fad'an? ". Habib ya tambaya cikin fad'a".



Manager nuna ma Habib Hassana ya yi da ke gefe ra kub'e, Habib juyawa ya yi, ya bar gun, ya ce, "Manager su saman a Office ".


Manager kallan Billy ya yi, ya ce, "Billy M. D, ya ce kusa mai a Office ". Billy office d'in Habib ta nufa, Hassana kuma ta mara mata baya".


Habib na zaune, yaji nocking. Izinin shiya ya bada , Billya ta shiga, Billya na shiga ba dad'ewa Hassana ma ta shiga".



Habib ya dad'e yana aikin gaban shi , sannan ya aje pen d'in hannun shi, ya kalli Billy ya ce, "Kafin mu d'aukeki aiki sai da akace miki babu fad'a, me yasa haka ta faru? ". Habib ya tambayi Billy yana kallan ta ".



Billy ma Kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib ba laifina bane, kowa yana bin doka a factory nan, amma banda Yarinyar nan". Billy ta nuna Hassana. Ta ci gaba da cewa. "Oga Habib, kullum sai tazo late kuma tana close lokacinda taga dama, shine yau nai mata magana akan late d'in da ta ke zuwa, shine fa nake mata fad'a ina nuna mata ba haka aike aiki ba. Shine fa daga haka sai mari wai ni ban isa in tsaya ina fad'a mata haka ba, wai duk factory nan babu wanda ya isa yasata abinda ba ta yi niyya ba, marinda tai min ne yasa na rama , Oga Habib, dan Allah ka yi hak'uri ".


Habib mai da kallan shi ya yi ga Hassana, ya ce, "Ke ma haukaciya ko?, baki da hankali ko?". Habib mai da kallan shi ya yi ga Billy ya ce, "zaki iya yanke mata hukuncin da ya yi dai-dai da abinda ta aikata".Billy cikin salon munafinci ta ce, "Babu komai na yafe mata Oga Habib ". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Rok'arta ta ya fe miki".


Hassana shiru ta yi kamar bata za tai magana ba, ta ce, "Oga Habib ni ban mata komai ba, hasalima ita tai min".


Billy kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib baka santa bane, ni ce zata rok'a yafiya, dan Allah ka barta kawai, ni ba sai ta rok'an ba ma, na barta da halinta zata had'u da dai-dai da ita".



Habib kallan Hassana ya yi alamun ba wasa, ya ce, "Ke rok'arta ta yafe miki? ". Hassana abinda ta mai-mai ta ma Habib ta kuma mai-mai mata mai. "Oga Habib ni ban mata komai ba, hasalima ita ce tai min".


Habib sosai

Please Login or Register in order to submit comment