Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dafe da kanshi yana rirrin tse ido. Hassana da sauri ta dawo cikin bedroom d'in, dan ita har yanzu bata gama yadda Habib ya warke gaba d'aya ba. Hassana cikin damuwa da yanayin da taga Habib d'in ta kamo hannun Habib d'in ta ce, "Ayyyah Oga Habib Sannu, nasan yunwa kake ji, inda yau kak'i cin komai, in kawo ma abinci kaci? ". Habib da mamaki ya d'ago kai yana kallan Hassana, gashi abin haushi yana jin kamar baya iya magana, tsananin ciwan da kanshi ya ke. D'agowar kan da Habib ya yi Hassana ta kalli k'wayar idon shi ta ga ta yi jawur. Hassana cikin tausan Habib d'in kamar zatai kuka, dan ita harga Allah bata mai kallan wanda ya warke gaba d'aya, kawai dai tana mai kallan ciwan nashi ya canza sifiri ne. Hakan yasa Hassana ta kuma cewa, "Oga Habib in kawo ma abinci ko? ". Hassana ganin Habib ba amsa mata zai yi ba, yasa ta rabu tashi ta je kitchen ta zibo mai jolop rice d'in da ta yi, ta kawo mai, dan dan tun jiya take fama da Habib akan cin abinci yak'i".


Hassana kusa da Habib ta zauna ta d'ibo abincin a spoon, kamar yadda ta saba yi ma Habib d'in wani lotun, ta ce, "Oga Habib bud'e bakinka please kaci ko kad'an, kaga tun jiya baka ci abinci ba". Habib ko da ciwan kai ya dama, da mamaki ya ke kallan Hassana ga magana ma wuyar yi ta ke mai. Haka nan Habib cikin k'arfin hali ya ce ahankali canciki, "Kin san Allah idan har biki bar d'akin nan ba, na tashi,,,,, ". Habib ya k'arasa maganar da girgiza kai". Hassana aje abincin ta yi, tana mai k'ara gasgata maganarta ta Habib ya warke. Hakan yasa Hassana aje mai abincin ta juya ta fita. Hassana wayar da Hajiya Turai ta bata ta d'auka, ta kira Hajiya Turai, Allah ko ya tai maka, kira d'aya Hajiya Turai ta d'aga".

Hasssana cikin murna, ta gaida Hajiya Turai, bayan sun gama gaisawa ne, Hassana ta ce, "Mommy Wallahi Oga Habib ya warke,yanzu haka maganar da nake yi dake Oga Habib na magana". Hajiya Turai cikin tsantsar farinciki ta ce, "Daughter nasan ba kimin wasa, dan Allah da gaske Habib d'ina ya warke?, kuma har kinji maganar shi? ". "Mommy Oga Habib ya warke tabbas, kuma naji maganar shi". Cewar Hassana. "Tom me yace miki, daughter? ". Hassana shiru ta yi, dan sai yanzu ne ma taji zafin abinda Habib ya ce mata".

Hajiya Turai ko jin Hassana ta yi shiru ya sa, ta ce, "Hello daughter kina jina, kuwa, ba Habib d'in wayar". Hassana koma wa bedroom d'in Habib ta yi, har yanzu Habib na zaune kamar yadda ta bashshi. Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "Oga Habib Mommy na magana a waya? ". Habib d'ago kai ya yi yana kallan Hassana, sannan jin ta ce, Mommy ya amshi wayar ya kanga a kunne, duk da yana jin kamar ba zai iya magana ba".

Hajiya Turai ko, cikin k'osawa ta ce, "Hello Habib kana jina? ". Habib cikin dauriya da jarumta da yadda ya ke ji, ya ce, "Eh Mommy inaji". Hajiya Turai cikin murya mai kama da ta kuka ta ce, "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! alhamdullah!!!, Allah nagode maka da kanuna min wannan rana, Habib kana jina? ". "Eh Mommy inaji". Habib magana ya ke so yima mahaifiyar tashi doguwa, amma ya kasa, tsabar ciwan kai".

Hajiya Turai cikin Sanyi ta ce, "Sannu Habib Allah ya baka lafiya baki d'aya, ina nan da wowa gobe insha Allah, yanzu ba daughter wayar". Habib daughter ya mai-mai ta azuciyar shi, yana mamakin ita d'in wacece.Habib mik'ama Hassana wayar ya yi, yana mai nuna mata hanyar fita, alamun ta amshi wayar ta fita. Hassana amsar wayar ta yi ta fita, tana mai sauraran Hajiya Turai. Hajiya Turai ko ta ci gaba da cewa, "Daughter naji har yanzu bashi da lafiya, tom nasan Habib da gaddama mare in kira Family doctor mu ya duba shi, amma insha Allah gobe da wuri zan shigo". "Tom mommy Allah ya kawoki lafiya, mommy ki kira idan da akwai Wanda Oga Habib zai yarda ya kwana da shi". Cewar Hassana. Hajiya Turai cikin sauri ta ce, "Daughter ke fa? ". "Mommy wallahi ya ce in dai ya tashi ya ganni a d'akin zan sani, ni dai Mommy dan Allah part d'in ki zani in kwana". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Tom shikenan daughter amma dan Allah da safe ki yi k'ok'ari kizo da wuri ki duba shii, dama Bilya na nan ne, tom kinga Bilya na zaria, amma zan kira shi yanzu in ce mai yadawo gobe". Hajiya Turai kashe wayar ta yi".


Hassana ko juyawa ta yi ta fita , ta nufi part d'in Hajiya Turai".

B'angaran Habib ko da kyar ya iya tashi ya d'auki abincin da Hassana ta kawo mai ya ci. Habib na gama cin abincin wani wahalallan bacci ya d'auke shi.
Shine fa Habib bashi ya farka ba, sai washe gari, dalilin Farida".


Farida na shiga gidansu Oga Habib, tsayawa ta yi dai-dai k'ofar Falon Habib d'in, ta ciro maganin da boka ya bata ya ce, ta tauna duk abinda ta ce ma Habib zai yi. Aiko haka Farida ta ciro maganin ta tauna, sannan ta ciro wanda ya bata ya ce duk abinda tasa Hassana ba za ta yi mata gadda ma ba, shima ta tauna, sannan ta d'akko na wanke fuskar ta wanke fuskarta, shi kuma wanda ya ce, duk wani aibunta da ya hana Habib d'in ya so ta, tom kamar shine ta wanke. Farida nagama magungunan ta, ta fara nocking d'in k'ofar falon Habib da k'arfi".

Habib da tun baccin jiya da ya kwanta bai tashi ba, bayan ya gama cin abincin da Hassana ta kawo mai. Habib cikin bacci ya jiyo yadda ake bun k'ofar, cikin mamaki da al'ajabi Habib ya tashi, Alhamdulillah yau sosai yaji k'arfin jikin shi, sai abinda ba'arasa ba, Habib cikin sauri yanu fa k'ofar dan ganin mara hankalin da yake mai nocking haka. Habib na zuwa cikin fad'a-fad'a ya ce, "Wa ye? ". Farida da k'osawa ta sa ta kasa fahimtar muryar waye, ta ce, cikin k'osawa, kuma ita ma cikin fad'a-fad'an dan ta zaci Hassana ce, ta ce, "Bud'e ki gani mana, 'yar rainin hankali, daga yau ne dai". Habib cikin b'acin rai ya bud'e k'ofar, yana kallan Farida fuska d'aure babu alamun fara'a ya ce, "Farida dama nafara wasa da ke? ". Farida cikin al'abi da mamaki ta ke kallan Habib, kai ko dai maganin da boka ya bani ne ya warkar da shi, tun kafin in sa mai, Farida kallan Habib ta yi tana sosa k'eya ta ce, "Oga Habib dama wata magana ce nake so muyi dan Allah ". Habib ko da mamaki ya kalli Farida, amma ganin sammakon da tayi, da kuma yana son tambayarta dan yana buk'atar amsar tambayar shi kafin Hajiya Turai ta dawo. Habib cema Farida ya yi, "Ok, inajinki? ". Farida ko najin haka ta kuma tabbatar da maganinta ya yi wato yana jinta, Lallai wata sabon gani, hakan yasa Farida dan k'ara tabbatarwa ta ce, "Uhm Oga Habib dan Allah mu shiga daga ciki mana? ". Habib batare da yayi ma Farida musu ba, yashiga, Farida kuma tabi bayan Habib tana mai tabbatar da aiki yagama yi".


Habib kallan Farida ya yi, alamun inajinki. Farida cikin bada umarni, ta ce, "Oga Habib so nake ka saki Hassana yau-yau d'innan ". Habib da mamaki ya ke kallan Farida. Farida kuma ganin Habib na kallata ta ce, "Ko ba zaka iya bane? ". Habib shiru ya yi, na farko abinda ya bashi mamaki ganin yadda Farida ke mai magana cikin bada Umarni, na biyu kuma, tabbas yarinyar da yagani jiya ita ce Hassanar, idan ita ce, tom meye dangan takar shi da ita? ".

Farida ko ganin Habib ya shiga kogon tunanin, ya sa ta kuma cewa, "Oga Habib dan Allah kai nake jira, kace ka saki Hassana saki Uku, idan Mommy ta tambaye ka kace mata kai bazaka iya zaman aure da ita ba, kai ni kake so".
Habib dafe ganshi ya yi, dan tabbas ko a yadda ya ke jin jikin shi ya tabbatar mai akwai abinda ke faruwa dashi, jiya ya farka yaga wata atare dashi ad'akin shi, yau kuma wannan ma haukaciyar tazo tana mai wasu maganganu marasa ma'ana, Habib kallan Farida ta yi, ya ce, " Tom jeki zanyi". Habib ya ce ma Farida haka ne kawai dan baya son ya kuma jin wata maganar da zata k'ara mai wani tunanin, hakan yasa ya ce ma Farida, tom ta je zai yi".Farida fita tayi tana mai jin dad'in furicin Habib, dan tabbas aiki ya yi, dan idan ba haka ba, tasan Habib sare da yazun ya yi maganin ta".


Habib ko zama ya yi shi kad'ai yama rasa kalar tunanin da zai yi, wai meke faruwa da shine?, me Farida ke nufi ne?".

Habib wayar shi ya fara naima ya kira Bilya dan samun amsoshin tambayoyin shi. Babu inda Habib be duba ba, amma ba wayar shi. Toilet ya shiga ya yi wanka, bayan ya fito ne ya shafa lotion ajikin shi, sannan ya bud'e sip d'in kayan shi, amma abinda ya bashi mamaki kayan mace agefan kayan shi, Habib cikin al'ajabi da mamaki ya ke bin kayan Hassana da kallo. Habib daurewa ya yi ya kauda komai, ya ciro kayan shi ya sa, ya adana tambayoyin shi sai Hajiya Turai ta dawo, amma tabbas ya san akwai babban al'amari da ke faruwa da shi, ko kuma ya faru da shi, dan ko yana yin yadda yake jin jikin shi yana kuma tabbatar mai da hakan.
Bayan Habib ya gama shiryawa, kitchen ya shiga, nanma yasha mamaki, nan ma dai haka ya kauda mamakin shi gefe ya had'a ma kanshi tea ya fito".


K'arfe goma sha d'aya na safiya jirgin su Hajiya Turai ya sauka. Kasan cewar Hajiya Turai ta san Bilya baya nan, yasa ta d'au drop d'in mota ta kawota gida".


Hajiya Turai direct part d'in Habib ta nufa. Habib na kwance ya ji nocking , ya zo sai dai sosai abin yazo mai a ba zata, dan bai yi tunanin dadowar Hajiya Turai yau ba , dan bata cewa gata nan tazo sai tai sati tana sa rana".

Hajiya Turai cikin tsantsar farincin da ta kasa b'oyewa ta rungume Habib tana mai cewa, "Alhamdulillah, tabbas duk abinda ya yi farko zai yi k'arshe, kuma babu abinda ya gagari Allah, Sannu Habib Allah yasa wannan ce k'arshen wahalarka a duniya da lahira"."Ameen Mommyna, mu shiga ciki ki futa".


Hajiya Turai tana rik'e da hannun Habib suka shiga ciki, Hajiya Turai zata zauna kenan, Habib ya ce, "Mommy karki zauna zoki ga wani abu". Hajiya Turai tashi ta yi ta bi Habib".

Habib ko wajan sip d'in kayan shi ya kai Hajiya Turai, bud'e sip d'in ya yi, sannan ya ce, yana mai nuna kayan Hassana ya ce, "Mommy kayan Waye nan?". Hajiya Turai kallan Kayan Hassana ta yi, dake jere kusa da na Habib. Hajiya Turai kama hannun Habib ta yi, ta ce,............ ✍️.



In kin karanta daure ki yi Comment sister 🤝.


Share
&
Comment please 🙏.

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*
TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).

https://chat.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7

https://m.facebook.com/groups/565235401564189/

Shafi na 50&51.



Hajiya Turai kama hannun Habib ta yi, ta ce" Habib ka yi hak'uri in nasamu natsuwa zuwa anjima sai mu yi magana". Habib da tom ya amsa ma ma haifiyar shi ba dan ya so ba, so ya yi ta bashi amsa yanzu. Hajiya Turai kallan Habib ta yi ta ce, "Bari in shiga ciki, zuwa anjima sai kazo muyi maganar inda naga ka matsu". "A'a Mommy ba wai na matsu bane, kawai dai ina mamakin yadda kayan mace ya had'u da kayana ne waje d'aya, kuma na farka naganta anan, tom shine abin ke ban mamaki, kuma duk bansan ta yadda hakan ta faruba, sannan yau Farida ta zo mun da wata magana wadda ta kuma tabbatar min da akwai wani b'oyayye al'amari da ke faruwa". Habib ya idasa maganar cikin damuwa. Hajiya Turai kallan Habib ta yi, sannan ta ce, "Shikenan ni zan shiga ciki, kasaman anjima kamar yadda na ce ma, sai muyi maganar".


Hajiya Turai fita ta yi daga side d'in Habib ta nufi nata part d'in. Hassana na kwance tun da ta tashi da safe ta ke kwance kan caution, haka nan Hassana ke jinta wani iri duk ba dad'i, kamar a mafarki Hassana ta ji sallamar Hajiya Turai. Hassana cikin nuna murnarta naganin Hajiya Turai ta tashi ta zauna tana, "Oyoyo Mommy". Hajiya Turai murmushi ta yi tace, "Oyoyo daughter". Hassana cikin fad'ad'a fara'ar fuskarta suka gaisa da Hajiya Turai. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter ya k'ok'ari na tafi na barki da mara lafiya, ikon Allah yau satina biyu kenan da tafiya". "Kai Mommy har kin yi sati biyu? ". Cewar Hassana. "Eh daughter, bari in shiga ciki in watsa ruwa in kwanta ". Hajiya Turai bedroom d'in ta ta shiga ta watsa ruwa sannan ta kwanta".


Hassana ko haka taita juyinta kan caution, ita kanta bacin kayanta na side d'in Habib da wanka ta yi, amma tasan ko karan hauka ya cijeta ba zata iya zuwa ba ta d'akko ba. Hassana na nan kwance har aka kira sallar azahar, tashi ta yi tai alwallah ta tada sallah, Hassana na zaman tahiyar k'arshe Habib ya yi sallama ya shigo falon. Kan 2 seater Habib ya zauna yana jiran fitowar Hajiyarsa, dan a tunanin shi tana ciki tana sallah. Shiru-shiru Habib ya ji har yanzu Hajiya Turai bata fito ba, dan in sallah ta ke, yaci ace ta idar. Habib jin shirun ya yi yawa, yasa ya nufi bedroom d'in Hajiya Turai, kwance Habib ya isketa tana bacci Sosai, kamar karya ta data, amma ganin lokacin sallah ya yi yasa ya tada ta. Hajiya Turai kallan Habib ta yi ta tashi zaune tana mai ma mamakin ganin lokacin da ta d'auka tana bacci. Habib ma kallan Mahaifiyarsa ya yi, ya ce, "Mommy anyi sallah fa". "Subhallah!, wannan wana irin bacci nayi haka, da har akai sallah ban ji ba ". Hajiya Turai ta shi ta yi ta nufi toilet, saida ta kuma sama jikinta ruwa sannan ta yi alwallah ta fito, lokacinda ta fito Habib ya fita ya koma falo. Hajiya Turai sai da ta shirya ta yi sallah, sannan ta je falon, inda ta iske Hassana zaune kan sallaya, Habib kuma kwance kan 3 seater kan shi sama. Hassana da ke zaune tana jinta duk a takure ganin Habib a falon, cikin na tsuwa Hassana ta kalli Hajiya Turai ta ce, "Barka da fitowa Mommy ". "Yauwa daughter, Maimuna ta ko san da dawowa ta?, ko ta shigo da abinci ne?". "A'a Mommy bata shigo da abinci ba, ina jin bata san kin dawo ba". Cewar Hassana. Hajiya Turai waya ta ciro ta kira Maimuna, maimuna nad'agawa, Hajiya Turai ta ce, "Hello Maimuna ya naga har yanzu ba'a shigo da abinci ba". daga can b'angaran Maimuna tace, "Hajiya Wallahi ban san kin dawo ba, kuma yanzu ba girki akema Oga Habib ba, amma yanzu bari ayi da sauri, me za ayi Hajiya? ". " ki yi Simple food kawai". Cewar Hajiya Turai, sannan ta datse kiran".


Hajiya Turai zama ta yi, sannan ta kalli Hassana ta ce, "Daughter zo ki zauna nan mana". Hajiya Turai ta nuna ma Hassana kusa da ita". Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "Mommy ina son zan yi wanka ne". "Tom ki je ki yi mana daughter, ki shiga toilet d'ina ki yi". Hassana tom ta ce, sannan ta ce, "Mommy kayana na can". Habib sai yanzu ya waigo ya kalli Hassana jin ta ce kayanta na can, wato ita ce ta sa kayanta cikin nashi".


Hajiya Turai sanyi ta yi itama , ganin yadda Hassana ta yi sanyi kamar a takure ta ke, dan ko yana yinda ta ke magana kasan takure ta ke. Hajiya Turai tashi ta yi tazo har inda Hassana ta ke tamo hannunta ta ce, "zo ki je ki yi wankan ki, kinada kayan sawa nazo muki da kaya bari in aika a d'akko miki, nabar jakar kayan wajan mai gadi, lokacinda na iso mai gadi d'aya ne awajan get d'in". Hajiya Turai na rik'e da hannun Hassan suka shiga bedroom d'in Hajiya Turai. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce, "Daughter ki saki jikinki mana, kinga ko yadda kike yi?, ko kina so Habib ya rainaki ne?, kina nufin Saboda Habib kike d'ari-d'arin nan?, tom banji dad'in ganinki haka ba, ina son in rik'a ganinki kamarda, in ma d'aurewrar Habib ce tom karki yi tunanin ko mai, nature na shi ne, haka Habib ya ke tun yana yaro, idan ba ni ba ko friend's d'in shi, tom zan iya ce miki babu wanda zakiga Habib ya zauna da shi suna fira, tun abin na damuna har ya ma daida damuna, kuma ak'idarsa ce ko nima bai cika min yawan magana ba idan yana ganin wani kusa, dan Allah daughter ki saki ranki ki dawo kamar da ". Bud'e baki Hassana ta yi za tai magana, Hajiya Turai ta rufe mata baki, ta sa mata d'an ya tsa abaki, ta ce, "ki shiga ki wanka daughter idan kin shirya sai muyi maganar da kike son yi". Hassana juyawa ta yi ta shiga toilet d'in, kamar yadda Hajiya Turai ta buk'ata. Ita kuma Hajiya Turai fita ta yi, ta sa aka d'akko mata jakar kayan da ta siyoma Hassana, ta kai ta bedroom d'in ta, ta ce, "Daughter ga kayan nan, naki ne duka kisa wanda kike so". Sanan Hajiya Turai ta fita ta koma falon. Hajiya Turai na zama Maimuna na shigowa ta ce, "Hajiya ko mai na dernin". "Ok, me kika dafa ne? ". Cewar Hajiya Turai. "Cous-cous". Maimuna taba Hajiya Turai amsa"..


B'angaran Hassana ko tana fitowa ta shafa lotion d'in da taga Hajiya Turai ta aje mata, sannan ta bud'e jakar kayan da Hajiya Turai ta ce tata ce duka, Sosai Hassana ta ya ba da kyan kayan, dogayan riguna ne kala-kala da riga da siket na kanti, da gyalilluwa da ta kallama na sawa masu kyan gaske, Hassana ganin kayan da yawa wata doguwar riga red color da ta ji adon stone ta d'akko ta sa, sannan ta d'akko d'an kwakin rigar da yake babba ne ta yafa ta samu gu ta zauna, dan tafi son lokacinda zata fita ace Habib baya nan ya tafi".


Can b'angaran Hajiya Turai ko jin Hassana shiru, tashi ta yi ta nufi bedroom d'in ta, zaune ta iske Hassana. Hajiya Turai girgiza kai kawai ta yi, sannan ta ce, "Daughter muje mu ci abinci, ke muke jira". Hassana bayan Hajiya Turai ta bi suka fita. Sai dai Hassana bata ji dad'i ba ganin Habib har yanzu yana falon. Hajiya Turai kallan Habib ta yi, ta ce, "Habib muje ga abinci can". Habib b'ata fuska ya yi ganin Hassana kusa da Hajiya kenan harda ita zasu ci, Habib sharewa kawai ya yi badan ya soba ya tashi ya nufi derning space d'in".


Hajiya Turai da kanta ta yi seven's d'in Hassana da Habib. Ba laifi Habib ya ci dadama amma Hassana tsakura kawai ta yi, Hajiya Turai dai na kule da Hassana, amma sai bata tanka mata ba. Bayan Habib ya gama cin abincin, kallan Hassana ya yi, ya ce, "Bamu gu zamu yi magana". Dama Hassana tun-tuni ta aje spoon d'in ta alamun ta k'oshi. Habib ko na cewa bamu gu, kamar jira ta ke ta tashi zata tafi. Hajiya Turai kallan Hassana ta yi ta ce ,"daughter koma ki zauna". Hassana komawa ta yi ta zauna. Habib haka d'in da Hajiyarsa ta yi, shi kuma sai ya b'ata mai rai, acewar shi bazai magana gabanta ba, hakan yasa ya tashi ya ce, "Mommy please ina wayata zan yi amfani da ita ne? ". Hajiya Turai kallan Hassana ta yi, ta ce, "Daughter ina wayar shi? ". Hassana cikin sanyin muryarta ta ce, "Mommy tana sip d'in k'ayan shi". "Ok jeki d'akko mai". Cewar Hajiya Turai. Hassana tashi ta yi ta fita".


Habib kuma ganin haka komawa ya yi ya zauna, ya kalli Mahaifiyarsa ya ce, "Mommy wai ita d'in Wacece?, kuma me ya kaita side d'ina da har zata aje kayanta anan?, wai Mommy taya haka ma ta faru bansani ba!? ". Habib ya fad'i maganar cikin damuwa. Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Habib wato abu mai girma ya faru da kai, idan zaka iya tunawa lokacinda zan tafi London ka ce min kana fama da wani irin ciwan kai, ahaka dai na tafi nabarka, mu kai da kai zaka je hospital adubaka, tom Habib bayan tafiya ta akakirani ake sanar dani wai baka da lafiya yanzu haka baka san inda kanka ya ke ba, kuma abinda ya tada masu Bilya hankali da sauran ma'aikatan wajanku sai ciwan yazo maka da duka, dan duk wanda ka rik'e sai an kwace shi , Hassana ka d'ai ya rinyarda ke aiki a Sanad yoghurt, yarinyar da ke zaune gidan nan, da ita ka d'ai kake yarda da ita,dan Habib ko ni da na dawo ban isa in shiga inda kake ba. Hassana kad'ai ke baka abinci ka ci, ita kad'ai ke baka magani kasha, ita kad'ai ke shiga inda kake ta zauna, amma in ba itaba duk wanda ya shiga sai an k'wace shi a hannunka, wannan da lilinne yasa na had'a ka aure da Hassana, dan ba zai yuwuba tana shiga inda kake har ta kwana a matsayinta na mace wadda ba muharramarka ba". Shiru Hajiya Turai ta yi, sannan ta ce, "Tom kaji abinda ya faru Habib, amma abinda baka gane ba zaka iya min tambaya".


Shiru Habib ya yi kamar ba zai yi magana ba, sai zuwa can ya ce, "Mommy ciwan hauka na yi kenan". Habib ya fad'i maganar cikin damuwa. "Eh Habib kusan haka za'ace, amma ai yanzu komai ya wuce sai dai kuma ka gode ma Allah da ya baka lafiya, da kuma Hassana , dan ita taima komai". Habib kallan Mahaifiyarsa ya yi ya ce, "Ko mai kamar me da me mommy? ". "Habib komai da kasani Hassana kema shi, danma wani abun da ka fara kwaikwayanta ne, aka samu sauk'i, kake ma kanka". Habib cikin damuwa da tashin hankali ya ce, "Wanka fa , wake min? "., ya yi maganar kamar zai yi kuka. Ita Hajiya Turai dariya ma yaso ya bata, sannan ta ce, "Habib yarinyar nan fa ba kad'an ta yi aiki da kai ba, ko mai da kasani ita kema". "Wayyo Mommy kin kasheni, taya ma za'arasa wadda zata kula da ni sai wannan yarinyar, haba Mommy wanan ma ai Islamicaly babu kyau! ". "A'a nikam banga rashin kyu ba, dan haka nema gudin sab'ama mahaliccin mu aka had'a ku aure". Cewar Hajiya Turai. Habib kallan Hajiya Turai ya yi, ya ce, "Mommy ina fatan babu wanda ya san da maganar auran nan a cikin friend's d'ina? ". "Eh babu". Cewar Hajiya Turai. "Yauwa naji dad'i, amma Mommy ai shikenan ko kin warware auran ko? ". Shiru Hajiya Turai tai ma Habib. Habib ko jin Hajita Turai bata bashi amsa ba, sai ya ce, "Shikenan Mommy nawa kika ga ya kamata a biya yarinyar?,, dan zuwa yanzu ma ya kamata ace ta koma gidansu". Nan ma dai Hajiya Turai shiru tai ma Habib bata tanka mai ba".


Habib ko bai gaji ba,

Please Login or Register in order to submit comment