Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah sarki tsaye suka iske Hassana ko ina najikinta rawa yake, aiko suna zuwa suka tasa k'eyarta suka ce"Muje ". Hassana ihu ta kama tana rok'ansu tana cewa, "Dan Allah ku yi hak'uri, dan Allah ina rok'anku..... ". Haka Hassana tai ta kuka tana rok'insu su rabu da ita, amma ko sauraranta basu yiba".


Suna zuwa dai-dai saitin Habib Hassana ta rik'o hannun Habib tana kuka, tana cewa, "Wayyo Allah Oga Habib dan Allah karka bari su tafi dani... ". Habib kallan Hassana kawai ya yi, yarasa bakin magana, idan ma zai yi maganar bai san me zai ce ba".


D'aya daga cikinsu ko tun kud'a Hassana ya yi da k'arfi wanda yasa ta saki hannun Habib bata shirya ba. Habib na tsaye yana kallan su haka suka fita da Hassana tana ihu tana kiran sunan shi".


Habib cikin tashin hankali ya ciro waya ya kuma kiran commissioner of police, amma bai d'aga ba, haka Habib ya yi ta kiran shi shi kuma yak'i d'agawa. Can Habib ya ji tashin bindiga kota ina. Habib bud'e k'ofar ya yi ya fito, ji ya yi an fisgo hannun shi. Cikin tsoro Habib ya ke kallan wanda ke rik'e da hannun shi. K'asa-k'asa wanda ya rik'e hannun Habib d'in ya ce, "Ranka shidad'e karka damu, ma'aikatanmu duk suna nan, tun da kakira ai muka zo, yanzu haka anbisu,ka yi hak'uri ka koma ciki insha Allah babu abinda zasu yi mata". D'an sanda kama hannun Habib ya yi ya maida shi har falon shi, sannan yaja mai k'ofar, ya fita".


Haka Habib ya zauna yana mai jiran tsammanin ganin andawo da Hassana amma shiru. Wayar shi ya d'auka ya kuma kiran commissioner amma bai d'auka ba. Habib ya'aje wayar kamar da minti biyar kira ya shigo wayar shi, d'agawa ya yi, yana d'auka akace ranka shidad'e Allah ya bamu sa'ar amsar yarinyar, amma bamu kama ko d'aya daga cikinsu ba". "Ok, ina yarinyar... ". Bai idasa fad'in abinda ya ke son fad'a ba, Hassana ta fad'o falon a rikice tana kuka. Tana zuwa ta fad'a kan Habib jikinta ko ina rawa ya ke, dan har yanzu ba wai ta dawo natsuwarta bane".

Daga can b'angaran D'an sanda ya ce, "Yauwa kamar ita ce ta shigo ko? ". Jin kukan Hassana da ya yi".

Habib da "Eh ". ya amsa mai, sannan ya ce, "Zamuyi magana gobe, saboda baya jin shi sosai saboda kukan Hassana".


Habib kallan Hassana ya yi dake rik'e da shi ga jikinta ko ina har yanzu rawa ya ke, Habib d'ago Hassana ya yi, yana kallanta, karo na farko kenan da Habib ya tab'a kallan Hassana haka. Girgizata ya yi sannan ya ce, "Ke kinatsu mana, sun wuce, ki tashi ki je ki watsa ruwa zaki ji sanyi". Habib ya fad'i maganar yana mai tashi da Hassana".


Habib daga ya saki Hassana sai ta tafi zata fad'i, Habib cikin fad'a-fad'a ya ce, "Wallahi ki mik'e ko in sake ki ki fad'i". Hassana cikin narkarkar murya ta ce, "Wayyo tom ni ka kaini bedroom d'ina". Habib tsaki ya yi sannan ya rik'e Hassana ya kaita bedroom d'in ta. Habib juyawa ya yi zai fita, Hassana ta yi saurin kamo hannun shi, kamar za tai kuka, ta ce, "Ayyah nifa tsoro nake ji". Habib tsawa ta yi ma Hassana,ya ce, "Tsoran ya kashe ki, dama nasani bari nayi suka tafi da ke kowama ya huta". Habib na fad'in haka yaja k'ofar Hassana ya fita".


Hassana guri d'aya ta dun k'ule tana kuka dan tsoro ta ke ji sosai, gani take kamar zasu dawo, ahaka dai wani wahalallan bacci ya d'auke ta".

B'angaran Habib ko koda ya kwanta tunane-tunane ya hana shi bacci, dan sosai abin da ya faru ya d'aurai mai kai, yana mamakin wanda ya aiko atafi da Hassana, dan daga ganin abin sasu akayi, ahaka dai bacci ya kwashe Habib ".


Washe gari daga Habib har Hassana makara su kai, Habib bayan ya gama shirinsa har zai tafi aiki, sai kuma ya yi wani tunani, fasa tafita ya yi, ya yi nocking d'in k'ofar Hassana".


Hassana ko tunda ta samu ta yi sallah ta koma ta kwanta, dan kanta ciwo ya ke mata sosai, bugun da akema k'ofar ta ne ya tadata, tana mai dafe da kai ta zo ta bud'e k'ofar. Hassana cikin sanyin ta gaida Habib ganin shi tsaye".


Habib bai amsa gaisuwar Hassana ba, sai cewa ya yi, "Karki sake kice zaki kira Hajiya ki fad'a mata abinda ya faru, sannan kuma dama dan Hajiya na nan ne na dakatar da ke zuwa aiki, dan haka ki koma aiki yau". Hassana da sauri ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib banda lafiya, dan Allah sai gobe". Habib tafiyar shi ya yi yabar Hassana nan tsaye ya ce, "kin dai ji abinda nace miki, ki zo aiki yau". Habib na fad'in haka ya bar Hassana nan tsaye shi kuma ya yi tafiyar shi".


Hassana ko tsayawa ta yi tana tunanin ta inda zata fara shiri dan ko a yanzu ta makara. Wanka Hassana ta shiga, tana fitowa ta shiga kitchen da sauri dan samarma kanta abinda zata ci. A falo Hassana ta ci karo da ledar kaya, tsayawa ta yi tana dubawa, atamfofi ne masu kyau sosai sun samu style masu kyau, sai dogayan ri guna na shadda guda hud'u dukan su duk gizina ne sai shampoo ,ka yan sosai suka burge Hassana, ko wanne da gyalan shi ahaka ta ka wo mata su. Hassana sosai ta ji dad'in ganin kayan. Cikin sauri Hassana ta had'a tea ta sha, sannan ta shiga wanka. Wata atamfa blue and brown color tasa, sai ta ya fa gyalan atamfar. Masha Allah sosai Hassana tai kyau. Tana fitowa ta samu Napep ta kaita har sanat yoghurt, lokacin 9:50Am. Ita da lokacin zuwanta ya ke 7:00Am".


Hassana koda ta je bata iske wani aiki ba, dan duk wani gu da take sweeping and mopping ta je ta iske duk anyi, hakan yasa ta je wajan su Amina tana taya su nasu aikin".



Amina kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana kina jin dad'in ki kinganki kuwa yadda ki kai kyau, sannan sai kinga dama kike zuwa aiki". Hassana Kallan Amina ta yi, ta ce, "Amina Wallahi ba laifina bane". "Tom kaifin waye? ". Cewar Amina".



Hassana kallan Amina ta yi, ta ce, "Ke dai kawai awuce maganar". Dariya Amina ta yi, ta ce, "Anwuce".shiru Amina ta yi, sannan ta ce, "An d'auki wata aiki anan, ita ma dai daga ganinta irin supervisor ce, amma abinda ke ban mamaki tun ranar da ta fara zuwa aiki ta ke tambayarki, wai kinzo, kullum tazo sai ta tambaye ki". Hassana shiru ta yi, tana tunanin tom ita wayasanta, can dai tace, "Kila bani ta ke nufi ba". Zuwan Supervisor ne yasa Amina ta yi shiru ta ci gaba da aikinta. Supervisor ko tsaye ta yi tana kallan Hassana sannan ta ce, "Ke !, wannan dama shine aikinki? ". Hassana kallan Supervisor ta yi, ta ce, "A'a da yake banzo da wuri bane, lokacinda nazo kuma angama duk aikinda yake amazaunin nau". Billy sosai ranta ya b'ace da maganar Hassana, wato ita sai ta ga dama take zuwa aiki, sannan idan tazo sai aikin da taga gama ta ke yi".


Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, "Ok, ki wanke duk wani toilet da ke wajannan". Hassana kallan Supervisor ta yi, ta ce, "kiban wani abun, amma bazan iya wankin toilet ba, saboda inada kyankyami ". Wani uban ashara Billy ta yi, sannan ta bar gun, direct Office d'in Maganar Billy ta je, tana zuwa ta kalli manager ta ce, "Manager ba fa zai yuwu ba, yarinyar nan sai ta ga dama take zuwa aiki, sannan idan tazo sai taga dama take aiki, aikinma in za tai sai ta zab'a, dan haka Wallahi yau dole ta yi abinda nasa ta".


Manager kallan Billy ya yi, ya ce, "Karki damu bari in mata magana da kaina zata yi".


Manager da kanshi yasa mu Hassana ya yi mata magana akan ta wanke toilet d'in da Billy ta sata. Hassana, "tom"tace ma manager saboda bata iya yi mai musu, haka Hassana ta wanke duka toilet d'in gun. Sosai ta gaji ga kanta da ke mata ciwo".



Yau Farida bata zo Sanat yughurt ba, koda su Habu suka jema Farida da labarin masu samu d'akko Hassana ba saboda harin da aka kawo musu, dan haka sai dai ta yi hak'uri, idan su kai aiki basu yi nasara ba basa kuma k'ara jarabawa, saboda gudin matsala".


Habib ko bayan ya tashi aiki police station ya biya akan maganar b'arin da suka shigar mai jiya, tare da amsar police biyu ya kai su gidan shi dan gadi, gudun matsala".


Bilya ne yaje ya d'akko Hassana bayan ya kai Habib. Hassana zaune ta iske Habib a falon yana cin abinci, azuciyarta ta ce daga gani dai nasiye ne".


Hassana tsayawa ta yi kamar ta wuce, sai kuma ta ga kamar hakan bai da ce ba, ta ce, "Barka da dawowa Oga Habib ". Habib d'ago kai ya yi kawai ya kalli Hassana ya koma yaci gaba da cin abincin shi".


Hassana kuma aje gyalanta ta yi ta shiga kitchen ta dafa indomie ta fito, har yanzu Habib na nan zaune, ya dai gama cin abincin. Hassana nesa sosai da Habib ta zauna. Tana cin indomie ta, tana satar kallan Habib da hankalinshi gaba d'aya ya ke akan waya. Can dai Habib ya tashi ya nufi side d'in shi. Hassana shiru ta yi tana tunanin yadda za ta iya kwana ita kad'ai, dan gani take daga ta kwanta b'arayin zasu k'ara zuwa. Sai da bacci ya fara kama Hassana , sannan ta daure ta nufi bedroom d'in ta ta kwanta. Haka Hassana ta samu bacci ya d'auketa tana cikin masifar tsoro. Can cikin dare Hassana taji k'arar bindiga cikin tashin hankali ta diru daga gadon ta fita d'akin da gudu, tana zuwa Allah ya bata sa'a k'ofar Habib a bud'e ta ke bai kulle ba. Hassana cikin tsoro ta haukan gadon Habib ta kwanta bayan shi".


Habib sai baccin shi ya ke kwata-kwata baiji shigowar Hassana ba".


Hassana ko ta dad'e cikin tsoro sai ta kai hannu zata tada Habib ta ce mai b'arayi sun dawo, sai ta tuna daga ta tada shi zai koreta d'akinta, hakan yasa Hassana ta bar Habib bata tada shi ba".

Habib ko bashi ya farka ba, sai asuba. Jin d'imin mutum bayanshi yasa ya juya. Habib da mamaki ya ke kallan Hassana dake baccinta abinta abayan shi, tunani ya farayi tom yaushema ta shigo d'akin, ya akai tazo bai ji zuwanta ba. Habib sauka ya yi daga gadon ya nufi toilet ya yi alwallah yazo ya tada sallah. Habib har ya idar da Sallah yana zaune kan dadduma Hassana bata tashi ba. Habib ta tashi ya yi cikin fad'a-fad'a ya ce, "Ke ". Hassana da sauri ta tashi zaune tana sosa kai tana kallan Habib, ta ce, "Uhm Wallahi Oga Habib b'arayi ne suka k'ara dawowa". Habib kallan Hassana ya yi, ya girgiza kai kawai , sannan ya nuna ma Hassana hanyar fita da hannun shi".


Hassana sakowa ta yi tafita. Habib kuma wanka ya shiga ya yi shirin aiki".


Hassana ma b'angaran ta ta gama shirinta tsab, Compound d'in gidan taje, dan tana son ganin Bilya. Aiko zaune Hassana ta iske shi cikin mota, yana jiran Habib".


Hassana lek'awa ta yi da kai ta ce, "Oga Bilya dan Allah ina son magana da kai". Bilya fitowa ya yi daga motar, ya ce, "Inajinki". "Oga Bilya dan Allah so nake kaima manager magana aban kud'in aikina, tunda na fara zuwa ba'a tab'a biyana ba, kuma yanzu amfani nake so inyi da kud'in ". Cewar Hassana ".


"Shikenan badamuwa zanma manager magana, zan amsa in baki". Habib tun daga nesa ya ke kallan Hassana da Bilya". Bilya kuma yana ganin Habib ya ce ma Hassana, "shikenan sai kin zo ga Oga Habib nan ya fito zamu wuce".


Bilya bayan ya kai Habib Office d'in manager ya shiga, ya yi mai maganar kud'in Hassana. Manager batare da gaddama ba ya d'akko kud'in wata hud'u yaba Bilya ya ce, gashi ka bata".


Hassana yau da wuri tai k'okarin zuwa aiki, tana sauka Napep Farida ma na sauka. Farida cikin jin dad'i tace shegiya ashe kin fara zuwa, ta yi maganar a zuciyarta".


Hassana da mamaki ta kalli Farida,sai ta d'auke kanta tashi ge ciki abinta.Farida ko da mamaki ta bi Hassana da kallo wata bazata gaida ni ba, zaki ci ubanki a gunnan yau".


Hassana na zuwa ta sweeping and mopping na gun baki d'aya kamar yadda ta saba. Tana gamawa ta samu gu tana hutawa, niyyarta inta gama hutawa ta je ta amshi kud'in da Bilya ya ce mata manager ya bata, ta yi amfanin da take son yi dasu".


Hassana na zaune tana hutawa sai ga Bilya da Farida sun nufo inda ta ke, suna nufota suna tattaunawa".


Billy kallan Hassana ta yi, ta ce, "me yasa nashiga toilet na gansu da datti baki wanke ba? ". Hassana batare da ta kalli Billy ba, ta ce, "Nayi aikin da yake ma zaunin nau, amma wankin toilet bashi cikin aikina". Farida ce ta amshe zancan da cewa, "Ke 'yar matsiyata zaki je ki wanke ne koko sai jikinki ya gaya miki? ". Hassana da mamaki ta furta, "duka kuma". "Eh ko bazaki bugu bane? ". Cewar Farida".



Dariya Hassana ta yi, sannan ta ce, "ko shi mai Sanat yughurt, wanda kuke aiki ak'ark'ashin nafi k'arfin duka agunsa, bare ku da kuke a k'ark'ashin shi... ". Marinda Farida tai ma Hassana ne yasa tai shiru".



Hannu Hassana ta d'aga da niyyar ramawa Billy ta rik'e hannun. Haka Farida da Billy suka taru sai bugun Hassana suke. Har hankalin staff ya kai kansu, ga manager baya nan. Da gudu d'aya daga cikin ma'aikatan ya ruga Office d'in Habib ya sanar da shi, ana fad'a".



Habib da dama tun d'azu yake jin hayaniya, tashi ya yi dan yasan manager baya nan, ya nufi inda ake fad'an".



Hassana kwance ak'asa da Billy da Farida sun taru sai bugun ta soke". Habib da bai san wama ake bugu ba,tsawa ya yi ma su Farida yana cewa, "Baku da hankali ne". Da sauri dukansu suka dawo hayyacinsu".



Hassana ko da ta bugu sosai, tana jin muryar Habib da sauri ta tashi tana layi ta rik'e Habib tana kuka".



Habib ko da mamaki ya ke kallan Billy da Farida,Habib ya dad'e tsaye yana masu wani irin kallo sannan ya ja hannun Hassana ya nu fi Office d'in shi da ita".


Duka ma aikan gun hankalinsu ya koma kan Habib, dan banda Farida da Billy babu wanda yasan akwai aure atsakanin Hassana da Habib ".



Habib ko yana rik'e da hanun Hassana suka shiga Office d'in shi..... ✍️


Idan kintaranta daure ki Comment sister 🤝



Share

Comment please 🙏.

📚 OGA HABIB 📚

💫💫
*🅙︎ARUMAI 🅦︎ WRITERS 🅐︎SSOCIATION📚🖊️*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausa💪*_

*💫(🅙︎.🅦︎.🅐︎)💫*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy baby).



Shafi na 66&67.



https://chaveryt.whatsapp.com/CrrZExGxsLSGblRVfxdnj7


https://www.facebook.com/groups/301023561618950/



HABIB ko yana rik'e da hanun Hassana suka shiga Office d'in shi. Suna zuwa bazato ma tsammani Habib ya wanke Hassana da mari. Ji kake "Tassss!. Hassana k'ara ta fasa ta dafe gurin ta d'ago tana kallan Habib. Habib ko nuna Hassana ya yi da hannu ya ce, "Ke wace irin fitinayyiyar yarinya ce?, me ye had'inki da su?,tom Wallahi daga nan har kibar aiki anan idan har aka k'ara fad'a dake agunnan zakiga abinda zan miki! ". Hassana zaman 'yan bori ta yi agun tana, bubbuga k'afa tana kuka, mai had'e da magana, "Wayyo kunnena ka fasa min kunne, Wayyo kaina, wayyo ko ina ajikina, Mommy dan Allah ki dawo zasu kashe ni..... ". Wata razanannar tsawa Habib ya yi ma Hassana, ya tsaya yana kallanta da mamaki, yama rasa me zai ce mata".



Hassana ko d'an rage sautin kukanta ta yi, sannan ta ce, "Ai baka san me sukai min ba, kuma ni ai ban musu ko mai ba, su suka fara tsokanata". Hassana cusa kanta ta yi tsakankanin cinyoyinta sai kuka ta ke". Habib manager ya kira awaya. Manager na d'auka ya ce, "Hello manager ka ki ramin Farida da Billy ". Habib na fad'in haka ya kashe wayar".



Hassana ko k'ara rage sautin kukanta ta yi. Billy da Farida tare suka shigo Office d'in, bayan sun gama tsara yadda su mak'alama Hassana laifin".



Habib ya dad'e yana kallansu, sannan cikin kausassar murya ya ce, "me ya had'aku da ita? ". Billy ce tai wuf ta ce, "Oga Habib sanin kanka ne, Hassana bata zuwa aiki sai taga dama, Yanzu haka satin da ya wuce gaba d'aya batazo aiki ba.... ". Hassana wuf tai ta ce, "Eh d'in ai da yake ba shi bane ya hanani zuwa". Wani mugun kallo Habib ya yi ma Hassana, amma bata yi shiru ba sai da ta idasa fad'in abinda ta ke fad'a".



Billy kuma shiru ta yi, dan gabanta ya fad'i da jin abinda Hassana ta ce. Sannan dai ta ci gaba da cewa, "Oga Habib sannan bata zuwa aiki sai lokacin taga dama, haka ma close lokacinda ta ga dama take tashi, kuma idan tazo bata aiki, idan ma zata yi sai aikin da taga dama take yi, sannan tai ta tara staff's su yi ta fira, kuma wannan dokar Company ce, banda tara ma'aikata gu d'aya ana labarin duniya, duk wani Company yana yak'i da haka. Tom ni yau badani ake fad'an ba ma, da Farida su ke yi, shine nazo ina mata magana akan abinda ta ke bata kyautawa, saboda naga fad'an nasu tun daga farko, ita ce bata da gaskiya, amma daga magana ta dawo kaina tana zagina.. ".



Hassana ita dai da mamaki ta ke kallan su. Habib kallan Farida ya yi, ya ce, "Farida me ya had'aki da ita? ". Farida cikin salon makirci itama, ta fara magana kamar haka, "Oga Habib tun lokacin da mu kai fad'an nan da Hassana , Hassana ke gaba dani, duk inda muka had'u sai harara tsakanina da ita,da maganganu marasa dad'i, tom hakan bai min dad'i, shine yau da nazo naji ta fara maganganun nata, nasa meta nace mata, Hassana ni dai bana jin dad'in wannan gabar ta mu dan Allah ki d'auka komai ya wuce mu dawo mu ci gaba da gaisawa kamar da, shi kenan fa daga wannan maganar , wai ko uwata bata isa ta yi fad'a da ita ba ta kuma shirya da ita bareni , wannan shine abinda ya zafafani na tanka mata Oga Habib.. ".



Ai Farida bata gama aje zancan ta ba, Hassana ta amshe da cewa, "Oga Habib duk abinda suka fad'a Wallahi k'arya suke muna fu.... ". Habib tsawa ya yi ma Hassana akan tai shiru, amma tak'i taci gaba da maganar da take". Jawo ta Habib ya yi ta dawo gaban shi, ya ce, "Ci gaba da magana! ". Hassana shiru ta yi ta turo baki tana harararar su Farida".



Habib ko babu alamun wasa ya kalli Billy ya ce, "Daga yau babu ruwanku da ita, aiki ne batazo ba, ko kuma k'in yi tayi, ke kome ma ta yi babu ruwanku da ita, ki zo ki fad'amin , ni zanyi maganinta". Habib mai da kallan shiga Hassana ya yi, ya ce, "Ke kuma aci gaba da saki abu kina k'inyi, Idan har kika sake aka kawo min k'ararki, zakiga abinda zan miki".



Hassana turo baki ta yi, ta ce, "Tom ai dai ni shairi su kai min, Kuma Wallahi ni bazan wanke toilet ba". Habib ko takan Hassana bai biba, ya ce, "Duk abinda aka sata bata yiba azo a fad'a min, zaku iya tafiya".



Farida da Billy fita sukai, ko wannan su da maganar da ya ke yi a azuciyar shi.Hassana ko ta dad'e a Office d'in, sannan ta d'auki maya finta ta fita. Habib ya bita da kallo dan shi yana jinjina rashin hankalinta, bai d'auketa mai hankali ba, shi yasa baya mai da kai a abubu nata da dama ".



Farida ko tun zuwanta Sanat yughurt aiki, ta samu Billy ta ce, mata ita tazo nai man aikine dan ta ci Uban Hassana, nan dai ta fad'a mata k'arya da gaskiya akan abinda ya had'asu da Hassana, amma ta b'oye mata tana son Habib".



Itama Billy b'angaranta k'arya da gaskiya ta fad'a ma Farida, akan Hassana ta rainata tana mata duk abinda ta ga dama, ita ma bata nuna ma Farida tana son Habib ba. Shine fa suka had'a hannu wajan yadda zasu yak'i Hassana, kuma duk abinda su kai mata Oga Habib yaga Laifin Hassana ne, wannan kenan".



Bayan su Billy sun fito Office d'in Habib, Farida kallan Billy ta yi da damuwa, ta ce, "Supervisor ina fa ganin kamar Oga Habib ya fara son yarinyar nan, kalli yadda ta ke mai hauka, amma duk ya d'auka,kuma dubu kashaidin da ya yi mana wai babu ruwanmu da ita duk abinda za tai, ni fa hankalina ya fara tashi". "Bana tunanin yafara sonta, saboda da yafara sonta da ba zai yadda da aikin da ta ke yi ba, ai shima yasan mafi k'ask'ancin aiki ta ke yi, kawai dai shi baya son ana fad'a a nan ne". Cewar Billy".



Hassana ko tana fita Office d'in Habib, ta nufi wajan Bilya, bayan sun gaisa ne, Hassana ta ce, "Oga Bilya kaban kud'in". Bilya kud'in da Manager ya bashi ya ba Hassana".



Hassana direct gidan su Habib ta wuce. Tana zuwa side d'in worker's d'in ta nufa. Aiko tana zuwa ta iske Jimmai zaune ta gama aikinta".



Jimmai da fara'arta ta tari Hassana ta ce, "Oyayyo amarya a gidan Oga Habib, kai amma amarcin ya amsheki, kinga ki yadda ki kai kyau". Hassana ta b'e baki ta yi, sannan ta ce, "Sister Jimmai nazo da kud'in muje inyi register, ga kud'in". Jimmai maya finta ta d'akko suka fita da Hassana".



Suna tafiya suna hira, ananne Hassana taba Jimmai labarin yadda su Farida ke ta kura mata, da bugun da su kai mata. Jimmai shiru ta yi, sannan ta kalli Hassana ta ce, "Hassana kina da laifi sosai, duk abinda Farida da Billy ke miki, akan fa Oga Habib ne, tom ke me zai hana kena kiyi fiye da abinda su ke yi ganin kin samu guri azuciyar Oga Habib. sufa nan yak'in nai man soyayyarshi suke, tom sai ke kice bazaki iya ba, ke da komai zaki zaizo miki a sauk'i, tom bari kiji bawai tanadin makaman yak'i zaki ba da su Farida, ta nadin yak'in nai man soyayyar mijinki zakiyi, ki futa daga harkarsu, Idan zaki iya Idan sun miki ki banza da su. Wallahi Hassana ki farka kisan abinda kike, ki tattali mijinki, dan ba wai su Farida ka d'ai bane ke yak'in nai man soyayyar Oga Habib, kawai dai sune kika sani, dan haka tun kan guri ya k'ure miki ya hango wata, ki zamar mai baiwa, ki yi turi da duk wani muskilancin shi, ba wai ki kin mai magana ba ya yi banza da ke dan haka ke bazaki k'ara yi ba, Ina karma ki kuskura ki haka, shi dama mai naima ai hak'uri dole ne ya yi shi, Idan kika sa hak'uri da jura sai kiga tun baya tanka miki watarana ya tanka miki, sannan kina had'awa da addu'a saboda ita ce takofin mumini, kirik'a karanta mai izazaza k'afa d'ari tana ta siri sosai wajan jawo hankalin mutum akanka".



Hassana kallan jimmai ta yi, ta ce, "Sister Jimmai na yarda da duk abinda kika ce, amma Oga Habib ya wuce tunaninki, amma zan jaraba duk abinda kika ce, nagode ". "Yauwa k'anwata". Cewar jimmai".



Haka Jimmai ta raka Hassana tai register, inda su kai zata fara zuwa gobe ".


Hassana daga nan bata koma Sanat yughurt ba, gida ta koma. Bayan ta huta, ta shi ta

Please Login or Register in order to submit comment