Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Dariya Hajiya Turai ta yi, ta ce, "Allah sarki Habib wai guduwa ka yi da matar taka ba Sallama, in banda abin ka ai tun da naga Hassana ta kwaremin baya na hak'ura, Allah ya baku zaman lafiya". Hajiya Turai kiran Habib tai awaya, yana d'agawa ta ce, "Habib tafiya kuma babu sallama". Habib da ga can, sosa kai ya yi, ya ce, "Mommy na zaci kin kwanta ne, shine wai kar in tada ki". Hajiya Turai dai dariya kawai ta yi, ta kashe wayarta".


Habib sai da suka biya ta Alheri suya ya sai masu gasassar kaza sannan suka tafi gida".


Suna zuwa Habib ya kamo hannun Hassan ya ce, "zo ki wanka , mun yi bacci da wuri, yau kin gaji da yawa".
"Uhm ni ban gaji ba, zan yi da kai na ma".
Cewar Hassana ".


Habib hannun Hassana ya kamo ya ce, "Haba 'yan matana, zan hutashshe ki ne, bazan kalli ko mai ". Habib haka ya shigar da Hassana toilet d'in ya taya ta tai wankan, tun tana nok'ewa har ta hak'ura Habib ya jajjagulata ahaka dai aka yi wankan aka gama".


Hassana na fitowa ta kalli Habib ta ce, "Oga Habib sai da safe".Hassana ta juya ta nufi side d'in ta. Habib bai tan ka ma Hassana ba, rabuwa ya yi da ita sai da ya yi sallar issha'i ya gama duk abin da zai yi sannan ya nufi side d'in Hassana. Hassana ko lokacin har ta kwanta,ta fara bacci. Habib bai tada Hassana ba gefanta ya je ya kwanta ya rungumota ta gefe gudin karta farka".


Hassana ko sai asuba da Habib ya ta data yin Sallah sanan ta san d'akinta ya kwana, Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib yau she ka shigo". "Kina can kina bacci". Habib ya ba Hassana amsa".


Hassana ko bayan ta yi sallah batare da Habib ya sani ba, ta fita ta shiga kitchen ta dama mai kunun gyad'a. Lokacin da Hassana ta shiga bedroom d'in ta bata iske Habib, wanka ta shiga, tana fitowa ta zauna ta yi shafa, yau Hassana har da su safa powder da lipstick, sannan ta d'akko cikin atamfofin da Hajiya Turai ta d'inka mata tasa wata,ta d'au aribian perfume ta feshe jikinta da shi, Hassana na fitowa da Cup d'in kunun Habib ta ci karo da Habib ya fito. Kallan kallo aka tsaya yi, Habib ringumo Hassana ya yi ya had'e bakin sa da nata yana tsotsa sannan ya rad'a mata cikin kunnan ta ahankali ya ce, "Nayi missing d'in sweet lips d'inki, anya ko zan iya fita". Hassana murmushi ta yi ta ce, "Uhm Oga Habib ina zaka da wuri haka? ". "Zan je Company ne, yan zu zan dawo". Habib ya ba Hassana amsa ".


Hassana hannun Habib ta kama ta ce, "Oga Habib na dama ma kunu, kasha tukun, nima zan rakaka". Habib jama ya yi Hassana ta mik'a mai kunun ya amsa yana sha, ya kai Cup d'in kunun bakin Hassana. Hassana kauda kai tayi ta ce, "Nasha ".Habib sha ya yi yabar Hassana dan ya lura ita kunun bai da meta ba. Hassana kallan Habib ta yi, ta ce, "Oga Habib manager ya dawo aiki? ". Habib kallan Hassana ya yi, ya ce, "Yauwa kin tuna min, bai dawo ba, na ce sai kin yarda". Hassana turo baki ta yi, ta ce, "Ni fa ban wani ji haushin manager , haushin Billy naji ai ita ce tasa ya maran". Habib da bai son Hassana ta je Sanat, kallan ta ya yi ya ce, "Sanat ki bari ba yau ba zaki je". Hassana mak'ema Habib kafad'a ta yi, ta ce, "Ni dai yau nake son zuwa, dan Allah, akwai abin da zan yi acan". Habib kallan Hassana ya yi ya ce, "Me zaki yi acan? ". "Mu je zaka gani".


Habib ba dan yaso ba ya tafi da Hassana Sanat Yoghurt".


Hasana bayan sun je, Habib ya nufi Office d'in shi, zai shiga Hassana ta yi saurin kamo hannun Habib ta ce, "Muje karaka ni in ga ya gurin ya yi, ka ga na rabu da zuwa ". Habib bin Hassana ya yi dan shima ya rabu da duba cikin Company yaga yadda ya yi. Duk in da su kai staff d'in gurin kallan su ka wai ake, inda duk in aka gaida Habib sai an gaida Hassana, Hassana da fara'arta ta ke amsawa.Dan yan zu kowa ya san matsayin Hasssana a Sanat. Billy tun daga nesa ta hango Hassana da Habib na zuwa. Hassana dai-dai saitin Billy ta tsaya ta kalli Habib ta ce, " Uhm Sweetheart yama sunan wannan? ". Hassana ta fad'i maganar tana nuna Billy. Habib ko sai da ya rintse ido dan jin dad'in su nan da Hassana ta kira shi da shi. Habib batare da tunanin komai ba, dan shi ya za ci Hassana da gaske ne ta manta sunan Billy, ya ce, "Billy ". Hassana kallan Billy ta yi, da fara'arta ta ce, "Sannu da aiki Billy gaskiya kina k'ok'ari, Ina manager fa? ". Billy bacin agaban Habib ne tabbas da babu abin zai sa taba Hassana amsa, amma babu yadda za tai dole ta ba Hassana amsa".


Billy d'agowa ta yi tana kalli Hassana ta ce, "Bai zo aiki ba". Hassana cikin sakin fuska ta kuma cewa, " Lafiya bai zo aiki ba". Billy kallan Habib ta yi taga hankalin shi yana kan waya, ta harari Hassana ta ce, " an dakar da shine". "Ok, ki kira shi awaya yazo yan zu, idan ya zo ku zo tare". Hassana na fad'in haka ta kamo hannun Habib ta ce, "Wayyo Sweetheart wannan tafiyar da nai har nagaji Allah, mu koma Office d'in ka". Habib kama hannun Hassana ya yi suka koma ya ce, "Dama ke kika matsa sai kin biyoni ai".


Billy kamar zuciyarta zata fashe haka taji. Da harara tabi bayan Hassana da shi, sannan ta tura ma manager text massage akan yazo yan zu".


Hassana ko suna zuwa ta zauna kan chair d'in da Habib ya ke zama ta ce, "Oga Habib yau zan futassheka zan yi duk aikin da za kai". Murmushi Habib ya yi, ya ce, "Wane ke yarinya".


Habib suna nan zau ne suna fira da Hassana Manager da Billy su kai nocking k'ofar. Habib izinin shiga ya basu".


Manager cikin girmama Habib kamar yadda ya saba ya gaida shi. Habib babu yabo babu fallasa ya amsa ma manager. Manager kallan Hassana ya yi, ya ce, "Barka da hutawa ranki shi dad'e". Hassana ma ta b'angaran ta babu ya bo ba sallasa ta amsa ma manager ".


Billy ko sosai taji ta kaicin gaida Hassanar da manager ya yi. Manager mai da kallan shi ga Habib ya yi, ya ce, "M.D, ance kana kirana? ". Habib nuna Hassana ya yi, ya ce, "Ga mai nai manka nan". Manager mai da kallan shi ga Hassana ya yi ya na jiran abin da zata ce".


Hassana kallan Billy ta yi ta ce, "Billy kawo min Yoghurt mai sanyi". Billy kamar ta ce bazata ba amma kuma babu damar haka ga Habib kusa, hakan yasa kamar zata sa ihu ta fita ta je kawo ma Hassana". Hassana kuma bata cema manager ko mai ba har sai da Billy ta dawo sannan ta kalli manager ta ce, "manager ka dawo kaci gaba da aikin ka, babu komai, ko mai ya wuce"."Godiya na ke ranki shi dad'e ". Cewar manager ".


Hassana kallan Billy ta yi da ke tsaye ta ce, "Ke fa lafiya? ". Billy cikin daurewa da yadda ta ke ji ta kalli Hassana ta ce, "ke ki ka ce in zo". Hassana kallanta ta yi sannan ta ce, "Babu da muwa zaki iya tafiya ki ci gaba da aikin ki". Billy fita ta yi tana mai jin zafin Hassana, sai dai ta san Hassana tai mata nisa nesa ba kusa ba, kuma tabbas yan zu Hassana duk wanda ta kora aiki ya koru".


Billy Office d'in ta ta koma tana kuka, Billy na nan tana kuka ta ga Manager ya shigo Office d'in. Manager cikin damuwa ya k'arasa gun Billy, manager kallan Billy ya yi ya ce, "Nasan abin da ya saki kuka, Billy hak'ik'a na soki kuma har yan zu ina son ki, tom amma wannan ita ce magana ta k'arshe da ke, ya maganar aure na da ke? ". Billy d'agowa ta yi tana kallan Manager ta ce, " Nayarda duk lokacin da ka shirya, zaka iya zuwa wajan kawuna". Manager cikin jin dad'i ya ce ma Billy, "zan je gobe". Billy kai ta d'aga ma Manager ".


Hassana ko sai 4:00Pm suka bar Sanat ita da Habib..... . ✍️



Idan kin karanta daure ki Comment sister 🀝





Share
&
Comment please πŸ™.

πŸ“š OGA HABIBπŸ“š
πŸ’«πŸ’«
*πŸ…™οΈŽARUMAI πŸ…¦οΈŽ WRITERS πŸ…οΈŽSSOCIATIONπŸ“šπŸ–ŠοΈ*


https://www.facebook.com/108544471437073/posts/108546644770189/?app=fbl

_*Marubuta masu aiki da jarumta domin wa'azantawa ilimantarwa, nishad'antarwa tare da fad'akarwa da jama'a bisa harshen hausaπŸ’ͺ*_

*πŸ’«(πŸ…™οΈŽ.πŸ…¦οΈŽ.πŸ…οΈŽ)πŸ’«*

TSARAWA DA RUBUTAWA FADILA SANI BAKORI (Faddy Baby).


πŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”šπŸ”š


Albishirin ku masu bibiyar littafin Fadila Sani Bakori.
Yau gani da daddad'an albishir gare ku, insha Allah daga na kammala Oga Habib, zan nisha d'an tar da ku da sabon littafina wanda na baje basirata acikin shi. Anyi amfani da salo na birgewa acikin littafin. Labari ne wanda ya ke d'auke da madarar Soyayya, mai d'auke da ban al'ajabi. Inda ta wani b'angaran labarin ke d'auke da ban tausayi mai tsayawa a zuciyar makaranci. Duk yadda zan sanar daku ba zaku fahimta ba, ke dai karki bari abaki labari.
Zaki samu littafin akan farashi mai sauk'i da rahusaπŸ‘ŒπŸ‘Œ.
Summary.
Abba tin ina yaro kana yawan fad'a min, duk abinda ya yi tsanani yana tare da sauk'i. Shin ni sai yau she sauk'i na zai zo! ?. Abba me yasa muta ne basa ganina, maganata kawai su ke ji!?.Abba me yasa muke rayuwa a daji mai makon cikin gari cikin mutane !?.
Abba kana gani Husna zata aure ni, duk da halin da nake ci!?.
Abba me yasa Husna ta kasan ce ita kad'ai ke ganina!?. Abba kace kai ba Mahaifinsa bane, tom waye Mahaifina, kuma me yasa muke rayuwa a jeji!?, Sannan me yasa Abdussalam kad'ai ke zuwa gurin mu, sannan Abba waye Abdussalam ?.
Haidar duk banda amso shin tambayoyin ka, nima ban san kai na ba Haidar, ban san waye ni ba, bare kuma kai!.
Labari mai tab'a zuciyar mai karatu.

Paid book

Akan farashi mai sauk'i da rahusa πŸ‘ŒπŸ‘Œ

VIP group 300 OnlyπŸ‘Œ , normal kuma 200 ne, zaki yi transfer ta account d'in nan 2111619333.
Account name Fadila Sani.
Bank Name Zenith bank.
Dan nai man k'arin bayani zaki iya managa ta wannan NumberπŸ‘‰ 08063830828



Shafi na 92&93.




Hassana ko sai 4:00 PM suka bar Sanat ita da Habib. Suna komawa gida Hassana ta shiga kitchen tai jolop rice. Habib na zaune Falon Hassana, Hassana ta fi ta nifo wajan Habib, Hassana zama ta yi, gefan Habib tana kallan shi, ta ce, "Oga Habib Yau ban ma kunu ba, jolop rice nai ma, zaka ci? ". Kai Habib ya girgiza ma Hassana alamun ba zai ci ba. Hassana turo baki ta yi, ta ce, "Ai ko yau gidan Mommy zan tafi in dai baka ci ba".Murmushi Habib ya yi yana sa hannu ya shafo lips d'in Hassana da ta turo ya ce, "Sorry Sanat mai da lips d'in ki, kar ya yi tsini, yafi dad'in Kiss ahaka". Hassana kuma turo lips d'in ta ta yi, Habib kai baki ya yi dai-dai kan lips d'in ta, ya d'an cizi lips d'in ka d'an, ya ce, "Ki mai da su karsu yi tsini, suna d'aya daga cikin abin da ke min kyau". Hassana sake turo bakin ta yi, ta ce, "Uhm dama du kana baki d'aya lips d'ina ne ka wai ya ke da kyau? ". Hassana ta fad'i maganar kamar za tai kuka. Habib kai ya d'aga ma Hassana alamun haka ne".


Hassana ta shi ta yi da sauri zata tafi, ta ce, "Aiko shima kabar ganin shi daga yau, gidan Mommy ma zan koma, inda duka na lips d'ina kad'ai kema kyau ". Habib da sauri ya jawo Hassana ya zaunar da ita kan cinyar shi suna fuskantar juna, ya ce, "Sanat ko mai naki mai kyau ne". "Uhm". Hassana ta ce, ta ce, "tom Dame-dame nau ke ma kyau? ". Habib hannu yasa yana shafa lisp d'in Hassana dan shi sosai shape d'in lips d'inta ke mai kyau, ya ce, "lips d'in ki, eyeliner, Breast d'in ki girman su dai-da, hips d'inki gir mansu ya yi min dai-dai, tsayin ki dai-dai, Uwa uba Babyna lips d'inki yan kar kiss ne, ke fa mai zafi ce, na yi ma missing d'in ki d'an bari in.... ". Hassana ta shi tai zata gudu Habib ya yi sauri ya rik'ota, ya had'e bakinsu guri guda. Ganin abin ya yi nisa na tafi zuwa dubo ma Hassana girkinta gudin karya k'one".


lokacin da na dawo a toilet najiyo Su Hassana, suna wanka. Habib da kan shi ya yi ma Hassana shafa sannan ya d'akko mata wasu kaya marasa nauyi tasa. Hassana bayan Habib ya gama shiryata ita ma tai maka mai ta yi ya shirya, sannan ta zibo masu abinci suka ci ".


B"angaran Manager ko har yaje gidan su Billy nai man auranta an bashi, dan yanzu Billy ta watsar da komai ta ringumu Manager hannu biyu, gudin kar tai biyu babu. Wata Uku aka tsaida auran Billy da Manager ".


akwana atashi babu wuya awajan Allah, Yau saura sati d'aya bikin manager da Billy".

B'angaran su Hassana ko fad'in irin soyyayar da suke, ina sai dai wanda ya gani, ko ya hasaso,Hassana zaman Soyayya sosai suke da Habib in da kowa ke k'ok'arin faranta ma d'an uwan sa. Hassana ta sake haske sosai fatar jikinta ta yi smooth ta ti clear, sai dai kwana biyun nan Hassana sun d'an samu matsala da Habib, in da har Hassan ta d'auki fushi da Habib, inda shi ma kuma Habib ya ke ganin dan yana nuna damuwar shi da Hassana ne ta ke mai haka, Shi yasa ya daure zuciyar shi ya fita lamuranta".


Yau kwana biyu kenan, gaisuwa kad'ai ke had'a Hassana da Habib. Idan abin ya damu dukan su. Hassana da ke zaune ta rasa tudun dafawa, tunanin kiran Hajiya Turai ta yi, tana kiranta ko kira d'aya ta d'aga. Hajiya Turai na d'agawa Hassana ta sa mata kuka, Hajiya Turai cikin rud'ewa ta ke tambayar Hassana mai ya faru. Hassana da kyar ta samu ta tsaida kukan ta ta fara yi ma Hajiya Turai ba yani kamar haka, "Mommy Oga Habib ya dad'e yana min alk'awarin zai kai ne garinmu amma yak'i, kullum nai mai managa sai ya ce in bari sai sati mai zuwa, kuma shine yan zu ya ke fushi dani! ". Hajiya Turai lallan shi Hassana ta yi sosai sannan ta ce, "Ki hak'uri ki bar kukan daughter bari in kira shi ".


Hajiya Turai na kashe wayar ta kira Habib, lokacin Habib na zaune Office d'in shi yana aiki, kiran Hajiya Turai ya shigo wayar shi".


Habib picking call d'in ya yi, bayan sun gaisa da Hajiya Turai ne, Hajiya Turai ta ce, "Habib kasan abin da kai bai da ce ba ko?, yan zu nakira daughter mu gaisa naji voice d'inta alamun tana cikin damuwa. Haba Habib yan zu ni bannan bare daughter ko gurina tazo taji sanyin, kai kad'ai ke gareta amma kuma kai har ka bar ta cikin damuwa, me yasa ne haka Habib? ".


Habib cikin damuwa ya fara magana kamar haka, "Tom Mommy ni ban san ya zan mata ba, ta matsa ita tana son zuwa garinsu, ni ba wai nak'i ma ta ba ne, in da ko ni ban da lokaci zan iya sa Bilya ya kaita, tom amma bata da lafiya kwanannan, kullum da zazzab'in dare ta ke bacci, nakira litama ya dubata ashe ciki ne". Habib ya fad'i maganar yana sosa kai sai kace Hajiya Turai na kusa da shi".


Allah sarki Hajiya Turai gaba d'aya wutarta d'aukewa ta yi na wani lokaci, sannan ta ce, "Habib amma shine baka kira kai min albishir ba, kuma waya cema ana barin bai ciki k'arami irin haka cikin damuwa!? ". "Wallahi Mommy ita ke fushi dani amma ni bana fushi da ita, na bata hak'uri ta bari sai ta haihu amma tak'i ji, tom ya zan mata? ". Habib ya fad'i maganar cikin damuwa ".


Shiru Hajiya Turai ta yi sannan ta ce, "Habib inda ta sa ranta akan zuwa gidan ka yi hak'uri ka kaita sai ta yi sati ka koma ka d'akko ta, in ba haka ba za fa a iya rasa cikin jikinta, bafa aso mai ciki tana zama da damuwa ko mai zai iya faruwa da ita, nima zan dawo Next week insha Allah ". "Tom Mommy Allah ya kawo ki lafiya". Habib na fad'in haka ya kashe wayar ".


Habib tashi ya yi ya rufe Office d'in shi ya nufi gida. Kwance ya iske Hassana akan Three seater tana zibba hawaye. Habib zama ya yi kusa da Hassana yana ka mota ya zaunar da ita kan cinyar shi, Habib handkerchief d'in shi yasa ya goge ma Hassana hawayanta, sannan ya ce, "Haba Sanat ni fa bawai na hanaki tafiya bane dan wani abu, kawai dan naga baki da lafiya ne, dan Allah ki yi hak'uri ki goge hawayanki Allah alk'awari na d'auka daga kin haihu zan kai ki". Hassana kallan Habibb ta yi hawaye ya na mai ci gaba da zubar mata, ta ce, "Ni fa ba wai nak'i bane, ni bana son basu san nayi aure ba kawai sai dai in je musu da yaro, sai dai in haka ne azubar da cikin dan ni ba zan iya zuwa musu da yaro ba". Habib shiru ya yi yana kallan Hassana, sannan ya ce, "Kin yarda in kaiki gobe amma kwana d'aya zaki mu dawo? ". "Hassana kai ta d'aga ma Habib ta ce mai ta yarda".


Washe gari da wuri Habib suka yi shirin tafiya Kano, kasan cewar da wuri suka fita hakan yasa k'arfe 1:00Pm suka sauka, inda Hassana ita ke nuna ma Habib hanya har izuwa local government d'in da suke akano".


Hassana wani irin sanyi ta ke jin yana ratsata lokacin da suka iso k'ofar gidansu, sai dai ta wani b'angaran tana daurewa ne kawai kar tai kuka ta tada ma Habib hankali, amma idan ta tuna zata gidan su babu Mahaifinta mai sonta, ji tai kamar tai ihu, dan sai mutuwar Mahaifinta ta dawo mata farko. Duk yadda Hassana ke danne kukanta abin ya ci tura, sai ta ta sa kuka, Habib da ya yi parking a lalataccan gidan da Hassana ta nuna mai ta ce nasu ne, jira ya ke ta ce su sauka, amma sai yaji kukanta, Habib cikin damuwa ya kalli Hassana ya ce, "Sanat ko mai narayuwa d'an hak'uri ne, dan Allah ki yi hak'uri ki goge hawayanki, in ba so ki ke ki sa ni damuwa ba ". Hassana da sauri ta share hawayan ta , ta ce, "Natuna da Mahaifina ne mai sona , mai tausaina, sanadin rashin shi yasa na gudu na bar ma haifata".


Habib lallashin Hassana ya yi sosai sannan ya ce, "ki shiga ciki mana, ko kin manta gidan ne? ". "A'a nan ne". Cewar Hassana ".


Hassana fita ta yi daga Motar ta nufi cikin gidan. Zaune Hassana ta iske Mahaifiyar Usaina 'yar uwarta, da Usaina, Hassana sallama ta yi tana mai k'arasawa inda suke".


Dukan su da kallo suka bi Hassana, dan basu gane ta ba. Hassana ko da fara'arta ta k'arasa inda suke ta ce, "Umma bugu gane ni ba ne, ?, yan zu kema Usaina bi ki gane ni ba? ". Usaina da taji Muryar Hassana zin bur tai ta mik'e tana kallan Hassana, ta ruga ta rungume Hassana ta ce, "Umma Wallahi Hassana ce!, Hassana ce ta dawo gare mu Umma!!! ". Usaina ta fad'i maganar da k'arfi tana fad'awa jikin Hassana".


Hassana ma rungume Usaina ta yi tana kuka, Allah sarki Usaina ma kukan tasa, sai da su kai sukan su sannan su kai shiru, ita dai Umma kallansu kawai ta ke tana share hawayanta ita ma ".


Usaina da katawa ta yi da kukan ta jawo hannun Hassana suka zauna. Umma cikin mamaki ta kuma kallan Hassana ta ce, "Hassana ke ce?, dama kina raye Hassana?, ina kika shiga ke ko?, Hassana kin tafi kin bar mu cikin damuwa ". Umma ta fad'i maganar tana share hawayan ta. Hassana ma goge nata hawayan ta yi, sannan ta ce, "Umma ku yafe min na gudu na barku, dan Allah Umma ki yafe min? ". "Hassana ai dole ki gudu, mun ta kura ma rayuwarki mun rabaki da abin da kike so, bakin cikin haka ya kashe mahaifinku, Hassana dole ki gudu ki bar mu, mu zamu rok'e ki yafiya, ki yafe mana Hassana, amma ke biki mana ko mai ba". Umma kallan Hassana ta yi, ta ce, "Hassana inji dai ba karuwanci ki ka je ba? ".


Hassana kuma goge hawanta ta yi sannan ta ce, "Umma banyi karuwanci ba, na bar nan da wata uku nayi aure, yan zu haka muna tare da wanda na aura". Umma bud'e baki ta yi tana kallan Hassana, ta ce, aure Hassana, amma naji dad'i da ba yawan banza ki ka yi ba, je ki shigo dashi, ya zaki bar shi waje ".

Hassana zuwa ta yi suka shigo da Habib. Umma sosai ta cika da al'ajabi da ganin Mijin da Hassana ta aura, lallai wanan shine ake kira da kyakkyawar k'addara".


Dama tun kafin Habib ya shigo an mai shim fid'a, Habib zama ya yi, sannan ya gaida Umma, suka gaisa da Usaina".


Umma kallan Habib ta yi, ta ce, "bawan Allah taya kuka had'u da Hassana? ". Habib zayyane ma Umma ya yi kaf yadda suka had'u da Hassana, da yadda akai auran su da Hassana".


Umma sosai ta yi murna, dan ta yi nadama sosai bayan tafiyar Hassana. Bayan Habib ya gama ba Umma labari ne, Umma ta kalli Habib ta ce, "Na san Hassana ta baka labarin halin da muka sata, wato Hassana bayan auran Kabir da Usaina, ina jin basu zaman wata uku cikakku ba, sai fad'a wulak'ancin yau da ban na gobe da ban. Hassana nayi nadamar rabaki da Kabir, amma kuma na godema Allah da na rabaki da Kabir in da sanadin haka ne yasa kika gudu, har Allah ya had'aki da bawan Allah nan, wato Hassana yan zu haka maganar nan da nake miki Usaina ta dad'e agida, da ta gaji da wulak'an ci da Kabir ya ke mata ta dawo gida, har yan zu ko zuwa bai yi ba, k'arshe ma munji labarin ya yi aure, jiya jiyan nan ya aiko mata da takardar ta". Hassana sosai ta tausayama 'yar'uwarta halin da ta shiga".


Sun dad'e suna hira sannan Habib ya ne mi Masallaci ya tafi yin sallah. Bayan Habib ya fita ne, Umma ta kalli Hassana ta ce, "Hassana kinga gidan ko girki ba muyi ba, me zaku ci Usaina ta tashi ta siyo miku? ". "A'a Umma Allah bana jin yunwa sai da muka ci abin ci a hanya ".



Habib na dawowa ya d'auki Hassana ya suka nufi dan gin mamarta da babanta, duk inda suka je ba wani dad'ewa suke ba, dama kuma ba wani damuwa da Hassanar su kai ba, garama yan zu da suka ga waye mijinta tom sun nuna damuwar su da ita".


Da daddare Habib cikin gari ya shiga ya siyo abin da zasu ci. D'akin Mahaifinsu Hassana aka gyarama Habib ya kwanta, ya so ya nemi hotel ya kwana Hassana ta hana shi".


Washe gari :
Duk in

Please Login or Register in order to submit comment