Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

al'ajabi, mamaki, farinciki,....


sannu su ummu suka shiga yimasa amma, sai suka ga be amsa ba, ya kurawa waje daya ido suma ahankali suka kalli in da yake kallo.

Ai suman tsaye sukayi dukansu ganin fu'ad atsaye.


Faheemah ce tayi karfin halin kiran sunansa cikin madaukakiyar farinciki kana su ummu....


Faheemah tace "ya fu'ad!".

Ummu tace "son!"


Fareesa tace "brother?"


Anwar yace "dude!"



Duk suka kira sunansa alokaci daya da muryan mamaki hade da zallan farinciki a fuskarsa...


Ware hannayensa yayi yayinda fuskarsa ke dauke da kyakyawan murmushi.



Da gudu ummu, fareesa, anwar, har ma da Faheemah suka yi awajensa atare, da isar su kuwa Faheemah ta kasa runguman shi wanda ita kanta batasan dalili ba...


jin dumin Ummunsa, kanwarsa,hadi da amininsa yasa shi lumshe ido hawayen dasuka cika idanunsa suka gangaro, haka kuma yana jin sanyi dadi na ratsa ko ina a jikinsa. Cikin zallan rudani, mamaki, hadi da farinciki, ummu tace


" Son da gaske kaine tsaye kan kafafunka?"..


Kara rungumesu yayi da kyau kana cikin unique voice dinsa yace

" ummunah nine, it's me your Fu'ad"..

kukan farinciki ummu tasaki hadi da yiwa Allah ta'ala godiya.


"I really miss you my brother"



"miss you more my kanwaty "

yafada kamar yanda yake zolayanta ashekarun baya. Dariya farinciki tayi kana tace

" Allah mun gode maka"


"oh my goodness dude! Am so happy for you, alhamdulillah ya Allah for making my only friend & brother standing back on his feet"
cewar anwar yana sake rukunkumeshi.

Murmushi mai sauti fu'ad yayi kana yace



" Thank you so much friend, indeed you are truly a best friend"

ahankali ya ware idanunsa dake aruntse kana ya sauke kan hallitta mafi soyuwa aransa, baya ga iyayensa...



Faheemah dake tsaye gefensu kuwa kuka take sosai amma mara sauti, kuka take na farinciki samun lafiyarsa, tausayinsu ummu, hadi da fargaban rasa shi. Ganin yanda suka rungumesa dukkansu yasa ta tsaya, domin sun fita bukatarsa, shekaru bakwai ba wasa ba, shekaru bakwai suka dauka suna jiran wanna ranar, sun cancanci fara zuwa garesa fiye da ita...



Ahankali ya zare jikinsa daga nasu ummu kana ya shiga takawa domin zuwa gareta batare da ya dauke idanunsa a kanta.
Baifi sauran taku biyu ya isa gareta ba, ya tsaya!


Cikin husky voice dinsan yace

" faheeeeta"

hadi da ware mata hannayensa, kukanta ne ya karu saboda ya tuna mata da umminta ita kadai ce ke kiranta da faheeta. Cikin sauri tafada jikinsa hadi da fashewa dawani sabon kuka mai fitar da sautin abubuwa masu yawa, lumshe idanunsa yayi, yana jin saukar kukanta adukkananin ila'irin jikinsa, besan meyake ji atare da ita ba, amma yana jin abu mai girma atare da wanna kyakyawar hallitan.

"Shhhhhh stop crying okay"

yafada yana dan bubbuga bayanta.

Shiru tayi sai sauke ajiyar zuciya take.

Ummu dake kallonsu ma ajiyar zuciya ta sauke hadi da murmushi domin ada tana yawan tunanin shin idan fu'ad din ya samu sauki zai karbi faheemah amatsayin mata kuwa?

Duk da a lokacin daza'a daura aurensu ta sanar dashi komai, kuma sanin cewa yana jinta amma babu bakin magana balle ta ji yanda ya karbi auren, but yanzu yanda ya nuna kulawarsa agareta yasa zuciyarta sanyi! Kuma tana da yakinin cewar Zasu so juna kamar ko wani ma'aurata wata rana.




"Diyata faheemah" jikin muryan ummu yasa ta sake shi da sauri domin ta manta basu kadai bane a parlour'n .........




Hannunta ummu ta kamo kana ta umarce kowa ya zauna, bayan duk sun nutsu ne ummu tace



"Diyata hakika ke haske ce ta ahalina, kin mana tuni akan abu masu muhimmanci wato addu'a, karatun Qur'ani , da sadakaq. Hakika dukkan abinda na lissafo warakace ga damuwa, ciwo, rashin lafiya dama dukkan wani misafa na duniya...

Numfashi tasauke kana ta cigaba, mun dauki cutar fu'ad a matsayin cutar da'a asibiti kadai ne zai samu lafiya, mun manta cewa Qur'ani babban magani ne ga dukkan cuta, hakika xurfin tunanin, hangen nasa ba sai babban Kadai ke iya wa ba, yaro ma zai iya domin Allah ke bawa mutum nutsuwa da har zaiyi tunanin hangen nasa, nutsuwar ki daga Allah take, Allahu ne yabawa son lafiya amma kece sila domin ke kikayi abinda mu ka kasa yi kusan shekaru bakwai, da haka nake kiran ku ya'yana ku rige alkur'ani da add'ua domin waraka ce daga dukkan cuta /damuwa. Allah ya albarkaci rayuwarki tare da baki zuri'a dayyiba diyata".
.

Takarasa tana share hawayen ta


"ameen"



dukkansu suka amsa, kana faheemah tace


"ummu haka Allah yaso, yanzu ne lokacin da Allah yayi zai tashi kafadunsa kenan, kidaina kuka ummunah"

takarasa tana share mata hawaye, jinjina kai ummu tayi, aranta tana yaba nutsuwa hadi hankali Faheemah...
Maza kuje kuyi sallah, sai kuzo muji abinci cewar uwa ta gari(ummu) anwar da fu'ad suka fita domin zuwa masallaci yayinda su faheemah suka nufi dakinsu domin yin tasu sallar...


Mataikatan gida kuwa mamaki sosai suka dinga yi ganin fu'ad akan kafafunsa.



Adamu mai bawa flowers ruwa rugawa yayi toilet dinsu , domin ganin fu'ad din yake kamar fatalwa domin shekaru bakwai mutum na kwance amma kawai yau tsullum ya ganshi tsaye dole ya shiga rudani, (sai dai ba abun mamaki bane, buwayar Allah ta wuce wasa, domin Allah zai iya canza komai alokacin daya so) dariya anwar yasaki har da rike ciki "dude kazama spirit kaga yadda adamu ya ruga akuje kuwa?" Yafada yana sake tsakin dariyar tsokana. Hararan wasa fu'ad ya jefa masa kana yayi Murmushi batare da yace komai ba, domin sarai yaga sanda adamu ya jefar da abun bawa flowers ruwa ya ruga a guje da'a ce yawan dariya dabi'arsa da babu abinda zai hana shi yi...
Bayan sun iddar ne, malam iro mai gadi yayiwa fu'ad murna sosai hadi da addu'a hakama sauran ma'aikatan gida, amma banda Adamu daya kulle kansa a toilet yaki fitowa... Lolz๐Ÿ˜น๐Ÿ’”



Zaune suke babu abinda kake ji sai karan spoons, amma banda fu'ad da faheemah


"diyata! son!!?" ummu ta kirasu atare, kana ta ษ—ora da cewa "ya naga ba ku cin abinci? "

"Ummu abinci ya min nauyi bazan iya ci ba"
cewar fu'ad yana shagwabewa ummuh.

murmushi ummu tayi domin tayi missing wanna shagawabar tashi idan yaso yi..


"son babu wani nauyi kawai dai dan ka dade baka ci abinci irin wanna ba, sai abu liquid (abu mai ruwa)"


juyowa tayi ga faheemah, tace


"ke fa diyata?

Murmushi tayi kana ta dauki spoon tafara cusawa ba dan tana jin yunwa ba, haka kawai taji batason cin abincin ganin bai ci ba


Maganar ummu ce ta katsa mata tunani,

"toh yanzu me zaka ci son?"


"Kunu"
ya fada ahankali

" No son! Inaso kaci abinci a yau kamar kowa yau, kai baka gaji ba? Shekaru bakwai kana shan cima kusan iri daya, saboda haka ka fadi wani abu"


dan Jim yayi kana yace "indomie"


"okay bari na dafa maka"

domin tasan bai fiye son cin abunci masu aiki ba.

"ummu ki zauna na dafa masa"

cewar Faheemah dake mikewa.

"Toh diyar albarka"

da kallon kasan ido ya bita sosai tafiyar ta ke birgesa komai a nutse take yin sa cikin ransa ya ce

"unique lady"


fareesa dake kallonsa kuwa matse dariyar ta take ganin yanda ya bita da kallo, "love dariya me kike?" Cewar anwar ya tambayeta kasa kasa, nuna masa fu'ad tayi, dariya shima yayi kana yace

" dude kula kar wuyanka ya kage"

ko kallansa Fu'ad baiyiba bare yasamu amsa, mikewa yayi domin so yake yayi wanka, duk jikinsa baya ma jin dadin ta....


"ummunah zan shiga nayi wanka"


yafada tareda yana sumbatar goshinta, kamar yadda ya saba ada, kana ya shiga takawa cikin tafiyarsa dabata gama kwari ba domin barin parlour



" okay my son a fito lafiya".


Tana shiga kitchen din ta fara hada indomie din wanna yaji red bell, onion , chicken minced meat, green bell, yellow bell, little oil , powder garlic kadan , kana ta sanya all purposes seasoning. Sosai kitchen din ke tashin kamshi wanda har su ummu dake parlor suna jiyo aroma din girkin ta.
Kwai shida ta soya masa kana ta Juye indomie a plate hadi da dora kwan daga gefen indomie, tray mai kyau ta dora akai kana ta dauki table water da fork ๐Ÿด ta dora daga gefen tray din wani plate din ta dauko ta rufe abinci kana ta fice zuwa parlor...



Tana zuwa parlor ta tarar da baya nan, sai ummu dake waya da hajiya sa'a (mahaifiyar anwar) tana sanar da ita tashin Fu'ad d'in.

Daga yanda muryan hajiya sa'a ketashi ta cikin wayan zaka Karanci farincikinta...




Sauke wayar ummu tayi, kana ce " diyata ya shiga dakin ku, ki kai masa can"


" toh"

ta amsa hadi da juyawa.


"Assalama alai...."

Sallamar ta makale abakinta ganinsa tsaye daure da towel yayinda ruwa ke diga daga glowing skin dinsa, juyowa yayi ganin ta tsaye kanta akasa yasa shi takowa ahankali zuwa gareta, tray din hannunta ya karba, ya ajiye a saman dressing mirror, numfashi tasauke kana ta juya domin barin dakin....



"Heyyyyy"



jin saukar muryansa akunnuwanta yasa ta tsaya cak!

"Dawo ki zauna "

asanyaye ta zauna tana ta faman murza wata danyar arzufa dake hannunta sai daukan ido yake, duk da babu wata kwallliya mai yawa ajikinsa, domin irin round din nan ne sai fararen stones da aka zagaye azurfan dashi, duk da yayi mata yawa domin da bakin zare ta nan nada shi kana yake dan zama ahannunta saboda sosai take son zoben.





Ahankali ta dago kanta ta ganshi yana brushing lallausan gashinsa yayinda yake sanya da black 3quarta trouser , sai red armless shirt wanna ya fito masa da siffarsa ta karfa'ffan maza, ajiyar zuciya ta sauke tana yaba kyawunsa aranta, yanzu tafi ganin kyawun sa fiye da da.......




Kusa da ita ya dawo ya zauna Wanda hakan yasata sake takura, domin ganin shi take tamkar bakonta, ganinshi take kamar wani sabon fu'ad, ganin shi take kamar ba fu'ad dinta dake kwance always ba, ganinshi take kamar ba fufu dinta da take masa masa surutu da goge jikinsa da kuma bashi abincinsa ba ne.


"Faheeeeeee am hungry"

ya fada tamkar mai rada.
lumshe manyan farare idanunta tayi jin sunan daya kirata dashi , sosai takejin dadin sunan baya ga umminta babu Wanda ya sake kiranta da hakan, sannan tana mamakin yanda ya rike sunanta ashe ya rike sunan ta. Mutumin dake kwance baya motsi bare magana amma sunanta daram abakinsa....



Janyo table dake gefenta tayi kana ta dauko abunci ta dora a table din, bude abincin tayi wanda hakan ya sa shi lumshe rikitatun idanuwansa domin sosai kamshin ya dakesa!



Mikewa tayi domin dauko masa cup din dazai sha ruwa domin ta manta dazu, dakatar da ita yayi kana yace

"zan sha haka karki damu"

zama tayi ta cigaba ta murza zobenta ganin bai ci ba yasa ta ce

" ka... k...a ci... Abinci karya yayi sanyi"


Ta fada cikin dan hardewan murya, kallonta yayi kana yace

"ke nake jira faheeee"

Kana ya sake cewa


" feed me as you always do"

kasa ta kara yi da kanta domin wani matsananci nauyinsa take ji

"please faheeeeeeeee ur fufu is hungry"

ji tayi kamar kasa ta tsage ta shige, daman duk kiran datake masa da wanna sunan m yana ji? "Wayyoni! Faheemah" ta fada aranta....


Ganin yanayin data shiga yasa shi sakin murmushin gefen baki kana yayi bismillah ya shiga cin indomie'n wanda dadinsa ke ratsa ji sosai...

Ruwa ya dauko zai sha tayi saurin rike goran ruwan tuno wani abu daya faru, kallon mamaki yayi mata.



Girgiza kai ta shiga kana tace "Dan Allah karka sha ka manta?"



Tafada fuskarta ta nuna tsoro, Murmushi Yayi tuno da abinda yasa ta yin hakan.



" Don't be afraid okay? Nasamu lafiya da yardar Allah, bayan ma duk kice kika dinga dura min ruwa ranar"



yafada cikin zolaya yana dan dungure mata kai. Cikn matsanincin kunya ta rufe fuskarta da tafin hannayenta kana tace,



"ai naga kamar kana jin kishiruwa ne da yawa shiyasa nabaka"



Tafada asanyaye domin tayi matukar tsorata ranar, Murmushi kawai yayi batareda yace komai.......





*(Team Faheemah &Fu'ad ya kuka ga awanna page din?๐Ÿ˜ Jarumin naku fa Allah yayi tashin sa, ku Cigaba dabin alkalamin noor dan ji yanda zata kaya arayuwar faheemah... muje zuwa my people much love.)*๐Ÿ’–


Thanks for reading my first novel

Noor Eemaan๐Ÿฅ€๐ŸŒธ

๐Ÿ’”RAYUWAR FAHEEMAH ๐Ÿ’”


_by NoorEemaan_๐Ÿ“šโœ๏ธ


kyauta ne (free novel)

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din..

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



"Life is the most difficult exam.
Many people fail bcos they try to copy others, not realizing that everyone has a different questions paper "๐Ÿ‘Œ



33-34

(Not edited)

Da misalin karfe 9:00 nadare zaune yake shi da ummu a had'ad'iyyar Parlor su, ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ummu ta gama bashi labarin yadda aurensu ya kasance, sosai yaji tausayinta domin ita din Karamar yarinya ce wacce a shekarunta bai kamata ta fuskanci wadan'nan wahalhalun ba, saidai kaddarartace hakan dole ya zomata, hakika yana bukatar jin cikakan labarinta, yafada aransa, kana ya ware lips dinsa yace

"Ummunah karki damu in sha Allah komai zaidawo yanda ya dace"


"Allah yasa son, domin inaso rayuwarta ta inganta inaso naga tana farinciki kamar kowa! Saidai hakan bezaiyu ba har sai ta daidaita da abbuhnta"

hannayeta ya kamo kana yace

"ki kwantar da Hankali ummu, i promise to do my possible best dan ganin komai ya dawo Normal."


"Allah ya maka albarka ya kuma Kara maka lafiya"

da "ameen" ya amsa cikin kaunar mahaifiyarsa.


Sumbatar hannunta yayi kana ya yi mata sai da safe ya fice daga parlor...



Tsaye take ajikin window wanda kai tsaye kana hango haraban gidan da aka kawa ta da fitilu kai kace da rana ne. Tunani take wanda baya wuce na yan gidansu, yayinda kuma wani bangaren na zuciyarta ke fargaban zai dauke ta a matsayin mata ko akasin haka? Da'alama batasan ya shigo ba, domin tayi nisa aduniyar tunani...
Kura mata ido yayi yayinda yabiki rigar jikinta da kallo wanda yakasance yellow mai gutun hannu, yakai mata har kasa sai dai Sam bai da nauyi, yayinda shape dinta na figure8 ya bayyana,wanda kana iya hagon shafaffen cikin, wanda hakan ya kara bawa wide hips dinta fitowa sosai.



Cikin tafiyar kasaitar shi wanda hakan ke nuna da shi din, tsayayye kuma lafiyayyen namiijine ya taraso wajenta, daidai saitin wuyanta ya huro mata iskan bakinsa...


Afirgice ta juyo zata kwalla kara domin kwata kwata bata sammanci hakan ba, kuma bata ji shigowarsa ba... Hade bakinsu yayi batare da yayi mata komai ba, bayan 2min ya cire bakinsa kana ya shige toilet batare da yace mata komai ba...



Tana nan tsaye har ya fito, bai kulata ba ya je gaban dressing mirror ya zauna kana ya yafutota da hannu, Cikin sanyinta ta karosa gabansa...


"are you not tired of standing?"

ya tambayeta yana dage girarsa daya, shiru tayi batare da tace komi ba.

"Babu amsa?"

Ya sake tambayarta, cikin zazzakar muryan ta tace


"Eh"

"okay fine"

yace yana dan tabe bakinsa.

Lotion ya miko mata, cikin duburbucewa tace

" me.. Zan.. Yi dashi?"

murmushi da iyaka labbansa yayi kana yace




"shafa min zaki yi"


kasa tayi domin batajin Zata iya shafa masa, domin kwarjini yake mata sosai, domin koda lokacin yana kwance tausayinsa ne ya danne nauyinsa hadi da kunyar sa har take sanya masa kaya batare da wani tunani ba......




Shi kuwa mamaki yake yanda ko kallansa bata iyawa yanzu saba'nin da

" faheeee am waiting for you nau"

ya fada a marairace, and idan kin gama ga kaya na nan yafada yana nuni da sleeping dress dinsa dake kan gado...



*( kaji fu'ad dinnan kabar mana faheemah ta huta hakanan a toh, baka warke ba... ko ya kuka ce fans?)*



jin saukar husky voice dinsa mai dauke da amo na musamman yasa ta lumshe idanunta kana hawaye suka biyo baya, tayaya zata sanya wa wanna babban kaya? Tafada aranta, kana cikin sheshekan kuka tace

" dan Allah kayi hakuri"

tafada tana hada hannayen ta yayinda zuciyarta ke dukan tara-tara wanda kana iya hango hakan ta yanda kirjinta ke sama da kasa...


Kura mata rikitatun idanunsa yayi aransa yana fadin ko me abun kuka kuma?

" gulma"

yafada kasan makoshi, shiryawa yashiga yi batare da ya kuma bin ta kanta ba..

Ita kuwa idanunta, ta runtse har yanxu bata bude ba...

Cak!

Taji an daga ta sama, waro manyan idanunta tayi ta sauke su akan nasa, tsare gida yayi alamun bayason musu ko korafi.

Shiru tayi tare da lafewa ajikinsa tamkar wata kitty ( jaririn mage)

shimfideta Yayi kana ya kashe kwayayyan dakin sai dim light dake beside drower ya bari, Gadon ya hau kana ya sake daga ta Cak! ya dora a saman faffadan kirjinsa.


Ajiyar zuciya ya sauke haka itama, saidai nata boyayyene.



Tunani ya shiga yi tayaya zai bata farinciki? Tayaya zai sata dariya domin ita mai muhimmanci ce agareshi, wani barin na zuciyarsa ya bashi amsar



"ilimi"

yeah! ummu ta fada masa yarinyar na matukar son karatu daga haduwar farkonsu ta fahimci hakan....





"Faheeeeeeta" ya ja suna ta, cikin bacci daya fara daukanta taji muryansa,


"Na'am" ta amsa cikin muryan bacci.


"meyasaki kuka dazu? And banason musu ko karya"

Ya tambayeta domin abun ya dan tsaya masa rai.

Be zai so zuciyar data masa hallaci ya zama shine silar damuwarta ko kukan ta ba.


Yawu ta hadiya kana cikin shagwaba hadi da sakalci da bata san ta iya ba ta ce


"ba kai ne kace na saka maka kaya ba, babba da kai" ta karasa tana turo dan karamin bakinta.

Murmushi kawai yayi jin saukar lips dinta akan kirjinsa domin rigar jikinsa mai budadden wuyane wanda kana iya hango lallausan Gashin kirjinsa dake ta sheki.

"Ni kike turowa baki?"

Dago kanta tayi kana ta shiga girgiza masa kai alamar "a'a" mayar da kanta yayi ya kwantar kana ya tofe su da add'ua, bubbuga bayanta ya shiga yi wanda in less than 1hour bacci mai dadi yayi nasarar dauketa, alarm ya saita 3:00am domin yin ibadan dare kamar yadda ya saba kafin kwanciyarsa jinya.

babu jimawa shima bacci ya dauke shi...




Uku daidai ya farka, ahankali ya zareta ajikinsa, saidai yana zareta ta tashi, be ce komai ba ya sauka a gadon, itama bin shi take kokarin yi cikin magagin bacci.


Ganin haka ya tsaya yana kallon yanda take hada hanya idanunta a rufe.



Lallausan hannayensa yasa ya shiga tapping fuskarta kana cikin cool voice yace

" faheee open your eyes "

jin muryan sa yasa ta bude idanunta kana cikin muryan bacci tace

" I want to follow you "

Tafada tana karya wuya gefe, kafadunta ya kamo kana yace

"alwala zanyi koma baccin ki" yafada yana kokarin zaunar da ita kan gadon.


"Um! Um!! Tafada cikin zallan shagwaba nima zanyi alwalan"

kansa kawai ya jinjina ya shiga toilet din, bayan ya fito ta shiga.



Bayan ta fito ta Tarar da ya shumfida sallaya, hijab ta dauko ya shiga jansu salla.....

Basu runtse ba sai bayan sallar

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment