Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shiga kunci. Kinji abunda nace miki?"

"Na...na...na... Ji bazan sake yi mata komai ba"

tafada a rarrabe bakinciki na cinta na soyaayar da yake nuna wa faheemah amma ba halin nunawa, wato saboda matarsa yasa aka gana mata wanna uban azaban? Yanzu duk son da take masa ya tashi a banza kenan? Domin bata ga alamun yana son ta ba, sai ma wani kallon tsana da yake mata.


Mikewa yayi zai bar dakin tayi saurin cewa "ya fu'ad ka taimakeni, na tuba wallahi ko kallon banza bazan sake mata ba, kayi hakuri zan mutu anan idan ban fita ba"


Wani murmurshi gefen baki yayi kana yace "ooh I see, Ashe ba dadi kike son kashe min mata da bakinciki, ke da barin nan sai kinyi hankali" ya fada hadi da barin dakin domin sosai rana ke dukan sa a dakin.


Bakin motar suka raka fu'ad cikin husky voice dinsa yace "nagode muku sosai, and gobe zaku koma bakin aikinku".( kasancewar a company din su Ummu samarin ke aiki, domin suna daga cikin din security a company, kasancewar fu'ad ya yaba da hankalinsu yasa suka yi masa wanna aikin) ya sake cewa "zan kira na sanar da lokacin da zaku sake ta".
Bandir din 1k guda biyu ya ciro masu hadi da bawa kowannen su daya, sosai sukayi masa Godiya domin shi din mai alheri ne, domin duk sanda zai zo company dinsu baya barin su haka, sun kuma yi imanin cewa umaimah gagarimin laifi tayi masa Wanda yasa shi yi mata wanna hukuncin.
Musabaha suka sake yi kana ya Shige motarsa ya bar gidan...


Bangaren umaimah sosai tayi kuka hadi da nadamar abunda tayi, domin abunda yake abayyane ne cewar ko kallo bata ishe shi,kai ko kafar matarsa bata kamo akomai ba, bare tasa rai zai so ta da munanan haleyanta.

A karon farko da tayi tunanin kai kukan ta ga Allah rabbu samawati, bayan tsawon lokaci, alwala tayi a toilet dake cikin dakin kana ta Shiga tunanin daga ina zata fara kasancewar ta mai wasa da sallah, sallan ta tayar tare da nadama fal ranta.........





Share and comment




Noor Eemaan ce🥀🌸
07082281566




Thank you for reading #rayuwar FAHEEMAH


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

💔RAYUWAR FAHEEMAH💔

_by noor Eemaan_📚✍️

wanna littafin kyauta ne ( free novel)


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din


YA ALLAH!!! Satisfy my heart with halal and keep me from everything which is haram and make me your obedience slave
AMEEN.



55-56

(Not edited)


Yana zuwa gida kai tsaye part dinsu ya nufa, sama ya hau domin sun fi amfani da dakinsa musamman in yana gida, kayan jikinsa ya cire kana ya shige toilet, zaro ido yayi domin kwata-kwata bai yi tunanin tana toilet din ba kasancewar ko motsi bata yiba.
jacuzzi da take kwance ya nufa, hadi da shigewa cikin jacuzzi'n sannan ya dora ta a saman sa, sai a lokacin ta bude idanunta masu cike da bacci, dariyar da bai yi niyya ba ta kufce masa, "wato ma bacci kike a toilet faheee?"



Turo baki tayi kana tace

"Allah my man baccin bai isheni please meyasa ka tashe ni?"

Tafada tana sakar masa kukan shagwaba hadi da Dan cizon chest din shi, Wanda ya sashi jin wani feelings na taso masa "arhhh!!!"
Yace kana a hankali ya hade bakin su waje daya ya Shiga bata hot kisses....


Bayan 10minutes ya xare bakin sa a hankali hadi da cewa "am sorry nina hanaki bacci ko? Bana gajiya dake sugar na shi yasa, please ki cigaba da nuna wanna jarumtar, and I promise to be the most best husband ever".



Cikin jin dadin kalamansa ta Shiga bashi wani sanyayyar kiss alamun godiya gareshi...

Sun dau 1 hour a toilet suna soyaayar su kana suka fito sanye da bathrobe, bayan sun shirya cikin kananun kaya, sannan ya sanar da ita gobe da karfe bakwai zasu yi jarabawan jamb, murna sosai tayi kana ta dauko pass questions din daya samo mata, ta dawo jikinsa ta Shiga karatu.....


★★★

Karfe biyar daidai ya kira su Oscar yace da karfe shida daidai su sake umaimah sannan su bata trollys dinta.


Kasa shiru tayi tace "my man wacece kake cewa a saka?"


Dan tsare gida yayi kana yace "shhhhh! ba ruwan ki, Dole ta fuskanci hukunci akan abunda tayi miki banaso ki ce komai matukar na isa dake!"

Shiru tayi domin taga alamun ransa ya fara baci, duk da bata ci dadi ba, amma soyaayar mijinta ya fiye mata wata umaimah, dan haka ta fara yi masa shrimen yarinyatar ta data san yafi so, nan da nan ya saki fuska suka Shiga bawa fure ruwa.


★★★

"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un!" hajja Hindu ta fada cikin karaji ganin umaimah da ta shigo kamar wata sabuwar kamu, a haukace tace "umaimah kece?" Ta tambaya unbelievable.


Ganin diyarta yar kwalisa ta dawo tamkar mahaukaciya.



"Rashin lafiya kika yi ne, ko wani abu?" Hajja Hindu ta kara tambaya cikin matsanancin tashin hankali.


Fashewa tayi da kuka hadi da fadawa jikin mamanta, tabass uwa daban take komai lalacewarta kuwa, soyaayar ta daban take, daba dan haka ba, bazata iya runguman umaimah ba saboda tashin da jikinta keyi cikin kuka tace
"mama na hakura da ya fu'ad har abada bayasona"
nan ta shiga bawa hajja hindu labarin komai.....


Cikin bacin rai hajja hindu tace "dan kinyi wanna abun zai miki haka? Ita matar tasa gwal ce? Yau ta fara shan wahala? Wace wahala ce kishiyar uwarta bata gana mata ba?"


"Nikam mama na hakura wallahi nayi nadama"

"ke yi min shiru! dole ki mallakeshi, dole muci dukiyar dana da de ina hari"


"wallahi ba ruwana mama bazan sake musu komai ba" tafada tana shigewa dakinta domin yin wanka....


"Hmmm dole yarinya ki koma domin gobe zan koma gidan boka" ta fada fuskarta na nuna zallan mugunta da zata yi( Allah ya tsare imaninmu ameen).


****★ ****★ ****★





*ABBUH*

A karo na barkatai ya shiga kiran sunan *FAHEEMAH*.

" Ina diyata take? Ina faheemah? Ina take nake tambayarki" ya fada cikin halin ciwo, yana kallo mami fuskar sa ba walwala, musamman tuno cewar gudan jininsa na dauke da cikin dan gaba da fatiha.

Jameela dake gefe tana sharar kwalla saboda tausayin halin da abbuh yake ciki, sai da gabanta ya fadi domin tun suna da kananun shekaru rabon da ta ji ya kira sunan "faheemah" Ganin babu Wanda ya bashi amsa yasa bai kuma magana ba, bangaren mami kuwa tama rasa me zatace, domin fuskar abbuh a daure bare tayi masa karya, da alamu kuma asirin jikinsa ya karye...



Likita ya shigo domin dubasa, ya matsa lallai a sallameshi shima Likitan bai ja magana ba ganin jikinsa ba wata matsala sosai daman shock ne ya kama shi.




Zuwan su gida abbuh ya dudduba bai ga faheemah ba cikin fusata yace. "hajara ina diyata?"

"Ummm...uh...uhmm...ta... bi... ta bi wani saurayi sun gud..."

tsawar daya daka mata yasa tayi shiru babu shiri ga wani gumi mai xafi na karyo mata.
Tabass komai ya lalace, abbuh yadawo alhajin sa.



"Koda wasa kada ki kara fadin haka ga faheemah, koda duka duniya zasu taru suce haka zan karya ta su, kuma matukar kinason xaman gidanan,toh kafin na dawo ki samo amsar tambayata"


yafice Cikin sauri domin bayaso yayi abunda zai yi nadamar hakan.
Jameela dake gefe ta fashe da kuka domin shiru da abbuh yayi mata akan cikin, yasake tayar Mata da hankali, mami kuwa ko lallashin Jameela takasa yi, domin tana cikin gagarumin matsala.

Domin Allah Allah take gobe yayi ta koma gidan boka kafin komai ya ida lalace mata.


★★★

Washegari
_5:50am_

su kayi sallama dasu ummu domin lafiya rubuta jamb din faheemah, domin wudil aka tura ta yasa suka yi sammako.
Kansancewar babu ababen hawa a titin sosai yasa cikin 55mins suka isa can. A hakan basu yi sauri ba, domin soyaayyar su suke sha, ga kuma sanyayar iskar asuba mai dadi dake ratsa su ya sa su jin wani shauki na musamman na diban su.



Kujerar baya suka Shige bayan sun zo makaranta, domin har lokacin gari bai ida wayewa sosai ba.

"kin gani ko, duk kin azalzaleni mu tafi my maan kada muyi latti, gashi ko mutum daya babu"

ya karasa cikin kwaikwayon muryan ta, hadi da Dan dungure mata kai, dariya tayi hadi da fadawa jikinsa.



"my man duk zumudi ne fa, am sorry kaji"

"na gani ai, keda tun karfe 4 kike ce mutaho"


" Allah naxata da nisa sosai Shiyasa nace mu taho" bai kuma cewa komai ba ya shige jikinta sosai yana shakar daddan kamshinta, ko minti 10 ba'a yiba taji saukar numfashinsa alamun yayi bacci.



Murmushi mai sauti tayi kana ta Shiga shafa lallausan gashin sa, lumshe idaunta itama tayi, tana jin kewar abbuhn'ta na ratsa ta, dama duka yan gidan duk da cewar ba sonta suke Ba, amma tana jin kewarsu kuma ko daya bata rike su a rai ba.


Hayaniyar data fara jine yasa ta ware idanunta, Had'add'en agogan hannunsa ta kalla bakwai da minti uku ta gani, cikin sauri ta Shiga tashinsa, shima idaunsa ya bude hadi da tashi a jikinta.


"My maan lokaci yayi"




"shhh! i know heemah" yana fadin haka ya kamo lips dinta ya bata sumbata na 3mins kana a kunne ya rada Mata
"good luck kisses" murmushi tayi hadi da bashi sumbata a kumatu tace "tnx my man" ita ma cikin rada, kana ta fito a motar, shima fitowa yayi ya riko hannunta har bakin wurin ya rakata kana ya tsaya, sai da suka gama yi mata duk wani abunda daya cancanci ta shiga dakin jarabawan kana ya koma mota, yana tsumayin fitowarta...




Bayan awa uku ya hango tahowar ta tana sharar kwalla gabansa ne ya fadi, cikin sauri ya fito domin baya fatan a samu wata matsala "goofy Angel" yafada yana rike kafadunta, "what is it? Did anything go wrong?"

Girgiza kai tayi, "then why are you crying?" Ya tambayeta fuskarsa kamar shima yayi kukan.

Ganin tayi shiru yasa a hankali ya janyo mayafin abayarta ya rufesu kasancewar kuma yana da girma ya sa ya rufesun.




"Please say something heemah"


"Wani ne ya shigo da waya jamb hall shine ya ke satar masa, aka kamashi hadi da kashe computer da yake amfani dashi, yanxu ya rasa jarabawanshi, Gashi can sai kuka yake amma sunki hakura. Muje ka musu magana su kyaleshi yayi jarabawan, ya ban tausayi"

Tafada tana jan hannunsa, fuskarta ya kamo yace "relax relax babe, bazan iya komai akai ba, domin ya karye doka ne"



"toh su basa yafewa tunda kaddarace ta hau kansa" ta fada tana turo baki.


murmushi yayi kana yace "ke kenan heemah mai saurin yafiya, ba kowa ne keda sauri yafiya ba. Duk da yafewa mutum abune mai matukar kyau, amma ba kowa keda zuciyar yafiya ba! Yanzu kisan me zaki mun? Kiyi shiru kibar kukan nan kada kanki yayi ciwo, kiyi masa addu'a Allah ya zaba masa abunda yake mafi alkhairi okay? Jinjina kai alamun eh tayi kana yace Oya smile for your fufu"



dariya ya bata domin ya tuno mata da wasu lokuta da suka shude, lokacin da baya iya tashi, lips dinta yayi wa light kiss kana ya gyara mata mafayin hadi da kamo hannu ta suka shige motarsa...



Yan makarantar da kallon sha'awa suka bisu domin yawancinsu har fatan samun miji kamar Fu'ad suke domin kulawar Da yake mata abayyane yake, ta idanunsa ma zaka Karanci soyayyar da yake mata, wasu kuma suna tunanin budurwan sace.



Amotar yake tambayarta ya exam din, " so sweet, sai dai fatan mu ci" ta amsa masa.


"in sha Allah angel I trust you" murmushi tayi kawai kana ta ce

" ina jin yunwa my maan"

"Bari mu samu restaurant muyi breakfast ko"

"Toh" ta amsa


restaurant suka samu mai kyau, yayi musu ordering chips da bread omelet hadi da ruwa swan da lemo. Bayan sun gama ya biya charges su din su kana suka cigaba da tafiya, rabi tuki rabi Soyayyya sai 1:30 suka iso gida.



★★

Mami kuwa sauri sauri take ta karasa wurin boko domin jiya rufe kanta tayi a daki bata bari sun hadu da Abbuh ba.

Tun daga nesa ta hango wasu sirarun mata tsaye, cikin mamaki take tunanin ko me suke? Domin bata taba ganin mutane a waje haka ba, tana karasa wajen taga Ashe daya daga cikin matan hajja Hindu ce tsaye cikin halin data kasa fahimta. Gaba daya ta manta fadan dake tsakaninsu tace "hajja Hindu lafiya? Mike faruwa?"



"Ya mutu! ya mutu!! Ya mutu!!! Hajara" take maimaitawa hannunta aka tana fadin

"na Shiga uku na!"


Cikin Dan akurkin dakin dayake ciki mami ta nufa, domin gani take karya ne, itama hajja Hindu rufa mata baya tayi domin daman bata shiga ba, labari matan data tarar su ka bata.

Toshe hancinsu sukayi saboda wani mugu mugun wari da ya ziyarci hancinsu, ga wani uban muni daya kara fiye da na baya, kudaje sai binsa suke ga wasu tsutsosi da ba'a San daga ina suke fitowa ba sun dabaibayeshi, ga allon tsafinsa agefen sa, da alama tsafin yake aka zari ran sa.*( innalillahi wa innah ilaihi raju'un. Duniya gidan aro, Allah ya ara masa lokaci, yayi abunda yaso ga yanda karshenshi ya kasance. Wai wanda yake tunanin zai iya kashe mutum, ya haukata mutum, ya raba soyaayar iyaye, soyaayar Mata da miji wai yau shine yayi mutuwan wulakanci, tunda ya iya wandannan munanan ayyukan meya sa bai dawaumma aduniyar ba? Tabass babu mai iko da kowa da komai face Allah subhana wata'ala , daya halicce mu ,shi ke yi a yadda yaso da lokacin daya so think wise ya jama'a)*.



Wani katon maciji bakikirin mai jajayen idanu ya faso kai Wanda basu san daga inda ya fito ba, kananande jikin boka Wanna micijin yayi, wani uban ihu su mami suka sa kana fito da gudu, matan dake waje duk sun watse, wasu sun tuba, wasu kuma sun Dora aniyar neman wani bokan *( Allah ya tsare imaninmu ameen)*.

Gudu sosai suke suna ihu a cikin dajin sun dau lokaci kana suka fito suna maida numfashi, ko takalma babu a kafafun su, sun yi mugun fita a hayyacinsu...






Share and comment


Thanks for reading my novel.



Noor Eemaan🥀🌸
07082281566



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


💔RAYUWAR FAHEEMAH💔


Wanna littafina na kyauta ne( free novel)


Wattpad @NoorEemaan *(Akwai wannan labarin a Wattpad, da ma duk wani book dana taba yi complete, ga handle nan, ina ta ganin karin followers ina godiya, dan Allah kuyi following dina, don't forget my Wattpad handle still remain @NoorEemaan)*



57-58

(Not edited)



Taxi suka tare Wanda da kyar ya dauke su bayan hada shi da Allah dasuka yi saboda yadda ya gansu ya dauka mahaukata ne.

Suna cikin lafiya ko kwakwaran motsi basa yi bare magana, domin har yanzu shock din bai sake su ba. Wani babban mota ne ya yi Karo dasu, cikin kankanin lokaci suka yi mumunan hatsari, sallati jama'a suka shiga yi kana mutane suka fara tururuwan zuwa ganin abunda ya faru, mai babban mota kam bai tsaya ba ya gudu abunsa. Kwata kwata bazaka taba gane su mami gaba daya jini ya gama bata dukkanin jikinsu babu kyaun gani. Wani iko Allah kuma babu abunda ya samu driver sai dan ciwo a guiwar hannunsa,duba motar ya yi aka sinci wayar mami ciki, kasancewar ba security yasa suka buga wa abbuh waya domin a sanar dashi.



Bangaren abbuh kuwa waya ya bugawa su kawo anas da mijin mummy zaynab akan su zo kano domin akwai Matsala sosai.


Ya ida wayar kenan kiran ya shigo wayarsa sunan mami ya gani a screen din wayar duk da ransa na matukar baci hakan bai hanashi dagawa ba ," akan nace ki gaya min inda diyata take kika bar gidan ko ? Kin kyaut....."..

"Bawan Allah ba ita bace, sun yi hatsari yanzu domin ko numfashi basa yi, zamu kai su asibitin Malam ka samemu acan" driver ya fada yana kashe wayar.

" Innalillahi wa inna illaihi raju'un" abbuh ya Shiga maimaitawa, Jameela dake zaune duk tayi laushi ta fashe da kuka domin duk ta ji abunda aka ce, kasancewar da hijab jikin ta yasa ta rufawa abbuh baya cikin sauri......

Isar su asibitin suka tarar an shigar da su mami emergency domin basu taimakon gaggawa. Sosai driver ya bawa abbuh hakuri hadi mika masa wayar mami, ya sanar da abbuh cewar zai tafi neman kudi ,amma zai dawo da yamma. "Babu komai abbuh ya ce masa, ya kuma kara da cewa da wasu marasa tsoron Allah ne da sun gudu, je ka nemawa iyalanka abunda zasuci na yafe zuwan naka gabadaya" godiya driver yayi kana ya fice yana yaba kyawun halin abbuh aransa.


Bayan awa biyar kana likitocin suka fito suna goge gumi domin ba kamarin wahala suka sha ba kafin Allah ya basu nasara,domin da farko ma sun zata mamin ta mutu.


"Meet me at my office alhaji" wani babban Likita ya fada da'a shekaru zai kai 45. Mara masa baya abbuh yayi suka shige office din likitan. " Have a sit please" doctor ya sake fada alamun girmamawa wa abbuh, bayan dan rubuce-rubuce da likitan yayi, kana ya d'ago fararren idanun sa ta cikin medicated glass dịn fuskar sa, ya kafe wa abbuh, kana yace
"asakamakon hatsarin da suka yi daya daga cikin matan ta rasa hannunta guda daya domin yankesa zamu yi saboda ya tashi a aiki, dayar matan kuma ta rasa kafarta guda daya da kuma hannunta daya shima yanke mata su za'ayi, dan haka idan ka amince gobe za'a Shiga theatre dasu"


Innalillahi wa innalillahi raju'un abbuh ke maimaitawa,domin duk da besan ko mami ce ta rasa hannu da kafa, ko hannun tarasa shikam yakasa bambamtawa? Hakuri hadi da nasihan doctor kewa abbuh akan amsar kaddara domin duka tunanin doctor matan sa ne su biyun.


murmushi mai ciwo abbuh yayi kana yayi wa Likita godiya ya fice. Charges din asibitin ya biya duka, duk da be San wacece hajja Hindu ba amma har nata ya biya. Zuwa yayi ya zauna kusa da Jameela datayi zuru zuru domin sosai take cikin kaduwa hadi da mamakin yadda komai ya kwabe musu cikin kankani lokaci. Tabbas har da sakacin mami da rashin kula da tarbiyyarta ya jefa Jameelan a wanna halin abbuh ya fada a ransa. Afili kuwa cewa yayi " wacece kawar maminku ko wacce suke yawan mu'amala tare?"



"Hmmm... am...Abbuh hajja Hindu ce duk da ban ganta amma itace"


"kina da number wani nata? Abbuh ya tambaya, eh ta amsa masa Kira ki sanar musu" cewar abbuh fuska adaure domin har yanzu yana matukar jin zafin Jameelan ,da kallo tabi shi tana fashewa da kuka domin ita tafison abbuh ya yi mata hukunci da wanna shiru da yayi mata akan cikin jikinta daya fara tasawa domin azahiri idan kaga cikin zaka zata bai wuce 2-3 month ba kasancewar cikin jikinta ya bi amma ya fi haka. Hawaye ta share kana tayi dialing number hajja Hindu...



umaimah dake zaune afalon su tana jiran zuwan mamanta domin babanta yadawo tun dazu yana jiran dawowarta. Ringing din wayar hajja Hindu dake kan kujera ne ya katse mata tunanin ta, domin daman agida ta bar wayan.




innalillahi wa innah ilaihun! Ta Shiga maimaitawa sakamakon abunda kunnenta ya jiye mata.... Kuka ta fasa kana ta Shiga kiran, baba! Baba!! Baba!!! Cikin sauri ya fito ta sanar abunda ya faru shima sallati ya Sanya kana suka nufi asibiti cikin sauri....



Abbuh tsaye yake a haraban asibitin yana kiran yan'uwa da abokanan arziki yana sanar musu. Bayan ya gama ne ya zauna anan haraban asibitin yana tunanin wacce duniya diyarsa take? Ina taje ? Wani hali take ciki? Sosai yake cikin kewar ta, musamman fuskarta mai tuno masa da maragaiya haleema ( Ummin faheemah) kasancewa suna kama, sai kuma ya tuno zancen mami, cikin sauri ya girgiza kai kana afili yace "wanna ba gaskiya bane,faheemah ta baxata taba yin hakan ba"



Yana son tambayar Jameela ina faheemah? Saidai Wanna kaddarar da ya faru ya hanashi, duk da yana cikin damuwa haka zai daure har mami ta farfado ta gaya masa domin be yarda da ita ba, baya ga haka zai so yan'wansa,da na mami, har ma Dana ummin faheemah domin so yake ayi komai agabansu...
.
Babu jimawa yaga wani mutum da wata budurwa sun fito a mota, haka kawai jikin shi ya bashi mijin hajja Hindu ne,Dan Allah yace "kaine mijin hajja Hindu?"


"Eh kwarai nine! Ok Tareda da matata sukayi hatsari cewar abbuh, jajjantawa suka yi wa juna,kana abbuh ya masa bayani abunda Likita yace.
Sosai baban umaimah ya jinjinawa wa abbuh, ya kuma yace ze mayar masa da kudinsa daya biya, amma sam abbuh yaki, Godiya baba umaimah yayi wa abbuh kana suka Shige ciki...


Umaimah kuwa ganin Jameela yasa ta karasa wajenta, gaisawa sukayi lami lafiya domin daga alamu dukkansu sun san wahalar da Kansu suke, domin wanda suke domin shi be san suna yi ba, ba kuma bazasu taba samun shi ba. Ga kuma halin da suke Shiga kwananan yasa komai fice musu aka.


Washegari aka yiwa su mami aikin Wanda yatafi successful, bayan nan aka mayar dasu dakin hutu kuma zuwa lokacin basu san waye akansu ba. Sai bayan kwana biyu aka fara Barin a Shiga duba

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment