Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da farko, domin ba'a son ana jika shi da ruwa saboda lalurarsa.

Wardrobe dinsa ta bude taga kaya a shake iri daban -daban, wasu kananun kayan ta dauko masa hadi da diaper ta sanya masa, sanna tayi oiling lallausan gashinsa ta taje masa tana sauke numfashi domin kula da namiji kamar fu'ad ba sauki saboda ingarman namjine sosai( giant). Yayi kyau kamar ka mai magana ya amsa,

"u look handsome "

ta fada cikin rada hadi da murmushi daya bayyana 1side dimple dinta.

Hakanan take jin farinciki kansancewar su tare, kayan data cire ta shiga toilet ta wanke masa hadi da shanyawa.

Gyaran dakin tayi ta fesa room freshener mai kamshi.

Wannan madannin tasake dannawa godon yadawo yanda yake, bargo ta rufa masa iya kirji kana takai jug din kunu kitchen tadawo, hannunsa ta rike tana wasa dashi dahaka bacci ya dauketa batare da ta shirya ba... ido ya kafeta dashi baya ko giftawa babu jimawa shima ya lumshe idanunsa...


Kiran sallar azahar ne ya tasheta, Jinta kwance jikin abu yasa tayi Saurin tashi...

"wayyoni! Kayi hakuri wallahi basan na kwanta maka a cinya ba"

tafada kamar zata saki kuka.

Ganin idanunsa arufe yasa ta gane bacci yake, alwala ta dauro tayi sallah bayan ta iddar ne taga idanunsa abude wannan karon.
Ruwa ta debo ta daura masa alwala domin yayi tasa sallah.


Bayan minti goma ta fita kitchen domin kawo masa kunun shinkafa dayayi fari shar gwanin sha'awa tashiga basa, bayan ya sha ta goge masa bakinsa inda ya zube, kana ta fice kitchen anan taga masu na aikin girki. Sannu da aiki ta musu suka amsa kana ta debi white rice kadan da miyar vegetable daya wadatu da namomi da kifi banda, a nan kitchen din ta zauna taci kana ta koma daki wurin ango fu'ad lolz

Haka ta wuni kula dashi a wanna ranar, kuma bata ji wata wahala sosai ba, tana kokarin canza masa diaper sun ummu suka dawo.

Shiru-shiru bata ji motsin shigowar su ummu ba hakan yasa ta mike domin duba su, kicibis sukayi akofar ta koma da baya hadi da tsunnawa ta gaishe da ummu tare da fareesa dake bayan ummu.

amsawa sukayi kana ummu ta riko hannunta izuwa gadon Fu'ad suka xauna.


"Diyata faheemah ya gida?'


"Lafiya lou ummu".

"Sannu kinji, Allah yamiki albarka I know is not easy kula da mai lalura irin na mijinki"


"Allah ummu ta fiki iya kula dashi, kinga har kumatu naga ya kara yau" ta fada cikin iyakar gaskiyarta.

Dariya maganar yabawa ummu, "toh daman fareesa ai tsakanin mata da miji sai Allah, kila ta fini sanin sirrin kula dashi ne" tafada tana kallon Faheemah da kanta ke kasa tana murmushi


dariya fareesa tayi kana ta kamo hannu fu'ad cikin kaunar yayanta tace



"brothernah kaga cute wife dinka ko?, burina yanzu naga ka tashi kana mana tafiyar nan taka cikin kasaita, tafada hawaye hadi da dariya suka taho mata lokaci d'aya tuno rayuwar su ta baya. Get well soon brother, i know kai da faheemah will be the most beautiful couples 💑 ever. Sai ta hada hannu faheemah da nashi, tace thank you so much Faheemah naji dadi yanda naga brother na karkashin kulawarki Allahu ya biyaki da gidan aljanna"



Da "ameen" ta amsa tana jinjina kaunar dake tsananin wanna ahalin. Labari ummu ta shiga bata yanda ta tarar da company din wasu abubuwan sai data gyara domin ganin babu idon mai company din yasawasu yin ha'inci, amma alhamdulillah ta gyara komai hadi da kafa musu sharudda, shiyasa ma basu dawo da wuri ba, amma ka'ida 4,:00 suke tashi.

"Allah ya kiyaye gaba"

Faheemah ta fada tana mamakin wasu Mutanen da basa tsoron Allah.....


Share fisabilillah
Comment


Thanks for reading my novel Rayuwar Faheemah.



💔RAYUWAR FAHEEMAH💔



_by Noor Eemaan_


kyautane (free novel)



The heart that believes and fears Allah shall always have peace&contentment. May u and ur family remain peaceful & contented. May Allah fufil all our needs, may he accept all our du'as, remove our difficulties, have mercy on our death, defeat our enemies, forgive our parents, guide our leaders to the right path, protect us from shaytaan & evil. Ameen ya hayyu ya qayyum juma'ah Mubarak to all my fans 💝


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


17-18
(not edited)

cikin wata daya ta saba dashi sosai duk da baya magana amma idan ta zauna ta dinga masa hira kai kace zai amsa mata ne, kusan rabin kayanta da komai ya dawo dakin. Saidai bayan Kwana biyu takan hau sama ta gyara dakinta.

"Jameela wai laifin me nayine? Yanzu kin canza min bakya daga wayata, idan ma kin daga ba magana mai dadi please idan na miki wani laifi ki gayamin nagyara...

" Dakata sani, wai meyasa kake takura wa rayuwata ne, wai dolene sai na cigaba da kulaka? kabarni dan Allah banason naci"

tafada cikin daga murya! mamaki ne yasa sani mutuwar tsaye, wai shi jameela mai son shi ke dagawa murya? Yafada aransa, afili yace "Jameela ya kamata mu fahimci juna idan ma laifi nayi wallahi zan baki hakuri, Ina son ki sosai"

yafada kamar zai yi kuka.

"Sani tun muna shaida juna karabu dani, ni babu abinda kamin, toh meyasa kika canza min? Wallahi Inasonki Jameela kada ki manta alkawarin auren damukayi please"

yahada hannayensa alamun roko

"Toh yanzu bana yi da kai sani, sai ya ya? nace sai ya ya?"

tafada cikin fada har mami ta taji muryan ta tayi Saurin fitowa,

"lafiya yar albarka keda wa?"

" na wuni mami" sani yafada yana durkusawa, lafiya ta amsa atakaice, kana tace "lafiya mekazo yi wurin yata?"
Shiru ya yi kansa a kasa domin baisan amsar dazai bata ba, saboda kansa ya daure.



"Sani kake ko saniya? Inaso ka kalli yata dakyau kaga kun dace ne? Mena kasa yaci bare yaba na sama kullum kana fama da babu, me gareka? dazaka iya kula da ita ta fada tana kallon machine din shi kirar lifan, kabar kofar gidanna kafin naci maka.... "



"Mami ya isa haka, ki yi shiru ki shiga gida ina zuwa" cewar jameela ka kace da sa'ar ta take. Sosai sani yayi mamaki uwar da yar, wai haka a halinsu yake? Lokaci daya duk sun sanja, cikin muryansa data yi rauni sosai yace, "jameela kada ki zama mai manta alkhairi"

dariyar rainin hankali tayi kana ta "nace meka taba min na a zo a gani? Ko wanna wayar?" Tafada tana daga wayar hannunta kirar infinixhot8 daya siya mata.

"Ba haka make nufi ba jameela..."

"toh ya kake nufi idan ma wayar ce zai mayar maka abunka domin nafi karfinta yanzu"

taja tsaki kana ta shige gida tana banko masa dan maidaidaicin gate dinsu mai kalan ash"

Asanyaye sani ya hau babur dinsa yabar kofar gidan, aransa yana tunanin meya sauya su haka? A wani bangare na zuciyarsa kuma yana nadama rashin bin umarnin iyaye ne ya ja masa, domin akwai wata cousin dinshi da akeso hadasu aure, amma ya murza wa idon shi toka yace lallai jameelan yakeso...



Yana kwance sambal kamar kullum tana gyara masa farce, surutu take masa kamar kullum saidai baya cewa komai sai kafeta da idanu da yayi.


"Kasan me ya fu'ad? Sanin baya magana yasa ta cigaba, wallahi na kagu naga ka fara tafiya, naga iya tsahonka sai kuma tayi murmushi nasan tafiyarka ma abun kallone" tafada sai ta sauko tana gwada tafiyar kasaita, haka take wuni yimasa sakalci kala Kala.


Shaving-cream hadi da shaving-stick ta dauko tafara yimasa shaving ba duka ta aske ba, sosai fuskarsa takara kyau sajen nan sai sheki yake bayan ta gama ne ta daura masa alwala itama tayi sallar, sai ta dauko kunun sa kamar kullum ta tana bashi kasancewar ba'a son ya na ci abu mai nauyi saboda lalurarsa.
Jin Saukar numfashin sa ya tabattar mata da yayi bacci, ganin shirun yayi yawa ga ba wani aikin yi, yasa ta fara dube dube. Idonta ne ya sauka kan wani babban littafi dake kamar karamin akwati, daukosa tayi tana budewa taga ashe photo album ne bude buttons din tayi. Hoton sane a farko zaune yake cikin office sanye da suit maroon color, yana amsa waya da telephone akan sai ya bada style mai kyau da alama kuma ya gama karatun shi tun yana da kananun shekaru saboda a hoton ba zai fi 26 ba, kallon photon take babu ko kiftawa domin yayi mata kyau sosai, haka ta dinga ganin hoton su kala kala wani yana karami, wani tare da abba da Fu'ad sun suit da alama ma a bank suka yi hoton, daga yanda suka yi hoton kadai zai tabattar da shakuwa da soyaaya dake tsakanin su, wani tare da fareesa da ummu, wasu a malaysia in da yayi karatu, sai kuma wani hoto tareda fuad da wani matashi da'a shekaru zai yi daya dana fu'ad din, haka ta cigaba da kallon hotonan har ta gaji ta ajiye domin hotunan nada yawan gaske.



Washegari bayan ta gama masa komai tabashi shayi mai kauri data hada masa kana itama tayi breakfast dinta, sama tahau domin gyarawa ummu dakin ta, bayan ta gama, ta gyara nata, kana ta kullo dakunan ta sauko.


A yau mummy zaynab ta kawowa kano xiyara burinta tayi tozali da yar gidan yayarta (Faheemah) ko zama batayi a gidansu dake dandishe ba ta taho gidansu faheemah.

Mami ce zaune afalon su dake da kyau ba laifi daidai rufin asiri, tana cin meat pie daya ji kayan hadi sosai, wanda saurayin jameela ne ya siyo mata jiya da d'ad'ad'are kasancewar bata ci wanda jameelan ta ajiyemata ajiyan ban sai yanzo.


Jin sallamar mummyn zaynab ne yasa gabanta faduwa, amma saboda ta kware a iya makirci sai tayi kalar tausayi hadi da tura meatpie din bayan kujera, cikin second 5 harta kakaro hawaye kana ta amsa sallamar cikin muryan kuka, shigowa mummyn zainab tayi hadi da tambayarta meke damunta?

"Ni hajara ya zanyi nashiga uku! Yarinyar nan bata kyauta min ba"

"wai wacce yarinya?"
cewar mummyn zaynab arude

rushewa tayi da kuka hadi da cewa "faheemah ce, yau kusan wata biyu bata gidannan ta gudu bansan inda ta nufa ba"

jin maganar mummyn zaynab tayi bambara Kwai, "anya aunty hajara kinsan me kike cewa kuwa?" Me zai sa Faheemah ta gudu?

" Wallahi ta gudu, akwai wani dan iskan saurayi da takeso, amma na hanata saboda yaron bashi da tarbiyya ko kodan, ashe suna tare nadauka sun rabu sai ran nan nagansu suna magana, toh bayan kwana biyu da asuba naga bata fito ba, babu inda ban duba ba amma ban ganta ba"

ta karasa tana hawaye

" innalillahi wa inna ilaihi raj'un yaushe duk hakan ta faru ba mu da labari?"

"A ina gidansu saurayin yake? "

Gabanta ne ya bada ras cikin duburbucewa tace " bansan gidansu ba kawai zuwa yake kuma na tambayi samarin unguwar nan sunce basu san daga inda yake ba".


Kuka sosai Mummyn zainab keyi , azuciyarta kuwa tunani take yaushe Faheemah ta canza haka,,? Mikewa tayi ba tare da ta sakewa cewa komai ba ta fita...


Mami kuwa share hawayen munafircinta tayi hadi da janyo meatpie dinta ta cigaba daci, idon ta ne ya sauka kan wata leda daga gefen kujera dauko shi tayi hadi da budewa, takalmi flat ne kala biyu red&black masu kyau, sai kuma doguwar rigar abaya mai kalan pink daya, hadi da dan mayafinsa wanda ta tabattar da mummyn zaynab din faheemah ta kawo wa. Jan takalmin ne dai ta gane na jameela ne ta size din, domin tafi faheemah girman kafa. Bata rai tayi bakinciki fal idanunta abayyane tace

"mayya kawai kowa ji yake da ita daga dangin uwar har na uban, sai kuma ta saki Dariya mugunta tace faheemah ta tafi, tafiya ta har abada, kuma sai na datsa tsanar ki azuciyar masu sonki ta fada kai kace da wata take magana. Ai kaya sun zama na jameela kuma".
(Allah ya tsaremu da son zuciya)

"Zaynab ki daina kuka, ki kicigaba dayi mata addu'a Allah ya dawo mana da hankalinta gida, inna dole inyi kuka ina tuhumar Kaina da batar Faheemah kamar da tsakacin rashin zumuncin ya janyo hakan. Kinyi gaskiya zainab, nidake kusa da su ma bana zuwa dubata, xumuncin yanzu sai a hankali, hakika muna wasa da zumuncin, bayan zumuncin abu ne mai matukar muhimmanci da Allah ke ba mu lada idan munyi."


" Hakane innah, amma inna duk ranar dana ga faheemah bazai yi mata kyau ba matukar na tabbatar da abun da maminsu ta fada"
(Mummy zaynab tana da zafi hadi da saurin fushi, amma tana da matukar kirki)

"A'a a'a zaynab ba'a haka, nifa ban yarda cewar yarinyar nan zata yi hakan ba, kibari mu bi komai a nutse kinji ko?"

"Toh innah" tace hadi da share hawayenta domin sosai take son Faheemah"......


Share fisabilillah

Comment



Thanks for reading my novel #rayuwar FAHEEMAH.


💔RAYUWAR FAHEEMAH 💔

_by NoorEemaan_📚✍️
kyautane (free novel)

"It is not the eyes that are blind, but the hearts." Qur'an 22:46


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


*Like i said earlier wanna shine novel dina na farko dana fara rubutawa, kafin na rubuta mijin Ammin ne sila, PAPI ne, Abraham, kyautar koda da Hoorain mai kusumbi rayuwar Faheemah shi na fara rubutawa, but funny a enough lokacin banda group na novel ko ɗaya, that was 2021, hakan yasa nake kara reposting din shi yanzu domin zan zo ku karanta saboda darasin cikin book din, dan Allah ki fara bi yanzu, kar sai nayi nisa sosai a ce daga farko*🥺😫🥰




19-20

(Not edited)


"Diyata faheemah kin duba result dinki kuwa?"



"A'a ummu"


" ok zan duba miki in sha Allahu , kin taho da exam card?"


"Eh" ta amsa cikin sanyinta...


★★★

Washegari bayan ta gama shirya shi kamar kullum, sai wani tunanin yazo mata, "Anya yana shan ruwa kuwa? Domin tunda nafara kula dashi ban bashi ruwa ba, haka ma banga Ummu ta bashi ba" fada abayyane..

Kitchen ta nufa ta dauko table water ta shiga bashi sosai kuwa ya sha ruwan, cikin tausayawa tace

"Allah sarki bawan Allah, kayi hakuri kaji? Amma meyasa baka nuna min alaman zaka sha ruwa ba?"

Tafada tana turo baki hadi da shafa suman kansa, da alama ta manta da baya magana, kafin zuwa azahar tabashi ruwa yakai roba shida babban gora.

Na karshen data bashi sai taga ruwan nabin hanjinsa da bakinsa sai kuma taga idanunsa na juyewa ba'a ganin bakin sai farin....

Sosai hankalinta ya tashi, meke damunka? Kadaina wanna abun kana bani tsoro tafada hawaye nazubo mata, ya fu'ad please kadaina kaji?

Ta cigaba ta jijjigasa, ganin ruwan bai daina fita a hancin da bakinsa bane yasa ta fita da gudu...



ummu na azaune aparlour sanye da medicated glass tana aiki a system kasancewar weekend ne.

Tana zuwa taja ahannu ummu, batare da tace komai ba zuwa dakin....

Ganin robobbin ruwa da yawa adakin, ga kuma halin data ga fu'ad din aciki yasa gabanta faduwa. Amma dan ta tabattar sai tace


"diyata faheemah kin bashi ruwa ne"?

A tsorace ta Ɗaga kai alamun

"eh"

tana mai toshe bakinta saboda kukan dake kokarin kubce mata.

Cikin gaggawa ummu ta lalubo wayar asibitin dasuke zuwa ta kirasu takuma ta gaya musu emergency ne..



Cikin 15minutes suka Kara so ,hadi da shigowa domin tafiya dashi cikin sauri da sanin makaman aikin ma'aikanta suka daukesa domin zuwa hospital...


Gaba daya Ma'aikantan gidan hankalinsu ya tashi musamman ma dasuka ga faheemah na kuka.


"dauko hijab dinki mu bisu"

duk da ummu bata nuna wani alama najin haushi ba, amma sosai taji tsoron ummun na shigarta, hijabi ta dauko tabi bayan ummu asanyaye.



Da isar su asibiti har an shigar da shi. Sai bayan 2hrs doctor usman ya fito yana share gumi, fuskarsa a daure yace wa ummu ta biyosa office.



Gaban faheemah ya bada ras, to me ummu zata masa? Kodai ya mutu ne?

"Innalilahi wa innah ilaihi raju'un! in sha Allah bazaka mutu yanzu ba, doctor kar ka ce wani abu ya sameshi, wayyo Allah ya fu'ad na"



ta fada batare da ta san maganar ta fito fili ba., sosai taba likitan dariya domin da yana cikin Good mood ba abinda zai hanashi dariya ko wa yace mata ya mutu ne oho?


"Please hajiya meet me at my office"

ya fada yana juyawa cikin tafiyar sauri daman maganar Faheemah ce ta tsayar dashi.


" Diyata Faheemah ki kwantar da hankalinki zauna ina zuwa"


ummu ta fada tana juyawa, domin itama fargaba ne fal ranta tana aro jarumta ne kawai.

"Hajiya kinsan lalurar fu'ad baya bukatan ana bashi abu mai ruwa sosai, idan ma za'a bashi once in a while ne, kuma bamai yawa ba"

yafada yana kokarin sauke temper dinsa domin sosai ranshi ya baci.



"Doctor usman akasi a kasamu matarsa ce ta bashi ruwan wallahi itama bata sani, ni kuma na manta ban sanar da ita ba"

cewar ummu asanyaye domin bata fatan wani abu ya samu danta mafi soyuwa a gareta.


" ni da abokan aikinka munyi iya kokarin mu kuma alhamdulillah cikin yardar Allah yadawo daidai amma zamu rike ku asibiti na sati daya domin sake tabattar da saukinsa"

"Okay doctor nagode, zamu iya ganinsa?"

" Eh kada ayi hayaniya please hajiya, jinjina kai ummu tayi kana ta fito"


Zaune ta tarar da ita tana kuka

"Diyata bazaki bar kukan nan haka ba?"

"Ummu kiyi hakuri Wallahi bansan cewa ba..ba'a bashi ru...wa... ba"
ta fada cikin muryanta dake cracking"

"nasani diyata laifi nane daban sanar dake ba, kibar kukan mijinki na nan da lafiyarsa kinji?"

Ajiyar xuciya tasauke da sautin sa ya fito, jikin ummu tafada tana sakin kananun kuka sosai taji tsoro, domin zuciya bata da kashi, bata so ummu tayi wani tunani daban. Kuma a yanda ta shaku dashi, duk da a kwance yake baya magana, amma sosai take jin dadi kasancewa dashi.


"Tashi mu shiga amma sai kinyi shiru domin doctor yace ba hayaniya" hadiye kukan tayi suka shiga


idanunsa abude suke, Kallonshi take tana jin wani abu mai girma na ratsa zuciyarta gami dashi.


Gaban gadon ta karasa ta riko hannayensa duka biyu, "dan Allah kayi hakuri, wallahi bansaniba kayafemin Kajiii danaga ina baka ruwan kana sha I thought sosai kakejin kishiruwa, shiyasa nayi ta baka, bazan sake ba ya Fu'ad" ta karasa cikin yanayi na kuka da shagwaba.



Murmushi ummu keyi dake nuna zallan farinciki ganin yanda faheemah ke nuna concern dinta akan danta, ganin faheemah ta manta da ita adakin ne yasa ta fice domin kiran fareesa ta kawo abubuwan bukata tunda kwana ya kamasu, kasancewar lokacin da suko taho tana school.


Bayan 40min sai ga fareesa da tare da masu aiki, ta kaya Niki -Niki, ahankalinta a tashe amma ganin jikin yayanta da kyau, yasa hankalinta kwanciya, masu aiki ma gaisuwa su ka wa ummu, ta amsa cikin kulawa, sanna suka tafi...



Bayan isha a kace mutum daya ne zai iya kwana da mara lafiya domin ka'idar asibitin ne, ummu cewa tayi su tafi gida ita zata kwana, ai matso kwalla faheemah

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment