Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyau anjima"

Tsoro ne yakamata ita kuwa me ta masa? Sanin cewar babu batada amsa yasa tayi shiru, shi kuwa dariya ce take cinsa amma ya gimtse ganin yadda tsoro ya bayyana a kyakyawar fuskarta. Anwar kuwa sai satar kallonsa yake ta mirror yana danne dariyar sa, aransa kuwa cewa yake dude mugu domin yaga yanda ta tsorata.

"So tell me, who design this for you"

yafada yana shafa kunshin in a circular motion.

"ummu ce ta kira mai kunshi, bansan taba".


"Zaki dinga yimin?
I like it!"

"Eh in sha Allah" ta amsa a sanyayye

"Good girl"

yafada wanda yayi daidai da isowar su gurin taron...




https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
..



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



Share
Vote
Comment


Thanks for reading
NoorEemaan🥀🌸



💔RAYUWAR FAHEEMAH 💔



_by NoorEemaan_ 📚✍️

kyautane( free novel)



Ya Allah! You know our problems, better than us, forgive us &, grant us what is best for all Muslim ☪ ummah. Juma't mubarak my fans.


39-40
(Not edited)






Tsayuwar motocin su yasa idanun jama'a ya dawo wurin su, babu ma kamar hindu da diyar ta, domin suna zaune babu wani k'wak'waran motsi baya da suka gaisa da ummu, shima cikin kunyar abunda sukayi mata, ita ummu kuma batasan suna yi ba domin sosai ta sake musu fuska.


Su fareesa ne suka fara fitowa, anwar ma ya fito, a hankali ya zura kafafunsa waje kana ya fito gaba dayansa, Dayan bangaren ya nufa ya bude mata motar dakansa, zuro kyakyawan kafafunta waje tayi, hannu ya mika mata, akunyace ta kama ya mikar da ita tsaye. Fareesa da meenal agaba sai kawayen fareesa biyu abaya sai ya zama na su fu'ad na tsakiya, yayinda su fareesa ke dan taka rawa, domin zuwa raka su fu'ad kujeran da'aka tanadar musu, hasken camera ne kawai ke ta haskaka su, yayinda wasu yara da'a shekaru bazasu wuje bakwai ba, su goma cikin shiga irin daya sai watso musu red flowers suke, dayawan daga cikin yammata nan tsuman tsaye suka yi domin dukkansu sun sanshi dayawa sun nuna suna sonshi amma, da lalura tasameshi wayam kake gani.



takawa suke ahankali yayinda music mai dadi da sanyi ketashi, ganin kyawun Faheemah ba karamin girgixa su tayi ba, domin sun zata Zasu ga wata yar kauye, domin aganinsu babu yar gari dazata yarda ta aureshi baya tafiya baya magana ba. Hajiya sa'a dake Zaune kusa da ummu a inda aka tanada wa iyaye, sai Murmushi take dokawa musamman ganin yanda fuskoki wasu da yawa ta bayyana zallan mamaki bare na hindu da yarta yaki boyuwa. Daman tasan hakan zai faru shiyasa ta Dage ayi party dinnan.


"Jama'a dan Allah zauna" muryan mc ta karade ilairin wurin wanna yasa su Hindu dawowa hayyacinsu. "Muna wa wandanan ma'arautan dasuka matukar dacewa da juna barka da zuwa! Dan Allah a tafa musu jama'a raf! raf!! raf!!! kake jin tafin mutane wanda idan ka Kalli wasu mutanen bai kai zuciya ba, domin matsananinci kishin Fu'ad dinne ke sukar su, ganin wanna kyakyawar matashiya a matsayin matarsa, sai gaba daya suka araina kyau da Kuma kwalliyar su, wanda sunyi ne domin burge shi.

Mc ya bukace FU'AD da FAHEEMAH su fito, ahankali ta mike yayinda fu'ad ya kamo hannunta suke shiga saukowa ahankali. Sosai suka dace juna, domin kyau ne ya hadu kyau. Cool music aka sa musu suka shiga taka Romantic dance domin Fu'ad ya zagaye hannunwansa akugunta yana dan jujjuya ta, yayinda ya kura Mata rikatatun idanunsa dake dauke da zallan sonta, Kana fuskarsa na bayyana zallan farinciki Wanda hakan ya ƙara bakanta zuciyar yanmmata domin basu taba ganin wanna

Murmushi afuskarsa ba. Faheemah kuwa batasan yana yi ba domin kunya take ji yanda ya riketa, ga ummu na kallonsu haka dai ta daure tana sakin murmushin duk da ta kasa hada ido dashi. Fu'ad ya zura hannun sa ta cikin babban rigarsa yan sababbin 1k ya shiga lika mata, sai ya matso daidai kunnenta ya ce



" ki bude pos dinki akwai kudi aciki ki likamin tunda shima sai na koya miki yar kauye "


yanda yayi maganar ya matukar burge mutane domin sai Kayi tunanin wasu kalaman soyaayaa yake gaya mata, yayi matukar bata dariya yanda yayi, bude pose din tayi ta shiga leka masa akunyace. Anwar yafara shigowa yana musu likin sababin Dari biyar , sai su hajiya sa'a, fareesa, yan'uwan ummu dana abbuh da sauran jama'a suka shigo suma suka fara liki. Masu bakin ciki ma sun boye bakincikin su, sai da Hindu ta fito domin ganin kusan fiye da rabin jama'a sun fita, liki ta shiga yi, wanda sai lokacin taga fuskar Faheemah sosai, gabanta ne yafadi, ina tasan fuskar wanna?

Ta fada aranta, Ganin cikin jama'a ne yasa ta koma ta zauna. Tana zurfafa tunanin...


Anwar ne ya karbi mic 🎤 domin baya jin zai iya shiru bai yabi Faheemah tare da nuna farincikinsa ga abokin sa nasamun mata kamar taba. Yafara ne da taya abokinsa murna, kana ya shiga yaba kokarin Faheemah data yi na kula da mijinta tsahon shekara da watanin, kafin Allah ya bashi Lafiya.




Yayi amfani da kalamai masu ratsa zuciya da kuma karye zuciya, sosai jikin yanmanta Yayi sanyi wasu ma har cewa suke dama sun amince kila dasu ne yanzu suka mallaki wanna kyakyawan kuma tsayayyan namiji.


Wasu sun hakura dashi, ganin yana da Faheemah mazai yi dasu? yayinda wasu suka kudurci mallakansa ciki harda salma dake aikin a bank dinsu. Sai rawar Kafan zuwa gaida ummu suke, ummu kuwa amsawa take babu yabo ba fallasa, domin tsaf ta karanci manufarsu...

Ummu kuwa sosai hakan Yayi mata, ko ba komai ya nuna wa duban jama'a Faheemah nada daraja gareshi. Domin tsoronta kada asamu matsala, duk da ta yarda cewa danta bazai bata kunya ba.










Hakama fareesa sosai taji dadi ganin yadda fuskar umaimah, aysha, da ma wasu mutanen ya nuna bakinciki.



Duk da ba'a gama liki ba, amma haka suka koma mazauninsu, haka aka cigaba da gabatar da biki cikin kwanciyar hankali, bayan kamar 10minutes Fu'ad ya riko hannu faheemah suka sake saukowa kasa, kana yafito da wani small box ring , fito da zoben mai farin stone yayi wanna sai kyalli yake yana daukar ido domin na zallan diamond ne, gwiwowinsa yasa akasa, kana ya rigo hannunta na dama, faheemah kuwa mamaki take mezaisa ya durkusa gabanta haka? haka su ummu dasauran jama'a, amma banda amwar daya san komai.

" will you forever spend the rest of your life with me?"

Sosai farinciki ya ratsa zuciyar ta, domin duk da bai taba nuna mata ko furta kalmar so agareta ba, hakan da Yayi ya nuna tana da daraja agareshi, kasancewar akwai manyan loudspeakers a kewaye dasu yasa duk jama'ar wurin suka ji abinda yace. Hannu daya tasa ta rufe bakinta saboda farinciki kana tace



"yes I will"


murmushi farinciiki yayi kana ya zura mata a kusa da karamin yatsn ta, sosai yayi kyau hannuta yayi mata das! Sowa aka sa kana aka shiga yi musu tafi.



Hindu da sai yanzu ta dawo daga duniyar tunani tayi wata zabura kana tace


" kutu......." ta lailayo ashar, kana cikin rudu da rikicewa tace

"wallahi ita ce! faheemah ce"

Kasancewar hankulan jama'a yana ga su faheemah yasa basu Jita ba.







Gumi ne ya fara keto mata, ta yaya hakan ta faru? Duk da sanjawa da kyau da ta kara yi amma tabass taganeta, ido ta kuro mata, matsanincin bakin ci da haushi na cinta,

"ba shakka Faheemah ce, ya akayi haka, ta auri fu'ad ko dai mafarki nake ne? "

Sanin cewar bata da amsa yasa ta lalubo wayar ta hannun na rawa, sai dai tana dora wayar akunnenta aka sanar da ita wayar wanda zata kira a kashe...

Faheemah kuwa Itama zoben zallar azurfa dayayi wa hannunta yayi mata yawa ta cire, kana ta war ware zaren daya taimaka wa zoben yadan samu mazauni ahannunta.

Kurawa zoben ido tayi idanunta suka ciko da kwalla, cikin muryan kuka tace


" ina matukar son zoben nan, amma ba nawa bane, dakai ya dace domin ajiya aka bani in ajiye maka" kallon karin bayani ya mata, ummina ce ta bani kafin ta rasu.."

Tafada cikin cracking
voice kana ta cigaba,

" tacemin, naso kwarai inga gwarzon mijin dazai yi nasaran auren faheeta, amma bazan ga ranar ba, ina jin haka ajikina Faheeta,
wanna zoben mahaifiyata ce ta bani kafin mutuwar ta, yayi miki yawa na sani, amma Inaso ki adana ta idan kinyi aure ki bawa mijin ki, kice masa kyautar ummin ki ne zuwa garesa, ki kuma ce ina gaida mijin yata"

ta fada daidai sanda hawaye suka zubo mata, zura masa zoben tayi a yatsan tsakiya, ikon Allah kuwa daidai hannunsa.

Yakuma sake kawata lafiyayyan farin hannunsa.

Cikin murya mai bayyana tsananin kewa tace


"ummina, Ayau na isar da sakon ki zuwa gareshi, ina fatan kina cikin kwanciya hankali, aminci, farinciki, salama, a kabarinki, ina son ki umminah"

takarasa cikin sakin kuka mai ratsa zuciya.


Ciki sauri ya mike ya rungumota jikinsa, domin sosai jikinsa, yayi sanyi, bama shi kadai ba, hatta ummu, hajiya sa'a, fareesa, anwar ma, sai da suka zub da hawaye, hakama wasu daga cikin jama' ar wurin sunyi kuka wasu kuwa jikinsu Yayi sanyi.




*Bayan 10minutes*


Ganin jikin jama'a da yawa Yayi sanyi, yasa mc fara nishadantar dasu tareda labarai masu ban dariya, cikin lokaci kankani lokaci suka ware, aka cigaba ta gabatar da bikin.


royal blue da golden cake dinsu mai step uku, mc ya bukaci su fito a yanka, shi ya fara tashi daga wurin zaman su kana ya mikar da ita tsaye, fuskarsa a tsake yace



"I know you're tired, amma ki daure mu yanka cake din sai mu tafi ki huta okay?"

Yafadi hakan ne domin ganin hill shoe dinta na damunta. toh ta amsa domin ta kagu ta cire takalmin yafara damunta domin bata saba saka irinsu ba.


Hannunta ta fara dorawa kana akan wukar yanka cake din, kana shima ya Dora nasa hannu akai. "1.. 2....3... go"

mc yafada sukayi kasa da wukar, kana ya yanko yasamata a baki, itama yankowa tayi tasa masa ai sowa wurin ya dauka domin Abun ya kayarta dasu...




Abincin Kala Kala aka shiga serving din mutane, danginsu, fried rice, jollof rice, tuwon semovota, da miya Kala Kala, alkubus, fankaso da miyar taushe , doughnut, egg roll, meat pie, semosa, ga drinks kala Kala, kaza kuwa saidai kaci ka ture saboda yawansa. Hakama anraba manyan kyaututuka( kala-kala.



Kowa ka gani fuskarsa dauke da fara'a amma banda masu jin haushin Faheemah. Ganin cewar saura minti goma atashi, yasa shi mikewa tareda mika godiyarsa da iyayensa da kuma abokan arziki da suka zo taya shi murna, kana ya mike ya kamo hannun Faheemah domin su tafi. Ganin yanda take tafiya, yasa shi daga ta cak, kokarin zillewa take, amma rikon dayayi mata bana wasa bane! Sowa aka shiga yi hadi da tafi domin abun ya burgesu, rasta Mutane ya fara ya yi yana wucewa, hakan ya kara bakanta wa wasu rai, domin yammata nan duk yanda sukayi koda gaisuwa ce ta hada su bai bari ba, sai rawar kafa zuwa daukan hotuna suke, domin ya kula su, amma bai basu fuska ba! Faheemah kuwa kunyar duniya taji ya lullube ta. Anwar daya biyoshi yayi Saurin bude masa motar yana dariyar tsokana, gogan ko kula shi bai yi ba. Shumfideta yayi abayan kujera kana ya shiga ya Dora kanta acinyarsa. Still idanunta a rufe tana sauraran bugun zuciyarta! daukar data sake ji ne, yasa ta fahimci sun iso, kara daukar ta yayi ya nufi dakinsu da ita. Kwantar da ita yakara yi,

"bude idon ki"

kara runtse idon tayi, murmushi gefen baki Yayi kana yace


"gulma"


cikin takun kasaitarsa ya fice, domin zuwa yayi sallama da abokan aikinsa da sauran jama'a........


Yana fita ta sauke ajiyar zuciya hadi da dariya wai

"gulma ooh ya fu'ad bai da dama"



Zuwa karfe 80:00pm aka tashi daga taron, kara shirya faheemah akayi cikn hadadiyar shadda lace peach color dinki riga da skirt wanda kudinsa zai kai 80k. An mata light make up Kana aka saka mata alkyabba mara dauyi black color mai yawan stones. Riko hannunta kanwar ummu tayi domin kaita wajen ummu.....



Falon aciki yake, domin bayan yan'uwa harda wandanda basu tafi ba, sai sun ga karshen abun, ciki kuwa harda su Hindu.
Sihirtaccen kamshi daya ziyarci hancin kowannensu dake zaune cikin parlour ya sanar musu da isowarta. Kanwar ummu ce ta riketa ta kaita har gaban ummun. Kukan da take rikewa ya kubce mata, ita kam yau abubuwa ya tarar mata, musamman tunanin gidansu, domin duk da babu mai nuna mata kauna acikin su amma tana matukar kewarsu hadi da tunanin ko wani yanayi suke ciki, "ummu dan Allah ke barni anan zan zauna dake" ta karasa cikin kuka mai ban tausayi, domin ita tsakanin ta da Allah tana son zama kusa da ummuh, Duk da cewar cikin gidan zata zauna amma tafison zama anan din, Murmushi Ummu tayi yayinda idanunta ya dan ciko da kwalla tace







"diyata faheemah ummu
ta kirata cikin kaunarta"



" Na'am ummunah" ta amsa cikin muryan Kuka



"inaso ki san cewar RAYUWAR aure daban take, inaso ki san cewar sabuwar makaranta zaki shiga, domin aure ba abun wasa bane! Ki kasance mai boye sirrin mijinki, kada ki bari wata ta baki wani gurbatacciyar shawara akan RAYUWAR aurenki ko mijinki, ki kasance kullum cikin neman zabin Allah. Na yarda dake dari bisa dari, Saboda haka nake son ki dore akan yadda nasanki, feel free ki gayamin Duk wata matsalarku da ya dace in sani, domin nidin uwa ce agareki, and I guess ya bata boyewa uwarta sirrinkan daya dace ta sani?"


Cikin zubda kwalla Faheemah ta daga kai ta cikin mayafin alamun "eh" saboda kukan daya ci karfinta.

"Toh masha Allah, Allah ya miki albarka ya baku zuri'a dayyiba".

Da ameen wasu daga yan dakin dake zaune suka amsa, kana yan'uwan ummu dana abbuh suka shiga yi mata nasu nasihar, domin sosai suke sonta....




Kuka take sosai wai yau za'a kaita dakin miji, amma babu wani dangi nata, wai yau zaka kaita dakin miji amma babu wani nata dazai mata nasihar zaman aure, nasihar daya dace iyayenta su yi mata, shine dagin sukurai ke mata, taya zata manta karamcin wandanan bayin Allah? umminta ne ya fado mata rai, hawayen kewa hadi da kaunar Umminta ya silalo mata, tasan cewa da umminta na raye duk haka bazata faru ba, sai dai bata mantawa kamar yadda umminta ta taba cewa

_*Allah baya barin wani dan wani ya ji dadi*_

Hanunta kanwar ummu nan dai ta sake kamawa domin kaita part dinsu, ai kankame ummu tayi ita wallahi da ita zata zauna. Sosai ta bawa wasu dariya ganin kuka take bilhakki, kanwar ummuce ta ce

"yaya da alama yar nan taki akwai shagwaba"


murmushi kawai ummu ta yi domin ita ma tana jin kewarta, duk da cewar cikin gida daya ne, amma bakamar yadda suke tare cikin flat daya ba, mikar da ita kanwar ummu ta yi, kana sauran suka mara musu baya..

"Masha Allah! Masha Allah!! Masha Allah!!!"

Shine abinda mutane sukai ta fadi, yayinda yan hassada kamar su mutu. Duk inda kake tunanin flat dinnan ya wuje nan, just kuyi imagin hadadden gida irin na masu hannu da shuni, Duk girma part din Ummu wanna ya ninka sa, sai biyu, ita kanta faheemah dake lullube cikin alkyabba tasan gidan ba karamin haduwa yayi, lallausan center part dake malale akasan tiles suka shiga takawa domin zuwa dakin faheemah.


Wow! Dakinta yayi matukar haduwa, komai tsadade ne, haka kuma mai Kyau ne, domin komai na Dakinta Sky blue ne da fari, hakama toilet. Zaunar da ita kanwar Ummu ta yi atsakiyar hadadiyar royal bed dinta. Yayinda yawanci aka fita domin ganin ko wani kusurwa na part din . bayan dakinta da parlour dakuna 5 akasan, cikinsu akwai kitchen da duk yawanci kayan sky blue da fari ne, musamman kitchen cabinet da, tukwane, sai babban store da kayan abinci ne iri daban -daban wanda baza su lissafu ba, da komai dai na amfanin gida akwai wanda Zasu dade basu siya ba. Sanan akwai toilet din baki, haka kuma akwai sitting room dake farko shigowarka part din, akwai dakin baki, dakuma toilet din baki, dining table yana daga gefen matatakalar bene, sai extra room da ba komai adakin sai tiles din dakin dake ta sheki.

Sama suka hau, Babban falo ne dake dauke da kayan alatu, sai uwar daki daya kasance bedroom ne, sai toilet dinsa da akwai komai na bukata hakuma na zamani.


A bedroom dinsa akwai babban king size bed da wadarobe, sai wani sofa dake gefen, akwai hadadiyar Chinese center kafet dake malale daga a tsakiyar dakin....

Sai wasu hadadun tumtum dake gefen da gefen gado, komai na saman dark blue ne sai dan touches din fari hakama kuma akwai dan maidaidaicin kitchen asaman dake gefen dakunnansa,, sai dakin gymming da akwai komai na excrise din maza har da na mata. Sai wani daki dake tamkar office domin Duk wasu kayan amfanin office akwai aciki.

Komai yayi domin ba karamin kudi aka narka wurin kawata part din ba, duk da babu wasu tarkace da yawa apart din amma komai tsadade wanda hakan ya sake kawata part din.

sosai mutane suka yi santin gidan, umaimah da tun dazu bakinciki ke cinta, kasa daurewa tayi ta saurin fita tana fashewa da kuka, yayinda hindu tayi saurin rufa mata baya ganin yanda ta fice cikin tashin hankali...


cikin wayo, kanwar ummu dake zaune tace

"my dear bari naje na dauko kayana anan zan kwana ko"?

Cikin sauri faheemah ta daga kai kana tace


"small mom muje tare"

"a'a my dear yanzu zan dawo okay?"



"Toh small mom karki dade"

Murmushi ta yi kamar yadda faheemah ta lura itama mai fara'a ce.


"maza fareesa kaiwa faheemah wanna na manta, Banason komawa part din, kema yanzu zaki dawo bance ki zauna ba"


"toh small mom" ( kanwar Ummu) kamar yanda suke kiranta.

jin motsin mutum yasa ta daga kai, ganin fareesa ce yasa ta saki ajiyar xuciya,

"amarya! amarya!! kin sha kamshi" cewar fareesa cikin tsokana. Rufe fuskarta Faheemah ta yi cikin jin kunya.

"Ke kadai suka bari"?

ta tambaya kamar bata san komai ba,

"eh ta amsa kana tace small mom zata dawo tare zasu kwana"

gimtse dariyanta fareesa ta yi ganin cewar Faheemah bata gane wayo small mom tayi mata ba.

zama tayi suka shiga hira jefi -jefi, da kamar 5mintues sai ga kiran small mom "wai uban me kike ne fareesa?"

"gani nan zuwa small mom" kawai tace ta kashe wayar.


"am matar bro bari na dauko mana abinci muci yunwa nake ji, kema nasan kina ji ko?"

" Eh muje tare mu dauko a'a yanzunan zan dawo" tafada tana ficewa cikin sauri...


Asanyaye ta zauna, shiru itama kusan 10minutes bata dawo ba.

cikin shagwaba tace



"small mom bata dawo ba, aunty fareesa ma bata dawo bah"

ledan da fareesa ta ajiye ta dauka, turaruruka masu yawa dangin su humra, kwallaca, hawi, kajiji, da sauran su, sai wata farar takarda dake ciki Wanda ke dauke da bayanin yanda zata yi amfani su.


A wardrobe dinta ta sanya su, kana ta daga labule tana kallon yadda haraban gidan ke da hasken lantarki ya haska gaba dayan gidan tamkar rana.






Kusan minti goma ta dauka a tsaye ganin ta gaji yasa ta kwanta rabinta a gado, rabinta akasa. Hawaye ne suka cika idanunta domin gidan ya mata girma ko ina shiru, shiyasa ta so A barta a part din ummu, ko banza zata ji motsin mutum...

Kuka ta fara kasa kasa babu jimawa bacci ya dauke ta...


Zaune yake gaban ummu sanyi da dakakiyyar shadda fara kal. Ajiyar zuciya ya sauke domin nasihar ummun tasa ta shigesa ba kadan ba! "Cikin cool voice yace in sha Allahu ummu zanyi duk abinda kikace , haka kuma zan riketa amana"

"madallah da yaro na gari"

" Allah ya maka albarka"


Da "ameen"

ya amsa kana ya dora kansa acinyarta, shafa kansa ta shiga yi cikin kaunar yaronta tace "Son bamu fa yafe lefen diyata bafa, dagowa yayi yana murmushi kana aransa yana mamakin kaunar da ummun tasa ke yiwa Faheemah.


Cikin son tsokanarta yace "ummu karki damu zanyi mata akwati daya amatsayina na mai adalci"


"ka fita idona in rufe son , diyata mai tsada ce tafi karfin akwai daya"


Ganin yadda yake ta bata rai ya sashi dariya, kana ya kamo ahannunta ya sumbata yace

"ki samun albarka zan tafi"


"Allahu ya albarkaci rayuwarka ya haskaka da haskensa Allah ya kade duk wata fitina arayuwar ku da ma sauran muslims ummah"

"ameen ya Allah ummunah"

ya masa cikin farinciki basket ta bashi na abincinsu duk da ya siyo musu kaza amma gwanda su dan ci abunci,domin dukkanunsu ta lura tun safe basu ci wani abun karki ba.


Ta sake jadadda maza maganar lefe, dariyar kawai yayi tare da cewa, toh ummu angama domin koda ummu bata gaya masa

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment