Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fareesa ta biyosa yabata tsarabarsu, sallama yayiwa ummu ya fita, fareesa ta take mai baya, wata yar madaidaiciyar jaka ya miko mata, kana yace

"parrot ina wayarki?"

Ita ta tsani wanna sunan wallahi,

"bada ke nake ba?"

" yana dakina"

ta amsa tana bata rai, sarai yasan dalilin bacin ran nata.

"ki kira ni"

"toh ni banda number ka"

tafada cikin kumburo baki, wayarsa ya mika mata, gane abinda yake nufi yasa ta dauki wayar hadi da sa masa lambar wayar

"kowa da sunansa a jikin tasa tsaraban"

"Toh"

ta amsa hadi da godiya ta shiga takawa domin barin haraban gidan, "parrot ba sallama?" Juyowa tayi fuska a turbune, tace "sai da anjima"


Ganin shigewarta yasa ya saki dariyar dayake ta rikewa, domin sosai yake enjoying ganin yana sata bata rai......


Ku dinga min share saboda Allah.


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



πŸ’”RAYUWAR FAHEEMAH πŸ’”

Written by Noor
Eemaan


Wattpad @NoorEemaan

kyautane (free novel)


Alhamdulillah for everything in my life.πŸ’˜
The good and bad Somewhere blessings and somewhere lessons.

https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851




23-24

(Not edited)


Tana shiga ta ajiye jakar gaban ummu, bude kayan tayi wanda kashi hudu ne kawo da sunansa, ummu daya, fu'ad daya, fareesa daya, sai faheemah daya, duk da bada ta yayi tsaraban ba, amma ya daukan mata abaya masu kyau da tsada guda biyu daga cikin na fareesa.


Albarka ummu ta shiga sa masa, kana tace Faheemah ta dauki nata dana fu'ad ta kai musu gida. Dauka tayi tana kallo tsadadun kananun kaya daya kawo wa Fu'ad din, duk da bazai sa suba ba ayanzu saboda lalurarsa, amma still ya siyo masa lallai wanna ya cika aminin kwarai ta fada aranta. Tana shiga dakin ta ga idanunsa biyu, Murmushi tayi ta karasa gabansa, kayan ta shiga nuna masa, kana tace

" ya fu'ad abokinka ne ya kawo maka, nasan zasu yima kyau sosai"
tafada ta kara masa rigar afresh skin dinsa, ido kawai ya zuba mata baya ko kiftawa, cikin shagwaba tace "ni wallahi kadaina yawan kallona haka, sai kasa nayi ta jin kunya kaji kadaina"



am still idanunsa cikin nata. ita kanta tasan baza ta samu amsa ba, amma haka nan take jin dadi yimasa magana, domin haka nasata farinciki, tana kuma fatan one day zata ji muryansa. Sumbatar goshinsa tayi kana ta shiga toilet...


Bangaren mummyn zaynab kuwa ta kudurtawa aranta cewa matukar faheemah ta bayyana hannunta zata dawo da zama. koda abbuh na so ko baya so...


Hakan yasa bayan ta koma kaduna ta gaya wa mijinta batar faheemah, ta kuma rokeshi ya bada cigiyarta agidan radio, kasancewar aikinsa ne. Babu musu ya amince domin shima yaji ba dadi lokacin ta matarsa ta sanar dashi....



"Sani! Sani!! Sani!!! Sau nawa na kira ka? Tambayarka nake"

mamaki ne ya sake kama sani domin yazata zuwa yanzu zata sauko, amma sai yaga abun kullum gaba yake....

" Tunda bazaka bani amsa ba, ta bari kaji na fito maka a mutum, sani yanxu bana sonka , na raina ajinka me gareka dazaka iya wadata ni dashi, banda kalaman so! so!! so!!! ko ana cin soyaaya ne? Ni kadaina takurawa min hakan nan ba dole a soyaaya"

ta kafada cikin daga murya!

Ransa ne yayi mummunan baci, duk da tarin hakurinsa amma bayason wulakanci...


"Jameela naji nagode da wanna sakayyar, amma kisani radadin dakika sawa zuciya ta ban yafe miki ba, domin kin cutar dani, idan da bakya sona akan me zaki sa na bata lokaci na akanki? Idan yaudara abu ne mai kyau ki cigaba zaki gani"

yana gaman fadin haka ya bar wajen Saboda hawaye na dab ta zubo masa kasancewarsa mai rauni, ya zama dole in bi umarnin iyaye na na auri zabinsa, ko zasu sauko daga fushin da suke dani, sani ya fada aransa yayinda wasu hawaye masu zafi suka zubo

"so babban cuta" yafada a bayyane yayinda domin wani kunci da zafi yake ji a ransa, gudun lifan dinshi ya karo domin zuwa sanarwa da iyayensa ya amince da auri cousin dinsa, ko zai samu sausauci a ransa..

"Mtsww"

jameela taja tsaki tana hararar bayansa, kana ta shiga gidan tana jinta sakayau ganin ta rabu da anaci acewarta.

"Yar albarka wai bazaki yiwa dan bazan yaron nan wulakanci da ko a hanya ya ganki zai canza wata ba, ai da so nake nagama wanna yankan nafito in mai wanki babban bargo, haba ayi mutum mai nacin bala'i"

cewar mami dake zaune tana yanka salak.

"Mami ai na sallameshi"

"yawwa ko kefa"


"mami ni wallahi yunwa nake ji bakya gama abincin rana da wuri, tafada cikin zallan rashin iya magana wanna hakan zai tabattar maka da ba'a kwabarta tun yarinta.

" Ai nagama girkin, saura wanna tumatar din da albasa ko zaki yanka min? Sai na wanke mana salak din"



Tab ni gaskiya bazan iya yankan albasa ba hannuna ya dinga wari"

ta fada tana yamutsa fuska kai kace bata cin albasan.

"Toh bari na yanka"

cewar mami bata ko damu da yanda tayi maganar ba".
Bayan mami ta gama tazuba masu abunci...



"Mami! wanna ai ya kusan zama tuwo, ba haka faheemah ke dafa mana ba, ni wallahi da kin barta ko ba komai zamu ci mai dadi" cewar jameela dake cakuda cous-cous da miyar stewa daya ji kifi



"toh ni yar nan wanna abun daman ban iya dafa taba, kuma bai dameni ba, dan dai kawai kince kina so ne"



Amma akasan ranta mami kuwa tanajin kamar dabata kori faheemah ba, dan ko bazan duka aikin nan datake sha yanzu da ita keyi, tanajin wani abu mai kama da kewar tafiyar faheemah, amma sosai take kin bawa zuciyarta daman amincewa da haka, taya ya yarinyar data tsana zata ji kewar ta? Ita kanta tasan bamai yuwa bane, kawai tana jin hakan ne Saboda aikin dake mata yawa wani bangaren na zuciyarta ya bata amsa.


*FAHEEMAH*
Zaune take adakinsu yayinda kyakyawan kafarsa ke kan cinyoyinta tana mai tausa, kamar kullum yau ma kuri yayi mata da ido saidai ba bakin magana. Dagowa tayi ta kallesa sai tayi idanunta suka fada nasa, cikin sakalci, yarinta, da shagwaba tace "Allah ya fu'ad kanasani ina jin kunya" ta shiga kare fuskarta Ita Allah dole kunya.

Tana bude idanunta taga idanunsa arufe, " lah har Kayi bacci?"

"Toh bari naje wurin su ummu indawo kaji?"

Tafada tana sauke kafarsa akan gadon, sai kuma ta dafe kanta tace " ooh Faheemah sai wani magana kika masa kamar zai baki amsa, sai kuma ta turo baki tace nima ba laifina bane kawai ina matukar son yi masa magana ne" tafada a hankali tana murmushi hadi da pecking goshinsa tabar dakin"....


Tana fita ya ware idanun sa ya hanyar da kallo, kana ya sake lumshe su...


"Ke ni ki daga ni, lazy girl kawai"

"Allah ummu jikina ciwo yake, aikin me kika yi? Dakika samu sauki yazo miki anwar ya dawo ai dole kice haka, lokacin da baya nan ai dole kije company, sanna kije
makaranta".




Dariya tayi kana ta tashi daga jikin ummu tace "ummu ai ba karamin taimaka mana yayi ba daya samo mutanan masu sanin ya kamata ya dauke su aiki gashi komai natafiya daidai"


" kedai bari fareesa har fa sauran states din da company dinmu yake yaje kuma alhamdulillah komai na tafiya yanda ya kamata acan, anwar badai kirki ba, shiyasa nake roka musu mata nagari shida yayanki gashi alhamdulillah shi ya samu saura shi Allah ya bashi ta gari domin da taimakonsa company ya zama standard"
cewar ummu.

"hakane ummu" fareesa ta fada cikin gamsuwa.



β˜…β˜…β˜…

"Assalama alaikum"


"wa'alaikumu salam,

suka amsa mata.

Ga matar brotherna oyoyo an gama sinke furen ne?"

Kasa Faheemah tayi da kanta domin maganar yabata kunya matuka, anty fareesa na bani kunya wallahi ta fada aranta.

"Fareesa meyasa bakida kunya ne? zo nan diyata rabu da ita"


Ahankali ta shige jikin ummu tana boye fuskarta, tsokanar ta fareesa ta cigaba dayi, da ummu ta gaji ta jefa mata pillow dake kan hadadiyyar kujerar falon. Dagudu tayi dakinta tana dariya, sai asanan faheemah ta dan sake suka shiga hira da ummunta

Fareesa na shiga daki taji ringing din wayarta, dagawa tayi tare da sallama, amsawa yayi kana yace

"parrot kin bar waya kin tafi surutu ko?"

Bata rai tayi domin ita har ga Allah batason wanna sunan, ni hira muke ba surutu nayi ba, ohh kina nufin nayi karya?"


" A'a nibance ba"

" Haka kike nufi mana ki shirya zuwa company yanzu akwai aiki dazaki tayani"


" wayyo ya anwar kamin rai banda lafiya"


" Meke damunki?"

"Ciwon kai"

"ciwon kai zai hana ki aiki ne? Common kizo ina jiranki"

"da gaske fa nake, ka kira ummu ka tambayeta"

" yanzu kuwa zan kirata idan ta tace ba haka ba kin kara wa kanki laifi"

ya kashe wayar yana dariya daman yasan bata son aiki musamman ma na office, kawai ya kira ne dan ta tsokaneta domin hakan na sashi nishadi"

Ajiyar zuciya ta sauke kana ta sauko kasa da gudu,

"ummu dan Allah ki rufamin asiri idan ya anwar ya kiraki kice masa kaina na ciwo"

" Kina nufin inyi karya kenan ko uwata?"

Cewar ummu cikin hararan wasa

" a'a wai nazo company ni kuma na gaji"

"aikin me kikayi dazaki gaji?

"Please ummu kataimaka, matar brother na kisa baki"

murmushi kawai tayi domin fareesa badai sa mutum dariya ba, gaba daya ta birkice

"kinji ummu dan Allah?"

" Toh naji"

" Yawwa sweet ummunah nagode"

murmushi kawai ummu tayi, Haka suka cigaba da hirarsu gwanin sha'awa....



*BAYAN SHEKARA DAYA*


har ila yau dai jikin fu'ad na nan yanda yake, haka babu abunda ya canza daga kula dashi da take, sai ma abun da ya karu, kuma sosai faheemah ta sake shakuwa dashi. kuma sonsa ya mamaye dukkan jini da tsokanta, saidai wani lokacin takan yi fargaba, shin zai karbe ta amtasayin mata? wanna tunanin kan sata shiga damuwa domin bata san a wani amatsayi zai karbeta ba. Ga kuma tunanin abbuh'nta dake nan daram aranta.





"yanzu jameela bazaki tayaki ni aikin nan ba,? kuma kayanki sunfi yawa aciki fa"
cewar mami kamar ta saki kuka.

"nidai wallahi bazan yi ba, duk laifi kine mami, duk masu mana wanki bakya son biyan su kudinsu, abbuh na baki kudi nima idan salman ya bani ina baki amma bakya son biyansu shiyasa suke ta guduwa ai"

Ta fada cikin tsantsar rashin tarbiyya.


"Ke"! Jameela baki da hankali ne?"

Cewar abbuh dake shigowa gidan.

" Mahaifiyarki kike gaya wa haka?"

" Toh ai abbuh gaskiya nafa...."

" Yimin shiru mara kunya. Zaki sa hannu ku yi wankin, ko kuwa?"

Baki ta turo tana magana kasa -kasa haka tasa ahannu tana shafa kayan don baza'a ce wankewa take ba.

A ran mami kuwa ta dan ji ba dadi da abbuh yayiwa jameela fada, domin a duniya idan akwai abinda bata kauna toh bacin ranta ne.



Amma abun na jameela ya fara damunta, domin kwana ki da hajja hindu tazo ba karamin kunya ta sha ba. Daga cewa ta duba mata ruwan shinkafar data dora ko ya tsotse...




Zuwa yanzu tafara raina kanta, domin ayyuka sun mata yawa har bata son gari ya waye, gashi masu tayata aiki bata son basu hakkinsu, saboda tsananin son kudi irin nata, sai abunci datake dan zuba musu, da sunyi na wata daya basu ga canji ba, sai su daina zuwa, daga barin Faheemah gidan zuwa yanzu ta canza masu aiki sun kai goma.


"Ba'a gama abinci ba?" Cewar abbuh,

"Alhaji wallahi ko dorawa banyi ba"

Ranshi a bace ya bar gidan, domin shi ba mutum bane mai yawan hayaniya.

Ganin Abbuh yafita yasa jameela cire a hannunta a wanki, ta shige dakinta.

fuskar mami kamar ta fasa kuka, tana ji da yanzu zata ga faheemah babu abinda zai sa bazata dawo da ita gidan nan,
Domin aikin nafara rinjayarta.

Bangaren hindu da yarta umaimah basu kara taka kafar su gidan ummu ba, saboda kunya, hakan yasa basu san da zancen auran fu'ad ba. duk da suna ta son zuwa ko don alkhairin da suke samu, domin ummu badai kyauta mai tsoka ba......





Thanks for reading my novel #Rayuwar Faheemah


Pls vote and follow on wattpad @NoorEemaan


πŸ’”RAYUWAR FAHEEMAH πŸ’”

_by Noor Eemaan_ πŸ“šβœοΈ

kyauta ne (free novel)


Be a girl with mind, A woman with attitude, a lady with class but most importantly, be a great muslimah with a strong faith.


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


25-26
(Not edited)


Kwance take kusa dashi, ta kurawa masa kyakyawan idanunta yayinda ta hada ahannuwansu cikin na juna, wani tunani ne ya zo zuciyarta wanda ya sata murmursawa har 1side dimple dinta ya bayyana. ahankali tace " meyasa banyi tunanin hakan ba tuntuni" mikewa tayi tare da sumbatar hannun nasa kana ta fice.


Ummu Kadai ta tarar a zaune sanye da medicated glass tana duba littafin hisnul muslimi sallama tayi wanda yasa ummu dagowa hadi da amsa sallaman.


"Ummuna"


"na'am diyata"

sai kuma tayi shiru tana murza hannunta, murmushi ummu tayi kana tace
"menene? Kina bukatar wani abu ne?"


Kasa tayi da kanta cikin sanyi da kuma zazzakar muryan tace, "wani tunanin nayi akan ciwon ya fu'ad sai kuma tayi shiru, cigaba inajinki cewar ummu, Inaso nayi masa na musulunci da yardar Allah za'a dace"


Kura mata ido ummu tayi tana mamakin kaifin tunaninta, tunda fu'ad ya fara rashin lafiyar nan babu wanda yayi tunanin yimasa maganin musulunci, domin atunaninsu tunda ba sihiri bane ko kuma shafar aljanu ba'a bukatar maganin musulunci. Jin shiru yasa ta dagowa, daram taji kirjinta ya buga kodai ummu bata ji dadin shawaranta ba? Saboda ganin yadda ta kura mata ido...

Cikin rawar murya tace "ummu kiyi hakuri idan na bata miki rai"

jin muryan Faheemah yasa ummu dawowa daga tunanin data lula, kwallar daya cika mata ido ta mayar kana tace, "hakika diyata faheemah ke haske ce ga wanna ahalin nawa, bakya bukatar amincewata domin mijinki ne kina da hakki, dama akanshi"


Sanyayar ajiyar zuciya ta sauke jin ba abinda take tunani bane,

"ummu ina bukatar ruwan zam-zam amma sai nan da kwana hudu nakeson fara wa" tafadi hakan ne saboda period da takeyi.




"Ok bayanshi akwai wani Abu da kike bukata?"

"A'a" ta amsa

cikin zolaya ummu tace "toh amaryan fu'ad angama ".


ai da gudu ta bar falon, murmushi ummu tayi tana jin kaunar faheemah aranta...


Tana shiga dakin ta sauke ajiyar zuciya hadi da dariya domin maganar ummu yasata kunya, kallonshi tayi taga idanunsa arufe, anutse ta taka zuwa gaban gadon tasa ahannu ta shafi kwantaccen sumansa bakin kirin sai sheki yake saboda gyara dayake Samu

" my fufu Allah ya tashi kafadunka in sha Allahu zaka tashi cikin yardar Allah da kudurarsa*

ta karasa tana dan kwantar da kanta kan faffadan kirjinsa ta shiga wasa da kwantaccen gashin dake kwance kan kirjinsa. Da haka wani bacci ya dauketa, domin jiya bata samu bacci sosai ba saboda menstrual pain data yi fama da shi".



******** ********




"hello abubakar kana jina? "


" eh inaji kawu service ne bakyau wallahi"


"Toh toh madallah, ya gida ya iyali?


"Lafiya lou suke kawu"


"Abubakar yakamata yaran nan suzo a sada zumunci an kwana biyu basu zo ba mana ba"


"In sha Allahu zata zo kuwa" cewar Abbuh.

Maganar tadan ba'a kawu anas mamaki amma bai nuna ba,


"toh ya faheemah in ce dai ta gama karatun?"


Shiru babu amsa, "hello abubakar baka jina?"


"eh kawu bana ji zan sake kiran ka"
Cewar abbuh, yana kashe wayar"



A bangaren kawu anas kuwa, yayi Mamakin jin abinda abbuh yace ransa ya maimaita "zata zo kawu" ba ma zasu zo ba? Shi kam yana lura kamar abbuh baya son ana masa maganar faheemah, amma ada idan suna waya zance daya biyu sai ya sako faheemah'n amma yanzu totally ya canza wani zubin ma idan ya tambayi faheemah shiru yake.

Ajiyar zuciya kawu ya sauke kana a fili yace " dole abubukar yazo mu tattauna wanna maganar tafi karfin waya idan ma wani laifi ta yi masa sai ayiwa tufkar hanci ya fada yana shige gidansa...




******** ********



"Baby nawane kudin da kika ce kina bukata?"

Cewar salman saurayin jameela.


"Dudu biyu ma sun isa har agama hidimar bikin"


Tafada tana matse muryanan.


Back seat din motar yamika hannu hadi da dauko wata yar jaka, zugewa yayi ya dauko bandir daya ya miko mata,

" thank you honey" tace

killer smile yayi kana ya kamo hannunta ya shiga murzawa cikin muryan yaudara yace



" yakamata kisa time mu fita"



Murmushi ta yi kana tace "toh zan saka"

"ya kamata dai saboda bazai yu ina faranta miki kullum, ke kuma kina yimun yawo da hankali ba" cewar salman


murmushi kawai tayi, domin ta lura salman irin samarin nan ne masu soyaayar shan minti, daga ranar dasuka hadu taga hakan atare dashi amma ta kasa taka mishi burki saboda son zuciya da kwadayi abun duniya ( Allah yasa mufi karfin zukatanmu. Hattara garemu yanmmata!)


Wani Murmushi ta saki kana tace "karka damu in sha Allahu zan saka mana time soon"

" okay fine inajiranki" yace in i don't care manner.


"Bakada Matsala"

Tace kana tadauki kudin tasa ajaka hadi da daukan ledar kaza da yoghurt da yasuyo mata ta fice daga motar...
Da ido yabi surarta kasancewar tana sanye cikin riga da skirt din atamfa wanna dinki ya matse ta matuka

Murmushin mugunta yayi yace " kina dab da shigowa ahannu na yarinya"


kana ya bawa motarsa wuta ya yabar unguwar a guje...


Abbuh dake tsaye tun dazu ganin wacce ta fito daga motar ya sashi mamaki, bin bayan jameelan yayi zuwa cikin gidan.


Jameela na kokarin shiga dakinta abbuh ya kwalla mata kira dawowa gabansa tayi kana tace

"abbuh ina wuni "




lafiya lou ya amsa.


"Wayeshi"?

gabanta ne yafadi domin duk abunta tana shakkar abbuh cikin in'in na tace abbuh ban gane ba.


" Karki raina wa kanki hankali wanda ya ajiyeki amota nake nufi"


" abbuh saurayi nane sunansa salman"


" Tun yaushe kuka tare dashi"?


"Shekara daya da'yan watanni"

ta fada kanta a Kasa.


" ina wacan yaron sani danake ganin ku tare, Ina ce shine wanda kika ce kina so?"

" A'a bamu daidaita da sani ba"


" toh kice inason ganin wanna din"

"toh abbuh"


dakin mami ta nufa ta ganta kwance.

"Lafiya? Mami?"..


"Wallahi jikina ke ciwo"

tafada tana ya mutsa fuskarta wanna ta hakan zaka fahimci tana jin jiki,
"kisha magani toh" cewar jameela .


"nasha, aiki danake sha ke sani wanna ciwon jikin"


Tabe baki jameela tayi kana tace "toh ko ansamo miki mai aikin basa dadewa saboda bakya biyansu, in ma abbuh ya bayar cinye wa kike"



Tafada babu ladabi Sam, shiru kawai mami tayi bata ce komai ba

"Me alhaji ke ce miki ne?"

"Wai nafadawa salman yanason ganinsa"

" toh fah"

mami tafada atakaice


"mami kinga salman wai na shirya mana fita"

" toh banda abinki yar albarka, ba kwai ku fita yawa ku dawo ba me aciki?"

cewar mami

"hmmm abinda yasani nake dan jin tsoro

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment