Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta fara bin bayan ummu domin gidan ya bata tsoro saboda girmansa.

"Hajiya sannu da zuwa"

" Yawwa malam iro"

"baba ina wuni"

cewar Faheemah asanyaye.

"yawwa yar baba sannu kinji"

murmushi ummu tayi tana yaba tarbiyyan faheemah a ranta.



"Oyoyo ummu sannu da zuwa"

"yawwa ya gida fareesah?"

" Lafiya lou, ummu Ina ta...."

Ai Karaf suka hada ido da Faheemah dake bayan ummu ai ihun murna fareesa ta saki kana ta rungume Faheemah, "wallahi ummu she's very cute, matar brother nah welcome to your home"


"Allah ya shiryeki fareesa, wai bazaki girma bane?"

" Allah ummu farinciki ne yamin yawa,ummu kin manta wahalar damuka sha? kafin mu samu wanna mai kyakyawar zuciya ta aminci da auren brother na". Tafada tana fashewa ta kuka mai ban tausayi.

kuka faheemah ta fara taya fareesa kasancewar ta mai saurin kuka, Domin abubuwa da yawa ne suka haΙ—ar Mata.

"ya isa haka! Kinga kin sata kuka ko, ko kuma na mayar da ita gidan su?" cewar ummu a zolaye.

"Allah nadaina ummu kibar mana ita" ta fada tana sharewa faheemah hawaye hakanan taji faheemah ta kwanta mata. Itama faheemah sharemata hawaye take, ummu na tsaye tana Murmushi kana tace fareesa ta kai ta dakinta tayi wanka sai su sauko su ci abinci.


"toh ummunah, muje matar brother nah" ta kama hannunta izuwa dakin da
'aka gyara musamman domin faheemah.



*ASALINSU*

FU'AD OMAR ISHAQ dane ga Alhaji Omar da hajiya kaltume. sanadiyar batan wayar Omar ne yayi haduwarsu.
kaltume ta sinci wayar a hanyarta ta dawowa daga makaranta. Sosai Omar yayi farinciki daya kira wayar ta sanar dashi address domin yazo ya karbi wayarsa kasancewar akwai abubuwansa masu muhimmanci aciki...
A hankali shakuwa tashiga tsakaninsu wanda yakaisu ga soyaaya.
Kaltume yar maduguri ce yayinda Omar dan gombe ne wanda bautar kasa ta kai shi garin su kaltume, bayan ya gama services dinsa ne yasamu aiki a banki kasancewar bangaren daya karanta kenan.

Bayan wata shida aka daura auren kaltume da Omar aka kawota gidanta dake kano saboda anan Omar yasamu aiki, yadawo da kaninsa kano saboda shi kadai ya rage masa domin iyayensa sun rasu adalilin zuwa ta'aziya jigawa suka samu hatsari. Kuma yace bayason barwa wani cikin dangi ya rike shiyasa ya taho da shi.



Bayan shekara hudu kaltume ta haifi danta kyakyawan gaske murna wurin omar bazai musaltu ba, ranar suna Yaro yaci suna " FU'AD" .
Fu'ad nada shekara biyar kanin alhaji Omar yakub ya auri hindu suka tare agidan da alh Omar ya siya masa tare da bude masa babban shagon siyarda kayan provision saboda Allah ya kara daukaka alhaji Omar anbashi directorn banki.
Bayan shekara daya shima yakub yayi aure, bayan wata tara matar yakub hindu ta haifi yarta mace ranar suna yarinya taci suna umaimah.


Umaimah nada shekara daya hajiya kaltume (ummu) ta sake haihuwar yarta mace kyakyawa, sosai fu'ad yayi murna ganin ya samu kanwa, ranar suna yarinya taci suna fareesah.


Hindu nada wani boyayyen hali wanda bata taba nuna wa su ummu ba.
Tana matukar jin haushi ganin ummu sun fisu arziki, domin a cewarta su suka dace su samu irin wanna uban arzikin. Duk da cewar babu abinda suka rasa domin suma masu kudi ne, amma saboda hassada na cinta da rashin godiyar Allah yasa take hangen na su ummu, kuma yanzu harkan kasunwanci yasake budewa yakub din, domin yanzu yana da manyan shaguna har biyu a kasuwar singa.

A halin alhaji Omar ishaq sun kasancewa family masu matukar son junansu, ga zaman lfy, gashi basu da kyamar talaka ko kadan hakan yasa duk ma'aikatar gidan ke jin dadi aiki a gidan.


*BAYAN WASU SHEKARU*

Fu'ad yagama secondary school dinsa, alhaji Omar (Abba) ya turasa kasar Malaysia domin cigaban Karatunsa wanda abbah yamai sha'awan karantan accounting aka yi sa'a ra'ayinsu yazo daya.

Bayan wasu shekaru yadawo da dimbin nasarori wanda yan kasar Malaysia suka so yayi aiki a kasar amma yaki, acewarsa yafiso yayi aiki a kasar sa ta haihuwa.

Aiki abbah yasamo masa awani banki babban banki, kansancewar mai kula da banki din gabadaya abokin sa ne.


ba bata lokaci yasamu saboda result dinsa yayi kyau sosai, a wanna lokacin ne faressa take shirin shiga level1
Umaimah na matukar son Fu'ad sai dai kwatata bata samun fuska awajensa, domin baya sake mata fuska saboda ya kula kanta na rawa, idan kanason ganin fara'ar sa toh yana tare da ummu, abbah, anwar, ko kuma fareesa tilon kanwarsa.


Wani lokacin takan zo tayi kwana biyu agidan su fu'ad duk da haka baya kulata tun bata nuna wa afili har ta fito ta nuna masa, am still biris yayi da ita saboda a tsarinsa bayason mace mai bayyanawa namiji tanason shi, acewarsa bata da aji...



Akwai wata rana da wanna alhalin bazasu taba mantawa ta itaba, ranar da zuciyarsu ta shiga kunci, ahankalinsu ya tashi, zuciyoyinsu ya shiga radadin rasa babban jigo arayuwarsu. Hak'ika rasa mutum aduniya kamar alhaji Omar (Abba) babban asarace! Domin mutum ne mai halin taimakon talakawa da kyaukyauta wa duk wanda zama ya hada su, amma dole suka dau dangana Domin Allahu daya daukesa ya fisu sonsa.
Yana hanyar zuwa gida bayan ya tashi a aiki yasamu accident din wanda ko shurewa baiba ya amsa kiran Allah, fu'ad na tuki yaji kiran wayarsa "abbahna" yagani arubuce sosai gabansa yafadi naganin kiran abba domin ko minti takwas basuyi da gama waya ba cikin zolaya da kaunar juna domin akwai shakuwa atsakaninsu sosai. Asanyaye ya latsa kore hadi da kara wayar akunnensa "hello Abbahna Kodai kana missing jin muryata ne ya fada azolaya, sai hakuri domin Allah yayiwa mai wayarnan cikawa Yanzu adaidai hanyar kabuga naga kaine mutum na karshe daya kira, cewar mutumin cikin tausayawa, stairing din motar ne ya kwace masa domin ya ji abun a bazata, duk yanda yayi ya taka burki abun ya citura domin anatukar rude yake, nan suka yi karo da wata babbar mota, nan take motar sa tayi kwatsa-kwatsa domin bazaka taba tunanin mutum zaiyi rai a motar ba, daga nan bai kuma sanin ina kansa yake ba...




Aranar ummu taga tashin hankali narasa mijinta ga kuma danta rai ahannu Allah, Sosai mutane suka tausaya mata, saidai tayi tawakalli Sosai ta kuma fawallawa Allah lamarinta...




Abun mamaki bayan sadakar bakwai din abbah ne FU'AD ya farka saidai baya iya motsa komi na jikansa Wanda yasa likitoci suka tabbatar da yasamu paralyzes suka kuma cewa tashin sa sai wani ikon Allah, sosai hankali ummu ya tashi bayan sadakar arba'in ta fitar dashi kasar India. Sunyi iya kokarinsu amma bawani sauki haka sukai ta zuwa kasashe dasuke tunanin suna da kwararun doctors, amma bawani nasara haka suka dawowa gida ba nasara....


Ganin idan suka cigaba a haka komai zai iya kare musu ne yasa ummu tunanin fara bussiness, gadon da abba ya bar musu ta bude company mai suna *FFK foods & drinks nigeria limited* tare da taimakon anwar abokin fu'ad company yazama standard.
Bayan shekara2 cikin ikon Allah da kudurarsa company ya samu riba mai yawan gaske, hakan yasa suka bude wasu branch a Lagos, delta, da kuma kaduna.


Fareesa na zuwa makaranta, duk ranar datake free kuma tana zuwa campany domin kula da wasu abubuwan. yayinda Ummu ke kulawa fu'ad agida, saidai company's din Yayi wa fareesa yawa ta kula dashi saboda ita kadai bazata iya handling ba. Gashi anwar baya kasar, Hakan yasa ummu tafara neman wacce zata kula dashi kafin tadawo office, ita kuma sai ta taimakawa fareesa da kulawa da campany's din.


Kudi masu yawa ummu tasa akan duk wacce zata kula dashi, zata ko zai mallakesu, saidai duk wacce taga irin laluran dake tare dashi sai su gudu, wasu ma sun yarda ummu ta biya su dasun ga yanda ummu ke mishi hidima sai su gudu da kudin, ganin suna asarar kudi yasa suka hakura. Kuma sosai hakan ya karyawa da ummu zuciya ganin mutane yanzu kowa kansa yasani, mutane basa taimakon junansu, amma kafin lalurar nan ta sameshi yanmmata kullum da wacce dazata zo gaisheta, amma yana shiga wanna halin duk suka gudu bama wanda yafi bawa ummu mamaki kamar umaimah har kyamar zuwa dubasa take, hakan yasa ummu sake tsorata da al'amarin duniya...


Ta kuma kudurta aranta cewa awanna yanayin da yake ciki ya dace yayi aure, domin ta hakane zai samu Soyayyar gaskiya, itama hankalinta zai fi kwanciya cewa ba dan wani kyalekyale rayuwa yasa ta aureshi ba, hakan yasa ta shiga neman mai auran danta, amma babu nasara, duk da zunzurutun kudin kuwa data sake sawa ma bata samu ba.. amma bata karaya ba, sai akan Faheemah ta dace.




*BACK TO STORY* (mun dawo labari)



nuna mata toilet tayi sanna tace ta shirya tana zuwa, kallon dakin faheemah ta shiga yi babban falo ne sai bedroom kitchen hadi da toilet sosai dakin ya tsaru komai pink &white ne, bedroom dinta ma yayi kyau sosai fiyeda tunanin mutum. Wai wanna ne dakina? Wanna katon gadonma nawane? ta fada aranta hawaye masu dumi suna zubo mata, ita da agidansu akasa take kwanciya

"Alhamdulillahil lazi bi ni'imati tatimun solihat "

ta furta can kasan makoshi kana ta ture kofar toilet ta shige shima ya hadu sosai wanka tayi cikin nutsuwa ta fito,wasu cosmetics ta gani akan dressing mirrori masu yawa lotion mai pink din roba ta dauko mai suna *so clear so pink* tafara shafawa, wai ita ce yau keda arzikin shafa mai, ita da wani zubin man kuli take shafawa agida, ba wai ba mai ba a'a, mami ke hanata. Kwalla daya ciko idanunta ta mayar, kana ta bude wardrobe taga kaya masu yawan gaske tsayawa tayi tana kallon kayan, can ta dauko wata jan gown mai A shape tare da dan mayafinsa, Sosai rigar ta zauna a hadadiyyar kuma kyakyawar surarta ta figure 8 kwalli kawai ta zizara tana kokarin fita fareesa ta shigo

"masha Allah kinhadu sosai matar brotherna"

"muje ummu na jiran mu"

Murmushi tayi kana ta yafa Mayafi, fareesa ta kamo hannunta suka sauko.

A dinning table suka tarar da ummu zaune tana waya suma zaman sukayi bayan ta gama ne ta kalli fareesa, "abokin yayanki ne wai nan da 2month zai dawo"


"Wai ummu ya anwar?"

"Eh"
ta amsa atakaice

"Alhamdulillah Allah yakawoshi lafiya"

"ameen" Ummu ta amsa kana ta kalli faheemah tace "diyata fatan kayan sun miki?"

" ko kina da bukatar wani abu ne? "

Kai ta girgiza kana ta durkusa kasa, "nagode nagode sosai ummu Allah ya biya ki da aljanna madaukakiya"

" ameen diyata "


ummu ta amsa cikin jin dadi addu'ar' kana ta kamo hannunta, babu godiya atsakanin mu, Ina jinki tamkar fareesa domin kinmin abinda mutane da dama suka kasa yimin, ke din ta dabance Ina alfahari da samunki cikin zuri'ata, koda a yanzu kika ce bazaki auri dana ba Wallahi zan rike ki amana tamkar yar dana haifa"

"Kada kice haka ummu kin wuce haka awurina kamar ummina haka na dauke ki, saboda haka umarnin zaki ban na miki alkawarin cika shi da dukkan iyawata" ta rasa a sanyaye tana sakin kuka mai ratsa zuciya , ummu da fareesa ma kuka suke...



Bayan kamar minti 5 ummu ta yi karfin halin rarashinsu kana tace " diyata kinsan meyasa najewa maminku amatsayin talaka?"

" A'a" ta amsa a hankali.

" saboda a yanda kika ban labarin rayuwarki na tabattar idan naje mata amatsayin mai wadata bazata yarda tabani keba nalura bata batason cigabanki shiyasa naje mata ta wanna sigar kuma zatayi mamakin daukakarki in sha Allahu. Sanna mahaifinki ki cigaba da mai addu'a inaji kamar akwai wata kulalliya akasa amma ba abinda yafi karfin Allah komai zan daidaita kinji" hawaye ta share tana gyada wa ummu kai alamun gamsuwa.





"Sanna Ina so sai anyi daurin auran kafin ki fara kula dashi, ni kuma sai in fara fita company domin taya wanna raguwar da ayyukan office' ta karasa azolaye.
Murmushi suka yi kana Fareesa tace "Allah ummunah ina kokari fa, mutane ne yanzu ba tsoron Allah komai sai anyi ha'inci shiyasa dole saidai taimakon ki wasu abubuwan xasu daidaita a campany's din" jinjina kai ummu tayi cikin gamsuwa, Kana ta umarcesu da su fara cin abinci...





*Idan kin karanta kiyi share zuwa wasu groups saboda Allah*



#SHARE
#COMMENT


πŸ’”RAYUWAR FAHEEMAH πŸ’”

_by NoorEemaan_


kyautane (free novel)


I would never get tired of saying alhamdulillah ya Allah bcos he never get tired of waking us up each day.


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



15-16



(Not edited)


Da d'add'adare ummu ta samu malam iro tasanar dashi daurin aure fu'ad da Faheemah da takeso a daura da asuba a masallacin dake wajen gidan wanda aka gina da sunan abba domin kai ladan kabarinsa.



sosai malam iro yayi murna, saboda shi shaida ne irin wahalar dasuka sha akan neman wanda zai auri oga karami kamar yadda yake kiran fu'ad, kana ya nemi alfarman ummu akan shi zai biya sadakin bawai dan basuda halin biya ba sannan zai zama waliyyinta, sannan kuma abokin shi dake aiki a gidan dake gaba da nasu zai zama waliyyin fu'ad.



Godiya ummu tayi sosai kana tace "amma malam iro dawainiyya baza tayi yawa ba?"

" a'a hajiya dan Allah kiban wanna damar domin nuna godiya ta akan karamcinki garemu nida mai dakina"

"Toh shikenan bakomai sai Allah ya kaimu Nagode" kana ta koma cikin gidan.


β˜…β˜…β˜…

Da asuba duban mutane da suka hallaci sallar asuba suka shaida daurin auren FU'AD OMAR ISHAQ da FAHEEMAH ABUBAKAR IDRIS akan sadaki naira dubu hamsin.

Hakan yayi daidai da zubar hawayen Faheemah, domin tana kan sallaya a lokaciin kasancewar ana jin komai ta loud speaker din masallacin. Wai itace aka daurawa aure? Tareda mutumin dabata taba gani ba, yau daurin aurenta amma abbuh'nta baya nan, ba wani daga cikin danginta sosai hakan yasa ta kuka.



Toilet ta fada tayi wanka hadi da brush domin sosai Allah yayi ta mace mai tsafta, koda a gidansu mami bata barin ta taba toothpaste(makilin) amma duk da haka tana wankewa da gawayi hakan yasa hokoranta keda tsananin tsafta hadi da haske.

Bayan ta shirya cikin doguwar rigar atamfa mai kalar fari, baki da dan ratsin lemon green kana ta fara saukowa daga matatakalar benen, ido hudu sukayi da mami dake kokarin shiga dakin fu'ad domin daura masa alwala.


"Mezan gani haka ni kaltume amarya da asubayin nan ta fito"
ummu ta fada cikin zolaya, kasa faheemah tayi da kanta cikin tsananin jin kunya, wai yanzu wanna kamilaliyyar mace mai halin kwarai surukartace?
Murmushi mai sauti ummu tayi domin ta fahimci kunya take ji, cikin takun nutsuwarta tazo gaban ummu ta durkusa, "ummunah ina kwana"

" lafiya lou diyata faheemah , ya kwanan bakunta?"

"Alhamdulillah"
ta amsa kasa kasa.

"ina alfahari da samunki a matsayin suruka ta, nagode sosai da kika amincewa auran nan, Allah yamiki albarka"

"ameen" faheemah ta amsa cikin jin kunya kana tace
"ummu wani aiki zanyi?"

Zaro ido ummu tayi cikin zolaya tace "rufamin asiri ni da sa amaryan fu'ad aiki"

murmushi tayi domin ta lura ummu irin masu barkwancin nan ne, tana matukar son ganin wanna fu'ad din mai sunan kaninta domin sosai takeson sunan...


"Kije ki huta akwai masu aiki zasuyi komai"

"ummu please kibani aiki nasaba bayan sallar asuba bana komawa bacci"

tausayinta ne ya ratsa zuciyar ummu ace mutum kullum cikin aiki, "toh yau dai kihuta babu abinda zaki yi, bari nace na shirya miki angonki"

Tsunne kai faheemah tayi tana jin kaunar ummu azuciyarta.

Dakinta ta koma tafara gyarawa duk da ba abinda dakin yayi, air freshener ta fesa tanajin kewar gidansu, lallai *sabo tirkin wawa* wai duk wahalar da take sha a gidan hakan bai hana ta jin kewar gidansu ba.


β˜…β˜…

Da misalin 8:30 ne duk suka hallara a dinning domin yin breakfast. bayan sun gama ne ummu ta ce


" diyata?"

"na'am ummu" ta amsa.


"inaga zaku koma part dinshi saboda kada ki takura, daman saboda lalurarsa yasa muka dawo dashi part dina"


"a'a ummu anan din ma yayi"

" Toh shikenan, gobe litinin zamu fara fita company tare da fareesa ko akwai abinda kike bukata?"


"A'a" ta amsa cikin sanyin muryanta.


"dakin dana shiga dazu anan mijinki yake, yau banaso kiyi komai saboda amarya kike"

dariya faressa tayi, cikin zolaya tace


"ummunah kina shagwaba surukar ki fa"


itama ummu cikin zolaya tace

" toh ya son ranki.

Murmushi fareesah ta sake yi wanna karon har da faheemah.
"ummu ina so muje salon da matar brother kanta na bukatar gyara".

"Toh sarkin yawo zaki fara koya mata ko?"


"Allah ummu ba haka bane, matar brother ai kinaso muje ko?"

Kasa faheemah tayi da kanta tana murmushi, "ba akwai komai na gyara ba? Ki gyara mata da kanki" cewar ummu kana ta danna wata kararawa dake gefen ta cikin mintuna kalilan duka ma'aikatan gidan suka hallara, nan ta gabatar musu da Faheemah amatsayin matar danta, sun gaisa cikin mutunci kana ta sallamesu.


Gyara mata kan fareesa tayi wanda har kwalla tayi saboda zafi domin gashin acike yake ga tsaho sosai, gashi a cunkushe yake adalilin rashin gyara, itama mai gyaran taji jiki saboda yawan gashin.



β˜…β˜…β˜…

A bangarensu mami kuwa duniyarsu suke ci da tsinke sun ma manta akwai wata hallita mai suna faheemah sosai suke jin dadi rashin ganinta agidan, ga kuma saurayin jameela dake sakar mata kudi sosai hakan ya musu dadi kwarai, abbuh kuwa bai nemi faheemah ba hakan yasa mami kicin karenta babu babbaka.


Washegari bayan ummu ta iddar da sallah ta daurawa wa fu'ad alwala yayi tasa akwance kamar yadda ya dauki tsohon six years yana yi...daga nan ta koma dakin ta sannan suka fara shiri domin zuwa aiki. 7:30 suka bar gidan breakfast ma a basket aka shirya musu suka tafi dashi....


Takwas daidai ta fito domin zuwa dakin Fu'ad, yau ta makara bata tashi da wuri ba, domin bata samu bacci da wuri ba saboda raba dare tayi tana ibada. Tana saukowa ta hadu da wata matashiyar mata da'a shekaru zata kai 28yrs tana mopping mai suna larai.
"ina kwana uwar dakina" cewar matar tana rissinawa, kunyace ta kama faheemah ganin matar da ta girme mata na gaisheta, itama russunawa tayi ta gaisheta kana ta nufi dakin Fu'ad din...



A hankali ta tura kofar dakin ta shiga dadaddan kamshi ya bugi hancinta, wanda hakan yasa ta lumshe fararen idanunta kana a hankali ta ware su a kansa dake kwance sambal kan babban gadonsa sanye da gajaran wando fari kal da bakar riga da'aka rubuta "HANDSOME" da manyan aruffa.


gabanta ta ne ya bada ras ganin kyakyawan halittan dake kwance, yanzu wanna kyakyawan ne mara lafiya? Ta fada aranta.


Lallai Allah yayi baiwar kyau anan, ta sake ayyana aranta. Cikin takun nutsuwarta takarasa kan gadon, kura masa idanunta tayi...
Farine sosai yana da wasu kyakyawan rikitatun idanuwa masu matukar haske, hacinsa dogo ne hakama bakinsa karamine mai dan tudu masu light pink color . Kyakyawan sajansa daya kwanta a kyakyawar fuskarsa ya kara masa kyau ainun, duk da a kwance yake amma dogo ne sosai haka ma yana da faffadan kafada da murdaden jiki wanna hakan ke nuna lokacin da yana da lafiya baya wasa da motsa jiki.


Saidai halin rashin lafiyar dayake ciki yasa shi dan rama, dan ma yana samun kulawa sosai daga ummun sa...

Ajiyar xuciya ta sauke bayan tagama kare masa kallo.

"Sannu kaji Allah yabaka lafiya"

ta fada tana share hawaye ganin lafiyayyan mutum a kwance amma bazai iya bakomai da kansa ba, lallai Idan Allah ya baka rai da lafiya ka gode masa, duk maganganun nan a ranta take yin su.


"Kana jin yunwa ko?"

Tafada tana shafa shafafen cikinsa masu dauke da six packs, kana tace "kayi hakuri bari naje na dama maka kunu zakasha ko?" ta sake fada kamar zata samu amsa kana ta fice tana waiwayansa zuwa kitchen, domin hakan nan ta ji ya burgeta.


Kunu daya wadatu da madara ta dama masa sanna ta dawo dakin, kamar yadda ummu da sanar da ita akwai wani madanni dake gefen gadon, shi kuwa ta danna nan, take gadon ya dage sama sai yayi kamar ya kishingida ne , kunun ta shiga bashi wani ya shiga bakin, wani yana bin gefen bakin ya zubo, amma ba laifi yasha sosai, daga baya idan ta zuba masa baya hadiya sai ya zubo hakan yasa ta fahimci ya koshi, goge masa bakinsa da hankachief tayi kana ta shanye ragowar kunun daya rage.



Toilet tashiga tahada ruwa mai dan dumi sai turaren wanka data zuba aciki sanna ta fito da ruwan, gadon ta hau tafara kokarin cire masa riga sai kuma ta tsaya, sosai take jin kunyar hakan saboda bata taba ganin namiji babba ba riga ba , sai wani kasa take da kai saboda kunya, amma yazama dole ta cire kunya ta kulada shi.

Lumshe idanunta tayi ta karasa zare masa rigar mistakely hannunta ya sauka akan wandonsa taji alamun yafara jikewa sake tabawa tayi taji alamun akwai "adult diaper "( pampers din manya) ajikinsa, zare wando hadi da diaper din tayi, kana ta koma toilet, komai tana yi ne cikin matsananinci kunyarsa domin bata da option.

Wani ruwan mai dumi tahado ta masa sarki, zubar da ruwan tayi kana ta goge masa jikinsa tas da ruwan data hada

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment