Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

all this years".






Wallahi tallahi a iya sani na bantaba yiwa abbuna laifi bah. Shafa bayanta ya shiga yi kana yace " I trust you heema, yi shiru komai zan daidaita ok?"

Jinjina masa kanta tayi hadi da sauke ajiyar zuciya.



Babu jimawa bacci ya dauke ta, kurawa fuskarta ido yayi, azihiri fuskarta yake kallo amma abadini tunani yake, wani murmushi ya saki kana yace "yes! Hakan zanyi Allah kabani sa'a ya fada abayyane" hadi da sumbatar goshinta babu dadewa bacci ya dauke shi...



Washe gari bayan duk sunyi breakfast apart din ummu, ya mike hadi da goge bakinsa da tissue, sumbatar ummu yayi a hannu kana ya ja kumatun fareesa cikn wasa wanda yasa ta sakin murmushi, ido suka hada da ita, saurin mayar da kwayar idanunta kasa tayi tana wasa da zoben hannunta, murmushi kawai yayi hadi da cewa




" shagwababiyyar ummu na tafi "


be jira amsar ta ba, ya fice cikin sauri Domin ya makara...
fareesa ta hau sama Domin shiryawa saboda tana da exam karfe takwas da rabi. Kan royal chair dake hadaddiyar parlor suka koma

"Diyata faheemah" ummu ta kirata.


"Na'am ummunah" ta amsa


"ina miki magana amatsayina ne a matsayin mahaifiya agareki bawai suruka ba, duk lokacin da mijinki zai fita office ko unguwa make sure kin rakashi ko da zuwa kofa ne ok?"

Cikin kunya hadi da kaunar ummu tace


"kiyi hakuri ummu zan gyara". Murmushi ummu tayi Tana mamakin sanyin halinta, "bakiyi mun komai ba diyar albarka"



Murmushi tayi hadi da kwantar da kanta akafadar ummu Tana jin soyaayyar surukarta na ratsa ta.


" inyee autar ummu (faheemah) irin wanna soyaayyar haka, I will like to be like you when I grow up" ta fada cikin zolaya.



Dariya faheemah tayi hadi ta rufe fuskarta...


"Ke fareesa bar mun diyata ta huta hakan nan"

"Allah ummu kina shagwaba autar taki da yawa fa"...

"ya son ranki toh" ummu Tafada tana Kara kwantar da kan faheemah ajikin ta "shikenan Matar brother ta kwacemin kujera ta na auta, ya na iya na ci girma na bar miki" Tafada tana kwabe fuska irin na shagwaba, dariya suka ummu suka sanya mata, fareesa badai abun dariya ba, Itama dariyar tayi kana tayi musu sallama ta fice domin Kiran ya anwar dake shigowa wayarta Wanda ya tabattar mata daya iso domin shi zai kaita makaranta...



Misalin karfe biyu na rana, bayan ya iddar da sallar azahar a masallacin dake gefen bankin yaji wasu matasa na fadin





"jibi za'a rufe registration din JAMB fa abokina Wallahi yau nasha wahala Sosai kafin nayi nawa register din..."




Ai bai jira yaji karshen maganar su ba, ya figi motarsa ya bar bankin, a ransa godiya yake wa Allah daya sa yaji maganar nan, amma ace yau saura kwana uku a rufe amma baida labari sai yau .....



"alhamdulillah ya Allah"

ya fada a bayyane daidai isowarsa cafe din mai suna albarka cafe dake gidan Buhari.

komai da ake bukata ya biya hadi da karban foam din ya fada musu zaiyi submitting zuwa yamma tunda suna kaiwa dare....


Office ya koma kafin
lokacin tashi yayi.
Isar gida ko part din ummu bai je ba ya nufi nasu part din.


" Inason faranta maka rai ya fu'ad, inason kuma bin umarnin ka, amma ina jin kunyar kayan nan sosai"


tafada abayyane, kana a karo na barkatai sai faman jan yellow T-shirt da tsayinsa ya tsaya daidai cinyar ta ne, sannan hannun rigar armless ce, yellow head band ta sa a gashinta, sai dan karamin barima mai yellow stone ta sanya , fuskarta kuwa light make-up ne, daga powder, white lip gloss, sai kajol data zirara sosai tayi kyau gwanin birgewa


"ya rabb kabani ikon tsayawa agabansa da wanna kayan" ta fada cikin sanyi muryanta.......



Ko gama rufe baki batayi ba taji sallamar sa hadi da bude kofarsa a lokaci daya, ai mutuwar tsaye yayi sosai hadadiyyar surarta ta figure 8 ta bayyana acikin rigar, jiyayi kamar ya hadiye ta ko ze samu sauki soyayaarta dake karuwa da duk bugun zuciyarsa. cikin kasalar daya saura masa yace

"Faheeeeeta"

Cikin dan sauri ta daga kanta domin tone dayayi amfanin wurin kiranta dashi...


Ganin ya ware mata hannayensa yasa cikin dan gudu- gudu tafada a faffadan kirjinsa.


Lumshe ido yayi saboda dada'ddan kamshin daya ziyarci hancinsa, cikin kunnenta yarada mata

"you look gorgeous my girl"


kana yabata light kiss a lips dinta hadi da janyo hannunta ya zaunar da ita agado, shima zama yayi hadi da ciro form din cikin jakarsa...


Mike mata yayi hadi da biro yace ta cike, kallon form din tayi madaukakin farinciki ya bayyana afuskarta domin ta fahimci form din kona menene, ta budi baki za tayi magana ya ce

"shhhhhhh! and just fill the form"

saboda farinciki Hannunta har rawa yake, fahimtar Hakan yasa shi dora hannunsa saman tata, cikin tausayinta

yace. "nutsu ki cike ok?"

kai ta jinjina masa cikin farinciki kana ta shiga cikewa cikin nutsuwa...


cikin 15min ta gama hadi da mika masa, Karba tayi kana yace

" inyee ashe diyar ummu likita zata zama"


yafada idanunsa akan rubutun mai matukar kyau da tsari. Murmushi tayi kana ta rufe fuskarta cikin kunya.....

Mikewa Yayi yace

"bari na kai musu nadawo kafin magriba"


binsa tayi abaya har bakin kofa dazai sada shi ta waje yatsaya hadi da kallonta domin yayi mamakin ganin ta biyo shi domin bata taba Hakan ba.

"zaki bini?"

Ya tambayeta, girgixa kai tayi, Kukan da take kokairin rikewa ya kwace mata, fadawa jikinsa tayi kana tace

" ya fu'ad thank you so much, bansan da wani irin kalma zan gode maka ba.
Allah ya biyaka da alkhairinsa ya rabaka da ummun Lafiya" ta karasa tana kara kankameshi....


Cikin kaunarta hadi da tausayinta yavshiga Bubbuga bayanta cikin farinciki addu'ar da tayi masa yace.


"ameen ya rabbil samawwati, yi Shiru no more cries okay"


"toh"


tafada cikin cool voice dinta hadi da breaking hug din ta masa adawo lafiya ta juya zuwa dakin ta, shima ba bata lokaci yabar gidan....



Ahanyar dawowa yayi sallar magriba kana ya nufo gida. Axaune dukkansu suke aparlon ummu sai hira suke ganin burgewa, sannan duk sanye da hijab suke da alama basu dade da iddar da sallar ba. Sallamarsa ta katse musu hirar tasu.


Amsawa sukayi kana su Faheemah suka gaisheshi, amsa yayi kana ya nufi ummu gurin ummu ya tsugunna hadi gaisheta, murmushi tayi kana ta amsa masa cikin kaunarsa.




Tambayarsa ina yaje tayi, a atakaice ya mata bayani, addu'a sosai Tayi masa hadi da sanya masa albarka. Cikin kaunar mahaifiyarsa ya shiga amsawa da ameen.


"Mami meyasa komai daya dace ace nina sameshi, Faheemah ke samu?"


"Ada ina ganin cewar idan na samu SALMAN na gama more miji, sai naga ashe shi ba komi bane akan mijjn Faheemah, inason shi Mami, tun daga ranar dana Dora ido na akan hoton sa, kiyi wani abu mami inason sosai Tafada cikin bayyana zallan abunda ke cikin ranta"



Mami dake fama da wanki ta dauraye hannunta kana ta zauna kusa da jameelan



" kada ki damu diyar albarka, ina mai tabattar miki ko zan rasa komai nawa sai kin mallakeshi, so nake na karbo kudin dashin nan naje wurin malam"(Allah y shirya, malam ko boka?)


Yawwa mami kiyi wani abu please akwai ma dubu hamsin dazan baki ki kara akai. Ai farinciki ne ya bayyana afuskar Mami jin za'a bata kudi, yawwa yar albarka"



******** *******

9:00pm kwance suke agado kowannensu sanye da sleeping dress, Faheemah tun tana jin kunya saka sexy wears dinnan har ta dan saba Domin ta lura yafi son ta sakasu...

" faheeta" ta Kira ta cikin hadadiyyar muryansa.

"Na'am" ta amsa cikin cool voice dinta.


"Inaso ki bani labari"

Domin so yake ya katse shirun dasuka yi almost 1hr babu mai magana acikinsu Domin dukkansu ba masu son hayaniyya bane ba.



"Ko bacci zakiyi ya sake tambayarta?"

"Aa yah.... Fu'ad" ta fada cikin cracking voice.



Kana tace "banda labari sai dai na baka labarin
RAYUWAR FAHEEMAH" tafada hawaye na cika idanunta.


Bai ga hawayen da suka cika idanunta ba hakan yasa yace


"ok na karkade kunnuwana ina sauraranki..."



"Sunana Faheemah abubakar idris asalin yar..................................."


Nan ta shiga bashi labarin komai na rayuwarta bata jin zata iya boye masa komai, ai duk dauriyan fu'ad saidai ya zubar da hawaye musamman inda mami ta zuba mata zallan attaruhu afarjinta. Wanna rashin imanin da tsanar har ina?


Ta tambayi kansa, take yaji wata tsanar mami na ratsa shi, sai kuma ya shiga mamaki meyasa abbuh yadaina kulawa da lamarin FAHEEMAH bayan kuma matsananci soyaayyar dayake mata a da?



Kankameta yayi yana jin soyaayyarta, kaunar, hadi da matsananci tausayinta na ratsa shi......



Kara matseta yayi a faffadan kirjinsa yayi yana bubbuga bayanta saboda kukan da takeyi, tabass ayau baya jin zai iya hanata kuka Domin wani kukan ma rahama ne, kuma yasan shi ya tado mata da mikin dake binne aranta, shine dalilin daya sa ta tuno da labarin rayuwarta mai cike da abun tausayi. Ayau baya jin zai cigaba da boye matsananci soyaayyarta dake karuwa akowacce dakika azuciyar sa Batareda ya furta mata ba....


Cikin had'add'iyar husky voice dinsa daya dan canza amo saboda kukan da yayi yace



"heemah I love you, I love you to the square of infinity"


sai kuma ya sumbace goshinta, tareda cigaba da zubo mata kallaman soyayya mai tsayawa arai. Ji tayi numfashinta ya tsaya cak!


Sai kuma wani matsananci farinciki hadi da shaukin sonsa ya shiga ratsa sa. A ranta tace "Yau ya fu'ad ya furta min kalmar *SO* ya rabb am so happy.
Alhamdullillahil lazi bi ni'imatihi tatimun solihat"


farincikin da take ciki ya kasa boyuwa a saman kyakyawar fuskarta.


"Mrs fu'ad did you also love me? Please say yes!"


Yafada cikin salon marairaita hadi da wani salon shagwaba da'a gabanta kadai yake irinsa, Domin yasan cewar ita din ta daban ce, sakar mata fuska ba zai sa ta raina sa ba, kamar yadda yayi tunani a da.

"Please faheeta say yes ya sake fada yana kokarin ganin fuskarta" cikin kunya ta bude karamin cute lips dinta tace


"I love you too ya fu'ad"

ta fada hadi da boye kanta a kirjinsa...


Sosai yayi farinciki
kana kuma yana jin kansa sakayau Domin ya amayar da abunda ke ransa tsawon lokaci.

Hade bakinsu yayi waje daya, ahankali ya kamo lallausan tongue dinta ya shiga kissing dinta passionatly...



*****β˜… *****β˜… *****β˜…


"Umaimah inaso kiji gidan ummunku kamar yanda kike yi ada, inaso ki hada su fada, ki datsa musu tsanar faheemah ta hanyar tuggu, ni kuma zan shiga zan fita har sai kin mallaki fu'ad amatsayin miji. "



"Wayyo sweet mamana shiyasa nake sonki, nayi farinciki da wanna maganar".


Bari naje na shirya kayana" tafada cikin zumudi kana ta nufi dakinta cikin sauri, kallo hajja Hindu ta bi yarta dashi cikin kaunarta, Domin tun bayan da fu 'ad yayi aure sai yau taga dariya afuskar yarta ta mafi soyuwa aranta


"dole nayi wani abu domin farincikin yata ta fada abayyane".
washegari bayan umaimah ta bar gidansu da misalin karfe 10:00 na safe ta nufi gidansu ummu da akwatin ta set biyu kai kace kasar zata bari.



Itama hajja Hindu shiryawa tayi domin zuwa wurin bokansu, tana dab da isa wurin bokan taga mami ta fito fuskarta dauke da murmushi. " Hindu" mami ta Kirata cikin zallan mamaki, domin bata yi tunanin ganinta a wanna lokacin ba.


Duk da tasan cewar hajja Hindu zata zo ko ba dade ko ba jima hakan ya sa tabawa bokan kudi masu yawa akan ya mata aiki, boka kuwa ya yi mata alkawarin cewa ze yi mata aiki tamkar yankan wuka, ya kara da cewa ko da hajja Hindu tazo bazai yi mata aiki ba, zai dai karbi aikin ne amtsayin zai yi mata aiki, hakan yasa bata da wata damuwa...




Dariya hajja Hindu tayi hadi ta tafa hannunwa sai ta bata rai kamar ba ita tayi dariya yanzu ba kana tace " eh lallai kan mage ya waye, wato har kinsan hanyar zuwa wurin nan kenan?



Toh ki Sani, ni Hindu sai inda karfina ya kare wurin mallakawa yata abun da takeso, Dariya mugunta itama mami tayi kana ta shiga yaba wa hindu maganganu, hmmm hindu muje zuwa Dan halak ka fasa shege Sai yanka, Allah ya bawa mai rabo sa'a...


Nan suka shiga yabawa juna magana zagi ta uwa da uba abun babu dadin ji, haka suka rabu baran baran tamkar ba aminan junan nan bane....





Wurin bokan hajja Hindu ta shiga, ta sanar dashi bukatarta tareda ajiye masa kudi har 1 million ganin kudi yasa boka rudewa ya amince nan take zai mata aiki mai tsananin zafi, sai kuma ya kwashi yanda suka yi da mami ya gaya mata, dariya kawai hajja Hindu tayi domin daman tasan za'a rina.


ya kuma sanar da ita aikin ze dauke shi dan tsawon lokaci kafin ya gama, domin so yake yayi mata aikin mai xafi da zai sa fu'ad ya kawo kansa da kansa wurin umaimah.




Domin yace sai soyaayar umaimah ya kusan haukatashi, yabata umarnin tafiya kana ya ce idan ya gama aikin zai kirata a waya, cikin farinciki ta bar cikin kusurmin dajin ta nufi gida......





Share
Comment
Vote






Thanks for reading

#rayuwar faheemah



πŸ’”RAYUWAR FAHEEMAH πŸ’”

_by NoorEeman_ πŸ“šβœοΈ

Wanna littafin kyauta ne


https://facebook.com/groups/943534712916776/



Happiness comes when you stop complaining about the troubles you have, and thank Allah for the troubles you didn't haveπŸ’πŸ‘Œ



45-46


Cikin tafiyar nutsuwarsa hadi da kasaitarsa ya nufi wurin babban malamin da ke unguwar kurna masallaci.


Zaune yake kan sallaya a daidai madaidaicin kofar agidansa, ga tarin littattafai addinin agefen sa, yayinda yake rike da Qur'ani yana Karatu cikin suratul Yusuf kasa kasa, kallo daya zakawa malam haroon ka tabattar da addnin Islam ya gama ratsa shi, sosai yake da kamala hadi da kwarjini irin na malamai magadan annabawa. Sallama yayi masa hadi da runtsunnawa alamun girmamawa agareshi kana suka gaisa cikin mutuntawa.
Bayan nan, sai ya shiga yimasa bayanin abunda ke tafe dashi, ya kuma sanar da shi abunda ya dace ya sani din, "ikon Allah" cewar malam haroon yana jinjina girman al'amarin, amma ba abun mamaki idan Mutum yayi duba da rayuwar yanzu. Cikin muryan nutsuwa yacewa Fu'ad " kada kadamu yaro, zanyi istahara adaran yau, duk da akwai abunda zuciyata ke rayamin, amma bazan yanke hukunci ko na fada kai tsaye ba. kadawo jibi kamar iyanzu in sha Allah babu abunda zai gagara da yardar Allahu". Godiya sosai fu'ad Yayi wa malam kana ya ajiye wa malam rafar Dari biyar guda biyu, Sam malam din ya ki karba saida Fu'ad din ya dinga magiya kana ya karba yana masa godiya hadi da kyakyawan adduo'i, motarsa ya fada kana ya bar unguwar, aransa yana fatan adace!
Horn daya ya danna malam iro ya bude masa gate, daidai parking space ya tsayar da motar sa kirar Bugatti divo.
Part din ummu ya nufa domin yau weekend hakama yana kyautata zaton shagwababiyyar tasa tana part din ummu.

Daidai yazo bude kofa yaji muryan wanda ya kasa tantance ko waye "asarariya yar gidan matsiyata da sannu wanna gidan nan zai gagareki, sai na lalata rayuwarki ta yadda babu Wanda zai sake rabarki bare nuna soyaaya agareki" domin tana bakinciki da yadda yan gidan ke haba haba da Faheemah kullum...



Saurin murda kofar yayi ya shiga, sadai yana shiga falon yaga wayam sai Faheemah dake zaune ta rufe fuskarta da hannayenta, ko kadan ba ta ji shigowar shi ba domin ta xurfafa atunani, tarasa me tayi wa umaimah? Tarasa meta tsare mata agidan nan? Ranar farko data zo tayi matukar mamakin ganin yanda take hararata amma data ga idanun su ummu Zai yo kanta Sai ta maza ta dora Murmushi a saman afuskarta. Wani lokaci ta banga jeba ta wuce, wani zubin tsaki take jamata, haka kuma tana hango tsanar aduk lokacin da suke tareda Fu'ad wani zubin har labe ta musu... Abun na matukar damunta, amma bata nuna wa kowa ba, domin Ita kam duk tunaninta ta kasa gano abunda ta wa umaimahn.

tattausan hannunsa ya dora a saman hannun ta dake saman fuskarta. Cikin sauri ta dago kanta, "heemah what's wrong?" Ya tambaye ta yanason tabattar da abunda yaji. Murmushi ta kakalo kana ta ce
"ba komi ya fu'ad " cikin rashin yarda da abinda tace yace

"are you sure heemah?"

Muryan wa nake ji tana kamar zagi some minute ago and da wa take?"
"zagi kuma?" ta fada kamar bata san komi kana tace "ba wanda yayi zagi saboda ni kadai ce a falon nan tun dazu, ummu ta shiga ta kwanta, anty Fareesa kuma tana school..."



" ok fine tunda kin ce haka amma idan na tabattar da abunda naji, bezai mana kyau ni dake ba" yafada a dan azafafe domin akwai abunda yake zargi...


Cikin shakuwa da zazafar so, daya shiga tsakanin su a yan kwanankin nan tace

"Afuwan my ya fufu bakowa fa nace, da gaske nake, ta karasa hadi da fadawa jikinsa, oya yimin murmushi please "

domin so take ya manta da maganar bama taso ya sani. Dan cije hancinta Yayi kana cikin zolaya yace " this small girl kin raina ni ko?"

"Wayyo ummunah!!! ya cinye min hanci na" tafada cikin zallan shagwaba hadi da yarfa hannu.



"Raguwa kawai I wonder idan mun zo babbar harka ya zakiyi am sure duka yan gidannan zaki taramin" ya fada yana daga girarsa daya



gabanta ne yafadi domin bai taba dauko mata wanna maganar ba sai yau, amma sai ta basar kawai tayi dariya hadi da rufe fuskarta.....



"faheee ina jin bacci, Muje ki tayani bacci kafin azahar" bata son mai musu dan haka ta gyada masa kai, daga ta Yayi cak! ya nufi ta kofar baya, ganin an rufo kofar cikin sauri yasa shi yin murmurshi gefen baki,hadi da yin kwafa domin yasan ko wacece ta musu labe, I will definitely deal with you ya fada kasa kasa " sarkin son jiki kuwa luf Tayi bata san meke faruwa ba...



Bayan magriba fu'ad yafita da babur din malam iro domin zai fi masa saukin fita,acewarsa bayason fita da mota, wanda hakan yasa malam iro jin dadi rashin girman kai irin nasa. "Albaik chicken" ya nufa, hadadiyar kazarsu mai dadin dandano ya siyi guda biyar hadi da farmfresh yoghurt na vanilla, yayinda ya siyowa su ummu farmfresh din na mango dan ita da fareesa sun fi son shi, tunowa Yayi da akwai umaimah yasa ya siyi mata itama domin idan bai siya ba ummu zata masa fadane.




Ahanya isha tayi masa dan haka saidai ya tsaya Yayi sallah a babban masallacin dake gadon kaya kana ya nufi gidansu dake janbulo first gate...



Godiya Yayi wa malam iro, bayan ya bashi mukulli hadi da bashi Leda daya na kazar mai dauke da tambarin albaik din. kunya ce ta kama malam iro domin baya mantawa Fu'ad din ne yasiya masa babur dinan da dadewa, dan ma bai fiye hawansa sosai hakan yasa lifan din keda sabunta har yanzu.



Direct part din Ummu y nufa, Zaune suke su uku Banda faheemah da daman ya ce kada ta fita, fuskarsa adan daure ya zauna kusa da ummu, sannu da zuwa suka masa ya amsa atakaice, kana ya gaida ummu fareesa ma fuskarta ba yabo ba fallasa domin sosai take jin haushin umaimah dan dai Ummu ta ja mata kunne yasa take sausauta mata, tarasa ummu wacce irin mai sanyi hali ce hadi da rama mugunta da alkhairi?


"ummu yau baxamu yi dinner a nan ba"


ya fada yana sosa kansa, domin sosai take karantar zallan zumudi a tare da shi wanda bata san ko na menene ba




"Meyasa toh?"

ummu ta tambaya tana sauraran Karin bayani daga gareshi, "Ummunah zamu ci wanna" ya fada yana nuna ledojin hannun sa.


"son banason haka fa, idan kai ka koshi diyata Faheemah fa?"


Ai karaf fareesa ta ce

"ummu ai brother da matarsa Abu daya ne, duk abunda daya yakeso, dole shima Dayan zai so shi"



" yawwa my little sis that's why I love you" yafada yana cewa mata High five ai kuwa ta bashi hannu suka tafa
Sosai ran umaimah ya baci, jin ana maganar Faheemah, musamman abunda fareesa tace, ( dama kuma fareesa ta fada da biyune domin taji haushi)



Murmushi ummu tayi kana tace" gidanku wato kun mayar dani kakar ku ko? Murmushi shima Yayi kana, ya sumbaci hannun Ummu yace sai da safenku yafada yana ficewa cikin sauri bayan ya ajiye musu tasu ledar domin ya matsu ya yi tozali da kyakyawar fuskarta.


zaune take ta takure waje daya atsakiyar gado, murmushi mai sauti yayi yarintar ta na burgeshi mafi yawan lokuta cikin matsananci soyaayyar hadi da kaunar ta yace


"goofy angel come to me"


yafada yana bude mata hannayensa...

cikin sauri ta sauko hadi ta fadawa jikinsa. Sai kuma ta dago kanta hadi da turo baki tace


"ya fu'ad shine katafi ka barni nikadai kuma ka hanani zuwa wurin ummunah ko" tafada tana dan cizon tsakiyar kirjinsa ta saman rigarsa...



"Auuchh!"

Ya fadamin yana shafa kirjinsa hadi da kwabe fuska, cikin salon maganar dake zautar da ita aduk sa'ilin da yayi yace " yarinyar nan kin zama muguwa ko?" Dariya ta kyalkykale da ita saboda yanda yayi fuska tamkar taro Dan shekara 3 dole ya baka dariya. Cikin muryan rada yace" zan Rama ne yarinya" yafada yana dan cizon cute soft lips dinsa.
Shagwabe fuska tayi dan ita ba ta fuskanci komai ba.

"kinyi sallar kuwa?"


" Eh" ta amsa cikin cool voice dinta.


"Good girl"


yafada yana dan bubbuga gefen fuskarta ahankali.


" dauko mana plate and cup kinjj?"

Da "Toh" ta amsa, bayan ta dawo tace

"ya fu'ad baxamu je wurin ummu cin dinner ba?"


"A'a my goofy angel anan zamuyi yau, and saina ciji bakin mai cewa ya fu'ad, kin manta hukunci dana miki da safe ko? "

Yafada yana dan dage girarsa.
Murmushi mai sauti tayi domin sosai take son sunan

"goofy angel "

daya data kiranta dashi, sai kuma ta kama kunnuwanta tace; am sorry ya fu.....
Au yi hakuri na manta"
tafada tana rufe bakinta.


bai ce komai ba ya shiga zuzzuba musu farm fresh yoghurt din,hadi da juye musu kazar a plate. "Oya open up?" Yace mata.


Cikin kunya ta bude bakinta ta amshi Naman da

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment