Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da 3weeks time....




*JAMEELA*


"The mtn number you dialed is switch off" shine amsar da wayar ke bata a karo na ba adadi amma ta ki hakura da kiran saboda halin rikicewa da kunci da take ciki....

Iska ta furzar tana yamutsa gashin kanta wanda bashi da yawan kirki, afili ta furta


" ko meke faruwa yau kusan sati daya kenan wayarsa bata shiga?"...



"Jameela! Jameela!! Jameela!!!"

Cikin sauri ta fito jin muryan abbuh, dakinsa ta shiga ta durkusa gabansa


"abbuh gani"


"jameela ya maganar mu ta zuwan yaronan?"


"eh... umm.. Abbuh yayi tafiya ne yace idan ya dawo zai zo". ta fada cikin Duburbucewa




" Wanna shine dama na karshe dazan baki karki sake kowa min wani excuse"


" toh abbuh"


" tashi kije Allah ya miki albarka"


" da ameen"


ta amsa kana ta fito tana tunanin ko mai dalilin kashe wayarsa?...





"Diyar albarka har yanzu wayarsa bata shiga? "



"Mami wallahi bata shiga, na shiga uku"

shiru itama mami tayi fuskarta na bayyana damuwa, domin tunda suka hadu da jameela suka cin dadinsa son ransu, amma yau sati daya ko kazar babu bare aje ga sauran kayan kwadayi...


Cikin son kwantar wa jameela hankali tace

"Ki yi a hankali so kike alhaji yaji ki?"


Tafada tana jujjuyawa, kana taja jameelan dakinta....

"ki kwantar da hankali yar albarka, kilama wayarsa aka sace, ko kuma yana kasar masu jajayen kunnuwa"


ajiyar zuciya tasauke domin maganar mami ya dan sanyayawa mata xuciya, mikewa mami tayi tace

"yar albarka nace ko zaki dan wanke min kwanunka nan na dora girki?"

Tafada tana dan murmurshi...


"gaskiya mami bazan iya ba, da wanne zanji dan Allah"
yafada tana yamutsa fuska


" toh, yi zamanki bari nayi"
cewar mami bata ko damu da rashin ladabin a maganar jameelan ba


"Yawwa yar albarka ya zancan kudin nan damu kayi zaki ban?"


" Oohhh mami zan baki anjima amma dubu 20 kawai zan baki, domin sauran kudin xan lallaba har yadawo ya bani wasu"

tace cikin kosawa

"Allah ya miki albarka" mami ta ce cikin murna,
tana fita jameela tace "mami son kudin bala'i ne da ita, ta dauko mai aikin taki, saboda bata son biyansu a hakkkin su"

take tunanin faheemah ne yafado mata a rai amma tayi saurin kawar da shi...



Share

Comment

Vote






Thanks for reading

Noor Eemaan 🥀🌸


💔RAYUWAR FAHEEMAH 💔


_by NoorEemaan_ 📚✍️

kyautane ne (free novel)



Be proud of how you've been handling things pass few months.
The silent battles u have fought, the moment you had to humble your self, the times you've wiped your own tears celebrate your strength💪❤️



35-36

(Not edited)



"Son ya batun komawarka aiki kasan abokin abbanku alhaji Aleeyu na yawan kirana ya tambaye jikinka, kasan baya kasar kusan 2years kenan, haka kuma ya ce idan Allah ya baka lafiya kujerar ka na office na nan"


numfashi ya sauke kana yace "ummu da nayi tunanin barin aikin banki, nayi focusing akan company's dinmu".

"No son! Wanna bazai hana ka aiki ba, and besides amintattun da anwar ya dauka suna kula da company's din, aikinsu na tafiya yadda ya dace, and akwai office dinka na musamman a company Wanda yake jirinka tun kana jinya, hoping that I day zaka warke , and gashi alhamdulillah kana zaune kan kafafunka, so idan kana free zaka iya zuwa domin kula da wasu abubuwan"


" ok ummunah" ya fada cikin kaunar mahaifiyar sa



ATM card ta miko masa tace "gashi wannan naka kason ne daga cikin riban company, wanda da gadonmu duka na fara shi, na kuma sanar da kai duk da lokacin baka magana, but am sure kaji lokacin da na sanar da kai fara bussiness din"



jinjina kai yayi alamun ya tuna lokacin data sanar dashi,
"toh wanna naka ne na tara maka asusun banki ka, yanzu kudin yakai million 15"



Hawaye ne suka ciko rikitatun idanunsa, ya zama speechless duk da shekaransa 7 kwance amma still ummunsa na tara masa kudi...

rugumeta yayi cikin husky voice dinsa yace


" thank You so much Ummunah Allah ya biyaki da gidan aljanna"

da "ameen" ta amsa cikin kaunar yaronta tana shafa kansa!



"Amma ummu kudin sunyimin yawa fa bana bukatar su matukar ina da ku".


Murmushi mai sauti ummu tayi kana tace, "kana bukatar su son, have u forgotting u have a wife now? So spend the hell out of the money for my daughter tunda kai baka so"

tarasa azolaye, dariya kawai yayi, "ni kam son ina diyata? Tun dazu ban ji motsinta ba"

"Na baro ta tana gyara wardrobe dinta ne" ya amsa mata.



" madallah! son ka riketa amana, nabaka amanar Faheemah ka kula da ita domin tana bukatar farinciki hadi da kulawa"


" in sha Allahu ummu" ya amsa cikin girmamawa...

"So... yaushe zaka fara zuwa bank din?"



"On Monday ya amsa a takaice!"


"Alright son Allah ya taimaka"


"zan kira alhaji aleeyu nasanar dashi, yakamata ka samo waya ko dan wasu abubuwan"

Shi kam duk wani abu na more rayuwa ta fice aransa ko dan ya jima baya amfanin dasu ne oho! yafada aransa...

afili kuwa yace, "zan siya idan na fita ranar monday"

sumba tar ta a kumatu yayi kana yafice a falon...

Zaune ya tarar da ita kan sallaya yayinda take gyara kyakyawan farcenta.


Sallama yayi ta amsa asanyaye tana jin bugun zuciyarta na karuwa, kura Mata ido yayi yana jin wani Abu mai girma atare da ita saidai bansan meye wanna abun ba. Ajiyar zuciya ya sauke kana ya shiga takowa zuwa gareta.


Ganin tsayayyun kafafunsa dab ta ita ne yasa ta tsaya da abunda take, ta kasa dago ido balle ta kalleshi, kodai wani Abu yake bukata ne tafada aranta? Cikin sanyi da kuma zazzakar muryan ta dake rawa tace


"ya...fu...ad...ka... ka... na... Son wa..ni.. Abu ne?"

Tafada tana murza zobenta, shiru yayi bai bata amsa ba domin har ransa baya jin dadin yanda take takurewa agaban sa, tana nuna alamun tsoro hadi da rikicewa, Wanda a lokacin da yake jinya bata hakan,


" what do I do now"

yafada cikin rashin sanin abun da yadace yayi domin yaga tana sakewa dashi. Jin shiru yasa ta dago idanunta dake cike da mayen kaunar sa ta sauke su anasa, ganin ita yake kallo yasa ta Saurin yin kasa da kanta, rage tsahonsa yayi sosai ta yanda har yana ganin full face dinta, cikin " voice dinsa dake rikita yammata yace

" faheeee"


shiru babu amsa yayinda kwalla suka cika idanunta batasan meyasa rauninta ke karuwa aduk sanda take tare da shi .


"Faheeee look me eye ball to eye ball"


ya umarceta, ahankali ta dago kanta ta kallesa wanda yayi daidai da saukar hawayenta.

runtse idanunsa yayi kana ya furta



"Ya rahman help me "

Ya fada kasa kasa hadi cije cute lips dinsa na kasa.



Tallafe fuskarta yayi cikin tattausan hannayensa kana ya shiga rarraba rikatattun idanunsa akanta, Faheemah kuwa wani Abu taji yana yawa ajikinta sakamakon jin soft palm dinsa a fuskarta.



Hawayenta ya share mata kana yace

"open your eyes"

a hankali ta shiga bude beautiful eyes dinta dake cike da kwalla.

"What is your problem? "


cikin cool voice tace " ba... bu...komi"


"Ohhh! kukan dadi yake miki?"

Ya tambaya yana dage girarsa daya!



Girgixa kai tayi domin hatta magana nauyi yake mata matukar yana kusa da ita haka.

Bai kuma cewa komai ba ya karbi nail-cutter din hannunta. Kafarta ya daura akan cinyarsa ya shiga gyara mata farcen. kura masa ido tayi tana kallon kyakyawar fuskarsa yayinda kusancinsu yasa take shakar dadaddan kamshina turaren sa na *love in oud* lumshe ido tayi tana sake bude yan kofofin hancinta. Dan kankare mata farcen yayi wanda yasa tafara musu musu da kafarka, batare da ya dago ba yace

"will stop that, so kike na yanke ki? "

nutsuwa tayi ya cigaba, ganin ta kasa jurewa yasa tasaki dariya sosai tana janye kafarta

"cak! Ya tsaya daga abunda yake, Anya yarinyar nan tana da lafiya? "

What is the laughing all about?"

Yafada calmly yana kallon ta


"wallahi ya fu'ad cakuli-kuli kake min a kafa"
tafada cikin tsantsar sakalci hadi da shagwaba.

A ransa yace "Yarinta na damun yarinyar nan, but i like it"

A fili kuwa yayi Murmushi, batare da yace komai ba ya mike zuwa toilet...



*Monday morning (safiyar litinin)*

_7:00am_.


Daga yanda ruwa ke diga a gashinsa zuwa jikinsa zai tabattar da maka da wanka ya fito. tsadadiyyar lotion din cetaphil ya shiga shafawa afresh dinsa, wardrobe dinsa zai bude domin dauka kayansa, idanunsa suka sauka kan wani suit mai kalan baki sai ta ciki daya kasance white da tsadaddan agogansa rolex, Suna ajiye agefen bed, jin yana kokarin yin tuntube da abu yasashi kai idanunsa kasa, black cover shoe hadi da black socks ne akasan. Murmushi mai sauti Yayi domin hakan ya masa dadi, " smart girl "yafada aransa domin duk da komai cikin sanyin take yinsa amma tana da sanin ya kamata.
Yayi matukar yin kyau cikin suit din yayinda kamshin sa ya cika dakin, Jakarsa ta ratayewa ya dauka wanda tun jiya ya hada important abubuwansa aciki...

Plantain mosa, tomato omelette, sai ruwan tea ta hada masa.
Fitowarta daga kitchen yayi daidai da fitowansa.

durkusa tayi tare da gaishesa "barka da safiya ya fu'ad"


cikin tafiyar kasaitarsa ya karosa gareta hadi da mike mata hannunsa, fahimtar abunda yake nufi yasa ta sanya hannunta cikin nasa, mikar da ita yayi kana cikin muryan rada yace " bana son irin wanna gaisuwar kin tashi lafiya ?" Ya dan manna ta da gefen k'irjin sa



"alhamdulillah "

ta amsa atakaice sakinta Yayi kana ya raba ta gefenta zai wuce...


"ya fu'ad ga breakfast dinka fa"


cak! ya tsaya, ya riga da yayi latti amma dole ya ci , domin baya so ko Kadan ta masa Kallon mara adalci ko wani abu. Zama yayi a dinning table ta shiga serving dinsa,

"Black tea ya isa karki sa milk"

da toh ta amsa , bayan ta gama, tana kokarin barin dinning area yace ta zauna, babu musu ta zauna. Cin abunci yake da dan sauri-sauri saboda ganin time ya kure bayan ya gama ya goge bakinsa da tissue kana ya rankafo kanta daidai kunnenta ya furta

" tnx Allah ya miki albarka "


lumshe ido tayi jin husky voice dinsa, domin sosai ya ratsa jikinta,

"ameen"

ta amsa cikin jin dadi domin tana matukar so a shi mata albarka. Cikin sauri ya fice bayan yace mata

"take care"

Mikewa tayi ta koma kitchen domin so take tayi breakfast dinsu da kanta a yau. Idan kuma tace zata hada tayi duka ba lallai bane ta gama kafin ya fu'ad ya tafi shiyasa tayi nasa daban...




Ahankali ya fito da kafarsa daya daga cikin motar yana karewa haraban bankin kallo, komai yana nan yanda ya bari sai dan canji da ba'a rasa ba. Shigarasa cikin bankin yayi daidai da lokacin da ma'aikatan bank din suka watso masa jajayen flowers masu matukar kyau, kana cikin hadin baki suka shiga rera mai wata waka ta turanci mai taken *welcome back*
murmushi farinciki yasaki ganin daga tsofafin staff har zuwa sababbi da basu san shi ba sun nuna farinciki su da dawowarsa. Bayan sun kai karshen wakar ya nuna Godiyar sa hadi da farinciiki sa, kasancewar safiya ce babu customers sosai yasa shi bin al'ameen zuwa office dinsa *( al'ameen abokin aikinsa ne domin lokacin yana jinya yana matukar kokarin zuwa duba shi)* hira suka dan taba kana ya fice zuwa office dinsa.......



Komai na nan yanda yake amma yanzu ya fi kyau domin an kara kawato office dinsa gwanin kyau haka kuma kana shigowa zaka ga akwai cikakan sunan shi da aka rubuta da manyan baki ajikin wani karamin board mai matukar kyau dake ta sheki yana ajiye akan table din, ya kuma san aikin alh aleeyu ne, duk da baya kasar, aransa yana mamakin kaunar da alhajin ya ke masa.



Nocking yaji ana yi a kofar office din,hakan yasa ya bada umarnin shigowa "yes! Come in" wani matashin saurayi ne ya shigo wanna a kalla zai girmewa fu'ad da shekara biyu haka.


"Gud morning"


"morning"

fu'ad ya amsa.

" I guess you are fu'ad omar ishaq right?"

Jin jina kai fu'ad yayi kana yace

"yeah i am"


"Good"

James yafada kana yace

"my name is James jonathan, Iam the one taking over since you left, i have heard alot about you, most especially your hard working, so welcome back and nice meeting you"



murmushi fu'ad yayi kana yace


"Thank you so much, nice meeting you too"


" you are welcome" James ya amsa, kana yace


" can we be friends "?

Shiru fu'ad domin baya son tarin abokai amma wulakanci baya cikin halinsa hakan yasa yace

" of course yes"

cikin farinciki James ya mika masa hannu suka yi musaba'a kana ya shiga nuna wa fu'ad inda ya tsaya a aikin kana ya mai sallama domin komawa office din da'aka mayar dashi....



Aikinsa ya shiga yi cike da kwarewa, saidai abin mamaki kyakyawar fuskarta kadai ke yi masa gizo, da kyar ya'yakice tunanin ta ya cigaba da aikinsa...




4:00am daidai ya tashi, yazo sauka ya hadu da salma dake bangaren customer care.


" Wow! My fu'ad ya dawo, daman ina ta sauri inzo kafin ka tashi, da safe ne banzo da wuri ba, aiki ya sha min kai, gsky nayi farinciki da dawowarka ga kuma kai tsaye kan kafafunka, u look handsome kamar baka yi jinya ba fatarka sai sheki take"

tafada tana kokarin rike ahannunsa, bata rai yayi yana janye Hannunsa, aransa yana jinjina rashin kunyar salma, lokacin da yake a halin jinya karara ta nuna kyama agaresa, duk da alokacin baya magana amma yana ganin yanayin kowa kuma yana ji.

"Wanna kyakyawar yanayin da kike gani atare dani ya samo asali ne daga jarumar uwa da kuma mata ta gari".

Ya amsa mata a taikace! dariya tayi batareda ta bawa maganarsa ta karshe muhimmanci ba.



"Fu'ad yakamata mu fahimci juna kasan ina Sonka"

murmushi gefen baki Yayi kana yace

" abun inyi amai gaskiya bazan iya zama in shaki wari ba" *( abunda salma tace kenan lokacin data zo gidan su fu'ad yana jinya, yayi bahaya, sosai ta nuna kyamar ta a fili daga wanna ranar bata Kara zuwa ba, haka zalika bata taɓa kawowa zai samu lafiya ba da bata yi maganar ba)*

" kin tuna?"


ya tambaye ta "haba fu'ad is not what you think"


"Oh really! yafada yana dage girarsa daya, kana yace "excuse me please I have important things to do"

ya raba ta gefenta ya wuce. Yana jiyo ta tana fadin

"Kai nawa ni kadai fu'ad dole in mallake ka bazan taba barin wanna cikakken namiji ya subucemin ba"

tafada tana raka fu'ad da ido.

Wurin atm dake jikin bankin ya shiga, kudi masu yawa gaske ya ciro kana ya tashi motarsa ya bata wuta...







Hadadiyyar wurin siyarda waya ya faka motarsa, tsad'add'un wayoyi ya siya wandan'da kudin ko wanne zai kai dubu dari biyar, kana ya siyawa malam iro infinix smart 5 domin zai fi masa saukin sarrafawa, domin lokacin da ummu ta sanar dashi shi ya biya masa sadakinsa sosai darajarsa ta karu idanunsa.
Kusa da shagon akwai inda ake register layin ko wani waya sai da ya siya masa sim biyu.


Horn ya danna cikin kankani lokaci malam iro ya bude masa yalwataccen gate din, danna hancin motarsa Yayi ciki, bayan ya daidaita parking, kana cikin tafiyar kasaitar sa ya karaso wurin malam iro, gaisawa sukayi kana ya miko masa tasa ledar dake dauke da tambarin wurin, sosai malam iro yayi farinciki wanna har ya bayyana asaman fuskarsa, addu'a hadi da albarka ya shiga shiwa Fu'ad domin daman wayar matarsa ta lalace yana son canza mata wata, amma yanzu zai bata nashi ya rike sabon

"kada kadamu malam iro, nagode nima da alkhairi gareni Allah ya saka da alkhairi"



"Babu komai, Ameen alhaji karami"

cikin jindadi malam iro ya fadi haka, domin yana matukar darajan yan gidan duk da tarin dukiyarsu amma basa wulakanci haka nan komai kankantar kyauta basa rainashi duk da sunfi karfinsa.



"Assalama alaikum"

muryansa ya karade ila irin parlor'n yayinda ummu da fareesa suka amsa masa.


"Sannu da zuwa brother" fareesa tafada tana bashi side hug kana ta karbi ledan hannunsa .

"Yawwa little sister, how was ur day"?

" Alhamdulillah big bro"


" Ummunah barka da yamma"

ya fada yana dora kansa acinyarta shafa kansa tayi kana ta amsa cikin son danta.



"Mikomin Ledar nan"



ya umarci fareesa, ummu yafara mikawa murna tayi kana ta kwararo masa add'ua ya amsa cikin jin dadi.




Na fareesa ya ciro ya mika mata, ai sosai ta saki ihun murna wanna har faheemah dake daki ta fito a tsorace domin ta dauka wani abun ne yasameta.



Ganin shi Zaune yasa ta koma dakin cikin sauri.




"Son ya kamata ku koma part dinku, nasa an gyara komai duk da kusan kullum ana gyara wa, kasanar da diyata domin ta sani da komawarku"

" Toh ummu Allah ya kara girma" da Ameen ta amsa.

" brother na akwai fa pics dinku dana yimuku da sallar wallahi Yayi kyau sosai xan tura maka" fareesah ta fada cikin farinciki samun sabuwar waya daya ki boyuwa a fuskarta

"ok kanwaty bari nayi chajin waya" yafada .


Tana zaune bisa gadon ya shigo, mikewa tayi ta karbi Jakarsa kana ta mai Sannu da xuwa, cikin sakewa ya amsa, Lemo hadi da ruwa ta dauko masa ya kuwa sha sosai domin daman yana tare da kishirwa.


kwallin wayan ya miko mata, amsa tayi fuskarta da alamun tambaya domin ita har ga Allah bata san ta ta bace

"It's yours" ya amsa a takaice

"me?"

ta ce cikin zaro ido, jinjina kai Yayi alamun tabattar wa.



Duk da bata ga amfanin rike waya ba a gareta ba, amma bata jin zata ki amsar kyautar sa, kuma bazai ji dadi na ba idan tace bata so tunda ya riga ya siyo.
Kokarin durkusa take domin yi masa godiya Yayi Saurin rike mata hannu hadi da girgiza mata kai alamun bayason hakan, xaunawa tayi kusa dashi kana cikin Sanyaya da kuma zazzakar murya tace

"ya Fu'ad Allah ya raba da iyayen ka lafiya,
Nagode sosai Allah ya saka maka da aljanna madaukakiya"

Jin saukar voice dinta a kunnensa yasa shi lumshe ido Kana ya ware cute light pink lips dinsa ya amsa da


" Ameen ya Allah"


ya amsa domin yaji dadin add'uar har ransa


Caji ya jona musu bayan ya saka musu layukan.




https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time
electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851

Comment
Vote
Share


Thanks for reading
Nooreemaan🥀🌸

💔RAYUWAR FAHEEMAH 💔(
_by Noor_📚✍️


kyauta ne( free novel)




you can talk
You can breathe
You can walk
You can see
You can feel
You can hear
NOW SAY ALHAMDULILLAH 💖


(Not edited)


37-38.





Misali

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment