Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Ita kuwa mezatayi da waya yanzu? Babu wanda zata kira babu mai kiranta bata ga amfanin rike waya ba yanzu, kallon muradin ranta alone yana rage kaso 60% na damuwarta. Cikin sanyin muryan tace

" Allah ya kara girma da arziki ummu amma... a yanzu bana bukatar waya" tafada cikin girmama wa surukar ta.



Itama ummu bata sake cewa komai ba, ganin hawaye sun ciko idanunta kuma baya rasa nasaba da tunanin yan gidansu ko tace abbuh'nta, yasa tace

" Toh diyata ba damuwa, amma duk lokacin da kike bukata ki sanar dani, am your mother not your mother in-law okay ?"

Cikin matsananci kaunar ummu ta amsa mata

" yes ummu".


"Bari nadan kwanta diyata"

" toh ummu afito lafiya"

" Allah ya yasa"


Bayan shigar ummu itama ta mike zuwa dakinsu, yana kwance kamar kullum fresh skin dinsa sai glowing yake kai baka ce majinyaci bane.


Kura masa ido tayi tana jin kaunar sa mai xafi na ratsa jini, tsoka, jijiya, da hadi da bargonta. Kasa kasa tace,, " ya Allah kasa yanda nake kaunar wanna bawan naka, Allah kasa yana jina aransa shima" tafada tana daga manyan farare idanunta sama.


Numfashi tasauke kana cikin takun nutsuwarta ta haye gadon, " ya fu'ad Allah ya baka lafiya, am eager to see you on your feet "
tafada tana shafa lallausan farin kafarsa tamkar ta jarirai.



★★★



"Hello"

"Parrot baki iya sallama ba?"

"Assalama alaikum"


"Wa'alaikumu salam"


"Good girl" yau ba rashin kunya kenan?

" Kai! Ya anwar ni bana rashin kunya, gashi kuwa kinyi kina turo min bakin rashin kunyan yanzu"


Kunya ce ta kamata wato yama san tana turo bakinta, abangaren anwar kuwa canka kawai yayi domin yasan zatayi hakan, sanyayar ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin gwara ya sanar da ita abinda ke ransa ko ya samu kwanciyar hankali. Ada yana tunanin idan ya sanar da ita zata rainashi tunda amatsayin kanwa ya dauketa, amma yanzu baida mafita daya wuce ya sanar da ita saboda kada yana kallo wani yazo ya mai shigar sauri.


"Jibi zanzo gidan akwai magana mai muhimmanci dazamuyi dake"


"Dani kuma ya anwar, Allah yasa lafiya?"

ta fada heart dinta na beating da sauri.

"Lafiyar ce ta kawo hakan yafada yana bata rai, shi Allah dole babban yaya.



"Toh Allah ya kaimu, da ameen ya amsa kana ya katse kiran"


"Mutum sai son girman" cewar fareesa kai kace da shine agabanta.

" ikon Allah duniyar nan gudu take wallahi, wai azumi ramadan Saura kwana biyar"

Cewar ummu dake Zaune a hadadiyar gadon ta yayinda faheemah ke jera mata kaya a wardrobe tace,

" hakane ummu Allah yasa mucika da kyakyawar karshe"


" ameen diyata,
Sannan gobe fareesa zata je yimuku shopping din kayan sallar, akai dinki da wuri"

Asanyaye ta juyo tace, "Allah ya kara arziki ummu, da ameen ummu ta amsa cikin kulawa".



★★★★


Ayau duban al'umman musluman duniya suka tashi da azumin abakinsu, ko ina yayi shiru mutane sai ahada-ahadar su suke yayinda duk inda ka shiga karatun qur'an hadi da wa'azizika ke tashi gwanin sha'awa da burgewa.



Bayan ta shiryar shi kamar kullum, ta shafa masa zam-zam adukkanin jikinsa, fita tayi domin dauko masa Kunun sa data dama aflask tun asuba, sanin cewa baya azumi saboda lalurarsa...
Saidai abun mamaki idan ta zuba masa abaki gaba daya sai su zubo ajikinsa, baya amsa ya sha kamar kullum, abun ya daure mata kai, kodai baiyi masa dadi ba ne? Tasake gwadawa akaro na hudu amma still baya sha, bama ya son bude Bakin kwata kwata ga wani da yake mata data kasa fassara yanayinsa, domin ba irin kallon da ya saba mata bane, asanyaye tace "Bakin ka yana ciwo? Ko bakason wanna? Tafada tana nuna kofin Kunun shinkafa daya ji madara, toh mikakeso? Kafada min kaji my fufu please" har hawaye na ciko idanunta duk ta shiga damuwa sai magana takeyi masa da alama ma ta manta baya magana, cikin sauri ta fita domin zuwa sanar da ummu.


"Ummu na bashi abincinsa yaki sha, muje kimasa magana" tafada tana kamo hannun ummu hadi da share hawaye da dayan hannu. Murmushi ummu tayi kana ta zaunar da ita kusa da ita



"Diyata faheemah haka mijinki yake, tunda ya fara wanna lalurar idan ramadan yazo baya amsar abinci har sai yaga alamun an sha ruwa, nima lokacin dana fara ganin nayi mamaki na kuma shiga damuwa na gwada bashi yaki amsa kamar yadda kika yi, amma kinsan ikon Allah ana shan ruwa nabashi ya budi baki ya karba, dana ga haka sai na dinga bashi abincinsa da sahur, saboda haka ki kwantar da hankalinki"


Jinjina ikon Allah faheemah tayi, aranta kuwa


"tace da alama lokacin yana da lafiya baya wasa da ibada. Kwarai kuwa son baya wasa da ibada, domin idan yana gidan nan sai ya tabattar yatashi kowa salla musamman na asuba wanna dabi'ar ta mahaifinsa ya dauko"


Kasa faheemah tayi da kanta domin batasan maganarta ta fito fili ba. Azolaye fareesa dake kwance flat akujerar 3sitter tace



"ummu bakiyi gaya mata cewar brother na nada miskilanci wani zubin ba. Karki damu matar bro zan samu time nagaya miki duk halin mijinki amma ki bari a sha ruwa tukunna"



"Yimin shiru malalaciya, jibi this is just 11:00am amma kin wani kwanta. Anya kuwa fareesa? Rayuwar aurenki da kallo"


"Allah ummunah ban cika cikina da sosai da sahur ba kuma azumin farko yafi bada wahala"


"Ai nan kika fi kauri acici, ki shirya karfe 4:00 dot xamu shiga kitchen yau har da ke"

wayyo! ummu ki taimaka mun dan Allah wallahi saidai ku kwashi gawata amma ba zan iya ba"

Fashewa da dariya faheemah tay,i tana mamakin rashin son girki irina fareesa, itama ummu duk yanda takai da matse dariyar ta saida ya fito domin yanda fareesa tayi fuska dole kayi dariya.


kiran wayar fareesa ne ya katse musu hiransu, mikewa tayi zuwa dakinta, yayinda

Faheemah itama ta mike domin kusa canza masa riga tunda wancan ya bace da kunu.

"Assalama alaikum ina kwana ya anwar"
Lumshe ido yayi kana yace

" lafiya lau my love, ya ibada? "

Gabanta ne ya fadi *my love* ta maimaita aranta kodai ya anwar Yayi mistake wurin kira ne?
Murmushi mai sauti yayi domin ya fahimci ta shiga rudani,

"am bansamu zuwa ba shekaran jiya saboda abubuwan sun sha min kai amma zanzo da yamma may be agidan ummunah zan sha ruwa, karki shiga rudani, zan sanar dake komai later, I love you my parrot" kit taji katse kiran
kasa motsi tayi

Anya ya anwar yana cikin tunanin sa kuwa? Tafada abayyane. Sai kuma ta tabe baki tace koma menene dai zan ji anjima ai.



*FAHEEMAH*


"Am sorry my fufu bansan cewa kadau azumi ba, zan dinga baka sahur kullum kaiji" tafada cikin tausayinsa tana kokarin cire masa riga domin canza masa wata.



*Bayan ansha ruwa*


"Barka da zuwa, an sha ruwa lafiya?

"yawwa alhamdulillah , kin sha ruwa lafiya my love?" Shiru tayi kanta akasa, ya sake cewa "Ashe my parrot akwai kunya haka?"



Gyara tsayuwarsa yayi jikin farar motarsa kirar 4matic yace cikin serious tune " I know kin yi mamaki canjin da kika samu daga gareni ko? Musamman sunan dana canza miki. Hakika wanna sunan na dade ina son kiran ki dashi domin shi ya dace dake! Fareesa Inasonki, tun ranar farko dana zo gidanan, toh a wanna ranar na kamu da kaunar ki, please ki ce kina sona my love"




Ai fareesa shiru tayi kamar ruwa ya ciyenta, "kin yi shiru ko bansamu kar buwa bane? Rufe fuskarta tayi kana cikin kunya, kara maimaitawa tambayar yayi, " kinasona fareesa?"



Waye zai ki namiji kamar ya anwar, Daga kanta tayi alamar "eh" kana ta ruga cikin gidan. Dariya yayi kana ya shiga motarsa yana jinshi sakayau domin ya amayar da abinda yake ransa...




Faheemah tayi ibadaarta sai fatan Allahu ya amsa, domin sallar tarawi, tahajjudd, karatun Qur'ani da duk wani aikin alkhairi/ lada bata yin wasa dasu a wanna watan mai daraja ba domin sau daya tak yake zuwa ashekara, wasu ma sun mutu kafin azumi ko cikin azumi, toh tunda Ita Allah ya barta da rai da lafiyarta, meya cancanci tayi idan bata bauta masa ba? Ta kuma yi addu'a sosai wa mijinta, abbuhnta, sai umminta d kullum sai ta tuna ta, sai kuma ta yiwa al'umman muslimai...


Gobe take sallah, mafi yawan gidaje idan ka shiga kamshi ke tashi, hakan take gidansu ummu aikin suke har da Fareesa da batason girki tun tana kumburo baki har ta saki jiki, aka cigaba da aikin cikin farinciki domin larai mai aiki nabasu labarin ban dariya, sai 11:50 suka tafi makwancinsu cike da gajiya.....




*RANAR SALLAH*


Washegari kowa kagani sanya yake da sabuwar kaya gwanin kyau, yayinda faheemah ke sanye cikin shadda mai kalar pink anyi mata dinki doguwar riga yayinda paint- work din ya kasance baki. Sosai tayi kyau ga daurin ta mai step -step daya kara fito da kyaun fuskarta!

" Wow matar bro kin ganki kuwa? Gaskiya kinyi kyau sosai muje namiki hoto da brother"

ta ja hannun Faheemah, murmushi ummu dake zaune itama cikin adon tsadadiyyar atamfa tayi, kana tace

"kiyi kizo kikai wa Hindu nata abincin"

"ummu Allah da nice bazan basu ba, mutanen da ba suda mutunci"


" kul! karna kara jin wanna maganar, nasha gaya miki rama alkhairi da mugunta sai kiga Allah ya dauka ka ki, ba gashi Allah ya bashi mata mai kyakyawar zuciya wacce bamu taba zato ba"

Murmushi tayi kana tace

"hakane kiyi hakuri"

ita kuwa Faheemah bata gane kan zancansu ba, haka tabi bayan fareesa dake jan hannunta...


Kwance yake shima sanye da tsadadiyyar yadi black color mara nauyi, yayi kyau sosai hasken sa ya sake bayyana


"zauna kusa dashi matar brother"

zama tayi akunyace, nan faressa ta shiga daukansu style kala kala, har da cewa ta kwanta kusa da shi ta dora kanta kan kirjinshi, hakan kuma sai ya bada style mai kyau domin sosai hotunan suka yi kyau.
Bayan ta gama ne tace

"bari nace my anwar yana jirana awajen shi zai kaini".

Jinjina kai faheemah tayi tana Mamakin soyaayar su, wanda bata buyo, tun ummu ma bata gane ba, har ta fahimta yanzu, Murmushi tayi tana kallon Fu'ad aranta tana add'uar Allah yasa ya sota kamar yadda ta mace akaunar sa....



"Hello honey"

"Yeah baby"

"Ina kofar gida fa kindai shirya ko? "

"Eh ganinan zuwa" ta fada tana sauke wayar daga kunnen ta.

"Mami ni na wuce sai nadawo, idan abbuh ya tambayani kice ke kika aikine"

" ai dole in gaya masa haka idan ba haka ai mun shiga uku agidan nan sai kin dawo"

cewar mami daketa wanke kwanunkan dasuka bata, zuwa yanzu mami na gasuwa da aiki sosai, domin dazata ga faheemah babu abinda zai sa bazata dawo da ita gidannan ta cigaba da aikin bauta acewar mami, domin azumin nan daya kare jiya taji jiki ba kadan ba, aiki yayi mata yawa batasan muhimmacin faheemah ba sai a wanna tsakanin. Duk da a ranta bata so ta yarda cewa faheemah nada muhimmanci garesu.


"Wow! honey gaskiya kin gama haduwa"

ya fada yana bin surarta da kallo cikin matsatssen fitted gown din jikinta , shiga motar tayi tana fari da ido cikin jin dadi tace
"thank you baby".

*Blue stars hotel*

Shine sunan da jameela tagani arubuce baro baro ajikin hotel din, parking yayi, kana ya riko hannunta suka shiga ciki, key ya amsa a reception kana suka nufi daki mai lamba 225.



"Haba honey me kike haka kamar ba wayayya ba? Idan kika bani hadin kai zan miki kyautar ban girma please ki amince".

Jin abinda yace yasa ta daina zallewa ta tsaya cak! Murmushin samun nasara yayi kana ya shiga kissing dinta hadi da zuge zip dinta, ganin surarta afili yakara dimautashi....



*Bayan 2hrs*
Kuka take wanda bana rasa darajarta bane.
Kuma take wanda bana rasa budurcinta bane.
Kuma take saboda zafin datake jin kasanta namata.


"Am sorry honey, please
kidaina kuka" yafada cikin muryan yaudara meke damunki yanzu? gaya mun pls

"nan kemun zafi "
tafada tana nuna masa

" ooh sorry bari na hada miki ruwa mai zafi okay " wanka yayi kana ya hada mata ruwan zafi. Bayan sun kimtsa suka fito daga dakin hotel din.


*( Hakika zina babban zunubine, zinah babban masiface ga mai yinta, amma awanna zamanin na yanzu wasu sun dauketa matsayin ado da wayewa, hattara garemu yanmmata, harma da masu aure da zaurawa. Ya Allah ka tsare mana imaninmu daga fadawa halaka, ya Allah ya shirya masu yin zina da duk wani aikin haramun, Allah kasa muyi kyakyawar karshe Ameen thumma ameen.)*

Bayan ya kawota layin, daga dan nesa da gidan yace


"Honey ga kyautar ki "
Yafada yana miko nata bandir din yan dubu dubu guda uku, hadi da galleliyar waya wacce kudinta zai kai 500k, abun mamaki sai ta amsa cikin farinciki har da sumbatar shi a labba, a Jakarta ta sanya, kana tace


"Toh yaushe zakazo kaga abbuh? Sosa keya yayi kana yace ranar juma'a"

Cikin farinciki ta fita amotar bayan ya tsake lallatsa ta.


Da abbuh taci karo asoro, gabanta ya bada ras!


"Jameela ina maganar mu ta ran nan?"

a duburbuce tace "yace zai zo ranar juma'a"

" Allah ya nuna mana abbuh yace yana fita daga gidan".


"Diyar albarka wai ya naga kina yamutsa fuska, na ga kuma kun dawo da wuri?"...



Babu kunya jameela tace "mami fitan da muka yi salman ya kusanceni fa"

tafada kai tsaye ko dar bata ji ba.


Dafe kirji mami tayi cikin tashin ahankali tace "nashiga tara ni hajara, idan kika samu juna biyu fa?" (Allah yasa mudace, wato mami ta juna biyu take bata ta rasa budurcinta)
kudin daya bata hadi da wayar ta zaro domin ta haka ne zata rufa wa mamin baki...

" wanna kudin fa? "..

"Shi ya bani yanzu"


ai rudewa tayi nan da nan fuskarta ya wadatu da fara'a, cikin lallabawa tace "amma yar albarka kada ki bari ya sake kusantarki saboda kada ki samu ciki"

cewar mami cikin lallama.

"toh naji"

jameela ta fada tana dora mata bandir daya a cinyarta, ai sake rudewa mami tayi cikin farinciki tace

"duka na wane wannan?"


Jameelah bata amsa mata ba, sai ma cewa tayi "Bari na kwanta mami".


"Toh toh yar albarka , bazaki kiyi wanka da ruwan zafi ba, Bari na dora miki ko?".



"A'a mami Idan na tashi zanyi"

tafada tana yamutsa fuska.


"Toh afito lafiya diyar albarka" cewar mami tana ta juya kudin hannunta cikin farinciki, a ranta kuwa addu'a take Allah ya tabattar da auren jameela dana salman din, domin irin mijin da takeso kuma take fata wa yar ta kenan...



Share
Comment
Vote


Thanks for reading


Noor eemaan🥀🌸
07082281566



💔RAYUWAR FAHEEMAH 💔

_by Noor Eemaan_

kyauta ne (free novel)


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


*TRUST* takes years to build, easy to break and forever to repair.



31-32

(Not edited)


*3weeks later*

faheemah ce ta fito daga toilet bayan ta wanke masa inners din sa hadi da shanyawa , yarfa hannunta mai dauke da danshin ruwa tayi, kana ta taba diaper dinshi, ta ji shi a jike, mamaki ya kamata domin yau nan da nan sai ta ga ya jike, cikin kunya da har yanzu bai sake ta ba ta shiga zare masa idanunta a gefe, domin dauriya take sosai, amma sosai take jin tsoron girman hallitan sa, sanin cewa dole ta canza ya sa ta shiga canza masa sabo, sai dai a yau din jikinsa bai saki kamar kullum ba, amma bata kowa komai ranta ba.

Bayan ta gama canza masa, kana ta sumbaci goshinsa, sau ta dauki mayafi domin zuwa sanar da ummu ruwan zam- zam din ya kare saboda ragowan ta shafa masa a safiyar yau....




*Babu abunda ya gagari Allah*

cikin buwayar Allah da hikimarsa yaji hannunsa na dama ya motsa, cikin madaukakiyar mamaki yaga na hagun ma ya motsa, dakyar ya daga Hannunsa na dama wanda suka masa nauyi ainun domin shekarun daya diba akwance ba wasa bane, shafa kyakyawar fuskarsa yayi da hannu domin tabattar da cewa shi d'in ne ke motsa hannunsa ko kuwa mafarkin daya saba yi ne? Murmushi daya taho da hawaye ya gangaro masa a lokaci daya, wanda rabonsa da wani abu wai shi murmushi shekaru bakwai kenan! Motsa jikinsa yayi ya ga sun motsa, hakama kafafunsa wani murmushi mai hade da dariya yasaki kana cikin murya Kasa kasa ya furta "Allah akbar" jin muryansa akunnensa yasa shi yin murmushi, wanda idan baka sa kunne sosai ba bazaka jiba domin shekaru bakwai yayi bai furta koda kalmar daya ba... Gwada zama yayi ya ganshi zaune daram agadon nasa, wani mamakin ne yasake kamasa ganin komai yake kamar amafarki, ahankali ya sauko da kyakyawan kafafunsa kasa wanda sanyi tiles din ya ratsa kafafunsa, lumshe rikitatun idanunsa masu dauke da zararan gashin ido yayi kana ya ware su hadi da mikewa ahankali domin jin kafafunsa yake babu kwari tamkar ta yaro mai koyon tafiya. Mikewa yayi sai jin yayi abu yayi masa nauyi akasan sa, hannu yasa ya taba adult diaper dinsa ( pampers din manya) kwalla ne suka cika masa amma ya mayar dasauri, cire wandon sa yayi kana yazare diaper din hadi da jifawa a kwando shara dake kusa da toilet kana ya shiga toilet din ya wanke jikinsa hadi fitowa, wardrobe dinsa ya bude ya dauko wani dogon wando mai Kalan fari yashiga zurawa, komai yana yine cikin sanyi domin babu karfi ko daya a jikinsa.
Sujjadul - shukur yayi hadi da kwararawa Allah buwayi gagara misali Kirari Cikin nutsuwa kana ya mike domin zuwa ganin mutane mafi soyuwa aduniyarsa..


*FAHEEMAH* zaune take kusa da ummu bayan ta sanar da ita karewan ruwan zam -zam din, ummu ta bada umarnin a siyo wani.
Fareesa na zaune tana karatu kasancewar tana da jarabawa gobe. Sallaman anwar ne ya katse su, Gaishe da ummu yayi kana su Faheemah suka gaisheshi.


" Ummu yunwa ce ta korani daga office bazan iya kaiwa gida ba"

yafada idanunsa akan dinning table murmushi ummu tayi domin tasan anwar baya wasa da cikinsa ko kadan.

"Ai kuwa yanzu aka gama abincin rana, fareesa kiyi serving dinsa"

"toh ummu ta amsa"


serving dinsa tayi suna sakar wa juna murmushi, sarai ummu ta gansu ta dauke kai....


Kwarewa anwar yayi da loman abinci dake bakinsa, saboda ganin abun

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment