Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, shima yana da niyyan Hakan...




Basket dake hannun sa ya ajiye akan dining table kana ya rufe ko ina, upstairs ya hau domin so yake yayi wanka. Kara sauka yayi cikin shigan fararan kayan bacci masu kyau da taushi dakinta ya nufa bakinsa dauke da sallama...
Jin alamun mutum adakin, yasa ta farka afirgici kana ta takure kanta kai kace dodo ta gani, kallon shi tayi sai kuma ta feshe da Kukan zallan sakalci,



"no! no!! no!!!" please ya shiga maimaitawa kana ya dora



"daga shigowata sai kuka"? Ya fada muryansa da dan bacin rai, domin ya tsani yaji Kukan mace, bare ita mai daraja agareshi.



"Meya faru"? Maimakon tabashi amsa, sai ta sake fashewa dawani sabon kukan.



Cikin tsawa yace "ke! Ya ishe ni haka. What is your problem? Will stop those silly tears ko sai na bata miki rai, Kuka! Kuka!! Kuka!!! Faheeee kullum, kuma sai kin ganin kike kukan, idan nine bakya son zama dashi, ko bakya son ganina then you tell me sai a nemi mafita".




Ya karasa a fadace, sai kuma ya fita adakin saboda baya so yayi loosing temper dinsa...


Faheemah kuwa tun daya fara fada tasa hannu ta rufe Bakinta tana kuka yanda bazai ji ba musamman dataga ransa ya yi matukar baci, ita batasan meyasa rauninta ke fitowa ba, musamman idan ta ganshi ba.


Sai juyi yake akan hadadiyar king size bed dinsa, duk yadda yaso shareta ya kasa, domin ita din amana take taresa bazai iya barinta baya ga haka Ita din rayuwarsa ce baya jin zai iya kyaleta haka. zuro kyakyawan kafafunsa yayi kasa kana ya fice, dinning area ya nufa ya dauki basket din abincin kana ya nufi dakinta. Tana nan zaune yanda ya barta saidai zuwa yanzu ta fara gyangyadi, murmushi dabai shirya ba ta subuce masa, ganin yadda take gyangyadi, gyaran murya yayi, firgigit ta farka, ganinsa yasa ta nutsu domin sosai ta tsorata dazu. Fahimtar Hakan yasa shi ji ba dadi, tabass baya jin dadi yanda take yawan kukan nan musamman Idan ta ganshi, bashi da zabi daya wuce yayi mata fadan ko zata daina, amma ban dan yaso ba.

" Faheeta"

ya kirata atausashe kana ya ware mata karfaffan hannayensa, dago kai tayi ganin ya kirata, kana ta sauko da dugu ta fado jikinsa hadi da sakin siririyar kuka

"ka...ka...yi hakuri dan Allah! Shhhhhh it's ok"

yafada yana shafa bayanta. Ajiyar zuciya ta shiga saukewa wani sanyi dadi na ratsa ta...

"Kinyi wanka?"

Ya tambayeta.

Girgixa kai tayi

"Maza yi Wankan muci abinci ok?"


"Toh"

ta amsa cikin sanyin ta, fita yayi adakin zuwa parlor domin yasan matukar yana nan bazata sake ba.

15 minutes later yadawo, ya ganta ta shirya zuwa baby pink pajamas sosai tayi mata kyau sai ta zura hula fari.

Tana zaune sai wasa take da diamond ring din hannunta ya shigo.


"Sauko"

yace mata yana zama kan hadadiyyar center carpet dake malale agaban gadon. Abincin ya zuba musu a plate daya kana ya zuba hadadiyyar Kazan daya siyo a albaik chicken sai tashin kamshi kawai kake ji, Spoon ya dauka yayi bismillah ya shiga cin fried rice din bakinsa, yayi 3spoon, yaga bata ci ko loma daya ba. Tabbas yana jin zan bi shawaran anwar awata hira dasuka yi,

_*dude sai fa ka jawota jikinka zata saba da kai sosai, kadaina tunanin xata raina ko wani abu, ita din daban take da sauran Matan, nasan ka san da hakan kuma yarinyar nada damuwa idan Bata Samu farinciki daga gareka ba, a Ina zata samu? nasan zaka dinga tunanun lokaci kana jinya tafi sakewa dakai, toh akwai bambamci mai yawa, daga lokacin zuwa yanzu, domin yanzu ganin ka zata dinga yi kamar sabon mutum agareta yanzu, ba yanda ta saba ba da*_



Ajiyar zuciya yayi bayan ya dawo daga tunanin daya tafi, abunci yakai bakinta babu musu ta bude small cute lips dinta ta amsa a kunyace, domin bata son mai musu domin ita kam tana matukar tsoron fada. Sosai suka ci abinci domin dukkansu suna tareda yunwa, haka kuma wanna shine karon farko dasuka ci abinci tare, wanda hakan yayi wa fu'ad dadi kwarai duk da bai furta ba. Fitar da kwaunka tayi kitchen ta wanke su, kana ta koma dakin. Yana nan zaune kamar yadda ta barshi , tazo wucewa ta gefen gado yasa mata kafa, ai Timm kake ji ta fado kansa

"Arhhhhh!!! ta fasa min ciki wayyo ummuna". Yafada yana turo baki irin na shagwabe.

Tsoron da ta jine ya miye gurbin dariya , yanda Yayi dole kayi dariya.


"Ooh dariya kikemin ko?"

Ya sake fada ashagwabe

"am sorry please"
ta fada cikin siririyar sweet voice kana ta hada hannunta alamun roko domin Ita kam bata gane cewa wayo yayi mata ba.


"Ai yarinyar kin jawa kanki, dama nace zan miki hukunci mai tsauri, kin manta?"

Yafada yana daga girarsa daya.

" Wayyon!i ya fuad kayi hakuri na daina Allah bansan laifi na ba".

Tafada hawaye na ciko idanunta, dariya ce take cinsa ganin yadda tayi kalar tausayi, aransa ya furta matsoraciya kawai

Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya domin yanda take mutsu mutsu ajikinsa yasa shi jin wani feelings nataso masa, saidai a fuskarsa bazaka gane hakan ba Saboda tsananin jarumta da dakiyarsa!


Domin bayason ya nemi wani agareta daya sha fi mu'amalar auratyya har sai ta sake dashi sosai, sannan kuma da amincewarta.

"Kaji ya fuad am sorry please kada kamun hukunci mai tsauri"


Murmushi kawai yayi domin yana matukar san ganin alamun tsoro afuskarta musamman idan shi ya bata Tsoron, domin kyau take Kara masa.

"Naji na hakura"

yafada yana kokarin mikewa da ita ajikinsa

"Yeeeehhh ya fu'ad nagode"

ta fada cikin murna domin ita aganinta dagaske hukuncin zai mata. girgiza kai kawai Yayi, kana kasa kasa yace


"shagwababiya kawai".

Kwantar da ita yayi agadon yaja duvet ya rufeta kana ya rankafo kanta cikin husky voice dinsa datayi sanyi kalau yace

"sleep tight heemah, have a nice and wonderful blessing night"

Lumshe ido tayi domin taji dadin sunan sosai"heemah" ta nanata aranta..





Saukar Sanyayar sumba data ji a forehead dinta yasata bude beautiful eyes dinta kana ta sakar masa sanyayar murmushi.



Duk da tana matukar tsoron kwana ita daya, amma takasa fada masa.






Cikin kasaita ya shiga takawa domin barin dakin.

Ya Kama handle din kofar yabude, sai kuma ya waiwayo, domin shima bayason barinta ita kadai, amma bayaso taga kamar yana yawan takura matane. Ai kuwa kwalla yaga sun cika idanunta.



"Ya salam!"

Yafada yana dawowa

"what again?" Ya tambayeta,






"ni ni ni wallahi tsoro nake ni kadai na kwana"

tafada hawayen sakalci na zubo mata, ciki farinciki dabai bari ya bayyana ba yace

"Zaki kwana dani a upstairs?"





Cikin sauri ta gyada kai.

Hannu ya miko mata ta kama suka bar dakin....




Shigarsu Had'add'en dakinsa suka kwanta bayan ya saita alarm yatashesu karfe 3:00am wanda zuwa yanzu faheemah ta saba da tashin daren itama.....





Share
Comment
Vote



Thanks for reading
my novel
#rayuwar faheemah
#NoorEemaan🥀🌸



💔RAYUWAR FAHEEMAH💔




_by NoorEemaan_📚✍️




kyautane( free novel)



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



"Death is coming without notification 🔔 😭 may almighty Allah make our last word to be kalimatus-shahada ameen"🙏.




41-42

(Not edited)







Washegari karfe 8:00am daidai, kowannensu ya shirya cikin shiga mai kyau, Faheemah sanye take da turkish abaya ruwan kwaiduwar kwai ta yana kanta da dankwalin abayan, sosai tayi kyau duk bata yi wata kwalliya ba daga powder sai kajol yayinda cute lips dinta suke kara yin ja, duk da bata shafa komai ba, uban gayya fu'ad kuwa sanye yake da wata dak'ak'iyyar gezne baki wanda yasa farar fatarsa dake glowing ta sake bayyana.


"Kin gama shiryawa?"
Ya tambayeta

"Eh"
ta amsa masa, batareda yace komai ba ya riko hannunta suka fice domin zuwa part din ummu.




"Assalama alaikum"

duka su biyun suka yi sallama atare, ilairin yan falon suka amsa fuskarsu dauke da fara'a.

Faheemah kunya kamar ta nitse duk yanda taso kafin su karaso part din ya saketa yaki... gaban ummu suka tsugunna suka gaisheta, cikin farinciki daya kasa boyuwa a saman kamilaliyar fuskarta ta amsa.
Yan'uwan ummu dana abbuh suka shiga gaisarwa cikin ladabi, kowannensu ya amsa cikin farinciki.

"har kun shirya da wuri haka?" Fu'ad ya tambaya.


"Eh gwara mu tafi tun yanzu, mu isa abin mu da wuri".

Aransa kuwa cewa yake hajiya innah kenan sai ka ce ba flight zasu bi ba.

Saukar muryanta ne ya katse mata tunani
"sai kuma mun zo suna ko yarinyar kirki?" tafada tana kallon faheemah.

Cikin kunya ta tashi ba tare da ta iya bata amsa ba ta zauna kusa da small mom kana cikin muryan kasa kasa hadi da shagwaba tace "shine small mom kikamin wayo jiya ko? Har da aunty fareesa ma"



fareesa dake gefen su ta saki dariya kamar yadda yake dabi'ar ta, ba tare da tace komai ba ta cigaba ta chat da anwar dinta.

"Sorry my dear abubuwa ne suka min yawa, har na sha'afa" cewar small mom cikin son wanke kanta.


"Kin hakura dai ko?"


"Eh bazan iya fushi da small mom dina ba".

"Good girl"

Small mom ta fada cikin kaunarta duk da basu jima da sanin juna ba amma sosai take jin kaunarta, domin lokacin da fu'ad yake jinya, babu yanda ummu bata yi ba akan a bawa fu'ad daya daga cikin yanmmata yan'uwansa ya aura suka ki a fakaice, domin basu fito baro baro cewa basu son hadin ba, daga dagin ummu har na abbah sosai sukayi nadama abunda su kayi, musamman da suka ga baiwar kyau, nutsuwa, hankali, irin na faheemah, tabbas bare zai iya maka abunda dan'uwanka na jini bai maka ba, domin jiya suna makwancinsu sai da innah ta kawo maganar ta kuma ce su nemi yafiyar ummu, small mom tace a'a acewar ta tunda komai ya wuce, abarshi a hakan, domin tasan ummu bata da riko saboda haka a bar maganar, sun amincewa maganar small mom din yayinda jikinsu yayi sanyi sun kuma yi nadama domin abunda suka Kasa yiwa dan su, bare yayi masu.



"Small mom"


faheemah ta katse mata tunani.


"Na'am dear"


"idan za'ayi bikin anty
fareesa kada mu zauna a wajenta da mun kaita zamu juyo ko?"


"Eh sosai ma tunda har ta iya bar min ke ke kadai jiya."


"Yawwa small mom"
tafada tanawa fareesa dariyar tsokana


"Tab Allah small mom bazan yarda ba"


Fareesa ta fada fuska amarairace.


" Yeehhh nima na rama" faheema tafada tana mata gwalo.


Hakan sai ya bawa small mom da fareesa dariya...



Wanda ya janyo hankalinsu ummu garesa, fu'ad kuwa ita yake kallon tun dazu, shi kam yana son childish ness dinta duk da baya jin me take cewa amma, yana karantar zallan sakalci da shagwaba a acting dinta, hakan kuma na burgeshi.


"Wai ke rabi'a ( small mom) me kike tattaunawa ne keda yarki taki kasa kasa ba'a so muji?"
Cewar wata tsahowa daga dangin abbuh mai suna innah suwaiba.

"Inna Sirrinmune ko my dear?"


Shigar da kanta jikin small mom tayi a kunyace kana ta jinjina kai alamun "eh "


"ke yarinya menene abun kunya? dazu nayi mgn keda mijinki ku mun shiru maganar haihuwar ce bakuso?" Dariya kawai su kayi domin daman sun san inna akwai Mita.

"Kinga yarinya an fa zama daya mu ma iyayenki ne kinjiko?"
Cewar innah suwaiba.

Kara shigar da kanta Tayi a jikin small mom din kana tace "toh "

"ja'ira sarkin kunya"

innah'n ta sake fada, dariya aka Sanya gaba daya ganin sai kara shigar da kanta take jikin small mom.



Mikewa sukayi domin tafiya, daman sun shirya jakankunansu gasunan tsakiyar falon.
Faheemah ce ta dauki akwati daya, ganin Hakan yasa fareesa daukan daya, meenal ma ta dau daya. Dayan daya rage fu'ad ya dauka, Hakan ya sake burge iyayen nasu duk da akwai masu aiki a Gidan amma bai hanasu dauka ba,
kuma sun san cewa ganin Faheemah ta dauka shiyasa su fareesa dauka suma, aransu suna yaba tarbiyyanta haka suna farinciki da samunta azuriyyan su, Ummu kuwa a ranta tana fadin zata aikata fiye da hakan, a lokuta da dama tana mamakin yanda faheema keda nutsuwa hadi da tarbiyya, domin bata da mai kwabarta tun bayan da uwarta ta rasu, domin matar ubanta bata kula da ita bare ta kula da tarbiyyanta, haka ma abbuhnta da bai san da zamanta ba, hakika tarbiyan faheemah daga Allah ne haka ma nutsuwarta....


Maganar fu'ad ce ta katse mata tunani, kasa kasa yace "ummu gashi ki basu dan Allah" yafada yana miko mata mata bandir uku na 1k Yakuma yi hakan ne domin bayason su masa godiya.



Murmushi Ummu tayi domin ta fahimce shi kwarai, Duk da itama ta basu kudi masu yawa amma, taji dadin yanda yayi.



"Kaltume tunda muna da yawa ku koma hakanan ba sai kun mana rakiya airport ba" cewar innah suwaiba.


Da "toh" Ummu ta amsa kana suka shishiga motocin biyun da zai kaisu, addua sosai su ummu suka musu na sauka lfy, sai da direba ya tashi motar Ummu ta Dora bandir daya na kudin a cinyar innah, sai kuma ta dora bandir daya a cinyar small mom dake dayan motan, sai kuma ta dora bandir daya cinyar meenal kana tace musu su raba inji Fu'ad.

Ai kafin innah da sauran su suyi magana drivers sun cilla hajin motocin waje...


Haka suka juyo gida cike da kewarsu, domin Faheemah har da kwallar ta domin ta saba da su babu laifi, musamman ma small mom.
Sai da ya bari su ummu sukayi gaba, kana ya matse hannunta daya, wanda ya kara gudun hawayenta.


Cikin dan hasala kana kasa kasa yace

"wata rana sai hawayen nan ya kare, da alama dadi kukan yake miki right?"


"A'a"
ta fada tana turo baki.

"Ok! maza share hawayen kinji banason su" Hannu tasa ta goge hawayen kana suka rufawa su ummu baya.


"Son kuyi breakfast dinku, munyi tareda su innah kafin ku fito"

da "toh" ya amsa, yayinda faheemah ta zuzzuba masa waffles, tea, da peppersoup, tayi, tana kokarin zuba nata ya dakatar da ita.
"ki kara ankan wanda kika zuba min muci a plate daya"


Dan xaro ido tayi ta juya domin ganin ko su ummu na nan, wayam ta gani ba Kowa. Girgixa kai kawai Yayi yana boye dariyar sa.


"ko me abun kunya a cin abinci a kwano daya?" Ta tambayi kansa kasa kasa, tabe baki yayi batare da ya kara ce mata komai ba...




Abincin ta kara ta dauki spoon ta fara ci a hankali, shi kuwa ko ajikinsa ci yake a sake, bayan sun kammala yace "tashi muje ki tayani shiryawa zan wuce aiki". Kasancewar Daman ya sanar bazai samu zuwa da wuri ba yau.



"Ni wurin ummu zan..."

Kallon daya jefa mata ne yasa ta mike babu shiri, Fu'ad kuwa kwata kwata bayason takurawa mutum a rayuwarsa amma idan bai yi mata haka ba, Baya tunanin zata sake dashi har suyi irin rayuwar daya tanadar musu.
Yana gaba tana binsa a baya ta doguwar corridor dake gefen benen suka bi sai gasu sun fito awani hadaden wurin mai yalwar furannin tamkar garden dai. Dan tafiya suka sake yi sai gasu a part dinsu, Faheemah ta danyi mamaki domin batasan da wanna bangaren cikin gidan ba.

kayansa ya cire ya daura sky blue towel kana ya shiga Wanka, bai wani jima ba ya fito, kayan sa dake ajiye gefen gado ya sanya bayan ya shafa lotion dinsa.

"yar kauye haka ake taya mutum shiryawa? zo ki samun neck tie"

asanyaye ta mike ta daura masa da murmushi saman fuskarta, ita kam idan ya kira ta da yar kauye dariya yake bata.

Lallausan gashin sa tayi oiling kana tayi brushing dinsa, agogo ya mika mata, sai kuma ya mika mata hannun yana dan bata rai shi ala dole ita zata daura masa. Murmushi kawai tayi ta daura masa kana ta fesa masa turarensa mai matukar kamshi...


Jakarsa ya dauka kana ya matso dab ita lips dinta na kasa ya yiwa sucking na minti 2 Wanda bandan ya jure ba da babu abunda zai hanasa cigaba saboda d'ad'add'an kamshin bakinta da saliva dinta...

Cikin rada yace 'take care heemah bye!" Yafada yana daga mata yatsun sa biyu, Kana ya fice cikin tafiyar kasaitarsa ...


" ooh ya rabb help me! zai kasheni da salonsa"
tafada tana sauke ajiyar zuciya.

Dakin ta shiga gyarawa duk da babu datti, kasa ta sauka ta shiga gyara wa shima, wanka ta shiga bayan ta fito ta shirya kana ta fice wurin ummunta...




*5days later*

Sosai yanzu faheemah tadan saki jiki da fu'ad wanda hakan ya sa shi jin dadi duk da bai furta ba.



"Hmmm faheemah ana can ana bauta aure, ana fama da nakashashen miji" cewar mami .

Dariya jin dadi jameela da Mami suka sanya kana suka tafa kamar sa'anin juna.
"mami xanso ganin Faheemah yanda ta koma, na san ta dawo lawashi daya sha rana tsabar laushi"
ta Karasa tana dariyar mugunta, mami na kokarin bata amsa wayarta ya shiga ringing.....



"Hello hajja Hajara wai meya Samu wayarki sai kira nake bata shiga?"


"Wallahi kila sharrin network ne, amma lafiya wayata take
"
"mtssssssd" ta ja dogon tsaki kana tace

"ya akayi haka? Munafur ta ta kika yi daman?"

"Ban gane ba hajja hindu?" Baki ta faɗa baki a sake.

"Kada ki raina min hankali hajara, kinaso ki ce min baki san gidan da wanna kod'add'iyar 'yar kishiyarki taki take aure ba?"


"Wai kina nufin Faheemah? hhhhhhh ai tana can tana bauta wa nakashashen miji"


jin an ambaci Faheemah yasa jameela mikewa tsaye, itama burinta mami ta gama waya taji abunda ake cewa.


"toh kina raina wa kanki hankali domin Faheemah na auren dan gidan maragayi alhaji omar ishaq ne!"


"Buro.........."ta lailayo wata lukutar ashar kana cikin rudewa da kidimewa ta mike har zaninta na kuncewa, cikin daga murya ta sake lailayo ashar kana tace

"bai dai Omar ishaq daya shahara a duniya ba?"



"Eh kwarai shi nake nufi"

" Innalillahi! ya aka yi haka toh hajja hindu?"
Cewar Mami amatukar rude.

A ranta sai fadi take Anya kuwa? Kai ba dai faheemah bace...





"Ai ke zan tambayi wanna hajara." Hajja hindu ta faɗa cikin jin haushin Mami, kamar ta shako ta ta cikin wayar haka take ji.


"Ai wanna ba maganar waya bace gani nan zuwa yanzu yanzu hajja hindu..."



"Mami menene wai?"

"Hmmm jameela muje gidan kwata hajja hindu mayi maganar acan, muje muje kafin alhaji ya dawo..."


★★★

"Mama wallahi inasonsa, bata isa ta kwace ji a hannuna ba, dani wanna daular ya dace! dana sani dana jure na kula dashi, da duk ni zai nunawa wanna gatan, dani zai nunawa soyaayar daya nuna mata a bainar jama'a" tafada cikin kuka har shidewa take


Ran hindu a matukar bace ganin tilon yarta na Kuka.


"Yi shiru umaimah Fu'ad naki ne, rabuda yar matsiyata, dake ya dace gaki yar'uwarsa ai kwarya ta bi kwarya. Kawai so nake hajara tazo gidanan inji tayaya tabari har Faheemah taje gidan ummun taku har ta samu matsayi da arxikin auren fu'ad"

"Mama daman kin san ta ne?"

" Kwarai kuwa umaimah" nan ta shiga bata labarin faheemah data sani.........



Gama maganarta keda wuya suka ji sallamar Mami, hawayen umaimah Hindu ta yi saurin share mata kana ta basu izinin shigowa.



"Hajja Hindu k'wak'walwata ta toshe na rasa nagane kan maganarki" cewar mami a kidime tana kokarin zama.


Wata harara hajja Hindu ta watsa mata domin a ganinta tasan komai...



"Hajja hajara kenan kina so kice min baki san dan gidan alhaji Omar ishaq faheemah ke aure ba?
Ko wasa kike min da hankali ne? ba ke kika bawa hajja kaltume auren ta ba,
Ko bada amincewarki ta bar gidan ba?"



"Hajiya kaltume kuma? ban san wacece haka ba? Kuma kinsan ni, kin san tsanar dana ke wa wanna yarinyar ta ya ya kike tunanin ina ji ina gani zan bari haka ta kasance?" Nan ta dora da bawa Hindu labari zuwan Ummu gidan .........



A karshe tace "Wallahi ki yarda da ni kawata, ban gane abinda kike nufi ba"



Wani yawu mai daci hindu ta hadiya kana cikin muryan fushi tace" kin yi kurkure babba domin gidan arziki hadi da duk Wani jindadi rayuwa kika kai faheemah,
amma ban san dalilin daya sa kika ki gane arziki atattare da matar a xuwanta gidanki ba"


" Innalilahi wai da gaske faheemah na gidan jindadi ba gidan talauci da bauta ba kamar yadda nake tunani ba?"



"Na fiki shiga tashin hankali hadi da rudani hajara, naga alamar kina kokwanto, wacece wanna?"


Ta hasko mata fuskar faskekiyar wayarta mai dauke da hoton faheemah da fu'ad dake Murmushi.


Ai tsuman Zaune mami da jameela sukayi, luuuuuu mami ta tafi ji kake gwarab ta zube a kasan tiles...


Salati suka sa, duk suka yo kanta jijiga ta suka yi shiru bata motsi, ruwa mai sanyi a fridge umaimah ta dauko ta yayyafa mata, doguwar zuciya tayi kana cikin fitar hayyaci tace



"karya ne!
Wallahi baki isa, wanna arziki banaki bane, wahala, kunci , bauta ya kamaci rayuwarki faheemah, Hindu Kara nuna min hoton in gani" hajja Hindu kuwa ta sake hasko mata fuskar wayarta, ai Kara tafiya tayi luuu zata fadi suka taro ta.., "algugunman yarinya, daman tana gidan hutu da jindadi amma bata zo garemu ba, Wallahi baki isa ba, wanna gidan sai kin barshi, da diyata ya dace"...



Jin abinda take fada yasa hajja Hindu daga mata hannu


" kin ga hajara in ma mafarki kike Wallahi ki daina domin yata umaimah shi take so kuma dan uwanta ne, kinga waya dace ya aura?"


Sai ta hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya kana ta ɗora da cewa
" Wanna auran sai na warwareshi ko ta halin kaka" Shiru mami tayi bata kuma cewa komai ba, domin tana dan shakkar hindu, haka kuma Wani tunani datayi da ita kadai ta bar wa kanta sani yasa tayi shiru...



Umaimah kuwa sai antayawa jameela harara take ganin yadda ta kurawa hotonsu fu'ad ido tana sakin Murmushi ko maganar dasu mami keyi duk ba ji take ba.


Dogon tsaki umaimah taja daya dawo da jameela hankalinta, basarwa tayi ta ajiye wayan kan centre table dake gabansu , kana itama ta zabgawa umaimah harara


Ganin hajja Hindu tana yaba mata kananun maganganu yasa suka tafi babu sallamar arziki kai kace ba tight

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment