Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

drugs instead of you sitting here crying" cewar uncle Solomon.

"Okay sir" ta amsa tana mikewa.
Ajinsu ta nufa cikinta na kugin yunwa saboda ko breakfast batayi ba ta taho.
Da magriba bayan abbuh ya shiga masallacin dake kusa da gidansu, fitowa ta yi wajen gidandomin ganin dawowarsa, bayan 10min sai gashi ya taho gabanta na faduwa haka ta gaishesa, ko amsa bata samu ba ganin yana kokarin wucewa ne yasa ta durkusawa gabansa hadi da rike kafafunsa "abbuhna kayi hakuri idan na bata maka rai, abbuh kayafemin dan Allah! kataimaka ka biyamin kudin waec da neco za'a rufe biya nan da sati uku, dan Allah abbuh...."


Tafada tana sake dora hannayenta kan kafafunsa.. Ran abbuhne ya baci itadin wacce dazata sha mai gaba har da kama kafarsa yafada aransa? ball yayi da ita ya shege cikin gidan.
karaf a idon jameela da sabon saurayinta salman ya kawota a mota.


*FAHEEMAH*

mikewa tayi tana sosa gwiwar hannunta data ji ciwo sakamakon ture ta da abbuh yayi, gida ta shige tana hawaye sosai, ganin tarasa hope dinta na karshe daman abbuh take tunanin zai taimaka mata gashi ko kulata bai yiba. Tana mamakin canzawar abbuhnta da wanna tunanin tayi alwala ta nufi daki.

Jameela ce cikin dinkin fitted gown daya matseta sosai, dakin mami tashige ta sanar mata abunda tagani, wato yarinyar nan bata jiko?cewar mami ranta inyayi dubu ya baci, fuuu ta nufi dakinsu faheemah....

Sallame sallarta keda wuya taji saukar duka abayanta, ihu ta tsalla saboda dukan ya shige ta matuka, "nizaki rainawa hankali? kinje kisamu alhaji akan kudi ko? Kina tunanin zai baki ne? AIHAJI YA MANTA WACECE KE..... Idan ma baki sani ba ki sani, munafuka, wawuya mai bakar zuciya sakarya kawa" Tafada tana kai mata bugu ta ko ina kuka sosai faheemah keyi, "mami kiyi hakuri dan Allah ki yafemin wayyo ummina!!!" Sai da mami ta gaji dan kanta kafin ta kyaleta, zuwa wanda lokaci muryan Faheemah ya dashe saboda kuka, ga idonta daya kumburan tsukutum sakamakon dukan daya sameta idon.
Mami kuwa na fitowa taga abbuh tsaye yana kallon dakinsu Faheemah. Gabanta ne ya bada ras! Kodai yafara dawowa da son yarsa ne ta fada aranta. A fili tace "Alhaji lfy kuwa kake tsaye?"

" Ina kikajene tundazu abinci zaki bani" cewar abbuh.

ajiyar xuciya ta sauke ganin ba abinda take tunani bane, "yi hakuri Alhaji" tafada tana bin bayansa domin zuba masa abincin


Misalin karfe tara da rabi nadare jameela ke tambayar mami "me faheemah tayi ne?"

"ra buda Mayyar..." Nan ta shiga labarta mata komai. Cikin farinciki jameela tace "Mami kinyi daidai wallahi, a tunaninta zata cigaba da karatu ne, ni wallahi a kullum kara tsanarta nake, saboda ta samu abinda yace ace ni na mallakesa! Gani nake wahalar da takesha yayi kadan kyaunta kamar karuwa yake bana son cigabanta ni mami wallahi"


"Ai yar albarka ki kwantar da hankali sai ta yabawa aya zakinta, bauta yanzu ta fara.... kuma kedai na tunanin ta fiki, kinfita komai" ta fada domin kwantar wa da jameelan hankali, amma deep inside her heart tsana da Bakin ciki ke cinta, saboda tasan tsakanin jameela da faheemah akwai tazara mai yawan gaske.



Marainiyar Allah kuwa, zazzabi ne ya rufeta sosai, tun tana kukan harta yi shiru, sai ajiyar xuciya take saukewa.
Ga yunwa domin bata ci abinci safe ba, sai na rana wanda jollof din spaghetti ne tadafa mami tace ta kwashe mata duka a flask, sai kanzon tasamu taci, tana a haka jameela tashigo tana mata dariyar mugunta hadi da murna ganinta a haka, saboda yanda idonta ya kumbura,wanda hakan yasa fuskarta dan sanjawa daga kamaninta, hayewa gado tayi ta fara chatting cikin farinciki tana fatan fuskar Faheemah ya tabbata ahaka.



Faheemah dake kwance a kasa ta mike zaune da kyar tuno da bata yi sallar isha ba,ta hada hanya a haka ta fita waje...


Bayan sati biyu wanda ya rage 1 week arufe registration. Sosai tashiga zullumi hadi da fargaba. Ga aiki daya yayi mata yawa fiyeda na baya ta sake ramewa da lalacewa, domin yanzu wankinsu duka ita keyi, ada wanki su ke kaiwa, ita kadai ke wanke nata agida, amma yanxu ita keyi sosai ta sake rama wanda hakan yayi wa su mami dadi.




Bayan kwana hudu, da misalin 7:20am tafe take kanta akasa hawaye na zuba idonta saboda ganin ana gab ta rufe registration amma har yau bata yi ba.



Wata kyakyawar mata ce zaune amotarta da ganin ta ilimin addini dana boko ya ratsa ta. Hango wata kyakyawar budurwa na kuka yasa hankalinta tashi kasancewarta mai saurin tausayi, balle murfin motarta tayi domin cimma wanna budurwan data yi mata dan nisa....



"Diyata" cak ta tsaya jin wata kamilar murya abayanta. Juyowa tayi asanyaye, "lafiya kike kuka a hanya?" Kuka mai sauti ta fashe kana ta rungume matar da bata san ko wacece ita ba. So take a rarasheta, so take tayi kukan ko zuciyarta zai rage radadin da yake mata, so take ta samu hug ko hakan zai rage mata damuwa.



Bubbuga bayanta matar tashiga yi, lokaci daya taji tausayi hadi da kaunar ta a ranta. Dago kanta tayi saboda ganin yanda ta bata tsad'add'iyyar mayafin matar da hawaye da majina, ganin ta kurawa mayafinta ido ne yasa matar kallon mayafin nata. Murmushi kwantar da Hankalinki matar tayi mata, kana tace

"ya sunanki diyata? "

"FAHEEMAH"

ta amsa cikin muryan kuka.


"diyata faheemah miyasa kike kuka? Feel free and tell me okay?" Nodding kanta tayi kana cikin rawan murya tace "kudin registration din waec da neco ne ba...ban... Biya ba, Kuma sauran kwana uku arufe registration" tafada ararrabe.

"Nawane kudin?" Saurin kallon matar tayi kana tace "du...dubu sittin da takwas ne..." Ta fada a tsorace, domin a tunanin ta kudin sun yi yawa.


Murmushi mai sauti matar tayi kana tace, "idan na biya miki will be happy?" Cikin Saurin tadago kanta jin abinda matar tace, gyada mata kai matar tayi alamun tabbatarwa "za... zaki biyamin kudin da gaske?" Sake gyada kanta matar tayi.


Durkusa tayi ta dafa kafar matar tana kwararo mata addu'a da godiya cikin kuka.


Dagota matar tayi tana share mata hawaye hakan nan take jin kaunar Faheemah aranta.

"Muje makarantar taku" cewar matar, bin bayanta Faheemah tayi domin hakanan take ji ta yarda da matar.


Suna cikin mota matar tace "ya sunan makarantar?"

A sanyaye tace "Brighter brains academy" Matar bata kuma cewa komai ba duk da akwai tambayoyi datakeson yi mata.


Bayan angama komai na registration din ne suka fito, Sosai bakin Faheemah yaki rufewa saboda murna hakan ya sanyaya ran matar ganinta cikin farinciki.

"Amma diyata FAHEEMAH zanso jin labarinki,
Inason Sanin ina babanki?
Ina mamanki? Ko kuma baki da kowa ne? kuma waye ya sanyi ki wanna makaranta? "

Hawayene suka ciko kyakyawan idanunta, bata jin zata iya musu ko kin gayawa wanna matar mai kyakyawar zuciyar labarin ta.


"Sunana Faheemah abubakar idris..... "

Haka ta shiga bawa wanna matar labarinta bata boye mata komai, domin taji matar ta kwanta mata.


Kuka Sosai matar tayi jin tsantsar mugunta Irin na matar uba Sosai ta tausayawa Faheemah.

"Kiyi hakuri diyata FAHEEMAH. Kwarai kinga rayuwa ada ina tunanin neman alfarma ko ince taimako wurinki saboda yarda dana miki lokaci daya... kinga rayuwa, but not anymore, faheemah u deserve some happiness..."


"kada kice haka hajiya, komai kikeso zanmiki, babban burina yanzu naga abbuh na ya dawo da kulawarsa gareni, sai kuma Karatu wanda kin cika min shi. Numfashi tasauke kana tace kifadi bukatarki wallahi Allah zan miki shi matukar bai tsaba addnin na ba..."


Murmushi matar tayi tana mamakin hankalin irin na yarinyar.

'yarona yana da lalurar *paralyzes* kusan shekaru shida kenan! Baya magana baya iya komai, komai yimasa ake, kullum yana kwance,
"Diyata Faheemah zaki iya auren dana?"

Gaban Faheemah ne ya bada dam! dam!! daram!!! Jin abinda matar tace, kasa tayi da kanta kalmar auren ne kawai ke yawo a kanta.

"Diyata kitaimaka ki amshi bukatata, ina bukatar mai kula min dashi, ina bukatar mai debe masa kewa, matar tafada tana hawayen tausayin danta, na kuma yarda dake shiyasa nake so ki kasancewa abokin rayuwar sa".



Duk da bata taba kowa wa kanta aure yanzu ba, amma gwara ta bar gidan tunda ko abbuh ta baya son ganinta, Ita wacece da zata zabi miji irin wanda takeso?
kamar yadda mami ta fada bauta shi ya dace da ita.

A fili tace " Ki daina kuka hajiya na... na.... amince"
tafada murya na rawa.

Farinciki matar bazai misaltu ba, cikin zakuwa tace "mekikeso diyata na baki? Matukar akwai shi aduniyar nan zan miki shi"

"Bana bukatar komai"

Faheemah tafada asanyaye.

"Ok Ki bani address din gidan ku" cewar matar.



Ba musu ta fada mata kana tace "hajiya malami ya shiga ajinmu xan tafi nagode sosai..."


" tsaya faheemah ni ba mamanki bace?"


Ahankali tace "ke mama na ce"

Matar tace, "toh kada ki kara cewa hajiya ki kirani da ummu sunan da yan'uwanki ke Kirana dashi kenan"




"Kiyi hakuri ummu bazan sake ba". murmushi matar tayi, ta na ji ajikinta cewa irin matar da danta ya dace ya aura Faheemah ce, tana ji ajikinta cewa Faheemah Ita ce sukurarta, mota ta shige ta bar makarantan tana mai farinciki....


Comment
Share


Thanks for reading Rayuwar FAHEEMAH.


💔RAYUWAR FAHEEMAH 💔


_Written by Nooreemaan_


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



kyautane( free novel)



"Its only when you take responsibility for your life that you will discover how power you truly are"



13-14

(Not edited)


Bayan Faheemah taje gida bata nunawa kowa komai ba, tayi sallar azahar ta fara aiyukanta data saba dare da rana ba hutu.


★★★

horn ta danna mai hadi ya wangale babban gate din ta shigar da motarta cikin gidanta.


"Hajiya sannu da zuwa"
cewar mai gadi.

"yawwa sannu malam iro, ya aikin? "

" Alhamdulillah hajiya ya amsa".

Bata kara cewa komai ba, da haka ta wuce,
Part uku ne a gidan na tsakiyar ta nufa...


"Fareesa!"


"na'am ummu"


"ya na gan ki a gida, Ina office din?"


"Ummunah Yanxu zan koma wani file nazo dauka"


"Okay idan kin dawo akwai albishir mai dadi"

" Allah ummunah?
Kigayamin please"


"toh sarkin garaje kije kidawo ai ba guduwa zanyi ba"


dariya tayi daya bayyana jerarrun hakoranta kana ta sumbaci ummu a goshi ta fice cikin sauri,
Da kallo Ummu ta bita tana sakin murmushi.




_5:00pm_

"Da safe dana je gidan rasuwar nan... toh bayan na fito ina kokarin tada mota ta na hango wata yarinya na kuka........."


Nan ta shiga bawa fareesah labarin a takaice, kuka fareesa tayi jin labarin *RAYUWAR FAHEEMAH*


"Alhamdulillah ya Allah mun gode maka"
cewar fareesa tana daga hannunta sama, kana ta kara da cewa
"ummu wallahi naji kaunarta tun kafin in ganta, amma Ina jin tsoro kada ta ce ta fasa ta idan ta ga halin lalurar da brother na yake ciki"
ta fada cikin murya mai bayyana damuwa.


"bana jin zatayi haka fareesa, idan ma ta fasa babu komai, wallahi zan kula da ita tana bukatar farinciki rayuwarta, and bana tunanin zata ki amincewa, ta banbanta da sauran yanmmata, Shiyasa na kudirta araina nake kuma addu'an ya samu matar aure awanna yanayin da yake ciki ta haka zan san cewa bata aureshi dan kyau, kudi, limi, ba. ko wani mata'ul hayat ba( kyalekyalen rayuwa) littafin margayiya mmn shureim Allahu ya gafarta miki yasa mutuwa hutu ce agareki dama sauran Muslims umma) domin sosai na tsorata lokacin da duk masu son dan'uwanki suka ja baya saboda lalurarsa shiyasa na kudurta a raina nake kuma addu'a Allah ya bashi mata awanna yanayin dayake ciki ta haka ne hankalina zai kwanta".

Jinjina kai fareesa tayi domin tasan wanna kudirin na ummunta tun ba yau ba, haka itama tana goyan bayan haka

"ummu kinsan wacece tafi ban mamaki? Wallahi aysha ta ban mamaki, Kiga yanda take mugun son brother, amma daga fara rashin lafiyan shi ta dauke kafa a gidannan"

" hmm fareesa ba abun mamaki bane, yar uwarsa umaimah da ta ki shi fa?"


"Hakane ummu, wallahi idan brother yasamu lafiya hmm...umaimah zata san tayi dani"

tafada tana jinjina rashin mutuncin dazata mata, kasancewar bata barin ta kwana.


" A'a a'a fareesa banason rigima, rayuwarta ce so tasan what's best for her saboda haka kada naji kona gani"


"Toh ummu"
kawai ta amsa.

Kana ta dora da cewa
"Yaushe zaki je gidansu ummu?"

"Ina tunanin sai sun gama jarabawan, bari naje naga ko yayanki ya tashi daga bacci"
ta mike nufi hanyar dakinsa...


★★★

*BAYAN WATA UKU*
Zuwa wanna lokacin faheemah ta gama jarabawarta, kuma har wanna lokacin abbuh baya kulata kuma bata fasa gaisheshi ba, amma baya amsawa, tsakanin jameela da mami ma bata canza zani ba sai ma abinda ya karu na muzgunawa dasuke mata....


Yau ta kasance asabar ummu ce zaune a kujeran mai zaman banza cikin mota, sanye da brown din hijab mai saukin kudi, yayinda fareesa ke tuki, "ummu yanzu bazaki bari nakaiki har layin ba?"

"A'a fareesa ki ajiyeni atiti zai fi, saboda banason wanna maminsu faheemah ta ganni, kowani ya ganni, inaso nake musu abamu da komai Ina ganin hakan xai sa komai ya tafi yanda nakeso, zandawo a adaidaita ki kula da yayanki bazan dade ba".


" Toh ummuna adawo lafiya" ta fada daidai sun zo titin .


Da kwantancen da Faheemah ta bata ta isa gidan.


"Assalama alaikum". Ummu tayi sallama bayan ta shiga gidan.


"Wa'alaikumu salam"
mami dake zaune kan tabarma ta amsa, yayinda faheemah ke duke tana wanki, sai zagi na uwa da uba mami ke antaya mata.


jameela kuma nadaga daki tana waya da salman dinta.


"Lafiya baiwar Allah?"

Cikin fuskar damuwa Ummu yace "Ba lafiya ba, ina neman taimako ne. dana ne bashi da lafiya kusan shekaru shida baya iya komai da kansa kullum yana kwance, babu wacce ke son aurenshi, shine nazo nan gidan ko zan dace, ki taimaka min dan Allah idan kina da y'a wacce zata iya auren dana kitaimake ni, ki taimaki marayan Allah bashi da kowa sai ni da kanwarsa ummu ta fada cikin kuka mai ban tausayi".


MaÉ—aukakin murmushi ya bayyana afuskar mami, hakika irin mijin da take so faheemah ta aura kenan. nakashashe, talaka, wanda zata kare rayuwarta a bauta, Tabbas! ta samu cikar burinta cikin sauki.



"Kwantar da hankalinki baiwar Allah, nan gidan kin dace, gata can na baki ita halak malak" ta nuna Faheemah dake gurzan wanki, takara da cewa"sannan banaso ganin koda gilmawarta aunguwar nan bare ta tako kafarta agidannan".


Sosai ummu tayi mamaki, domin bata taba tunanin wanna maganar zai sa mami amincewa tabata faheemah cikin sauki haka ba, idan ita mai cutarwa ce fa? Sai kace kaza ta bada kyautar ta batareda nazari ba, bata ma yi wanna tunanin ba lallai duniya akwai abun tsoro, ta kuma sake tabattar da muguntan mami.

"Ke! Bar wanki nan ki kwaso kayanki ki bita" mami ta fada akausashe.

Gaban Faheemah ne ya bada ras! jin abinda mami tace dago kanta tayi idanunta suka fada cikin na ummu, tabbas ta shaida ta, amma meyasa ummu ta biyo ta hannun mami? Meyasa bata samu Abbuh ba?


" zanmiki diban albarka badake nake magana ba?" Cewar mami cikin tsawa!


Durkusawa tayi tace "dan girman Allah mami kiyi hakuri dan Allah kada ki kore ni" takalmi mami ta jefa mata, ya kuwa sameta afuska, ganin mami na kokarin nufota ne yasa cikin saurin ta nufi daki ta kwaso kayanta cikin Ledan viva daman bawasu kayan arziki gareta ba.


"Na zata sai me gidan yadawo an daura aure zata bini" ummuh ta fada a sanyaye.


"A'a kuje can ku nemi wani ya daura mata aure ba dai anan ba, bata da uba a gidanan, in ma zaman dadiro zata yi, can ku karata, babu ruwana" mamaki ne ya sake kama ummu.


Faheemah ce ta fito cikin kodaddiyar bakin hijab dinta yama fara brown - brown saboda kodewa, ta durkusa gaban mami wanda hakan yayi daidai da gama wayar jameela.

"Mami ki taimake ni naga abbuh na kafin na bita, ki bari nayi masa kallon karshe dan Allah!" ta kama kafar mami tana kuka Sosai.

Fincike kafarta mami tayi kana tace "Wawuya, sakarya, mara zuciya kawai, sau nawa zan ce miki bakya gabansa, da zaman ki da rashin sa duk daya ne awajensa, maza kibi ta ku tafi kafin na mangare ki, munafuka kawai"

"Wayyo Allah! mami kiyi hakuri aunty jameela ki taimakani".

Wani abu mai Kama da tausayi ke kokarin ratsa zuciyar jameela, Saidai kiyayyar faheemah ya rinjayi tausayin ta saboda tun bata san tsana ba, mami ta datsa mata tsanar faheemah azuciyarta.


"wai baiwar Allah bazaki dauketa kubar gidannan bane?"
Cewar mami cikin daga murya!

A sanyaye ummu ta janye faheemah daga gaban mami, bata taba tunanin muguntar mami ya kai nan ba.


"Wayyo Allah mami kiyi hakuri! aunty jameela ki taimakani. abbuhna kazo! kazo!! dan Allah"
abinda Faheemah keta maimaita tawa cikin kuka dake bayyana abinda ke zuciyarta kenan.

Riketa ummu tayi suka bar gidan itama tana sharar kwalla tausayin faheemah wanna wacce irin matar uba ce"???



"Mami wai me kike haka ne? Idan abbuh yazo mezaki ce masa? Bama wanna ba idan yan'uwan maman faheemah kona abbuh suka zo mexaki ce musu?"

Dariyan nishadi mami tayi sannan tace nasan amsar da zan basu, Kuma wanna abun danayi saboda ke nayi, banaso ta samu mijin dake ya dace kisamu, banaso taji dadi kwata- kwata a rayuwarta inaso ta mutu cikin wahala da bauta, sanna kema ranki bazai dinga baci ba idan kin ganta sanna kindaina fargaban kada wani mai arzikin ya ganta ya aura inason cika miki burin ki ne yar albarka ta"



"Amma mami dakin barta ai kullum tana gidan nan ina zata fita bare wani ya ganta yace yanaso, kuma kika sani ko wanna matar na da kudi? Bakiga fatarta akwai alamun huta ba?"

"Yaro Yaro ne da tana da arziki da bata bar danta ciikin jinya kusan shekaru shida ba, ai da ta nema masa magani. (Rashin sani)"

"Har naji dadi mamina, na huta da ganin wannan kodadiyar fuskar tata"

sai kuma ta bata rai tace "amma mami wanki, girki da duk wani aiki wa zai cigaba dayi dan ni gaskiya kin san bazan iya ko daya ba" cewar jameela tana turo k'ak'auran labbanta masu dan fadi.

"kwantar da hankalinki yar albarka ai ke yar hutu ce, zan kira wanna almajirin ya cigaba da mana wanki da sauran aikace aikace ni kuma zan dinga yi mana girki shiyasa nake miki addu'an samun attajiri wanda ya amsa sunanshi domin ki huta kuma da alama kin samu"
rungume mamin tayi cikin farinciki....

★★

"Diyata faheema kiyi shiru haka kinji, bazaki taba nadamar bina ba, I promise you this"

nodding kanta tayi tana sharan hawaye, wata almajira ummu tagani a karkashen wata bushiya,
Hakan yasa ta karbi ledar hannu faheemah zata mikawa almajiran, ai damke ledar faheemah tayi, cikin zaro ido da marairaice tace

"banda wasu kayan duk duniya sai wadannan dan Allah ki bar min su".


Dariya ummu tayi ganin yanda ta rike ledar tamau.


"saki ledar faheemah ummunki zata baki wasu kaya kinji?"

" Toh" tace hadi da sakarwa ummu ledar Almajira kuwa sai add'ua ta dinga kwararawa ummu da haka suka nufi titi....



*Janbulo first gate*

daidai wani tangamemen gida ummu tace mai adaidaita ya tsaya, 1k tabashi yana kokarin bata canji tace ya barshi sosai yayi murna hadi da godiya.

"Muje mana diyata kada ki ji tsoro bazan cutar dake ba"


asanyaye

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment