Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da mami indian domin gyara kafar ta yanda ba sai da sanda zata dinga tafiya ba, cikin ikon Allah aka gyara kafar tareda taimakon karfin da aka sa mata a kafa take tafiya duk da hakan dai idan tana tafiya zaka gane cewar kafar akwai Matsala, wani abun karin mamaki kuwa ya siyawa abbuh babban gida a shagari quarters suka koma can, har da kara bude masa babban store a kasuwa bayan na shi, ya kuma ce abbuh yasa haya a tsohon gidansa. sosai mami ta yi kukan nadama, domin ta silar wacce ta tsana ada aka gyara mata kafa ta dan samu saukin tafiya, duk da cewa kafar ba zai taba dawowa dai dai ba, amma yanzu yafi lokacin da suka yi hatsarin, idan kaga mami yanzu ta shiryu sosai, ranar da ta kira faheemah akan ta taya su godiya wurin fu'ad. Ai kukan dadi tayi tana godiya ga Allah hadi da alfaharin samun miji kamar fu'ad, domin ko da wasa bai sanar da ita ba, daya dawo daga office, har kasa ta tsugunna domin nuna godiyar ta a gareshi ya yi saurin dora ta a cinyar sa, a cewarshi ta zama komai nasa ita din rayuwarsa ce domin ko rabin hallacin data masa baya tunanin zai biya ta, duk da a da yaji haushin mami ko yace tsana akan wahalar masa da Mata da tayi amma ya manta ya kuma hakura, tunda ita wacce aka wa ta yafe, shima dolen sa ya manta komai...


★★★

A Yanzu faheemah na fama da yawan bacci ga zazzabi, Ganin kullum tana fama da zazzabi musamman cikin dare ta dinga kuka kenan, idan an wayi gari kuma ta tashi garau, ba bata lokaci ya shirya ta washegari suka je asibiti gwajin farko ya nuna tana da shigar ciki na wata biyu, sosai fu'ad yayi murna rungumeta yayi a office din Likita ya Shiga bata Sumba ta, sai da Likita ya yi gyaran kana yace

"toh lovers bird Ku zauna na muku bayanin yanda zaku kula da babyn Ku"...


ai tun a hanya ya hanata sakat sai faman shafa cikinta yake, sai da tace ya kula kada ya zubesu a titi kana ya bari amma still duk minti daya sai ya juyo ya kalleta, sarai tana lura da shi sai dai ta yi murmushi kawai.


Tun a hanya ya fara sanar da mutune Cikin harda Ummu, abbuh, sai anwar daya dinga masa tsiya wai su zama daddy bai saurareshi ba ya katse kiran.


★★

Anyi bikin su fareesa da anwar dinta, wanda ta tare a hadadiyar gidan su dake nasara gra wanda gidan mallakin fu'ad ne, ya kuma bar masa halak malak bawai dan ba shida kudin yin gini ko siyan gida ba, a'a a cewar fu'ad sun wuce abokai sai dai yan'uwan juna. ya kuma ce baya son barin Ummu shi yafi son zama kusa da mahaifiyar sa, haka ma faheemah na goyon bayan hakan.



Ai faheemah cikin mugun cin abinci yake sa ta, ga kuma cin yaci, yajin ma sai Mai tafarnuwa take so, kullum haka yake fama da ita daya dauke yajin sai ta sakar masa kukan shagwaba domin yanzu sai abinda ya karu a shagwaba, baya son kukan sai ya ajiye mata yace duk laifin Ummu ne dake sa a daka Mata yajin.


Yanzu cikin Jameela ya shiga watan haihu kuma har yanzu babu wani labari daga wurin salman.


Bayan kwana biyu ta fara nakuda kuma abbuh da Kansa ya kai ta asibiti domin yayi tawakkalli kuma ya yafe Mata.


Babu bata lokaci ta haihu da na miji mai Kama da salman sak, sai dai kafin a sallamo su dan ya yace ga garin ku nan.

Sosai tayi kuka domin taso ta raini dan nata, duk da cewa ta tsani ko da jin sunan salman yanzu, faheemah dake fama da cikin ta Ita ce mai rarrashin ta har tayi shiru.



*** *** ***



*Bayan wata biyar*

faheemah ta fara nakuda, sosai taji jiki domin nakud'an kwana uku tayi, wanda fu'ad ya shiga damuwa har kuka yayi, domin ya tausaya mata sosai, Ummu ce mai karfin halin rarrashin shi....






Share and comments


Thanks for reading my novel


Noor Eemaan🥀🌸
07082281566

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



💔RAYUWAR FAHEEMAH💔


Wanna littafina kyauta ne (free novel)



#Ending



69-70

(Not edited)


A cikin daren rana ta ukun ne ta haifi yan biyu mace da Namiji, zuwa lokacin ta galabaita domin ko motsi bata iya wa, sai da safe bayan anyi wa babies wanka da mummyn su aka Shigar dasu dakin hutun.

Sai a lokacin aka bawa su Ummu damar Shiga, ai fu'ad na Shiga wurin matarsa ya nufa. "faheee ta are you okay? Mike miki ciwo yanzu sannu wiffy! Yanzu me zaki ci"

Ya tambayeta Cikin alamun damuwa, riko hannu sa dake kan fuskar ta tayi kana ta ce "my maaan wacce tambaya kakeso na amsa maka yanzu?"



"Dukkan su Wiffy, I just want to be sure if you are ok"

"Am fine zauj, am very fine"

Murmushi jin dadi yayi Kana ya bata light kiss a lips dinta da suka yi jaa saboda walahan nakuda. Lolz.


Dan zaro ido tayi ganin yayi kissing dinta a a gaban ummu, kallo ummu tayi taga sam hankalinta na ga twins ajiyar zuciya ta sauke, dariya ta bashi yana tunanin ko yaushe zata daina kunyar nan mai yawa, duk da yana son kunyar ta

Ummu ce ta miko masa baby girl din, kura mata ido yayi yana jin matsananci soyaayar ta na ratsa shi, Namijin Ummu ta sake Dora masa a cinya, ai dariyan farinciki yayi, dukkan su Kama suke dashi kamar yayi kaki.
Haka kuma soyaayar yaran sai ratsa zuciyar sa take, godiya yayi ga Allah daya bashi kyautan yara har biyu at once.


"Fahee na miki wayo babu wanda ya yo ki a babies dina" Yafada yana mata gwalo.
Dariya Ummu da fareesa sukayi har da anwar da ya kawo fareesan Yanzu.

Kwabe fuska tayi kana a hankali yadda su biyu kadai zasu ji tace "zan rama nima next" kashe mata ido daya yayi yana dariyar tsokana.

Kasancewar lafiyar su lau yasa aka basu sallama, direct gidan suka nufa domin abbuh yace ta zauna a gidan ta zai fi tunda ba addini bane yace lallai sai mace tazo gida wanka, baya ga haka yasan cewar Ummu zata kula da ita kamar yar da ta haifa, sosai hakan yayi wa fu'ad dadi, domin daman yasa a ransa idan ma aka ce zata je gidan su murje ido zai yi yace bai amince ba.
Hakan yasa Mami tace zata je gidan ta taya Ummu kula da faheemah'n.
Duk da bakomai zata iya yi ba saboda hannunta daya, amma abbuh yaji dadi kwarai, ya kuma yarda lallai mami ta tuban gaske.



Ranar suna yaran suka ci sunan baban fu'ad ( Omar) da kuma sunan Ummin faheemah ( Haleematusa'adiyya ) amma za'a dinga ce musu Ayman da Aymana.
Sosai faheemah taji dadi haka ma abbuh domin fu'ad yayi musu Kara.



Sai da suka yi arba'in, kana mami ta koma gida.


Jameela ta hadu da sani a lokacin da mami ta aiki ta kasuwa. yi yayi kamar bai ganta ba, saurin shan gaban sa tayi ta roki shi gafara, kasancewar shi mai sanyin hali yasa shi yafe mata domin yana da labarin duk abunda ya sameta. cikin wata daya suka sake saba wa kasancewar har yanzu akwai tsohuwar soyaaya yasa suka daidai ta Kansu domin daman kwadayi ya sa ta bar shi, bai boye mata yana da aure da yarinya daya ba, ta amince masa, ta fara kokarin gaya masa haduwarsu da salman ya dakatar da ita kana yace mata ya san komai, hakan ya bata mamaki kwarai, bayan wata daya aka daura musu aure ta tare a gidansa Wanda kuma alhamdulillah suna zaune lafiya da kishiyar ta.


★★★


Zuwa yanzu FAHEEMAH ta Fara zuwa northwest university dake kano (YUMSUK)
domin tace tafi sha'awar yin karatu a kasar ta, Kuma jihar ta.
a ranar da zata fara zuwa fu'ad ya bata kyautar had'add'iyar mota mai kalan ja, a cewar shi duk ranar da yake busy sai ta kai kanta school domin baya son ta hau mota driver ya tuka ta, yayin da lUmmu ke kula da yan jikokin ta tareda taimakon masu aiki.

Karatunta take cikin kwanciyar hankali haka kuma tana samun support din gwarzon mijinta....


Fu'ad ya ginawa faheemah katon supermarket mai dauke da sunanta. ranar ya shirya mata surprise domin bata da labari, yana tsayar da motar ya fito hadi da zagayawa ya bude mata kofa, bayan ta fito yace "look up faheeeta" daga manyan idanunta tayi taga an rubuta *FAHEEMAH SUPERSTORE* ai wata runguma ta masa ta shiga zuba masa godiya, sauri sa hannunsa yayi a lips dinta alamun bayaso, Sosai tayi murna mara misaltawa, domin bayan sun shiga har staffs din wani girmamawa na musamman suke bata, har office dinta ya nuna mata gwanin kyau... A ranar ta faranta masa sosai domin nuna godiyar ta agareshi.


Bikin umaimah saura sati biyu, har gida ta kawo wa fu'ad katin aurenta, ta kuma sake neman yafiyar su, sun kuma yafe mata domin sosai faheemah ta lallabashi kafin ma ya yarda ya fito.

Da za ta tafi fu'ad ya bata 1million a matsayin wedding gift dinta, wanda faheemah taji dadin yanda ya manta komai, Shiyasa take alfahari da gwarzon mijinta a kodayaushe...



Washegari faheemah da fu'ad suka je gidan malam haroon dake kurna, domin sun bar yan biyu wa kakar su( ummuh) Sosai malam haroon yayi murna bayan fu'ad ya gaya masa cewa abbuh ya dawo tunaninsa, daza su tafi fu'ad ya bashi bandir daya na 1k ya dinga shi musu albarka.



*4month later*

Cikin kuzari suke excerise a dakin motsa jiki dake part ɗin su, gaba daya sun hada gumi a sakamakon excerise din, tana bangaren kayan training din mata, yayin da shi ma yake bangaren kayan training din maza, cikin kwarewa yake daga karfe yayin da duka faffadan kafadunsa sun fito, ga babies kwance cikin Walker dinsu suna ta wutsil wutsil da kafa, after 30minutes faheemah ta sauko yayin da shima ya ajiye karfen, ruwan gora mai sanyi ya balle murfin ya sha rabi hadi da Sanya mata rabin a baki ta shanye tana sauke numfashi, murmushi yayi kana cikin tsokana yace

" raguwa"


bubbuga kafafu ta Shiga yi cikin shagwaba, saurin hade bakinsu yayi kana ya dauke ta cak kamar baby doll domin duk da ta haihu jikin ta na nan da kyaunsa kamar ba ita ta haifi cute babies din nan ba.

Aymana ce ta fara kuka a hankali ya xare bakinsa, ya jawo hannu ta kana ya zaunar da ita a sofa dake gyming room din, dauko aymana yayi ya Dora mata a cinyar ta kana ya daga half- vest dinta da Kansa ya sanya wa yarinyar, ta kama mama ta fara sha, ayman ya dauko shima ya Sanya masa a baki ya fara tsotsa.

Kwabe fuska tayi kana kalli fu'ad ta ce "Allah my man Aymana ta fiye ci, abbana ya fita hakuri"

murmushi yayi kana yace "bar min ummina ta ci please, baya ga haka inason ganin kina basu mama ,you look more beautiful than ever goofy angel"

Murmushi tayi kana tace
"I so much love you my man, the father of my children".

shima yace "I love you too Mrs fu'ad you are my everything"

Murmushi ta sake yi kana tace "Allah yabar mu tare har a aljanna domin kai din tamkar GARKUWA ne a *RAYUWAR FAHEEMAH*"
ta fada tana sakar masa kyakyawar murmushin ta, shi ma cutest smile dinsa ya sakar mata idanunsa cike da mayen soyaayar ta ya sake cewa
" I love you" hadi da bata Peck a goshinta dake cike da gashi kwatance kamar na jirarai.

Zagayo wa yayi ta bayan su kana ya dauke su Selfie da wayar sa fuskarsu cike da annushuwa.




*Nasan zaku ce ban kuma sako labarin salman ba. Kwarai hakan na faruwa a rayuwa kaga mutum ya shigo rayuwar ka da sharri ko alkhari , amma kuma ba lallai bane ka sake ganin shi, wani hisabin sai a lahira kawai. Allah yasa mudace*




ALHAMDULILLAH
THE END.





Special thanks to Abdul_rasheed mustapha (budu mie) for the support.


Special thanks to:

Sawun Giwa novels

S square novels

Noor Novelist world

Sarautau's library

Fitar rana group

Surrayhms novels

Nana haleema palace

Fadar Ummu Affan

Daular dalingo

Matan buri fans

wallahi groups din da yawa, time ba zai bani damar lissafo ku ba, amma ina godiya agare ku gaba-daya, Allah ya bar kauna.




*Kuyi hakuri banyi editing wasu wurare a book din ba saboda wasu uzurori nawa, so idan kunga typing error ku min afuwa, sannan wanna shine littafina na farko, shi na fara rubutawa kafin na yi mijin Ammi na ne sila, papi ne, kyautar koda, Abraham, Hoorain mai kusumbi. Na kuma ngd da yanda kuka karbi Novel ɗin, duk da kara reposting din shi nayi*🥰



Anan na kawo karshen book dina mai suna RAYUWAR FAHEEMAH kurakuran Dana yi a ciki Allah ya yafe min da ma Wanda ya karanta, Wanda nayi daidai Allah ya hadu mu a ladan (ameen).






Ban yarda a juyamin labari nan ta kowacce siga ba, idan kunne ya ji......



⚠️RAYUWAR FAHEEMAH
Hakkin mallakan NoorEemaan ne⚠️




All characters in this story are all drawn from my imagination any resemblance of story or life style should be considered as a coincidence.


Allah ya karbi ibadun mu a wanna watan radaman din da muka shigo Allah ya sa muyi ibada karbabiyya ameen.



Gaisuwa dubu ga masoyana a duk inda kuke, Noor na muku sahihiyar kauna💞




I love my fans
07082281566



https://facebook.com/groups/943534712916776/


I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851





An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment