Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta shiga yi, amma ta Kasa magana.

Murmushi ummu tayi domin sarai ta fahimci nufinta,

"diyata ku wuce gida ki huta kinji gobe saiku dawo"


matsawa jikin fareesa tayi ta mata rada akunne, dariya fareesa tayi hadi da kamo a hannu ummu," ai ummu yar ki ta huta sheki mu wuce abunmu kawai"



kunya ce ta kama Faheemah ta gudu ta shige dakin dayake...


Murmushi suka bita dashi, kana fareesa ta shige ta dauko abinda yadace a mayar gida,"

" toh matar brotherna a kula dashi sosai mu mun tafi, asha soyaaya lafiya" tafada cikin tsokana, kasa faheemah tayi da kanta tana murmushi har ta fice....


Kusa dashi ta kwanta bayan ta canza kaya zuwa wata doguwar riga mara nauyi mai gajeran hannu, kasancewar gadon babba ne yasa ya ishe su, kallon kyakyawar fuskarsa take, yayinda idanunsa ke a rufe hakan yasa ta ganin zararan eyelashes dinsa, hannu takai ta shiga wasa da eyelashes din, ahaka har bacci ya dauketa...



karfe 2:00 nadare ta farka da salati abakinta ganin a hanunta afuskarsa yasa ta zarewa ahankali tana murmushi. Domin wani mafarki mai dadi tayi a kansa, kallonsa tayi taga idanunsa arufe, taba diaper dinsa tayi taga ya cika, Allah ma yasa bai bata short nicker dinsa ba. Canza masa tayi, kana ta dauro alwala tashiga kai Kukanta ga rabbil samawati, addu'a sosai tayi akan Allah ya bawa fu'ad lafiya, sanna tayiwa umminta, sai kuma tayi akan Allah ya adaidaita tsakaninta da abbuh, sanna tayiwa sauran Muslims ummah, da asuba ta daura masa alwala, kana ta shiga wanka hadi da yin brush, ta shirya cikin riga ta skirt, sosai tayi kyau domin zuwa yanzu fatarta tayi kara kyau sosai.

Shima brush tamasa hadi da goge masa jikinsa kana ta canza masa kaya hadi da feshe su da turare mai dadin kamshi, jin za'a shigo dakin yasa ta yafa mayafi golden color, doctor ne ya shigo ya duba shi , sanna ya fita.
Dakamar 15minutes ummu suka shigo tareda da Fareesa, "kaga matar brotherna irin wanna kwalliyar dakuka sha haka sai kace ba za'a mutum ba" Cewar Fareesa cikin shekiyanci.


Kamar kasa ya bude ta shige haka Faheemah taji duk da ta san fareesa mutum ce mai barkwanci amma ta Kasa sabawa har yanzu, duka ummu takai mata kana tace " Fareesa kibarmun yarinya ta huta" kaucewa dukan tayi tana dariya.
"Ummu ina kwana" cewar faheemah a ladabce, kana ta kalli fareesa ta gaisheta, duk amsawa suka yi cikin kulawa.....


Share
Comment



Thanks for reading my novel #rayuwar faheemah.


💔RAYUWAR FAHEEMAH 💔

_by NoorEemaan_📚✍️
kyautane (free novel)

"It is not the eyes that are blind, but the hearts." Qur'an 22:46


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


*Like i said earlier wanna shine novel dina na farko dana fara rubutawa, kafin na rubuta mijin Ammin ne sila, PAPI ne, Abraham, kyautar koda da Hoorain mai kusumbi rayuwar Faheemah shi na fara rubutawa, but funny a enough lokacin banda group na novel ko ɗaya, that was 2021, hakan yasa nake kara reposting din shi yanzu domin zan zo ku karanta saboda darasin cikin book din, dan Allah ki fara bi yanzu, kar sai nayi nisa sosai a ce daga farko*🥺😫🥰




19-20

(Not edited)


"Diyata faheemah kin duba result dinki kuwa?"



"A'a ummu"


" ok zan duba miki in sha Allahu , kin taho da exam card?"


"Eh" ta amsa cikin sanyinta...


★★★

Washegari bayan ta gama shirya shi kamar kullum, sai wani tunanin yazo mata, "Anya yana shan ruwa kuwa? Domin tunda nafara kula dashi ban bashi ruwa ba, haka ma banga Ummu ta bashi ba" fada abayyane..

Kitchen ta nufa ta dauko table water ta shiga bashi sosai kuwa ya sha ruwan, cikin tausayawa tace

"Allah sarki bawan Allah, kayi hakuri kaji? Amma meyasa baka nuna min alaman zaka sha ruwa ba?"

Tafada tana turo baki hadi da shafa suman kansa, da alama ta manta da baya magana, kafin zuwa azahar tabashi ruwa yakai roba shida babban gora.

Na karshen data bashi sai taga ruwan nabin hanjinsa da bakinsa sai kuma taga idanunsa na juyewa ba'a ganin bakin sai farin....

Sosai hankalinta ya tashi, meke damunka? Kadaina wanna abun kana bani tsoro tafada hawaye nazubo mata, ya fu'ad please kadaina kaji?

Ta cigaba ta jijjigasa, ganin ruwan bai daina fita a hancin da bakinsa bane yasa ta fita da gudu...



ummu na azaune aparlour sanye da medicated glass tana aiki a system kasancewar weekend ne.

Tana zuwa taja ahannu ummu, batare da tace komai ba zuwa dakin....

Ganin robobbin ruwa da yawa adakin, ga kuma halin data ga fu'ad din aciki yasa gabanta faduwa. Amma dan ta tabattar sai tace


"diyata faheemah kin bashi ruwa ne"?

A tsorace ta Ɗaga kai alamun

"eh"

tana mai toshe bakinta saboda kukan dake kokarin kubce mata.

Cikin gaggawa ummu ta lalubo wayar asibitin dasuke zuwa ta kirasu takuma ta gaya musu emergency ne..



Cikin 15minutes suka Kara so ,hadi da shigowa domin tafiya dashi cikin sauri da sanin makaman aikin ma'aikanta suka daukesa domin zuwa hospital...


Gaba daya Ma'aikantan gidan hankalinsu ya tashi musamman ma dasuka ga faheemah na kuka.


"dauko hijab dinki mu bisu"

duk da ummu bata nuna wani alama najin haushi ba, amma sosai taji tsoron ummun na shigarta, hijabi ta dauko tabi bayan ummu asanyaye.



Da isar su asibiti har an shigar da shi. Sai bayan 2hrs doctor usman ya fito yana share gumi, fuskarsa a daure yace wa ummu ta biyosa office.



Gaban faheemah ya bada ras, to me ummu zata masa? Kodai ya mutu ne?

"Innalilahi wa innah ilaihi raju'un! in sha Allah bazaka mutu yanzu ba, doctor kar ka ce wani abu ya sameshi, wayyo Allah ya fu'ad na"



ta fada batare da ta san maganar ta fito fili ba., sosai taba likitan dariya domin da yana cikin Good mood ba abinda zai hanashi dariya ko wa yace mata ya mutu ne oho?


"Please hajiya meet me at my office"

ya fada yana juyawa cikin tafiyar sauri daman maganar Faheemah ce ta tsayar dashi.


" Diyata Faheemah ki kwantar da hankalinki zauna ina zuwa"


ummu ta fada tana juyawa, domin itama fargaba ne fal ranta tana aro jarumta ne kawai.

"Hajiya kinsan lalurar fu'ad baya bukatan ana bashi abu mai ruwa sosai, idan ma za'a bashi once in a while ne, kuma bamai yawa ba"

yafada yana kokarin sauke temper dinsa domin sosai ranshi ya baci.



"Doctor usman akasi a kasamu matarsa ce ta bashi ruwan wallahi itama bata sani, ni kuma na manta ban sanar da ita ba"

cewar ummu asanyaye domin bata fatan wani abu ya samu danta mafi soyuwa a gareta.


" ni da abokan aikinka munyi iya kokarin mu kuma alhamdulillah cikin yardar Allah yadawo daidai amma zamu rike ku asibiti na sati daya domin sake tabattar da saukinsa"

"Okay doctor nagode, zamu iya ganinsa?"

" Eh kada ayi hayaniya please hajiya, jinjina kai ummu tayi kana ta fito"


Zaune ta tarar da ita tana kuka

"Diyata bazaki bar kukan nan haka ba?"

"Ummu kiyi hakuri Wallahi bansan cewa ba..ba'a bashi ru...wa... ba"
ta fada cikin muryanta dake cracking"

"nasani diyata laifi nane daban sanar dake ba, kibar kukan mijinki na nan da lafiyarsa kinji?"

Ajiyar xuciya tasauke da sautin sa ya fito, jikin ummu tafada tana sakin kananun kuka sosai taji tsoro, domin zuciya bata da kashi, bata so ummu tayi wani tunani daban. Kuma a yanda ta shaku dashi, duk da a kwance yake baya magana, amma sosai take jin dadi kasancewa dashi.


"Tashi mu shiga amma sai kinyi shiru domin doctor yace ba hayaniya" hadiye kukan tayi suka shiga


idanunsa abude suke, Kallonshi take tana jin wani abu mai girma na ratsa zuciyarta gami dashi.


Gaban gadon ta karasa ta riko hannayensa duka biyu, "dan Allah kayi hakuri, wallahi bansaniba kayafemin Kajiii danaga ina baka ruwan kana sha I thought sosai kakejin kishiruwa, shiyasa nayi ta baka, bazan sake ba ya Fu'ad" ta karasa cikin yanayi na kuka da shagwaba.



Murmushi ummu keyi dake nuna zallan farinciki ganin yanda faheemah ke nuna concern dinta akan danta, ganin faheemah ta manta da ita adakin ne yasa ta fice domin kiran fareesa ta kawo abubuwan bukata tunda kwana ya kamasu, kasancewar lokacin da suko taho tana school.


Bayan 40min sai ga fareesa da tare da masu aiki, ta kaya Niki -Niki, ahankalinta a tashe amma ganin jikin yayanta da kyau, yasa hankalinta kwanciya, masu aiki ma gaisuwa su ka wa ummu, ta amsa cikin kulawa, sanna suka tafi...



Bayan isha a kace mutum daya ne zai iya kwana da mara lafiya domin ka'idar asibitin ne, ummu cewa tayi su tafi gida ita zata kwana, ai matso kwalla faheemah ta shiga yi, amma ta Kasa magana.

Murmushi ummu tayi domin sarai ta fahimci nufinta,

"diyata ku wuce gida ki huta kinji gobe saiku dawo"


matsawa jikin fareesa tayi ta mata rada akunne, dariya fareesa tayi hadi da kamo a hannu ummu," ai ummu yar ki ta huta sheki mu wuce abunmu kawai"



kunya ce ta kama Faheemah ta gudu ta shige dakin dayake...


Murmushi suka bita dashi, kana fareesa ta shige ta dauko abinda yadace a mayar gida,"

" toh matar brotherna a kula dashi sosai mu mun tafi, asha soyaaya lafiya" tafada cikin tsokana, kasa faheemah tayi da kanta tana murmushi har ta fice....


Kusa dashi ta kwanta bayan ta canza kaya zuwa wata doguwar riga mara nauyi mai gajeran hannu, kasancewar gadon babba ne yasa ya ishe su, kallon kyakyawar fuskarsa take, yayinda idanunsa ke a rufe hakan yasa ta ganin zararan eyelashes dinsa, hannu takai ta shiga wasa da eyelashes din, ahaka har bacci ya dauketa...



karfe 2:00 nadare ta farka da salati abakinta ganin a hanunta afuskarsa yasa ta zarewa ahankali tana murmushi. Domin wani mafarki mai dadi tayi a kansa, kallonsa tayi taga idanunsa arufe, taba diaper dinsa tayi taga ya cika, Allah ma yasa bai bata short nicker dinsa ba. Canza masa tayi, kana ta dauro alwala tashiga kai Kukanta ga rabbil samawati, addu'a sosai tayi akan Allah ya bawa fu'ad lafiya, sanna tayiwa umminta, sai kuma tayi akan Allah ya adaidaita tsakaninta da abbuh, sanna tayiwa sauran Muslims ummah, da asuba ta daura masa alwala, kana ta shiga wanka hadi da yin brush, ta shirya cikin riga ta skirt, sosai tayi kyau domin zuwa yanzu fatarta tayi kara kyau sosai.

Shima brush tamasa hadi da goge masa jikinsa kana ta canza masa kaya hadi da feshe su da turare mai dadin kamshi, jin za'a shigo dakin yasa ta yafa mayafi golden color, doctor ne ya shigo ya duba shi , sanna ya fita.
Dakamar 15minutes ummu suka shigo tareda da Fareesa, "kaga matar brotherna irin wanna kwalliyar dakuka sha haka sai kace ba za'a mutum ba" Cewar Fareesa cikin shekiyanci.


Kamar kasa ya bude ta shige haka Faheemah taji duk da ta san fareesa mutum ce mai barkwanci amma ta Kasa sabawa har yanzu, duka ummu takai mata kana tace " Fareesa kibarmun yarinya ta huta" kaucewa dukan tayi tana dariya.
"Ummu ina kwana" cewar faheemah a ladabce, kana ta kalli fareesa ta gaisheta, duk amsawa suka yi cikin kulawa.....


Share
Comment



Thanks for reading my novel #rayuwar faheemah.
💔RAYUWAR FAHEEMAH 💔


_by Noor Eemaan_


kyauta ne( free novel)



When two people meet each other. Who should greet first with peace? The prophet Muhammad s. a.w said; the one closet to Allah will greet first.


21-22

(Not edited)




Breakfast sukayi dukkan su, bayan sun gama ne, Faheemah ta bashi kunun da su ummu suka kawo ya sha, haka suka wuni asibiti har dare.....




Washegari abokin fu'ad anwar ya duro kasar, direct gidan ummu ya nufa, domin yana son yimusu *suprise* sanar dashi ma'aikatan gidan suka yi suna asibiti...


Hankalinsa a tashe ya isa asibitin ya kira ummu a waya, mamaki tayi ganin numbern Nigeria

"anwar yaushe agari?"

"Yanzunan ummu isowata kenan ina asibitin, wani ward kuke"?

Fadamasa tayi cikin abinda baifi 3minutes ba ya shiga dakin, bakinsa dauke da sallama

Amsawa dukkan su, sukayi yayinda yayi hugging ummu hadi da gaisheta, amsawa tayi tana tambayarsa ya ya iso...


"lafiya alhamdulillah"
ya amsa Kana ya karasa gadon da Fu'ad yake, idanunsa kuri a kan anwar sai dai ba Bakin magana, "dude!" ya kira shi hadi da kamo a/hannayensa cikin nasa alamun musaba'a...


" ina wuni"

yaji wata zazzakar murya ta fada domin ta gane shi, shi ne wanda tagani a photo album ne dake dakin fu'ad

amsawa yayi fuskarsa da alamun tambaya, ummu ce tace,

"matar fu'ad ce fa"

sosai yayi mamaki daman akwai wacce zata yarda ta auri babban amininsa? dama akwai sauran masu kyakyawar zuciya aduniya?

Cikin farinciki yace " ummunah how comes u didn't tell about this all this while "

ya fada fuskarsa dauke da madukakiyar fara'a.


"Ai so nake na maka suprise kamar yanda kamana zuwan bazata"

cewar ummu cikin zolayan daya kasance tamkar dabi'arta...
Dariya yayi kana ya kalli faheemah

"Mrs Fu'ad mun gode fa sosai Allah ya baku zuri'a masu albarka".

"Da ameen" ummu ta amsa, yayinda faheemah kanta ke kasa tana murmushi


*** Juyowa yayi ya kalli fareesa dake zaune kamar ruwa ya cinyeta "ke parrot (aku) babu gaisuwa?"

Yafada fuska a dan daure, "ina wuni" tafada kamar an mata dole, "saida na roka, rike kayanki?"

Cikin kunkunni tace " Shikenan yazo kenan zai takurawa mutane"

" mekika?"

" Cewa nayi ya anwar ya hanya?"

" Lafiya"

ya amsa atakaice, kana suka shiga hiran duniya shida ummu.

Bayan 2hrs anwar yace zaije gida xuwa yamma zai dawo, adawo lafiya suka masa, kana ummu tace "a gaida min hajiya sa'a"

"toh ummu xataji, amma bata san kuna asibiti bako?"

"Toh anwar lalurar nan kusan 6 years yake yinta, so banga dalilin dazai sa ayita tayarwa da jama'a hankali ba idan jikin yatashi"

cewar ummu murya a karye, domin sosai take jin ba dadi ganin fu'ad din a kwance...

" hakane ummu, in sha Allahu komai zai wuce, Allah yasa anwar maza kaje gida kahuta sai ko dawo".


Da yamma sai ga anwar tareda mummyn sa "hajiya sa'a, yanzu anwar sai daka taso matar nan kuka taho?"

Murmushi yayi daya bayyana jerarun hakoransa, hajiya sa'a kuwa zama tayi tana kallo fu'ad kana tace

" ango ka sha kamshi sai kace bamai jinya ba da alama 'yar tawa tana kulawa da kai"

dariya suka sanya gabadaya domin hajiya sa'a ma ba baya ba wurin zolaya, kasa faheemah ta sauka ta gaisheta hakama fareesa, amsawa tayi cikin kulawa, kana suka gaisa da ummu. "Allah dai yayi miki albarka yar nan hakika na yaba miki sosai, ai da anwar ya fada na karyata, naxata tsokanar ce ta mosa, murmushi ummu tayi kana ta shiga bata labarin abinda yadace tasani...

Sai bayan isha suka bar asibitin dukkansu har da su ummu, shirya shi faheemah tayi domin su kwanta, hannunsa ta kamo ta kura masa ido, wani feelings da bata san kona menene ba yana ratsa ta, wani lokacin takan yi tunanin idan Allah yabashi lafiya ya ki ta amatsayin mata fa? Yaya zatayi? Domin ta shaku dashi matukar, bata fatan abunda zai raba su.


Sai kuma tafashe da kuka tuno da abbuhn ta , domin sosai take jin kewar gidansu, lokuta da dama takan ji kewa hadi da radadin rashin yan gidansu dabasu nuna damuwarsu akanta ba, saidai takan boye damuwarta domin batason su ummu suga kamar ta raina ko kuma bata appreciating kulawan dasuke bata, haka ta cigaba da kukanta har bacci ya dauketa tafada jikinsa batare da ta sani ba, karfe dayan dare ta farka ganinta ajikinsa yasa ta kallonsa, idanunsa abude kuma sun yi dan ja, yunkurawa tayi ta mike zaune cikin muryan bacci tace masa "kayi bacci kaji" hannu tasa ta rufe masa idanu wai dole sai yayi bacci. Sake bude idanunsa yayi, ganin hakan yasa ta turo baki, cikin sakalci tace

"bazaka yi bacci ba? dare yayi faa ka yi bacci Kaji"

ta fada tana bubuga bayansa.... Bayan kamar minti ashirin ta leka fuskarsa taga taga idanunsa arufe, Murmushi tayi kana tace " lah Ya fu'ad badai jin magana ba" lolz

Haka suka kasance asibitin har aka sallamesu suka dawo gida.


"Ummu meye amfani mun dan Allah idan baki huta ba? na tabattar da'ace aminina na da lafiya nasan bazai bari ki ta zuwa company kullum ba. Saboda haka dan Allah kibari nacigaba da kula da company din, kuma zan samo amintatun wandanda zasu iya kula da company's din koda babu idanun ki, kinji ummu ki amince" cewar anwar cikin magiya.

Murmushi ummu tayi kana tace wanna magiyar na menene? Kafin tafiyarka kasar waje kaini mai kula da company din, so banada da shakku akanka nagode kwarai dan albarka"
Murmushi jin dadi yayi.

" wani hanzari ba gudu ba anwar"

cewar ummu, kana ta dora da cewa " to yazaka yi da zuwa duba masu aikin ka?"

"Ummu akwai manager na gidan man zai kula komai, koda bana nan, idan ma wani abu ne ya taso zasu kirani sai inje".


Anwar na da gidan mai suna AAG Oil&gas Nigeria limited, akwai daya a sharada, akwai daya a kabuga. Mass communication ya Karanta, dadynsa ya samo mai aiki a babban gidan TV, amma yace bayaso, su ma yan gidan tv sunso daukarsa aiki domin awaje yayi Karatunsa gashi result dinsa Masha Allah wanda anan ne suka hadu da fu'ad amma yaki, acewarsa yafi son sana'a.
Wanna kenan!



Washegari ummu tasa faheemah dauko mata exam-card dinta. Da kanta tayi driving domin zuwa cafe. Result yayi kyau Masha Allah yan cafen sai yaba result din suke, akan yakarawa ummu jin dadi, bayan ta dawo ne ta shigo dakin da fu'ad yake....

Faheemah kuwa ganin ummu ta wasu papers hannunta yasa gabanta faduwa, Domin bata so taji ta fadi jarabawar nan, duvet ta ida rufawa fu'ad da idanunsa ke a rufe.

Kana ta karasa gaban ummu, cikin sanyin amon murya tace

"ummunah nafadi ko"?

Mika mata takardda biyun ummu tayi, asanyaye ta amsa ta shiga dubawa waec dinta 9credit yayinda neco taci 8credit hausa ni tasamu d7.

Ai bata san sanda ta rungumi ummu ba cikin farinciki, "wayyo ummu! Wayyo dadi!! Wai nikeda wanna kyakyawan result din?"


"Alhamdulillah ya Allah nagode maka"

" Allahu shine abun godiya" cewar ummu tana bubuga bayanta.

Zamewa kasa tayi zata yiwa ummu godiya, mikar ta ita tsaye ummu tayi kana tace, "kul, babu godiya atsakaninmu kin manta ke diyata ce? Sanna in sha Allahu zaki cigaba da karatu har sai kince ya isheki"

Murmushi mai sauti faheemah tayi tana jin kaunar matar na ratsa zuciyarta, domin ta cancanci a so ta Saboda kyakyawar zuciyarta...


Ummu na barin dakin tafada kan bawan Allah tana tsalla tsallanta ajikinsa da alama ta manta mara lafiya ne. Tallafo fuskarsa tayi cikin farinciki sosai tace " ya fu'ad katayani murna kaga result dina kuwa"? Tafada tana sake fadawa jikinsa...


Fareesa ma data samu labari bayan ta dawo sosai tayi mata murna . domin abinci na musamman ummu tasa aka shirya aranar harda baking cake, ummu tayi hakan domin sa faheemah farinciki...

Suna gama cin abinci anwar ya iso Saboda wani maganar business daza su yi da ummu.

Gaishesa faheemah tayi ya amsa cikin kulawa domin sosai yake ganin kimarta.

Fareesa gudun karta yi laifi yasa tace "ina wuni" amsawa yayi kana ya gaida ummu tareda gaya masa abunda ke tafe dashi wanda na karuwar company ne.

Bayan su gama ya shiga ya duba jikin anwar, kana ya fito yace

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment