Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karfe 9:00pm daidai na dare zuwa lokaci wayoyin duk sun cika yanda ake bukata.
Miko mata ta ta yayi, hannun ta sa ta amsa aranta ta fadin

"wai nice da tsaleliyyar waya?
abunda kafin haduwar ta dasu ummu, bata taba tunanin samu a wanna lokacin ba, Allah nogode maka bisa ni'imarka gareni"


Wanka ya fito yana daure da bathrobe fari ajikinsa.

" je kiyi wanka mu kwanta akwai tashin dare"

mikewa tayi domin cika umarnin sa, domin tana matukar jin dadi ibadar dasuke cikin dare, hakan na rage kaso 80% daga cikin damuwarta domin addu'ar ta akullum Allah ya dawo da
Hankalin abbu gareta, haka kuma tun lokacin dasuke yi takan ji Sanyi hadi da nutsuwa azuciyarta....


haka zaki shiga wanka da kaya?"

Yafada yana kallo A Shape gown dinta mai kalan fari sai flowers bakake ajikin

"A'a zan cire aciki"

tafada tana saurin shiga toilet din.

Murmushi yayi kana ya tabe baki a bayyane yace "funny girl"



Ruwa mai dan zafi ta hada cikin Bathtub din kana ta shiga tana lumshe ido domin ruwan ya mata dadi sosai, a kalla ta dau 15minutes kana ta fito, saida ta fito ta tuna cewa bata dauko hijab ba, bathrobe red color ta dauka tana tunanin fita ahaka, dabara ce ta fado mata, rigar data cire tadaura wanna hakan yadan suturta jikin ta domin ya sauko zuwa cinyarta, cikin sanda ta shiga fitowa, ajiyar zuciya ta sauke ganin baya dakin, sai kuma tayi dariya tace

"Allah ya shiryeni ni Faheemah"

saboda tuno yanda take sanda kamar mara gaskiya.


Agurguce ta shiga shiryawa light green din wata doguwa riga mara nauyi tasa domin mutum zaiyi baccin sa babu takura.



Tana kokarin daura cap a kanta, ya shigo zubawa cikakken gashinta dake da tsaho sosai...



"Masha Allah" ya furta aransa. Domin yana matukar son mace mai gashi.


Faheemah kuwa sai kokarin cusa gashi take yaki shigan hulan duka, dama haka take fama saboda yawansa da tsayinsa.


" may I help you" yace cikin cool voice


tace "yes please!"

takowa yayi zuwa gareta " sit " ya sake cemata, zama tayi akujerar dake gaban dressing mirror.


Tattara gashin ya shiga yi wanda da kyar ya shige cikin hula saboda yawa.


"Nagode ya Fu'ad"


"don't mentioned faheee"

yace kana sanar da ita ta shirya kayanta gobe zuwa jibi zasu koma part dinsa, bai jira amsar ta ba, ya haye gado ya kwanta....




Ita kuma gabanta ne yafadi, tayaya zata jure zama dashi a flat daya? Shin baisan yadda take matukar jin nauyinsa bane? Tunda ya samu sauki take jin shi kamar bako, duk da yanda sonsa dake nukurkusan zuciyarta kuwa.


Ba ummu, ba Fareesa sai su Kadai? ita kam tafison zama tareda su ummu. Duk da kuwa cikin gida daya ne amma nan din yafi mata. Haka ta shiga motso kananun hawaye tun tana yin mara sauti har ya fara fitowa.




Rintse idanunsa da karfi yayi, "wai wanna yarinyar ko aljanun kuka gareta?" yafada aransa. Gashi yayi zaune kana ya kirata, asanyaye ta zo garesa kana yace

" what!? "


cikin shesheka tace

"ni...ni... Bazan koma can ba, nafison nan"



Ajiyar zuciya ya sauke kana yace "ki sanar da ummu banda Matsala da hakan".


" Toh "


ta amsa asanyaye, janyota yayi suka kwanta...



*Washegari gari*

suna breakfast wanda su uku ne kacal, Fu'ad ya fita aiki. Diyata akwai magana a bakikinki menene? Cikin kunya hadi da shagwaba tace

"ni ummu anan zan zauna banason waccan party din"


Murmushi ummu tayi kawai, bayan sun kammalla suka bar dining area zuwa hadadiyar falonsu.




"Diyata faheemah ba wani wajen zaku bafa part kawai zaku sauya, so ki kwantar da hankali ki, wanda da aure ke kaisu wani gari ko wata kasa fa? Saboda haka ki kwantar da hankali ki"

Rau rau tayi da idanunwa kana tace "Please ummu ki taimaka min".



*(Manufar ummu nayin hakan shine Saboda su samu fahimtar juna, domin ta lura dukkanin su babu wata karfafan alaka atsakanin su, saidai kuma zatayi amfanin da wanna damar ta gyara diyar tata.)*


Dan haka afili tace " shikenan na amince zuwa lokacin daza'a gama party da'aka shirya"

Murna ce ta koma ciki amma bata bari ummu tagane ba. Fareesa kuwa tsokanarta take wai


"wata zata rabu da mamanta Allah sarki, wallahi ummu dama gidan brother dake G. R. A suka koma"




"Ummu kinga aunty fareesa ko"



cewar faheemah adan shagwabe. Ki rabu da ita, Kila akaita china wa ma ya sani"



dariya suka sanya gaba daya, da haka suka shiga hiran su cikin kaunar juna.







***** ***** *****








"Mama ni fa bangane ba, wai wani ya Fu'ad dinne za'a yi party taya murnan samun lafiyarsa? Wai kuma har da party murnan auransa da ba su iya ba lokacin yana jinya"






cewar umaimah, tana ta jujjuya hadadiyar invitation card din hannunta take, domin shi kanshi katin abin kallone, haka kuma sai kara Karantawa take domin gani take kamar bata karanta daidai. umaimah ni kaina na shiga rudani, domin da badan fareesa ce ta kawo katin nan ba, dasai nace batan gida sukayi cewar Hindu cikin tashin hankali , domin ko kadan basu da labarin tashinsa hakama aurensa, mama Anya ba karya bane yaushe ya warke, kuma wace mara sanin ciwon kanta ce ta aureshi yana kwance kamar gawa? Hmm nima abinda ya tsaya min arai kenan domin talakawan ma sun kishi bare nace kwadayin kudinsu yasa ta amince. Toh mama muje mu gane wa idon mu mana, a'a umaimah kin manta rabon da gidan shekara daya da watanni kenan? Gwara mu bari sai ranar, zamu gani.





" Mama idan da gaske ne ya Fu'ad ya warke, gaskiya sai nasan yadda nayi ya so ni domin daman ina sonsa kawai dai bazan iya bautar jinya bane kuma abun kunya ace ina mijina? na nuna shi a kwance kamar gawa"




cewar umaimah acikin tashin hankali dake nuna wa karara afuskarta. Hindu kuwa kasa bata amsar Tayi domin ita kam kamar ta jawo ranar haka take ji...................


*Three days to the party*

zuwa wanna lokacin idan kaga faheemah ta Kara kyau sosai, haka ma golden skin dinta sai sheki yake, sosai ta sha gyara ciki da waje na ingantatun magunguna da hajiya bilkisu sudan ta tsumata dasu.


domin sosai ummu ta narka mata kudi domin ta mata gyara mai kyau. wanda na 14days ne gobe za'a gama.




Abangaren Fu'ad kuwa sosai yake jin kewar ta domin daga lokacin da aka fara Mata gyaran baya ganinta kwata - kwata, zuwa yanzu yana jin abu mai girma gaske atare da ita, domin abunda yake ji ya wuce so.


Sai dai ya kirashi da "kauna" kuma ya kasa tambayar ummu ina take? domin yasan duk inda take da sanin ummu.


Haka yake daurewa Duk da azabtuwar da zuciyarsa ke masa na rashin ganinta, haka kuma sosai yake mamakin when, how, kaunarta ya masa wanna babban kamu.





Domin wani mugun sonta yake dawainiyya dashi, kuma bai farga da hakan ba saida tayi masa nisa cikin kwanakin nan.
Bangaren ummu kuwa sarai ta fahimci yanda yake raba idanunsa yana neman ta afakaice amma bata nuna ta gane ba.




Washegari kamar yadda kowa yasani asabar ranar hutun kowani ma'aikaci ne, misalin karfe 7:00am daidai yafito domin zuwa kitchen ya hada black tea domin gidan shuru ba motsin kowa, wani da'daddan kamshi mai tafiya da nutsuwa hadi ruhin mutum ya ziyarci hancinsa, lumshe rikitatun idanunsa yayi kana ya ware su ya shiga bin inda kamshin ke tashi domin so yake yaga kowa ya kunna wanna kamshi da bai taba jin irinsa ba...




" maza kanwata ki shiga wankan ki fito"



cewar hajiya bilkisu sudan.



Wankan ta shiga domin wanke hadin dilka dakuma wasu sinadarai dake ciki na gyaran jiki da aka kwaba mata a jiki. Bayan ta fito hajiya sudan tace tayi tsukunno bayan ta nuna mata kaskon turaren dake ajiye a kasan tiles, sai kamshi hadi da hayaki ke tashi aciki....




babban bargo ta miko mata, sai da ta lullube jikinta kana ta zare towel din jikinta, Karba hajiya bilkisu tayi ta nufi toilet domin ita ma tayi wanka.



Tsugunnawa tayi yayinda kamshin ya shiga ratsa jikinta...


Daidai kofar da kamshin ke fitowa ya tsaya yana mamakin ko waye da sassafe nan da kunna wanna kamshin. Tura kofar yayi ya shiga yayinda idanunsa suka sauka kan mutum lullube da bargo bama ya iya ganin fuskar wanda ke lulluben.




Cikin tafiyar kasaitarsa ya shiga takawa ahankali zuwa gareta, zanin ya shiga yayewa, idanunsa ne suka fada cikin nata, sosai fuskarsa ya nuna mamaki domin bai taba tunanin ita bace. Dama nan take all this while? Ganin ya yaye mata bargo gashi babu kaya jikinta, yasa ta runtse ido kana ta ware small lips dinta zata saki ihu! Ganin tana shirin Tara masa mutane ne yasa Cikin sauri ya durkusa hadi da sanya bakinsa cikin nata....




Sosai ya zauce a kanta domin kamshin bakinta yayi matukar tafiya dashi ga kuma kamshi turaren daya fi komai dagula masa lissafi, FAHEEMAH kuwa kasa koda kwakwaran motsi tayi jin abinda bata zata ba, domin

"this is her first kiss" haka kuma yazo mata a bazata, takasa motsin kirki haka kuma takasa hana shi....


Shi kuwa kara rikicewa yayi, sosai ya cigaba da sumbatar ta. Sai daya kai 10 min kana ya xare bakinsa cikin kasala data saukar masa, idanunsa ya shiga rabawa akanta kamar yana neman wani abu.


numfashin take saukewa da sauri-sauri kana hawaye suka shiga gangaro mata, harshe yasa yana dauke hawaye kana ya rungumota jikinsa sosai, jin saukar naked skin dinta a jikinsa ya sa shi jin wani lafiyayyan feelings na taso masa, sosai yayi kokarin wurin controlling din kanshi, Kara matse ta ajikinsa yayi wanda har saida tayi yar kara. Sausauta rikon yayi kana cikin rikitaciyyar murya daya samu kansa aciki yanzu yace


"Kiyi shiru, otherwise I will kiss u over&over again"


dip kake ji kukan ya dauke,

"abinda kikayi yayi daidai Faheee? Kin barni cikin kewa all this day's why? Dama haka ake mata ta bar mijinta without his permission?"


" Ka... Kayi... ha.. ha.. Ku..ri"

ta fada ararrabe haka kuma ciikin fisgo numfashi, ganin kamar bata cikin nutsuwarta yasa yafara shafa gashin kanta wanda yake nasa kamshin na musamman.

"Shhhhhh is okay relax"

ya ce mata yana dan bubbuga bayanta. Sun dauki kusan minti 3 haka kana ya shiga kokarin raba jikinsa da nata domin sosai mood dinsa yafara sanjawa...


rukunkumeshi tayi sosai taki bashi daman haka,, cikin voice dinta dayayi Sanyi kalau tace

"nidai ka rufamin bargona Dan Allah!"

Ajiyar zuciya ya sauke kana yace

"toh sake ni in dauko miki"


"A'a " Tafada ashagwabe tana kwabe fuska. Ganin haka yasa ya mika hannunsa yadauko bargon dake yashe kasan tiles, rufamata yayi amma banda fuskarta kana ya mike Kallonta yayi na 5seconds kana ya fice cikin sauri....





Fitarsa keda wuya hajiya bilkisu Sudan ta fito, kallon kaskon tayi wanda har wutan yayi kasa sosai hakama hayakin,

" faheemah kamar magana na ji, akwai wanda ya shigo ne?"

Gabanta ne yafadi, tayaya zata sanar da ita shi ya shigo? Duk bata iya karya ba, kuma batason yi amma dan babu yanda ta iya.

"A'a babu kowa"

tace cikin rashin gaskiya wanda da'a ce hajiya Sudan ta lura data fahimta,

"okay maza kisa kaya kizo kisha wanna hadin mutafi salon din a miki gyaran gashin".

Tafada tana nuna dan madaidaicin jug dake gefen bed side wardrobe. Dan bata fuska tayi domin ita kam tagaji da shan wadan'nan abubuwan da kullum sai an bata, *(a tunanin hajiya Sudan mu'amala auratayya ya shiga tsakaninsu yasa take tsumata babu kama hannu yaro lolz)* yarinya gata ake miki kike bata rai, maza tashi kisha domin zaki ban labari, kuma kada daga baya kizo kina min yar murya nabaki wasu magungunan domin nasan zaki ji dadin su tarasa a zolaye, cikin kunya faheemah ta tashi ta shiga shiryawa...


daidai Fu'ad ya fito a kitchen anwar ya shigo parlor domin su tattauna yanda gobe zata kasance.

""What's up dude? Katashi lafiya, lafiya lou friend " Fu'ad ya amsa yana kokarin zama akan hadadiyar kujerar falon


"wait! Wait!! Dude!"

cikin rashin fahimta Fu'ad yace "what!? "


"dude wani kamshi naji kana yi irin na turaren mata" cewar anwar cikin dariyar shekiyanci,

murmushi dabai shirya ba bane ya subuce masa tuno moment dinsu na dazo.


Afili kuwa bata rai yayi kana yace dan sa ido kawai yafada yana kai masa bugun wasa a kafada.



Dariya anwar Yayi yana kaucewa domin tsaf ya gano abokin nasa.

Cikin serious tone fu'ad yace

"friend jokes a path a da ina tunanin tausayinta nake ji tun ina jinya nake jin wani abu atare da ita na dauko tausayinta ne, sai yanzu na farga da cewar abunda nake ji atare da ita ya wuce tausayi. Seriously kaunarta yamun babban kamu wanda nake mamakin yanda take yawan min gizo sometimes har muryan ta nakeji yana ratsa kunnu wanna, duk da ada soyaaya bata cikin tsarina domin wasu matan they're after what you have, but ita daban take acikin miliyoyin mata haka kuma Ita din ta musamman ce agareni"

yafada yana dafe saitin zuciyar.


"Dude ta cancanci ka so ta, sosai na yaba da kokarinta lokacin dana dawo daga waje ummu tace matar kace, domin ni shaida ne akan matan da ba za su kirgu ba da suka ki aurenka lokacin kana jinya, dan haka ka riketa amana, in sha Allah friend nagode, kafada mata kuwa?"


Dan bata rai Yayi kana yace friend narasa ta yanda zan fara.


"She's still a baby girl fa, banaso ta rainani"

Wani dariyan mugunta anwar Yayi kana yace. "raini na nawa kuma? yarinyar da tayi jinyar ka meye bata gani ba?"


Tashi kawai yayi batare da kula anwar ba, lemme fresh up kawai yace yana wucewa, daga murya anwar Yayi ta yanda zai shi yace "mutum dai ya rage fadin rai da son girma tsiya tun kafin lokaci ya kure masa"

Ko kula shi bai yi ba ya shiga dakin...



★★

Da misalin karfe 3:00pm na rana zuwa lokacin hajiya sa'a tazo domin tace kwana zata yi abu nasu lolz. Haka sauran yan'uwa ummu dana mahaifinsu fu'ad sun sauka a yau domin taya su ummu murna duk da ba'a garin suke ba.



Domin lokacin da ummu tayi musu surprise ba karamin farinciki suka yi ba kasancewar ummu bata gaya musu da wuri ba sai da party ya rage 1 week.


Hakama burinsu suga yarinyar data yarda ta auri dansu duk da lalularsa. Gidajen radio ma ana ta sanar da bikin gobe, wandanda suke sauraran radio kuwa sunji domin tun saura kwana uku ake sanar wa hakama wasu sunyi alkawari zuwa domin ganewa idanunsu, musamman wadan'da suka san waye FU'AD OMAR ISHAQ.



Zaune suke adakin da'ake mata gyara ita, faressa da kuma wata yar yayan ummu meenal dasuka zo, sai hirarsu suke gwanin sha'awa. Yayinda ake faheemah zana mata jan kunshi( red henna) hannu da kafa. Sosai jan henna design din ya zanu haka ma ya zauna daram a golden skin dinta mai matukar sheki.



Yau ta kasance lahadi wanda yayi daidai da ranar daza'ayi party'n

karfe 4:00,pm daidai aka saka za'a fara bikin. wanda zuwa yau din gidan ya kara cika dankam da jama'a yayinda ummu, hajiya sa'a ta hana afito da Faheemah duk da yanda ake ta tambayar ina matar fu'ad ciki kuwa harda uban gayya fu'ad da yayi iya yinsa ganin yasata a idanunsa Tun jiya amma hakan baiyu ba. Karfe 3:45pm daidai Sosai hayaniya ke tashi sakamakon jama'a da suka cika gidan ba matsaka tsinke. Hakan kuma Yayi daidai da iddar da sallar la'asar da faheemah domin afara mata make up.

Kwararriyar mai make up artist dinnan wato LUCCY MAKEOVER ce ta shiga tsara mata hadadiya kuma tsadadiyyar kwalliya. Duk da ba'a cika mata kwalliyar ba domin simple makeup aka mata, amma sosai tayi kyau, da ta zo samata eyelashes taga baiwar ta Allah yayi mata na yawan da kuma tsayin gashin ido yasa tace

"ai ke ki godewa Allah basai an sa miki ba amarya kina dashi "

ajiyar zuciya tasauke domin daman tsoro yanda xa'a samata take domin ita kam abun bai yi mata ba.

" ko dai kina tsoro ne baki taba sawa ba LUCCY ta tambaya?"

murmushi daya bayyana 1side dimple dinta tayi batare da tace komai.

mascara kawai tasa wanda sai ka rantse artificial gashin ido ne saboda yanda yayi. Sosai makeup din ya kara fito da ita domin wani mugun kyau tayi mai ban mamaki, LUCCY ma kasa shiru tayi sai yaba kyaun ta takeyi.

.tsadadiyyar material mai kalan royal blue wanda gabadaya jikinsa stones ne sai walwali yake, dinkin doguwar riga aka yi mata wanda asama ya kamata yayinda daga kasa yabude sosai, material din yayi matukar haskaka golden skin dinta, head golden color, Luccy ta mata daurin zamani mai kyau yayinda ta dan yi baya da head din kadan lallausan gashinta ya bayyana, white gel ta shafa mata a gashin gaban goshinta kasancewarta mai suma har saman goshinta wanda hakan yasa yasake kwanciya hakama yayi curling tamkar gashin jarirai, net mai shara shara aka tsakala ta bayan daurin nata aka danne da pin daya rige net shima har kasa hakan sai ya zama tamkar mayafi kuma sosai yakarawa dressing dinta kyau.


Tsadadiyyar sarka, dan kunne, awarwaro, sai anklet dake cikin set din yan kunne wanda bakaramin kyau yayiwa kafarta ba.

Takalma hill mai dan fadin dunduniyya tasa, kana tadau pose mai yalwar stones shima golden! *(Makaranta bari na tsaya iya nan kuyi imagine irin kyau da Mrs Fu'ad tayi)* fareesa, meenal, da kuma wasu kawayen fareesa guda biyu suka shigo domin fita da amarya Saboda kowa ya hallara ita ake jira, sosai suma sukayi kyau cikin shigar su, Bakin su yaki rufuwa sai Masha Allah suke fadi Saboda bayyananan kyawun datayi.


Allah Allah fareesa take su fita domin jama'ar suga matar bro dinta, musamman hindu da yarta umaimah sai sauran yanmmata dasuke matukar son sa kafin jinyarsa, wanda bata kara ganin kowa ba sai yanzu da Allah ya bashi lfy...



Kasancewar compound ( haraban gidan) mai girma ne sosai yasa akayi amfanin da ita sai masu decoration dasuka kawata ko ina da kwalliyar royal blue & gold. Sosai wurin Yayi matukar kyau kowa ka gani cikin shiga mai kyau yake daga masu aikin gidan har zuwa wandan 'da suka hallici taron. Wata yar'uwar ummu ce ta radawa mc magana akunne kana ta koma. Sanarwa mc ya shiga yi muryansa mai amsa amo.

"Aha jama'a muna Kara muku barka da zuwa wanna biki mai albarka, kowa ya xauna domin yanzu masoyan Zasu shigo"



ai tsit kake ji kowa burin sa su shigo a gansu...

DJ ne yasaka wata sanyayar waka mai ratsa zuciya...

Su faheemah nafitowa, suka ga hadadiyar mota blue color kirar *Bugatti* sai sheki yake da alama ma sabo ne yau aka fara hawanta.

Anwar ne azaunin driver yayinda fu'ad ke bayan motar. Yayi matukar kyau cikin tsadadiyyar gezner royal blue da aka masa dinkin babbar riga kwaliyyar jikin gezner din kuwa golden ne, sai hula tsadaddiyar hula golden mai dan ratsin royal blue din, sai Rolex watch asaman lafiyayyen farar fatarsa, sai takalmi half cover din na maza mai matukar kyau shima golden. Sosai Yayi kyau kamar ango, ( koda yake yau yake angon lolz) murmushi fareesa tayi ganin haduwar brother ta sai tayi mai alamar hakan👌domin kwalliyar tayi ba karya.

Gogan naku kwatata bai sa tana yi ba, domin suman hucin gadi yayi na ganin baiwar kyau, Hannu faheemah suka kama suka shigar da ita cikin motar, kana su hudu har da luccy suka shiga motar fareesa domin karasa wajen duk da ba nisa amma haka suka tsara baza su karasa akafa ba, motarsu fareesa ce agaba yayinda ta su anwar ke a baya.

A hankali suke tukin motar domin idan mai tafiyar kasa ya jera dasu tsaf zai wucesu. Shigar ta cikin motar yasa shi dawowa tunaninsa musamman ma da kamshin ta da nasa ya hadu sai ya bada fragrance mai dadi.

"Ya anwar ina wuni " tafada cikin cool voice dinta.

"Lafiya lou amaryan mu ya taron"?

"Alhamdulillah"


ta amsa asanyaye, so take ta gaishe shi amma kunyar abinda ya faru tsakanin su ya hana. Murza zobenta takeyi, Wanda idanunsa suka sauka kan hadadiyyar kunshinta. Hannunta ya kamo ya kurawa flowern ido, batare da ya shiryawa hakan ba ya sumbaci hannun domin yana matukar son jan kunshi. Matse hannunta yayi Wanda ba dan anwar ba dababu abinda zai hana ta yin kara.

"Babu gaisuwa?"

yatambayeta yana raba idanunsa a kyakyawar fuskarta! Musamman gashin gaban goshinta daya kwanta luf luf sai lips dinta daya sha pink din jan baki mai dan duhu, sai brown din eyepencil da'aka mata lining din lips dinta sosai lips dinta ya sake dawowa mai tsut tamkar gidan tsusa har wani shape din love yayi, he feel like kissing her cute lips, amma sai ya kai zuciya nesa.
Aransa kuwa gode wa Allah yake daya bashi wanna tsad'ad'iyyar kyauta, domin in ba Allah ba basirar sa ko kokarinsa basu isa ya mallaki wanna tsalelliyar ba. Domin duk abinda yakeso tareda matar aurensa tana da fiye da yanda yayi expecting.

Kwallan shagwa'ba ne suka cika idanunta amma bata bari sun xubo ba, cikin cracking voice tace "hannu na please! Kayi hakuri, ina wuni" tarasa tana turo dan bakinta.

murmushi yayi kana ya sausauta rikon da ya yi wa hannunta domin sosai ta bashi dariya yanda tayi maganar...


"ki shirya amsar hukunci mai tsauri bayan taron nan"

zaro manyan idanunta tayi

"ni kuma menayi" tafada a duburbuce


" zaki tambaye ni da

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment