Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

su, ranar su umaimah sunyi kuka sosai yayinda nadama,da tsoron Allah ya Shige su har sukayi nadamar halin dasukayi abaya musamman ma Jameela.
.

*bayan wata uku da kwana biyar*


zuwa wanna lokaci jikin su ya dan warware har suna gane waye a kansu, ranar dasuka dawo hayyacinsu sunyi kuka Mara amfani domin lokaci ya kure musu, nadama sosai sukayi, dole duk Wanda ya gansu ya tausaya musu halin dasuke ciki. Ranar dasu ka cika wata daya da kwana ashirin aka basu sallama, kuma zasu na zuwa ana duba su every week, sandan da ake ba marasa kafa musamman masu kafa daya aka bawa mami, ai ranar kuka tayi kamar zata shede.


ance naka naka ne komai lalacewarsa, ABBUH ma sai da ya share kwallan tausayinta.
Hajja Hindu kuwa sai faman boye ahannunta take domin sosai take jin kunyar a ganta da hannu daya...


Basu bar asibitin ba saida hajja Hindu ta nemi alfarma akan tana so ahadu a gidan su maragayi Omar ishaq wan Baban umaimah, kuma maganar duka ta shafe su...



Gaban mami dana baban umaimah yafi faduwa domin sai yanzu da aka Kira sunan wanshi ya tuno da iyalansa da rabon daya gansu ya manta, Wanda baisan dalilin daya sa ya wofuntar dasu ba.


mami kuwa sarai tasan dalilin hajja Hindu na fadin haka, duk da tana tsoron abunda zai faru, amma tana fatan kada hakan yayi affecting aurenta.


Hakan take ga hajja hindu, domin tana tsoron abunda zai faru idan mijinta yaji abunda tayi, amma dole su tona asirin kansu mutuwa ta riskesu, sannan su samu sausauce aransu, sai ta kalli Abbuh hadi da cewa "alhaji inda hali ka taho da yan uwan daza su zo gobe tare ayi komai agabansu domin suma ta shafesu.


Sosai abbuh dama baba umaimah sukayi mamaki amma babu Wanda ya musa ko tambayar ta dalili, tunda yau da gobe duk daya ne a wurin Allah....




Share and comment



Thanks for reading #rayuwar FAHEEMAH

Noor🥀🌸


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din

I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851

💔RAYUWAR FAHEEMAH💔



Wattpad
@NoorEemaan


Wanna littafin kyauta ne (free novel)



59-60

(Not edited)



*Washegari*

Yau ta kasance Saturday ranar hutun ko wani ma'aikaci, zaune take a jikinsa sai faman zillewa take kamar small baby.


"kinsan Allah goofy Angel sai na duba result dinnan yau! ace kullum kice baxa'a duba ba kusan wata nawa kenan, for long zaki cigaba da tsoron nan? Ko baki son yin jami'a?"

Asanyaye tace "inaso"

"good then ki bari na duba miki"


jinjina kai tayi hadi da rungume shi gam tana runtse ido.

Dariya ta bashi domin shagawabar ta da yarinyarta karuwa yake a kullum.

Data ya bude kana ya shiga duba mata, babu jimawa ya ga result ya bayyana a screen din wayar shi, wani murmushi farinciki yayi hadi da furta

"alhamdulillah ya Allah"
can kasan makoshi.


Amma saboda yana son tsokanar ta yace

"innalillahi wa Inna ilaihi raju'un!"


Cikin sauri ta dago a jikinsa hadi da cewa "daman na sani, sai da nace kada ka duba kada ka duba, nasan ban ci bako?"
Tafada hawayen sakalci na zubo mata.


"gaskiya i'm disappointed in you faheee, ace duk karatun da kika yi mark din da kika ci 200?"



kara rugumeshi tayi hadi da cewa "kayi hakuri my man, kayi hakuri na saka ka bata kudin ka da lokacin ka a kaina amma gashi banyi abunda za ka yi alfa'ari da ni ba" tafada Cikin kuka domin kwata-kwata bata ji abinda yace ba Saboda rudewa.


Dariya sosai ta bashi, A yau kasa rike dariyar, cikin muryan dariya yace "faheeee cewa fa nayi kin ci 200mark fa, tsokanar ki nake"


Ai wani ihun murna ta fasa hadi da kara rungume shi gam -gam ajikinta.

Sai fadin alhamdulillah ya zuljalali majeed take hadi da dariyan farinciki, sai kuma ta kwabe fuska hadi da dan dukan kirjin sa kana ta ce" shine ka ban tsoro ko?"

Murmushi kawai yayi yana dage mata gira daya, sauka tayi a jikinsa ta nufi part din ummu cikin zumudi, da kallon zallan kauna ya bi ta da shi kana ya sauke wata ajiyar zuciya domin farinciki Faheemah shine nashi, haka zalika walwalarta ma na shine.


"Allah ka bani ikon kula da ke faheeta da dukkan iyawata" ya fada abayyane.



Tana Shiga part din ummu ta tarar da ita a zaune tana kallon tashar sunnah tv, sallama tayi kana ta kwantar da kanta a cinyar Ummu tace
"naci 200mark a jamb" ta fada tana sakin dariya murna..

"Masha Allah, Alhamdulillah" Ummu ke fadi hadi da shafa kanta.

"Diyata faheemah akwai kwanya kam, Allah ya kara miki ilimi mai amfani."


"Ameen ya Rabbil izzati ummunah" sun dan taba hira da Ummu na kamar minti 5 kana ta koma part dinsu...



★ Motoci uku ne iri daya kirar sienna a gate din su Ummu.
Horn daya daga cikin matukan motar ya danna, Malam iro ya leko ganin hajiya Hindu acikin motar yasashi wangale musu had'add'en gate din, daidaita parking suka yi a haraban gidan kana mutanen cikin motar suka fara fitowa....


Kawu anas, malam iliyasu, bintu matar kawu, mahaifin mami, mummyn zaynab tareda mijinta, mami, hajja Hindu, abbuh, Baban umaimah daya kasancewar kanin mahaifin su fu'ad. Sai umaimah, Jameela sune suka fito daga cikin motoci ukun nan, gaban kusan mutane hudu ne ya fadi a cikinsu.
Mami tana tunanin yau babu wata rufa rufa asirin ta zai tonu, ga ganin katon gidan da bata taba zaton faheemah zata shigo cikinsa ba, yayinda Baban umaimah yaji wata matsananci kunya hadi da faduwar gaba, domin ya manta yaushe rabon daya zo gidan Wan sa, wanda shi kam bai San dalilin rashin zuwan sa ba.
Abbuh kuwa gabansa ya fadi ne haka kawai yana kuma tunanin menene ya kawosu wanna tamfatsetsen gidan? Haka ma tunanin Jameela yake daya dana mami. Umaimah kuwa kunya ce ta kamata tun kafin tayi ido hudu da yan gidan.


Hajja Hindu ce ta Shiga ta sanar da Ummu da har yanzu take zaune a falon cewa tana tareda baki, sai dai wanna Karon har da fareesa a falon.

"Su shigo" Ummu kawai tace duk da zuciyarta cike yake da mamaki ko su waye bakin?


Bayyanar su a yalwatacce Kuma had'add'en falon yasa Ummu matukar mamaki har ma fareesa domin ganin fuskar da rabon yazo gidan anjima sosai (wato mahaifin umaimah) duk da sun yi mamakin ganin wasu sababbin fuska amma basu nuna ba.
Bayan gaishe gaishe daya gudana a tsakaninsu, mahaifin umaimah kuwa kunya ma ta hana shi gaisawa da ummu, sarai ummu ta lura dashi amma bata nuna ba...


Ummu tace wa fareesa taje ta yi wa yan aiki magana su kawo wa baki abun sha da snacks.


Sosai Mami ke kallon ummu, Domin ta ganeta, duk a wannan lokacin shigar ta ya bambamta, domin sanye take da rantsatsen lace da ganinsa kadai zai tabattar maka da tsadarsa.


A sanyaye hajja hindu tace "ummun su nace in fu'ad na gida yazo tare da matarsa suma maganar ta shafe su" zuciyoyi ne suka sake shiga zullumi da fargaban wanna cakwakiyyan, amma basu ce komai ba.

Waya ummu ta daga ta kira shi, bayan ya yi picking ne tace "son kazo yanzu kai da diyata munyi baki"

da "toh ummu" kawai ya amsa .



cikin mamaki ya kalli faheemah dake kokarin xura hadadiyar doguwar rigar Turkish material mai kalan sea green, ya sanar da ita abunda ummu tace, gabanta yayi wata irin bugawa dayasa ta furta "ya salam" kasa- kasa


"are you okay goofy angel?" Ya tambayeta.


Cikin danne abinda take ji tace "ooh yes! Am fine" ta karasa tana murmushi karfin hali, sarka da yan kunne na gwal tasa hadi da awarwaron sa da zobensa wanda kudinsa zai kai 1millon sosai tayi kyau sai walwali take, powder ta shafa ,sai kwalli da ta zizara hadi da shafa dark pink jambaki dauri mai kyau tayi , sosai tayi mugun kyau ,duk da komai cikin karfin hali take yin sa, yana lura da ita amma ganin babu lokaci ne yasa shi kamo hannunta bayan ta yafa bakin mayafi madaidaici suka fito...


Ummu na shirin sake kiran wayan shi taji sallamar su.

A hankali ta dago kanta, babu inda ya sauka sai kan yan gidansu, cikin xallan mamaki ta tsaya domin maganar ma makalewa Yayi, "shin mafarki nake yi" ta tambayi kanta?
Dan murza idanunta tayi still su din ne zaune a parlon Ummu, a ranta fadi take Allah kasa kada na tashi daga wanna mafarkin, a fili kuwa cikin son tabbatarwa tace "abbuhnaaaa" abbuh bai lura da shigowar su ba, domin ya tafi duniyar tunanin yar sa faheemah, jin muryan da ko a mafarki ya ji zai gane ya sa shi dago Kansa hadi da mikewa tsaye cikin kad'uwa da mamaki hadi da murna yace

"faheemah'n abbuhnta..."
Kana ya Shiga tahowa gareta cikin sauri sauri, itama hannunta dake cikin na fu'ad ta xare ta nufeshi cikin gudu, cikin farinciki ta rungumeshi hadi da fashewa da kuka mai matukar ratsa zuciya......






Share and comment




Noor eemaan

Thanks for reading #rayuwar FAHEEMAH


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851



💔RAYUWAR FAHEEMAH💔


_by NoorEemaan_ 📚✍️


Wanna littafin kyautane( free novel)


https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din



when you truly care for someone, their mistakes never change your feelings because it's the heart that get angry but the heart still cares. ✌😍



61-62

(Not edited)


Gaba daya yan falon cikin mamaki suke, suka shiga bin su da kallo, amma sam wandan da suka san dangantakar dake tsakanin Faheemah da abbuh basu yi wani mamaki ba, yayinda Mami da jameela suka shiga wani hali wanda kai tsaye ba zaka fassara su ba, musamman Ganin yanda faheemah tayi mugun kyau ta murje abunta, mahaifin umaimah mai suna Yakub kuwa tambayar kansa yake a ransa cewa yaushe Fu'ad Yayi aure bai sani ba? domin iya tunanin sa Fu'ad na tareda Lalurar paralyze yaushe ya warke be sani ba?


"Abbuh kada ka kuma barina, kada ka kuma juya min baya, ka yafe min idan na bata maka rai, kada ka kuma kin amsa gaisuwata, kada ka ki bani kulawar ka please abbuh na" ta fada tana sake k'ank'ame shi sosai yayinda hawaye ke zuba a idanunta tamkar an balle famfo.


Hawaye ne masu zafi suka sauka a idanu abbuh, sai ma yanzu yake komai ke dawowa masa dangane da shariya, hantara, kyara, daya aikata ga faheemah suka shigo dawowa kwakwalwarsa a yau... Shima Kara rungume ta Yayi sosai hadi da cewa

"kiyi hakuri diyar abbuh'n ta, ki yafewa abbuhnki kinji, hakika ban rike amanar umminki haleema ba, amma ina mai tabattar miki bansan dalilin yin hakan ba, ban ma san nayi ba"


"nina sani kuma nice sila" suka ji saukar muryan Mami ya daki dodon kunnen su.

Gaba-daya yan falon da suke sharar kwalla tausayin Faheemah dama abbuhnta suka yiwa Mami kallon mamaki banda hajja hindu dama jameela da ta san wasu Daga cikin mugun tan da mami tayi.

Ahankali Faheemah ta kalli mami hakama abbuh fuskar ko Wanne da neman karin bayani zama Abbuh yayi domin tsayuwar ta fara gagarar sa, Faheemah kusa da abbuhnta ta zauna hadi da dora kanta a kafadar sa, Fu'ad da tun shigowar su bai zauna ba ya nemi gefen ummu ya zauna tausayi heemahnsa fal ransa yayin da wani mugun tsanar mamin ya sake darsuwa a ransa.


"Na sani ni din muguwa ce, mai raba soyaayar ya da uba, a yau banda mafita daya fi in tona asirin kaina, amma wallahi nayi nadam...."

Wata tsawa mummyn zaynab ta daka wa mamin kasancewar ta mai sauri fushi kuma bata daukan raini musamman da maganganun mami ya soma karyan ta maganar Faheemah na cewar tabi saurayi sun gudu..


" ki fito ki fada mana Kawai ki daina jan magana" hannun mummy zaynab mijinta ya kamo alamun rarrashi domin yasan halin matarsa sarai tana da hot temper.


Mik'ewa Ummu tayi, hadi da yiwa fu'ad da fareesa ido akan su tashi, cikin kamilalliyar muryar ta tace "am... bari mu baku waje idan kun gama zamu dawo domin wanna maganar family issue ne"


"A'a a'a hajiya ku dawo Ku zauna dan Allah, domin wanna maganar har daku za'a yi mun zama daya, tun da kuka rike mana diyar mu bisa amana ai babu wata boye-boye atsakanin" mu cewar kawu anas.

Ummu bata ce komai ba ta koma ta zauna haka ma su fu'ad.


Wani yawun tsoro mami ta hadiya kana cikin cracking voice ta soma cewa "ni ce naje wurin boka ya raba soyaayar faheemah da abbuh'n su tare da taimakon hajja hindu"

Zaro ido sukayi dukkansu cikin kad'uwa da mamaki!


Nan ta shiga basu Labarin komai tiryan tiryan ko tsallake bata yi, daga muguntar data gana wa mahaifiyar faheemah, zuwa duk wahalar data bawa Faheemah, har ma zuwan ummu gidan, da zuwan mummy zaynab da irin karyar da ta yi cewa tabi saurayi sun gudu, da raba tsakanin Faheemah da Fu'ad da suka so yi ita da Hindu domin ko waccen su so take yarta ta auri fu'ad din har zuwa gidan boka da mutuwar wulakancin da Yayi har izuwa hatsarin dasuka yi....




Gaba dayan dakin ya kaure da Kuka hadi da mamaki irin mugunta, son zuciya, ko suke son duniya irin na mami... cikin kuka mai taba zuciya faheemah tace "mami why! Why!! Why!!!! Mami? Meyasa baki cigaba da dukana ba? Meyasa baki cigaba da bani aiki ba? Meyasa baki cigaba da gana min azaban ba? Domin zan jure hakan akan raba ni da abbuh na da kika yi tsawon shekaru, daman abunda kike nufi da ALHAJI YA MANTA WACECE NI kenan" ta karasa tana fashewa da kuka mai taba zuciya, gaba-daya tayi mugun fita a hayyacin ta.

A karon farko a rayuwa da Mami da taji tausayin faheemah, lallai a yau an kai faheemah bango tunda har da iya bude baki tayi wa mami wadannan tambayoyin, domin bata taba yiwa wa mami magana irin wanna ba, saboda tsananin hakurin ta.

Tabbas ta cutar da ita da yawa ita kanta ta san da hakan, sai dai son kai, da son zuciya hadi da tsantsar mugunta ya rufe mata ido. " ki yafe min faheemah, nasan ni mai laifi ce babbba a gareki, na cutar da ke na cutar da umminki a zamanmu, gashi bata duniyar bare in nemi yafiyar ta, kaico nah da son duniya irin nawa, gashi bai amfane ni da komai ba, ku yafe min dan Allah, kalli Allah ya yi miki sakayya tun a duniya Faheemah, nayi hatsari na rasa hannu daya da kafa daya, hajja Hindu ta rasa hannu, a dallilin son duniya irin nawa yar'uwarki Jameela tayi ciki kuma saurayin ya gudu, har da alhakinki ne yake bibiyar mu"

Sai yanzu faheemah da ma sauran wandanda basu sani ba suka lura da hannu da kafar mami hakama hannu hajja Hindu, ihu hadi da salati Faheemah tayi tana boye fuskarta a jikin abbuh domin yanayin hannu da kafar mamin yayi muni, ita ma faheemah Kuka take sosai, lallai mami tayi nadama ita ta kira anty Jameela da yar'uwarta ayau, ita ke mata magana cikin sanyi murya ba kyara, ba hantara, ba zagi? duk ta ayyana hakan a ranta tana shirin bude baki tayi magana taji muryan abbuh...


"Nagode miki kwarai da irin sakayyar da kika min hajara, banda abun da xan ce miki, domin tun avduniya kin fara girban abunda kika shuka, waya sani ko ke kikayi sanadiyyar mutuwan matata?" Abbuh ya fada wani daci ya cika bakin sa.


Ai kuka mami tafara tace "alhaji wallahi tallahi ban taba kisa ba, ka yafemin, duk da bana da imani amma bazan iya kashe rai ba, duk da bana shiri da haleema a zaman da mukayi, amma bazan iya kashe ta ba, hajja Hindu ke gaya masa wallahi ban kashe ta ba".

*(Illar mugunta ko wani hali Mara kyau kenan domin koda Baka yi Abu ba za'a ce kayi, domin mugun halin zai iya sawa mutane suyi tunanin kai ka aikata )*

cikin kuka itama ta fara tonon asirin kanta, ciki har da asirin data yiwa baban umaimah ( yakub) saboda irin kulawar da ta ga yana bawa ya'yan Wansa a lokacin da mahaifin su fu'ad ya mutu, saboda daman tana matukar jin haushin ganin su Ummu sun fisu arziki, kana ta sanar dasu cewa ita ta bawa umaimah karfin guiwan xuwan gidan akan ta raba su faheemah da Ummu, domin ita umaimah tasamu ya aureta sai ta kare da cewa "alhaji kuyi hakuri har da laifi na da gudunmawata a wahalar RAYUWAR FAHEEMAH kuma wallahi ba ita ta kashe mahaifiyar faheemah ba domin har shawaran hakan na bata ta ki, nice nan na nuna mata gidan boka, Ku yafemin dan Allah. Baban umaimah na tuba na yi nadama"

sallallami da koke -koke ke tashi a dakin...

*(duniya ina zaki damu ne? Mutuwa ake a kullum amma mutane basa tunanin komawa ga Allah, wasu mutane sun dauko xasu dauwamma ne a gidan duniya! Ga dai mami da hajja Hindu ce ta nuna mata hanyar bata, amma sai ya zamana ita mami tana neman fin Hindu yin mugun tan. Ya Allah! Kasa mufi karfin zuciyar mu ka tsare imaninmu ameen)*.


"Bazan iya zama dake ba hajara, domin ban san wani muguntar kike shirya mana nan gaba ba Dan haka na...."



"Dakata abubakar! idan hankali ya bata, hankali ke nemo shi, yanzu idan ka rabu da da ita me aka yi kenan? Ta tuba tunda ta tono asirin kanta da kanta, matukar na isa da kai, ka kuma daukeni uba toh kada ka rabu da ita".

Shiru abbuh yayi domin kawun ya masa komai a rayuwa baya jin zai iya yin butulci ga kawun"


Shima Baban umaimah dage wa yayi zai rabu da da Hindu domin cewa yayi ita din masifa ce ga ahalin sa, ita din mai bata zumunci ce, kawu da Malam iliyasu ne ke basu baki hadi da yi musu nasiha musamman akan hakuri da yafiya.



Ganin hakan yasa mahaifin mami bai ce komai ba, domin yayi tunanin cire ta a sahun y'ay'an sa domin ta aikata abun Allah wadai, sai dai tunda wandanda tayi wa sun hakura yasa shi yin shiru, amma tabass yaji haushin halayenta kwarai kuma zai mata hukunci personal a matsayin shi na uba....







Share and comment



Thanks for reading
# rayuwar FAHEEMAH

Noor Eemaan🥀🌸




I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851

💔RAYUWAR FAHEEMAH💔


Wattpad
@NoorEemaan



Wanna littafina na kyauta ne (free novel)


63-64

Not edited


https://facebook.com/groups/943534712916776/




"Jameela"!!!

Kawu ya kira sunanta a dan kausashe

"na'am" ta amsa kanta a kasa cikin matsananci kunya .



"Kin bani mamaki, kin bi son zuciyar ki, gashi kin jawo mana abun Allah wadai a zuri'armu, wanna maganar ya kamata ace a gidan abubakar mahaifinki zamu yi ta, amma na zabi yin ta anan saboda ya zama iznah ga dukkan mu.... numfashi ya sauke kana yace Jameela kin San illar zinah kuwa? Bayan shirka (hada Allah da wani) sai zinah a manyan laifuka.
Yakamata mu lura da cewa kofofin zina guda biyar ce kamar haka;

*kallo zuwa ga abinda Allah ya haramta.

*Shigar batsa

*Kalaman batsa

*Kebancewa da matar da ba muharramarba ka.


*Sha'awa mai karfi babu aure



Allah ta ala yace:
kada ku kusanci zinah.

Zina tana cikin manyan Manyan laifuka, Wanda Allah ta'ala ya haramtata, annabi Muhammad( s.a.w) ya haramta ta, Kuma zina haramun ce har izuwa ranar alkiyamah, hakika duk sakon shar'iar Allah da aka saukar sun hadu akan haramcin zina.

Alqur'ani mai girma da sunnar annabi ( s.a.w) da dukkan malamai sun hadu akan haramcin zina.

Ana tabattar da zina ta hanya uku.


1. Shaidu
2. Mutum yayi ikirari Dan Kansa
3.samun mace da ciki babu aure, ko shubha bisa sharuddan da aka sanyawa ko wanne,

Abubuwan da suke jawo zina daga bangaren mace guda bakwai ne

1Bayyana tsiraici, shigar banza, da Santa tufafi masu shara shara, ko masu dame jiki.


2. Yin kwalliya a lokacin fita ta bayyanar da ita akan titi, mafiyawan kwalliya ta shafi kafa, wuya, kirji, da sauran guraran jikin mace.


3.shafa turare mai mugun tashin kamshi da tayar da sha'awa a lokacin fita unguwa ko a gaban wadanda ba muharamar kaba.


4.rangwada, make murya domin tayi dadi a wajen Wanda ba muharamar ka ba.


5.yin rangwada a lokacin tafiyada karairaye agaban maza.


6 cakuda da maza .


7.kebantuwa da wasu maza ko wani namiji da ba muharamarka ba.


Yin zina tsakanin baxawari da baxawara duk sun aikata babban

1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment