Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mami saboda yana yawan kawo hannu jikina ni kuma gaskiya banaso".


mami bata ji dadin abinda jameela tace salman nayi ba, domin babu uwar dazata so ayi wa yarta haka komai lalacewarta kuwa, maimakon ta tsawatar mata amtsayinta na *Mahaifiya* amma saboda kwadayin abun duniya, sai ta shiga nunawa jameela hakan ba komai bane, shiru jameela tayi tana jin gurbatacciyar shawaran maminta.

"Ya baki kudin kuwa? "
yaban dubu biyu cas, tafada tana fito da kudin daga Jakarta


"Wanna yaron dan albarka ne, jameela ki rike shi da kyau domin kafin kisamu kamarsa zai wahala"


" wallahi kuwa mami shiyasa duk abinda yake min nake barinsa, domin ki duba fa tun haduwarmu kullum sai munci kaza"

ta fada kai kace da kawarta take hira, domin babu kunya ko kadan a yanayinta.


Mamin dariya tayi tace

"sai ki yi waya a kawo mana ankon mu kaiwa tela tun yanzu"

batare da ta ba mami amsa ba tace "ga kazar niyau bana jin cin kazar"

washe baki mami tayi, hannu biyu ta sa takarba, hadi da cewa "amma wanna ya min yawa"


"Toh kuci da abbuh" inji jameelah

idanu mami ta zaro "rufamin asiri yar albarka! Salon yanzu ya fara min fadan meyasa nake barinki karban abun saurayi"

kazar ta bude ta shiga ci, yayinda jameela ke latsa tsadadiyyar wayar da salman ya kawo mata, tsohowar wayar da sani ya siya mata kuwa mami ta barwa, wanda abbuh ba shida matsaniyya akan duk abinda ke faruwa...


โ˜…โ˜…โ˜…โ˜…


a yau tayi wanka domin jinin ya dauke! Fita tayi ta sanar da ummu cewa asiyo zam-zam din.
Babu jimawa aka siyo manyan - mayan jarkoki na zam zam din, ummu da kanta ta kawo mata daki, lokacin tana shafa masa lotion dinsa wanda kamshi ya karade dakin.
Sallama ummu tayi hadi da shigowa, ai ta sauri ta zare hannunta cikin jin kunya kamar kasa ta tsage ta shige....

Ajiye zam-zam din ummu tayi kana tace

" diyata faheemah ga zam-zam din nan"

"toh ummu"
ta amsa a kunyace, Murmushi mai sauti ummu tayi kana ta fice tana tunanin yaushe faheemah zata sake da ita sosai, duk da kunyarta na matukar burgeta domin kunya ado ne ga ya mace, da wanna tunanin ta haye upstairs...


Ajiyar zuciya ta sauke san da taji fitar ummu, sai kuma tasaki dariya tuno yanda ta mike zumbur dazu, kammala shiryashi tayi tana sauke numfashin gajiya domin fu'ad giant ne irin sosai dinnan.


Karfe tara ta gama masa komai kamar yadda ta saba, kana tashiga wanka hadi da dauro alwala bayan ta shirya cikin saudiyya abaya hadi da farin hijab, sai ta dauko ruwan zam-zam din da qur'anin ta, kan sallaya dake shimfide daga gefen gado ta Zaune ta bude ta fara da ummul kitab wato (suratul fatiha) ta tofa, kana ta dora da "suratul Bakara" ta shiga Karantawa a hankali cikin zazzakar muryata, tana yi, tana tofawa, sai da ta gama tofa surar gaba daya cikin ruwan zam-zam din, kana ta mike domin gobe da asuba zata cigaba kasancewar izu 60 din take son Karantawa cikin ruwa zam-zam din, kallon shi tayi ta ga har yayi bacci...


Share
Comment


Thank you for reading my novel #Rayuwar FAHEEMAH


๐Ÿ’”RAYUWAR FAHEEMAH๐Ÿ’”



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851 https://facebook.com/groups/943534712916776/



_by Noor eemaan__

kyauta ne ( free novel)


When you truly care for someone,
Their mistake never change your feelings because it's the mind that get angry but the heart ๐Ÿ’šstill care. โœŒ




27-28
(Not edited)


Gadon itama ta haye ta tofa musu addu'ar kwanciya bacci ta shafa musu, kana ta ja blanket da rufe su, duniyar tunanin yan gidansu ta fada musamman abbuh wanna kullum ta Allah sai tayi shi, hawaye ne masu zafi suka zubo mata wanda ita bata san ko na menene ba.



4: 50am na asuba ta farka da addu'ar tashi daga bacci a bakin ta tace

"Alhamdu lillahil-lazee ahyana ba'ada ma amatana wa-'ilayhin nushoor"

kana ta sauke kyakyawan kafafunta kasa ta shige bathroom tare da karanto addu'ar shiga bandaki tace

"bismillah Allahumma inni azubika minal kub'si wal khaba'is)"

alwala hadi da brush tayi kana ta fito tare da addu'ar fita a bandaki tace "gufarnak".

Dogon hijab ta sanya ta gabatar da raka'atun fajir anutse. Bayan ta iddar ne ta fara tapping fuskarsa, a hankali ya bude rikitatun idanuwansa, murmushi tayi kana tace " ankusa tayar da sallar"
bowl mai dauke da ruwa da dauko ta daura masa alwala, babu jimawa aka tayar da sallar asuba, jam'i tabi domin ana jin komai daga masallaci dake wajen gida.


Karatun jiya ta cigaba dayi bayan ta yi shafuka masu yawa ta tofah aruwan zam-zam din kana mike domin ganin rana ta fito sosai, agoga dake makale adakin ta kalla taga 7:50am daidai.


Kitchen ta shiga domin so take tayi abun sadaqah ta raba. *( Idan har wani ciwo yana damunka ka kasa maganinsa, toh ka yawaita sadaqah magani ce, waraka ce, kuma kariya ga dukkanin cututtuka. Sanna sadaqah ladansa yana gabbatuwa wajen Allah. ko da dabbobi kayi wa sadaqahn, bare mutum mai darajar)*.



Gaisawa tayi da masu aikin data tarar a kitchen, amsawa suka yi cikin jin dadin yanda take da sauki kai hadi da girmama na gaba da ita duk da kansancewar su masu aiki.


" amaryar yallabai me kikeso amiki? Inji larai mai aiki"


murmushi Faheemah tayi kana tace " karki damu anty larai zanyi da Kaina "
itama larai murmushi tayi batare da tace komai ba, tunanin me ya kamata tayi wanda bazai dau lokaci ba...



"fanke" zuciyarta ta raya mata aikuwa nan da nan ta hada ingredients din kana ta shiga kwabawa...
Bayan awa daya da rabi ta gama suyarta domin yana da yawa, masu aikin dake kitchen ta debar musu, sai ummu da Fareesa tazubawa a flask domin batajin xata ci, domin a cike take jin cikinta ko dan suyar data yine oho!

fita da ragowan waje tayi, cikin abinda baifi 10min ba, tadawo da empty roba.

Tana shigowa parlorn, ummu na saukowa daga hadaddiyar benen su,

"diyata Faheemah ina kikaje haka?"

Maimakon ta amsa, sai ta durkusa tace

" Ina kwana ummu"

"tafiya lau *yar albarka*"

take kwalla suka ciko idonta, domin umminta kadai ke kiranta da hakan sometimes, bata bari sun zubo ba tace

" ummu abun sadaka na raba awaje, inaso nayi hakan har zuwa kwana bakwai da nake sa ran zan kamalla saukan"


Shiru ummu tayi domin sosai mamaki ke kamata, abunda bata damu dayi ba, Faheemah keyi yanzu, hakan sai yazama tamkar tunatarwa ce take mata.


"Allahu ya albarkaci rayuwarki " tafada tana dago ta.


Cikin sweet voice dinta ta amsa da,

"Ameen ya rabb"

kana tace

"ummu bari na kawo miki fanke, jinjina kai kawai tayi.

Daukowa tayi ta ajiye akan dining table, kana tace, "ummu dame dame zanyi serving dinki?"

"Ina ga da fanken amaryan fu'ad zan fara sai tea"

cewar ummu azolaye kasa tayi da kanta akunyace, tea mai kauri ta hada mata kana ta bude fanke ta shiga zuba mata, wanda yayi daidai da saukowar fareesa


"wayyo dadi ina aka samu pufpuf (fanke)?"

Harara ummu ta zabga mata tace "sai aukin ci amma bakya son girkawa"

dariya tayi ta karaso dinner din, gaisuwa sukayi da faheemah ta ajiye flask din a gabanta ta fara ci lumshe ido tayi domin dadin daya ratsa ta.

" Ummu dan Allah waye Yayi?"

"Diyata mana"

ummu ta amsa mata


"wow! gaskiya tayi dadi, yana cikin favorite din brother na, nima inasonsa, amma naki yafi kowanne dana taba ci dadi, zaki koyamin naki method din? "

"Sai kace gaske, a hakan za a koya miki abu kina da da son jikin" cewar ummu,

dariya Faheemah da Fareesa suka yi tare.
Kitchen din ta koma ta dama masa kunun gyada daya sha madara sai kamshi yake, yana kwance sambal kamar kullum, idonsa abude, karasowa tayi ta haye gadon hadi da tallafar fuskarsa atafin ahannayenta

" Gud morning my fufu" ta fada tana sumbatar goshinsa, "afwan nabarka kai kadai" ta sake fada

sanin babu amsa yasa ta dauko Kunun ta shiga bashi ya sha rabi, sai ta shanye rogowar kana ta shiga gyara shi...


kullum sai tayi abun sadaqah ta rabar, hakama karatun qur'ani kullum sai ta tofah aruwan zam-zam ahaka ta kasance kullum, har izuwa kwana bakwai sanna ta sauke Qur'ani mai girma da daraja cikin ruwan zam-zam din...

Agoga ta kalla ta ga karfe 2:00:am na dare tagama, sai ta mike ta a dana zam -zam din zuwa safiya take son fara mai amfani dashi.

gadon ta haye domin kwanciya, zaro manyan idanunta dake ciki ta bacci tayi,

"ya fu'ad baka yi bacci ba? kana son wani Abu ne?"


Tafada kai kace zata samu amsa, tasan da wuya ya farka cikin dare haka sai da dalili, dan haka sai ta taba diaper dinsa ai kuwa acike take dam.


Cikin matsananci tausayinsa ta sauka domin dauko sabon diaper, aranta kuwa addu'ar samun lafiya take ga mijinta....

Mutum har mutum amma ba iya tashi, ba bakin magana, marabarsa da jariri babu yawa Kowa da kaddararsa, Tasa kaddarar kenan!...



Da wanna tunanin ta canza masa diaper d'in kana tofe su da addu'a, blanket ta rufa musu tana shiga shafa lallausan gashinsa da haka bacci ya dauke ta.



Washegari bayan ta gama masa komai kana ta dama masa zallan kunun madara wanna yayi kauri sosai hadi da haske gwanin sha'awa...

Shayar dashi tayi sai data ga alaman ya koshi ta barshi, suratul bakara ta shiga karanta masa a kunnensa hagu da dama, kana ta zuba ruwan zam-zam a cikin wani bowl hadi da yin bismillah kana tabashi ya sha , sai ta shafa masa ragowan a dukkan ila'irin jikinsa.


Jug hadi ta cup da suka yi amfani da shi ta fitar kitchen kana tadawo dakin, wanna karon idanunsa a rufe suke, murmushi tayi aranta tana mamakin yanda yake da saurin rufe ido, jitayi wani shauki na dibanta wanda batasan sanda ta karasa garesa ba, sumba mai sanyi ta sakar masa akumatu, dan she can deny it anymore, hakika ta fada sonsa wanna batasan lokacin da soyaayarsa mai karfi ya shigeta ba,

"get well soon, I wish you speedy recovery my fufu" Ta fada a bayyane


Bayan kamar minti biyar ta mike domin zuwa gaida ummu, ai da tsokanar fareesa ta fara cin karo

" Barka da safiya lover's bird kwana biyu kin buyo bakya fitowa, idan zan shigo ummu ta hana ni saboda kada na katse miki karatu, Sannu matar bro Allah ya biyaki" ( lallai Fareesa kin amsa sunanki na parrot, anwar ya iya zaben suna ๐Ÿ˜œ)



Da "ameen" ta amsa , kana ta durkusa kamar kullum tare da gaida ummu, amsawa ummu tayi cikin kulawa da kaunarta kana ta ce tayi breakfast, tea kawai ta hada tana sipping a hankali yayin da hankalinta ke wajen fufu dinta, ( wai fufu faheemah kenan, kin iya zaben suna lolz๐Ÿ˜น๐Ÿ’”)

aranta kuwa tana addu'ar Allah ya bashi Lafiya tayi alkawarin yin azumi uku dan nuna godiyar ta ga Allah buwayi gagara misali.



Tana gama breakfast sai ga sallamar anwar, mutuniyar tasa tuni ta cuno baki ganin mutumin nata, gaishe da ummu yayi, kana suka gaisa ga faheemah amutunce,

"anwar je Kayi breakfast"
" toh ummu kamar kinsan banyi ba kuwa, murmushi kawai ummu tayi

"ke! Parrot zo ki hada min breakfast"

Kunkuni ta shiga yi kasa Kasa

" ni Sunana ba parrot ba, kaji sai kace uba na sai bada order yake wa mutane"


"mekike cewa? yafada yana tsare gida,

bata rai tayi kana tace " bance komai ba" kwafa yayi domin ya dan ji wasu abubuwan daga maganarta

"zanyi maganin bakin rashin kunyar nan"


shiru tayi kamar bata jiba.


Faheemah dake jin dramar su sai danne dariyarta take, bayan ya gama ne ya shiga ya duba jikin abokinsa kana ya fito ..




"ummu sababin ma'aikatan nan angama musu interview din and they are all qualified mun daukesu aikin"

murmushi ummu tayi kana tace "madallah dan albarka sannu da kokari, in sha Allah gobe zan leko naga yanayin aikin nasu duk da ka ma yar dani yar hutu dole" ta karasa azolaye

" dariya yayi kana yace ummu kin cancanci hutu meye amfanin mu?"

cikin jin dadi tace Allah yamuku albarka, suka amsa da

"ameen"



*JAMEELAH*


"Baby abbuh yace yanason ganin ka fa"


"lafiya dai ko honey?"a cewar salman.


"Lafiya ba matsala
Toh yaushe Kika shirya fitar mu?"


"Ina ganin idan mun gama exams yayi ko? Ko kefa honey gaskiya yau kin sa ni farinciki"


yafada yana tsakar mata murmushi yaudara!

Itama murmushi tayi aranta kuwa cewa take gwara ayi fitar nan na huta da maganar fita kullum, afili kuwa cewa tayi

"amma honey yaushe zaka zo wurin abbuh na?"

Sosa keya yayi kana yace ina tunanin bayan mun fita outing dinan Zan sa lokacin zuwa wurin Shi"


Toh shikenan bari na shiga cikin gida, haba honey haka zaki shiga babu wata kyakyawan sallama?"


Kallo karin bayani ta masa kana tace "toh ka gaida gida bye"

bata rai yayi kana yace "ba irin wanna sallaman nake nufi ba, I know kin fahimci abunda nake nufi, bari kiga"
yafada yana laluban labb'anta....


bakinsa ya sanya cikin nata ya shiga kissing dinta azafaffe, kamar gunki haka ta tsaya batare da ta dakatar dashi ba....


Kusan 7min ya dauka yana kissing dinta, kafin dan kansa ya zare bakinsa yana sauke numfashi kana yace

"gaskiya yau kin burgeni bakiyi gardama for that ga wanna"

ya miko mata bundle din yan dari biyar -biyar, abun mamaki sai tasa ahannu ta amsa cikin farinciki, aransa kuwa cewa yake "yar matsiyata kwadayayya kawai , ai nasan logonki son kudi"....


"Honey baka jine?"

Firgigit yayi daga tunanin kana yace

"na'am me kikace? "

"nace na shiga gida"

" okay my honey Sai na kiraki ga kazar nan ko kin manta?"

Dawowa tayi ta dauka hadi da rufe masa mota ta fice cikin farinciki samun kudin, domin dama bikin da sukayi duk kudin daya bata ya tafi a karyan arziki....




"Wai wai amma wanna yaron dan albarka ne ya iya kyautar ban girma"

dariya jameela tayi domin duk lokacin da salman yabata kudi haka mami ke wanna rudewar, "nace ba, diyar albarka ya zancen kudin da kika ce zaki bani?"

" Kai mami! Wallahi na rasa ina kike kai kudi kullum cikin bani bani kike, gadai dubu ashirin" tafada tana miko mata


Cikin farinciki ta amsa tana sa mata albarka bata ko damu da yanda jameelan tayi mata magana cikin rashin ladabi ba...





*Tnx for reading my novel #rayuwar faheemah (littafin kyauta ne)*



Noor ce๐Ÿฅ€๐ŸŒธ


๐Ÿ’”RAYUWAR FAHEEMAH ๐Ÿ’”
_by Noor Eemaan_๐Ÿ“šโœ๏ธ

kyauta ne( free novel)



https://facebook.com/groups/943534712916776/

Masu amfani da Facebook sai kuyi join wan nan link din
I'm selling data to all Nigerian network Thank you for contacting Sdeendtm!
BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE
I'm
selling MTN data with this cheap price
MTN DATA PACKAGE*
500MB@===200
1GB@=====300
2GB@=====600
3GB@====900
5GB@====1,500

Dial *131*4# or
*460*260# to check Data balance Validity 1 month
Airtel,9mobile and Glo also available.

*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Whatsapp OR
Call 0806626851


SPEAK only when you feel your words are better than silence. ๐Ÿ‘Œ



29-30


Zaune suke a falo, Ummu ta dago ta kalli faheemah tace

"diyata faheemah "


"na'am ummunah " ta amsa cikin sanyin amo.

"Nace ya maganar wayar damukayi har yanzu baki zabi wacce kikeso ba, ko kuma kin ban zabi ta karasa maganar cikin sigar tambaya"




1 Comments On RAYUWAR FAHEEMAH
avatar
muhammad-2-2

11 months ago

Reply

My

Please Login or Register in order to submit comment