Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

A ƙasin benin su Doctor Roshan nan ma ɗakuna uku ne a jere a ɗaya daga cikine aka ajiye Baiwar ALLAH, sai kuma ta kusa da ɗakinta ɗakin Aunty Yolash ce idan tazo hutu,


Baiwar ALLAH tana zaune a bakin gadonta Ummy itama tana zaune ta gefenta tana riƙe da hannunta tace "Please Aunty Meye sunanki?..."

Baiwar ALLAH kallonta tayi tare da sau murmushi tace Baiwar ALLAH...."

Cike da mamaki Ummy take kallonta tace "ikon Allah sunanki kenam? Allah sarki, toh ki kwantar da hankalinki bazaki sha wahala acikin gidan nan ba Insha Allah, kar kiji fargaban Hajiyar mu just saidai tayi barazanar ta....."

Haɗiyar yawu Baiwar ALLAH tayi tare da jinjina kai tana murmushi ba tareda ta ce komai ba,

Aunty Yolash tana tsaye tana jinsu idonta akan Baiwar ALLAH ta ce "duk abinda akayi miki acikin gidan nan na wulaƙanci kiyi gaggawar sanar mun, za'a ɗau hukunci akai..." ta kalli Ummy sannan ta kuma cewa "Uwar masu gida idan kika ga anyiwa baiwar Allah abinda bai dace ba to ki sanar mun, Ni kuwa na sanarwa Abbanku kinji koh?....."

Ummy jinjina kai tayi tare da faɗin "Insha ALLAH Aunty..."

daga nan Aunty Yolash tayi musu sallama tace "Ni zan koma Bauchi saina sake zuwa..."

Ummy tace "TOH Aunty ko nazo na rakaki ne?..."
Aunty Yolash tace tana murmushi ta ce "Ni da zan tafi a motar! ki kwantar da hankalinki ganan amanar Baiwar ALLAH an baki ita ki kula mana da ita, yanzu tashi ki nuna mata gurare acikin ɗakin da toilet kafin ku fita yin siyayyan kayayyaki...."

Ummy tana murmushi itama tace "TOH Aunty..."

daga nan Aunty Yolash ta tafi...

Bayan Ummy ta nunnuna mata gurare har cikin toilet tacewa Baiwar ALLAH "ganan ɗakinki, yanzu dai tinda yamma ta gabato mu bari sai gobe da safe muje super market koh! saboda idan mun fita yanzu dare zai iya mana, kuma inada burin mu zazzagaya har gidan zoo da waran wasanni, mu ɗan je yawon shakatawa, yanzu dai bari naje na dubo miki kayan da zaki chanza acikin kayana sai kiyi wanka kafin na dawo kiji...."
tana kaiwa nan tayi ficewarta.

Baiwar ALLAH murmushi kawai take domin Ummy ba ƙaramin burgeta take ba, tashi tayi ta shige toilet kamar yanda Ummy ta umarceta, da shigar ta brush ta farayi sannan tayi wanka tare da ɗauro Alwala..
tana fitowa kuwa ta tarar da Ummy harta kawo mata kayan ta ajiye a saman gado, saidai tana kawowa tayi ficewarta,
Murmushi Baiwar ALLAH ta ƙara saki sannan a fili tace "Allah Sarki a duniyan nan yanda kaga maƙiyanka haka zakaga masoyanka..."

ɗaukar doguwar rigar tayi ta zura har ƙasi sannan ta ɗauki dogon hijab ta shimfiɗa sallaya ta tsaida sallah,


Misalin ƙarfe 8 na dare bayan kowa ya zazzauna a dinning za'a ci abinci, zama sukayi suna jiran fitowar Hajiyarsu domin bame fara cin abinci sai kowa ya hallara haka dokar yake, Ummy ganin mommy batada niyar fitowa yasa ta ɗauki ɗaya daga cikin kulolin abinci zata nufin ɗakin Baiwar ALLAH domin tasan yau ne farkon zuwanta gidan bazata iya cin abinci a cikin mutane ba ,

Jin murya kamar daga saman yasa Ummy tsorita da sauri ta ɗaga kanta sama ganin Mommynsu tayi tana tsaye a saman Upstairs tana kallon na ƙasan falon,
Cikin ɗaga murya tace "ina zaki kai mun kular abincin?..."

Ummy idonta akan Mommynsu ta ce "mommy a baƙuwar mu zan kai, ba lallai ne ta iya ci acikin mutane ba ....."

Hajiya Kilishi kasa yin magana tayi ta zuba mata ido ganin yanda shishshigin Ummy yayi yawa, ji take kamar ta dirƙo daga saman stairs tazo ta rufata da duka,
tana hararar ta tace "kinibibi, iyeyi, kisisina, rawar kai, da son gwaninta wallahi zaki ci ƙaniyarki ne a wajeni idan baki kikiyayeni ba, saboda ubanki yana goya miki baya shine zaki raina mutane ko?
Ita ɗin baƙuwar dan ubanta tafi ƙarfin fitowa tazo ta karɓa saidai akai mata? kije kice ta fito inji Ni matar gidan, ba'a kawota don ta ci ta sha ta kwanta ba...."

Ummy jiki ba ƙwari tazo ta ajiye kular sannan ta nufi ɗakin baiwar Allah! harta kusan isa Hajiya Kilishi ta tsayar da ita tare da faɗin "na fasa aikenki ma dawo ki zauna domin bana ƙaunar ki haɗa alaƙa da waccan yarinyar da batada asali...."

ta kalli yanda ƴar Tiny take zaune sai faman tura abinci take domin ita bata jiran sai kowa ya hallarun Nan, Hajiya tace "Auta je ɗakin ƙazamar yarinyar nan da aka kawota ɗazu ki ƙira mun ita...."

Ƴar Tiny da gudu ta nufi ɗakin tana cewa "TOH mommy...." ta ƙarasa maganar daiden lokacin da ta tura ƙofar ta shiga...


Minal harara ta gallawa Ummy tana faɗin "munafukar Banza kawai, idan baki kama kanki ba sai nayi miki dukan tsiya wallahi mttssw...."

Ummy tana jinta ko ɗagowa batayi ba balle ta kalleta sai ji tayi su twins suna faɗin "anya kuwa Ummy jinin gidan nan ne kuwa? naga ɗabi'unta gaba ɗaya babu kala...."
A daidai lokacin da Hajiya Kilishi ta ja kujera ɗaya ta zauna itama fuska a haɗe domin bata farin cikin kawo baiwar Allah, hatta ƴan aiki basa zama mata a gida saidai suzo suyi aikinsu su tafi, bata ƙaunar ganin baren mutum a kusa da ita....


Ƴar Tiny tana zuwa ta tarar da baiwar ALLAH tana kwance saman katafaren gadonta sai shan bacci take bayan tayi Isha'i,
Ƴar Tiny tana huro hanci tare da Turo baki ta kai hannu ta ɗauki wata ƴar ƙaramar allura akan mirror ta Cakawa Baiwar ALLAH a saitin ɗuwawunta, dan ma da hijab a jikinta, a zabure baiwar Allah ta tashi tana salati domin mintsinar ba ƙaramin ratsata tayi ba, har cikin ƙwaƙwalwata,

Baiwar ALLAH tana kallon Ƴar Tiny kamar zatayi kuka tana sosa wajenda ta caka mata allurar,

Ƴar Tiny tana farfara ido tace "ke ɗin meya kawo ki gidan mu, kuma har da saka kayan Aunty Ummy to ki cire mata kayan ta kar ki shafa mata datti...."

Haka ƴar Tiny ta kai hannu tana jan rigar jikin baiwar Allah wai saita cire kayan Aunty Ummy, har da fashewa da kuka tana ja...

Baiwar ALLAH gaba ɗaya hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, ta rasa yanda zatayi da ƴar Tiny,
Ita damuwarta kar ƴan gidan suce dukanta tayi.......





*DAN ALLAH KUYI HAƘURI DA WANNAN PAGE ƊIN, KU ƊAN RAGE SANNAN KUYI MUN UZURI BANA SAMUN YI MUKU UPDATE DA WURI, AKWAI ƊAWAINIYA SOSAI A GABA NANE, AMMA INSHA ALLAHU GOBE INSHA ALLAHU ZAMU KOMA GIDA SABODA GOBE ZAMU KAMMALA EXAM, DA ZARAR NA KOMA KOMAI ZAI ZO DA SAUƘI, KUYI HAƘURI.....*


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 15 to 16



꧁꧂


Jin ihun da ƴar Tiny take yasa twins suka shugo ɗakin da gudu suna faɗin "meya faru ne Auta?..."
suka kalli yanda Baiwar ALLAH take a zaune suna jifanta da harara baki a haɗe wajen cewa "la'ananniya me kika mata?..."

Baiwar ALLAH tana zubda ƙwallah tace "wallahi ba abinda nayi mata, ina kwance ta caka mun allura sannan ta fara ihu...."
bata ƙarasa maganar ba taji Pinky ta darara mata tsawa tare da faɗin "yimun shuru Mayya kawai, karuwar waje toh bari kiji gidan nan bawai kin shigo shi don hutu bane sai zallar wahala, kisa a ranki cewar a matsayin ƴar aiki aka kawo ki yarinya...."
ta ƙarasa maganar tare da jan hannun ƴar Tiny suka fice, itama Ruky harara ta watsa mata tare da jan dogon tsuka suka fice...

Baiwar ALLAH fashewa tayi da matsanancin kuka tana cikin wannan halin taji an dafa kafaɗarta ana bubbugan bayanta cikin sassanyar murya
Tace "kiyi haƙuri komai yayi farko zaiyi ƙarshe, ki tashi muje kici abinci...."

Baiwar Allah ɗagowa tayi tana kallon Ummy da rinanan idanuwanta haka ta tashi jiki ba ƙwari sukayi falo,
A dinning table Baiwar ALLAH ta zauna itama Ummy zama tayi a kusa da ita tana zuba mata abinci a plate,
Baiwar ALLAH ɗaukar spoon tayi tana ɗibar abinci tana ci kamar wacce ta shekara bata ci komai ba, tsabar yunwa tura abincin kawai take har tana ƙoƙarin ƙwaruwa, dasauri Ummy ta ɗauki cup mai ruwan sanyi ta bata tasha, suna cikin wannan halin saiga Minal ta sauƙo daga stairs idonta akan Baiwar ALLAH wacce take ta tura abinci, cike da izzah tazo waran ta tsaya tana yamutsa fuska tace "Keee!..."

Baiwar ALLAH ɗagowa tayi a hanzarce tana bin Minal da kallo, Minal harara ta watsa mata tare da faɗin "kar ki sake haɗa eyes dani, inba haka ba saina carkwane idon...".

Dasauri ta sunkuyar da kanta ƙasi sannan ta cigaba da cewa "Meye matsayinki acikin gidan nan?..."

Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi ba tare da tace komai ba,
Tsawa Minal ta daka mata cewar "ba magana nake miki ba?..."

tana kuka tace "Nima ban sani ba wallahi ...."

Minal tace "okay zaki sani ai, bakida wani matsayi acikin gidan nan don haka kada na sake ganin kin ɗosana ɗuwawunki acikin ɗaya daga cikin kujerun dinning ko na falo, na haramta miki wannan umarni nane, saboda haka yanzu ki sauƙa ƙasi ki zauna mayyar abinci kawai....."

Baiwar ALLAH tashi tayi daga kan chair ta zauna a ƙasi da plate ɗin abincinta a hannu,

Juyawa Minal tayi zata tafi Ummy tayi saurin cewa "amma gaskiya Aunty Minal baku kyautawa, ki tambayi Abbah ya rigada ya bata matsayi a cikin gidan nan, itama ta zamo ƴar gidan....."

bata ƙarasa maganar ba taji Minal ta darara mata tsawa
"Shutt uppp! your very stupid idan baki shiga taitayinki ba wallahi i will teach you a lesson, naga kwana biyun nan tsutsar kanki na motsi, bari Abba ya tafi kiga aiki da cikawa...."
taja dogon tsuka tare da wucewa fuuuu kamar zata ɗaga sama, hanyar waje tayi zata fice....

Ummy girgiza kai tayi tare da faɗin "ALLAH ya sawwaƙe ya kuma shirya mana zuri'a..."

Ummy ta kalli Baiwar Allah sannan tace "ki cigaba da haƙuri wata rana sai labari, sannan duk abinda sukayi miki ki daina nuna damuwa ƙarara a fuskarki dama zuciyarki gaba ɗaya domin su haka suke so su rinƙa ganinki acikin damuwa, idan kina biye musu ciwo ne zai kamaki banda yawan kuka please...."

Baiwar ALLAH ta jinjina kai sannan tace "Insha ALLAH Sister zanyi ƙoƙarin yin hakan...."

da murmushi a fuskokinsu haka suka kammala kowa ya kama waran makwancinsa, Ummy ta haura upstairs ita kuma Baiwar ALLAH ta wuce ɗakinta, tana shiga ta nufi toilet ta watsa ruwa ajikinta tare da ɗauro Alwala sannan ta fito ta tsaida sallar isha'i....



꧁𓇽꧂


🇾 🇦 🇷➪🇦 🇲 🇦 🇳 🇦 🧚🧚🧚🧚

tana kwance akan katifarta kamar yadda ta saba kullum, a wannan lokacin misalin ƙarfe 1 ne na dare, acikin bacci take jin ana ƙiran sunanta a hankali yasa ta buɗe idanuwanta gaba ɗaya tana ɗarɗar ga kuma daman a tsorace take tin ranar da ta laɓe a jikin ƙofa taji ana faɗin acikin satin nan za'a tura ta can ƙasar waje domin an rigada anyi cinikinta, da sheƙeta za'ayi daga baya kuma suka canza shawari, a ruɗe ta tashi zaune tana waige-waige ganin babu kowa sai hasken nepa da yake kashewa yana kunnuwa da kansa, Ƴar Amana fashewa tayi da kuka ganin babu wata mafita, wata siririyar murya taji anata tintsirewa da dariya ga hasken ɗakin ya ɗauke gaba ɗaya sai duhun daya biyo baya,
tana cikin wannan halin taji an ɗagota sama tare da yin hajijiya da ita sai ɓatt ta ɓace gaba ɗaya, ana ɓacewa da ita sai hasken ɗakin ya bayyana,
Ƴar Amana bata tashi tsintar kanta ba sai a bakin ruwa, wajen tsittt babu motsin kowa sai ƙarar ruwa wanda yake kai kawo ga kifaye yanda suke tashi sama suna tsunduma cikin ruwan, bata iya hango ƙarshen ruwan ba tsabar faɗi da tsayi ga kuma zurfi, ga wani irin sanyin da yake ratsata, ƙasar wajen laushi babu gudan dutsi ko ɗaya,
tana ta faman waige-waige amma babu alamun mutum ko wani abu mai rai, gaba ɗaya a kiɗime take tana cikin wannan halin tada an ajiye wata ƙatuwar jita da red flower akai sannan taga an ajiye wata jar doguwar riga da takalmi ba tare da taga ko waye ba, idonta akai haka take matsowa gurin a hankali lips ɗinta na kakkarwa, domin ƴar Amana idonta idon ganin jita ko wani irine saita taɓa, tana zuwa wajen taga lokaci guda an sanya mata doguwar rigar da takalmi sannan anyi mata gyaran gashi, abun ba ƙaramin mamaki ya bata ba, kallon kanta take sosai ta cigaba da kallon gefe da gefenta ko zata ga wani amma babu motsin kowa, hannu na kakkarwa takai kan jitar tana daddannawa a hankali yana bada sautin kiɗa, acikin tanayi a hankali harta komo tana daddannawa da ƙarfi ga wani irin sauti mai daɗin gaske yanda yake tashi, haske ne ya fara bayyana a wajen mai farfatsin wuta kala-kala, lumshe idonta tayi a hankali tana wasa da yatsunta akan jitar....


🇧 🇦 🇮 🇼 🇦 🇷➪🇦 🇱 🇱 🇦 🇭 
Dake kwance saman katafaren gadonta jin sautin kiɗa yana dukan dodon kunnenta yasa tayi saurin buɗe eyes ɗinta domin tasan kalar sautin nan irin na ƴar Amana ce, dasauri ta sauƙa daga kan gadon taje jikin window ta buɗe tabulen window tare da zuge glass ɗin window, wani irin haske taga yana tashi sama mai kaloli kala-kala ga kuma yanda sautin yake tashi amma saidai ba murya, murmushi Baiwar ALLAH tayi tasan wannan Ƴar Amana ce domin iya kiɗa take badawa babu bakin magana,
Lumshe ido Baiwar ALLAH tayi sannan ta fara bin yanayin kiɗan tana rera waƙar a hankali, da kaɗan kaɗan har sound ɗinta ya fara tashi da gaske tana bin sautin tana rera waƙar itama ido a lumshe tana daga cikin ɗaki a tsaye a gaban window....

Ƴar Amana itama tana ɓangarenta wanda bata san a yanda take ba haka take jiyowa muryar Baiwar ALLAH yana dukan dodon kunnenta yanda take bin sautin tana rerawa, a gaggauce Ƴar Amana ta buɗe idonta tana kallace-kallacen ko zata ganta amma sai dai iya haske kawai take gani yana ta farfatsi hakan ya ƙara ƙarfafa mata gwiwa tana daddanna jitar tana bada sautin, itama Baiwar ALLAH tana can tana rera waƙar, haka kowa yake jiyo wa ɗan uwansa...


Yana kwance akan lallausar gadonsa mai girman gaske yana lumshe da kyakykyawan idanuwansa ga kyakykyawar fuska kamar mai yin murmushi, a hankali yake shan baccinsa kamar a mafarki yake jiyo sauti mai daɗin gaske da kuma murya mai kashe zuciya suna dukan dodon kunnensa, ganin kamar ba'a cikin mafarki yake jiyowa ba yasa ya fara buɗe eyes ɗinsa a hankali yana lumshe su gwanin burgewa, jin har yanzu bai daina jin sautin da muryan da ake rera waƙar ba yasa ya ƙara miƙewa zaune yana waige-waige, tashi yayi a hankali yana taku har ya isa bakin ƙofar bedroom ɗinsa yana shirin buɗewa yaje falo ko plasman ne a kunne, har yakai hannu zai buɗe idonsa ya sauƙa akan window dake bai gama sauƙar da labulayen ba, wani irin haske yake gani ta waje yanata tashi mai farfatsin wuta kala-kala, cike da mamaki yaje jikin window yasa hannu ya ƙara buɗe labulen yana kallon wannan hasken, ga sautin kiɗa yanda yaketa tashi sannan zazzaƙar murya yana kan dukan dodon kunnensa, wani irin sanyi ne ya fara ratsa shi a hankali yake lumshe idonsa,
Sautin kiɗan da yake ji ba ƙaramin kashe masa jiki yayi ba,
A hankali yake motsi da lips ɗinsa ido a lumshe ya ce "WHO is dis girl? me suke nema a gareni?...."
still bai buɗe idonsa ba ya cigaba da cewa "ƴan mata biyu! ɗaya tana kaɗa jita, ɗaya tana rera waƙa, kullum saikun zo mun a mafarki yanzu kuma sautin kiɗa da kuma sautin Muryar ku sun fara bayyano mun a zahiri shin me kuke nema a gareni? shin ku ɗin aljanu ne ko mutane? ku bayyana mun kanku mana, ku daina azabtar da zuciyata haka, ku daina hanani bacci please, idan wani abu kuke buƙata ku bayyanar mun da kanku,
Ku gaya mun me kuke so! me kuke so!! me kuke so!!!
I said tell me what do you want from meeeee......"
A tsawace ya ƙarasa maganar tare da bugan jikin glass ɗin window da ƙarfin gaske har sai da ya dagargaje glass ɗin, hannunsa yaji rauni sosai daiden lokacin da komai ya ɗauke cakk babu hasken nan sannan babu sautin kiɗa kuma babu Muryar waƙar,
ya faɗa saman gadonsa yana caccakuɗa sumar kansa tare da yin ihu tsabar juyawar da kansa ke yi ga wani irin ciwonda yake yi haka yake ihu har sai da sojoji masu gadinsa suka jiyo ihunsa, da gudu suka turo

Please Login or Register in order to submit comment