Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafin Uncle Deen ya juyo ya bashi amsa har Marshall ya yi saurin buɗe murfin mota ya fice,
kai tsaye waran su ya nufa, yana zuwa ya fara ɗaga musu hannayensa biyu sama tare da dakatar dasu da cewa "ku dakata! Ku dakata!! Ku dakata haka....."

kafin kace mai gurin yayi tsit idanuwansu akansa, sai wata tsohuwa ce tayi ƙarfin halin cewa "meye damuwarka damu? nan yankin mu ne sai muyi abinda muke so...."

wata daga ciki itama ta ce "idan wucewa zakayi yau mallakarka sai dai ka juya baya ai ba nan ne kaɗai hanyar wucewa ba...."

Marshall yasau ajiyar zuciya tareda faɗin "kunga kuyi haƙuri, ba wai dakatar daku zanyi ba nima ɗan uwanku ne mai son kiɗe-kiɗe amma yanzu dai ku ɗan ara mun yarinyar ku zanyi magana da ita....."

wata daga cikinsu ne ta buɗe baki zatayi maganar cewa kurmiya ce!
Ƴar Amana tayi saurin ɗaga mata hannu akan tayi shuru karta sanar masa,
domin duk abinda zai ce zata ji shi mayarwa ne bazata iya ba,
A hankali take taku cikin ƙasaita ta nufi yanda yake ta tsaya dab dashi tana fuskantarsa tare da goya hannayenta ta gaban ƙirjinta,

Marshall haɗiyar yawu yayi wanda bai san ya yi shi ba, gaba ɗaya yarinyar ce ta fara bashi tsoro ganin irin ƙarfin halin da take da shi, still ya tuno da cewa ita ce take wahalar da Major acikin mafarki gaba ɗaya sai yaji wani irin gumi ya yanko masa,
tin daga kan ƙafarta ya fara binta da kallo ganin tana sanye da farin takalmi toes, sai wani gajeren wando wanda ya tsaya mata a iya gwiwarta da rigar Best wanda bai ƙarisa rufe cibiyarta ba daga nan eyes ɗinsa suka sauƙa akan kyakkyawar fuskar ta wanda yake a ɗaure babu wani annuri a tattare da ita,
ga wasu murɗaɗɗun gashi wanda ya baje mata har gadon baya,
yana gama ƙareta da kallo ya juya da gudun gaske ya nufi yanda motarsu take, a cikin motar ya tarar da Uncle Deen zaune yana kallon duk abinda yake faruwa,
ba tareda ya shiga cikin motar ba ya zura kansa ta cikin glass yana haki yake cewa "Major haƙiƙannin gaskiya na yarda cewa wannan yarinyar itace take fito maka acikin mafarki domin zubinta irin na Aljanu ne sak,
Amma sai dai yarinya ce ƙarama domin ko Nono bata fara ba,
bari na koma gurinta yau zanyi magana da Aljana....."

haka ya juya ya koma yanda ya baro ta,
Shi dai Uncle Deen yana jinsa amma ya kasa cewa komai saboda Marshall yana shirin bashi dariyar da rabonsa daya yi tin yana yaro ƙarami....

Marshall tsayawa yayi shima yana fuskantar ta saida yayi gyaran murya kafin ya soma magana kamar haka
"Am da farko dai sunana Marshall Mohandas daga ƙasar U.S,
ke ina son jin sunanki....."

Ƴar Amana gyara tsayuwarta tayi idonta akansa, ta ɗago da hannunta ɗaya tana yiwa mutanenta alamar su gaya masa,
Gaba ɗayansu a tare suka buɗe baki waren faɗin
"ƳA DAGA ALLAH...."

ɗan zaro eyes ɗinsa ya yi cike da mamaki ya ce "kenam daga sama ta faɗo?...."

baki a haɗe wajen cewa "kana tantama ne?...."

Dasauri yake girgiza musu Kai alamar "a'ah..."

sunkuyar dakai yayi ƙasi yana maganar zuci "Tabb Jesus Christ! ban taɓa ganin Aljana ba eyes to eyes ba sai yau...."
bai ankara ba yaji ta ɗago hannu sama ta riƙo haɓarsa sai faman juyar masa da idanu take,
cikin rashin fahimta yake binta da kallo jikinsa har ɓari yake jin Aljana ta taɓa shi,
wata tsohuwa ce ta ce "tana maka alamu ne daka zo kuyi rawa...."

zaro ido waje ya yi tare da faɗin "Rawa kuma?
okay tam ku jirani ina zuwa....."

Juyawa yayi ya nufi motarsu, yana isa ya kuma tsayawa a jikin motar yana fuskantar Uncle Deen ta glass ya ce "wallahi Major tsoronta nake ji kuma tace muyi rawa...."

murmusawa Uncle Deen ya yi sannan ya ce "kar ka damu mutum ce kamar kowa, kaje kayi abinda ta saka...."

Marshall ya ce "okay tam kunna mana waƙa...."

Ba musu Uncle Deen yasa hannu ya kunna Audio domin yana son faranta mata so yake yaga murmushinta ko sau ɗaya ne....

Kafin Marshall ya isa wajen har Ƴar Amana ta fara cashewa da rawa jin sautin ƙida mai daɗi, shima Marshall jujjuyawa ya fara yi yana rawa,
kafin kace mai sauran mabaratan ma duk sun mimmiƙe suma suka fara jujjuyawa da masu ƙarfin jiki da marasa ƙarfin jikin duk rawan suke,
Gurage suma haka suke rawa a zaune, Kutare suma salon rawansu daban yake har da makafi,
a wannan lokacin kowa ya kasance cikin farin ciki da annashuwa,
Ƴar Amana ganin yanda tsofaffi suke cashewa yasata kwashewa da dariya ba tare da sautin ya fito ba, wannan dariyar da tayi akan idon Uncle Deen tayi shi,
Dariyar ba ƙaramin yi mata kyau yayi ba shima yana zaune ta cikin motarsa bai san lokacin da ya sake wata ƙayatacciyar murmushi ba,
babu wanda yasan da mutum acikin motar domin Black glass gare ta,
Marshall shima lokaci guda ya tsinci kansa cikin farin ciki duk wata damuwa babu ita,
wasa-wasa shima ya zage sai girgizawa yake yana tintsirewa da dariya,
saida sukayi rawarsu mai isarwa sannan yaje ya ɗebo tilin maƙudan kuɗaɗe yazo ya rarraba musu,
ya tafi yana ɗaga musu hannu cikin nuna farin ciki, suma sunyi matuƙar farin cikin kasancewa da shi,
Da haka Uncle Deen yaja mota suka tafi cikin kewar rashin ganin Dreamer sa.....


𝙄𝙉𝙏𝙀𝙍𝙑𝘼𝙇



Da yamma liss misalin ƙarfe 5 Baiwar ALLAH tana zaune a ɓangaren swimming pool wanda ya kasance a bakin ruwan akwai jerukan kujeru na alhurma masu ƙayatarwa da tables, hakan na nufin waran shakatawa kenam, tana zaune akan kujera ita kaɗai tasa ruwa a gaba wanda ya kasance launin blue gare shi,
tayi tagumi da duk kan alamu doguwar tunani ta faɗa,
fuskarta ya nuna tsananin damuwa ƙarara ita kaɗai tasan matsalar dake damunta,
tana cikin wannan tunanin taji an dafa kafaɗarta, a zabure ta miƙe tsaye tare da juyowa tana son ganin wanda yake bayanta,
Ganin Roshan yasa ta kawar da kanta gefe tana faɗin "taya kasan ina nam?...."

dogon numfashi ya sauƙe tareda faɗin "Ummy ce ta sanar mun cewa taga kinyo nan, wai me yake faruwa ne naga kamar bakida lafiya...."

"Lafiya ta ƙalau...." a takaice tayi maganar fuskar ta na kallon gefe,

Murya ciki-ciki ya ce "Ammata me yasa kike gudu na? bakya son haɗuwa dani! Abbah ya ce na ɗauke ku ke da Ummy kuje ku zaɓi kayan furnitures amma ke sam kin ƙi zuwa sai da iya Ummy na tafi,
me yake faruwa?...."

Hawaye ne yake shirin zubo mata tayi saurin sunkuyar dakai saboda kar ya gane a taƙaice ta ce "babu komai, bani da lafiya ne ..."

A ruɗe ya ce "Subhanallahi Ammata bakida lafiya shine baki sanar mun ba? meye amfanin aikin likitanci na indai bazan iya kula dake ta hanyar bada magani ba..."
ya jawo ta jikinsa yana faɗin "gaya mun me yake damunki? bana son ganinki cikin damuwa...."

lokaci guda ta fashe da matsanancin kuka daman jira take a taɓota tayi kukan da ya tsaya mata a rai,
a firgice ya zaro handkerchief ɗinsa daga aljihu yana ƙoƙarin goge mata hawayen fuskarta,
shima kamar zai fashe da kuka yake faɗin
"Ki daina mun asarar hawayenki mai matuƙar tsada, dan ALLAH Ammata nah,
ina jin zafin haka a raina....."

Sam bata son Auren nan amma gaba ɗaya kamar wanda aka ɗaure mata baki ta kasa sanar masa,
Soyayyar Uncle Deen zai hallakata, ta kamu da matsanancin sonsa bana wasa ba,
inta tuno cewa bashi zata Aura ba sai taji kamar ta hallaka kanta,
cikin takaici da baƙin ciki bata san lokacin data ɗago daga rungumar da yayi mata ba, tasa hannu da iya ƙarfinta ta ture shi baya daman yana dab da ruwa, ƙafarsa ta zame sakamakon tsantsin tiles dake wajen ya yi baya ya tsunduma cikin ruwan swimming pool,
Da sauri ta nufi hanyar fita daga part ɗin tana kuka, har ta fara hawa saman beni zata fita ta waiwayo bayanta jin ko motsinsa bata ji acikin ruwan,
Gaba ɗayansa ya nutse ciki sai saman ruwan da ya shafe,
A tsorace ta juya da gudun gaske ta nufi bakin ruwan tana ƙiran sunansa
"Ya Roshan! Ya Roshan!! Dan ALLAH ka fito kar ka mutu a ciki, na shiga uku na, banaso nayi sanadiyar mutuwarka dan ALLAH Ya Roshan, wayyo Allah nahhh...."

Ganin babu wata mafita yasa itama ta faɗa cikin ruwan, dake bata iya ruwa ba haka ta rinƙa facal-facal a cikin ruwan, tana nutsewa tana ɗagowa da haka itama ta nitse numfashi yana shirin ɗagewa,
Lokaci guda saiga Roshan ya ɗago saman ruwan yana riƙe da kunkumin Baiwar ALLAH, tana fitar da numfashi sama-sama har ta sume akan faffaɗar ƙirjinsa,
Ɗarata yayi saman kafaɗar sa yake yana taka matakalar da zai fidda shi daga cikin ruwan,
Kwantar da ita yayi a ƙasin tiles duk jikinsu a jiƙe jirip, a hankali ya haɗe hannayensa biyu ya ɗora kan ƙirjinta yana dannawa a hankali daga bisani kuma yakai fuskarsa saitin nata yareda ɗora ɗan lips ɗinsa kan nata yana hura mata iskar bakinsa, cikin lokaci ƙanƙani numfashin ta ya dawo a hargitse,
tari ta fara yi tana amar da ruwan da tasha, daga baya ta buɗe lumshashshun idanuwanta kamar maijin bacci,
yana kwance ta gefenta eyes ɗinsa akanta itama shi take kallo haka suka shiga kallon juna ba tare da wani ya ƙibta a cikinsu ba,

A zabure suka dawo hayyacinsu jin magana kamar daga sama ance "iyyyeee soyayya haka...."

Ummy ce tayi maganar tare da juyawa da gudu tabar wajen,

Suma tashi sukayi, kafin ya ankara harta bar wajen da gudu itama,
tsayawa yayi yana kallon ta har ta ƙule masa,
shima jiki a jiƙe yake shirin barin part ɗin....

Da Daddare misalin ƙarfe 9 bayan an gama dinning,
Roshan ne zaune akan sopa 3 seater hannunsa riƙe da ledar Maganinnuwa har da Allurai, yayi tagumi alamar dogon nazari yake,
Ummy ce ta sauƙo daga upstairs da tarar da shi a cikin wannan halin, a hanzarce ta nufi wajensa tana ambaton sunansa
"Yaya Roshan!.." shuru bai ɗago ba ta ƙara maimaita ƙiran sunansa har sau kusan biyar saida ta bubbugi kafaɗarsa tukun yayi firgitt ya ɗago yana kallon Ummy,
Zama tayi a kusa da shi ta zuba masa eyes cike da mamaki take faɗin "Ango kuma a cikin damuwa?
Yaya Roshan me yake damunka alhalin kana shirin mallakar farin cikinka, kamata yayi a ganka cikin farin ciki...."

Ɗan tsuka yaja acan cikin harshensa yana dafa goshinsa ya ce "bansan me yake damun Ammata ba, gaba ɗaya guduna take bata son kasancewa tare da Ni, duk hanyar da zai haɗamu bata ƙaunar biyo wajen bansan me yasa ba...."

Sauƙe numfashi Ummy tayi tana hararar Roshan ta ce "Ɗazu ba ku na gani a swimming pool ba?...."

Girgiza Kai yayi cikin nuna damuwa ya ce "Ni na bita wannan wajen sannan da hannunta ta tura Ni cikin ruwa tana kuka zata bar wajen, bansan meya dawo da ita a wannan lokacin ba itama ta faɗa ruwan,
Nifa na fahimci kamar ba sona take ba....."

Zaro ido waje Ummy tayi tare da faɗin. "koda wasa kar kayi tunanin nan, domin Aunty Baiwar ALLAH tin kafin ku dawo take muradin son ganinka, idan taga hotonka har wani irin murmushi take saki na farin ciki,
Zai iya yuwa yanzun kunyarka take ji saboda an kusan ɗaura muku Aure, daman indai Amarya tanada kunya toh har ayi Auren bata son haɗa Ido da Angonta....."

kallonta yayi ya ce "wai da gaske kike?...."

cikin fara'a ta ce "sosai ma...."

Sai yanzu yaji zuciyarsa tayi wasarrr, murmushi ya saki tare da faɗin
"Ma sha ALLAH! indai rashin ganina shi zaisa tayi farin ciki to Ni kuwa nayi Alƙawari har a ɗaura Aure bazan ƙara barin mu haɗu ba,
tinda Amaryata kunya gare ta...."

Itama Ummy murmushi ta saki tare da kai hannunta kan ledar hannunsa tana faɗin "meye wannan?..."

Ɗan harararta yayi tareda faɗin "to Sarkin kwaɗayi pharmacy ne na ɗauko a medicine room zan bawa Matata ta ce mun tana jin zazzaɓi,
Kuma na bubbuga ƙofar ɗakinta taƙi buɗe mun...."

Ummy ta ce "ai nasan bazata buɗe ba indai tasan kaine, kawo nakai mata...."

Ya ce "Ok please kiyi ƙoƙarin ganin tasha maganin sannan kiyi mata Allurai tinda kema Doctar ce...."

Murmushi tasau tare da cewa "Insha ALLAH...."

ya miƙe tare da nufan upstairs dazai kaishi part ɗinsa, har yayi nisa ya juyo ya ce yana faɗin "gobe bazaku tashi ku ganni ba saboda da sassafe zamu tafi ƙasar Jidder Ni da twins, na baki Amanar Matata....."

Ta ce "to Allah ya kiyaye hanya My Sweet Bros...."

ta nufi room ɗin Baiwar ALLAH shi kuma ya wuce part ɗinsa,

Ummy a hankali taje tana knocking door tareda ambatar sunanta
"Aunty Daughter! Aunty Daughter ki buɗe ƙofa Ni ce pah......"

Kafin ta ƙara furta wani abu har tazo ta buɗe mata,
murmushi Ummy tayi tana faɗin "wato a Yayana ne baza'a buɗe ba koh?..."

Baiwar Allah ta koma ciki tare da ɗosana mazaunanta a bakin gado,
Itama Ummy zama tayi dab da ita tana kallon ta cike da mamakin ganin yanda ta rame tayi fari sol kamar ba jini a jikinta,

Baiwar Allah kallon front ɗinta take ko annuri babu a fuska,
Ummy ta ce "am daman magani akace na kawo miki, sannan zanyi miki allura..."

Baiwar Allah kallon Ummy tayi ta ce "waya ce miki bani da lafiya?...."

Ummy ta ce "labarin zuciya a tambayi fuska, gashi jikinki ya nuna cewar bakida lafiya..."
ta ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye ta nufi frig ta ɗauki ruwan jarkan ta koma side ɗin Baiwar Allah ta zauna,
buɗe ledar tayi ta curo Maganinnuwan gaba ɗaya tana ɓarewa tareda ƙoƙarin bata,

Girgiza Kai Baiwar ALLAH tayi ta ce "Ni lafiyata ƙalau bazan sha ba....."

Ummy cikin ɓacin rai ta ce "wallahi sai kin sha ko kuma naje na haɗaki da Abbah domin shi yace na kawo miki...."

Jin haka yasa ta karɓa ta watsasu a baki tare da kafa bakin jarkan ta korasu da ruwa,
Bayan ta kammala shan su gaba ɗaya, miƙa hannunta tayi Ummy tayi mata Allurai,
tashi Ummy tayi tace "saida safen ki...." tabar ɗakin domin ta fahimci kwana biyun nan Baiwar ALLAH bata son yiwa kowa magana,
Itama tashi tayi taje ta rufe ƙofar ɗakinta sannan ta shige bathroom tayi wanka, tazo tayi shigar sleeping dress ta ƙwanta zuciyarta cike da tsananin kewar Uncle Deen da son kasancewa tare da shi sannan tana muradin ganinsa.....

Asubar farko Yaya Roshan ya kammala haɗa jakarsa wanda zai tafi da ita domin zai iya kasancewa suyi kwana uku kafin su dawo,
ya kammala shirinsa tsab ya fice daga part ɗinsa zasu je masallaci, a falo ya tarar da Abbah yana zaman jiransa, a tare suka fice....



Shima a ɓangaren Uncle Deen bayan ya dawo daga masallaci zama yayi akan ɗaya daga cikin jerukan kujerun falon farko, zaro wayarsa yayi

Please Login or Register in order to submit comment