Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

idonta domin ba ƙaramin tausayinta take ji ba,
tana zaune har dare bata yunƙura ba sannan babu alamar motsin mutum, sai can misalin ƙarfe 12 na dare kowa da kowa yayi bacci saita fara jin motsin mutum a tsorace ta miƙe tsaye zuciyarta na bugun 3+3 tana tunanin har ta saddaƙar domin ta tabbatar da Yallaɓai ne, zai iya zuwa mata a kowani lokaci balle yaga ta fake gefe guda...
ji tayi ansa key an buɗe ƙofar a hankali aka shugo, bata iya ganin ko waye ba saboda tsananin duhun ɗakin, saida aka kunna hasken torch sannan taga ashe Aunty Habiba ce wacce take kula dasu, murya na kakkarwa Baiwar ALLAH ta ce "Aunty Habiba kece 🥹..."
Dasauri Aunty Habiba tasa hannu ta toshe mata baki alamar tayi shuru, a hankali ta soma cewa "Yallaɓai ya ce kada wanda yazo gurin da kike balle a kawo miki abinci ko ruwan sha, kuma ba'a san ranar fitar dake daga cikin wannan akurkin ba, nima a ɓoye nazo Ni domin na tabbatar Yallaɓai ya tafi gidansa zuwa anjuma zai iya dawowa ya bincike ki, yanzu abinda nakeso dake shine zan fitar dake a ɓoye ki gudu ki bar wannan gidan domin rayuwarki tana cikin hatsari Baiwar ALLAH..."

Baiwar ALLAH tana kuka ta ce "Aunty Habiba yanzu idan kika fitar dani shin baza kiyi laifi ba?..."
Aunty Habiba ta ce "kar ki damu dani babu wanda zai san Ni na fitar dake..."
Baiwar ALLAH taja dogon numfashi sannan ta ce "a gaskiya bazan iya tafiya nabar Ƴar Amana ba, ban san a wani hali zata kasance ba..."
Aunty Habiba ta dafa kafaɗarta ta ce "Baiwar ALLAH kar ki damu zan kula da Ƴar Amana sannan itama zuwa wani ɗan lokaci zan fitar da ita..."
Girgiza kai Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "a'ah gaskiya ki bar Ni kawai, insha ALLAHU zuwa gaba ALLAH zai kawo mana mafita ta wani hanya, domin nasan idan na fita bansan ina zan nufa ba, rabon dana leƙa cikin gari tin zuwana wannan gidan ina ƴar yarinya ta, yanzu bansan ya kalar garin yake ba, zan iya fita na tarar da waɗanda zasu kashe Ni ko su sace Ni, zan cigaba da zama tareda ƴar uwata Ƴar Amana...."

Aunty Habiba ta ce "shikenam Baiwar ALLAH duk yanda kika yanke Ni dai ina tare da ke, kuma bazan iya barinki da yunwa ba dole kullum zan rinƙa kawo miki abinci kuma kinsan yau da gobe sai ALLAH asiri na zai iya tonuwa shiyasa naso ki gudu, amma tinda kin ƙi bazan gajiya ba, ga wannan leda abinci ne a ciki idan kin ci saiki jefar da ledar ta cikin wancan ƙofar sannan ga pure water..."

Baiwar ALLAH rungumar Aunty Habiba tayi tana kuka ta ce "Nagode sosai Aunty Habiba amma ina tsoron kar a kama ki, da kin barni hakan nan idan ALLAH yaso zan rayu zan cigaba da rayuwata..."
Aunty Habiba tace "hakane amma bazan iya barinki da yunwa ba Baiwar ALLAH, yanzu dai zan tafi kar azo a ganni..."
har Aunty Habiba ta juya zata tafi Baiwar ALLAH ta tsayar da ita tareda faɗin "Aunty Habiba banyi sallah ba, dan ALLAH ki temaka mun zanyi sallah..."

Aunty Habiba ta ce "tashin hankali yanzu ya zanyi? Amma jira Ni ina zuwa..." Da sauri Aunty Habiba tabar wajen ba tareda ta rufe ƙofa ba, cikin ƴan mintuna sai gata ta dawo hannunta rinƙe da butar Alwala tana zuwa ta shiga cikin akurkin ta kunna light, ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske ganin babu Baiwar ALLAH ta fice, waige-waige ta soma yi tana faɗin "ina kuma taje? Na shiga uku...."

ajiye butar hannunta tayi sannan ta nufi compound ɗin ɗakunan yaran dasauri zata hau upstairs gida na sama sai taji ana buɗe gate ɗin gidan Yallaɓai ya dawo da mota zai shugo, gaban Aunty Habiba ne yayi wani irin yanke wa addu'o'i kawai take jerowa domin tasan halin Yallaɓai bashida mutunci, da gudu ta ƙarasa hawa saman beni kai tsaye ɗakin da Baiwar ALLAH suke ta nufa domin zata iya cewa zata gano Ƴar Amana, tana buɗe ɗakinsu kuwa saiga Baiwar ALLAH tana rungume da Ƴar Amana sai kuka suke ta sha,

Aunty Habiba ƙarasa shugowa tayi a ruɗe tana faɗin "yanzu Baiwar ALLAH abunda zakiyi mun kenam? so kike asirina ya tonu to Yallaɓai ya dawo kuma nasan zai iya zuwa yanda kike ya dubo ki..."
Baiwar ALLAH a ruɗe take kallon Aunty Habiba ta ce "bazan iya wuni guda banga Ƴar Amana ba..."
Aunty Habiba bazata iya jin abunda Baiwar ALLAH zata ce ba
a gaggauce tasa hannu zata jawota su koma kwatsam Ƴar Amana ta riƙe Baiwar ALLAH sosai tana girgiza kai alamar babu yanda Baiwar ALLAH zata je...

Aunty Habiba ta kalli Baiwar ALLAH sannan ta ce "ki sani cewa zaman ki a cikin ɗakin duhu shine zai ceceki daga tozarcin da za'ayi miki, yanzu kuwa idan har Yallaɓai ya ga kin fito toh kuwa zai iya ƙudurta abunda yayi niyar yi miki, saboda haka ki temaki kanki kizo mu koma kafin ya ankara dake..."
Baiwar ALLAH jin abunda Aunty Habiba ta faɗa yasa ta fara janye jikinta daga na ƴar Amana tana ƙoƙarin zamewa ita kuwa Ƴar Amana ta ƙanƙameta sosai da hannu ɗaya taƙi sakinta, Baiwar ALLAH tana binta a hankali saboda kar ciwon hannunta ya fame amma ita Ƴar Amana fur taƙi sakinta daƙer Aunty Habiba tasa hannu suka fincike hannun ƴar Amana wanda ta riƙe, da gudu suka fita itama ƴar Amana tabi bayansu kafin ta iso bakin ƙofar Aunty Habiba taja ƙofar ta rufe ta kulle ta baya...
a hankali suke bin jikin gini suna tafiya, da haka har suka sauƙa daga saman beni kafin su wuce dole sai sun bi ta gaban bakin ƙofar office ɗin Yallaɓai kuma gashi ƙofar a buɗe take haske ta ko ina, ƙafewa sukayi a gurin suka rasa yanda zasuyi, Aunty Habiba ce ta ɗan leƙa cikin office ɗin taga yanata bincika wasu takardu, ganin haka yasa ta kamo hannun Baiwar ALLAH suka wuce da gudu kafin ya ɗago,
Daiden lokacin da Yallaɓai ya ɗago gani yayi kamar wurgawar mutum, tsaya kallon bakin ƙofar ya yi kafin daga bisani ya miƙe tareda nufan bakin ƙofar ya fice, waige-waige ya tsaya yi amma baiga alamun mutum ba ga haske ta ko ina, girgiza kai ya yi sannan ya koma ciki a tunaninsa mutanen ɓoye ne suke wasa saboda yanzu misalin ƙarfe 1 ne na dare, kuma babu wanda zai iya shugo gidan saboda security dake can bakin gate, kuma babu wanda zai iya fita sai ma'aikatan gidan...

Suna isa wajen Aunty Habiba ta ce "toh ganan buta kiyi sauri kiyi alwala zan rufe ki ne..."
Baiwar ALLAH ta ce "to Aunty Habiba..."
haka ta samu tayi alwala sannan ta shige Aunty Habiba ta ce "ganan mayafina ki shimfiɗa kiyi sallah, na barki lafiya...". tana kaiwa ƙarshen tasa key ta rufe ƙofar sannan tayi tafiyar ta...
Haka Baiwar ALLAH tayi zaman ƙunci da kaɗaici tayi sallolinta tareda addu'o'i sannan taci abincin da Aunty Habiba ta kawo mata a leda tasha ruwa, tana zaune bata rintsa ba saida aka ƙira sallar asuba sannan ta tashi tayi sallar asuba saboda ta riƙe alwalar da tayi....


Shi kuwa Yallaɓai har zuwa wayewar gari bai wani tuno da Baiwar ALLAH ba, shi har ya manta da tana can cikin ɗakin duhu domin shi ALLAH ya ɗora masa cutar mantau, cikin ƙanƙanin lokaci zai iya manta abu saidai a tuno masa, kuma saiya ga mutum tukun yake tunawa dashi, harkokin gabansa kawai yake...


After one week
Har zuwa wannan ranar Yallaɓai bai tuno da baiwar ALLAH ba, kuma babu wanda ya tuna masa ko ya labanta masa, itama tana can kullum hankalinta a tashe yake gaba ɗaya ta gaji da zaman ɗakin duhun nan ga sauro kamar bala'i duk jikinta tabon cizon sauraye ne ko iya bacci bata yi saboda kullum acikin fargaba take especially idan dare yayi,
Kuma har zuwa yanzu Aunty Habiba takan kawo mata abinci da ruwan sha a ɓoye...

Ƴar Amana karayar hannunta sai dai Masha ALLAH ta fara samun sauƙi, duk ta rarrame na rashin ganin Baiwar ALLAH amma sai dai ana kula da ita sosai akwai wacce take zuwa ɗakinsu tayi mata wanki da gyaran ɗaki sannan ta temaka mata wajen yin wanka, Ƴar Amana kullum tana ɗaki bata fita ko ina,
abinci har ɗaki ake kawo mata,
Aunty Khadija kenam ita take ɗawainiya da ita bayan tafiyar Baiwar ALLAH, amma sai dai Ƴar Amana damuwarta shine taga Baiwar ALLAH!..

Misalin ƙarfe 5 na yamma Ƴar Amana ta fito bayan ɗakuna wajen lambu tana tsugune kamar mai tunanin wani abu, dama jira take hannunta ya fara samun lafiya kafin ta fara ɗaukarwa Yallaɓai hukuncin ta, faɗan kurma baya taɓa shigewa akwai tarin mugunta tarin-tarin azuciyar Ƴar Amana,
tana zaune ta ɗauki baƙar leda ta ɗaure tafin hannunta sannan ta fara ciran ƙarara tana sawa a leda, ta tashi ta bar wajen ba tareda kowa ya ganta ba, saida duhu ya fara gabato kafin a kunna Sola ta shiga office ɗin Yallaɓai cikin sa'a ta samu ya shiga toilet ɗinsa dake cikin office ga kayansa akan kujera yanda ya cire kafin ya shiga wanka, a gurguje ta fara zazzaga masa ƙarara a cikin kayansa riga da wando gaba ɗaya, zaiyi wanka anam saiya koma gidansa kafin yake chanza kayan sawa sai kuma ya ƙara dawowa haka yake wannan zirga-zirgar daga gidansa sai gidan marayu amma ba haka kawai yake yawan zaman gidan marayun ba saboda yana rage zafi sosai akan ƴan matan gidan, duk wacce yaso ya nema zai samu babu mai dakatar dashi...

Ƴar Amana tana gamawa ta fice kai tsaye saman beni ta haura ta nufi ɗakinsu,
Shi kuwa Yallaɓai fitowa yayi daga toilet yana ɗan raira waƙarsa tareda goge jikinsa da towel yana sanye da gajeren wando mai pant iya cinya,
ɗaukar wayansa yayi ya danna ƙira a waya cikin ƙanƙanin lokaci ya fara magana "Hello Maman Haneef ki dafa mun abinci mai daɗi ganinan zuwa sannan ina buƙatar ferfesun kifi..."
yana kaiwa nan ya katse ƙiran, ya ɗauki wandonsa ya zura sannan ya saka t-shirt ɗinsa mai roba-roba mai dogon hannu,
Gashi daga rigar babu singlet, ɗaukar key ɗin motarsa yayi da wayarsa yana shirin fita sai ji yake kamar ana mintsinan shi sai mil-mil yake taji, hannu yakai yana sosawa kafin kace mai duk jikinsa ya ɗau ƙaiƙayi, nan ya fara rikicewa yana sossosa jikinsa da hannu bibbiyu, kafin wasu seconni cikin wandonsa shima yaɗau ƙaiƙayi, hura iskar bakinsa yayi da ƙarfin gaske tareda tamƙe AK-47 ɗinsa saboda wani irin ƙaiƙayi da ya fara masa, acikin yana jurewa har ya koma yana ihu yana sose-sose haka ya haɗe bayansa da jikin gini yana gogawa kafin kace mai hawaye har ya wanke masa fuska,
Tinin hankalinsa ya fice daga jikinsa ya fice daga cikin officer ɗin da gudu yana kurma ihu, saida yazo tsakiyar filin gidan ya doku a ƙasi yana birgima tareda kurma ihu da ƙarfin gaske,
Jin ihu yasa duk mutanen gidan suka fiffito da gudu gaba ɗaya sun tsorita, haka aka taru da ma'aikatan gidan gaba ɗaya babu wanda bai fito ba, manya da ƙananu, ga haske dadau-dadau ta ko ina kamar hasken rana, duk da duhu bai gama shiga ba ƙarfe 6 amma har an kunna hasken Sola a duk gidan,
Yallaɓai haka yaketa birgima yana faɗin "wayyo ALLAH al'umma ta ku temake Ni ku sosa mun, wayyo ku sosa mun! ku sosa!! ku sosa mun!!!...."

a gigice ya miƙe tsaye ya cire rigarsa ya jefar gefe guda, sannan ya zamar da wandon jeans ɗinsa ya zauna daga shi sai gajeren wandonsa, haka yake tsalle yana jumping abu ba kyan gani gashi baƙi ƙirin dashi,
"Wayyo ku kawo mun ruwa, ku kawo mun ruwa jikina ƙaiƙayi..."

Haka mutanen wajen nan suke dariya kamar cikinsu zai ƙulle, dake zallar mata ne a wajen sai sautin dariya ne yake tashi, hatta ma'aikatan matan saida suka ɗan dara, a yayin da wasu suka je ɗauko bokitan ruwa suka kakkawo masa wajen bokitain biyar, haka suke kwara masa ruwa a jikinsa yana sosawa amma abun kamar ƙaruwa yake a gigice ya danna uwar ihu yana faɗin "wayyyyyooo ku daina zuba mun ruwa zan mutu, ɗuwawu naaaa zai fice ku ƙira mun likitoci, asibiti akaini..."
yana wani irin lanƙwasa kamar mai yin rawa yana tsalle ganin tsayuwar bazaiyu ba yasa ya ƙara kwanciya a ƙasi yana birgima da juye-juye da shanbe-shabe, hannunsa ɗaya yana sosa jikinsa ɗaya kuma yana riƙe da AK-47 ɗinsa gamm...

Ƴar Amana kuwa tana saman beni tana kallon duk halinda ake ciki, ta haɗe rai babu alamar Annuri a fuskarta, duk abubuwan da yakeyi ko kaɗan bata ji tausayinsa ba sannan ko dariya bai bata ba saima ƙara jin haushinsa da take yi,
Ga gashin kanta buzuzu duk ya rufe mata fuska sai wanda taɗan janye gefe yanda zatana kallon komai,
Ganin batada lokacinsa yasa ta koma cikin ɗakinsu...


Yallaɓai fa abu sai ƙaruwa yake, ɗan ƙaramin gajeren wandon mah haka yasa hannu ya janye gaba ɗaya ya zauna haka tsirara, ya miƙe tsaye yana jujjuyawa zigidir...

Nan Ma'aikatan wajen suka fara koran yaran gidan, amma yaran furr sunƙi koruwa haka suka fara ele suna ihu tareda faɗin "wayyo Yallaɓai tsirara Yallaɓai tsindir! Yallaɓai tsirara Yallaɓai tsindir!! Yallaɓai tsirara Yallaɓai tsindir!!!..."
suna tafa hannayensu suna masa waƙa,
Su kuwa manyan kowa rufe idonta tayi wasu suka jujjuya da gudu wasu kuma suka rufe fuskokinsu da hannayensu masu hankalin kenam, wasu ma'aikatan ne suka nufi bakin gate da gudu zasu je ƙiran security dake da nisa sosai zuwa bakin gate shiyasa duk abunda akeyi security basu sani ba...

Shi kuwa Yallaɓai haka yake tsalle yana girgiza tareda faɗin "ku sosa! ku sosa!! ku sosa mun ku sosa!!..."
Yaran kuwa suna faɗin "Yallaɓai tsirara Yallaɓai tsindir...."


Sai da security suka zo suka fara bulale yaran suna kora kowa cikin ɗakinsa, haka suka zurawa Yallaɓai doguwar jallabiya sannan aka sakashi a mota sai hospital, acikin motar ma haka yake wannan haukar gaba ɗaya baya cikin hayyacinsa....


Aunty Habiba ganin haka yasa ta wuce gurin Baiwar ALLAH, tana zuwa ta buɗe mata dake key ɗin a wajenta yake,
ta ce "Baiwar ALLAH fito yau kam babu kwanan wahala, kije ki kwanta acan ɗakinku..."
Baiwar ALLAH cike da mamaki ta ce "Aunty Habiba lafiya kuwa? meya faru, kodai Yallaɓai ya fitar dani .."
Aunty Habiba ta ce "Yallaɓai yayi tafiya kuma nasan zaiyi kwana biyu kafin ya dawo..."
cike da farin ciki Baiwar ALLAH ta ce "yau zanga Ƴar Amana ALLAH sarki rabin raina ALLAH yasa tana lafiya..."
Haka suka wuce suka bar wajen, Baiwar ALLAH da gudu ta haura saman beni kai tsaye ɗakinsu ta wuce tana zuwa ta tura ƙofar ta shige, Ƴar Amana tana zaune a saman gado ta naɗe sawayenta kamar mai cin tuwo kai a sunkuye gaba ɗaya gashin kanta ya rufe mata fuska...

Baiwar ALLAH tana shugowa ta haura saman gado yanda Ƴar Amana take tasa hannu ta jajjanye mata sumar gashin sannan ta ɗago da haɓarta tareda faɗin "Ƴar Amana ga Baiwar ALLAH ki ta zo gare ki..."
Ɗagowa Ƴar Amana tayi tana kallon Baiwar ALLAH nan danan hawaye ya soma gangaro mata a gigice ta rungumeta tana kuka, itama Baiwar ALLAH rungumarta tayi sosai tana kuka tana bubbugan bayan Ƴar Amana alamar rarrashi.....





🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥

𝘾𝙊𝙈𝙈𝙀𝙉𝙏 𝘼𝙉𝘿 𝙎𝙃𝘼𝙍𝙄𝙉𝙂...


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (4)



꧁꧂


Baiwar ALLAH tana riƙe da hannun Ƴar Amana tana kallonta cike da tausayawa tace "ƴar uwa ya na ganki kamar kina cikin matsala?..."
Aunty Habiba dake tsaye ta zuba musu ido tareda yin murmushi ta ce "Baiwar ALLAH kenam kin dai san halin kayanki ita Ƴar Amana ai ba'a gane farin cikinta da kuma baƙin cikinta kullum acikin haɗe fuska take, Ni tinda nake daku ban taɓa ganin Ƴar Amana tayi murmushi ba balle naga haƙwaranta....."
Ƴar Amana tana sunkuye da kanta ƙasi duk tana jin tattaunawar da suke yi akanta sai dai babu baki,
Baiwar ALLAH tana shafa sumar kanta ta ce "ALLAH sarki ƴar uwa, ki kwantar da hankalinki komai zai zo ƙarshe insha ALLAH...."
ta ƙarasa maganar tareda ɗago kanta tana kallon Aunty Habiba cike da mamaki ta ce "Aunty Habiba kince Yallaɓai yayi tafiya shin ina yaje? amma naga Yallaɓai baya tafiya yayi kwana biyu baizo nan ba..."

Aunty Habiba tayi murmushi sannan ta ce "baki san abunda ya faru da Yallaɓai bane shiyasa..."
Nan Aunty Habiba ta kwashe komai ta gaya mata halinda Yallaɓai ya tsinci kansa.


Please Login or Register in order to submit comment