Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baiwar ALLAH har saida tayi dariya itama ta ce "amma wacece tayi masa wannan aika-aika?..". Aunty Habiba ta ce "waye zai sani? Bayan anyi abu a ɓoye amma duk randa Yallaɓai ya gano ko wacece toh kuwa kashinta ya bushe, Allah dai ya rufa mata asiri, amma Ni naji daɗin hakan sosai saboda nima ba ƙaramin jin haushin Yallaɓai nake ba wallahi..."
Baiwar ALLAH sunkuyar da kai ƙasi tayi tana maganar zuci
"Babu wacce take da ƙwarin gwiwar zuwa tasa ƙarara acikin kayan Yallaɓai sai Ƴar Amana, domin ta daɗe tana ƙulle ƙullen yanda zata hukunta yallaɓai amma nake dakatar da ita, duk yanda akayi Ƴar Amana ce wayyo..."
tana cikin wannan tunanin taji Aunty Habiba tana faɗin "kunga dare yayi na barku lafiya, amma Baiwar ALLAH kada fa ki fita waje saboda za'a iya kulla miki makirci ace kece kika fito kika sawa Yallaɓai ƙarara..."
Baiwar ALLAH ɗaga mata kai kawai tayi ba tareda ta ce komai ba..

Bayan fitar Aunty Habiba dasauri Baiwar ALLAH ta juyo tana kallon Ƴar Amana tareda faɗin "kece koh? nasan ke ce amma ki kiyayi ranar da asirinki zai tonu domin babu ruwa nah...."
ta ƙarasa maganar tana ɗora kanta akan filo ta jawo mayafi ta rufe kanta gaba ɗaya,
Ƴar Amana ganin yanda Baiwar ALLAH take mata magana cikin ɓacin rai yasa ta fusata ta ɗauki filon gefenta ta fara doka mata, a ruɗe Baiwar ALLAH ta yaye mayafin data rufu ta taso tana faɗin "ke kinada hankali kuwa? me kuma nayi miki?.."
haka ƴar Amana take kwaɗa mata filo a duk yanda ta samu a jikinta, ganin bazata daina ba yasa itama baiwar ALLAH ta ɗauki filonta ta soma rausa mata itama haka kowa yake dukan kowa, ganin abun bazaiyu da filo ba yasa suka fara kaiwa juna duka da hannu bibbiyu, Ƴar Amana ce ta kafa bakinta a kan dantsen Baiwar ALLAH ta galla mata uban cizo, a firgice Baiwar ALLAH ta cafki sumar kan Ƴar Amana bata san lokacin datayi wulli da ita ba har saida ta faɗo daga saman gado, ƴar Amana kifa kanta tayi a ƙasi saboda tsananin buguwa da tayi akan hannunta mai ciwo, kuka take yi amma sai dai babu sautin kukan sakamakon sihirin da akayi mata tin tana jaririya, ko kuka zatayi sautin baya fitowa balle tayi ihu...
Itama Baiwar ALLAH dafe dantsenta tayi har fatan gurin ya ɗan ɗaga gurin yayi jawur har da hawayenta tsabar zogin da gurin yake yi mata...

Sun ɗau mintuna sosai a haka babu wacce ta kalli kowa har zuwa yanzu Ƴar Amana tana nan a ƙasi bata ɗago ba,
Ganin shuru yasa Baiwar ALLAH leƙa ƙasi yanda Ƴar Amana take, a hankali ta sauƙo da ƙafafunta sannan ta zauna a ƙasi tareda jawo Ƴar Amana saman cinyarta tana rarrashinta cikin kulawa, cikin sassanyar murya Baiwar ALLAH take faɗin "Duk ke kika jawo amma ko kaɗan banaso nayi faɗa dake, bansan wani irin zuciya Allah yayi miki ba, Ƴar Amana dan ALLAH ki zamo mace mai haƙuri da juriya, ki rage wannan fushin nakin sannan ki rinƙa kaiwa zuciyarki nesa, baki san yanda rayuwa zata kasance damu ba, ke gashi yanda ALLAH ya yoki babu bakin magana amma na tabbatar da cewa kina jin duk abunda ake faɗa, kinje kin saka ƙarara a kayan Yallaɓai dakinyi haƙuri ma komai zai wuce...."
kasa ƙarasa maganar tayi sai wasu zafafan hawaye yanda yake zubo mata, suna zaune a haka har bacci ɓarawo ya jidesu,
Ƴar Amana tana kwance kan cinyar Baiwar ALLAH, ita kuma Baiwar ALLAH ta ɗora kanta a bakin gado da haka suke shan baccin su...


Misalin ƙarfe 2 na dare Baiwar ALLAH ta farka daga baccin da ya ɗauketa daiden lokacin take tashi yin sallar dare, ganin babu ƴar Amana akan cinyarta yasa ta waiga bayanta ko tahau saman gado nan ma bata nan, tunani tayi ko ta shiga toilet ne, haka tayi ta zaman jiran fitowar ta amma shuru, hakan yasa ta miƙe tsaye taje bakin toilet ta fara knocking a hankali tana ambatar sunanta
"Ƴar Amana!
"Ƴar Amana!!
"Ƴar Amana!!! me kike yi ne har yanzu a toilet?..." ganin ko motsi babu a cikin toilet yasa ta buɗe ƙofar toilet nan ma wayam ba kowa....
Ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa da ƙarfin gaske a ruɗe ta ce "TOH ina taje a wannan daren?...". ta ƙarasa maganar tana zazzaro manya manyan idanuwanta, da hanzarinta ta nufi bakin ƙofar fita tana zuwa ta buɗe ta fice a gaggauce, nan ta shiga neman ƴar Amana amma bata ganta ba, har ƙasin beni ta sauƙo tana lelleƙa ko ina amma babu alamunta,
Baiwar ALLAH ba ƙaramin tsorita tayi ba na rashin ganin Ƴar Amana....
kai tsaye hanyar lambu ta nufa da gudu domin yawon Ƴar Amana baya wuce nan, tana yawan zuwa lambun cikin gidan wanda yake da rata sosai da filin harabar gidan, sai kayi tafiya sosai kafin ka iso lambu, wurine a tsabtace, ga bishiyoyin mango da kashu dasu Apple da sauran kayayyakin fruits, ga wasu flawowi agurin gwanin burgewa ba abunda zakaji a gurin sai kukan tsuntsaye, waɗannan kukan tsuntsayen ne suke jan hankalinta sosai
kuma ita ƴar Amana ba ta cika son zama acikin mutane ba, tafi son ta fake ita kaɗai kuma ta kasance mai son kaɗa jita ..

Baiwar ALLAH tana isa gurin lambun tsikar jikinta ya fara tashi wani irin tsoro ne yake ziyartar ta, dake akwai hasken Sola sosai a wajen bata wani damu sosai ba,
kunnuwanta ne suka fara jiyo mata sautin kiɗan jita mai daɗin sauraro acikin flawowin wajen, murmushi tasau jin wannan sautin jita tasan Ƴar Amana ce, a hankali tasau ajiyar zuciya sannan ta ce "Alhamdulillah tinda na same ki..."
tana cikin wannan maganar zuci taji a dafa kafaɗarta ta baya, da murmushi asaman fuskarta ta juya tana faɗin "Ƴar Amana meyasa kike son fitowa acikin daren nan kam.." bata iddasa maganar ba taga Ƴar Amana kai a sunkuye sumar gashin ta duk ya rufe mata fuska, hannu Baiwar ALLAH takai tana gyara mata sumar kan natan ai kuwa a slow ta ɗago da wasu rikitattun idanuwa mai ban tsoro da firgici, ƙwayar idanuwanta zallar fari ne babu ɗigon baƙi ko kaɗan, a tsorace Baiwar ALLAH tayi saurin kawar da hannunta daga kanta baki a buɗe ta gagara rufesu a firgice ta ce "Ƴar Amana ke ce?..." murya na kakkarwa take wannan tambayar,
Aljanar dake gabanta buɗe baki tayi tana wani irin dariya kamar na yara, a firgice Baiwar ALLAH ta juya da gudu zata bar wajen, ita kanta bata san ina take yi ba ashe ƙara tusuwa cikin lambun take, anan ta samu jikin bishiya ta jingina bayanta tana sauƙe numfashi sama sama still ana kan kaɗan jita, ga wani irin sauti mai ratsa zuciya amma bata san a yanda ake wannan kiɗan ba amma tabbas acikin wannan lambun sautin yake fita,
Baiwar ALLAH tana cikin wannan halin taji an shaƙo mata wuya ta bayan bishiya da ƙarfin gaske, ƙoƙarin ceton kanta take amma ta gagara ƙwace wa haka taketa mutsil-mutsil tana shanbe-shanbe domin ba ƙaramin shaƙa akayi mata ba, har numfashinta yana shirin ɗagewa, idanuwanta sun fiffito waje haka hawaye yake bin saman fuskar ta, ganin ta kusan sheƙawa kuma babu wata mafita yasa ta fara jero addu'o'i acikin ranta, kuma babban abunda ya jawo mata wannan shine ta shugo cikin lambu kai tsaye babu addu'a ta manta batayi ba tsabar ta rikice a neman Ƴar Amana, kuma ƙa'ida ne daga mangarib an dena shugowa cikin lambu saboda akwai tarin hatsarurruka aciki sai mai ƙarfin imani ne zai iya tsallake wa,
Ƴar Amana ce kawai take iya shugowa cikin lambun nan a kowani lokaci kuma ta fita lafiya ƙalau ba tareda wata matsala ba, ta rigada ta zamo nasu sun zaɓeta a matsayin tasu...

Baiwar ALLAH har idanuwanta sun fara lumshewa kawai taji an sakar mata wuya, lokaci guda ta faɗin ƙasi tana riƙe da wuyan, numfashi daƙer take iya fitar wa, ba ƙaramin jiki tasha ba, wannan sautin jitar ne yake dukan dodon kunnenta a hankali ta zaburo ta tashi zaune daƙer ganin bazata iya miƙewa tsaye ba yasa ta fara rarrafe a wajen tana jero addu'o'i, tana rarrafe tana nufan wajen da take jin sautin jita, tana cikin wannan halin har ta iso wajen, ganin Ƴar Amana tayi tana zaune a bakin bishiyan Banana tana ta kaɗa jitanta mai kyan gani da kuma sauti mai daɗi, Ƴar Amana ta iya kiɗan jita sosai,
Baiwar ALLAH tunani ta fara yi kar taje kuma ba Ƴar Amana bace, haka take ƙarewa Ƴar Amana da kallo a ɓoye cikin flowers,
Ƴar Amana kanta a sama tana kallon hasken farin wata, fuskarta ɗauke da murmushi wanda bata taɓa nuna murmushinta a kowa sai idan tana fake waje ɗaya nan ma kamar yanzu cikin dare da hasken farin wata, wannan yanayin yana sata nishaɗi sosai...

Baiwar ALLAH haɗiyar yawu tayi gumi duk ya wanke mata ilahirin jikinta a cikin ranta ta ce "Allah dai yasa Ƴar Amana ce...". ta ƙarasa maganar tana rarrafawa a hankali sai gata a gaban Ƴar Amana hannu tasa ta riƙo hannayenta wanda take kaɗa jita dasu, a hankali Ƴar Amana ta sauƙo da fuskarta daga kallon sama da take yi, ta kafa idonta akan Baiwar ALLAH tana wani irin tunani a ranta ganin a halin da Baiwar ALLAH take ba'a cikin kwanciyar hankali ba...
Baiwar ALLAH ta ce "Ƴar Amana meya kawo ki nan cikin dare, shin bakya tsoro ne? tashi mu tafi kinji..."
Ƴar Amana zamar da hannunta tayi zata cigaba da kaɗa jita Baiwar ALLAH tayi saurin riƙo hannun tana girgiza mata kai ga hawaye shaɓe-shaɓe a saman fuskarta, Ƴar Amana ganin yanda Baiwar ALLAH take kuka yasa ta miƙe tsaye zasu tafi amma ba'a son ranta ba,
kamar yanda mutane suke son sautin kiɗan jitar Ƴar Amana haka suma Aljanun shiyasa suke biye da ita saboda wannan sautin jitar ta,
da haka suka bar cikin lambun Baiwar ALLAH tana riƙe da hannun Ƴar Amana har suka isa harabar filin gidan, daga nan suka haura saman beni kai tsaye ɗakinsu suka nufa,

Bayan shigarsu ɗaki Ƴar Amana saman gado ta haura ta zaune ga jitarta a gefe guda, ita kuma Baiwar ALLAH toilet ta nufa taje ta watsa ruwa a jikinta sannan ta ɗauro Alwala, tana fitowa tareda faɗin "ki tashi kema kiyi alwala kizo muyi sallah, tinda Allah yasa ba bacci kike ba..."
Ba musu haka Ƴar Amana ta tashi itama ta shige toilet tayo alwala sannan ta fito itama ta sanya hijab ɗinta kamar yanda Baiwar ALLAH tayi, daidaita tsayuwarsu suka yi sannan suka fara sallah a nutsu...

Bayan sun idar Addu'o'i suka yi na neman tsarin Ubangiji sannan ko wacce addu'arta baya wuce Allah ya bayyanar mata da iyayenta lafiya, bayan sun gama ne Baiwar ALLAH ta juyo tana kallon Ƴar Amana cike da mamakinta na abunda ta gani yau a cikin lambu, ta ce "Ƴar Amana Ni meyasa kike yawan zuwa lambu ne cikin dare? Bayan kinsan akwai tarin Aljanu a cikinsa, idan kaɗa jitarki zakiyi why bazaki bari sai gari ya waye ba?..."

Ƴar Amana itama zuba mata fararen idanuwanta tayi kamar wacce zata yi magana,
Baiwar ALLAH ta kuma cewa "shin kinsan abunda ya faru dani a cikin lambun kuwa?..."
still idon Ƴar Amana akanta ko ƙibtawa bata yi sai daga bisani ta motsa tareda zuwa gaban mirror ta jawo drower jikin mirror ta ɗauko wani littafi da biro sannan tazo ta zauna a bakin gado ta soma rubutu...

Cike da mamaki Baiwar ALLAH take binta da kallo tana mamakin tayaya Ƴar Amana ta iya rubutu balle karatu? ita da ta nuna bata jin komai sannan bata taɓa shiga aji ba, tana cikin wannan tunanin taji an jefo mata littafi da biro tayi firgit ta dawo hayyacinta, bin littafin tayi da kallo daga baya ta ɗauka tana karantawa kamar haka

( Kada ki sake bina gidan lambu cikin dare...)

zaro ido Baiwar ALLAH tayi cikin nuna farin ciki ta ce "Ƴar Amana daman kin iya rubutu? indai haka ne ai sai mu rinƙa yin chatting ta rubutu...".
ɗagowa Baiwar ALLAH tayi taga har Ƴar Amana ta kwanta tareda rufe kanta acikin mayafi, girgiza kai kawai tayi sannan ta fuskanci gabar ta cigaba da addu'o'inta, ƙa'idanta shine idan tayi sallar dare bata komawa bacci har sai an ƙira sallar asuba...


Bayan wata guda da misalin ƙarfe 10 na safe bayan an kammala breakfast kowa ya wuce ɗakinsa saiga wata mota ƙarama ƙirar jeep an buɗe mata gate ta tafo da gudun gaske, baiyi parking a ko ina ba sai a harabar gidan, ya fito yana sanye da 3quarter a jikinsa irin na ƴan kwallo da rigarsa mai hannun singlet, tsayawa yayi yana bin gidan da kallo lokaci guda yasa wusir a bakinsa ya hura da ƙarfin gaske yanda kowa na gidan zaiji daga gidan ƙasa har zuwa gida na sama, kafin kace mai saiga mutanen gidan sun fara fiffitowa da gudu, ganin yallaɓai ne ya dawo yasa duk suka shiga taitayinsu, haka kowa ya zo filin gidan suka tsatstsaya duk suka saka shi a tsakiya,
Bin kowa yake da kallo fuska ba Annuri, can baya ya hango Ƴar Amana kai a sunkuye yana taku cikin salo yaje gabanta yasa hannu ya ɗago haɓarta suka haɗa ido huɗu, fuska ba walwala ya ce "ina ƴar uwarki take?..."

Ƴar Amana shuru tayi bata bashi amsa ba ya darara mata tsawa yana kuma tambayarta amma Ƴar Amana ko girgiza batayi ba balle ta nuna cewa taji tsoron tsawar da ya yi mata...

Wata daga cikin ma'aikatan ce ta ce "Yallaɓai ka manta ne ita ɗin Kurmiya ce bata jin abunda kake faɗa..."
sai a yanzu ya tuno ashe Kurmiya ce, cikin mugunta ya damƙi sumar kanta sannan yazo da ita tsakiyar filin yana faɗin "ina zargin ɗaya ce daga cikinku wata ta sanya mun ƙarara acikin kayana, ko ke ko Baiwar ALLAH....."

A gigice ya daka uwar tsawa yana faɗin "Ina Baiwar ALLAH ta fito nan..."
still yana riƙe da sumar gashin Ƴar Amana wacce ita kuma tana ta kai kawo tana kokarin zamar da gashinta domin ba ƙaramin riƙo yayi mata ba,
Aunty Habiba tana tsaye ta ce "Yallaɓai ai tin kafin ka tafi kasa a rufe ta a ɗakin duhu..."
kafin ta ƙarasa maganar ya daka mata tsawa itama tareda cewa "ƙarya kuke munafukai, nasan kun daɗe da fito da ita shin tana inaaaa?..."
Baiwar ALLAH tana laɓe tana ganinsu ganin yanda yake riƙe da sumar gashin Ƴar Amana yasa ta fito domin bazata iya juran ganin hakan ba, fitowa tayi ta nufo gurin da suke, matan wajen ne suka fara buɗa mata hanya ta wuce har tsakiyar mutanen ta tsaya tana kallon floor,

Yallaɓai ganin Baiwar ALLAH yasa ya saki kan Ƴar Amana yazo har gabanta suna facing juna, wani irin kallo yake mata daga bisani ya ce "ke ce kika saka mun ƙarara acikin kayana?..."

Baiwar ALLAH tace "lokacin da akayi haka ina can ɗakin duhu .."

Yallaɓai ya kuma cewa "kenam wancan yarinyar ce?..."
ya ƙarasa maganar yana nuna yanda Ƴar Amana take..

Nan ma Baiwar ALLAH ta ce "ba ita bace.." tayi maganar ba tareda ta ɗago ba

Yace "taya kika san ba ita bace?.."

Tace "saboda nasan bazata aikata ba ."

tintsirewa da dariya yayi sannan ya ce "na tabbata duk marayun matan dake cikin gidan nan babu wacce zata iya mun wannan abun sai ku biyu ke da Ƴar Amana..."

ɗagowa Baiwar ALLAH tayi tana kallonsa tace "saboda sun baka haɗin kai shiyasa? mu kuma saboda munyi Allah wadai da halinka shine ka ɗora mana tsanarka akan mu ?..."

tana ƙarasa maganar ya zabgeta da mari yana huci yace "ke Ni zaki tsaya a gaba kina gaya mun maganganu? saboda kin raina Ni?..."

wata ce daga cikin yaran gidan ta ce "Yallaɓai ai tinda muka ganka tsirara zancen raini ya ƙare..."
duk suka kwashe da dariya, haushi kamar zai kashe Yallaɓai cikin tashin hankali ya darara musu tsawa tareda faɗin "duk ku sunkuya kuyita tsallen kwaɗo har yamma..."
haka kuwa suka hau yin tsallen kwaɗo banda Baiwar ALLAH da Ƴar Amana da suke tsaye sai sauran ma'aikatan,
Yallaɓai yana zazzaro ido waje yana fuskantar Baiwar ALLAH yace "ke kika saka mun ƙarara ko ƴar Amana?..."

Shuru Baiwar ALLAH tayi bata bashi amsa ba, yana jinjina kai ya ce "okay don't worry Ƴar Amana yau saita gane kuranta..."

ya juya zai nufi yanda Ƴar Amana take a tsaye ta ƙura masa ido Baiwar ALLAH tayi saurin cewa "Ni ce na saka maka ƙarara acikin kayanka, babu laifin Ƴar Amana..."


Please Login or Register in order to submit comment