Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba ɗaya kayan abincin suka watse, ga miyar Ogusi yasha tsala-tsalan naman kaji aciki duk miyar ya kife gaba ɗaya....

Baiwar Allah bata san lokacin da ta fara furta "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un,
Allahumma ajurni fi musibatin wa akhlifli khairan Minha,
Ƙalu innalillahi wa inna'ilaihi raju'un....."

Saida ya bari ta gama addu'o'inta sannan ya ɗago yana kallonta fuska a hargutse,
Ita kuma hannayenta biyu ta haɗe guri ɗaya ta ɗago dasu alamar roƙo, bakinta ne yake kakkarwa zatayi magana amma ta kasa furta komai sai kukan da take yi ....

Ya ce "ki haɗiye mun kukan Nan,
kin ci sa'a yau murnar ƙarin shekara ta kuma shekarar rasuwar mahaifiyata, bazan yi murna ba kuma bazanyi jimami ba, zan sassauta miki hukunci, abunda zakiyi shine kisa bakin ki duk ki shanye miyan da kika zubar akan carpet, sannan kizo ki mun mopping....."

Kamar yanda ya ce a hanzarce ta kifar da kanta ƙasin carpet ta soma Shan miyan Nan kamar wata Akuya,
tass saida ta shanye miyan Nan dake Allah ya temaketa iya miyar ce kawai ta zube sauran abubuwan duk akulle suke da marafansu, bayan ta kammala tashi tayi ta tattare kulolin ta fice dasu,
Daga baya ta sake dawo da abun goge-goge da bucket mai ɗauke da ruwa a ciki tazo ta fara mopping duk da goggoge wuraren da ya ɓaci,
Sannan ta sake fita da kayan aikin,
Ba jumawa ta sake shugowa da wasu kulolin abinci daban kuma du a hankali take tafe ta ƙarasa gurin dinning ta jejjera masa kayan abincin....

Shi kuwa yanata uzurin gabansa ko kallon yanda take beyi ba,
Bayan ta kammala daƙer ta daidaita tsayuwarta sannan ta ce "na kammala...."

Tasowa yayi yana Jan ƙafa kamar mai tambayar ƙasi ya ƙarasa dinning ya zauna akan chair, itama zuwa tayi ta zuba masa a plate taje ta buɗe frig ɗinsa ta ɗauko cold water da su juice da milk ta kawo masa,
kafin ya fara cikin abincin saida ya sata tazo tayi one spoon saboda gudun kar yayi irin na jiya,
ta juya zata tafi ya dakatar da ita tareda faɗin "ina Zaki je?....."

juyowa tayi tana kallonsa ta ce "zanje a duba mun ƙafata ...."

Ya ce "ai baki gama karɓan hukuncinki ba, kiyi mun kneel down a tsakiyar falon Nan...."

cike da takaici take kallonsa har taji ta tsane shi saboda muguntarsa, ba yanda ta iya haka ta durƙusa daƙer tayi kneeling...

tsiyayar juice yayi a glass cup sannan ya kurɓa ya ajiye yana shirin Kai abinci bakinsa ya ce "rest your hand up...."

Nan ma tayi yanda ya ce tana wurga masa harara ta gefen Ido ba tareda ya sani ba.....


Suna cikin wannan halin suka ji sallama,
Roshan ne ya shugo domin duba Ɗan uwansa ya tarar da Baiwar Allah durƙushe a ƙasi ta ɗaga hannaye sama ga hawaye yanda yayi sharkab akan fuskarta, jikinta ne yayi kakkarwa tsabar gajiyar da tayi ga ƙafarta yanda ta gurɗe yayi tsami sosai sai azabar ciwonda yake mata...

Roshan idonsa akanta Wani abu ne kamar kibiya yaji ya soki saitin zuciyarsa, dasauri ya lumshe eyes ɗinsa tareda cije lips ɗinsa na ƙasi....

Uncle Deen yana kan dinning idonsa akan Roshan ya ce "are you okay...."

Girgiza Kai Roshan yayi ya nufi yanda Baiwar Allah take yasa hannu ya ɗagota, kasa tsayuwa tayi sai luuu ta faɗa Saman ƙirjinsa tayi ƙasi zata faɗi ya yi saurin riƙota ya riƙeta sosai, yana jin yanda ta fashe da kuka ji yayi kamar shima ya yi kukan,

Uncle Deen cike da mamaki yake binsu da kallo ya ce "Twins what happens?..."

Roshan cije lips ɗinsa na ƙasi ya kuma yi sannan ya ce "My heart so painning me...."

"Why...."
A cewar Uncle Deen..

"Because of this girl....". Roshan ya ƙarisa faɗa yana bin Baiwar Allah da kallo wacce ta narke masa a jiki..

Uncle Deen yamutsa fuska yayi sannan ya ce "I don't understand, what do you mean?...."

Roshan ɗagowa yayi yana kallon Razhdeen kamar Wani ɗan maraya ya ce "she's my life ....."

Cikin rashin fahimta Uncle Deen ya ce "Who?....."

Roshan ya ce
"This girl......"

A zabure Uncle Deen ya miƙe tsaye daga zaune tareda faɗin "Whattttttt!!!!
Are you a mad?....."


Cikin ɓacin rai Roshan ya ce "am not a mad, nasan abunda nake yi, this girl she's my destiny and my life, so please I begging you don't try to hurt her again, because am going to marry her soon....."

Uncle Deen cike da mamaki yake bin Roshan da kallo tinda suka taso Bai taɓa tsayawa a gabansa yana gaya masa maganganu ba sai yau, abun ya kulle masa Kai ....."

Roshan ɗaukar Baiwar Allah yayi saman kafaɗarsa yana shirin fita da ita,
Uncle Deen ya dakatar da shi tareda faɗin "kada ka kuskura ka fita da yarinyar Nan, umarni ba shawara ba....."

Roshan cike da mamaki shima ya juyo yana faɗin "Umarni? wai Umarni kake bani? ....."

Uncle Deen ya ƙaraso gabansa da cewa "Yes! bazaka fita da yarinyar Nan ba saboda inada right ɗin da zanyi Iko da ita sannan na hukuntata da zaran tamun laifi...."

Roshan girgiza Kai kawai yayi ya juya zai fita cikin ɓacin rai Uncle Deen yasa hannu ya finciko Baiwar Allah daga Saman kafaɗarsa ya cillata kan kujerarsa 3 seater,
A kiɗime Baiwar Allah tasau ƙara lokacin guda ta sume a wajen saboda irin tashin hankalin da ta tsinci kanta a ciki...

Roshan ganin yanda yayi wurgi da Baiwar Allah yasa ya zuciyo Bai san lokacin da yakai wa Uncle Deen naushi a saitin lips ɗinsa ba.....

Razhdeen hannu yasa ya kama bakinsa idonsa akan Roshan cike da mamaki yake binsa da kallo, tin suna yara basu taɓa samun matsala har takai da duka ba, kuma Bai taɓa ganin Roshan yayi faɗa da kowa ba sai yau akan mace, abun ya sosa wa Uncle Deen rai yayi niyar yakai wa Roshan naushin da saita sume a waran amma lokaci guda zuciyarsa ta sauƙo saboda sonda yake yiwa ɗan uwan nashin bazai iya cutar dashi ba,
Amma sai dai yayi niyar masa hukunci ɗaya shine bazai bashi Baiwar Allah ba tinda har ya gano itace rauninsa kuma har zai iya ɗaukar hannu ya naushe shi saboda ita,

Kafin Roshan ya motsa ya nufi yanda Baiwar Allah take tinin Uncle Deen har yaje ya ɗauketa da hannu ɗaya ya wuce da ita bedroom ɗinsa sannan yasa key ta ciki ya kulle...

Dasauri Roshan ya nufi bedroom ɗin tura ƙofar yayi yaga har ansa key, kamar zaiyi hauka haka ya ringa buga ƙofar da ƙarfin gaske........


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 39 to 40



꧁꧂



Tsararren masarauta mai cike da ƙayatattun kayan alatu wanda fadawa ne da kuyange suke ta faman zarya a cikin masarautar,
Sarkin ƙasar Jidder wato mai martaba Abubakar Al-Saddiq yana zaune a katafaren kujerarsa na alhurma da wasu manyan mutane dattawa su biyar suma suna Zazzaune akan kujerun fadar, da duk kan alamu suna tattaunawa ne akan wani abu mai muhimmanci,
wata matashiyar yarinya ce ta shugo da sallama a bakinta tana riƙe da tray a hannunta wanda aka jejjera kayan fruits aciki dasu lemuka sai wasu ƙananun glass cups waɗanda za'a tsiyayi juice a ciki, ajiye tray ɗin tayi akan table wanda yake tsakiyar falon fadar, saida ta gaggaishe su kafin ko wanne ta kai masa abun maƙulashe saitin gabansa, tana kammalawa ta miƙe zata koma ciki taji wani daga cikinsu ya ce "sannunki da ƙoƙari...."

juyowa tayi ta kalle shi sannan ta ce "Nagode Baba...."

haɗe rai mutumin yayi jin ta ƙirashi da Baba kuma har cikin zuciyarsa yarinyar ta burge shi, kafin ya ɗago kai ya kalleta har ta fice...
Mai Martaba ne ya kalle shi sannan ya ce "lafiya kuwa Alhaji Ahmed? naga lokaci guda ka sauya...."

Murmushi Alhaji Ahmed yayi sannan ya ce "Mai martaba shin wannan yarinyar ɗiyarka ce? Amma kuma naga kai tin ɗiyar daka haifa aka rasata baka sake haihuwa ba, shine abun yake bani mamaki kuma gata yarinyar batayi kama da Baiwa ba...."

Dogon numfashi Mai martaba yaja tare da jinjina kansa ya ce "hakkun Alhaji Ahmed abinda ka faɗa gaskiya ne, ita wannan yarinyar Ƙanwar matata ce ta farko wato Hajia Mamy, tin yarinyar tana ƴar shekara biyar ta ɗaukota take riƙe da ita har zuwa girmanta, kun dai san Mamy bata taɓa haihuwa ba, ita kuma matata ta biyu A'isha itace ta haifa mun ɗiya mace wato Reemah wacce har ilah yau bamu sake jin labarin ta ba tin tana jaririya yau kimanin shekaru sha biyar ana shirin shiga ta sha shida....."

wani daga cikinsu ne yayi magana wato Alhaji Hamza idonsa akan Mai martaba ya ce "Allah sarki shin tana raye ne ko ta mutu Allahu a'alamu, idan har tana raye Allah ka bayyanar mana da Reemah, idan kuma ta mutu Allah yasa mai ceto ce a ranar alƙiyama....."

Duk suka amsa da Ameen...

Alhaji Ahmed bayan yayi jimm kaɗan ɗagowa yayi tareda faɗin "Ni kuwa Mai martaba idan za'a bani dama inaso na fara neman yarinyar nan wallahi, ta burgeni sosai....."

Duk sauran mutane huɗu da suka rage ne suka haɗe masa baki da cewar "yanzu kai Alhaji Ahmed ina zaka kai wannan yarinyar da shekarunka, matanka biyu, yara takwas ɗaya tana gidan mijinta harda jikanka....."

Alhaji Ahmed cike da mamaki yake binsu da kallo ya ce "yanzu fisabilillah saboda Allah ya bani waɗannan sai akace karna ƙara Aure? namiji fah an bashi damar Auran mata huɗu...."

Suka ce "ehh amma saika nemi dai-dai dakai ba yarinya ba, domin mun tabbata bazata yadda taje kan ta uku ba...."

Cikin fusata Alhaji Ahmed ya ce "toh Ni yarinya nake son Aura...."

Suka ce "toh Allah ya temaka ya bada Sa'a ...."

Ya ce "Ameen..." Tareda fuskantar Mai martaba wanda ya tsaya yana sauraron su,
Ya kuma cewa "mai martaba inason jin daga bakinka akan manufata, Ni nayi alƙawari indai za'a bani yarinyar toh zan tsara mata gidanta da ban ta wataya ita kaɗai babu wani takura....."

Mai martaba ya ce "duk naji batunka Alhaji Ahmed, yanzu dai babu abinda zan iya cewa akan al'amarin nan domin bani zan zauna dakai ba, ita yarinyar da zata zauna dakai kaje ka fara tuntuɓar ta idan ta amince Ni bani da wata matsala....."

Alhaji Ahmed jikinsa ne yayi sanyi domin yana ji ajikinsa za'a samu matsala daga wajen yarinyar tinda har ta ƙira shi da Baba!
Murya a sanyaye ya ce "amma mai martaba nake ga idan har kai kayi mata magana zata fi ɗaukar mahimmanci maganar har ta amince mun, naga yarinyar tanada tarbiyya tana jin maganarka sosai....."

Jinjina kai mai martaba yayi yana maganar zuci cewar "Uhmmm! Rashin sani yafi dare duhu, amma inda kasan halin Matata Mamy da kuma Ƙanwarta Ramlat da bakayi gaggawar furta cewar yarinyar tanada tarbiyya ba...."

Jin Alhaji Ahmed ya katse shi da cewa "yadai mai martaba?...." yasa yayi firgit tareda faɗin "shikenam zan samu Ƴar uwarta Babbar Matata muyi magana da ita, idan har ita ta amince toh komai zai dai-daita kai dai kayi addu'a...."

Alhaji Ahmed yayi masa godiya cikin girmamawa daga baya sukayi sallama da mai martaba duk suka tafi, ko wannen su da zugegiyar motarsa yake tafe babu talaka a cikinsu, asalin manya-manyan masu kuɗi ne,
shima mai martaba barin cikin falon yayi ya shige cikin gidan......


Shiga cikin wani katafaren ƙaton falo yayi wanda ya tsaru sosai da kujeru,
Part biyu ne acikin falon wanda saika hau saman beni kafin ka shige room ɗin matan gidan,
kai tsaye part ɗin da yake ɓangaren dama mai martaba ya nufa, saida ya haura upstairs sannan ya shige room ɗin Hajia Mamy ya tarar da ita tana zaune a bakin gadonta sai faman danne-danne take a waya, tasha makeup sosai tana sanye da less a jikinta,
Kana ganinta kasan tana shan hutu sosai tayi wani irin ƙiba, ta ko ina a cike yake babu rama, Baƙa ce amma tana da kyan ta,
Sallama yayi mata kafin ya samu guri ya zauna dab da ita idonsa akanta, cikin fara'a ya ce "Uwar gida bakya laifi...."

Juyowa tayi ta kalle shi tana yamutsa fuska ta ce "bana laifi kuma? Sai dai kaje ka yabe Amaryarka acan ɓangaren ta ...."

Murmushi Mai martaba yayi sannan ya ce "ke matsala dake kenam ba halin kiyi wasa da mijinki..."

Mamy tana ɗaga kafaɗu ta ce "taya zanyi wasa dakai wannan ai sai Amarya, Ni kuma kaga ba Amarya ba ce....."

Dogon numfashi yaja tareda cewa "shikenam,
yanzu dai ba wannan ba akwai maganar da nake so nayi dake akan Ramlat,
Daman wani Aboki nane ya ganta ya ce yana so shine........"

kafin ya ƙarasa maganar tayi saurin katse shi da cewa "meeeee?
wa kenam?....."

Ya ce "ha'a meye abun firgita kuma? Alhaji Ahmed ne ...,"

Miƙewa tayi tsaye tareda kama kunkumi ta ce "impossible wallahi, wannan dattijon zata Aura? hakan ma itace ta uku? wallahi mai martaba baka son mu da alkhairi haba dallah......"

Kallonta yayi ya ce "toh yanzun ya kike so ayi?...."

Saida ta wani juyar da idanuwanta tana gatsine ta ce "idan har kana son mu da alkhairi kuma kana sona da gaske inhar kanason haɗa jinsi dani toh ya zama dole ka Aurar mun da Ramlat a Razhdeen,
Domin mun gama maganan nan cewa zaka ƙira Yayanka a waya ka sanar masa cewar ka bayar da Ramlat wa Ɗansa Razhdeen, idan kuma baka ɗauki Ramlat a matsayin ƴa ba shikenam....."

Mai martaba gaba ɗaya ya rasa yanda zai yi akan wannan batun shi kuma fargaban ƙiran Yayansa yake akan maganar bayan haka yasan halin Razhdeen ba Amincewa zaiyi ba,

Hura iskar bakinsa yayi sannan ya ce "Amma Mamy kin dai san halin Razhdeen, ba irin mutanen nan ne masu sauƙin kai ba! ba lallai ya yadda ba
ina laifin kice Roshan amma Razhdeeeeen kaiiiiii ......"

tinin harya haɗa gumi domin lamarin Razhdeen sai Allah amma Mamy ta kasa ganewa ita burinta ta haɗa Ramlat da Razhdeen,

yana cikin nazari yaji ta fashe masa da kuka tana faɗin "saboda ban taɓa haihuwa ba shine komai na roƙa ba'a yarje mun, yanzu fisabilillah so nake na haɗa jinsi da ahalinku sakamakon bana haihuwa amma furr kaƙi yadda ......"

Mai martaba ya ce "kina ji ba, bawai nine ban yadda ba sannan ba Yayana bane bai yadda ba shi kanshi Razhdeen ɗin ne bazai yadda ba....."

A tsawace ta ce "toh baza ku saka shi dole ba? ku ba iyayensa bane? dole idan kuka tsayar masa zai amince....."

Ya ce "Uhmmm! Mammy kenam Razhdeen ba yanda kike tunani bane shi, meyasa bazaki zaɓi Roshan ba sai Razhdeen wanda yafi ƙarfin ai masa dole,
Ai yanzu Mace ma ba'a mata dole balle namiji....."

Gaba ɗaya Mamy ta kasa fahimtar shi sai faman zuba masifa take, ganin bazai iya jurewa ba yasa ya tashi zai fice a room ɗin......

Duk tattaunawar da sukayi Ramlat tana tsaye a bakin ƙofa tana jinsu, jin mai martaba yana shirin fitowa yasa tayi saurin tura ƙofa zata shiga da sallama a bakinta dai-dai lokacin da zai fito shi kuma,
Cikin ɓacin rai ya wuce yayi tafiyarsa,

Ramlat ce ta ƙarisa gurin Mamy tana faɗin "wai ke Mammy meye damuwarki da dole saina Auri Uncle Deen? Na gaya miki Ni Yaya Roshan nake so, inasonsa sosai har cikin zuciyata....."

Mammy ta ce "ke Dallah rufe mun baki, ai ke mahaukaciya ce shiyasa baki san rayuwa ba,
Meye Roshan yake dashi?....."

Ramlat ta ce "a'ahhhh ai kuwa Mamy bazaki ce Roshan ba kyakkyawa bane....."

Mammy ta ce "Shashasha rufe mun baki, wani kyau kuma? Ai kuɗaɗe sune kyau, duk wanda yafi kuɗi toh shine kyakkyawa,


Please Login or Register in order to submit comment