Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Baiwar Allah ganin Hajia bata kulata ba yasa ta kalli Roshan taga ita yake kallo shima ta gaishe shi, cikin murmushi ya amsa mata,
Abbah ya kalli yaran gidan fuska a haɗe ya ce "ku ɗin bazaku gaisheta ba ne?....."

duk suka ɗago suna kallon Abbah cike da mamaki,
Banda Ummy cikin sakin fuska ta ce "gud morning Aunty Daughter...."
ta ƙarasa tana dariya itama Baiwar ALLAH murmusawa tayi,
Roshan ne ya ce "wato kema kin bi bakin Abbah Koh?...."
yayi maganar idonsa akan Ummy..

Pinky ce take kallon Abbah cikin takaici ta ce "Abbah mu fa mun girmeta, ita ya dace ta gaishe mu...."

Itama Rukky ta ce "gaskiya yanzu fa we are almost 23 years ita kuma nasan bazata wuce 20 or 21 ba....."

Minal dai ko ɗagowa batayi ba tanata pressing phone ɗinta,

Abbah ya kalli Minal ya ce "kepah Amina kema bijire mun zaki yi ne?...."

Cike da mamaki Minal ta ɗago tana kallon Abbah ta ce "au wai har da Ni?...."

Abbah ya ce "kina shakku ne?...."
ta juya tana kallon Baiwar ALLAH tareda faɗin "gaskiya ba'a mun adalci ba indai akasa na gaishe da wannan yarinyar....."

Abbah ya ce "adalcin kenam tinda yanzu itace sama daku...."

Hajia Kilishi a fusace ta ce "how comes zata zamo sama dasu? kawai dai kanason zamar mun da yara Agolai waɗanda basu da ƴanci...."

Abbah ya ce "Zata zamo matar Yayansu Kinga kuwa dole su darajata su mutuntata...."

Kallon juna Ƴanmatan gidan suka shiga yi abu yazo muku kamar almara,
Hajia Kilishi cikin rashin fahimta tana jifar Baiwar ALLAH da wani irin mummunan kallo ta ce "ban fahimta ba...."

Baiwar Allah kanta a sunkuye ita kanta bata san ina Abbah ya dosa ba,
Abbah ya ce "ƙwarai da gaske na yanke shawarar Aurawa Roshan Daughter,
Roshan ya sanar mun cewar yana sonta zai Aure ta bayan na bashi labarin ta, haƙiƙannin gaskiya naji daɗin haka sosai domin inaso na sauƙe nauyin dake kaina tabar hannuna ta koma hannun mijinta Roshan,
Amma hakan bashi zaisa na daina lura da al'amuranta ba dole zansa ido akan yanayin zamantakewar ta da mijinta da kuma ku masu nuna ƙiyayyarku akanta tinda ba wani guri za'a Kaita ba, a cikin gidan zasu zauna amma part ɗinta daban,
Ni nayi Na'am da Auren nan....."

a firgice Rukky ta kalli Pinky haɗi da cewa "daman na gaya miki......"
Pinky kamar zata haɗiyi ranta ta ce "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un, amma za'a yi babban buro uba a gidan nan....."
sunyi maganarsu acikin raɗa ba tare da anji su ba

Minal cike da mamaki take bin Baiwar ALLAH da kallo fuska a murtuƙe ta ce "taya zamu zauna da wacce bamu san asalinta ba?...."

Abbah ya ce "ta yanda kuke zaune da ita yanzu...."

Roshan ganin yanda suke ta hararar Baiwar ALLAH yasa yaɗan motsa yana kallonsu ɗaya bayan ɗaya ya ce "kunga ku dakata haka! na farko baku zaku Aura mun ita ba sannan baku zaku zauna mun da ita ba yakamata ku fuskanci yanda rayuwa take, kuma ku samo mazajen Aure kuyi Auren ku....."

kafin ya ƙarasa Hajia Kilishi ta ɗaga masa hannu tare da miƙewa tsaye tana fuskantar sa ta ce "ka dakata haka Roshan, wannan cin mutunci da cin fuska ya isheni haka! kenam kana musu gorin Aure ne ko meye?
Wawan yaro wanda baka san inda yake maka ciwo ba,
In banda ƙaddara meya haɗaka da wannan yarinyar da ba'a san asalin ta ba, wata ƙil ƴar cikin shege ce aka jefar da ita ta tashi a gidan marayu,
kaine wanda za'a ce ka fuskanci rayuwa yanda take kaje ka nemo ƴar asali bawai ƴar tsintuwa ba......"

Abbah ne shima ya miƙe tare da zabga mata mari a gefen fuskarta,
saida ta faɗa kan kujera tana riƙe da fuskarta,
Duk acikin yaran babu wanda bai zabura ba, ko wacce zuciyarta na bugun 3³,
Baiwar Allah ta kasa ɗago da kanta domin yanayin da take ciki yana shirin fin ƙarfin tunaninta, kuka take ba ƙaƙƙautawa, bata san meyasa wannan al'amarin yake shirin afkuwa ba,

Abbah cikin zafin rai ya ce "idan kika sake faɗin mummunan kalma akan yarinyar nan wallahi zanyi miki abunda bakiyi zato ba...."

Hajia Kilishi ganin bazata iya juran kalar wannan wulaƙanci ba a gaban iyalanta yasa ta tashi a fusace cikin zafin rai take nunawa Abbah yatsa tare da faɗin
"Na faɗa ita ɗin ƴar cikin shege ce marar asali kayi duk abinda zakayi, tinda har wulaƙancinka yakai ka rinƙa dukana a gaban ƴaƴana to meya rage yanzu,
kuma wallahi tallahi bazan taɓa bari ayi Auren nan ba saidai In wata amma banda wannan ƴar jagaliya,
Kuma koda mahaifiyarsa tana raye bazata taɓa barin ya Auri wannan marar asali ba,
saboda bani na haifeshi ba shine zaka nuna mun ban isa dashi ba,
toh sai ayi Auren mu gani ai....."

Murmushin takaici Abbah yayi ya ce "ki cigaba da nuna mun yatsa wata rana zan ɓalla ƴar yatsar ne,
Kuma da kike cewa baza'ayi Auren ba basai kina gidan daki dakatar ba......"

Hajia Kilishi cike da mamaki ta ce "oh kana nufin korata zakayi?...."

Abbah ya ce "ehh! kije ki na sakeki saki biyu...."

A zabure Roshan ya miƙe tsaye yana faɗin "Abbah meye kake shirin aikatawa?...."

Abbah juyowa yayi yana kallon Roshan ya ce "bawai nake shirin aikatawa ba, na ma aikata an gama ka nemi guri ka zauna...."

Roshan ba yanda ya iya haka ya nemi guri ya zauna domin baya ƙaunar kaucewa maganar Abbah,

Minal da Pinky da Rukky da kuma Ummy duk miƙewa sukayi tsaye domin hukuncin da Abbah ya yanke akan Mommy yayi tsauri,
Minal tana kuka ta ce "Abbah yanzu ɓacin ranka har zaisa ka sallami Mahaifiyar mu muna raye?....."

Pinky da Rukky babu bakin magana sai kuka,
Ummy ce taje gaban Mommy ta tsaya tana kuka ta ce "Mommy kinsan fa ke babbar mai laifi ce agurin Abbah har ma agurin Ubangijinki meyasa bazaki kiyaye ba,
Meyasa bazaki bi umarnin mijinki har ki nemi yafiyarsa akan laifin da kika aikata masa ba?....."

Bata ƙarasa maganar ba taji Mommy ta hankaɗata baya har saida ta faɗi ƙasin carpet tana faɗin "Maryam ki kiyayeni tin kafin na illata ki,
ke wata iriyar jakar yarinya ce marar kishin mahaifiyarta, a gaban ki Mahaifinki ya mare Ni amma baki ji zafin hakan ba, a gaban ki Mahaifinki ya sake Ni bakiji zafin haka ba, anya kuwa ke jinina ne?......"
kafin ta ankara Abbah ya ƙara zabga mata mari ata ɗayan gefen fuskarta again yana huci ya ce "daki taɓa uwar masu gida gwara kin rama marin da nayi miki, domin idan ina ganinta tamkar ina kallon mahaifiyata ce, duk duniyan nan babu mai ƙiran sunan Ummy kai tsaye da asalin sunanta sai ke saboda bakya respect ɗin mahaifiyata......"

Minal da gudu tayo kan Mommy ta riƙeta tana kuka,
Hajia Kilishi cike da raɗaɗin baƙin ciki ta ɗago itama takai hannu ta zabgawa Abbah mari,
Ummy tsabar firgita bata san lokacin data ɗago daga kwance ba sai faman zazzaro ido take waje,
suma sauran yaran ido kawai suka firfito waje cike da mamaki,
A ruɗe Roshan ya miƙe tare da nufan yanda Hajia Kilishi take cikin zafin nama ya ɗauki hannu zai mareta yaji an riƙe masa hannu ta baya,
A firgice ya juyo yaga waye ya dakatar da shi idonsa ne suka sauƙa akan Baiwar Allah tana kuka ta ce "dan Allah ku dakata haka, bazan iya juran ganin wannan mummunan ta'agazan ba ...."

Hajia Kilishi tana bin Roshan da wani irin wawan kallo ta ce "ai na rantse da Allah inka sake hannunka ya taɓa jikina da sunan mari saina yi maka abinda bakayi zato ba, dana nuna maka cewa Ni Hajia Kilishi nafi ƙarfin wulaƙanci......"

Abbah jiki na zaƙami yana riƙe da fuska tsantsar mamaki ne ya hanashi sauƙar da hannunsa daga kan fuskar,
murya na kakkarwa ya ce "nayi danasanin Aurenki kuma uwa uba dana haɗa zuriya dake tirrr, nayi nadama matuƙa da ban samarwa ƴaƴana uwa ta gari ba,
nayi alhinin rashin matata Fatima mutumiyar arziƙi ko musu bata taɓa mun ba, Allah sarki mutuwa tayi mun yankan ƙauna,
yanzu ki fita mun a gida tin kafin na hallaka ki, yarana kuwa ko dake ko ba ke zasu rayu tinda duk cikinsu babu ƙaramin yaro sai Auta,
akwai jariran da ana haifansu suka rasa mahaifiyarsu kuma sun rayu kamar dai su twins Roshan da Razhdeen......"

Hajia Kilishi murmushin takaici tayi sannan ta ce "Da kyau! Ban damu ba dan ka koreni daga gidanka, ƙarewa ka kori ɗan daka haifa a cikinka ma balle Ni da kawoni akayi kuma zan tafi....."

Abbah cikin tsawa ya ce "to kije mana tsayuwar me kike? daman abinda kike nema kenam kije ki cigaba da yawon iskancinki,
Uwar masu gida tana ɓoye mun abubuwa akanki bata san na rigata sani ba, hotel ɗin da kike zuwa na sani, gidan Alhaji Shehu da kike zuwa kuna yawon barikinku na sani,
ce miki akayi aikin sojan da nake yi a banza nake yinsa? ko kuma tafiye-tafiye ƙasar wajen da nake zuwa duk shashanci ne bana lura da iyalai na? duk wani motsinki na sani, akwai waɗanda suke samun ido akan iyalaina gaba ɗaya ko ina nan ko bana nan,
ki je ki bana buƙatarki yanzu......."
Abbah ya ƙarasa maganar tare da fashewa da matsanancin kuka a yayinda ita kuma Hajia Kilishi gaba ɗaya jikinta ne yayi sanyi jin an tona asirinta a gaban yaranta, sannan shi kansa Abbah ya sani bawai iya Ummy bace....."
Itama fashewa tayi da kuka cikin jin kunya ta haura upstairs, ba jumawa ta sauƙo da akwatinta a hannu ta nufi bakin ƙofar fita,

Abbah zama yayi akan sopa yana huci ya tsayar da idonsa guri guda kamar mai tunanin wani abu, ya ce "kuma idan kuna buƙatar bin mahaifiyarku ku bita ban hanaku ba,
Idan kuna son kasancewa tare da ita ku bi bayanta amma inaso ku sani cewa daga yau kar ku ƙara ganina a matsayin mahaifinku muddin ku ka bita,
Ni inaso rayuwarku ta inganta ne....."

Durƙusawa Minal tayi a ƙasin carpet ta fashe da matsanancin kuka mai cin rai, babban takaicinta halin da Mommy ta jefa kanta aciki na yawon hotel,
Suma su Pinky zama sukayi suna kuka, Ƴar Tiny kuwa daman tin fitowar Baiwar ALLAH bata fito ba kwanciyarta tayi akan gado har bacci ya ɗauketa,

Abbah ya ce "duk ku zauna ku fuskance Ni..."
ya kalli Baiwar ALLAH sannan ya ce "Daughter kiyi haƙuri da abinda kika gani da kuma kika ji,
tambaya ɗaya zan miki yanzu inhar kin Amince,
shin kina son Roshan zaki Aure shi?...."

Baiwar Allah tana kuka ta ce "Abbah taya zan Auri Yaya Roshan bayan Ni kaina bansan asalina ba shin wacece Ni?...."

Abbah ya ce "duk wannan maganar ki barshi inhar kin ɗauke Ni a matsayin mahaifi toh ki dena sawa a ranki cewar bakida kowa, Ni na zamo miki kowa uwa da uba duk....."

Baiwar Allah ta jinjina kai tare da faɗin "shikenam Abbah duk yanda ka yanke dai-dai ne, Ni bani da zaɓi...."

Abbah ya ce "ba komai Daughter Allah ya miki Albarka....."

ta amsa da Ameen....

ya kuma cewa "insha Allahu zuwa next week za'ayi taron ɗaurin Aurenku....."

Dasauri Baiwar ALLAH ta ɗago tana kallon Abbah ta ce "Abbah dasauri haka?...."

Murmushi yayi sannan ya ce "toh me za'a jira Daughter, nafi son ayi abu a wuce gurin...."

Kallon Roshan tayi da rinannun idanuwanta, a yayinda shi kuma yake fama sake mata murmushi,
Sunkuyar da kanta tayi ƙasi tana sabinta kukanta sakamakon tuna Uncle Deen da tayi, a yanzu shine a ranta saboda tsananin shaƙuwar da tayi dashi, tin daga lokacin da ya mata wanka ta fara ƙaunarsa da irin kulawar da ya bata tana ciwon cikin nan,
Gaba ɗaya sai taji kamar ta sanar wa Abbah cewa Uncle Deen take so, amma sai dai abune mai wahalar gaske ta furta hakan......

Abbah ne ya juyo da kallonsa kan Pinky da Rukky sannan ya ce "ku kuma bayan biki da kwana biyu zaku koma ƙasar London ku cigaba da karatunku, hutunku ya ƙare,
Nima zan koma Ethiopia sai bayan shekara ɗaya na dawo"

ya kalli Minal ya ce "zan bar miki Amanar gidan nan a hannunki saboda kece babba,
Uwar masu gida da kuma Auta zasu kasance a ƙarƙashinki yanzu kece mahaifiyarsu,
Duk abinda kuke buƙata ku tuntuɓi Roshan, kuma zai rinƙa zuwa yana duba ku...."

Minal tana sauƙe numfashi ta ce "insha Allahu Abbah..."

Ya kalli Ummy sannan ya ce "uwar masu gida tinda bakya son barin Nigeria na sama miki school of nursing zakina zuwa da dawowa, akwai security da zai rinƙa kai ki kullum sannan ya ɗauko ki....."

Itama ta amsa da "toh Abbah...."
ta kuma cewa "Amma Abbah Yaya Roshan bazai koma gurin Aikinsa bane?...."

Abbah ya ce "akwai wani aikin da zai gudanar anan Nigeria sai yayi two years kafin ya koma Egypt shi da matar sa....."

Ummy tana hawaye ta ce "what about Uncle Deen? Dan ALLAH ka dawo dashi cikin Ahali muna buƙatar sa....."

Ajiyar zuciya Abbah ya ja kafin ya cigaba da cewa "ina sane dashi bazan taɓa barinsa ba ai, nasan a yanda yake domin nasa anbi mun bayansa,
inaso yaje can ya huta ne kuma ku huta da fargabansa...."

Cikin farin ciki Ummy ta ce "toh ina yake?...."

Abbah ya ce "yana gidansa na can ƙwarimpa...."

Abbah ya kuma cewa "yanzu dai ku tashi kuje kuyi mun lissafe-lissafen abubuwan da ake buƙata na biki, sannan Roshan ka ɗauki Daughter da uwar masu gida kuje su zaɓo kayan furnitures, da kayan lefe da duk abubuwan da ake so,
Sannan gobe inaso kaje ƙasar Jidder ka gano Uncle ɗin ku domin tinda kuka dawo baku je ba, idan zaka tafi kabi ka ɗauki Ɗan uwanka Razhdeen ku tafi tare....."

Abbah yana kaiwa nan ya haura upstairs, suma kowa tashi yayi ya koma muhallinsa iya Baiwar ALLAH da Roshan kawai aka bari a falon....
✓✓✓✓✓

Uncle Deen yana kwance saman katafaren gadonsa ya ɗora hannu akan goshi ido a lumshe kamar meyin Bacci,
tsananin yunwa ne yake damunsa ga shi kaɗai ne a gidan balle yasa a nemo masa abinda zai ci, sannan bai taɓa shiga kitchen ba balle ya iya cooking, ga wani irin kasala da yake ji balle ya tashi yaje restaurant tako ina ba sauƙi,
yana cikin wannan halin yaji wayarsa tana ringing, a hankali yakai hannu ya rarumo wayar dake saman chest ɗinsa, ido a lumshe yakai wayar saitin kunnensa ba tareda yaga sunan dake rubuce akan screen ɗin wayar ba,
"ℎ𝑒𝑙𝑙𝑜 𝑚𝑦 𝑂𝑔𝑎ℎ! a𝑚 o𝑛 𝑚𝑦 wa𝑦t𝑜 𝑁𝑖𝑔𝑒𝑟𝑖𝑎..."

"𝐴𝑟𝑒 𝑦𝑜𝑢 𝑠𝑢𝑟𝑒?..."
a cewar Uncle Deen, domin ya rigada ya dauki murya..

ta 6angaren Marshall kuma cewa yayi
"𝑌𝑎𝑛𝑧𝑢 ℎak𝑎 in𝑎 airpor𝑡 𝑛𝑎 𝑠𝑎𝑢𝑘𝑎 𝑎 𝑁𝑖𝑔𝑒𝑟𝑖a, daman na 𝑔𝑎𝑦𝑎 maka zuwan bazata zanyi maka...."

Uncle Deen kara narkewa yayi akan gadonsa domin baya jin zai iya tashi balle yaje airport
ya ce "look! you know 𝑤ℎ𝑎𝑡? kazo gidana na nan 𝑘𝑤𝑎𝑟𝑖𝑚𝑝𝑎 am here, but are you together with escorts?...."

Marshall ya amsa masa cike da mamakin yanda yake jin muryar Abokinsa kamar 'Dan maye
ya ce "na bana tare 𝑑𝑎 kowa but are you 𝑜𝑘𝑎𝑦? naji muryarka kamar baka da lafiya, and meyasa baka gida 𝑦𝑎𝑛𝑧𝑢𝑛?....."

Uncle Deen jin bazai iya amsa masa wadannan tambayoyinsa yasa shi cewa
"𝑃𝑙𝑒𝑎𝑠𝑒 𝑐𝑎𝑟𝑟𝑦 𝑦𝑜𝑢𝑟 𝑠𝑒𝑙𝑓 𝑎𝑛𝑑 𝑐𝑜𝑚𝑒 𝑡𝑜 𝑚𝑦 ℎ𝑜𝑢𝑠𝑒 𝑟𝑖𝑔ℎ 𝑛𝑜𝑤, 𝑎𝑚 𝑛𝑜𝑡 𝑓𝑒𝑒𝑙𝑖𝑛𝑔 𝑏𝑒𝑡𝑡𝑒𝑟...."
yana kaiwa ƙarshen maganarsa yayi ƙitt ya yanke ƙiran
tare da jan dogon numfashi......


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔

Daga Alƙalamin

Asma'u Muhammad Auwal Giade

𝘼𝙎𝙈𝙀𝙀𝙏𝘼𝙃✍️

𝙁𝙄𝙉𝘼𝙇 𝙊𝙁 𝙏𝙃𝙀 𝙁𝙄𝙍𝙎𝙏 𝙎𝙏𝙀𝙋✅

𝙏𝙃𝙀 𝙎𝙀𝘾𝙊𝙉𝘿 𝙎𝙏𝙀𝙋 𝙄𝙎 𝘾𝙊𝙈𝙄𝙉𝙂 𝙎𝙊𝙊𝙉✍️



𝙩𝙝𝙚 𝙚𝙣𝙙 𝙤𝙛 𝙨𝙩𝙚𝙥 𝙤𝙣𝙚
49 𝙩𝙤 50


Knock! Knock!! Knock!!!

jin yanda ake ta ƙonƙosa ƙofa yasa ya ɗan buɗe shanyayyun eyes ɗinsa waɗanda bacci yake shirin yaƙarsu,
ɗan

Please Login or Register in order to submit comment