Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son ranki, uwa uwace pah koda ta kasance mai tsinetsine ce akan bolaa......"
Baiwar ALLAH bata ƙarasa maganar ba taji Ummy ta katseta da cewa "uwa uwace amma gwara mun uwar da take yawo tsirara akan titi ta fiye mun wannan uwar....." ta ƙarasa maganar tana nuna Hajia Kilishi da yatsa......
tana ƙarasa maganar tayi gudu ta haura saman Upstairs tayi ɗakinta da gudu tana kuka......


Hajiya Kilishi dokuwa tayi akan carpet ta ɗora hannu aka ta fara rausa ihu tana faɗin "na shiga uku na lalace ɗiyata ta tsane Ni, bansan me nayi Wa Ummy ba ta tsaneni, Ni na haifeta a cikina, na ɗauki tsawon wata tara ina ɗauke ta ita acikin cikina sannan Ni nasan irin azabar dana sha a haihuwarta, nazo na shayar da ita har tayi shekara biyu amma abinda Maryam zatayi mun Kenam?....."

Minal ce ta durƙusa itama ta rungumi mommy tana rarrashinta, Pinky kam cewa tayi "ai Ni banyi mamakin jin hakan ba saboda tin ba yau ba nake cewa Ummy ba ƴar gidan nan bace, chanza mana asalin Ummyn mu akayi da wannan masifaffiyar yarinya...."

Rukky tace "ehhh! ana ce mana marasa tarbiyya ga cikakkiyar marar tarbiyya nan ai...."

Ƴar Tiny fashewa tayi da kuka itama ganin mommynsu tana kuka,
Baiwar ALLAH bazata iya sauraron jin kukan Hajia Kilishi ba yasa itama ta haura upstairs ta wuce ɗakin Ummy, tana shiga ta tarar da ita tanata zuba kaya acikin wata ƙatuwar akwati,
Baiwar ALLAH ƙarasa shugowa tayi ta zauna a bakin gado idonta akan Ummy tace "Ina zakije kuma?...."

Daƙer Ummy take motsa lips ɗinta tace "ina kuwa zanje Ni da gidan ubana...."
Murmushi Baiwar ALLAH tayi sannan ta ce "kina ganin kin kyautawa kanki? Mahaifiyarki ta fashe da kuka saboda ke, shin ribar mai zaki samu idan kin ƙuntata mata?....."

Ummy ko kallon Baiwar ALLAH batayi ba tace "TOH ina ruwana...."

Baiwar ALLAH cike da takaici ta ce "Allah sarki wasu suna rayuwa ba tare da iyaye ba, suna so suga iyayensu amma babu hali, ki godewa Allah daya bar miki mahaifiyarki......"

Kafin Baiwar ALLAH ta iddasa maganar ta Ummy ta katseta da cewa "Kinga Aunty Baiwar ALLAH da wannan uwar tawan gwara ace uwata daga haifata ta mutu wallahi tallahi,
Uhmmmmm! kinaso kisan wani abu ne akan wannan mahaifiyata? bawai bana sonta bane ɗabi'unta da halayyar ta sam ba masu kyau bane,
Duk da har yau babu wanda yasan abinda mahaifiyata take aikatawa amma ya zama dole na fasa ƙwai domin bazan iya juran ganin ana cin amanar mahaifina ba inaji ina gani a matsayina na uwar masu gida wacce akafi yadda da ita akan kowa...
Uhmmmmm!
Aunty Baiwar ALLAH Inaso kisan cewar mahaifiyata mazinaciya ce....."

A razane Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye tana furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un....."

Ummy ta cigaba da cewa "Yes! Ita tayi sanadiyar rabani da masoyina wanda nake matuƙar so da ƙauna kuma nake burin Aura,
akwai wanda mahaifiyata take zuwa wajensa suna yawan haɗuwa a hotel, hotel ɗin kuma anan mahaifin saurayina yake aiki, wata rana saurayina yaje hotel gurin mahaifinsa dake basuda ƙarfi sosai sai kawai ya kalli mommy da wani ƙaton mutum mai ƙaton ciki sun karɓi key, dake ita mommy bata taɓa ganin saurayina ba saidai taji labarinsa, sai saurayina yake tambayar Babansa cewar mai wannan matar take zuwa yi anan sai mahaifinsa ya sanar masa cewar ai kusan kullum suna zuwa, saurayina baiyi ƙasa a gwiwa ba haka ya bibiyesu har ya samo ɗakinda suka shiga cikin rashin sa'a basu rufe ƙofa ba, a take ya zaro wayarsa ya fara musu video suna kwance a cikin mayafi ga kayansu a gefe guda,
Daga baya ya ƙirani a waya yake cemun wai in rinƙa yiwa mahaifiyata nasiha da wa'azi domin ita yanzu ba ƙaramar yarinya bace, a lokacin na samu matsala sosai dashi saboda a tunanina ya raina mun mahaifiya ne sai daga baya ya Turo mun video ta WhatsApp, a lokacin ji nayi kamar na kashe kaina, tin daga wannan lokacin na fara bibiyan wayar mommy, nayi nasarar saka mata waya a recording sannan nayi tracking phone ɗinta , duk wayar da zatayi ina jinta sannan ina sakawa ana bibiyanta duk yanda zataje, tana zuwa wajen aiki amma daga wajen aiki take wucewa hotel shiyasa bata dawowa gida da wuce sai dare, idan aka tambayeta sai tace aiki ne yake riƙeta,
Amma kuma bata zuwa wannan yawon idan Abban mu yana gida saboda tasan baya wasa idan lokacin dawowarta gida yayi zai fara sa ido har saita dawo ko acikin yaran ne ma,
hakan yasa na tsani mommy kuma har zuwa yanzu ta kasa chanza hali, kuma yau bata je wajen aiki ba, wuni tayi a gidan mutuminta dake shima matarsa bata nan, kuma karki manta matar mutumin ƙawarta ce, inasa ana bibiyan mommy duk yanda taje sai an ƙirani an gaya mun,
Jira nake Abbah ya dawo za'ayita ta ƙare......"

Baiwar ALLAH ta girgiza tajin wannan labarin
Sai furta "innalillahi wa inna ilaihi raju'un kawai take..
Can Baiwar ALLAH ta kamo hannun Ummy ta zaunar da ita ta rungumeta a hankali take faɗin "kiyi haƙuri Ummy abinda nake so dake kar ki bari kowa yasan da wannan maganar, ki samu hajia ki zauna da ita kuyi magana ta fahimta kiyi mata nasiha na tabbata zata bari, idan ma tasan kinsan a halinda take ciki zata bari kodan saboda ke...."


Jin ummy bata kulata ba yasa ta ɗago da manyan idanuwanta tana kallon Ummy, taga Ummy ta kafa ido guri ɗaya, da sauri Baiwar ALLAH ta waiwaya tana kallon bakin ƙofa taga me Ummy take kalla sai kawai taga Hajia Kilishi tana tsaye ta jingina bayanta a jikin bango kanta a sama tana zubda ƙwallah ko magana babu, a zabure Baiwar ALLAH ta miƙe tsaye ido a zare tana kallon Hajia Kilishi..........



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 21 to 22



꧁꧂


Hajia Kilishi zama tayi a bakin gado dab da Ummy, ta juyo tana kallon Baiwar ALLAH wacce ta miƙe a zabure tana tsaye kai a sunkuye taji Hajia tace mata "Inaso ki bamu guri zanyi magana da ɗiyata...."

Ba musu taja sassanyar jikinta tayi hanyar fita har zata buɗe ƙofa taji Ummy tana cewa "jirani mu fita tare..."
itama ta nufi bakin ƙofar!

Hajia Kilishi miƙewa tayi tsaye cikin ƙunan rai ta ce "Ummy gurinki fah nazo..."
Ummy ta juyo tana mata wani irin kallo ta ce "gurina kuma? au na ɗauka ziyara kika kawowa ɗakin ai,
toh indai gurina kika zo ƙafata ƙafar Aunty Baiwar ALLAH, domin yanzu itace jinin jikina, in babu ita babu Ni sannan in babu Ni to kuwa babu ita saboda haka duk abinda zaki faɗa a gabanta zakiyi idan kuwa ba haka ba wallahi bazan saurareki ba....."
ta ƙarasa maganar tana yamutsa fuska.
Hajia Kilishi kamar ta haɗiyi ranta tsabar takaici daƙer ta iya motsa baki ta ce "toh shikenam naji duk ku zauna...."

Ummy tace "okay yanzu naji batu..."
ta ƙarasa maganar tareda ɗosana mazaunenta akan kujerar mirror tana fuskantar Hajia Kilishi, ita kuwa Baiwar ALLAH tsayawa tayi ta jingina bayanta a jikin bango tana kallon ceilling, tana mamakin Ummy ta yanda take da ƙwarin gwiwar gayawa mahaifiyarta maganganu son ranta, hakan sam baiyi mata daɗi ba, ga yanzu tace indai Baiwar ALLAH bata tsaya ba itama bazata saurareta ba hakan yasa Baiwar ALLAH tsayuwa amma badan haka ba ai uwa da ƴa suna buƙatar sirri especially halinda ake ciki yanzu...

Hajia Kilishi gaba ɗaya duk ta haɗa zuffa domin a tsorace take taji duk maganganun Ummy akan ta, daƙer ta iya samun ƙarfin halin cewa "Ummy dan ALLAH kiyi haƙuri...."

Ummy itama kallonta take cikin rashin fahimta tace "sorry for your self...". ta ƙarasa maganar tare da kawar da kanta gefe...

Hajia Kilishi kallon Baiwar ALLAH tayi sannan ta jinjina kai ita bataso ace Baiwar ALLAH tasan da wannan sirrin ba amma dan babu yanda ta iya ne, gashi yanzu mutuncinta ya zube a idon Baiwar ALLAH, haka take ta wannan tunanin....

ta Kuma cewa "duk naji maganganunki wanda dalilin da yasa kika tsaneni Kenam amma Inaso ki sani cewar dolenki Ni ce mahaifiyarki, ko ki soni ko ki ƙini Ni na haifeki Ummy, amma akwai Right ɗin da ƴa zata zauna ta bawa mahaifiyarta shawarwari masu kyau da inganci, haka itama anaso uwa ta gari ta zaunar da ƴaƴanta tayi musu nasiha da shawarwari masu kyau, amma sai dai Ni ɗin ban kasance a irin tsarin iyaye masu yin haka ba, hakan yana matuƙar damuna sosai...."

Dakatar da yin maganar tayi jin yanda Ummy take kwashewa da dariya harda kama ciki, ba hajia ba hatta Baiwar ALLAH abun ya bata mamaki da kuma haushi, saida Ummy ta daidaita nutsuwarta tukun ta kalli Hajia Kilishi ta ce "ehen! cigaba mana ya kika tsayar da tatsuniyar...."

Baiwar ALLAH ce ta buɗi baki zata yi magana taga Hajia Kilishi ta ɗaga mata hannu alamar dakatarwa cikin fushi ta ce "ki dakata mun bada ke nake magana ba kada naji kin tsoma mun baki,
duk abinda tayi taga daidai ne a gurinta shiyasa...."
Sannan ta juyo kan Ummy ta daidaita nutsuwarta sannan ta ce "Ummy dariyar me kike?...."

Cike da mamaki Ummy take kallon Hajia sannan tace "naji kince ƴa ta zaunar da mahaifiyarta tayi mata nasiha da shawarwari shine na hasashoki yanzu fisabilillah Mommy kece zaki zauna ƴa tayi miki nasiha? nasihar mijinki ma yaushe kika ɗauka balle na ƴaƴa,
Uhmmmmm yanzu da kika ga babu wani sarki sai Allah shine zaki zo ki cikani da zaƙin baki koh? saboda Kinga asirinki yana dab da tonuwa ...."

Miƙewa Hajia tayi taje gaban Ummy tana hawaye sannan ta durƙusa da gwiwowinta a ƙasin carpet ta kamo hannun Ummy tana rirriƙe su,
Ba Baiwar ALLAH ba hatta ita kanta Ummy saida jikinta yayi sanyi ganin mahaifiyarta acikin wannan halin kuma saboda ita, taji ba daɗi a ranta sosai,

Hajiya Kilishi ce ta soma magana cikin sassanyar murya ta ce "Ummy ƴata kisani ko mai zaki mun bazan taɓa tsanarki ba balle na gujeki, ina sonki har cikin raina , Ummy dan ALLAH ki rufa mun asiri, wallahi tallahi matsala ce tasa nake aikata haka amma yanzu nayi nadamar aikata haka a rayuwata, ba wai don saboda kar mijina ya rabu dani bane a'a saboda Inaso na tsira da mutuncina ne, shin idan aka tambayeni meya rabani da mijina mezance? idan akace saboda yawon bin hotel ne yasa mijina ya rabu dani shin ya zan kasance? shima kansa Abban nakun zaiji kunya matuƙar ace yana matsayin Chief of Army's amma matarsa tana bin wani namiji awaje, hakan bazai yuba, dan ALLAH Ummy ki temake Ni duk da ance da kunyar lahira gwara ta duniya amma duk ina neman tsari daga jin kunyar lahira dana duniya, domin a duniya matsayina ya wuce wannan layin, sannan Inaso na jawa ƴaƴana mutunci a gurin al'umma, Ummy yanzu idan kika tona mun asiri yanzu zakiga an fara yaɗani a social media da television domin mijina ba ƙaramin mutum bane haka zalika nima kuma abun kunya ne a gareku....."
bata ƙarasa maganar ba kuka ya kuɓuce mata ta kifa kanta akan cinyar Ummy....

Ummy itama kukan take ta zamo daga kan kujerar ta zauna a ƙasin carpet yanda Mommynta take, tana kallon Hajia ta ce "mommy gaya mun meyasa kika zaɓi wannan ƙazamar rayuwa wanda ko mu ƴaƴanki baza muyi haka ba ..."

Hajia Kilishi ta ce "akwai dalilin da yasa na zaɓi wannan rayuwar...."

Ummy cike da mamaki ta ce "shin ci kika rasa ne ko sha? ko kuma kuɗin kashewa?..."

Hajia Kilishi cikin nuna damuwa ta ce "ko ɗaya ban rasa abubuwan da kika lissafo ba, amma saidai na rasa lafiyar jikina shine dalilin da yasa nake bin wani a waje..."

Ummy idonta akan Hajia Kilishi ta ce "bangane mai kike nufi ba ..."

Hajia Kilishi tana kuka tana riƙe da hannun Ummy tace "Ummy duk cikin ƴaƴana daga ke sai Tiny a ƙarantar shekaru kinada yayu amma kuma duk kin fisu hankali da tunani mai kyau, hakan yasa na zaɓi na gaya miki sirrin abinda ke damuna tinda kema naga kin damu dani shiyasa duk sanda zan fita kike sawa a bibiyeni abinda ko Minal bata taɓa yin ƙoƙarin hakan ba, Ummy bansan wani irin halitta ne dani ba na ƙarfin sha'awa, inada munguwar sha'awa wanda idan nayi kwana biyu zuwa uku ban samu namiji ba akwai matsala babba, yawan zuwa hospital da nakeyi akan wannan matsalar ne tinda Allah ya bani miji ba mazauni ba, mahaifinku sam bai damu da mace ba, hakan yasa idan ya tafi ƙasar waje baya dawowa da wuri sai yayi watanni har shekara bai dawo nan gida Nigeria ba, shin da haka zan rayu? idan cikina ya murɗa ji nake kamar zan bar duniya tsabar azaba har saina ga namiji a kusa dani ,
Amma duk da hakan ban taɓa barin wani namiji daban wanda ba mijina ba ya shigeni saidai na tsaya a iya Romance, da haka zanji sanyi a raina,
Ban san ya zanyi ba wallahiiii......."
Nan ta ƙara fashewa da matsanancin kuka mai cin rai...

Ummy juyowa tayi tana kallon Baiwar ALLAH wacce itama tana tsaye ta zuba musu ido ba ƙaramin tausayawa Hajiya tayi ba,
Ummy gaba ɗaya ta rasa mai zatace abun yana shirin fin ƙarfin ƙwaƙwalwarta, ganin babu abinda zata ce yasa ta kai hannu ta rungumo mahaifiyarta tana rarrashinta tare da faɗin "kiyi haƙuri Mommy wallahi inasonki wannan rayuwar da kika ɗauko ne banaso Amma tunda lalura ce tasa Insha ALLAH zan nemo miki mafita amma ba wanda kike ciki yanzu ba, shin Abbah yasan a halinda kike ciki na lalurar nan?....."

Hajiya Kilishi ɗaga kai tayi alamar eh!
murya na kakkarwa ta ce "ya sani tin kafin a haifeku amma sai dai yaƙi ɗaukar maganata da serious, wani sa'in idan nayi mishi maganar nan sai yace na dena takura masa, duk da shima yana iya ƙoƙarinsa niɗin ce dai Inaso infi ƙarfinsa amma abun nashin yayi yawa shekara guda bai kusanci matarsa ba duk yana can yawon tafiye tafiyen ƙasashen waje....."

Ummy gyaran murya tayi sannan tace "mommy wata ƙil ke harija ce koh?...."

Hajiya Kilishi tana kuka lokaci guda ta tintsire da dariya tana dukan Ummy a gaba cikin zolaya take faɗin "ke dan ubanki aina kika san akwai Harijai ?..."

Ummy murmushi tayi sannan tace "mommy nifa inada burin zama Doctor kawai dai ƙasar waje ne bazan fita ba, dole Abbah ya rinƙa guduwa kullum baya zama saboda kina shirin ƙarar masa da ruwan jikinsa, mommy inaga Aunty Minal ma ke ta ɗauko domin itama tana cikin wannan halin amma saidai ita bata bin maza, akwai maganinda take sha ta samu sauƙi kafin wani lokaci kuma du, zanje na ɗauko miki kema kina sha zaki samu sauƙin abun sosai...."

Hajiya Kilishi zaro ido tayi cike da mamaki ta ce "Kenam Minal tana fama da irin matsala ta? tabbas tana yawan ciwon ciki amma banyi tunanin akan haka bane, Minal tana buƙatar Aure amma saidai taƙi kawo tsayayye wanda za'a aura mata, ta nace a wancan Christal na ƙasar Australia shi kuma Abbanku bazai taɓa Aura mata shi ba...."

Ummy ta ce "tana masifar son Mohandas ɗan gidan Chief of Defence staff na ƙasar Australia amma sai dai shi ba musulmi bane kuma iyayensa bazasu barshi ya musulunta ba haka itama baza'a barta ta Auri christal ba, but suna son junansu basa son rabuwa....."

Hajiya Kilishi kamar zata ƙara fashewa da kuka jin Minal irin matsalar gare ta tayi matuƙar tausaya mata sosai cikin yanayin damuwa ta ce "TOH tace idan ba Mohandas ba bazata Auri kowa ba TOH ya zamuyi mata?
Kedai Ummy kisan yanda zakiyi ki temaka mun dan ALLAH, bayan isha'i ina jiranki a room ɗina...."

tana ƙarasawa ta miƙe tsaye ita har ta manta da Baiwar ALLAH tana cikin ɗakin sai yanzu tayi ido huɗu da ita, bata ce komai ba tayi ficewarta........



*GA WANNAN KUYI MANAGE ZUWA DARE ZAKU GA ANOTHER PAGE KUYI HAƘURI BANDA CHAJI NE A WAYA SHIYASA.....*


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ

Please Login or Register in order to submit comment