You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
Baiwar ALLAH farin ciki kamar bazata mutum ba, sai murmushi take ta zabgawa ganin a gidan da zata zauna, amma lokaci guda data tuno da Ƴar Amana sai taji kamar ta rausa ihu, babu yanda ta iya haka take danne zuciyarta domin bata son General ya fahimci akwai damuwa a tattare da ita...
General ne yace mata "tashi maza na kaiki ciki yanda mutanen gidan suke koh?..."
Dasauri ta miƙe tana ɗingishi daƙer take jan ƙafar, General ganin haka yasa shi cewa "what! meya faru dake haka?..."
Girgiza masa kai tayi tare da faɗin "babu komai" idonta akan sojan dake tsaye yana jinsu,
General idonsa yakai kan sojan cikin ɓacin rai yace "ku baku san mace bace? daga ganin mutum baku san dame yazo ba shin da Alkhairi ne ko da sharri baku sani ba, just kun fara ɗaukar hukunci akai, wani irin abu ne haka? ku kiyaye saurin ɗaukar hukunci banaso...."
Sojan dake tsaye yana kallon gabansa ya ce "Yes Sir, Insha Allah zamu kiyaye..." daga baya General ya ɗaga masa hannu akan ya wuce, Bayan fitar sa itama Baiwar ALLAH fitowa tayi tare da shi General, kai tsaye compound dazai sadasu da cikin babban falon na gidan suka shige,
General ganin yanda Baiwar ALLAH take ta kallace-kallace yasa ya riƙo hannunta suka ƙarisa shigewa, a cikin babban fallon suka tarar da kowa na gidan duk sun hallaru dake a yau Aunty Yolash dake Bauchi itama tazo ta abunda ya kawota shine ta'aziyyar Hajia Aliya,
Hajiya Kilishi ce zaune itama da zankaɗa-zankaɗan ƴan matan gidan wato yaran Hajia Kilishi dake duk yaranta mata ne su biyar, Babbar cikinsu wato Minal tana kwance akan sofa 3 seater ta ɗora ƙafa ɗaya akan ɗaya tana sanye da gajeren jeans wanda ya tsaya mata a iya gwiwa sai faman daddanna wayar hannunta take mai ƙirar iphone 15 sai tauna ciwgum take tana ƙararass, asalin ƴar girman kai kenam ga iya ɗaukar fashion, bata hulɗa da ƙananun mutane sai manya-manyan ƴaƴan masu kuɗi kamar yanda take ƴar Babban mutum, ta tsani ganin talaka marar class a rayuwarta, yanzu tanada shekara 25 ta kammala Degree ɗinta a ƙasar England.....
Sai waɗanda suka biyo bayanta wato
Pinky and Ruky ƴan biyu ne duk mata Hajia Kilishi ta haifa, waɗannan yaran sune masifaffun gidan, banda wulaƙanta mutum ba abinda suka iya, ga gadara da isa da burga, Pinky and Ruky their are too stubbornness, yaran masu kuɗi kenam jiki duk madara, su biyu suna kwance suma akan 5 seater wannan ta ɗorawa wannan ƙafa wannan ma haka, sai faman danna wayoyin hannayensu suke maka-maka, yanzu suke da shekara 20 cif cif suna karatun Degree ne a ƙasar London.....
Sai gambonsu wato Ummy dake zaune a 1 seater ta nannaɗe ƙafafuwa ta sanya farin glass akan dararan idanuwanta kana ganin glass ɗin kasan na medical ne mai tsadar gaske, dake tanada matsalar ido, tana riƙe da ƙaramin littafin Alkur'ani mai girma baki da motsi a hankali take karantawa acikin zuciyarta domin yayunta sun tsawatar mata akan cewa kada ta toshe musu kunne da karatunta, Ummy uwar masu gida Kenam, full name Maryam mai sunan mahaifiyarsu General da mai martaba sarkin ƙasar Jidda da kuma Aunty Yolash, Ummy batada matsala ko kaɗan Sarkin haƙuri, bata fiye yin magana ba, ta kammala Secondary school anan school of Nursing, ana son turata ƙasar waje akan taje ta cigaba, tace ita bata son zuwa ƙasar waje tafison tayi school anan Nigeria dalilin da yasa bata cigaba ba Kenam saboda mahaifiyarta Hajia Kilishi tace nan duniya duk ƴaƴanta babu wacce zata cigaba da school a nan Nigeria tace saidai yarinyar tabar karatun kwata-kwata indai a Nigeria zata yi,
shiyasa Hajia Kilishi bata sa Ummy a ranta ba saboda ita kaɗai ce bata ɗauko halinta na rashin mutunci ba,
yanzu Ummy uwar masu gida tanada shekara 17 a duniya amma sai halin dattawa......
Daga kan Ummy Hajia Kilishi ta dakatar da haihuwa domin a cewar ta yawan haihuwa yana lalata mace, bata son tara yara kamar ɓeraye a gida, waɗannan huɗun sun isheta Minal, da twins Pinky and Ruky sai Ummy, bayan nan ta ɗau shekaru bata sake haihuwa ba sai daga baya ta samu cikin Ƴar Tiny ba'a son ranta ba, bata san ya akayi ta samu cikin ba domin ba ƙaramin planning tayi ba, anan sun samu matsala sosai da General mijinta akan saita zubar da cikin, shi kuwa yace saidai ya sake ta, haka ta haƙura babu yanda ta iya harta haifi Ƴar Tiny, tasha wahala sosai Saida aka mata Operation, ganin mace ta ƙara haifa yasa tace a cire mata mahaifa saboda ta fidda rai akan samun yaro namiji gashi yara sun taru mata, tayi kuka sosai duk yaranta babu namiji...
Ƴar Tiny yanzu shekarar ta 5, fitinanniyar yarinya ga rashin jin magana da yawan ɓarna,
Ita kaɗai ce a tsakiyar falo tana zaune akan carpet sai wasa da ƴar tsanarta take tana mata kitso,
Aunty Yolash itama tana zaune akan kujera 2 seater idonta akan wayar hannunta tana jiran shigowar General tanaso tayi masa sallama zata koma Bauchi,
A yayinda ita kuma Hajia Kilishi take kan 3 seater itama tana press ɗin wayar ta tana tauna ciwgum, inta ɗago saita harari Aunty Yolash domin basa jituwa sosai akwai ƴar tsama a tsakaninsu,
Ita Aunty Yolash a rayuwarta ta tsani mutum ya cika wulaƙanta ɗan Adam don yanada ƙarfin iko, shiyasa Aunty Yolash bata shiri da Hajia Kilishi domin halinta Kenam wulaƙanci da girman kai gashi harta koyawa yaranta banda Ummy wacce ta fita daban a cikinsu sai Tiny wacce ita yarinya ce ba'a san wata kala bace ita....
Suna cikin wannan halin saiga General ya shugo yana riƙe da hannun Baiwar ALLAH da sallama a bakinsa,
Baiwar ALLAH gaba ɗaya tayi bususu da ita ga ƙafa ba takalmi ga tayi wani irin datti har farinta yaɗan disashe,
Aunty Yolash ce da Ummy kawai suka ɗago tare da amsa masa sallama a yayinda ita kuma Hajia Kilishi da sauran yaran ko ɗagowa basuyi ba domin sun san da cewar Abbansu ne ba wai wani ba,
Ƴar Tiny ce ta tashi tana faɗin "Abbah Oyoyo! Abba ina abinda nace a siyo mun, ina alƙawarinaaa...."
Abbah yace "kiyi haƙuri Auta ki bari sai kowa yayi bacci da daddare zan baki kinji koh...."
turo baki Tiny tayi ta ce "toh Abbah wacece wannan yarinyar..." ta ƙarasa maganar tana farfara ido, kama kuncinta yayi yana wasa da ita yace "Auntyn ki ce?..."
Ƴar Tiny ƙara turo baki tayi tare da faɗin "cabb ɗin wannan mai dattin ce Aunty na?..."
Hajia Kilishi dasauri ta ɗago domin tabbatar da abinda ƴar Tiny take faɗi, ai kuwa idonta ya sauƙa akan Baiwar ALLAH nan take ta miƙe tsaye tana harararta cike da takaici ta ce "wannan kuma aina ka samota General?..."
ya ɗago yana kallonta yace "Baƙuwa kukayi kuma zata cigaba da zama ne acikin gidan nan...".
A zabure Hajia tace "whattt!!!! Impossible I swear, ko wani jaki da dabba da alade sai a kawo mana gida? TOH yarana ma sun isheni bana buƙatar ko wani ƙazami ...."
cike da takaici General Yake binta da kallo, ya girgiza kai sannan yakai idonsa kan Aunty Yolash wacce ta taso tazo gaban Baiwar ALLAH ta kamo hannunta tana faɗin "your welcome Baƙuwar mu ki shugo kinji koh...."
Fuskarta ɗauke da ƙayataccen murmushi, ta zaunar da ita akan kujera, Baiwar ALLAH ganin kallon da Hajia Kilishi ke mata yasa tayi saurin zamewa ƙasin carpet tace "a'a Aunty a ƙasi ma ya isa...."
Minal juyowa tayi tana wurga mata harara lokaci guda taja tsuka ta cigaba da press ɗin wayar hannu ta,
Pinky da Ruky ƙusu ƙusu suke suna magana ciki ciki Pinky tace "zata ci durun uwarta ne tinda ta kawo kanta kurkukun azaba..."
Ruky tace "barta Ni kaɗai ma na isheta saita ƙwammace gwara tayi zaman daji wallahi, ai ina Abbah ba mazaunin ƙasar nan bane to ai tazo da sauƙi...."
haka suketa wannan mita a junansu....
General ne ya kalli Ummy uwar masu gida da murmushi akan fuskarsa domin aduk lokacin da ya kalli Ummy ko yana cikin ƙunci sai yaji sanyi a ransa, yana matuƙar ji da ita sosai ga mai sunan mahaifiyarsa ce Abar ƙaunarsa,
Yace "Uwar masu gida ga Abokiya na kawo miki...."
itama murmushi tayi ta taso daga zaunenda take tare da ajiye littafin Kur'ani tazo yanda Baiwar ALLAH take itama ta zauna a ƙasin carpet ta rungumeta tana faɗin "Abbah ai wannan tafi ƙarfin Abokiya sai dai Aunty...".
ta kalli Baiwar ALLAH tace "Barkan ki Aunty nah...."
Itama Baiwar ALLAH murmushi ta saki tana kallon Ummy ga glass ɗin yayi mata kyau sosai gata fara ce itama tass,
Hajia Kilishi ta dararawa Ummy tsawa tace "taya ta zamo Auntynki dan ubanki munafukar banza...."
tanayi tana kallon General domin in kanaso ka ƙuntata masa TOH ka zagi Ummy, anan zaku samu matsala,
kafin ta ankara ya wurga mata wayar hannunsa zai kai mata mari Aunty Yolash tayi saurin riƙo shi tana faɗin "kayi haƙuri Yaya, ka ƙyaleta abinda take nema kenam, tinda bata kama girmanta ba kai kuma saika nuna mata ka fita sense ko dan saboda yaran gurin nan...."
General yana Huci ransa ba ƙaramin ɓaci yayi ba,
Hajia Kilishi tana hararar Aunty Yolash tace "Ni ce banida hankali Kenam, ki tsaya a iya matsayinki na ƙanwar mijina karki nemi ki shiga mun gonata wallahi...."
Aunty Yolash ta dubeta dakyau sannan tace "daman ke har gona ce dake? Mttssw....."
General cikin ɓacin rai yake kallon Hajia Kilishi yatsarsa akan Baiwar ALLAH yace "akan wannan yarinyar zakiyi sanadiyar rasa igiyar Aurenki wallahi tallahi...."
Dasauri Hajia Kilishi ta juyo tana kallonsa cike da mamaki.
Minal dake kwance Saida ta miƙe zaune tana faɗin "whatttt!...."
Pinky da Ruky kam sake baki sukayi jin abinda Abbansu ya gayawa Ammynsu...
Minal tashi tayi taja dogon tsuka zata haura upstairs yanda ɗakinta yake, Abbah ya darara mata tsawa yana faɗin "your very stupid, Amina are you mad? ina magana shine zaki ja mun tsuka kibar mun gurin? Ko mahaifiyarki gata nan batada wannan ikon da ina cikin mata magana taja tsuka tace zata bar gurin, Amina ki kiyaye Ni i swear to God zan rufeki a gadurun kiyi kwana biyu muga girman kan nakin..."
ya cigaba da cewa "wallahi tallahi duk yarinyar da naji labarin tana musgunawa yarinyar nan saina sa an rufe ta a barrack aita azabtar da ita kunji da rantse koh, ku bar ganin bana zama a Nigeria duk inajin labarin rashin mutuncin da kukeyi, kuna jamun magana a gari a matsayina na General Sojoji amma ƴaƴana babu tarbiyya tirr wallahi...."
Pinky ce ta kalli Ruky a hankali tace "kuttt buro ubaaa akan wannan matsiyaciyar za'a rufe mu a gadurun?...."
Abbah ne ya kalleta yaji duk abinda tace duk da a hankali tayi maganar, cikin ɓacin rai ya ƙira sunan Ƴar Tiny yace "Auta kije gaban Balkisu da Ruƙayyat duk ki mammare su..."
Ai kuwa da gudun gaske ƴar Tiny taje gabansu da ƴar ƙaramar hannunta ta seta fuskar Pinky ta zabga mata mari sannan ta zabgawa Ruky mAh, ta dawo ta zauna tana dariya,..
Pinky da Ruky abun yayi musu ciwo sosai harda hawayensu,
Abbah yace "wannan shi ake ƙirada ramuwar gayya, tsabar raini ina magana kuma kuna yi TOH mu cigaba...."
Minal zama tayi kai a sunkuye sai zubda ƙwallah take a rayuwarta ta tsani ayi mata faɗa hakan yana ƙuntata mata rai sosai...
Aunty Yolash tana rarrashin Abbah tace "kayi haƙuri Yaya, idan ka biyewa yarannan hawan jininka zai iya tashi, nayi waya da twins Razhdeen da Roshan next week suna kan hanya, ka kusan hutawa da hayaniya...."
Hajia Kilishi ƙirjinta ne yayi wani irin bugawa jin an ambaci sunan Twins zasu dawo, tana matuƙar jin shakkar su da tsoronsu uwa uba Major general Razhdeen wanda suke ƙiransa da sunan Uncle Deen...
Sauran yaran ma sun girgiza sosai dajin dawowarsu
Ko wacce jikinta ne ya soma kakkarwa, especially Minal Babbar cikinsu duk tasha jinin jikinta....
Banda Ummy wacce take farin cikin dawowarsu,
Ƴar Tiny kuka ta soma yi tana faɗin "banaso su dawo, Uncle Deen dukana yake yiiii..."
𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.
𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦♀️🤦♀️
𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢
𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.
𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈
ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..
𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:
1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.
3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.
4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.
𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 13 to 14
Aunty Yolash gaban General ta tsaya cikin nuna damuwa tace "Yaya idan ba damuwa ka bani yarinyar na tafi da ita mana tinda mutanen gidan ba son zamanta a gidan suke ba, zata sha wahala ne a gurinsu.."
General a fusace yace "dole zata zauna a cikin gidan nan, kuma naga wacce ta isa ta takura mata, gobe da sassafe zan hau jirgi zan tafi Maleshiya akwai meeting ɗin da zamu gudanar acan, zanyi two weeks wata ƙil su Roshan su rigani dawowa..."
Aunty Yolash girgiza kai kawai tayi tare da faɗin "shikenam TOH, daman Nima yanzu nake son komawa Bauchi..."
General yace "ok akwai saƙon da zan tura miki zaki gani kafin ki isa..."
ya kuma cewa "Ita kuma yarinyar nan ku kaita ɗakin da zata zauna...."
ya kalli Ummy yace "uwar masu gida ganan Auntynki nan zan baki kuɗi kuje ɗaya daga cikin security yakai ku super market kiyo mata siyayyan kayayyakin da zatayi amfani dasu..."
Ummy tace "toh Abbah...."
shi kuwa wuce wa yayi ya haura upstairs yanda ɗakin kwanansu yake,
ita kuwa Ummy hannun Baiwar ALLAH ta riƙo suka miƙe tana cemata "tashi na kaiki ɗakinda zaki zauna koh..."
ɗakinda yake ƙasin stairs ta shigar da ita, itama Aunty Yolash bin bayansu tayi, a yayinda Hajia Kilishi take binsu da harara ta kasa cewa ƙala, cikin takaici taja dogon tsuka itama ta haura upstairs can bedroom ɗinta,
Itama Minal jiki a sanyaye ta miƙe ta nufi bedroom ɗinta wanda yake saman Upstairs,
Kana shigowa cikin babban falon zaka tarar da gidan beni Three part,
ta bangaren dama akwai beni mai hawa uku , kana kai ƙarshe zata tarar da layi gida biyu right and left, idan kabi layin right shine zai kaika har part ɗin Major general Razhdeen, da ɗan rasa kaɗan kafin ka isa part ɗinsa....
Layin left kuma shine zai kai ka har part ɗin Doctor Roshan shima kafin ka isa akwai ɗan tazara...
Idan ka sauƙo falon kuma still akwai gidan beni ta bangaren hagun mai hawa biyu shi kuma, kana kai ƙarshen Benin zaka tarar da ɗakuna guda biyar a jere, ɗakunan ƴan matan gidan Kenam kowa da ɗakinsa, ɗaki na farko shine ɗakin Minal sai na biyu kuma ɗakin twins pinky and Ruky ɗakinsu ɗaya sai ɗakin Ummy ta gefensu sai kuma ɗakin Ƴar Tiny amma a waran mommynta take kwana ita sai ɗayan ɗakin da babu kowa a ciki,
Kowa ɗakinsa da ɗan tazara dana ɗaya,
Kana komowa falon kuma zaka ƙara tarar da gidan Beni ta tsakiyar right and left, nan ma hawan beni uku ne kana hawa zaka tarar da ɗakuna biyu, ɗakin Hajia Kilishi da kuma General,
A ƙasin falon kuma a ƙasin benin su General wani wantamemen dining table ne sai ƙaton kitchen ata gefe guda da kuma store na kayan Abinci,
A ƙasin benin ƴan matan gidan kuma ɗakuna uku ne a jere wato ɗakin baƙi idan sun zo,
Book Chapters
Chapter 9
Chapter 10Chapter 11Chapter 12Chapter 13Chapter 14Chapter 15Chapter 16Chapter 17Chapter 18Chapter 19Chapter 20Chapter 21Chapter 22Chapter 23Chapter 24Chapter 25Chapter 26Chapter 27Chapter 28Chapter 29Chapter 30