Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 23 to 24



꧁꧂


Hajiya Kilishi har ta fita ta ƙara dawowa ta ce "yawwa Ummy kuɗinki dana ɗau zan baki, har ma zan ƙara miki 2millions su zama 5 sai kuje kuyo siyayyar ko? Amma yanzu dare zai yi muku ku bari saida safe idan ta kammala ayyukan gidan...."
ta ƙarasa maganar tana kallon Baiwar ALLAH sannan taja ƙofa ta rufe tayi tafiyarta,

Baiwar ALLAH da sauri ta nufi yanda Ummy take cike da farin ciki tace "gashi na gaya miki komai a hankali ake bin abu, Kinga kuwa kinyi nasara akanta ta sanadiyar fahimtar juna yanzu kuma naga tayi sanyi sosai...."

Ummy ta ce "uhmmm! Sai naga tayi wata guda bata wuce yawonta ba tukun na yadda da nadamar Mommy, a yanzu dai jikinta yayi sanyi akan batun nan amma indai akanki ne mommy bazata ja ki ajiki ba, ai mai hali da wuya ya canza amma ina roƙon ALLAH duk rashin mutuncinda zatayi da wulaƙanci ya tsaya a iya haka banda yawon zina, domin shine babban illar dake damu na a raina, zan temaka mata INSHA ALLAHU....."

Baiwar ALLAH ta ce "Allah sarki!
Allah yasa ta chanza har abada sannan Allah ya kawo mata ɗauki ya bata sauƙi....."
Ummy ce ta amsa mata da Ameen!
A yayinda ƙwayar idon Baiwar ALLAH suka sauƙa akan wani photo dake cikin akwatin Ummy dake buɗe bata zuge ba,
Ummy jin Baiwar ALLAH tayi shuru ne yasa ta waiwayo tana kallonta, itama idonta takai kan photon da take kalla, murmushi Ummy tayi sannan ta kai hannu kan photon ta ɗauka tana kallo,
Idonta akan photon ta ce "wannan shine......"
Bata ƙarasa maganar ba taji Baiwar ALLAH tayi hanzarin cewa "RAZHDEEN...."
ta ƙira sunan a yayin da zuciyarta ke bugun uku² gumi ne yake keto mata a duk ilahirin jikinta, wani irin yawu ta haɗiya still idonta akan photon da Ummy take riƙe da shi,

Murmushi Ummy ta kuma yi sannan ta ce "yanayinsa yayi zubi da sunansa, jarumin maza Kenam kallo ɗaya mace take masa ta razana, daga kallon photonsa gaba ɗaya kin fita hayyacinki shin ina da kin ganshi a zahiri?..."
ta juyo tana kallon Baiwar ALLAH ta kuma cewa "yadai? shin kina jin wani abu akansa?..."

Dasauri Baiwar ALLAH ta girgiza kai tareda faɗin "ko kaɗan wallahi, wannan ba mutum bane, kyansa yayi yawa sannan ga ƙirar jiki kamar basamude sannan ga sumar gashi har gadon baya kamar mace, ina! Ina!! Ina!!! Sam bana yinsa...."

Zaro ido Ummy tayi ta ce "Uncle Deen ne ba mutum baaa?, gashi yana sanye da kayan Sojansa gwanin burgewa....."
ta jinjina kai sannan ta ɗauko wani photo ta ce "wannan pah?...."
sakin fuska Baiwar ALLAH tayi tare da sauƙe nannauyar ajiyar zuciya sannan ta ce "wannan shine Roshan koh?...."

Ummy murmushi tayi tace "zubinsa yayi kama da sunansa Sarkin murmushi kenam...."

Baiwar ALLAH ta ce "yanzu ma gashi da kyakykyawar murmushinsa, dimple a lotse ga farin glass akan darara eyes ɗinsa gwanin burgewa wannan shine jarumi nah....."

Murmushi Ummy ta kuma yi tare da ajiye photunan acikin akwatinta ta ce "saima kin ganshi anan zaki zauce ganin kyakykyawar murmushinsa dake ƙayatar da kyakykyawan fuskarsa....."

BAIWAR ALLAH ta ƙagu da taga wannan kyakykyawan mutumi mai kyakykyawan zuciya wato Roshan,
a hankali ta furta "wow that's awesome, ma sha ALLAH 🥰....."






🇾 🇦 🇷  ➪ 🇦 🇲 🇦 🇳 🇦 

Sai da tayi wata guda a wannan yankin bata motsa ko ina ba, ga jita a waran saidai ta kaɗa jitarta ta kwanta a ƙasin wajen mai laushin gaske har bacci ya ɗauke ta, da zaran ta farka kuma zata tarar da ƙayatattun girke-girke masu ɗaukar ido, kullum da kalar abincin da ake kawo mata ga nama baje-baje haka zata zauna ta take cikinta tam tasha lemuka kala-kala, har zuwa yanzu babu mutum ko ɗaya wanda ta gani, kayan sakawa kuwa sai dai taga an chanza mata kaya Kuma kullum acikin ƙamshi take,
yanzu ma kamar yadda ta saba tana zaune da wata ƙaramar jita a hannunta tanata kaɗawa sauti mai daɗin gaske yana tashi, tana cikin wannan halin taga wani ƙaramin kifi ya fito bakin ruwa ya kasa komawa sai mutsil-mutsil yake, a hankali ta miƙe tsaye tana riƙe da jitarta a hannu ta nufi bakin ruwan wanda tinda aka kawota nan bata taɓa zuwa wajen ruwan ba balle tayi ƙoƙarin shiga sakamakon ganin kalar ruwan mai launin green ne sai ruwan yake bata tsoro,
a wannan lokacin tazo dab da ruwan da niyar temakawa kifi tasa hannu ta ɗauki kifin a hankali ta zura hannunta acikin ruwan ta maida kifin ciki, wanin irin sanyi taji ruwan yayi mai ratsa jiki, jin daɗin ruwan yasa ta zura ƙafafunta ciki ta zauna a bakin ruwan tana murmushi, ta ɗauki jitar ta fara kaɗawa a hankali, gani tayi ƙafafunta sun fara komawa kalar ruwan wato green, yana bin duk ilahirin jikinta nan danan fatar jikinta ya koma launin green har fuskarta,
Daga wannan lokacin bata tsinci kanta ba sai a bakin titin ƙwalta tana kwance ga jitarta a gefe tana riƙe dashi amma saidai ba'a cikin hayyacinta take ba,
Bata tashi farfaɗowa ba sai tsakiyar dare sakamakon ruwan sama da aketa zabgawa domin ruwan ne ya farfaɗo da ita, tashinta ta fara waige-waige ko zataga wani a gefenta amma babu kowa ga yanda ruwan sama yake dukanta, ta koma asalin launin jikinta daman wannan ruwan shine zai kai mutum ainahin yanda yake da zarar ka shiga wannan ruwan, a yanzu dai Ƴar Amana ta tsira daga zaman can ta dawo Nigeria yanda take, yanzu kuma zata fara neman mafita akanta tinda a halin yanzu ba'a hannun kowa take ba, tana free.....



Bayan Watanni Uku

(Three months later)



Wasu Manyan Jirage ne suka sauƙa a airport guda biyu,
Ɗaya jirgin Australia (U.S)
Ɗaya kuma jirgin ƙasar Egypt ne,
Sai jerukan motoci guda ɗari manyan baƙaƙen motoci masu taya ta baya guda hamsin sai motoci masu kakin Soja suma sunada taya ta baya guda hamsin,
Ga manya-manyan security masu manyan bindigu, security masu baƙaƙen kaya sune motocinsu baƙaƙe sai kuma motoci masu kakin Soja su kuma sojoji ne aciki,

Wanda yake jirgin ƙasar Egypt ne ya fara fitowa,
Innalillahi wa inna ilaihi raju'un 😳😳
wani kyakykyawan gabjejen saurayi ne fari tass yana sanye da fararen kaya suit ajikinsa, fuskar nan yana ɗauke da kyakykyawar murmushi, hannunsa ya miƙawa na gefensa wanda yake escort nashi ya miƙa masa wani ɗan siririn farin glass saida yasa farin handkerchief sannan ya goge ya ɗora glass ɗin akan dara-daran idanuwansa farare masu ɗaukar ido, haka yake bin security wajen da kallo da ko ina still da wannan murmushi akan fuskarsa, ga wasu ma'aikanta waɗanda suke jan akwatinansa zuwa motocin da aka tanadar musu,
Wani ne daga cikin security sa masu baƙaƙen kaya yazo gabansa yana faɗin "your welcome Doctor, we should go......"

Hannu ya ɗaga masa ba tare da yace komai ba, idonsa akan jirgin Australia yana jiran fitowar twins ɗinsa,

kafin ya ɗage eyes ɗinsa sai ga wani sangamin mutumi ya sauƙo daga nashi jirgin,
Innahu min Sulaimana wa Innahu Bismillahi Rahmani Rahiim,
Alla ta'àlu alayya wa'àtuni muslimiinn........

RAZHDEEN yanda kasan ba jinsin mutane ba tsabar kyau da ƙirar sura mai kyau ga sumar gashi mai ɗaukar ido sai sheƙi yake tsabar baƙi shi kuwa kamar jini zai fito a jikinsa, Sojan hutu kenam,
Duk farin Roshan da kyansa bai kamo ƙafar Razhdeen ba duk da shima Roshan ɗin Duniya ne,
Fitowar Razhdeen tsayawa yayi yana lumshe Golding eyes ɗinsa, yana sanye da farar t-shirt a jikinsa ga rigar ta kama jikinsa sosai sai ƙirar ƙarfin jikinsa kake gani yana bayyanowa, wandon jikinsa kuma kakin Sojan U.S ne, takalminsa mai sawu ciki ne na sojoji shima mai kakin Soja, sumar gashinsa yasha gyara sosai zuwa sajen fuskarsa ba ƙaramin kyakykyawan mutum bane Razhdeen sai dai fuskar nan ba Annuri ko kaɗan,
A hankali yake taka ƙasi kamar mai tambayar ƙasa nufan gurin Roshan yayi,
Shima Roshan da murmushi a fuskarsa ya nufi yanda Razhdeen yake, suna haɗuwa suka rungumi junansu sosai kowa yana kewan ɗan uwansa, daga bisani suka rabe jikinsu Roshan kamar zai tashi sama tsabar farin cikin ganin ɗan uwansa twins ɗinsa tsawon shekara guda ba'a haɗu da juna ba,
Cikin nuna farin ciki Roshan ya ce
"I missed you my Man...."

Shima Razhdeen duk da ba dariya yake yi ba sannan ba murmushi yake ba amma fuskarsa a sake yake alamun nuna farin ciki shima ya ce
"I missed you too my twins...."

suka sake rungumar juna a karo na biyu daga bisani suka rabe jikinsu suka jeru suna taku cikin ƙasaita da nuna mulki, duk da tsayin Razhdeen amma da kaɗan yafi Roshan tsayi domin shima Roshan gabjejen mutum ne ba laifi amma saidai Razhdeen yafi Roshan faɗin jiki da faɗaɗɗan ƙirji sosai....

Duk wanda ya gansu sun jerun nan suna taku sai ya yabesu domin ba ƙaramin burge mutanen wajen sukayi ba,
Suna isa dab da wata kyakykyawar mota wanda sabo ne yau aka ɓarota saboda twins, a gaggauce Security yayi saurin buɗe musu murfin motar duk suka zauna a back seat iya su biyu sai wanda zai yi driving nasu,
Sauran yawan motocin kuma duk ƴan rakiya ne,
Motarsu ce ta fara yin gaba sai sauran motocin suka biyo bayansu a jere cikin slow ake bin motocin ba hayaniya ko jiniya,
wannan taryar da akayi musu ko president iyakaci, duk yanda suka wuce sai an tsaya ganin motocin da yawansu kuma gasu a jere suke tafiya, sauran motocin kan hanya ne suka fara kakkauce musu,

RAZHDEEN ganin suna kutsawa cikin gari yasa shi cewa "YOU...."
security mai driving ne ya dakatar da tuƙin yana sauraron Razhdeen,
kamar bazaiyi magana ba murya ciki-ciki wanda saika kasa kunne kafin ka jiyo shi kuma magana ɗaya yake yi baya maimaitawa ya ce "bana son wuce wa ta cikin gari, mu zagaya ta bayan gari...."

Security ya ce "okay Sir...."

ya karya kwana suka wuce ta wata hanya wanda zai zagaya dasu bayan gari,

Roshan ne yayi murmushi yana jinjinawa Twins ɗinsa tareda maganar zuci
"My Man Kenam har yanzu kana nan da wannan halin nakan...."

Sauran motocin ne suma suka bi bayansu,
tafiya suke sosai domin ba ƙaramin ƙarawa kansu nisa sukayi ba, inda ace ta cikin gari suka bi da yanzu sun isa gida,
kaɗan ya hana su fita cikin gari su zagaya kafin su isa gida,
Razhdeen yayi saurin dakatar da security tare da faɗin "wait...."

dakatar da tuƙin akayi suma motocin bayan tsayawa sukayi,
Roshan ne ya juyo yana kallon Razhdeen cike da mamaki ya ce "My Man! ya zaka dakatar damu acikin jeji?...."

Razhdeen ƙwayar idonsa ya wurga cikin jejin yana bin jejin da kallo sakamakon jin sautin jita yana tashi kaɗan-kaɗan, irin sautin da yake ji acikin mafarkinsa,
Juyowa yayi yana kallon Roshan cikin sassanyar murya ya ce "bakaji wani irin sauti mai daɗin gaske yana tashi ba?....."

Girgiza kai Roshan yayi tare da faɗin "Nop i didn't hear any sound, na dai ji kukan tsuntsaye, please my man let us go home ina tsoron waran nan ......"

Razhdeen buɗe murfin motar yayi tare da furta "Uhmm! har yanzu baka zama jarumi ba, zanje na dubo aina sautin nan yake tashi...."

har zai kutsa cikin jejin Roshan yayi saurin riƙo shi yana girgiza masa kai ya ce "Please my man kazo mu wuce gida, babu abinda zaka gani acikin jejin nan sai abin cutarwa...."

Suma sauran Sojojin ganin twins sun fito yasa duk suka fiffito da bindigu a hannayensu,
Sai a yanzu kowa ya fara jin wannan sautin yana tashi da ƙarfin gaske, sautin ne yake dukan dodon kunnen Razhdeen, lumshe eyes ɗinsa yayi yana sauraron sautin mai kashe jiki exactly irin sautin da yake ji acikin mafarkinsa ne,
Razhdeen yana shirin fizge hannunsa daga riƙon da Roshan yayi mishi zai shiga cikin jejin, Roshan ya kuma riƙe shi sosai yana faɗin
"My Man Nima inajin sautin amma idan na barka ka shiga baka san me zaka tarar ba, wata ƙil Aljana ce take ruɗanka da wannan sautin, please kazo mu tafi don't worry komai zai zo maka cikin sauƙi....."

Daƙer Roshan ya samu ya shawo kan Razhdeen da lallami suka shige motar, suma sauran Sojojin shigewa sukayi suka fara tafiya,
Still idon Razhdeen a saitin yanda yake jiyo sautin yana tashi, daga bisani ya kwantar da kansa akan kujerar motar tare da lumshe kyakykyawan idanuwansa, sai bayan sun shiga cikin gari tukun ya daina jin sautin jitar.....
Basu yi tafiya mai nisa ba suka sha kwanar da zai sadasu da ƙayataccen unguwarsu mai ɗaukar ido, suna shiga layin unguwar tin daga farkon layin har ƙarshenta sojoji ne a jere ko wanne yana riƙe da bindigarsa....


Gidan kuwa an tsara shi yayi mungun kyau ta ko ina filawowi ne a gidan,
Idan aka zo kan babban falon gidan Wayyo Aljannar Duniya Kenam, musamman ƴan aiki aka ɗauko daga ƙasar waje domin su gyara gidan, da masu abinci girke-girke kala-kala kusan guda 15 ko wanne da kalar abinci acikin flask duk saboda dawowar twins,

A yaran gidan kuwa duk babu mai wargi da walwala sai Ummy, itace mai nuna farin cikin dawowarsu,
Hajiya Kilishi tana can upstairs cikin bedroom ɗinta domin tinda su Razhdeen suka dawo shikenam babu farin ciki daman ba ƙaunarsu take ba,

Minal da ƴanmata twins Pinky da Ruky suna zazzaune akan kujerun falo sunci kwalliya sosai amma sai dai ba walwala, bawai basa farin cikin dawowarsu bane don saboda daga yanzu zasu Fara takura, bazasu samu ƴancin kansu kamar baya ba,

Ummy kuma sai zarya take acikin falon tana jiran shugowarsu,
jin an buɗe last gate wanda daga shi sai babban falo yasa Ummy razana cike da zumuɗi ta kwallawa Baiwar ALLAH ƙira wacce itama a kitchen take tana fargaban ganin twins domin jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba, sai wani ɗarɗar take tana jin tsoro, jin ƙiran Ummy yasa ta razana tana sauƙe numfashi sama-sama ta ce "na shiga uku sun shugo...."

Ummy ta ce "ganan Yaya Roshan kiyi saurin kawo Apple ɗin, farkon dawowa farkon cin Apple kar ki bari su wuce....."

Baiwar ALLAH jin an ambaci Yaya Roshan yasa tayi saurin ɗaukar tray mai ɗauke da kayan fruits tayi cikin falo da sauri,
Domin Hajia Kilishi ce ta sanarwa Baiwar ALLAH cewar suna shugowa ta kai musu kayan fruits da juice duk da bata sonsu amma hakan bai hanata sa a kyautata musu ba....

Baiwar ALLAH zuwa tayi ta tsaya a bakin ƙofa wanda suna shugowa zasu ɗauka, amma kuma a tsorace take sosai har jikinta ɓari yake,
Ummy tana daga bayanta tana tsaye tanaso taga yanda Baiwar ALLAH zatayi idan tayi ido huɗu dasu,

Su Minal kuma sunyi shuru duk sun sha ruwan jikinsu, kowa da abinda yake tunani a ransa na haɗuwa da Uncle Deen domin shine macijin mai sara....

Buɗe ƙofar falo akayi a yayin da security masu escorting suka tsatstsaya a bakin ƙofar falon shi kuwa gogan ya shige,

Baiwar ALLAH ta tafo da sauri akan zata miƙawa Yaya Roshan ya ɗauki fruits acikin glass tray kawai idanuwanta suka sauƙa akan kyakykyawan fuskar Uncle Deen ga sumar gashi sun sauƙo har kafaɗa, sajen nan ya kwanto har zuwa gemu da waran gashin baki duk sun kwanta yayi luf sai

Please Login or Register in order to submit comment