Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gwara ciwo na yaita tashi akan na yaron nan wallahi...."

Doctor ya ce "it's okay! But meye musabbabin faruwar hakan? Sannan tin jiya da aka kawo Roshan banga ɗayan ɗan nakan ba wato Razhdeen shin kodai ya koma U.S ne?....."

Abbah kamar zai haɗiyi ransa tsabar takaici ya ce "bani da Ɗa mai sunan Razhdeen, Roshan kawai nake Da...."

Doctor cike da mamaki yake bin Abbah da kallo,
Hajia Kilishi itama dasauri ta ɗago tana kallonsa,
Itama Minal dake zaune buɗe baki tayi tana kallon Abbah a yayinda take riƙe da phone ɗinta,
Pinky da Rukky kuwa kallon juna suka shiga yi ko wacce fuskarta a hargutse,
Ummy cike da mamaki ta ce "Abbahhh......"

Ɗaga mata hannu Abbah yayi tareda faɗin "kada ko waccen ku ta kuskura tayi mun magana indai akan Razhdeen ne, baya daga cikin jerukan ƴaƴana, na fidda shi ba Ni ba shi daga yau....."

Doctor cike da mamaki ya ce "Subhanallahi amma me yayi zafi haka Chief?...."

Abbah ya ce "haka kawai na yanke hukuncin nan domin bazan taɓa haifan yaron da zai saka mun ciwon kai ba ko ya bijirewa maganata ba impossible,
haka kuma duk wacce zata bijirewa maganata toh wallahi zan cire hannuna ne akanta sai dai ku nemi wani uban, koda zan zauna babu yaro ko ɗaya ......"
ya ƙarashi maganar yana nuna su da yatsa,
Hajia Kilishi ganin ya sako ƴaƴanta aciki yasa ranta ya ɓaci sosai ta ce "amma ko wani irin laifi suka yi maka bai kamata kayi musu wannan hukuncin ba, faɗan da kake yi ma babu daɗin ji....."

Abbah ya ce "dole abi dokata indai anason zaman lafiya kuma kema harda ke ban ware kowa ba, zan iya baki takardar sallamarki indai baki canza ɗabi'unki ba....."

Zaro ido tayi tana kallonsa cike da mamaki acikin ranta kuwa cewa tayi "anya kuwa ba shaye-shaye Chief yayi ba?...."

Abbah kallon Doctor ya yi sannan ya ce "yaushe za'a iya sallamar mu?...."

Doctor ya ce "gobe da safe insha Allahu domin a daren yau akwai allurar da zamu yi mishi, kuma gaskiya Yakamata indai anason kwanciyar hankalinsa toh a faranta masa, abinda yake nema a bashi insha Allahu za'a dace......"

Abbah ya ce "toh shikenam ba damuwa...."

Daga nan Doctor yayi ficewarsa,
Itama Hajia Kilishi tashi tayi tana kallon yaranta ɗaya bayan ɗaya ta ce "ku tashi mu koma gida...."

Minal tashi tayi ta nufi bakin ƙofa zata fice duk sauran ma tashi sukayi banda Ummy dake zaune ta ce "Ni zan zauna da Yaya Roshan....."

Abbah ya ce "ki tashi ki bisu zan cigaba da zama dashi....."

Ummy jiki ba ƙwari haka ta tashi tana jan ƙafa daƙer ga hawaye yanda yake go slow akan fuskarta,
Abbah ganin halin da Ummy take ciki yasa ya ƙira sunanta cikin sassanyar murya ya ce "uwar masu gida....."
waiwayowa tayi tana kallonsa cikin damuwa,
ya kuma cewa "dawo ki zauna...."
sakin fuskarta tayi tareda ɗan sau murmushi ta koma ta zauna,
Hajia Kilishi fuska a haɗe ta fice,
Sojoji biyar ne sukayi escort ɗinsu zuwa gida,
Motar ɗaya nasu, ɗaya kuma sauran sojoji ne aciki daman motar biyu ne a yayinda aka bar wasu sojojin a hospital.....

suna isa gida babu wanda ya iya shiga kitchen domin girka abinda zasu ci,
Ɗaya daga cikin sojoji suka aika yaje restaurant ya siyo musu abinci,

A ranar su Abbah a hospital suka kuma kwana,
yau kwanansu uku a hospital....


Razhdeen bayan ya idar da sallar Asuba, miƙewa yayi ya nufi falo yanda yake kwana akan doguwar kujera sakamakon wani irin sarawa da kansa ke yi,
buɗe frig yayi ya ɗauki maganin ciwon kai ya ɓare tareda since murfin gorar faro ya kafa a baki saida ya shanye ruwan nan tass yana sauƙe numfashi sama-sama,
ya wurgar da gorar gefe sannan ya nufi 3 seater ya kwanta ba tareda ya cire jallabiyar jikinsa ba, yana riƙe da goshinsa nan danan wani irin dogon bacci yayi awun gaba da shi,

can ya fara jin ƙinƙishin kuka, yana ji amma bai kula ba a tunaninsa mafarki yake, ganin da gaske yake jin kukan yasa ya fara yunƙurin buɗe eyes ɗinsa waɗanda bacci basu gama isarsu ba,
a hankali yakai idonsa saitin yanda yake jin kukan, eyes ɗinsa ne suka sauƙa akan kyakkyawar fuskar Baiwar Allah sai sharar kuka take tana durƙushe a gabansa,
A hanzarce ya tashi zaune idonsa akanta daƙer ya iya motsa lips ɗinsa ya ce "lafiya kuwa....."

Cikin kuka take faɗin "yau satina guda a cikin ɗakinka ka ƙi barina na fita, ya kake so nayi da rayuwata? Ni idan baka son zamana a gidan nan ne zan tafi nabar gidan, amma zaman kaɗaici ya isheni haka, bansan me kake nufi da hakan ba....."

Nan ta ƙara fashewa da matsanancin kuka mai cin rai,
Lumshe eyes ɗinsa yayi sosai ya juma bai buɗe su ba daga bisani ya buɗe a hankali domin ba ƙaramin ciwo kansa ke yi ba,
Ganin bazai iya juran jin kukanta ba ga ciwon kai yasa shi cewa "ok tashi na fitar dake don't worry....."

dasauri ta miƙe tsaye cikin nuna farin ciki, shima tashi yayi yasa hannunsa a aljihu ya ciro key ɗin ɗakin, har sun nufi bakin ƙofa suka ji an fara bugan ƙofa da ƙarfin gaske,
Muryar Abbah suka ji yana faɗin
"Razhdeen kayi ƙoƙarin buɗe ƙofar nan tin kafin nasa a ɓalle ƙofar kuma wallahi baza kaji daɗin abinda zanyi maka ba,
kafin nan da mintuna uku ka fito da yarinyar nan,
idan kuma nima so kake ka kashe Ni kamar yanda kayi sanadiyar mutuwar ɗan uwanka Roshan shikenam kayi ta zama da ita....."

Abbah ya ƙarasa maganar yana fashewa da kuka yabar wajen kai tsaye falo ya nufa.....

Razhdeen a kiɗime ya zaro da dara-daran idanuwansa waɗanda lokaci guda suka kaɗa launin ja, bai san lokacin da yayi baya ya doku akan kujerar falon ba,
wani irin gumi ne yake tsirto masa, sumar kansa gaba ɗaya ya harhargutse ya baje tsabar tashin hankali da ya shiga lokaci guda,

Baiwar Allah kuwa hannu tasa ta toshe bakinta sai faman zazzaro ido take nan danan hawaye har ya wanke mata fuska,
tanaso ta fitar da kukanta amma sai taji muryarta ya dishe gaba ɗaya, ƙoƙarin shiɗewa tayi taji ya riƙo hannunta da ƙarfi jikinsa har wani zaƙami yake ya jata suka nufi bakin ƙofar ɗakin, key yasa ya buɗe yana janta suka fice,
A hanzarce ya sauƙo downstairs tare da Baiwar Allah,
Ganin mutanen gidan yayi gaba ɗaya suna zazzaune ko wacce da hawaye akan fuskarta, idonsa yakai kan Aunty Yolash wacce ta samu zuwa daga Bauchi jin rasuwar Roshan domin tin da asuba ta kamo hanya, shi kuwa Roshan ya rasu ne tin cikin dare misalin ƙarfe 2,
yanzu haka ƙarfe 9 ne na safe, ana jiran isowar su Sarkin Ƙasar Jidder da iyalansa zuwa ƙafe 10 ko 11 ayi jana'izar sa domin mutuwarsa har ta bazu ko ina, iya Razhdeen ne bai sani ba shida yake cikin ɗaki,

Bayan ya gama kallesu gaba ɗaya sannan idanuwansa suka sauƙa akan Gawar Roshan dake kan makara an gama lulluɓe shi da likkafani jana'izarsa kawai ake jira ayi....

Razhdeen ganin Roshan yasa yayi baya zai faɗi tsabar wani irin hajijiyar da ya ɗebe shi, dasauri yasa hannu ya riƙe jikin bango yana fitar da numfashi sama-sama,

Baiwar Allah da gudu ta ratsa ta gefen Razhdeen ta nufi wajen da su Ummy suke a zaune a ƙasin carpet,
Ummy rungumar Baiwar Allah tayi tana kuka tareda faɗin
"Yaya Roshan ya rasu, Aunty Baiwar Allah Yaya Roshan ɗin mu ya tafi ya bar mu, kin ganshi nan kwance ki ce ya tashi dan Allah kar ya tafi ya bar mu......."
ta ƙarasa tareda fashewa da matsanancin kuka, itama baiwar Allah kukan take tana rarrashinta,

Abbah ne ya sauƙo daga upstairs yana riƙe da Bindiga a hannunsa gadan-gadan ya nufi tsakiyar falon ya tsaya yana fuskantar Razhdeen ya ɗago da bindigar ya saita shi yana kuka......

Razhdeen tsayawa yayi yana kallon Abbah shima hawaye yaƙi tsayuwa masa,

Dasauri Aunty Yolash ta miƙe tsaye tareda faɗin "Yaya me kake shirin aikatawa?...."

Duk sauran Yaran suma miƙewa suka yi suna zazzaro ido waje hatta Hajia Kilishi itama ta tsorita da ganin abinda Abbah yake shirin yi..

Abbah yana kuka
Ya ce "Razhdeen ka cuceni wallahi, kayi sanadiyar mutuwar ɗan uwanka mafi soyuwa acikin zuciyata, ka bijirewa maganata, ka toshe kunnuwanka a yayin da nake rarrashinka game da lallaminka akan ka buɗe ƙofar ɗakin ka, kasa yarinya a ciki ka kulle baka tunanin halin da zata shiga ga Ɗan uwanka har ya kwanta a gadon asibiti sakamakon ciwon zuciyarsa har takai ga ya rasa rayuwarsa, alhalin kasan ciwonsa zai iya tashi a kowani lokuta,
yanzu shikenam kayi farin ciki ko?
kaji daɗi Roshan ya mutu yabar maka duniya, daman so kake ka kashe shi ta hanyar ƙuntata kuma gashi ya mutu, falillahil hamdu nasan kayi farin ciki a yayinda Ni kuma baƙin ciki nima zai kashe Ni....."

Girgiza Kai Razhdeen yake yana kuka sam baya jin daɗin kalaman Abbah,

Abbah ya cigaba da cewa "bazan juri ganinka a doron duniya ba, kaima zaka je wajen da ɗan uwanka ya tafi, na ƙwammace gwara na bisineku ku biyu nasan zanji sanyi a raina,
Banaso na cigaba da kallonka a matsayin maƙiyi nah gwara kawai ka mutu kaima...."

ya ƙarasa maganar tareda kunna kunamar bindigar
Ummy ce ta zo yanda Abbah yake ta durƙusa tareda kama ƙafarsa tana kuka tana roƙonsa akan kar yayi kisan kai,
"Abbah dan Allah kayi haƙuri kar ka raba mu da Uncle Deen, mun rasa Yaya Roshan bamaso mu rasa Uncle Deen ka temaka mana ...."

Suma sauran durƙusawa sukayi suna roƙan Abbah akan ya ƙyale shi,

Razhdeen yana kuka ya ce "Daddy nah indai mutuwata ce zatasa kayi farin ciki dan Allah ka harbe Ni a saitin Nan....."
ya ƙarasa maganar yana nuna saitin zuciyarsa da hannunsa,
ya cigaba da cewa "ciwon zuciya ne ya kashe mun twins ɗina asanadiya ta don haka nima ka harbe Ni a saitin zuciyata domin ɗaukan fansar ɗan uwana......"

Shima fashewa yayi da kuka yana kallon Abbah,
Abbah shima kukan yake,
Aunty Yolash ce ta nufo gurin da Abbah yake zata fizge bindigar kar tsautsayi tasa ya harbe shi, a tunaninta barazana Abbah yake masa,
ai kuwa kafin ta ƙarasa Abbah ya yi saurin harba bindigar, bullet bai sauƙa a ko ina ba sai a saitin ƙirjin Uncle Deen......

A duk yaran gidan Babu wacce batayi ihu ba, Ummy kam ƙafewa tayi a wajen idonta akan Uncle Deen wanda yakai ƙasi,
Aunty Yolash itama zaro ido tayi tareda ƙamewa a wajen baki a buɗe,
Hajia Kilishi itama hannayenta tasa ta toshe bakinta da su tareda zaro ido waje,

Baiwar Allah kam batasa lokacin da ta yanki jiki ta faɗi sumammiya ba.....

Durƙusawa Abbah yayi tareda fashewa da matsanancin kuka ga bindiga a hannunsa,

Sojoji ne suka shugo falo da gudun gaske jin harbin bindiga......


A Razane Razhdeen ya farfaɗo daga doguwar baccin da ya ɗauke shi ya tashi zaune yana haki da ƙarfi-ƙarfi gaba ɗaya ya kiɗime game da haɗa gumi yayi sharkafff,
Addu'o'i ya fara jerowa yana waige-waige yaga ashe MAFARKI YAYI......

Idonsa yakai kan Baiwar Allah wacce take zaune a dinning table da farantin Cake a gabanta domin ta tashi da matsanancin yunwa,
tayi wankanta ta sanya doguwar baƙar jallabiyan sa, tayi kyau sosai sai haskenta ya ƙara bayyanowa ta ɗaure sumar kanta da rawani mai ɗigon ɓaki da fari.....

Itama juyowa tayi tana kallonsa ganin halinda yake ciki, itama tasan yayi mummunan mafarki ne ganin a yanda ya tashi a firgice...

Uncle Deen numfashi yake fitarwa sama-sama yakai idonsa kan Agogon ɗakin yaga yanzu ƙarfe 10 na safe ne,
ba shiri ya tashi ya nufi yanda Baiwar Allah take a zaune ya kamo hannunta ya ɗagota tareda jan ta suka nufi bakin ƙofa,
Ita dai kallonsa take ta gagara cewa komai,
Key yasa ya buɗe suka fice yana jan hannunta...

Suna sauƙa downstairs suka tarar da Abbah yana zaune dab da Roshan yana rarrashinsa akan ya kwantar da hankalinsa,
Ga sauran Yaran gidan suma suna zazzaune akan kujeru,
Roshan na ganinsu yayi saurin miƙewa tsaye idonsa akan su,
Shima Abbah ɗagowa yayi yana kallon Razhdeen cikin ɓacin rai........





WAYYO YAU DAI NASAN NA HARHARZUƘA ZUCIYOYIN MASU KARATU 😁😁😁😁
MUSAMMAN AUNTY KHADIJA KAR ZUCIYARKI TA BUGA MAFARKI NE,
YARONKI ROSHAN YANA NAN .......



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 45 to 46



꧁꧂



"Daddy......"

Dakata Razhdeen,
Abbah ne yayi maganar tareda ɗaga masa hannu ya miƙe tsaye yana fuskantar sa ya ce "babu abinda zaka gaya mun Razhdeen, ka ƙuntata mun matuƙa....."

Razhdeen sunkuyar da kansa yayi ƙasi a yayin da ita kuma Baiwar Allah ta ratsa ta gefensa ta ƙarasa sauƙowa falon, Roshan ne ya nufi inda take kafin ta ƙaraso yasa hannu ya rungumota yana sauƙar da ajiyar zuciya alamun farin ciki,

Jin hayaniyar Abbah yasa gaba ɗaya ƴan matan gidan suka sassauƙo falo,
Ita kuma matar gidan a saman upstairs ta tsaya tana kallonsu,

Abbah ya cigaba da cewa "tinda har bazaka ji maganata ba to zama dakai bashi da wani amfani,
Saboda daga yanzu ka kama hanya ka fita mun a gidana, kaje duk yanda zaka je amma babu ruwa na, duk abinda ya sameka babu hannuna,
Bazan tsine maka ba amma kaje na dena ganinka a gaba na balle na ƙunshi baƙin cikin ka......"

Dasauri Razhdeen ya ɗago yana kallon Abbah ga hawaye yanda yake gangaro masa, lips ɗinsa na kakkarwa daƙer ya iya cewa "Please Dad......"

Abbah ne ya ƙara katse shi da cewa "am not your Dad, please stay away from me,
zansa a duba mun yarinyar idan har wani abu ya sameta toh wallahi zanyi maganinka domin saina shigarka kotu an yanke maka hukunci....."

Abbah ya juyo yana kallon Baiwar ALLAH ya ce "Daughter gaya mun shin ya miki wani abu? kamar dai fyaɗe...."

Dasauri Baiwar ALLAH take girgiza Kai alamar a'a, tana zubda ƙwallah sam bata ji daɗin hukuncin abinda Abbah ya yanke wa Uncle Deen ba,

Abbah ya ce "Kinga kar kiji tsoronsa ina tare dake ki gaya mun gaskiya, kar kimun ƙarya....."

Baiwar Allah fashewa tayi da kuka tana faɗin "wallahi Abbah babu abinda ya mun....."

Abbah ya ce "okay shikenam..."
ya juyo yana kallon Razhdeen ya ce "Allah ya temake ka, now leave my house....."
ya ƙarasa maganar yana nuna masa bakin ƙofa,
Roshan ne ya matso dab da Abbah kamar zaiyi kuka ya ce "please Daddy kar ka kore shi, wannan hukuncin yayi tsauri, dan Allah ka ƙyale shi we need him...."

Abbah fuska a murtuƙe ya ce Da Roshan "babu ruwanka...."

Abbah ya kuma cewa "Razhdeen in har baka bar mun gida kafin na ƙirga ɗaya zuwa biyar ba wallahi zan tsine maka Albarka yanzun nan....."

Zaro ido Roshan yayi yana kallon Abbah cike da mamaki, shi tinda yake bai taɓa ganin ɓacin rai a fuskar Abbah irin ta yau ba,
murya na kakkarwa Roshan ya ce "Daddy......"
Abbah yayi saurin katse shi da cewa "I said shut up......"

Shi kuwa Razhdeen tin tinin har ya haura upstairs ya nufi part ɗinsa kafin ɗan wasu mintuna har ya dawo hannunsa riƙe da troley, eyes ɗinsa har sunyi jawur, haka ya sauƙo yayi hanyar waje,

Roshan ne ya tsayar dashi da cewa

Please Login or Register in order to submit comment