Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ƙaramin baki wanda yaci red sosai kamar wanda ya shafa jan baki, fuska kuwa ba Annuri...

Baiwar ALLAH ganinsa yasa ta ƙafe a wajen idonta kuwa akansa duk da ba'a cikin hayyacinta take ba,
Wani irin kallo ya watsa mata ganin yanda ta fita hayyacinta lokaci guda
Ko sauraron ta bai tsaya yi ba haka yabi yana taka matakalar Beninsu yanda zai kai shi part ɗinsa domin a gajiye yake yana buƙatar hutu baya son hayaniya....

Su Minal duk miƙewa sukayi tsaye suna mishi your welcome amma ko kulasu bai tsaya yi ba da haka ya wuce abinsa....

Ita kuwa Baiwar ALLAH baya tayi zata faɗi Ummy tayi saurin tarota, har ta sume a wajen, daƙer Ummy ta jata ta shige da ita bedroom ɗin ta wato ɗakin Baiwar ALLAH shine a ƙasin falo...


Shima Roshan yana can yana ta gaggaisawa da mutane, Abbansu ma ya dawo shima yana waran taron manya-manyan mutane waɗanda sukazo ganin twins wato Razhdeen da Roshan, shidai Razhdeen ƙin tsayawa yayi domin baya son yawan hayaniya....

Ƴar Amana kuwa tana cikin jejin da su Razhdeen suka wuce domin ita take kaɗa jitarta.....



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 25 to 26



꧁꧂


Abba ne ya fara shigo wa cikin falon yana ɗauke da murmushi alamun yana cikin farin ciki sosai, ya zauna a ɗaya daga cikin jerukan kujerun falon, kallo ɗaya yayi wa ƴan matan gidan yasan akwai matsala domin ko wacce babu Annuri a fuskarta especially Minal babbar cikinsu sai Pinky da Rukky dake zaune a two seater,
yasau fuskarsa tareda faɗin "Meya sameku na ganku a haka ana cikin farin cikin dawowan ƴan uwanku?...."

Minal ce ta fashe da kuka hannunta akan fuskar irin kukan sakalcin nan,
Abbah ya ce "A'ahhhh sirikata ya haka kuma, gaya mun meya faru?...."

a cikin kukan take faɗin "yanzu fisabilillah Abbah shin ya dace haka?...."

Abbah ya ce "ehen go ahead inajinki...."
ta cigaba da cewa "tsawon shekaru uku yanzu bamu gana da Uncle Deen da Yaya Roshan ba, munata zumuɗin ganinsu amma Uncle Deen saboda bai damu da mu ba muna mishi ur welcome but he didn't answer us why Abbah? wani irin laifi mukayi masa ne wanda bazai iya yafe mana ba, tin muna yara bamu tashi munga Uncle Deen cikin fara'a ba, kodai baya son kasancewar mu acikin gidan nan ne? Abbah gaya mun Ni saina bar masa gidan...."
ta ƙarasa maganar tana kuka...

Abbah gaba ɗaya jikinsa ne yayi sanyi 🥺 nan take yaja wata doguwar ajiyar zuciya yana kallon yaran ɗaya bayan ɗaya ya ce "kuyi haƙuri bawai manufarsa haka bane, daman can Razhdeen haka halinsa yake tin yana yaro, kunga kuwa tin kafin a Auro mahaifiyarku kenam balle yayi tunanin za'a samo ku, ga misali ɗaya shin haka Roshan yake? kunga dai twins ne amma ko wanne da kalar halayyarsa, sauƙar Razhdeen daga cikin mota bai tsaya kula kowa ba haka ya wushe al'umma waɗanda suka taru saboda su yayi tafiyarsa, ko Ni nam Razhdeen bai tsaya saurarona ba balle ku, so saboda haka kuna masa uzuri inda sabo ai kun saba da halin Razhdeen saidai ku bada labarinsa a wasu, kuyi haƙuri Sirikata babu yanda zan yi da Razhdeen sai dai Addu'a......"

Suna cikin wannan halin sai ga Roshan ya turo ƙofa da sallama a bakinsa yana ɗauke da Ƴar Tiny a kafaɗarsa,
Pinky da Rukky ne suka tashi da sauri suka nufi yanda yake, shima da murmushi a saman fuskarta ya rungumosu jikinsa yana faɗin "wow my beautiful twins, ƴanmata an girma...."

Dariya suka yi suna faɗin "your welcome Yaya Roshan, we really missed you...."

Shima dariya yayi tare da faɗin "me too my beautiful twins...."

Minal tana daga zauna akan kujera tace "your welcome My Bros...."
Kallonta yayi tare da sauƙar da ƴar Tiny dake hannunsa yace "ke ɗin bazaki taso kimun oyoyo bane?..."

Murmushi tayi sannan ta tashi tana zuwa yanda yake ta rungume shi tana dariya, shima dariya yake ya ce "well done Amaryar Marshall Mohandas...."

Dasauri ta kifar da kanta saman ƙirjinsa a hankali take faɗin "please Yaya Roshan kar kasa Abbah ya fusata..."

Shima raɗa yayi mata a kunne tare da faɗin "Kenam har yanzu ana kan chaƙwakiyar ne?..."
ta ce "uhmmm Yaya Roshan Kenam kaima kasan inba Marshall ba bazan Auri kowa ba, sai dai a cigaba da drama...."
Duk acikin raɗa suke maganar ba tare da kowa yaji abinda suke faɗi ba,
ɗagowa tayi suna dariya,
Abbah ya juyo yana kallonsu ya ce "Auu munafurcin mai ake yi ne nake jin ƙusƙus......"

Ƴar Tiny ce ta nufi gurin Abbah da gudu tana faɗin "Abbah bayi na gaya maka Aunty Minal ce ta ce bajata Auyi kowa ba inba Yaya Matall Moandas ba...."
ta ƙarasa maganar cikin tsatstsamar bakinta...

A fusace Abbah ya kalli Minal cikin ɓacin rai! kafin kace me Minal tayi gudu ta haura upstairs kai tsaye ɗakinta ta nufa domin tasan Abbah yanzu zai fara tadawa kowa hankali akan batun nan.....

Hajiya Kilishi ce itama ta sauƙo tana sanye da wata danƙareriyar less ɗinta mai bala'in tsada, tasha makeup ba ƙaramin kyau tayi ba, tayi fari fat da ita duk da tana ɗan haɗawa da bleaching,
ta nemi kujera ɗaya itama ta zauna dab da Abbah idonta akan Roshan ta ce "ur welcome Son..."

Shima yana ɗauke da murmushi ya ce "thank you Hajia, fatan na sameku lafiya..."
kamar baza tayi magana ba can ta ce "we are all fine..."
ya ce "Ok thank God...."

Abbah ya ce "Amm Roshan kaje ka rage kayan jikinka kayi wanka sai kuzo ga kayan abincin da aka tanadar muku, gaba ɗaya zamu haɗu a dinning ne inka fito sai kayi wa Razhdeen magana...."

ya ce "okay Dad..."

Har ya fara haura saman stairs ɗinsu ya dawo yana baza eyes,
Abbah ya ce "lafiya kuwa?...."

yana ɗauke da ƙayataccen murmushi ya ce "where is my love?...."

Abbah murmushi yayi domin duk gidan babu wanda bai san ita kaɗai yake ƙira da haka ba, shima Abbah cewa yayi "Nima sauran kaɗan na tambayeta ka rigani..." ya kalli Pinky ya kuma cewa "wai ina Uwar masu gida ne? ban ganta ba tinda na shugu...."

Pinky ta ce "uhmm tana ɗakin Baiwar ALLAH..."
Abbah ya ce "ha'a toh su fito falo mana, ita uwar masu gida tasan lover ɗinta ya dawo shine bazata zo yi masa oyoyo ba..."

Rukky tayi saurin cewa "Abbah Baiwar ALLAH ganin Uncle Deen yasa ta sume shine Ummy ta tafi kaita ɗakinta...."

Abbah kallon Hajia yayi yaga ko Annuri babu a fuskar nan ya ce "ikon ALLAH, ita kuma ganin Razhdeen ya sata suma, ba shakka indai Razhdeen ne kaɗan Kenam daga aikinsa....."

Roshan ganin bai fahimci maganganunsu ba yasa ya haura upstairs tare da faɗin "saina sauƙo..."

Bayan haurawarsa da mintuna talatin saiga Ummy ta fito tana tura lips cikin sakalci take jumping da sawayenta tace "Ni har yanzu My love bai shugo bane?....".
Pinky tana zaune idonta akan Ummy tana harararta ta ce "ke dillah bama son hauka...."

Ummy turo baki tayi ta ce "Ni bada ke nake ba kiyi mun shuru...."

Rukky ta ce "tselan uwa sakalcin banza dan ma bake bace Autar yau da an shiga uku ...."

Ummy tana nuna Rukky da yatsa tace "Kee nutsu ki kama kanki ai ba'a kanku nake ba...."

Abbah ya katse su da cewa "Kinga uwar masu gida jeki masoyin nakin yana can ɗakinsa,.."
ya kalli su Pinky ya ce "ku kuma babu ruwanku da ita..."
Rukky tace "ai wallahi Abbah kai kake goya mata baya shiyasa ta raina mutane..."

Abbah ya ce "ku kuka jawa kanku raini dai, yanzu da bakuyi mata shishshigi ba ai baza tayi ƙoƙarin gaya muku magana ba...."

Pinky ta kalli Rukky sannan ta ce "zo mu koma ɗaki..."
suka wuce suna turo baki, sai ya rage daga Abbah sai Hajia sai kuma ƴar Tiny wacce itama tashinta kenam wai zataje gurin Uncle Deen.

Abbah ganin har zuwa yanzu Hajia bata saki fuskarta ba yasa ya matsa kusa da ita ya riƙo hannayenta yana murzasu a hankali idonsa akan fuskarta
ya ce "ya akayi ne matar bindiga?..."

Kallonsa tayi sannan ta ƙara kawar da fuska gefe ta ce "babu komai..."
Yace "no kina cikin damuwa ne yakamata ki sanar mun koh? tinda na dawo yau sati guda amma babu walwala kodai nayi miki laifi ne?...."

Girgiza kai kawai tayi alamar a'a tace "bana jin daɗin jikina ne..."
"Meya same ki?"
yayi maganar cikin sassanyar murya,
kamar zata yi kuka ta ce "marata ciwo....."

murmushi yayi domin yasan damuwarta ya kamo hannunta ya ɗago da ita yana faɗin "sorry my dear muje daga ciki ko kafin yaran su fiffito dinning...."

tashi tayi itama tana murmushi suka haura upstairs yanda part ɗinsu yake ....



A Ɓangaren Doctor Roshan yana kwance saman katafaren gadonsa wanda yasha gyara ɗakin sai fitar da ƙamshin turare yake, yana lumshe da ido kamar meyin bacci tsabar zunzurutun gajiya,

Ummy ce ta turo ƙofa cike da zumuɗin ganin masoyinta kuma ɗan uwanta, shugowa falon tayi taga wayam babu kowa sai jerin tsararrun kujeru na alhurma ga plasman a manne a jikin bango sai showing indian Film ake, gefe guda kuma wani ɗan ƙaramin frig ne gwanin burgewa, sai kuma ƙaramin dinning table wanda iya mutum biyu kawai yake ɗauka, falon ya tsaru sosai,
Murmushi Ummy tayi a fili tace "yanzu haka yana cikin bedroom ɗinsa..."
tana zuwa dab da bakin ƙofar bedroom tasa hannu tana knocking a hankali gudun kar ta kutsa masa kai tsaye bata san a wani hali yake ba,

Yana kwance yaji ana knocking ido a lumshe ya furta "Yes come in...."

turo ƙofar tayi ta shugo tana ganinsa a kwance tayi gudu ta nufi yanda yake tayi tsalle ta faɗa masa jikinsa tana dariya....

shima dariyan yake ya ce "kai kai Kaiii my love wannan ai saiki karyani irin wannan tsalle haka...."
Ta ɗago tare da faɗin "oyoyo my love wallahi nayi kewarka sosai, amma kai baka damu dani ba tinda har ka shugo baka nemeni ba......"
ta ƙarasa maganar cikin shagwaɓa

jan kuncinta yayi yace "Ni na isa naƙi damuwa da uwar masu gida wane niii, kina raina sosai kamar yanda nake ranki tinda naga kullum saikin ƙira masoyinki Roshan a waya...."

Dariya tayi ta ce "yawwa Yaya Roshan ina tsaraba taa..."
Saida ya tashi zaune yana fuskantar ta ya ce "tsaraba kam sunanan lodi-lodi sai kin zaɓa kin darje kafin sauran su ɗauki nasu...."

ta ce "wow shiyasa nake ji dakai Yaya Roshan ɗina saboda kaima kana ji dani ...."

yana kallonta fuska ɗauke da murmushi
ya ce "ya za'ayi bazan damu dake ba? kepah kinada darajoji da yawa a gurina...."

zaro ido Ummy tayi tare da bugan ƙirjinsa tace "kaiiii Yaya Roshan toh lissafo mun...."

Saida ya gyara zamansa tukun ya fara cewa "na farko ke mai sunan Hajiyar mu ce marigayiya wato mahaifiyar Abban mu wacce tin muna jarirai take riƙe damu, ita ta sakaltar damu, bata son ko cinyaka ta cije mu, duk abinda muke so zatayi ƙoƙarin yi mana, shiyasa muke matuƙar ji da kakar mu har Allah ya karɓi rayuwarta,
Na biyu kuma again sunan my first lover gareki, Allah sarki Maryama ta mutumiyar kirki ga yawan fara'a, kyakykyawar hallita lokaci guda nayi rashinta, da yanzu na tabbata munada ƴaƴa amma mutuwa tayi mun yankan ƙauna, a waɗanda nafiso a raina daga mahaifiyata wacce ta rasu sanadiyar haihuwar mu sai kuma Kakar mu wacce tayi rainon mu har rai yayi halinsa sai kuma Abar ƙaunata Maryama wacce tayi hatsarin mota tabar duniya....."

Ummy Turi baki tayi cikin shagwaɓa ta ce "Kenam Ni banda Ni acikin sahun masoyanka? daman nuna soyayyarka bai je zuciya baaa...."

Yaya Roshan ya ce "ki fahimce Ni My love! inada waɗanda nake so da yawa, waɗannan wanda na lissafo su sune sukafi soyuwa a cikin zuciyata, in hakane ai ban lissafo da Abbah ba kuma Kinga ai bazance bana sonsa ba...."

Ummy fuska a turɓune ta ce "toh wacece ta huɗu?..." tayi tambayar a shagwaɓe,
ya sauƙe ajiyar zuciya sannan ya ce
"My man! wato twins ɗina Razhdeen sai ta biyar kuma itace Uwar masu gida wato my love...." ya ƙarasa yana jan kuncinta ya cigaba da cewa
"sai na shiga kuma Abbana, sai kuma sauran masoyana waɗanda suke sona nima nake son su....."

Ummy tana jinjina kai ta ce "wato Ni ce ma ta biyar uhmmm hakane...."
tintsirewa yayi da dariya yana jan lips ɗinta domin ba ƙaramin dariya ta bashi ba,
Saida suka gama shan hirarsu sosai kafin ya tashi yana faɗin "uhmmm my love idan na biyeki sai mu kwana muna zance, yanzu dai bari na shiga wanka, naji Abba ya ce gaba ɗaya zamu haɗu a dinning kar su fara jiran mu...."

Itama Ummy tashi tayi ta ce "TOH my love idan ka kammala muna jiranka a ƙasi...."
Ɗaga mata hannu yayi tare da shigewa toilet.....

Bayan fitar Ummy kai tsaye part ɗin Uncle Deen ta nufa tana zuwa ta tsaya a bakin ƙofa tana knocking a hankali domin tasan halinsa muddin ta shiga bada izininsa ba saiya korota duk da baya yawan zama a falonsa sai dai idan wani aiki zai yi a computer yakan zo falo ya zauna akan sopa computer kuma tana kan ƙaramin glass table na tsakiyar falon,
tana cikin knocking taji muryar ƴar Tiny tana faɗin "yeshhh coming..."

Ummy acikin ranta tace "shegen iyeyi har wani yesh coming..."
shugowa tayi da sallama a bakinta ta tarar da Uncle Deen yana zaune sai faman danna computer yake ita kuma ƴar Tiny tana gefensa da wani ƙaton Biscuit mai madara a hannunta, motsa baki kawai Uncle Deen yayi ba tare da anji mai ya ce ba, amma alamu ya nuna cewar amsa sallamar yayi,
zuwa tayi ta zauna gefen ƴar Tiny tace "Uncle Deen your welcome...."
a taƙaice ya ce "Ok" ba tare da ya ɗago ba,
Ɗaga kafaɗa Ummy tayi alamar bata damu ba, domin kaɗan Kenam daga halayen Uncle Deen, inka san halin mutum saika sha maganin zama da shi....

Ummy kallon ƴar Tiny tayi sannan ta ce "Tiny ɗan sammun biscuit ɗin mana, Kinga babu kalar shi a Nigeria na daɗe banci ba...."

Ƴar Tiny hararar Ummy tayi sannan ta ce "wayyayi tayyayi balan bayal ba, ki tambali Unkui Deen mana...."

Ummy cikin ɓacin rai ta ce "shegiya mai tsatstsamar baki....." bata ƙarasa maganar ba taga Uncle Deen ya jefo mata wani irin kallo har sai da ta razana, ga yanayin juyowar nashin yasa sumar kansa wantsilowa zuwa fuskarsa sai dara-daran idanuwa kake gani ta cikin sumar gashin,
Haka ƙirjinta yake bugun uku uku sai yanzu ta tuna ashe ba'a zagin Ƴar Tiny a gabansa saboda takwarar mahaifiyarsu ce wato FATIMA BINTU, sunan mahaifiyarsu Razhdeen da Roshan, shine aka sanyawa ƴar Tiny sunanta,
Amma Razhdeen da Roshan basa ƙiranta da ƴar Tiny saidai Mama...



Please Login or Register in order to submit comment