Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ummy tashi tayi suƙu-suƙu zatayi waje yayi saurin dakatar da ita tare da nuna mata wata ƴar jaka wanda cikinsa zallar biscuit ɗin ne, jiki ba ƙwari haka taje tasa hannu ta ɗauka tare da yin godiya,
idonsa akan computer ya ce "tsarabar Mamana ne saboda haka a ita zakiyiwa godiya...."

Ummy ta kalli ƴar Tiny tace "Nagode Tiny..."

turo baki ƴar Tiny tayi sannan ta ce "a shaye zaki yi mun gojiyar? ki durkusha kashi kimun gojiyar....."

wani irin yawu na baƙin ciki Ummy ta haɗiya cike da jin haushin ƴar Tiny ta durƙusa da gwiwowinta ta ce "Nagode sosai Ƴar Tiny...."
ta miƙe idonta akan Uncle Deen wanda yasa hannu yana ture sumar kansa zuwa baya eyes ɗinsa akan computer ko kallonsu bai yi ba,

Ummy taja ƙafa zata fice taji Uncle Deen yayi magana,
Dasauri ta waiwayo tana kallonsa ta ce "na'am!..."
Domin sam bata ji me ya ce ba, amma taji kamar yayi mata magana, murya ne kamar ba'a halitto shi ba bayason fitar da Muryar,
Shi kuwa a ƙa'idarsa magana sau ɗaya yake yi baya maimaitawa,
Jin yayi mata shuru ya cigaba da uzurinsa yasa ta kalli ƴar Tiny ko zata temaka ta maimaita mata abinda ya ce,

Ƴar Tiny tana tura biscuit a ɗan ƙaramin bakinta ta ce "waiii Keee kuymiya ce? aka ce kije ki kiyawo An uwanki shu jo Nam...."

Ɗaga kai Ummy tayi tare da faɗin "tam shikenam...."

Dasauri tabar ɗakin domin ba ƙaramin ƙuluwa tayi da ƴar Tiny ba,
A cikin ranta kuwa cewa tayi "wannan ƴar Tiny saina ci ubanki wallahi, ƴar Banza kawai tsatstsamar bakinki ma ya isheki...."

Da wannan takaicin ta sauƙa falo tana sauƙa kuwa ta tarar da su gaba ɗaya suna zazzaune, tazo ta tsaya a kansu tare da faɗin
"TOH Guys Big bros yana ƙira...."

Minal ta ce "ke dallah in zakiyi magana ki buɗe baki mu sa'anninki ne..."

Ummy ta ce "a'ahhh zakuyi bayani ne to Uncle Deen ne ya ce duk a ƙira masa ku...."

Pinky Sarkin tsoro a razane ta miƙe tsaye tareda dafa ƙirji ta ce
"Mun shiga uku me mukayi kuma daga dawowarsa?...."

Rukky ta ce "ke kina magana a hankali Kinsan yanada kunne wallahi...."
ta ƙarasa maganar tana riƙe da hannun Pinky wanda duk ɗinsu jikinsu ne yake ɓari kamar masu jin sanyi,

Minal miƙewa tayi itama tana kallon Ummy ta ce "lafiya kuwa? kodai wani abu ne?...."
Itama a tsorace take sai dai bata nuna tsoron natan a fili ba...

Ummy ta ce "Uhmmm kuma dai kunsan ƙiran Uncle Deen ba lafiya bane, sannan kuna ɓatawa kanku lokaci ne, in har bakuje da wuri ba akwai matsala ga takaicin ƴar Tiny da zaku shaƙo...."

Minal ta ce "kunga kuzo muje koma menene tinda ba kashe mu za'ayi ba ai da sauƙi..."

Har sunyi gaba suka juyo sukaga Ummy ta nemi guri ta zauna Minal ta kuma cewa "haka kuma idan ƴar aike bata koma ba akwai matsala...."

Ummy tsuka taja tare da miƙe wa tabi bayansu itama duk suka haura upstairs can ɓangaren Uncle Deen......


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 27 to 28



꧁꧂


Jiki a sanyaye suka tura ƙofar ɗakin Uncle Deen da sallama a bakinsu, Minal ce ta gaba su kuma Pinky da Rukky suna daga baya² jiki sai ɓari yake,
Ummy ce tayi ƙarfin halin cewa "Uncle Deen ga sunan ..."

yana zaune a yanda yake ko motsawa baiyi ba still eyes ɗinsa akan computer sai faman danne-danne yake ko sauraronsu baiyi ba,

Sai da suka ɗau tsawon mintuna 15 suna tsaye bai kulasu ba, sai ƴar Tiny ce ta ce "Ankui Deen gashunan sunata shaye tin ɗaju....."

Daiden lokacin ya ɗago da kansa tare da rufe computer sa yana binsu ɗaya bayan ɗaya da kallo, ya miƙe tare da faɗin "kuyi mun kneel down a wajen tinda baku iya gaisuwa ba, today I will teach you how to respect someone...."

duk zaro ido sukayi a tsorace, Minal ce ta ce "Uncle Deen shugowarka munyi maka magana baka kula mu ba...."
kafin ta ƙarasa ya juyo a fusace yana mata wani irin kallo na ɓacin rai, ai tinin duk suka durƙusa kamar zasuyi kuka, Ummy itama ƙafarta ne yake kakkarwa ta ɗan sunkuya ita bata durƙusa ba sannan kuma ba'a miƙe take ba tana son jin abinda zai ce dangane da ita tinda tazo ta gaishe shi,
har zai shige bedroom ɗinsa ya sake juyowa yana kallon Ummy ya ce "you leave my room...."

Da hanzari Ummy ta fice a ranta take faɗin "Better...."

sannan ya nuna Pinky da Rukky ya ce "two of you go and wear your trousers...."

a tare suka haɗa baki waran cewa "akwai wandina a jikin mu...."
suka ƙarasa murya na kakkarwa,
ya ce "Ok stand your legs up...."

Pinky da Rukky kallon juna suka shiga yi domin sun san abinda yake nufi,
kafin su ankara suka ji ya darara musu tsawa tare da faɗin "ko baza kuyi bane?...."

Dasauri suka ɗaga ƙafafuwansu saman jikin bango, hannayensu a dafe a ƙasi suna kallon ƙasin carpet, ga hawaye shaɓe-shaɓe....

ya kalli Minal wacce take durƙushe itama tana kallon gefe guda, tsananin takaici ne a ranta, tana tunanin wai har yaushe zata yi girman da za'a daina hukuntata....
tana cikin wannan tunanin taji ya ce "You rest your hands up..."

Hakan kuwa tayi ta ɗaga hannayenta sama gwiwowinta a kife ƙasin carpet,
yana gamawa dasu yayi shigewarsa ciki,
Bayan mintuna talatin Abbah da Mommy ne suka sauƙo downstairs,
Abbah ganin falon wayam yasa shi cewa "ha'a ina mutanen gidan? ina ce ai sun hallaru a dinning...."

Mommy tana yatsina fuska ta ce "Uhmmm!..."

iya abinda ta iya furtawa Kenam saboda tsananin izzah...

duk zama sukayi a dinning saiga Ummy ta fito daga room ɗin Baiwar ALLAH,
Abbah ya ce "Uwar masu gida ina kuka shiga ne haka, ina Dota ta farfaɗo ne?...."

Ummy fuska a sake tana murmushi ta ce "Abbah ta samu farfaɗowa yanzu haka na barta tana sallah ne...."

Daiden lokacin da Yaya Roshan ya sauƙo down yana sanye da farar jallabiya, shima nufan dinning yayi yana faɗin "gud Afternoon my parents...."

Abbah shima amsa masa yayi da murmushi akan fuskarsa ya kuma cewa "sai yanzu duk kuka samu damar fitowa Kenam..."

Roshan yana sosa ƙeya ya ce "Abbah bacci ne ya ɗauke Ni shiyasa...."

Abbah ya ce "sai yanzu da yunwa ta tasheka kenam koh?...."

Murmushi yayi sannan yakai idonsa kan Ummy wacce take tsaye, ya ce "yadai Ƴar gidan Soja bakya gajiya da tsayuwa ne?...."

Abbah ya ce "ina sauran ne suzo mana..."

Ummy ta ce "duk suna ɗakin Uncle Deen suna karɓan tsarabar hukunci..."

Hajia Kilishi ta ɗago tana kallon Ummy cikin ɓacin rai ta ce "whattt? daga dawowarsa har ya fara azabtar mun da yara? wani irin abu ne haka, gaskiya bazai yuba ƴaƴana ba jakuna bane suma sunada ƴancin kansu acikin gidan nan tinda suma gidan ubansu ne ba agolanci aka kawo su ba....."

Abbah sam baiji daɗin kalamanta ba amma saidai bai nuna hakan ba sai cewa yake "wait mana ki saurareni! ba maganar agolanci bane shin Razhdeen bashida iko idan yaran sunyi laifi ya hukunta su? meyasa kike nuna banbanci a tsakanin yaran nan ne kam? gani nake Razhdeen da Roshan da ƴaƴanki duk ɗaya suke babu ruwanki da shiga shirginsu, haka akeson uwa ta kasance...."

Mommy ta ce "au memakon ka ɗau hukunci akai shine zaka goya masa baya? daman na daɗe da fahimtar bason yarana kake ba kamar yanda ka nuna kafi son mahaifiyarsu Razhdeen akaina ...."

ta ƙarasa maganar tare da kawar da kanta gefe tana zubarda ƙwallah!!!!

Abbah ganin ya fara fusata ne ya ce "Kinga ki tsayar da wannan kishin nakin a haka, ita wancan ta rigada ta bar mana duniyan nan da yake cike da ƙalƙal banza da wofi, sannan kafin na fara tarayya dake da ita na fara, in badan mutuwa ba da tayi mun yankan ƙauna aina zan ganki balle na Auro ki, Ni banida ra'ayin zama da mata biyu, kuma nayi niyar mutuwar matata BINTU cewar bazan ƙara Aure ba haka zan zauna, amma babu yanda na iya haka aka tilastani akan Aurenki bawai bana sonki ba, amma Inaso kiyi adalci shin Ni na ganki nace Inaso? babu wannan! haɗamu akayi ba tare da mun san juna ba har akayi Auren lokacin ma bana Nigeria...
Saboda haka ki dena haɗa kanki da Fatima domin ko a halayya ne tayi miki nisa...."

Roshan yana zaune ganin abun yana shirin wuce gona da iri yasa shi cewa "Please Abbah ya isa haka, babu daɗi irin haka..."
ya kalli Ummy wacce itama tana tsaye tana jinsu duk da bataji daɗin kalaman Abbah ba amma tafi jin haushin Mommynta domin ita ta fara..
Roshan ya kalli Ummy ya ce "My love jeki ƙira yayun nakin mana...."

Ummy ta dafa ƙirji tare da faɗin "waaaa! cab wallahi Yaya Roshan daƙer na tsiratar da kaina daga ɗakin Uncle Deen...."

Murmushi yayi sannan yace "okay bari naje na dubo su...."
kai tsaye upstairs ya haura sannan ya miƙi part ɗin Razhdeen,
yana zuwa yasa hannu ya tura ƙofar ɗakin, ganin yanda su twins suke ƙafafu a sama jikinsu sai ɓari yake duk da sanyin A.C dake ɗakin amma gumi suke tsabar azaba gaba ɗaya sunyi lukus, idanuwansu har sunyi jawur tsabar kuka,
hannu yasa ya tallafosu yana faɗin "ku tattaso maza..."
haka suka tashi suna sakin numfashi, itama Minal tashi tayi tana kuka domin abun da cin rai, 25years take amma dizgata ake agaban ƙannenta...

Roshan ya ce "kuyi haƙuri ku daina kukan nan..."
Shi baima lura da Ƴar Tiny ba sai yanzu da ya ji maganar ta tana cewa "Yaya Yoshan wayace ka ceceshu, ajiyaishu fa aka bani, Ankui Deen ya ce duk wacce ta taci na gaya maca...."
ta ƙarasa maganar tana turo baki..

Roshan ya ce "laifin mai sukayi?...."

Ƴar Tiny ta ce "meyaca bacu jo shun gaiceci ba...."

Roshan ya ce "TOH ki ce masa yayi haƙuri a wannan lokacin sai sun ƙara tukun...."

Saiga Uncle Deen yana sanye da Black jallabiya ba ƙaramin kyau yayi ba sai farinsa ya ƙara fitowa ya fito yana faɗin "babu yanda zasuje su cigaba da karɓar hukuncinsu...."

Roshan yaje har gabansa yana faɗin "haba my Man yau fa ka dawo, ka bari sai bayan kwana biyu saika fara bayyanar da dabi'unka mana ..."

Uncle Deen yamutsa fuska yayi sannan ya ce "ɗabi'una ai a bayyane suke a ko ina, saboda haka ka bar mun su anam...."

Roshan ya ce "Abbah yana can yana jiran mu gaba ɗaya, kayi haƙuri Please...."

Saida yayi kamar bazaiyi magana ba can ya ce "Ok...."

yana faɗan haka da gudun gaske Pinky da Rukky suka bar ɗakin sai kuma Minal tabi bayansu ita da Roshan a tare suka sauƙa,

Duk zama sukayi, Abbah ya ce "ina yake shi ɗin?...."

Roshan ya ce "yana sauƙowa...."

Abbah baiji daɗin ganin yanda idanuwansu suka canza launin ja ba saboda kuka, amma sai dai yaja bakinsa yayi shuru ko tambayarsu baiyi ba cewar me sukayi ba,
Amma yasan Razhdeen baya hukunci haka kawai sai da dalili,
a ransa ya ce "yanzu haka basuje sun gaishe shi bane, kuma kamata yayi duk subi ɗakunansu suje su musu sannu da dawowa, a tarbiyance ba wai a gaisa sama-sama ba, kuma daman yaran sunada irin wannan ɗabi'ar na rashin gaisuwa...."

suna zaune Saida suka jira Razhdeen ya fito hannunsa riƙe dana ƴar Tiny suka ƙaraso dinning,
Abbah dariya yayi yana kallon ƴar Tiny ya ce "wato ke Auta dake ake shiri Kenam, ahhh lallai kin ciri tuta agurin Ankui Deen ɗinki 😅...."

turo baki tayi ta ce "babu yuwanka da Ni Abbah, muyi faca...."

zaro ido Abbah yayi waje ya ce "yau ɗin dani akayi faɗa? saboda kina tare da da Uncle Deen koh? ai zai tafi zakizo ki sameni daramm...."

Kawar da kai gefe tayi tana harare-harare......

Uncle Deen ganin ana zaune ga kuloli ba wanda ya tashi balle ya zuzzuba yana hararar kulolin tare da shan kanwa ya ce "Meye amfanin zaman mu anam?...."

Itama ƴar Tiny ta ari bakinsa da cewa "wai Ni ina wan can yalinyal ne tajo ta juba mana abincin mana, Ni wayyayi lunwa nace ji....."

Ummy tana harararta ta ce "ke dallah rufe mana baki sa'arki ce ita?...."

Ƴar Tiny zaro ido tayi tana nuna Ummy da ɗan ƙaramin yatsarta ta ce "ceee wayyayi tayyayi cema ciciyaye Ni...."

wani irin dogon tsuka Uncle Deen yaja yana ƙoƙarin tashi,
Roshan yayi saurin riƙo hannunsa tare da faɗin "wait My Man yanzu za'a zuzzuba...."
ya kuma cewa "Ni wacece mai zuba abincin ne kam gashi Man ɗina ya gaggauta...." ya ƙarasa maganar yana binsu da kallo.

Ummy ce ta ce "Aunty Baiwar ALLAH ce kuma tana fitowa yanzu...."

Banda Abbah da Ummy duk cikinsu babu wanda baiji haushin Baiwar ALLAH ba jinkirin fitowar da tayi ga kowa najin yunwa....

Itama kuma Baiwar ALLAH tana ciki tsananin tsoro ne da fargaba ya hanata fitowa, sai tazo zata fito saita koma da gudu, yanzu ne na ƙarshe Saida tayi addu'a kafin ta jefo ƙafarta na dama waje tukun ta fara taku a hankali jiki duk ba ƙwari, kamar marar lafiya haka take ƙanƙame jikinta kanta a sunkuye sam bata ƙaunar ganin Uncle Deen....

da haka ta ƙaraso wajen da sallama a bakinta,
Uncle Deen ko ɗagowa baiyi ba kai a sunkuye yana pressing phone ɗinsa,
Roshan ne ya ɗago tare da amsa sallamar data yi, yayi ido huɗu da ita, gabansa ne yayi wani irin yanke wa kamar wanda yaga abun tsoro, a hankali ya furta "ƙalu innalillahi wa inna ilaihi raju'un......" ba tare da kowa yaji shi ba,
ya cigaba da cewa "godiya ta tabbata ga sarkin hallitun duniya, ALLAH na gode maka daka halitto wannan kyakykyawar halitta...."

Duk waɗannan maganganun acikin ransa yake yinsa,
yana cikin wannan sambatun yaji Hajia Kilishi ta darara mata tsawa tare da faɗin "Meye amfanin ki acikin gidan nan? Kenam mu zamu zo muna jiranki saboda isarki da gadara? wannan shine na ƙarshe na gaya miki...."

Baiwar Allah kai a sunkuye ta ce "kiyi haƙuri Hajia bazan ƙara ba INSHA ALLAHU...."

Abbah ya ce "kinga Dota zo ki zuzzuba abinci kema ki zauna ki ci koh...."

A hankali ta furta "tam Abbah nagode...."

kafin ta fara zuba abincin Saida taje gefen Razhdeen ta durƙusa ƙasi ta gaishe shi,
hannu kawai ya ɗaga mata ba tare da ya furta komai ba,
Sannan taje gefen Roshan wanda idonsa akanta ya gagara ɗagewa sai ji yayi ta gaishe shi,
Amsawa yayi cikin kulawa ya ce "Barkanki da fitowa Gimbiya...."



Please Login or Register in order to submit comment