Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take bi da gudun, gaba ɗaya ta shagaltu, bata tashi ankara ba saida taji an girbe mata ƙafa da ƙarfi wanda saida tayi sama kafin ta doku a ƙasin floor wanda duk unguwar a zagaye yake da floor babu ƙasa ko ɗaya,
Goshinta ne ya bugu da ƙasi bata san lokacin da ta sau ƙara mai ƙarfi ba,
lokaci guda tayi shuru saida ta ɗau kusan minti 30 kanta a kife kafin ta soma motsawa a hankali tsabar buguwar da tayi hatta jikinta saida yaji,
A hankali ta fara ɗago kanta ga goshi har ya fashe sai jinin da yake zuba, lumshe idonta ta fara yi saboda tsananin hasken da yake shirin kashe mata ido, ba hasken komai bane illa hasken unguwar da kuma layin gidan data biyo wanda layin gidan yake cike da manya-manyan security sojoji masu jajayen handkerchief a ɗaure saman goshinsu,

Baiwar ALLAH ganin sawun takalmin sangamemen soja a gabanta yasa ta fara bin ƙafar da kallo tana binsa da kallo har saida ta ɗage kanta sama sosai kafin ta iya ganin fuskar mutumin yana ɗaure da jan ƙyalle akan goshi sai huci yake, mai ƙirar samudawa jikinsa sai zaƙami yake yana sanye da kakin sojoji,
Ganin wannan soja yasa ta ƙara kifar da kanta alamar suma tayi...........



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 9 to 10





꧁꧂


a hankali take ƙoƙarin buɗe idonta daga doguwar sumar da ta tafi, jin tanata lilo ta kasa tsayuwa guri ɗaya yasa tayi hanzarin buɗe idonta a gaggauce domin taga a wani hali take, bata tsinci kanta ba sai a saman ƙarfen transformer ata Tsakiya an ɗaure mata ƙafafu kanta na kallon ƙasa sai lilo take kamar igiyar shanya, ganinta a haka yasa kanta ya fara juyewa saboda ganin ƙasa take kamar zata faɗo ga anyi sama da ita sosai nan danan ta fara jin hajijiya bata san lokacin data rausa uban ihu ba a kiɗime,

wani soja ne a gurin yana tsaye zaman gadinta a yayin da sauran sojojin suke can bakin aikinsu na tsaron layin gidan General, dake transformer ata bayan layin yake can akaje aka ɗaure Baiwar ALLAH....

ihu take bana wasa ba shi kuwa yana tsaye ko kulata baiyi ba, sai wayar hannunsa irin wanda sojoji suke aiki dashi ya kara a wajen bakinsa yana magana ta turanci cewar "wannan yarinyar pah ta tashi, ya za'ayi da ita?...."
amsa ɗaya aka bashi sannan ya katse ƙiran ya ɗaga kansa yana mata wani iri kallo da jajayen idanuwansa, shima kansa saida ya ɗaga kansa sosai kafin ya yake iya kallonta domin da igiya aka jata sama, zuwa yayi ya since igiyar da aka ɗaura a jikin transformer sai gata ta tafo zuuuuu tayo ƙasi, sauran kaɗan kanta ya doku da ƙasa sojan yayi saurin tarota sannan ya zaunar da ita domin ƙafafunta a ɗaure suke guri ɗaya, kwana tayi a saman transformer jikinta ba ƙaramin ciwo yake mata ba tare da hajijiya duk ta gama haɗa gumi tayi jirippp,

Gani tayi sojan ya durƙusa a gabanta ya ƙafe mata jajayen idanuwansa yana riƙe da ƙarfen shocking a hannunsa ganin shocking yasa ta zazzaro manya-manyan idanuwanta waje tana karkaɗa masa kayi tareda haɗiyar wata nannauyar yawu wanda ya tsaya mata a maƙogaro,
Shima ido ya zazzaro mata murya a dire yace "wacece ke?..."

Cike da firgici murya a shaƙe cikin ƙinƙina ta soma cewa "wallahi wallahi Ni ba kowa bace, bansan kaina ba...". kuka mai ƙarfi ne ya yanko mata,
A tsawace ya daka mata tsawa tare da faɗin "shut up! ur very stupid, I asking you who are you, and what are you planning?..."
tana maƙale da murya tace "dan ALLAH kuyi haƙuri ku barni in tafi wallahi ban san ko inaba bansan kowa ba?...."
bata ankara ba taji sauƙar zazzafar mari akan fuskarta har sai da lips ɗinta ya fashe, ga goshi a fashe yanda aka girbeta, buɗe baki tayi ta fara kuka ya ƙara ɗaukan hannu zai mareta tayi saurin yin shuru tareda ƙanƙame idanuwanta, cikin zafin nama irin na sojoji ya sauƙar da hannunsa ya fasa marinta ya miƙe tsaye yana faɗin "zakiyi bayani...."

haka ya tafi ya barta a wajen ƙafa a ɗaure tareda hannaye, tasha kuka sosai kamar ranta zai fita kamar yanda ta kwana a wajen haka tin safe take nan har ana ƙiran mangarib yanzu, yunwa da ƙishi ba ƙaramin azabtar da ita suke ba, sai a lokacin wani daga cikin sojojin ya waiwayo ta wannan kam yafi wancan zafin rai domin yana zuwa ya sameta harta gyangyaɗa tana shan baccin azaba, cike da mugunta ya jona mata shocking dake hannunsa a saitin ƙirjinta, tana bacci bata san lokacin da ta zabura ta rausa uwar ƙara har sai da sojan ya toshe kunnensa, daga nan ta nemi hankalinta ta rasa ta sume a gurin,

Su sunyi tunanin ko ƴar mafiya ce, ko kuma tazo da abun cutarwa domin ba kowa ne yake shugowa cikin unguwar nan ba sai masu arziƙi na gaske waɗanda suka sanu, hannu yasa ya fara bubbugata amma shuru ko motsi babu hakan yasa yaja uban tsuka yace "foolish girl, raguwar banza....." haka shima ya tashi yayi tafiyarsa, a waran Baiwar ALLAH ta kwana a sume saida gari ya kuma wayewa kafin Allah yasa ta farfaɗo da matsanancin ciwon kai, ga sanyin duniya ga yanda ƙwari suke hawa kanta wasu na cizonta, a kwana biyun nan har ta fita hayyacinta tayi baƙi, idanuwa sun shanshanye duk ta rame,

tana cikin wannan yanayi na ƙunci idonta na kallon gefe guda kamar mai tunanin wani abu sai hawayen dake tsiyaya kamar pampo, bata san lokacin da wani daga cikin sojoji yazo ya tsuguna a gabanta ba ya ƙura mata ido, gyaran murya yayi mata ganin har zuwa yanzu bata san da mutum a gurin ba, a zabure ta waigo ta kalle shi, ganin soja ne yasa ta zaro ido waje tana shirin fashewa da kuka domin a yanzu bata ƙaunar ganin ko wani soja, ta tsani ganin kakin sojoji balle su kansu,
Ganinsa yasa ta saddaƙar cewar shima da kalar muguntar da zaiyi mata,
kula ya ajiye mata a gabanta da pure water yana faɗin "sorry ba cutar dake Zanyi ba, abinci na kawo miki...."
yasa hannu ya buɗe kular abinci yana ƙoƙarin saka spoon zai bata a baki ganin hannayenta a ɗaure suke kuma ba'a bashi damar sinceta ba domin shima yaron su ne bashida wani iko akai,
Babu yanda ta iya haka take buɗe baki daƙer yana bata domin yunwar da take ji yana shirin fin ƙarfinta kwana biyu batasa komai a cikinta ba ga azabar da ake gana mata,
haka ta kammala cinye abincin tass ya bata ruwa tasha,
tashi yayi zai tafi domin ya gama aikinsa tayi saurin dakatar dashi tare da cewar "dan ALLAH yaushe za'a since Ni? na gaji sosai Inaso na nemawa kaina mafita, bansan komai ba, bansan kowa ba, dan ALLAH ka temaka mun, tinda har ka ciyar dani da hannunka nasan akwai imani a tattare dakai dan ALLAH......"
Dogon numfashi yaja sannan ya juyo ya kalleta cike da tausayawa ya dawo gabanta ya tsaya yace "kiyi haƙuri da zan iya temaka miki da zan temaka ko baki ce ba saboda nasan a halinda kike ciki, banida wani iko akai duk oganni nane amma kiyi haƙuri ki ɗan jira General ya dawo yau insha ALLAHU zai dawo daga ƙasar Egypt yaje wa Yaronsa Doctor Roshan visiting sannan yau yake Birthday jiya ya tafi amma yau yana kan hanyar dawowa, da zaran ya dawo za'a sanar masa halin da ake ciki, zai buƙaci ya ganki daga nan zai iya temaka miki domin mutum ne mai son mutane da temako amma sai idan kin sanar masa gaskiyar cewar ke wacece sannan daga ina kike, mai kika zo yi, waya turoki idan kika sanar masa gaskiya toh zai temaka miki, amma idan kika ɓoye masa gaskiya General yanada saurin kama mai laifi zakiyi bayani, saboda haka You better known what are you going to say...."

yana kaiwa nan yayi tafiyarsa....

wani abu ta haɗiya kamar wanda ta haɗiyi dutsi tsabar takaici, lokaci guda ta fashe da kuka mai cin rai tare da faɗin "Yaa ALLAH ka dube Ni da idon rahama, ya Allah ka kawo mun sauƙi acikin lamura na, Yaa ALLAH kasa na cinye wannan jarabawar da nake ciki, ina cikin mawuyancin hali amma nasan ƙaddara ta ce tazo mun a haka, ya Allah kada kasa na wuce a haka,
Yaa ALLAH ka fini sanin yanda ƴar uwata ƴar Amana take, Allah kada kasa ta kasance a irin halinda nake ciki domin ita ɗin bata san ciwon kanta ba har yanzu, Allah ka temake mu....."
haka take kuka tana kaiwa Allah kukanta,
tin daga safiya har zuwa yamma misalin ƙarfe 5 babu sojan da ya ƙara waiwayota sai yanzu, yana zuwa yasa hannu ya fincikota yasa ƙaramar wuƙa ya yanyanke mata igiyar da aka ɗaureta dashi, yana nan fuska ba Annuri wannan daga ganinsa babu wasa,
Baiwar ALLAH kai a sunkuye domin bata ƙaunar haɗa ido dashi domin ta gane shi shine wanda ya shona mata shocking, yana gamawa ya miƙar da ita sannan yaja ta akan su tafi, bata ankara ba tajita a ƙasi sakamakon kumbura da ƙafarta yayi bazata iya tafiya ba a halin yanzu, ƙafar ba ƙaramin ciwo yake mata ba ga hannu ya ɗangale babu halin miƙar dashi tsabar tsamin da yayi shima ya kumbura sosai, ganin haka yasa sojan bai jira wata-wata ba ya ɗagata ya ɗorata saman kafaɗarsa ganin zata ɓata masa lokaci....

Saida sukayi tafiya mai nisa kafin taga sun iso layin wani ƙanƙararren gida wanda kana shigowa layin ka daina taka ƙasa sai floor, ga wasu zankaɗa-zankaɗan sojoji kusan su ashirin ko wanne yana riƙe da ƙatuwar bindiga ga jajayen ƙyalle a ɗaure saman goshinsu idanuwansu jajaye babu alamar wasa a fuskarsu, tana saman kafaɗarsa amma tana ƙare ko ina da kallo amma bata bari ta haɗa ido da soja ko ɗaya ba, gani tayi an buɗe musu wani makeken gate wanda ya tsaru mai tsayin gaske, ginin gidan gaba ɗaya a zagaye yake da tiles, suna shiga ciki wasu sojoji ta ƙara gani su biyar sun ƙame guri ɗaya ko motsi babu, ga jerukan motoci kala-kala ko wanne da design ɗinsa da kuma kamfaninsa sun kai guda ashirin domin duk ƴan gidan babu wanda bashida mota duk ba'a barinsu suyi driving saidai security yakaisu duk inda zasu je, ga wasu irin flowowi na alhurma masu kyan gaske, a cikin motocin ne ya zaɓi guda ɗaya ya saka Baiwar ALLAH a seat ɗin baya sannan shima ya shiga, domin babu yanda zaka iya shiga gidan ba tare da mota ba, saida suka ƙarayin tafiya mai nisa kuma du wasu security suka ƙara buɗe musu wani gate na biyu, suna shiga taga wani makeken swimming pool a tsakiyar filin gidan wanda a tsakiyar ruwan wani abu kamar flower ne yake bada feshin ruwa sai ruwan yayi sama kafin ya zubo a cikin S-pool amma sai dai wannan swimming pool ɗin bana wanka bane just anyi shi ne don ado domin flowers ne a ciki, saida suka zagaya wannan S-pool tukun zaka iya bi ta ɓangaren dama sannan zaka iya zagayawa ta ɓangaren hagun domin a tsakiya yake, ta order side wani makeken filin ball ne wanda yake can nesa dasu, nan ma suka sake miƙar hanya,
ata gaba aka sake buɗe musu wani gate na uku kuma du, Baiwar ALLAH zaro ido waje tayi ganin tafiya taƙi ƙarewa, saita fara tunanin kodai gidan masu satan mutane ne, nan danan gumi ya fara keto mata, wannan part kam basu yi wata tafiya mai nisa ba taga anyi parking a waran ajiye motar, cikin zafin nama yasa ƙafa ya ture murfin motar sannan ya zagayo ya ɗauketa saman kafaɗarsa, kai tsaye cikin compound suka nufa anan ne part uku ya kasu, part ɗin da yake ɓangaren dama suka nufa nan ne babban falon General wajen da yake ajiye manyan baƙinsa, part ɗin da yake tsakiya kuma babban part ne wanda ɗakunan kowa yake ciki idan ka shiga ciki yayi jirgi ya sauƙa a iya falon kawai tsabar girmansa,
Baiwar ALLAH kallon gidan take a baibai domin tsarin gidan ya fara wuce misali, ganin kanta take kamar ba'a Nigeria take ba, ga wani irin sanyi mai daɗin gaske yanda yake ratsa sansanin jikinta, gidan ne ta ko wane ɓangare ansa A.C mai bada sanyin gaske, da cemerori ga flowowi masu bada nasu sanyi suma, tana cikin wannan yanayin bata san lokacin da aka direta ƙasi ba, saita para tangal-tangal zata faɗi ƙasi domin ji take kamar zata nitse ƙasi ne tsabar tudun carpet da laushisa, ko ciwon ƙafar ma ta daina jinsa tsabar yanayin jin daɗin data tsinci kanta a ciki, weather falon Chief of Army's mAh ya isheta jin daɗin rayuwa, ga wani irin ƙamshin da yake badawa, falon ta tsaya kallo gaba ɗaya ta rikice tsabar tsaruwar falon,
kafin General ya fito daga cikin order room ɗin na falon domin nan ne bedroom ɗinsa idan yanason hutawa, Sojan yana mata magana akan ta zauna amma sam bata jin mai yake faɗi tsabar hankalinta yana kan tsaruwar falon, cike da takaici yasa ƙafa ya girbe mata ƙafafu sai yaraf ta faɗi a ƙasan carpet, a nan ne ta dawo cikin hayyacinta, faɗuwar da tayi a ƙasan carpet mai makon taji ciwo saima ƙara miƙewa da tayi ta baje tayi shame-shame tana lumshe ido a hankali, tama manta ina suka zo, sanyin falon ne da ƙamshinsa duk ya ruɗe ta,
wani irin harara sojan ya wurga mata amma ko kallon yanda yake batayi ba, yana shirin yi mata mugunta yaso ya taka ruwan cikinta saiga General ya fito yana sanye da jallabiya fara har ƙasi, yana ganin Baiwar ALLAH a kwance bai wani damu ba saima murmushin da ya sake tare da zama yana gyaran murya, jin anyi gyaran murya yasa ta firgita ta tashi a zabure tana kallace-kallace, daƙer ta iya tsayar da idonta akan General ta ƙura masa ido kamar wanda ta sanshi, a cikin zuciyarta tana raya abubuwa da dama a cikin ranta take faɗin "wannan kamar na sanshi, wasu lokuta yana zuwa gidan marayu, tabbas shine domin daman soja ne...."

General maida idonsa yayi kan sojan yace "Tall man ya akayi ne?..."

Anan Tall man ya kwashe Abinda ya faru ya sanar masa amma bai sanar masa zaluncin da sukayi mata ba, ya ƙarasa maganar da cewa "daman mun riƙeta ne akan saika dawo tukun, duk hukuncin da ka yanke shi zamu aiwatar...."


General ya jinjina kai ya maida idonsa kan Baiwar ALLAH.......



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (11 to 12)



꧁꧂



Ƙura mata ido yayi kamar me tunanin wani abu, ita ko bata san yanayi ba sai kallace-kallacen da take, daga bisani ya ce "meye sunan ki?..."
kamar daga sama taji Muryar ya ɗuro mata kan dodon kunne a firgice tace "amm Baiwar ALLAH..."
cike da mamaki yace "ke ki gaya mun sunan ki saiki tsaya kina mun shirme, what do you means?..."
kamar zatayi kuka ta kuma cewa "wallahi tallahi bansan sunana ba, haka na tashi naji ana ƙirana da Baiwar ALLAH..."

Tallman dake tsaye ganin yarinyar tana shirin rainawa Ogansu hankali yasa yayi saurin kai mata ƙafa a saitin baki, ya yinƙuro Kenam General yayi saurin ɗaga masa hannu alamar ya dakata, cike da mamaki General yace "daga ina kike? sannan me kika zo yi nan area?..."

Baiwar ALLAH kuka ta soma yi ta kwashe komai ta sanar masa, bata ɓoye masa komai ba,
Jinjina kai General yayi sannan yace "Kenam kece yarinyar da Hajia Aliya ta bari a hospital?..."
dasauri Baiwar ALLAH ta ɗaga masa kai cike da fargaba,

Jinjina kai General yayi sannan yace "ina sane dake daman, kafin rasuwar Hajia Aliya ta bani duk wani information ki, ta ce kina cikin damuwa zaman gidan marayu bazaiyu ba domin akwana a tashi wata rana zaki wayi gari bakya doron duniya, hakan yasa na yanke shawarar idan an sallame ku a hospital saita kawo ki nan gidana ki cigaba da zama kafin Allah yasa a samu iyayenki, daga baya nake jin labarin mutuwar Aliya, naje har hospital domin duboki amma bakya nan kin tafi,
Yanzu dai tinda Allah yasa kin kawo kanki yanda zaki zauna ki cigaba da rayuwarki cikin ƴanci Alhamdulillah...."



Please Login or Register in order to submit comment