Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"gud Afternoon Yaya Roshan...."

ya amsa musu cikin kulawa, saiga Minal itama ta fito tana ɗaure da fuska daman ita koda yaushe a haka take kamar wanda ake aiko mata saƙon mutuwa, idan kanason ganin fararen haƙwaran Minal toh ka zauna kusa da ita a yayinda take waya da Marshall Mohandas,
zama tayi tana motsi da lips ɗinta ciki ciki ta ce "well done Yaya Roshan...."

Itama amsa mata yayi yana tsokananta da cewar "Amaryar Marshall ba son raini...."
saiga Ummy itama ta sauƙo daga part ɗin su Abbah ta sanar musu cewar an kammala girki....
zuwa tayi ta zauna a gefen Roshan suka saka shi a tsakiya ita da Baiwar ALLAH,
Pinky abun ya ɗaure mata kai cike da mamaki ta ce "Yaya Roshan naga kai kam kai maka abincinka ake can room ɗinka, meyasa yau ɗin kuma?...."

murmushi yayi tare da gyara farin glass ɗin idonsa ya ce "yau ɗin tare zanyi lunch da Ammata nah...."

zaro ido Pinky tayi ta ce "wacece kuma Ammatan ka?..."

Rukky ce ta tsoma baki da cewar "mu mana, su waye Ammatan inba mu ba, tare zamu ci...."

Girgiza kai yayi yana murmushi domin shi yasan abinda yake nufi.....
Su Abbah ne suma suka sauƙo, duk zama sukayi dai-dai lokacin da Baiwar ALLAH ta miƙe tana ƙoƙarin zuzzubawa kowa,
a wannan zaman Ƴar Tiny bata nan tana school, tinda safe idan ta tafi sai yamma take dawowa misalin ƙarfe 6 saboda harda islamiyya take haɗawa.....



꧁꧂


Uncle Deen wuni yayi a wannan dajin yana neman abun harinsa wato wacce take damunsa da sautin sarewa, acikin bacci har a ko ina, abun ya bashi mamaki jin har zuwa yanzu bai ji sautin na tashi ba kuma a waran kwanaki yaji...
Haka ya gama kewaye dajin har ya gaji ya shiga motarsa zai koma gida,
Hanyar daya bi yazo bata nan ya koma ba domin a 'ka'idarsa baya maimaita hanyar da ya bi,
zagaye yayi yabi ta wani layi wanda tsakaninsa da gida akwai rata sosai,
yana shiga wani road ya tarar da wasu mabarata suna zazzaune ganin mota yasa duk suka tashi da hanzarinsu suka kewaye motar suna bara da'a temake su dana Annabi,
shi tinda yake bai ta6a biyowa ta wannan layin ba amma ya fuskanta duk masu neman temako ne,
tsayar da motarsa yayi ya bud'e wani d'an boxe wanda yake cike da kud'ad'e ya ciro bob guda a 'kalla kud'in zasu yi million guda, ya bud'e murfin motar ya fito duk sun cika shi da hayaniya sai dai babu yanda ya iya dasu, a hikimance yake musu magana cewar "ko wacce ta koma waran zamanta zan zo yanda take ...."
ba'a son ransa yake d'aga murya ba sai dai yazo wajen da dolensa ya bud'e murya yayi magana domin duk waran tsofaffine babu wacce batayi jika da shi ba,
haka ya rin'ka lalla6asu har suka zazzauna ya fara bawa kowacce dubu hamsin hamsin domin sunada yawa sosai,
saida ya bawa kowa yaje zai shiga motarsa yaji wata tsohuwa tana masa magana daga zaune domin gurguwa ce bazata iya tashi ba,
juyawa yayi yaje har gurinda take zaune sannan ya dur'kusa yana kallonta,
ta ce "daman akwai wata yarinya ce 'karama taje siyo mana abinci to itama kurmiya ce shine nace ko zan iya kar6a mata sadakar da kake bayarwa...."

jinjina kai yayi sannan ya mi'ka mata sauran kud'in daya rage masa a hannu dubu d'ari cib,
tsohuwar kar6a tayi tana masa godiya tareda shafar fuskarsa tana sanya masa albarka, da haka ya tashi ya shige motarsa nan danan ya yabar wajen a d'ari....

yana tafiya saiga Yar Amana ta dawo hannunta ri'ke da kwanuka guda biyu tata dana tsohuwar kusada ita wacce ta kar6a mata temakon....
Tsohuwar haka ta mi'ka mata kud'in nan ko d'aya bata zara ba a yanda suke,
Yar Amana tana zaune ta kar6a cike da mamaki ita tinda take bata ta6a ri'ke kud'i mai yawan gaske kamar na yau ba, dasauri ta d'ago kai tana kallon tsohuwar alamun tana bu'katar bayani..
Tsohuwar ta ce "yau kam da sa'a muka fito, yanzun nan wani mutumi yazo ya raba mana kud'ad'e, shi ba mace ba sannan shi ba namiji ba domin yanada sumar gashi kamar mace amma yanayin jikinsa irin 'karfaffun mazan nan ne, to waya sani ko mata maza ne sai Allah...."

Yar Amana kallon tsohuwar take domin tsab tana jin duk abunda take fad'i mayarwa ne bazata iya ba,
takai idonta kan kud'in ita kanta bata san mezatayi da kud'in nan ba.....



꧁꧂



Duk suna zazzaune a dinning,
kowannen da shinkafarsa da miyan chicken akan shinkafar da shi kansa chicken ɗin amma sai dai abinci ya gagara ciyuwa tsabar tsananin yawan gishirin dake cikin miyan ferfesun,
kowa yayi gumm babu wanda ya ce ƙala, Hajia Kilishi kam dafa goshinta tayi ta sunkuyar da kanta ƙasi tsabar takaici ga gishirin yayi mata yawa a baki ko haɗiyar yawu ta kasa yi,

Shima Abbah yana zaune tinda yayi loma ɗaya bai ƙara motsawa ba, ga abincin a cikin bakin ya kasa tofarwa sannan ya kasa motsi da bakin,
Rukky kam fashewa tayi da kuka tana faɗin "Wayyo Allah nah yunwa nake ji amma abincin bazai ciyu ba..."

Pinky daman yanda tasa abincin a baki haka ta tofar dashi a cikin abincinta sai faman kora ruwa take....

Minal kuma tashi tayi dasauri ta shige kitchen domin shine a kusa taje tana kwarara amai acikin sink na wanke-wanke,

Ummy itama tana kaiwa loma ɗaya bata ƙarasa taunar abincin ba ta zubar acikin hannunta tana yatsina fuska tare da faɗin "Haba! haba!! haba!!! Daman ai nasan za'a rina....."

Baiwar ALLAH itama tana zaune yanda ta kai lomar abincin bata ƙara motsa bakin ba, ita bata haɗiye ba sannan bata tofoshi waje ba abincin nanan acikin bakin kamar yanda Abbah yayi shima,

Roshan shikam sam bai nuna wani reachen ba duk da shima daƙer ya haɗiye abincin daya kai bakinsa, daga nan saiya ɗebe miyar da naman kajin ya zuba a wani plate daban ya fara watsa iya zallar shinkafar a bakinsa yana faɗin "to ya za'ayi ai dai baza'a zauna da yunwa ba, ko wacce ta barbaɗa oil da maggi ta ci,
Ni banga laifin abincin nan ba kawai dai ɗan tazarcen salt akayi....."

Minal ce ta fito gadan-gadan da masifarta tazo tana nuna Baiwar ALLAH da yatsa tare da faɗin "ke wawiya ce, so kike ki kashe mu? Bayan ga wunin yunwa baki kammala mana girki da wuri ba hakan ma kizo ki zabga mana salt acikin girkin so kike mu hallaka koh? toh wallahi ahir ɗinki dan ubanki kuma ki tashi kije ki sake mana wani girkin...."

bata ƙarasa maganar ba taji Abbah yana ɗaga mata hannu tare da cewa
"Uh'ummm! Uh'ummm!! Uh'ummm!!!....."
baki a ƙunshume yana ɗaga hannu, tashi yayi ya nufi upstairs yanda part ɗinsa yake,
yana shiga ya nufi toilet yaje ya zubar da abincin bakinsa sannan ya ɗauki makilin da brush ya wanke bakin tukun ya sauƙo falon ...

yazo yana faɗin "ya akayi abincin yau yayi gishiri?...."
Ummy tana daga zauna ta ce "Abbah yau fah girkin manyan Maza muka ci, Yaya Roshan ne yayi mana ferfesu mai ban burgewa da ɗanɗano....."

Abbah ya ce "Roshan kuma? meya iya da za'a bashi girki...."

Abbah ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "ya akayi Roshan yayi girki kuma Dota?...."

Baiwar ALLAH kai a sunkuye ta ce "Abbah shine yace ya iya girki na bashi yayi...."

Abbah ya ce "shi Roshan ɗin ne ya iya girkin?...."

Roshan ɗagowa yayi yana kallon Abbah sannan ya ce "na iya mana Abbah, haba ya ake ɗauka na kamar ƙaramin yaro ne...."

Abbah jinjina kai yayi ya ce "ahhhh ba shakka ka iya girki sosai..."
Abbah ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "ina sauran girkin da akayi ina fatan dai duk bashi yayi su ba?...."

Baiwar ALLAH kamar zata yi kuka ta ce "wallahi Abbah duk shi ya zuzzuba gishiri acikin girke-girken da akayi, kamar yanda wannan yake haka waɗancan ma suke....."

Abbah girgiza kai yayi sannan ya ce "lahaula kuce yau anyi wasten abinci acikin gidan nan, na tabbata ko karnukan gidan nan bazasu iya cin wannan girkin ba sai dai akai can Bola...."
Abbah ya kalli sauran yaran ya ce "kunga ku tattaso duk muje restaurant...."

Minal ta ce "ta sake girka mana wani...."

Roshan yayi saurin katseta da cewa "saidai Ni zan sake girka muku domin ta gaji, muddin ita zata sake yin girki to kuwa saidai Ni zan yi ...."

Abbah ya ce "batun sake girki duk bai taso ba domin ita ba boyi-boyi bace,
Kuma daga yau ban yadda Yarinyar nan ta cigaba da ayyukan gidan nan ita kaɗai ba, duk zaku fiffito ku rinƙa tayata...."

Minal ta ce "gaskiya Abbah aiki zai mun yawa, kasan da sassafe nake fita gurin aiki sai Azahar kuma, ga gajiyar aikin office sannan nazo na tarar da aikin gida? gaskiya a'a ganan su cima zaune su Pinky basa zuwa ko ina...."

Ummy ta ce "Ni daman ina tayata aiki yawwa...."

Pinky fuska a ɗaure ta ce "mu ai mun kusan komawa school London, don haka mu ba cima zaune bane...."

Abbah ya ce "toh kafin ku koma London zaku na tayata aikin gida daga yau,
ku tashi mu tafi restaurant...."

Duk tashi sukayi har da ita kanta Hajia wacce taketa fushi bataso tayi magana Abbah ya dizgata acikin yaranta shiyasa tayi shuru....

Abbah ya kalli Baiwar ALLAH ya ce "ki taso mana kema..."

Girgiza kai tayi sannan ta ce "a'a Abbah zanci shinkafar da oil da maggi, kuma Inaso kafin Uncle Deen ya dawo zan sake girka masa abinci...."

Shima Roshan cewa yayi "Nima bazanje ba zan ƙarasa ci da oil da maggi sannan nayi wanka nayi bacci...."

Abbah ya ce "toh kai kam waya gayyace ka duk bakai bane ka fallashe mu, rabon da muje restaurant har mun manta sai yau saboda kai....."

yana kaiwa ƙarshe yaja yaran gidan zasu fice,
Roshan ya ƙwalla ƙiran Ummy tare da faɗin "kema wato har dake za'a guje mun abinci koh?...."

Ummy ta juyo tana riƙe da kunkumi ta ce "cabb wazai ci wannan girkin a kwana ana gudawa da zawayi....."

Dariya Roshan yayi idonsa akan Baiwar ALLAH wacce ta zauna tayi shuru kamar mai tunanin wani abu, ga shinkafar bakinta yanda ta tofar itama a tafin hannunta........



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 33 to 34



꧁꧂


Roshan da Baiwar ALLAH su kaɗai aka bari a cikin gidan basu fita ko ina ba,
suna zaune akan dinning babu wanda ya kula kowa, ita dai Baiwar Allah ta barbad'a maggi da oil tana ci hankali kwance dake ta saba ci irin wannan abincin a gidan marayu da ta zauna, shi kuma Roshan ya zuba mata eyes yana kallon yanayin yanda take taunar abincin kamar bazata ci ba, ga dimple yanda yaketa lotse wa sai ya 'kara fito da asalin kyanta sosai, ji yake kamar ya rungumeta tsabar tsananin so da 'kaunarta da ya shige cikin zuciyarsa lokaci guda,
a hankali yake motsi da lips d'insa bai san lokacin da ya furta cewar "you're the Beautiful Queen of kingdom my part of mine, i love you so much with all my heart....."

Dasauri Baiwar Allah ta waiwayo tana kallonsa cike da mamakin furucin da ya yi, lokaci guda ta tintsire da dariya tana tafa hannayenta tareda fad'in "woooo lallai Yayana wannan first lady takan ta zautar dakai da yawa, kana zaune amma kana tunaninta? to ni ba ita bace ni Ammatanka ce not your Queen ehen, ka farfad'o daga mafarkin zaunen da kake....."

Kafin ya ce wani abu har ta mi'ke tsaye tana 'ko'karin tattare kulolin kan dinning,
baice komai ba harta gama tattarawa ta shige kitchen, tashi yayi ya bi bayanta,
yana shiga ya tsaya ta bayanta yana tunanin sanar mata cewar yana sonta, bata san ya shugo ba ta juya da sauri zata fice suka mannu da juna,
a rud'e take fad'in "innalillahi wa inna'ilaihi raju'un...." har tayi baya zata fad'i yayi saurin tarota tareda mannata asaman 'kirjinsa, kwantar da kanta tayi kan kirjinsa tana maida numfashi domin ba 'karamin tsorita tayi ba,
saida suka d'au tsawon mintuna biyar a haka kafin ta fara motsawa tana kokarin d'agowa,
Roshan tintinin har ya fita hayyacinsa tsabar tsananin feeling dake kawo masa hari,
a hankali take d'ago da kanta saitin fuskarsa nan suka had'a ido, babu wanda ya kawar da kansa haka suka cigaba da kallon juna, daga bisani ya fara matso da fuskarsa saitin nata numfashinsu na hargutsuwa, a hankali ya kai hannunsa ya tallafo ha6arta yana shirin had'e musu baki, itama Baiwar Allah ta shiga yanayin da tinda take bata ta6a shigarsa ba a hankali ta lumshe idonta domin ba 'karamin kashe mata jiki yayi ba da irin sallonsa wanda shi kad'ai yasan sirrin abunsa,
cikin salo ya kamo lips d'inta ta 'kasi ya fara socking kamar wanda ya samu lollipop,
ita kuwa 'yar uwa bata san lokacin da ta zagayo hannayenta ta bayansa ba, ta rungumeshi sosai kamar zata mayarshi cikinta,
cikin salo da kwarewa yake fitar da ita daga hayyacinta ta hanyar lips socking, itama lokaci guda ta fara mayar masa da martani a hankali kamar babu rai a jikinta,
suna cikin wannan halin suka ji an turo 'kofar kitchen, a rud'e Baiwar Allah ta kawar da kanta gefe tana 'kokarin kwacewa,
shi kuwa ya ri'ke ta sosai ganin yanda take a rud'e bata cikin hayyacinta, fashewa tayi da matsanancin kuka tana girgiza kai had'in da cewa 'ni ka sake ni dan Allah, na shiga uku ka rufa mun asiri ka sake ni, banasoooo....."
Jawo ta yayi ya rungumeta sosai a jikinsa yana bubbugar bayanta a hankali alamar rarrashi,
Roshan ko waiwaya wa baiyi ba balle yaga wanda ya shugo sai ji yayi ance

"Ya iyaha iyayya! Yaya Yochann me kuceyi haka? wa ce ce ka yunguma ?....."

Ba tareda ya juyo ba ya ce "kinga Mamana jeki waje maza, barkwano ne ya shige mata ido shine nake hure mata, banaso tayi kuka a gabanki ne...."

kafin ya 'karasa maganar ta katse shi da cewa "wayyayi tayyayi bay yadda ba, ai naga cocan bacinta kaceyi, kuma! kuma!! kuma!!! cena gaya wa Ankui Deen da Abba da Mommy....."

tana kaiwa nan ta juya da gudu ko tsaya sauraronsa batayi ba,
yanata 'kiran sunanta "kinga Mamana tsaya mana kiji...."
harta fice abinta...

Baiwar Allah ce ta fizgi kanta daga jikinsa tareda zabga masa mari akan kunci,
tana kuka har idonta yayi jawur tana fad'in "wallahi ka cuce ni, ka zubar mun da mutuncina da kimata acikin gidan nan, yanzu idan Abbah yaji wannan batun ya zanyi da rayuwata, idan Hajiya ta ji shikenam kashina ya bushe......". bata 'karasa ba kuka yaci ranta, da'ker ta iya dakatarwa ta cigaba da cewa " kasa nayi abunda tinda nake a rayuwata ban ta6a aikatawa ba, ata sanadiyarka kasa mutuncina ya zube a idon yarinya 'karama...."

Roshan idonsa a kanta yana ri'ke da kuncinsa ta 6angaren dama yanda ta

Please Login or Register in order to submit comment