Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

garin ɓatan ƴar Amana, a daren jiya Baiwar ALLAH kwana tayi bata rintsa ba sai kuka, abinci kuwa ko loma ɗaya batasa a bakinta ba balle ruwa, a ranar da masu bincike suka zo sun bincika ko ina, basu samu wata hujja ba, hatta security masu gadin gidan suma babu wata alamar data nuna cewa an shugo gidan ko kuma an fita, saida sukayi waran sati guda suna bincike kafin suka samo wata ɓoyayyar hanya acikin gidan ta bayan gidan, hanya ce wanda saika bi ta cikin ƙasa kafin ka fice a gidan, wato gidan ƙasa, abun ya bada mamaki a kowa na cikin gidan babu wanda yasan da wannan hanyar, haka sauran mutanen gidan suka fara tsorata...

Bayan an gama bincike an gano hanyar an yanke cewar Ƴar Amana guduwa tayi bawai ɓata tayi ba ko saceta, abun ya bada kowa mamaki sosai, an faɗi hakane saboda a kawar da maganar ɓatan ta, waɗanda suke faɗin hakan sune shuwagabannin masu gidan marayun, mutane da yawa basu yadda da hakan ba, amma saidai babu yanda aka iya, haka maganar ta baza cikin gidan da hukumomi cewar ƴar Amana ta gudu daga gidan marayu..

Baiwar ALLAH jin maganganun da aketa yayatawa yasa ta ɗora hannu akanta ta fara ihu kamar ranta zai fita, kuka take sosai a filin gidan, har tana ƙoƙarin shiɗewa tana kuka tana faɗin "shikenam an ɓatar mun da Ƴar Amana, nasan Ƴar Amana bazata iya tafiya ta barni ba...."

Sauran ƴan matan gidan ne suke rarrashinta suna bata haƙuri,
Baiwar ALLAH gaba ɗaya ta fita hayyacinta idanu sunyi zuru-zuru tsabar rikici da tashin hankali ta faɗi a wajen sumammiya....

Ƴar Amana tinda aka sato ta aka jefar da ita acikin wani ɗaki bata farfaɗo ba yau sati guda domin ba ƙaramin guba aka sheƙa mata a hanci ba,
An ɗaɗɗaure hannayenta da ƙafafuwanta da igiya tana kwance saman wani wantalelen katifa, ɗakin ɗan ƙwaƙwas, amma sai dai ɗakin acikin jeji yake bayan gari, ga masu gadinta wasu zabga zabgan maza su biyar ko wannensu yana riƙe da ƙaton bindiga a gannunshi.....



𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (6)



꧁꧂


Bayan sati biyu da ɓatan Ƴar Amana!

Har wannan lokacin Baiwar ALLAH bata samu ƙwanciyar hankali ba, kullum acikin kuka take ba ci ba sha gaba ɗaya ta fita hayyacinta ta rarrame sai kurmin ƙashin wuya, idanu sun kukkumbura sunyi lufu-lufu abinka dame manyan eyes, fuska duk ya kokkoɗe dake farar mace ce kamar ba jini a jikinta tayi fari fatt, tana fama da jinya a jikinta amma babu wanda ya sani ita kaɗai tasan abinda take ji ajikinta, ga damuwar ƙazafin da akayiwa Ƴar Amana cewar ta gudu ne daga gidan marayu!

A gidan marayu kuwa an kawo musu wata shugaba mace Madam Aliya, wannan lokacin sunyi dacen samun shugaba ta gari mai jin tausayi da son temakawa al'umma, Ƴan matan gidan sun samu sauyin yanayi sosai na jin daɗin rayuwa, yanzu wata guda da kawo Madam Aliya kowa yana harkokin rayuwarsa cikin farin ciki, babu tsaro na takurawa, maganar Ƴar Amana kuwa tin tinin an rufe shafinta ba'a maganar ta, tin daga lokacin da Ƴar Amana ta ɓata Baiwar ALLAH bata ƙara fitowa filin gidan ba, daga ɗaki sai ɗaki, iya Aunty Habiba ce kawai take zuwa mata, takan kawo mata flask na ruwan tea saboda iya ruwan tea kawai take iya sha, sannan Aunty Habiba tayi iya kokarinta akan akaita asibiti amma Baiwar ALLAH taƙi yadda kuma taƙi yadda ta haɗu da sabuwar shugabar da aka kawo musu saboda tasan ko bataso dole sai an kaita asibiti, taji labarin matar tanada kirki sosai, a haka take ƙunshe da rashin lafiyarta, hatta sallah a zaune take yinsa tsabar hajijiyan dake ɗinbar ta, ga yawan ciwon ƙirji da take fama dashi,

Ƙarfe takwas bayan sallar isha'i Baiwar ALLAH tana zaune akan sallaya yanda ta idar da sallah tana jan carbi cikin nutsuwa taji an buɗe ƙofar ɗakinta tareda yin sallama, cikin sassanyar murya ta amsa ba tareda ta waiwaya ba saboda tasan Aunty Habiba ce, Aunty Habiba ƙarasa shugowa tayi ta nemi bakin gado dake gefen Baiwar ALLAH ta zauna tare da zabga uwar tagumi idonta akan Baiwar ALLAH,
Baiwar ALLAH kallon Aunty Habiba tayi tare da sau murmushi tace "Aunty lafiya kuwa ki kayi tagumi?..."

Aunty Habiba ta ce "dole nayi tagumi Baiwar ALLAH, kina yarinya dake amma kina so ki sanyawa kanki hawan jini, bakida lafiya kin ƙi sanarwa kowa kuma kin haneni na sanar shin meye dalilin yin haka ?..."

Kasalalliyar murmushi Baiwar ALLAH tayi tana kallon guri guda kamar me yin tunanin wani abu, bayan ƴan mintuna da zurfafa tunaninta sannan ta buɗi baki tareda faɗin "ban san a wani hali take ciki ba, ita ɗin yarinya ce ƙarama kuma Kurmiya, ina tsoron kar wani abu ya cutar da ita, ban saniba ko tana cin abinci ko bata ci shin taya zan iya cin abinci kuma taya zan iya yin bacci alhalin ƴar uwata bata samu yinsu ba aciki...."
kafin ta rufe baki kuka ya kuɓuto mata kamar daman jira take ayi magana tayi kuka, tsabar tausayi Aunty Habiba itama saida ta share hawaye ta sauƙo ƙasan sallaya tareda rungumo Baiwar ALLAH jikinta tana rarrashinta cikin kulawa...

Aunty Habiba bata tashi barin ɗakin ba sai da ta tabbatar da cewar Baiwar ALLAH tayi bacci tukun itama ta tashi ta fice a ɗakin bayan ta kwantar da ita,

Around 1:30AM cikin dare Baiwar ALLAH ta tashi da matsanancin ciwon ciki, wanda a wannan daren ta kasa tashi tayi sallar da ta saba yi koda yaushe, tana daga saman gado ba abunda take sai juyi haɗe da nishin azaba, tana cikin wannan halin bata san lokacin da ta faɗo daga kan gadon ba, ganin ba wani sarki sa ALLAH yasa ta nufi bakin ƙofa da rarrabe tana kuka game da faɗin "wayyo temako! zan mutu wayyo ciki na, dan ALLAH temako...." muryarta ba wani fitowa yake sosai ba Saboda tsantsar azaba daƙer take iya motsi da leɓɓenta, da haka tayi nasarar ficewa daga cikin ɗakin tana rarrabe ita kanta bata san ina ta nufa ba, ganin mutum tsaye a gabanta tsargagam ko motsi babu yasa ta dakata ta fara binsa da kallo tin daga ƙafarsa har zuwa ƙarshen kansa, sai dai abun mamaki yana sanye da baƙar hula a kansa da fuskarsa gaba ɗaya, a ruɗe ta juya zata koma daga inda ta fito mutumin yayi saurin cabko sumar kanta ya ɗagota sama yana ƙareta da kallo, ita kuwa ƙoƙarin ta shine taga ta zame masa tana so tayi ihu amma sai dai muryar ya shaƙe,
a hankali ya furta "Baiwar ALLAH kwanakin ki sunzo ƙarshe, ki sani cewar Ƴar Amana tana hannu na, itama na kusan gama wa da ita, ku kukayi sanadiyar tarwatsa mun rayuwata, don haka saina kashe ku, zan fara ne daga kanki...."
Baiwar ALLAH cikin firgici ido a zazzare daƙer ta iya cewa "wanene kai?..."

kafin ta sake cewa wani abu ya haɗe kanta da jikin bango ya gwara nan danan jini kamar da bakin ƙwarya haka yake bleeding, yasa hannu ya toshe mata baki sannan ya kawo bakinsa saitin kunnenta yace "Ni sunana Ɓoyayyen mutum, ki shirya yin bankwana da duniya yanzu..."
cikin zafin nama ya janyo ta saitin tagar beni sannan ya kifar da kanta ƙasin tagar yanda zatana kallon can ƙasin benin,
Ita kuwa ba abinda take sai haki domin ba ƙaramin wahalar da ita yayi ba, ganin yanda ta zubawa ƙasin benin ido yasa ta fara jin hajijiya da jiri ga ido yanda ta zazzaro su tsabar tsoro da firgici game da tashin hankali,
Dariya mutumin ya soma yi irin ta manya manyan mungwaye waɗanda suka shahara wajen yin mugunta, lokaci guda ya dakatar da yin dariyar yana huci yace "shin kinsan ina kike kallo? TOH mutuwarki kike kallo kuma yanzu zaki bita ku tafi...."
kafin Baiwar ALLAH tayi wani motsi har ya ɗago da sawayenta ya dungurar da ita ƙasin beni mai tsayin gaske,
kafin ta ƙarasa faɗawa ƙasi wani irin gigitaccen ihu tayi mai raunana kunnuwa wanda ba iya mutanen gidan Bama hatta masu gadi zasu jiyota......


A firgice ta yaye mayafin data rufe jikinta dashi tana kurma ihu kamar ranta zai fita,
Da gudu wasu mata suka turo ƙofar ɗakin ta suna tambayarta cewar "lafiya kuwa Baiwar ALLAH meya faru dake haka kike ta ihu ko ina ana jiyo ki..."
wata daga ciki ne itama tace "Baiwar ALLAH tinda muke dake bamu taɓa jin kinyi irin wannan ihun ba sai yau, shin me yake damunki haka?...."

Ita dai Baiwar ALLAH haka take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya duk ta haɗa gumi kamar wacce ta watsa ruwa a jikinta, ga idanuwa yanda sukayi jawur sai jan numfashi take daƙer,
abubuwan da suka faru da ita ne a cikin mafarki suke dawo mata ƙwaƙwalwarta, lokaci guda ta suma jin hajijiya da matsanancin ciwon kai, ganin batada ta cewa yasa ta fashe da kuka....

tsabar tsayin mafarkin da tayi bata san gari ya waye ba har ana neman wajen ƙarfe 8 gashi ko sallar asuba bata yi ba...

Suna cikin tambayarta halinda take ciki saiga Madam ta shugo ɗakin ita da Aunty Habiba, tana shugowa taje ta samu bakin gadonta ta zauna cikin tausayawa takai hannu ta jawo Baiwar ALLAH jikinta tana rarrashinta tareda faɗin "kiyi haƙuri kinji koh! Habibah ta sanar mun duk halinda kike ciki, but don't worry I will find something else for you okay..."

Madam ta kalli sauran matan da suke tsatstsaye a ɗakin tace musu "Please kuyi haƙuri ku fita kowa ta kama gabanta tana son hutawa..."
hakan kuwa sukayi sai iya Aunty Habiba ce kawai ta tsaya, Madam ta kalli Aunty Habiba sannan tace "jikinta zafi sosai, Inaso zan kaita hospital yanzu, ki kula mun da Office ɗina duk wacce take buƙatar abu saiki bata Please...."
Aunty Habiba ta amsa mata cikin girmamawa, Haka Madam ta tallafawa Baiwar ALLAH suka tashi tana janta a hankali har suka bar cikin ɗakin, a halin yanzu Baiwar ALLAH bata san a wata duniyar take ba domin ta rigada ta jikkata sosai, kana ganinta kasan babu jini a jikinta domin ba ƙaramin fari tayi ba har wani yellow ² tayi fuskar tayi fattt, da haka suka sauƙa down stairs, suna sauƙa kuwa tasa aka kawo mata motar ta har wajen da suka tsaya saboda majinyaciyar bazata iya zuwa har wajen parking ba domin ya yi mata nisa sosai,
Lokaci guda Madam taji wuyan Baiwar ALLAH ya karye mata a saman kafaɗatar ta, a ruɗe ta kalleta ido a zazzare ganin bata motsi kwata-kwata, a tsorace Madam ta sakata cikin motar ta itama ta shiga ta buƙaci ɗaya daga cikin matan gidan ta shiga motar itama zata raka su, ai kuwa a ɗari Madam ta finciki motarta sai bakin gate......




MA SHA ALLAH
SABODA RANAR FARKO NE YASA NA TURO MUKU PAGE ƊAN KAƊAN SBD WASU NASAN BASU DAWO A HUTUN SALLAH BA
BUT NEXT DA YAWA ZANYI MUKU ....


𝘁⃪𝘆⃪𝗽⃪𝗶⃪𝗻⃪𝗴⃪ 🤳𝗮⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗴⃪𝗶⃪𝗮⃪𝗱⃪𝗲⃪.



𖣔𖣔𖣔𝙈𝙔 𝙀𝙉𝙀𝙈𝙔𖣔𖣔𖣔
✰𝐌͢𝐚͢ƙ𝐢͢𝐲͢𝐢͢ 𝐍͢𝐚͢𝐡͢✰🤦‍♀️🤦‍♀️

𝐁͢𝐎͢𝐎͢𝐊͢ 𝐎͢𝐍͢𝐄͢ 𝐟͢𝐢͢𝐫͢𝐬͢𝐭͢ 𝐬͢𝐭͢𝐞͢𝐩͢

𝗗⃪𝗲⃪𝗱⃪𝗶⃪𝗰⃪𝗮⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗱⃪ 𝘁⃪𝗼⃪ 𝗺⃪𝘆⃪ 𝘀⃪𝗲⃪𝗹⃪𝗳⃪.

𝗔⃪𝘀⃪𝗺⃪𝗲⃪𝗲⃪𝘁⃪𝗮⃪𝗵⃪ 𝗡⃪𝗼⃪𝘃⃪𝗲⃪𝗹⃪ (𝙂𝙞𝙖𝙙𝙚)
𝘁⃪𝗵⃪𝗲⃪ 𝘄⃪𝗿⃪𝗶⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ 𝗼⃪𝗳⃪ 👇
𝚃𝙷𝙴 𝚆𝙸𝙵𝙴 𝙾𝙵 𝙰 𝚃𝙸𝙶𝙴𝚁🐅
👉ᵐᵃᵗᵃʳ ᵈᵃᵐⁱˢᵃ👈
𝙰𝚗𝚍 𝚗𝚘𝚠 𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈
👉ᵐᵃƙⁱʸⁱ ⁿᵃʰ👈

ᶠʳᵒᵐ ᵗʰᵉ ᵇᵉᵍⁱⁿⁿⁱⁿᵍ, ᶠᵒˡˡᵒʷ ᵗʰᵉ ˡⁱⁿᵏ ᵗᵒ ʲᵒⁱⁿ ᵐʸ ᵍᵒᵘᵖ
👇👇👇
https://chat.whatsapp.com/CYC0vxQRZ269ISx36l1Dmt

ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿˢᵃⁿ ᵇᵃᶻᵃ ᵏⁱʸⁱ ᶜᵒᵐᵐᵉⁿᵗ ᵇᵃ ᵏᵃʳ ᵏⁱ ˢʰⁱᵍᵃ ᵐᵘⁿ ᵍʳᵒᵘᵖ,
ⁱᵈᵃⁿ ᵏⁱⁿ ˢʰⁱᵍᵃ ᵇᵃⁿᵈᵃ ᵗᵘʳᵃ ˡⁱⁿᵏˢ..

𝙼𝚈 𝙴𝙽𝙴𝙼𝚈 𝙱𝙾𝙾𝙺 𝙿𝚁𝙴𝚂𝙴𝙽𝚃:

1--->𝙈𝘼𝙅𝙊𝙍 𝙂𝙀𝙉𝙀𝙍𝘼𝙇 𝙍𝘼𝙕𝙃𝘿𝙀𝙀𝙉 (M.G.R)ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

2---> 𝙎𝙐𝙍𝙂𝙀𝙊𝙉 𝘿𝙊𝘾𝙏𝙊𝙍 𝙍𝙊𝙎𝙃𝘼𝙉 (S.D.R) ᵗʰᵉ ᵗʷⁱⁿˢ.

3---> 𝘽𝘼𝙄𝙒𝘼𝙍 𝘼𝙇𝙇𝘼𝙃.

4---> Ƴ𝘼𝙍 𝘼𝙈𝘼𝙉𝘼.

𝗰⃪𝗵⃪𝗮⃪𝗽⃪𝘁⃪𝗲⃪𝗿⃪ (7)



꧁꧂


Ledar jini ne yake ɗiga ɗis! ɗis!! ɗiss!!! a yayin da ita kuma wacce take kwance a saman gadon hospital take bacci ido a lumshe gwanin burgewa, a hankali jinin yake shige mata hannun da aka ɗaura mata,
haka take fitar da numfashi slowly,
jin yanda sanyin A.C yake ratsa jikinta yasa ta ɗan soma mutsil-mutsil tana yatsina fuska still ido a lumshe, daƙer ta iya fara buɗe eyes ɗinta, a cikin tana ganin dishi-dishi har idon ya washe, haka take bin saman ceilling da kallo ko ƙibta idon bata yi, jin wani irin la'anannen ƙamshin turaren da yake bugan hancinta yasa ta ɗan juyar da kanta saitin yanda ƙamshin yake tashi, abinda ta fara gani shine zara-zaran yatsun hannu fari ƙall ga yatsun hannun sun sha zobina da warwaraye na gwal tana ɗauke da wata makekiyar waya wanda a ƙalla zai kai 2millions, ga wani danƙarariyar Abaya mai bala'in tsada wanda duk rigar a jere yake da duwatsu masu ƙalƙali da ɗaukar ido, a hankali take bin zazzafar ƙirar jikin matar dake zaune akan chair da kallo har zuwa kan kyakkyawar fuskar ta, ganin matar yasa ƙirjinta yayi wani irin bugawa a razane take ƙoƙarin tashi zaune ido a zazzare, a yayin da ita kuma matar hankalinta duk yana kan wayar hannunta sai daddannawa take alamun chatting take,
tasha kitson Attach har gadon bayanta sai gyalen rigar da ta ɗora akanta...

Daiden lokacin da Madam Aliya ta shugo cikin room ɗin hannunta riƙe da ledoji guda uku, ganin yanda Baiwar ALLAH take a razane idonta akan Madam Parveen yasa ta ƙaraso da sauri tana faɗin
"Lafiya kuwa Baiwar ALLAH? kin tashi ne? ya jikin nakin?...."

haka take jero mata tambayoyi tsabar yanda take jinta a ranta, domin tinda tayi ido huɗu da Baiwar ALLAH taji ta shiga ranta sosai da kuma tausayinta ,
tana ƙarasowa ta zauna a bakin gadon da Baiwar ALLAH take still idonta akan Madam Parveen,
Madam Parveen jin shigowar Madam Aliya yasa ta ɗago da kanta tana binsu da kallo daga bisani ta tsayar da idonta akan Baiwar ALLAH yanda taga kallon da take mata kamar wacce ta santa...

Madam Aliya tana riƙe da ɗayan hannun Baiwar ALLAH tace "Baiwar ALLAH shin kin santa ne kike kallon ta?...."

A hankali ta soma girgiza kai alamar a'ah!

Madam Aliya ta kuma cewa "ita ɗin Babbar Aminiyata ce, tare mukayi primary school to secondary, sunanta Madam Parveen, jami'ar C.I.D ce wato Agent Madam Parveen, Matar Chief of Defence staff
General Suraj Mahendra Marka shugaban sojojin ƙasar Australia (U.S).
Jiya ta shugo Nigeria domin gudanar da wasu ayyuka na kwana biyu daga nan ta koma can, ta kawo mun ziyara ne taji labarin ina nan hospital tare da ke shine tazo...."

Tinda Madam Aliya ta fara kora jawabai Baiwar ALLAH ta sake baki tana kallonta tareda kasa kunne tana sauraron duk abinda take faɗi, bata ankara ba taji Madam Parveen ta dafa kafaɗarta tareda faɗin "what's ur name?..."

Baiwar ALLAH girgiza kai kawai tayi domin ita kanta bata san sunanta ba...

Madam Parveen ganin bata ba ta amsa ba yasa ta mata magana ta Hausa yanda zata gane, a tunaninta bata iya turanci ba ne,
Ta kuma cewa "Dota Ya ya sunan ki?..."

Madam Aliya ce ta kwashe da dariya jin har yanzu Madam Parveen bata ƙware a Hausa ba,
wani irin harara Madam Parveen ta wurgawa Madam Aliya ganin dariyar da take yiwa Hausar ta,
Ta ce "what are you laughing for?...."

Girgiza kai kawai Madam Aliya tayi ba tareda ta ce komai ba sai ƙunsar dariya take...

Madam Parveen sharar da Madam Aliya tayi ta juyo ta cigaba da tambayar Baiwar ALLAH cewar " wa ne ne ya sameki kike kwanta a hospital? typhoid or maleria?
Ga babu jini a body naki sorry my Dota....."
ɗaga mata kai kawai Baiwar ALLAH tayi domin bata san wani amsa ɗaya zata bata ba....
suna cikin wannan halin saiga Doctor ya shugo da wasu nurses su biyu suna biye da shi,
yazo duba lafiyarta sannan ya cire mata allurar jinin da aka ɗaura mata domin kaɗan ne ya rage,
ya kalli Madam Parveen yace "ke ɗin Mamanta ne ko Auntyn ta?...."
dasauri Madam Parveen ta girgiza kai tana faɗin "No no noo bani santa ba, I have a Daughter but I lost her since 20 years later.....".
tana kaiwa ƙarshen maganar ta tayi saurin sunkuyar da kanta ƙasi sakamakon hawayen da yake shirin zubo mata....

Doctor ya girgiza kai sannan yace "sorry Madam I think you are her mother because naga kuna kama sosai ...."

yana kaiwa nan yayi ficewarsa tare da nurses dake biye dashi!


Please Login or Register in order to submit comment