Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍


Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki. Tare da fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW), Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.

Hakkin Mallaka nawa ne ni Fatima Idriss Bello wacce kuka fi sani da Fadrees_20✅.
09020588802

Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.



All rights reserved ©fatimaidrissbello
Fadrees🖋️



🤴* YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello 🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; Fadrees_20
Arewabooks; Fadrees20



Page 1

A shekara ta 1950 a watan Afrilu.

WANI GIDA ne mai karamin ƙofa, irin kofar katako dinnan kuma ginin ƙasa (Bricks) ne, gidan ba wani babban gida bane domin daga gani kaga gidan mai ɗan rufi asiri ne.
Da zarar ka bude kofar gidan kuwa zaka ci karo da zaure me dauke da dakuna biyu masu kallon juna (opposite), daki ɗaya na maigidan ne dayan kuma na samarin gidan. kana shigowa asalin cikin gidan kuwa da kwanuka da butoci da ledoji zaka fara cin karo.

Ɗaga kai na kuwa ke da wuya dakuna na hango a jere guda uku da yar rumfar (veranda) su a kowacce gaban dakin, gashi kuma ko wanne daki labulensa daban hakan ne ya tabbatar min gidan da kishiyoyi.

Ban tabbatar da hakan ba kuwa sai da naga wasu mata magidanta ɗaya na suyan ƙosai ɗayar kuma tana dafa wani abu kamar kunu daga ganin yawan shi za kasan na siyarwa ne, ata gurin da suke sana'ar tasu akayi musu ƙatuwar rumfa a matsayin madafa (kitchen), suna yi suna harare-hararen juna ga wani uban tarkace a gaban su.

Wani yaro wanda ba ze wuce shekara sha ukku ba na hango ya fito daga ɗaki na tsakiyan cikin ɗakunan, jikinsa ajike alamar yayi fitsarin kwance, da misalin karfe shida na safiya, ko kallon iyayensa da suke aiki beyi ba ballantana suyi tsammanin gaisuwa daga gare shi, yana hamma tare da rufe bakin sa da hannu ya nufa banɗaki ya shiga, se kuma ya fito bayan ya duba yaga babu ruwa a cikin butan banɗakin, fitowa yayi yana ɓata rai, se wani murza ido yake kamar sabon barawon da aka kama, ɗaga kansa keda wuya ya ga buta babba ata gefen da yake tsaye ɗaukan butan yayi, jin a cike da ruwa yayi murmushin jin dadi, daman beyi Asuba ba sannan ga ruwa Allah ya kawo a cikin buta, bari kawai yayi wanka sai yayi alola da sauran, se ya sa hannu ya dauka, ya juya kenan da niyyar sake shiga bandakin ya ji an kwala masa kira me cike da gargaɗi

"Sadiqu", karka sake ka taɓa mun ruwa wallahi ko kuma inci ubanka" juyar da kaina nayi ba zata na hango wata kyakkyawar budurwa da baza ta wuce shekara sha bakwai ba tana wani uban sauri tana zuwa ta buga masa dundu ta kwace butan daga hannun shi tayi shigewarta banɗakin ba tare da ta gaida masu girkin ba, itama daga ganin yanayin ta da kyar in tayi sallar asuban.

Mahaifiyarsa dake kan sana'ar ta ne ta miqe rai a ɓace ta kama masifa, sai caa take
"Bantan Ubancan, 'Ke Hafsa dan Uban ki meya miki kika masa wannan uban dundun, tsabar mugunta da rashin da'a? Ke ko kunya bakiji ba a gabana Ni mahaifiyar shi kike dukan sa?, mikewa ma tayi gaba-daya tabar suyan kosan ta kama zage zage, sai habaici take tayi takai minti goma tana girgiza kamar wanda aka sata rawar dole ita a dole an daki danta daidai lokacin da Hafsan ta fito daga banɗakin kenan tana murkuda baki cike da rashin kunya, tare da faɗin, "haa'a da waya aike shi ya taɓa min ruwana tsabar asara fitsarin kwance fa yayi, gardin yaro kamar wannan ace yana fitsa.." Rankwashin da tajine yasa ta yin shirun dole tare da juyawa

Ko ba'a fada ba tasan waye ne, 'haba mama me nayi da za'a rankwashe ni' Uwaki kikayi bana hana ki maida musu magana ba? Suma fa iyayen kine. Tukunna ma kin gaida su? "Çapdi jamm" ta sake fadi cike da faɗa aiko Maman ta sake buge mata bakin, aikuwa ta bata rai tana yatsina ta nufi hanyar ɗakin su ko gaida sun bata yin ba.

Tana shiga dakin nasu na karshe daga jerin ɗakunan ta hango kanwarta Jamila a kwance tayi ɗaɗɗaya da kafafu tana sharar bacci aiko ta hau bubbuga bayan ta.
"Ke Jamila ki mike ki je kiyi wanka kapin inyi Sallah kar muyi lattin makaranta kinji?"
Nan ko Jamilar ta mike ta fice a dakin da saurinta

Dayake butan da Sadiqun yayi niyyar dauka babba ne dashi take wanka wataran, to yanzun ma hakan ne ta kasance ta kwarfo ruwan ta daga rijiya ta ajiye a bakin banɗakin kafin taje ta dawo shine ta tarar da shi yana shirin dauka mata

Idar da Sallan ta yayi daidai da shigowan Jamilar dan se da tayi gewaye gewaye kapın tayi sallan, nan kuwa Jamilar ta hau shirya wa, da shike ita tun asubar tayi Sallan, Hafsan ne daman taki ta tashi tayi.
Nan da nan suka sanya kayan makarantar su sai gasu fes
Zama sukayi suna jiran Mama ta kawo musu kalacin su, suka jiyo Dije da Azima, wadanda suka kasance sa'annin Hafsan ne, ƴaƴan kishiyoyn Mama, suna cacar baki, akan kayan makarantar su.
_______
"Yanzu fi sabilillahi wannan yaron har yanzu yana fitsarin kwance? Caa nake ya dena ashe be dena ba
Aiko nine daidai kai dan ubanka
daga yau asuba tana yi zanzo in kwara maka ruwan sanyi, dan iskan yaro kawai" Yaya Lawan kenan (yayansu babba) da ya shigo cikin gidan, sai wani cika yake yana batsewa, kuma kullum idan ya zo sai ya maimaita abun da ya fada amma be taba aikatawa ba.

"Salamu alaikum"
Maigidan Malam Sule mai rini ne yayi sallama yana tuntube da kwanuka, daga ganin yanda yake sauri kamar ya fire sama zakasan mantuwa ce yayi aiko ana ganin shi akayi shiru shiko harkar gaban sa yayi, masu gaisuwa nayi masu yan noke noke nayi.
Yana gama abinda ya kawo sa ya fice a gidan.
Su Hafsa kuma Mama ne ta shigo musu da dumame, fitar da tayi dazu shine ta dumama musu. Zama sukayi sai sauri sauri suke suna ci duk dan kar suyi latti Malam Sidi ( Malamin horon su na makaranta) ya jibge su, sun fito kenan sukayi kiciɓus da su Dijen suna zage zage ahaka suka fito da misalin ƙarfe 9 suka kama tafiya hanyar makarantar tasu da take da ɗan nisa da gidan nasu

"Hafsa" Su Dukan su suka juya ganin mai kiran sunan Hafsan, aiko da gudu gudu ta ƙaraso
Kawar Hafsan ce Habibah, suna ɗan ɗasawa da itane saboda ita kadai take iya tolerating halayen Hafsan.

Habibah kece dayin latti yau? Kice yau Malam Sidi ya samu nama, Hafsa ta karashe tana dariyar mugunta, su dai su dije sai sana'ar suke wato ashar a haka su kaci gaba da tafiya

A gida kuma Baba ne ya sake shigowa yazo yace a kai masa abincin sa dakinsa, tare da yi musu nasiha akan tsafta domin da Mama tana sharewa duka tsakar gidan sukai ta bakar magana har da faɗan su akan cewa sai dai a raba kowa yana gyara sashensa, haka aka raba mama kullum tana kokarin ganin sun canza amma abu sai karuwa yake,
Sai ya zamto kawai Mama dakin ta da rumfar gaban dakin ta ne zaka ga tsaf tsaf, su Lantana kuwa tsabar ƙazanta idan suka wuce ta gefen ka harwani bashi bashi za ka ji suna yi
Wai su ahaka suke sana'ar ga shegen ƙazanta kamar me, Mama kam har mamakin masu siyan abunsu take ana suya ana fyace majina ko kaga ana tufar da yawu abun dai ba kyan gani.

_____________
Su Hafsa kuwa suna cikin tafiya suka ci karo da wani uban taro an hana kowa wucewa, gashi ba daman subi ta dayan hanyar zasu yi latti, Fadawa suka fara hangowa suna wucewa sai sukaga da mota a tsakiyar su, a hankali motar take tafiya, motar zamanin daa ce ana kiran ta da 'volkswagen' a turance, 'Hajiya ba ɗuwawu' a hausance.

Tsabar wulakanci dogarai har duka suke yi in suka ga an zo kusa da su, abun ka da mutanen da ba kowa bane yasan mota shiyasa aka taru ana ta kallo, su a zaton su Mai martaba ne ma yazo wucewa ashe Yarima ne
Su Hafsa kuma wani Uban latti sukayi har sunso su koma sai suka tuna da fitinar Malam Sidi, double case kenan aiko ba yanda suka iya haka suka jira tukunna suka tafi, Suna isa makarantar nasu kuwa suka tarar da me tsaron bakin kofa.

Yana ganin su ya kwashe da dariyar mugunta yace
"Lallai ma kuɗin nan zakuci Ubanku yau, yanzu wasu suka zo ba da jimawa ba kunga dukan da aka musu?

Hahaha Kuma albishirin ku Malam Sidi ya sayi sabon dorina mai baki shid.." ai bai kai ga gama magana ba sai ga wani jibgegen mutum sai hura hanci yake da ka ganshi ka ga basamude hannun sa rike da ƙatuwar dorina mai baki takwas
"Kuzo nan" shine abinda yace kafin Jamila ta saki fitsari


Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.


>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍




🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello 🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; Fadrees_20
Arewabooks Fadrees20

Page 2


"Kuzo nan" abinda Malam Sidi ya fada ke nan yayinda fitsari yabi ta ƙafan Jamila, karamar cikin su kenan
Aiko nan take Azıma wai ita mara tsoro tayi gaba ta tsaya ƙeƙam kanta a sama
'Gani' shine abinda tace
Ai be jira ta cewar taba ya ɗaga katotuwar dorinar ya zabga mata nan take ta zube ƙasa tsabar zafi har idanunta kakkafewa suke.
Sauran kuwa ganin abinda ya faru a take suka ja da baya, tsoro nan take ya tsarga musu duk da sunsha yin latti yana bugun su amma sun kasa sabawa, babu abinda suke sai roƙon Malam Sidi akan yayi musu rai amma bawan nan ko gezau
A haka yabi kowannensu yai musu bulala takwas-takwas wai ahakan yaji tausayinsu da suka ce an hana su wucewa ne, Jamila ce aka mata hudu dashike dukkanin su suna aji na bakwai in kacire Jamilan da take aji biyar, Hafsa kuwa nan da nan ta kullace shi a ranta, a take ta dau aniyar ramawa.
Shigar su aji suka zauna a ƙasan tabarma domin malami har ya shiga aji an fara darasi.
Malam Bala shine yake ɗaukar su Yaren Hausa, ya kasance mutum ne guntu sosai sai dan karen tsarguwa, abinda be kai ya kawo ba zai maida shi serious gashi sai dogon baki da kananun ido
Yayi musu batu akan insha'i da aka gama darasi sai ya bada aikin aji.

Kasancewar da ba kamar yanzu bane da idan yaro zashi makaranta za'a zuba masa abinci a kwano, kaga ya tafi dashi yaci a break time, Yanzun kuma sai kuna da shi ne zaka ga mutum ya dan kai kayan makulashen sa yana ci yana wa mutane yanga, Hakan ta kasance kuwa Ana cikin aikin ajin wata yarinya mai suna Zaliha ta paki idon Hafsa sai ta watsa mata ruwan maɗi akan littafin ta ai kuwa suka fara cacar baki,
'Menene yake faruwa hakane'? Malam Bala ya tambaya. Buɗan bakin Zaliha sai tace "Malam zagin ka takeyi wai kai guntu ne idan aka gwada tsayi zata iya finka, Ni kuma nace zan faɗa maka shine tace in na faɗa sai ta zubar min da maɗi na shine fa ta ɗauka ina ja itama tana ja hakan ne yasa ya zuba mata a kan takaddan ta,
Toh sanin halin Hafsa da rashin kunya yasa Malam Bala ya fusata ya sata zuba guiwoyinta a kasa, ranta a dagule tare da niyan kece raini in aka tashi take tunani har aka gama darasi Malam yafita.

Sun sake yin darrusa kusan uku kafin karfe sha biyu yayi dai dai da lokacin tashin su daga makaranta ai kuwa suna fita Hafsa ta cakumo wuyan Zaliha dambe ya kaure da kyar aka raba su,
Hafsa bata wa kowa magana ba tayi tafiyar ta gida, bayan tayi wa Zaliha jina jina ai ko babu komai dai ta rama.
Tun daga bakin layin su ta hango samarin layin su yan zaman kashe wando masu zaman majalisa suna tsallen kwado, bata kwashe da dariya ba sai da ta hango Ashiru (saurayin Azıma) yana yin nashi daban ga fadawa sun taru a gurin hannayensu da bulalai sai hura hanci suke,
Meye Hafsa zatayi in banda dariya, aiko suna haɗa ido da Ashiru ya wani duburburce ya rikice, ma'ana baya son yan gidan su Azıma su ganshi a irin yanayin nan domin idan zaizo hira har wani extra mai yake shafawa a giran sa da saman ido wai shi a dole gaye yazo yana wani babbanƙarewa shi ala dole gaye.

A zuciyarta kuwa caa take Allah ya kawo Su Azıma suzo suga Ashirun da ake mata gori akan sa yana tsallen kwaɗo yana wani sussunne kai, Addu'ar ta bata karbu ba domin su Dije ko kwana basu kusa ba, Shi kuwa baa zata yaji saukar bulala a gadon bayan shi, ai nan take ya ƙara himma,
Sai da aka musu lilis taga wata budurwa da baza ta wuce sa'arta ba ta fito daga lemar da aka kafa mata ta sha kayan sarauta kai kace Sarauniya ce, ɗaga hannu budurwar tayi alamar ya isa a kyale su
"An gaishe ki ranki ya dade, Gimbiya tace abarku, talakawa asararru" abinda wani bafade ya faɗa kenan aka barsu ita kuwa budurwar ɗalewa kan dokin ta tayi suka yi gaba.
Sakar baki Hafsa tayi har taga wucewar su kamar haɗin baki sai gasu Azıma, Dije da Jamila sun karyo kwana.
Tana ganin Azıma ta kwashe da dariya sai da tayi mai isar ta sannan ta shige gida tare da cin karo da ledoji da robobi, tsaki tayi ta nufa hanyar dakin su, sai ga Yaya Lawan shima ya fito daga nasu ɗakin dai dai shigowan su Jamila kenan

Azıma ce tace " nikam Yaya Lawan taron nan da hayaniya na menene?, mun dawo mu kaga samari sai jan jiki suke meye faru ne?
Lokacin da tagama tambayar sa lokacin su Kulu suka fito
"Wai ma yar waziri ce tazo wucewa da fadawanta shine jikinta ya bata kamar ana kallon ta aikuwa taga samari sun cika maƙil ana zaune a majalisa shine tace a hukunta mata ya'yan talakawa "Ya ƙara da faɗin " ai ni Allah ne yamin alam nashra tare pa muke zaune kamar an tsikare Ni na mike nayo gida fitowa ta zan koma kenan naga abinda yake faruwa shine na tambaya aka gayamin, kar ku so kuga Ashiru yana tsallen kwaɗo" ya ƙarashe maganarsa yana dariya
Meye Hafsa zatayi in banda dariya
Ahaka Lawan ya fice daga gidan a cewar sa zai tafi jaje ne
Mama Lantana kuwa iya ƙuluwa ta ƙulu.

_________

Gidan dai kowa fitinar sa daban, ita Hafsa tayi degree a harkar rashin kunya da iya dambe, ko da kuwa da namiji ne, ita kuma Jamila bata da hayaniya, su kuma su Dije sai aikin ashar da suka yi masters akan shi, dalilin hakan yasa aka kore su daga makarantar allo, domin sun fitini kowa musamman Hafsa.

_________
Malam Sule mai rini haifaffen garin Bauchi ne nan cikin unguwar Wunti in da a yanzu ma yana unguwar tare da iyalan sa, a lokacin Bauchi bata zama jiha ba amman babban birni ce kuma sarauta ita ce ake ji da ita a lokacin, da yake karatun boko ma bai iso ba yawancin mutane sunfi bada himma a makarantar allo ko kuma a kai yaro koyon sana'a zuwa garuruwa daban daban to hakan ce ta faru da Sule aka kai shi Almajiranta da yayanshi Musa da shike su uku aka haifa sai kanwarsu ƙarama Hansatu.
A haka suke Almajiranta har girma ya riske su bari kana suka samu sana'a,
Musa shi sana'ar fata yakeyi, shi kuma Sule da kyar ya samu aiki a fada a matsayin dogari haka dai rayuwa tayi ta tafiya har Musa yayi auren fari yaransa biyu Salisu da Ramatu sannan ya kuma neman wata a lokacin shi kuma Sule ya haɗu da Kulu har an saka rana anyi komai sai ga wata wai ita Lantana daga ƙasar Gombe.

Tana zuwa ta haƙiƙance akan cewa duk duniya babu wanda take so kamar Sule a haka aka haɗa auren kasancewar Lantana marainiya ce, lokacin ne Sule ya gane akan su mugayen ƙazamai ne yayi taƙaici da hakan matuƙa, bayan auren da shekara Kulu ta haifi Lawan sai bayan shekara biyu Lantana ta samu ciki itama kuma Kulun tana da çıkın lokacin, domin har Kulu ta fara ma Lantana gorin rashin haihuwa
Sai da Lantana ta haifi Adamu da sati biyu Kulu ta haifi Garzali sai da suka sake shekara biyu kafin Kulu ta haifi Fati ita kuma Lantana ta haifi Halime.
Alokacin ne wataran Sule yaje fada ya gama aikinsa a hanyar sa na fita ne ya hango wata kyakkyawar yarinya bazata wuce shekara sha takwas ba. Jikinta kuma kayan bayi ne.

A zaune ya hango ta tayi tagumi nan take tausayin ta ya kama shi ya karasa gurin ta tare da yi mata sallama
Barkanki"
"Barka dai, Ya tsinci muryar ta da cewa
Meya sah meki?
Kawai ta pashe da kuka

Shin wacece yarinyar?

Ban yadda wani yayi amfani da wani sashe na littafin nan nawa ba, ba tare da amincewa na ba, domin zan dauki tsattsauran mataki akan hakan, dan haka a kiyaye.

Idan littafin nan kake nema, complete ko wani sashe toh ga nan numbern waya na a sama duk me san yayi min magana, ya min ta nan.

Da fatan an fahimta.
Nagode.



>>>>>>>>>>>>>💻🖋️🤍







🤴*YARIMAN HAFSA.....!!*🤴
(A 1950's Royal Love Story)




Na Fatima Idriss Bello 🖋️🖋️
09020588802
Wattpad; fadrees_20
Arewabooks Fadrees20



Page 3

Nan take sai ta fashe da kuka
"Kaje kaima kar na jawo maka" Abinda tace kenan
Haba baiwar Allah me yasa meki? Ya tambaye ta
"Duk namijin da ya nuna damuwarsa akaina sunansa 'GAWA'"
Ai ko Sule dajin haka sai yayi baya jikinsa ya soma ƙyarma nan take ya soma jan addu'ar da yazo bakin sa sai da ya ɗanji nutsuwa sannan yace, '
me kike Nufi da haka?
"Ni bansan koni wacece ba, nidai kawai nasan nabuɗe idona na tsinci kai na acikin Masarautar nan a matsayin baiwa, kuma mutum uku dogarai sun dade da zuwa barzahu saboda na farko ya nuna yana son aure na, a daren ya margaya sauran biyun kuma don sun nuna tausayi akai na kawai, kamar yanda kake ƙoƙarin yi a halin yanzu suma suka fece" sai kuma ta sanya kuka
Taci gaba "ina cikin mawuyacin hali a cikin masarautar nan kowa hattara ta yake yi wai don.... "
Ai bata ƙarasa ba ya rufe mata baki da hannun shi yana rarrashin ta
"Ni zan aure ki"
Ai a take ta mike tsaye
Karki damu Gobe ma haɗu'
Da haka ya tafi,

Kasancewar shi almajiri a da sai ya kwana yana addu'o'i da ikon Allah babu abinda ya same shi amma yayi mafarkai barkatai
Da sassafe ya tara matan shi akan ya faɗa musu zai ƙara aure
Ai da jin haka suka fara ashar dalilin da yasa bai faɗa musu da dare ba da sun hana shi baççi
Bai saurari ko wacce ba yayi sammako zuwa gidan yayanshi ya faɗa masa
Dajin haka yace sai ahaɗa da na ƙanwarsu Hansatu
Hakanan yaje ya samu yarinyar jiya da ya naɗa wa suna Zenabu
Tayi matuƙar mamakin ganinshi da rai
Ya tambaye ta in ta yarda ta aure shi tare da faɗin yana da mata biyu da yara
Aiko ta amince, yaje ya samu Sarkin gida suka gama zance sati biyu da ya zagayo aka daura musu aure ta tare tare da ƙanwarsu Hansatu. Besha wahalar shawo kan Sarkin bayi da Sarkin gida ba domin akan a 'yantata ba kasancewar ta ƙi kowa a cikin masarautar

Ai babu irin habaicin da su Kulu basa mata da sukaga bata kula su ne yasa suka sanya mata Salama
Shekara da ta zagayo Kulu ta haifi Dije
Ranar suna ta zo masu Malam sule da Malam Musa da baqin ciki Sanadiyyar rasa qanwarsu Hansatu da sukayi, tazo haihuwa ita da abinda yake cikin ta suka rasa rayukansu a ranar kuma Zenabu ta haifi yar ta ranar bakwai aka maidawa yarinyar sunan Hansatun ana kiran ta da Hafsa wani Sati me zuwa kuwa Lantana ta Haifi Azıma

Shekarunsu biyu Zenabu ta qara haifan mace aka sa mata Jamila daga nan haihuwa ta tsaya mata
Shekarun Jamila biyu Lantana ta haifi Sadiqu. Wannan kenan

Suna nan suna zaman su har turawa suka zo da karatun boko aka saka su Lawan a makaranta duk da Kulu bata so hakan ba.

Shekarar su Halime sha bakwai bakwai akayi musu aure. Fati aka haɗa ta da Salisun kawu Musa, Halime kuma dama da saurayinta, Lokacin Ramatu yar kawu Musa ta daɗe da yin auren ta.
Lokacin su Garzali sun daɗe da barin makaranta ma, su kulu sun hana su zuwa
Shi Lawan yana yar sana'ar sa ta hannu amma yana zama a majalisa Garzali kuma shida Adamu an kai su Birnin Gombe dan yin Sana'a Adamu yana zuwa wataran, amma Garzali kam sai ya ga dama yake zuwa yanzu haka ma ya kusa shekara açan amma har yanzu bai zo ganin gida

Please Login or Register in order to submit comment