Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 01

بسم الله الرحمن الرحيم.


__ Sassanyar iska ke tashi, wadda ke haɗuwa da ƙamshin jar jiƙaƙƙiyar ƙasar da ke malale a tsakar gidan. Hakan ne ya sa iskar da ke shiga hancin duk mahalukin da ya shaƙe ta, ta kasance daddaɗa. Ruwa ne kwance a wani gefe na tsakar gidan, ya yin da wani wajen ƙasar ce kawai a jiƙe. Wanda hakan ze alamta maka cewa ba a daɗe da ida ruwan sama ba. Tana zaune a kan kujera 'yar tsuguno, gaban murhu da tukunya ke ɗore a kai tana fifita wutar da ke ƙoƙarin mutuwa. Sautin sauke numfashin da ta soma jiyowa daga cikin ɗaya daga cikin ɗakunan da ke gidan ne ya sanya ta dakatawa daga fifita wutar da take. Ta sake ƙanƙance idanunta da suka ɗan sauya kala saboda yajin da ke shiga cikin idanunta, na icen da ke ci cikin wuta.

"Wayyo Allah! Wayyo.." Ta sake jiyo sautin a wahalce. Ba ta san lokacin da ta jefar da mificin hannunta ba, ta miƙe da sauri har tana ƙoƙarin tuntuɓe, ba ta tsaya ba ta yi gaba kai tsaye zuwa cikin ɗakin. Hannu ta saka ta yaye yalolon labulen da ya hana ta ganin abin da ke faruwa cikin ɗakin, har sai da ta shiga. Ta sauke idanunta a kan motsatstsiyar katifar da ke cikin ɗakin. Matashiyar budurwa ce zaune a kan katifar tana sauke numfashi a wahale, hannunta ɗaya dafe da turtsetsen cikin da ke gabanta, ya yin da ta yi amfani da ɗayan hannunta wajen damƙe gefen katifar da wani irin ƙarfi da ba ta san tana da shi ba. Idanunta a rufe suke gam tana jujjuya kanta cikin tsananin azabar naƙuda. Jin alamar an shigo cikin ɗakin ne ya sanya ta buɗe jajayen idanunta ta yi ƙarfin halin kallon matar da ta shigo. Cikin raunanniyar murya ta ce

"Dada marata, Dada zan mutu.." Ta ƙare maganar tana yarfe hannunta da ta ɗauke daga kan cikinta. Duk da ba ta da tabbacin ko Dadar za ta taimaka mata, ko za ta bar ta ne ba tare da ta yi yunƙurin taimaka mata ba. Murmushi wadda aka kira da Dadar ta yi tana faɗin

"Alhamdulillah!" Ta ƙare maganar tana maida idanunta kan Inna-wuro. A ranta tana ji kamar ta taka rawa don tsananin murna. Cikin ƙarfin hali tare da danne duk wani abu da take ji tace

"Sannu Inna-wuro." Ta faɗa tana ƙarasawa kan katifar. Duk da tsananin azabar da Inna-wuro ke ji hakan be hana ta kallan Dadar ba, ta lumshe idanunta tana jin wata ƙwalla na tarar mata a cikin idanunta. Duk wani ƙoƙari da za ta iya dan ganin Inna-wuron ta haihu lafiya Dadar ta din ga yi. Kasancewarta Ungozoma ya sa ba ta nemi wani taimako ba, ko yunƙurin kiran wani dan a kai ta asibiti ba. Ita dai burin ta kawai Inna-wuro ta haihu lafiya, ko da abin da ke cikinta be fito lafiya ba wannan ba damuwarta ba ce. An kwashe wajen minti 30 kafin wani dattijon bafulatanin mutum ya shigo cikin gidan da sallama ɗauke a bakinsa. Dada ba ta iya amsawa ba saboda cigaba da taimakawa Inna-wuro da take.

"Kina ina ne Uwar gida." Ya faɗa yana zame hular kansa. Shirun da ya ji ya sanya shi ƙarasowa cikin gidan, yana dab da ƙarasawa Dada ta fito. Ya kalle ta sosai yana nazarin yanayinta. Tun kafin yace komai ta ce

"Naƙuda ce ta tasowa Inna-wuro." Zaro idanunsa ya yi, da sauri ya kai hannunsa yana lalubar aljihunsa.

"Bari na kira..."

"Ka kira wa?" Ta katse shi da faɗin hakan bayan ta tattaro girar sama da ƙasa ta haɗe waje ɗaya. Dakatawa ya yi daga ƙoƙarin lalubo wayarsa da yake, cikin 'yar rikicewa ya ce

"A'ah.. wai da a kira shi a sanar da shi ta soma naƙuda." Numfashi Dada ta sauke har lokacin ba ta saki fuskarta ba, ta ce

"Toh ga ka ga wayar nan ai sai ka kira." Daga haka ta juya ta koma cikin ɗakin. Fahimtar gatse take masa ya sanya shi bin ta da kallo kawai ba tare da ya sake yunƙurin taɓa aljihunsa ba. Daidai lokacin da ta saka ƙafarta cikin ɗakin, ya yi daidai da lokacin da kukan jariri ya cika cikin ɗakin. Da sauri ta ƙarasa, cikin mamakin yadda haihuwar ta zo wa Inna-wuron a sauƙaƙe duk da kasancewa ta fari ce. Kukan jaririn da take ji be sanya ta kula inda yake ba. Sai ƙarasawa da ta yi cikin tashin hankalin da ya rufto mata lokaci guda. Ta sanya hannu ta riƙo Inna-wuro da tun da babyn ya fito ta zube a wajen ba ta sake motsawa ba. Idanunta da ke motsawa a wahalce ne ya sanya Dada sakin ajiyar zuciya. Sai a lokacin sannan ta miƙe ta saka hannu ta ɗauki babyn da ke ta rusa kuka. Ta sanya shi cikin zani ta ajje gefe. Farawa ta yi da gyara Inna-wuro, cike da kulawa kamar wani ƙwai haka take kula da ita. Abin da ya saka Inna-wuro sakin baki tana kallanta cike da maɗaukakin mamaki. Sai dai ba ta ce komai ba, ta cigaba da bin komai da ido.


.. "Zan iya sanar da shi abin da aka samu?" Baffa da ke zaune a kan kujera ya faɗa yana kallan Dada da ta fito daga cikin ɗakin.

"Hohoho.. Wai ni kam Malam me ye damuwarka da wannan haihuwar ne? Yoh har wani ma abin alfahari ne a wajenmu da yarinyar nan ta haifi mace? Ka dai san a kan yarjejeniyar da aka rabu, saboda haka don Allah ka dena mini maganar nan. Ka bar ni in ji da abin da nake ji."

Lumshe idanunta ta yi lokacin da kunnuwanta suka gama jiyo mata maganganun Dada. A hankali ta kai kyawawan fararen idanunta kan babyn da ke kwance cikin zani tana bacci. Hannunta ta kai ta ɗauke ta, ta ɗan gyara zamanta tana runtse idanunta. Murmushi ne ya suɓuce mata a kan fuska lokacin da idanunta suka sauka a kan kyakkyawar farar fuskar jinjirar da ke bacci cikin kwanciyar hankali, tana sauke numfashi a hankali. Kafe ta ta yi da idanunta tana jin wata irin ƙaunar ta na ratsa duk wata gaɓa ta jikinta. Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci idanunta suka fara juyewa zuwa ja. Ƙalubalen da ke cikin rayuwarsu shi ya soma faɗo mata. Shin ko ita ɗin mahaifinta ze yi farin ciki da zuwanta duniya? Shin mahaifinta ze karɓe ta kamar yadda kowanne uba ke karɓar ɗan da ya haifa? Shin akwai mutanen da ke farin ciki da zuwan wannan halitta duniya ko kuwa ita kaɗai da ta haife ta ita ke farin ciki da zuwan ta? Sabuwar ƙwallar da ta tarar mata a idanu ita ce ta sanya ta lumshe idanunta, tana jan kyakykyawar babyn ta rungume a ƙirjinta. Wani irin sanyi na ratsa ta. Soyayyar ɗiyarta na shigar ta.

Kwana 5 da haihuwar jikinta ya soma komawa daidai. Ta ji daɗin jikinta ainun. Babynta ma da yake tana samun isasshen abinci ya sanya ta yi kyau abin ta. Duk a tsawon kwanakin nan ta ɗauka za ta ji Dada ko Baffa wani ya ce mata Alhaji Baita ya kira ta a waya dan jin lafiyarta. Sai dai har aka shafe kwanaki ba ta ji daga gare shi ba, duk da dai ta san da ma hakan kan iya faruwa.


... "Ya ce a ɗauki kuɗin rago cikin kuɗaɗen da yake turowa, sannan ya kuma ba ki wuƙa da nama a kan zaɓar wa 'yarki suna. Ba shi da matsala da hakan, saboda haka wane suna za a raɗa mata?" Baffa ya faɗa yana kallan Inna-wuro. Wani irin yawu me ɗaci ta haɗiye, karyayyiyar zuciyarta na sake karyewa. Tausayin rayuwar ɗiyarta na sake kama ta. Kenan har rashin muhimmancinta, da kuma son nuna be damu da abin da ta haifa ba ya kai ya kasa sakawa 'yarsa suna? 'yar da ya haifa da cikinsa? Ta ja wani numfashi da ƙyar kafin ta ce

"Baffa ka saka mata duk sunan da ya maka." Ta faɗa cikin ƙarfin hali, tana jira ta ji amsar da za ta fito daga bakin Baffan. Kamar yadda ta tsammata kuwa sai cewa ya yi

"A'ah, kin ga ni fa cewa na yi ki faɗi sunan da za a sanya wa yarinya. Me ye garin gamina da ita kuma? Ubanta ma be saka mata suna ba sai ni karan kaɗa miya?" Ya ƙare yana nuna kansa. Daidai lokacin da Dada ta fito daga cikin ɗakinta tana kallan su. Ta taɓe baki kafin ta wuce banɗaki. Dalili kenan da ya sa ba ta son cika magana da Baffan nata, don abubuwa da dama kan zo cikin ƙwaƙwalwarta, tana sake ji duniyar na mata zafi, komai yana sake juye mata saboda halin da Baffan ke nuna mata. Baffan nata da be daɗe da sauyawa ba.

"DANEEN, Allah Ya raya ta da imani." Ta faɗi abin da daga shi har Dadan suka kasa faɗa tun da ta haihu. Tana gama faɗa ta miƙe.

"Ameen." Baffa ya faɗa. Ita kuma Inna-wuro ta wuce cikin ɗaki. Daidai lokacin da babyn ta soma kuka, ta ƙarasa da sauri tana sakin murmushi ta ɗauke ta. Ta yi amfani da hannunta ɗaya wajen ɗauke ƙwallar da ta sakko mata a kan fuska.

"Ya isa haka Shalele." Ta faɗa tana ƙarasawa ta zauna, ta shiga shayar da yarinyar tana kallan kyakykyawar fuskarta da kullum kyawunta sake fitowa yake yi. A duk lokacin da za ta kalli fuskarta sai ta tuna abubuwa da dama, abubuwan da suka faru a baya, da ma waɗanda take hasaso tabbas za su faru nan gaba, idan dai ba Allah ne Ya taƙaita ba.

A ranar aka yanka rago aka kuma sanya wa yarinya suna DANEEN. Haka Inna-wuro ta cigaba da kula da ɗiyarta cikin kulawa, so da kuma ƙauna. Ta gefe guda kuma Dada na sanya ido a kan duk wani motsinta, sai dai ga mamakinta ba ta taɓa damuwa da ya Daneen ta tashi ba, ya ta kwana, kullum burinta ta san lafiyar Inna-wuron. Dalili kenan da ya sa ta maida hankali sosai wajen kula da 'yarta, tun da dai ita kaɗai ce ke son rayuwa da kuma lafiyarta.


.. Cike da damuwa ta ɗauki Daneen ta taɓa jikinta da ya yi zafi zau kamar wuta. Ta runtse idanunta tana jin duk jikinta babu daɗi, ƙirjinta har wani bugawa yake saboda tsoro. Kuka yarinyar ke yi sosai, Inna-wuro na rarrashinta. Tun tsakiyar dare har sai wajen asuba kafin zazzaɓin ya sauka. Sai a lokacin sannan wani wahalallen bacci ya kwashe ta. A hankali ta sauke ajiyar zuciya tana kafe Daneen da idanunta. Tausayinta na kama ta. Addu'a ta karanto ta tofe ta da ita, ta ɗan ja zani ta sake lulluɓe ta da shi tana addu'ar Allah Ya sa kar zazzaɓin ya sake dawowa.

.. Dada na tsakar gida tana dama kunu lokacin da ta fito daga cikin ɗakin, Baffa kuma na kan kujera suna hira da Dadar. Ƙarasawa ta yi a hankali ta tsuguna, ta gyara kwanciyar Daneen da ke hannunta ta ce

"Baffa don Allah alfarma nake nema a wajen ku." Ta faɗa tana jin ƙirjinta na bugawa, duk wani fatanta a ce su amince da abin da za ta faɗa. Ba tare da ya ce komai ba ya ɗaga kai ya kalli Dada da ta juyo tana kallan Inna-wuro.

"Me ya faru?" Dada ta faɗa cikin tsare gida. Sauke numfashi ta yi tana tunanin ta inda za ta fara. Sai dai ta yi ƙarfin halin soma faɗin

"Don Allah Dada ku taimaka ku kira mini shi a samu a kai yarinyar nan asibiti. Wallahi kullum da zazzaɓi take kwana cikin dare. Kun ga har ta fara ramewa wallahi." Ta ƙare tana sauko da Daneen daga kan kafaɗarta. Ba tare da kowannen su ya ce komai ba, Dada ta kai hannu goshin yarinyar ta taɓa. Ta ja tsaki kafin ta soma faɗin

"Maƙaryaciyar banza, ina zazzaɓin yake a nan? Kina jin jikin yarinya sanyi ƙalau ki ce zazzaɓi? A'ah asibiti ne a kanta." Girgiza kai Inna-wuro ta yi ba tare da ta kalli Dada ba ta ce

"Wallahi da gaske nake Dada. A kwanakin nan kullum cikin dare da shi take kwana, ko bacci ba ta iya wa sai ya sauka. Toh ina tsoron kar wani abu ya faru kuma."

"Ki ji nemawa kai bala'i kuma.." Dada ta faɗa tana riƙe haɓa.

"Kin ga ke.. Inna-wuro, maza koma ɗaki ki zauna tun da dai babu zazzaɓin. Yoh ki je ma ki cewa likitocin me tun da babu zafi jikinta? Ki zauna duk sanda zazzaɓin ya dawo sai a san abin da za a yi." Baffa da tun ɗazun be ce komai ba ya faɗi hakan. Ba ta sake cewa komai ba, sai miƙewa da ta yi a sukwane, jikinta a matuƙar sanyaye ta saɓa Daneen a kafaɗarta ta wuce ɗakinta.

"Ko dai a kira shi a ji ta bakin nasa ne?" Baffa ya faɗa bayan ya ga shigar Inna-wuro ɗaki. Da sauri Dada ta juya ta kalle shi

"Wai ni kam manta yadda aka yi da shi ka yi? Dududu kwana nawa ya rage ta bar gidan nan? Idan mun yi haƙuri da kansa fa ze zo ba sai mun kira shi ba. Kamar yadda aka yi da shi wata biyu ciff bayan haihuwar, ina da tabbacin ba ze ƙara ba. Toh ni dai kar na sake jin kana wani zancen kiransa. Mu kira shi mu masa me? A'ah don Allah."

"Toh shi kenan Uwar gida, ai komai kika ce ya zauna." Ya ƙare yana murmushi. Ita ma murmushin ta yi tana maida hankalinta kan kunun da ke hannunta a cikin kofi.

.. Cikin ikon Allah kwanakin da suka biyo baya Daneen ba ta sake kwana da zazzaɓin ba. Farin ciki kamar me haka Inna-wuro ta ji, ta din ga gode wa Allah tana cigaba da kula da 'yarta. Bayan wasu kwanaki ga maɗaukakin mamakinta sai ta ga Dada da kanta ta soma gyara ta. Magunguna kala-kala, da na sanyi da na gyara jiki haka ta din ga ba ta. Ita dai jiki a sanyaye haka take bin Dadar, don ba kirki ne da ita ba. Ba ta ƙi ta ci mata cin mutunci ba a kan ko mene ne.


... Tana zaune a cikin ɗakin, hannunta ɗauke da Daneen da ta yi wayo sosai. Ta ƙara kyau, jikinta ya murje matuƙa. Ita kanta Inna-wuron ta ƙara wani irin kyau, don sosai jegon ya karɓe ta, ta murje ta yi kyau abinta. Tun ɗazu take jiyo hayaniya daga tsakar gida, sai dai ba ta yi ko da yunƙurin fita ba ne, tana cikin ɗakin tana hira da ɗiyarta.

"Inna-wuro! Inna-wuro." Ta jiyo muryar Baffa daga tsakar gida. Da sauri ta miƙe, sai dai cike da takatsantsan, saboda Daneen da ta fara bacci. Ta kwantar da ita a hankali tana sake jin kiran da Baffa ya yi mata har cikin kanta. Cikin ruɗewa ta amsa tana miƙewa ta fice, hannunta ɗauke da ɗankwalin atamfar jikinta.

"Na'am Baffah." Ta sake faɗa daidai lokacin da gama fitowa daga ɗakin. Mummunan ganin da ta yi, shi ne ya sanya ta dakatawa. Take zuciyarta ta soma harbawa lokacin da idanunta suka sauka a kan Alhaji Baita, da ke zaune kan wata kujera, ya yi shirim. A ƙalla a shekaru ya ba wa 40 baya. Don a haife ya haifi Inna-wuro, wadda take da shekaru 18. Sai dai ba kowa ba ne shi, face mijinta, mahaifin abin da ta haifa. Mutumin da kwata-kwata ba ta so ƙara ganin fuskarsa a rayuwarta ba, ko don saboda nunawa da ya yi ƙiri-ƙiri ba ya son abin da ta haifa. Sauke idanunta ta yi ƙasa, tana ji duk jikinta na yin sanyi, ko'ina na jikinta ya ɗauki rawa. Ba ta san lokacin da ta zube a wajen ba, tana jin wata irin ƙwalla na taruwa a cikin idanunta. Shi kuwa Alhaji Baita, tun da Baffa ya soma kiran sunan Inna-wuro ya kafe ƙofar ɗakin da idanunsa, har zuwa lokacin da ta fito. Ya kafe ta da jajayen idanunsa, gaba ɗaya hankalinsa na tafiya kan jikinta. So yake ya ga ko akwai wani canji da ze gani a jikinta. So yake ya ga ko ta sauya daga ainahin Fatima, me kyau, me diri, wadda ta haɗa duk wani abu da yake buƙata a wajen mace. Don kuwa ko daidai da canji ɗaya ya gani a jikinta, ko raguwar kyawunta, ko kuma yamutsewar wani sashe na jikinta, toh tabbas a wajen zai sakar musu 'ya ba tare da an je ko'ina ba. Wannan rawar jikin da duk wani abu da suke ba ze yi tasiri a wajensa ba...



Toh Alhamdulillah, bayan wani lokaci yau Allah Ya sake haɗa mu cikin wannan tafiyar, fatan za ku karɓi wannan labarin da hannu bibbiyu kamar yadda kuka saba. Ina faɗa muku zazzafar tafiya ce, me tsaya wa a rai. 😍❤️

*♡☆DANEEN☆♡*

Zahra Yusuf (Mhiz Innocent)

Mikiya Writers Ass..

Book 1
Pg 02

__ Sai dai ga maɗaukakin mamakinsa, sai idanunsa suka ganar masa tamkar ma sauya masa Fatiman aka yi. Ta ƙara kyau, ta wani irin murje. Duk da da ma Fatiman ba baya ba ce wajen kyawun jiki, amma yanzun ta ƙara cika ta ko'ina. Ya saki murmushi har lokacin ya kasa ɗauke idanunsa daga kanta. Hannunsa ya kai ya shafa kumatunsa kafin ya lumshe idanunsa yana sauke wani gajiyayyen numfashi.

"Ina kwana?" Inna-wuro ta yi ƙarfin halin faɗin hakan, saboda wata uwar harara da Dada ke jefa mata kamar idanunta za su faɗo ƙasa.

"Ahh lafiya ƙalau Fatima." Ya faɗa yana murmushi, kafin ya ɗora da faɗin

"Ya kamata mu tashi mu tafi koh?" Ya ƙarasa maganar har lokacin yana kallan Inna-wuro. A hankali ta ɗaga idanunta da suka yi laushi ta kalli Baffah, sai dai maimakon idanunta su faɗa cikin na Baffah sai suka faɗa cikin na Dada. Tana shirin kautar da kanta ta jiyo muryar Dada na faɗin

"Ai kam dai ya kamata.. Ka ganta nan ta yi kyau abinta, ai tun jiya na gama gyare maka ita tass, kawai tafiya za ku yi babu wani ɓata lokaci. Malam ɗakko kayan Inna-wuro da na shirya mata cikin jaka." Kallon Baffahn da ya tashi zungwui-zungwui Inna-wuro ta yi, tana mamakin jin wai har an haɗa mata kaya amma duk ba ta sani ba. Toh yaushe? Kuma tana ina hakan ta faru?

"A'ah, dawo ka yi zaman ka. Ba sai an ɗauko komai ba, ni da ma Fatima na zo ɗauka ba wani abu ba." Alhaji Baita ya katse Baffa daga yunƙurin shiga ɗaki da yake. Sai ya juyo yana faɗin

"Kai dai kullum ba ka gajiya da ɗawainiya. Toh madallah." Ya ƙarasa maganar yana murmushi, lokaci guda kuma yana neman waje ya zauna. Miƙewa Alhaji Baita ya yi yana gyara zaman babbar rigar jikinsa, ya saka hannu ya zaro kuɗi a aljihunsa ya dire a gaban Dada yana faɗin

"Ta same ni a mota." Daga haka ya juya don ficewa daga gidan. Cikin farin ciki Dada take faɗin

"Mun gode sosai, Allah Ya saka da alkhairi, Ya ƙara arziƙi." Be ce komai ba ya fice daga gidan. Sai a lokacin Baffa ya kalli Inna-wuro ya ce

"Maza tashi ki wuce ku tafi, kar ki bar shi yana jira." Idanunta ta ɗaga ta kalli Baffa, kallo irin wanda take fata ya ji tausayinta, ya kalle ta da idon mahaifi, ya kalle ta da soyayyar mahaifi, ya kalle ta da wannan tausayin da yake kallan ta da shi tun haihuwarta, soyayyar nan tata da ta ƙaru a wajensa tun da ta rasa mahaifiyarta. Sai dai kashh, wannan kallan ya daɗe da zama tarihi. Wannan tausayin ya daɗe da zama shuɗaɗɗe. Baffan da take gani yanzu zaune a gabanta ba halinsa ɗaya da Baffanta na da ba.

"Ki tashi ana miki magana, kin zauna kin kafe mutane da idanu kamar za ki cinye mu. Kin tashi ne ko sai na tashi na kai ki da kaina." Dada ta faɗa a zafafe. Miƙewa ta yi a hankali tana jin yadda jiri ke ɗibar ta. Ba ta damu da hakan ba sai shiga ɗaki da ta yi, ta saɓa Daneen da har lokacin take bacci a baya. Ta ɗauki dogon hijabi ta saka. Abubuwan da ta san dole tana da buƙatar su ta tsaya ta ɗauka a gurguje sannan ta fito. Gaba ɗaya jikinta ya yi wani mugun sanyi haka ta fito, kamar ba za ta ce komai ba sai kuma ta lumshe idanunta ta ce

"Na tafi." Daga haka ba ta jira sun ce komai ba ta fice daga gidan. A cikin motar ta hango shi ya yi ƙwam a driver seat. Ƙarasawa ta yi ta ƙarasa buɗe murfin gaban motar da ya soma buɗe mata, ta shiga ta zauna. Kamar yadda be ce komai ba haka ita ma ba ta ce komai ba, ya tashi motar suka bar wajen. Sun yi nisa da fara tafiya ya kalle ta, ya saki murmushi kafin ya maida kansa kan titi kana ya ce

"Kin ƙara kyau abin ki 'yar fara tass tawa." A hankali ta ɗaga idanunta ta kalle shi, ta lumshe su tana jinjina kai, ta buɗe baki a sanyaye ta ce

"Na gode." Bai sake cewa komai ba har zuwa lokacin da suka ƙarasa ficewa daga rugar gaba ɗaya, suka miƙi hanya cikin gari. Ga mamakinta maimakon ta ga sun yi gida, sai ta ga ya yi parking motarsa cikin wani private hospital, ta juya ta kalle shi cikin son jin ƙarin bayani. Be kula ta ba sai fita daga motar da ya yi ya ce yana kallan ta.

"Fito." Ya yi maganar cikin bayar da umarni. Sake kallan cikin asibitin ta yi, ita dai ba

Please Login or Register in order to submit comment