Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
ABDUL JALAL
WRITTEN BY AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)
1.1
Bismillahirrahmanirahim da sunan Allah me Rahma me jinkai Allah kayi salati abisa shugabanmu annabi Muhammad salallahu alaihi wassalam
Bayan haka ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wataba nayishine domin nishadantarwa dkuma wa azantarwa kubiyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa
Ina maraba da shawarwari, sharhi, kokuma gyara nagode.
This is my first novel

Misalin karfe biyu na ranaa a cikin garin kaduna, lokacine da rana ta kwalle tayi zafi sosai mutane wasu na hada hadarsu wasu Kuma sun koma gefe suna hutawa, tafiya take a hankali kaman batajin zafin ranar jikinta sanye da uniform take ratsa lungunan anguwarsu harta karaso wani matsaikacin Gida dayake rukunin gidajen layin dayakasance gamayyar masu kudi da masu rufin asiri, a kofar gidansu taci karo da wata hadaddiyar mota baqa, tana ganin mortar tayi murmushi ta shiga Gida da Sauri tundaga tsakar Gida tafara sannu dazuwa kawuna kuma babana, oyoyo da kyakyawar yata kuma ya tagari Cewar wani babban mutum dake zaune a daya daga cikin kujerun wani matsakaicin palour gefensa kuma wata matashiyar matace a zaune a kasa daka ganta kaga mahaifiyar wannan yarinyar saboda kamar dasukeyi, a kasa tazube tana gaida mutumin ya amsamata cikin sakin fuska yata ya makaranta lafiya kalau kawu aniyi mana Hutu yau mungama mock zanshiga ss1, masha Allah Ashe yarinyartawa ta girma shikenan faduwa tazo dai dai da zama kishirya anjima zan koma dake zan tafi muje kimana hutun acan to kawu d fara artata juyo ta kalli mamanta mama yau zan tafi ke Kadai zaki dinga kwana mhmmm Kawai mama tace amma har ga Allah bataji dadi ba batason yarinyarta ta yi nesa da ita amma yadda Alhaji imam yke nunawa yarinyarta so bazata iya cewa a'a ba kasancewar yarinyar yar Dan uwansa ce, ita kuwa murna take koba komai kwana biyu zata huta da fadan mama.
Misalin karfe Biyar na yamma sukashigo garin kano ta dabo jalla babbar hausa, rukunin gidajen sharada NNDC quarters ananne Inda gidan alhaji imam yake, gidane babba Wanda akayiwa gini na zamani gidan yyi matukar tsaruwa, yaran gidanne sukafito domin Tarar mahaifinsu suna masa sannu dazuwa ai daganin shida wadda yake tare suka dau murna, murna farinciki ya mamayesu Nana ce tariqo hannunta tana naji dadi JALILAH Hutu zeyi dadi πŸ’ƒπŸ’ƒ ta rungumeta suka shiga cikin gidan, matar gidan da fara arta take fadin sannunku dazuwa yau munyi babbar bakuwa murmushi JALILAH tayi tazube har kasa tana gaida matar amsamata tayi Nanace tajata dakinta tace shiga ki watsa ruwa kizo musha hirar yaushe gamo,
karfe takwas na dare iyalan gidan suka hallara domin cin abincin dare, daga bakin kofa sukajiyo muryarsa kai kai kai wanake gani haka kaman wata Yar kauye nake gani cewar wani matashi dabaze wuce shekaru ashirin da biyuba yayin shigowa palourn dariya suka kamayi wuce nan wlh Niba Yar kauye bace, murmushi yayi yace to Yar birni saukar yaushe Nana tayi caraf tace saukar dazu da abbah yaje yataho da ita hakan yayi kyau Cewar matashin haka sukacigaba da hirarsu gwanin sha awa.

*****************************
Zaune yake a cikin parlour yadora qafa daya kan daya yanata busa shisha sekace salansar tifa ta hanci ta baki gefensa mp ce ke fitar da sautin kida a hankali se lumshe ido yake alamu yanayin yayi masa dadi wayarsa ce ta dau ringing yanaji har ta katse be kulaba takuma ringing ya kallah seyaga mum a jiki ya kauda kai yacigaba da busa hayaqinsa karo na hudu wani kiran Yakuma shigowa a fusace yadaga wayar what's is it ne mum kinkira ban daukaba ai seki hakura kinsan INA wani abunne haba Dan Allah 😱😱😱 jalal kazo yanzu inason ganinka akace daga daya bangaren am having rest now komene let's meet tomorrow bejira mezata kuma cewa ba ya kashe wayarsa yasata a flight mode yacigaba da babbakar hayaki qaramar wayarsa ce itama tafara ringing yaja wani dogon tsaki ya dakko Dan duba waye jeje ne akan screen din wayar dagawa yai kara wayar a kunnensa be maganaba ya danyi shiru yace karkutafi gani nan...
...............
Jalilah tawayi gari a cikin garin kano, da garin Allah ya waye tareda Nana suka Shiga kitchen suna hada breakfast sunayi suna hirar makaranta Nana CE ta dubi jalila tace sister dama kiyi zamanki a kano sekicigaba da karatun a an an kinga bani da Yar uwa mace se jimmai house girl din Ummi inajin dadin zama da ita amma ita kullum cikin yawon biki take, hmmm ajiyar zuciya jalila tayi taace idan nadawo kano mama fa in barta ita kadai a Kaduna naana bazan iyaba kam, Dama nasan bazaki yaddaba dallacan matsa kiban guri murmushi kawai jalila tayi, suka cigaba da aikin dasuke, wajenkarfe shadaya suna dakin Nana suna hira jalila take cewa gaskiya Nana garin kano tanada kyau matuka na Dade rabona da kano, ai ba kya ziyara taya zaki Sani ba kya zumunci kullum kina like da mama, kudin zuwa kuke ai hargara ni kuma ai bazuwa kuke ba dalla bari mu tambayi Ummi muje kiga gari Yar kauye kawai wuce nan wallahi kema Yaya jawwad dince ko dariya sukayi sukasa hijjabai suka fito parlour Ummi ta dubesu se INA Ummi zamuje gidansu nusaiba ne jalila ta danga gari kinsan kifin rijiyace, murmushi Ummi tayi tace to adawo lafiya akula da kai kuma karku Dade to Ummi sukasaka kai suka fita sunata hirarsu gwanin sha away Layinn shiru se kukan tsuntsaye dasuke shawagi akan manyan bishiyoyin dasuke cikin wasu daga gidajen dake unguwar suna tafiya suna hira,
a guje wata mota ta taho da gudu kaman zata tashi sama se uwar kura datake tashi kwataΒ² tukin rashin hankali akeyi galalala jalila tabi mortar da kallo Nana ta tabota yadai tab amma nana direban motan nan bashi da Rabin hankali in akasamu akasi ya bige wanifa, hmm ko a jikinsa jalila me tukin nan baya ganin kowa da kima a anguwarnan babu me fadamasa yaji haka rayuwarsa take ko iyayensa basu ISA dashiba Yaya jalal kenan abokin Yaya jawwad ne, tab amma ya akayi Yaya jawwad yake abota da irin wannan Sam halinsu be kamaba, jalila kenan kema kyafada anyi2 arabasu abu yaci tira Allah ne yahada jininsu yana matukar son Yaya jawwad, hmmm Allah y kyauta Cewar jalila Nana tabita da Ameen, haka sukaje suka dawo suna ta hirarrakinsu, wayar hannun Nana Ce tafara ringing ta daga tayi sallama jalila bata iya jin abinda ake fada a wayar se dai murmushi da Nana tayi tace sorry mun Dan fitane sister tace tazo muka fita bari mu biyo, ta kashe wayar jalila zomuje wata qawatace tazo kai wannan hutun zemun dadi gaki ga ilham mtseww kekin cika gayyar kawaye wlh ni nagaji gaskiya, Dan Allah kizo muje to shikenan muje sarkin naci.
Kofar palourn ya tura ya shiga yanufi kitchen kai tsaye ya Shiga yadakko abinci a Warmer's yana shirin fita jalal yaji ankira sunansa be waiga ba yatsaya INA ka kwana jiya matar ta jefomasa wannan tambayar yayinda take sakkowa daga kan bene ba magana nake maka ba INA ka kwana jiya juyowa ya kalleta a club yafada kansa tsaye batare da wata shakkaba jalal wato kai ko kimata baka gani kankaa tsaye kake gayamin a club ka kwana ohhh my God mum tambayata fa kikayi nagayamiki shima kuma laifi nayi I don't want the way u are treating me mum kibarni inyi abinda ya dace dani cikin daga murya da gadara yake maganar Wanda yayi daiΒ² da shigowar su jalila tundaga waje suke jiyo hayaniyar jalal da mahaifiyarsa abin yyimatukar bawa jalila mamaki itakuwa Nana ko a jikinta Dan ta saba jin irin wannan rashin ta idon da abokin yayanta yakeyi yaja wani dogon tsaki yafito waje, mommy INA wuni yawwa sannunku nana, mummy INA ilham tamin waya tazo nuni mummy tayimana da dakinta cikin damuwa ta koma sama, mukuma muka nufi dakin data nuna mana muna Shiga suka rungume juna suna murna, nana wannan sister dinkice kuna kama matuka eh kanwata ce sannu ya sunanta jalila nana tabata amsa hmm nice name thank u kawai jalila tace amma hankalinta na kan abinda tagani yau wannan Sa insa tsakanin da da mahaifiyarsa abin yabata mamaki kuma yadameta,
bayan sun koma Gidane jalila ta kalli nana tace nana gidan da mukaje dazu wlh wannan din nan bashi da tarbiyya wallahi wakenan kike nufi oho ban San sunanshiba wannan din nan me dogon hancin nan kaman tattasai tooo dariya nana takamayi tattasai ni banganeba mtseewww is not joke nana y kalli mahaifiyarsa yace mata a club y kwana yana mata shouting haka, mhmmn bakiga komaiba India jalal ne jalal ta maimaita sunan yeahp shine me driving a mortar nan dazu kafin kibar kano zakigane wayeshi bakiga komaiba, amma a haka Yaya jawwad yake abota da shi jalila ta tambaya cikin tuhuma, jalila ba se lallai hali yazo daya ake abota ba soyayya da shaquwa gamon jinine tsakaninsa da Yaya jawwad Allah ne yahada jininsu, Yaya jawwad se yasaka jalal ABU yayi amma mummynsa bata isaba, ga shaye shaye a cikinsa yawon club ba Wanda ba yayi, tabdijan nana wannan abotar bame yiwuwa bace inji jalila kaman yaya, basu dace da abotar ba wannan Sam bashi da tarbiyya Dan haka sena rabasu bashida tarbiyya Nana tirkashi!!!!!!!!!!!
More comments more typing


πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)


PAGE- 2
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

_My first novel_


Kallonta Nana tayi, ta ce
"kaman ya se kin rabasu, ina ruwanki dasu? kinga Jalila ba ruwanki dasu, Maaama ma tayi ta Hakura, Jalal ba ze iya rabuwa da Jawwad ba, bayan abokansa na banza ina ga Yaya Jawwad ne kawai mutumin kirki, kika sani ko Allah ya shiryeshi a sanadin sa? kawai muyi musu addu' a."

Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce "Nana abotar Yaya Jalal da Ya Jawad sam bata dace ba,
barazana ne ga tarbiya da rayuwar Yaya Jalal mutumin dabe ji maganar Wanda suka kawoshi duniyaba ne kike zaton ze wani shiryu sanadin wan?i yau da gobe se Allah yasha giya ya kwana club yayi sa'insa da mahaifiyarsa shi kike tunanin ze shiryu sabodaa wani aboki Sam bashi da tarbiyya Nana ."

Jalila Allah shi yasan manufar hada abotarsu duk da banbancin halayensu, kawai muyi musu addua shine mafita mukuma muyi abinda ke gabanmu."

"Nana ni kam nacji amma ban gamsu da bayanan ki ba , zanyiwa Yaya Jawwad magana,"

" to Allah yatemaka inji Nana, amma kome zakiyi karki shiga harkar Jalal."

Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce "karki wani damu Yar uwata, ni dai fatana yafita shirgin yayana, bana so yazama irinsa ya lalatamin Dan uwana,
tunda shi lalataccene ma tayashi da addu a."

"To Allah ya baki Sa' a, nima da naso hakan".

********************************

Sanye yake da kananan kaya, wando 3quater fari da Riga T-shirt itama fara, yayi kyau sosai, yasa hannu ya dauki turare ya feshe jikinsa dashi, ya dauki wayoyinsa dake kan mudubi da mukullin motarsa yafito.
Kai tsaye ya nufin inda akayi parking motoci, sekuma ya juya ya nufi cikin gidan.

yanazuwa kofar parlour ya budee ya Shiga, ba sallama ba komai fuskanan tashi a daure tam babu alamar fara'a
parlour shiru se kamshin turaren wuta dana abinci da ya gauraye parlourn, gefe kuma Ilham ke kwance kan kujera 3seater tana kallon Tv.

"keee!!"
ya fada cike da gadara ,
a dan tsorace ta dago Dan batasan ya shigo ba, "Yaya Jal sannu da zuwa"

Ta fada tana kallon sa tare da yaba kyawun da yayi acikin ranta, be amsa ba yace


" Ina matar gidan nan take?"

"matar gidan nan kuma?"
ta maimaita tana dubansa
"ba kiji bane ko kuma tsabar rainin hankaline?"

Adan daburce ta ce "ai jinai kace matar gidan nan, wai mummy kake nufi?"

" Yaushe raini ya shiga tsakanina dake ne? har nake magana kina maimaitawa, akwai wata mata a gidan nan banda itane?"
Mamakinta ne yakasa boyuwa, lallai yaya Jalal abin nasa ya girmama, mummyn tasa ma bata tsiraba wai matar gidan nan? tabdijan, amma ta dake ta boye mamakinta ta bashi amsa da
"ta fitane, taje saloon"
"mtseww" ya Dan jaa tsaki , "inta dawo ki ce ta kirani a waya, ina da magana da ita."

Bai jira mezatace ba yasa kai yafita,
"ohh God ni Ilham, yaushe Yaya Jalal ze fara sakarmin fuska ne yana kulani? kullum mutum fuska a daure Yaya Jalal whyyyy?? "

tafada tana jifa da pillon hannunta,
"I must do something!"
tafada tare da mikewa tabar parlour.

**********************************
JALILA ce zaune akan carfet tana waya da umminta,
"masoyiyya nayi missing dinkifa irin sosai din nan ummina",
"bawani nan tunda kika iya tafiya kikabarni,"
"ummina kenan kina birnin zuciyata fa",
" ke tafi can ya mutan gidan naku kowa lpy?"
"ummi garin kano ya hadu kinsan na dade banzoba zuwan yayi min dadi"
"to hakan yayi kyau",
"ke dazu wata kawarki tazo ta bani sako in gayamiki amma wayata babu caji in anjima mayi waya yanzu fita zany"'
"ina zakije kuma ummi?"
"inda kika aikeni"
"huh ummina ta kaina adawo lafiya anjima zankiraki insha Allah"
"to shikenan ki gaida ya'n uwannaki ki gaidamin da halima(Maman su jawwad) kar inkirata tazata dankina gidanne nakirata to Ummi zasuji insha Allah".

"To shagwababbiya Yar gidan Ummi wannan shagwaba haka kinfa girma JALILA Cewar JAWWAD

Murmushi JALILA tayi tare da fadin "Allah yatemaki babban Yaya ai ba a girma a gurin iyaye mussaman iyaye mata"
Murmushi yayi tare da fadin "kekam halinki yana nan baki canza ba kome mutum yagayamiki kinada amsa dai dai da abinda yace JALILA baki abun magana,
dariya sukayi gaba daya
"yace ba wannan ba tukuna yanzu dai ya studies dinki komai lafiya dai ko?"
"Alhamdilillah Yaya JAWWAD komai lafiya ina karatuna yadda yakamata,"

" to masha Allah haka akeso amma kamata yayi kiyi waec a ss2 se Asama miki admission a BUK kidawo kano gaba daya".
"Tab to umminawa fa shikenan in batta acan"
" murmushi yayi yace haba JALILA wataran fa aure zakiyi kitafi gidan miji ko me rabawa taraba (MUTUWA!!!)"
" Kaman yadda ta rabani da banana ko ta fada idonta cike da hawaye Yaya jawwad karkamin wannan fatan, idan narasa ummina yanzu wanake dashi daze soni kaman su,
abbana yatafi yabarni bana fatan ummina ta barni, nafiso in mutu in barta"
"Haba JALILA kinga share hawayenki kinji qanwata bahaka nake nufi ba yanzu idan Abba yaji furucinki na wa kike dashi baze jidadi ba Abba yana matukar sonki ya daukeki kaman yanda ya daukemu ko kinrasa kowa ni INA tare dake kanwata har abada yayanki yana tare dake duk wuya duk dadi zan kasance tare da ke".

Taji dadin kalaman yayannata mutum ne nagari me kirki tayama zata bari abotarsa ta dore da wancan sakaran yabata matashi baze yiwuba dole tayi wani Abu, "Yaya JAWWAD inason in maka wata magana....

Mamansu jawwad kuwa da tazo shigowa parlourn ta riski hirar tasu ta labe tana sauraransu abin se ya kular da ita, me jawwad yake nufi da ze kasance tare da yarinyar nan duk rintsi aikuwa baze yiwu ba, dole tayiwa tufkar hanci bazata taba bari danta ya auri jalila
ba in ma sonta yakeyi danko maqiyinta tagani ze aureta tahanashi saboda gudun bacin suna ahaka dai gata kamilar yarinya tagari me da a amma babu asali me kyau ta danyi tsaki
( 😱😱😱 tooo wata sabuwa me ummu jawwad take nufi ne)

Wayartace takama ringing Wanda yasa dole ta fito badan tagama jin hirar tasuba tare da kakalo murmushin yake Yaya da kanwarsa hira akene "wlh kuwa maaamaa, ni zan wuce zan raka JALAL wani gurine,
gaban jalila ne yafadi jin ya ambaci jalal ta dago a Dan razane tana kallonsa,
"to sekun dawo ka kula da kanka Cewar maaama",
"sisy akwai damuwane" yafada yana kallon JALILA,
girgiza kai tayi yace to sena dawo, "safe journey"
tafada a takaice yace thank u sisy maaama sena dawo to asauka lafiya Allah yasa ya amsa yafice.

Maaamace ta amsa wayarta data cigaba da ringing salamu alaikum tafada ta danyi shiru to shikenan inkin dawo da magariba zan turo su Nana su karbarmin to nagode,

********************************
Banyan sallar magariba maaama ta aiki su Nana tace su shiga gidansu JALAL zasu karbo mata sako gurin mummynsa,

da sallama suka shiga suka Tarar zata fara cin abinci, gaisawa sukayi suka fadamata Aiken
" tace to bari in dakko muku sakon" "aa tunda kinzuba abinci kigama tukuna Cewar JALILA,
Eh momy gama bari muje gurin ILHAM kafin kigama inji Nana to shikenan sekun fito.

Tana zaune a palour tana cin abinci yashigo yasamu guri ya zauna ya kalleta
"ILHAM bata gaya miki saqona ba?" "tagayamin"
tabashi amsa a takaice,
"meyasa baki kirani dakika dawoba?" nace inason magana dake "ban niyyaba" tabashi amsa

Dakin ilham suka shiga ta kwanta rub da ciki tana kallon hotunan JALAL
sallamarsu yasa tayi firgigit ta aje wayan
"yan matan maama sannunku dazuwa
"yawwa sannu" JALILA ta amsa haka kurum ILHAM intaga jalila se gabanta ya dinga faduwa tarasa meyasa,
NANA takalli ILHAM "" daddawar daki wannan zuwannaki ba yawone?"

" ke dai bari wani abu ke damuna wlh,"
" tooo menene inji Nana "
kedai bari semun hadu kawai",

jalila tunawa tayi zasuyi waya da umminta in anyi sallar magariba tabaro wayar a Gida maybe tana can tana kirana, "Nana bari inje indawo inazaki inji Nana yanzu zan dawo tafito da Sauri

"Dubai nakeson tafiya next months
kudi zaki turamin a account"

" mezakaje kayi a Dubai?"
" aa meye kuma na tambayata ina daddy yace idan INA bukatar kudi abani to mene na tuhumata kuma"

se kajira ubannaka yadawo seyabaka sangartaccen banza yaushe rabonka da makaranta Baka zuwa karewama sokake ka tsallake kabar kasar karatun ko oho ko?

"Wait please meye kuma namin fada kibarni in tsara rayuwata yadda nakeso ba ruwanki da abinda nake aikatawa makaranta ko inje ko kar inje ai bada kudinki ake biyaminba duk kin takuramin kin tsaneni ni am doubting ma if u are my biological mother 😱😱😱

"Allah wadaran naka ya lalace tur da Dan daze tsaya gaban mahaifiyarsa tana fada yana mayarwa,
Anya kana Neman albarka a rayuwarka asara ta tabbata ga me sabawa iyayensa
Gaba daya suka waigo domin ganin me maganar........

More comments more typing





πŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈπŸ–ŠοΈ
[8/31, 8:26 AM] Safiyya: 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

_ABDUL JALAL_

_WRITTEN BY AISHA HUMAIRA_
(Daddy's girl)

PAGE- 3
PART 1

_Bismillahir Rahmanir Rahim, da sunan Allah me Rahma me jin kai, Allah ka yi salati a bisa shugaban mu Annabi Muhammad (salallahu alaihi wassalam)
Bayan haka, ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wata ba, na yi shine domin nishadantarwa, da kuma wa'azantarwa, ku biyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa.

Ina maraba da shawarwari, sharhi, ko kuma gyara, nagode.

_My first novel_

Gaba daya suka waigo suna kallon inda jalila take maganar, taci gaba da fadin
"duk d'a nagari me fatan nasara a rayuwarsa, baya fad'i in fad'a da mahaifiyarsa wannan ba halin d'a nagari bane me neman albarka,
wannan ba komaibane kake face tsantsar rashin tarbiyya!!"
ta kare maganar tana kallon cikin idon jalal,
ta kalli mummyn Jalal tace "mummy seda safe Nana ta taho da sakon"

Idanuwansa ne sukayi jawur jijiyar kansa ta daddaga ganin yarinya Karama ta tsaya tana gaya masa miyagun maganganu,
Wani yunkuri yayi da nufi ya karasa inda jalila take ya hukunta ta

mummy tasha gabansa ta rikeshi gam, duk da ta danji ba dadi da Jalila takira Jalal Mara tarbiyya amma ta dake tare da fadin

"Karka kuskura ka tabata abinda tafada gaskiya tafada kadan kagani Indai haka zakacigaba dayiwa rayuwarka, indai zaka cigaba da gayamin maganganunu daka gadama kana wuakantani agaban mutane."

fizge hannunsa yayi da karfi
"kicikani wallahi sena kakkarya yarinyar nan ni zata gayawa wannan maganganun wallahi sena koyamata darasin da harta mutu bazata mantaba,"
Da gudu jalila ta ruga ta fice daga palourn.

hannunsa ya fizge daga cikin na mummy ya rufa mata baya a zuciye, amma kash kafin ya fito harta bace kaman walkiya yanemeta yarasa, har bakin gate yafito amma be ganta ba, yanufi dakin me gadi Yakama buga masa kofa iya karfinsa,
a sukwane me gadi ya fito babban mutum amma haka ya zube agaban jalal jiki na bari "ranka ya dade...." Begama ba JALAL ya katseshi

"kaii yarinyar da ta fita yanzu INA tayi," jalal ya katseshi

"Ranka ya dade sallah nakeyi banga fitar kowa ba"
" shut up!!! Useless man Sam bakasan aikinkaba dakiki kawai,"

A fusace ya shiga part dinsa zuciyarsa na tafasa, he wish Yakama yarinyar nan da ya nuna mata waye

Please Login or Register in order to submit comment