Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ai ta soke shege balle babu, tace
Babu Ya Zaid, yace good, ki shirya ynz, tace a
shirye nake sai dai brkfast yace dont worry
zamuci a chan, ta juya tace ok bari na kira
Aunty Badiyya, da sauri ya fincikota yace dont
ever mention her name to my face again, ya
saketa ya shige daki a fusace, be son ganinta ko
sunanta be sonji, dukda suna zaune cikin gida,
shi sakinta ma zaiyi, ya dauko giyarsa cikin firij
zai bude, da sauri Maysah ta yi sauri isowa ta
amshe gwangwanin, ta kalleshi ta girgiza kai,
tace its too early Yazayd, na shirya muje koh?
haka kurum ya ji zuciyarshi tayi fes,Zabin tsoho
ta wanke mai duk wani baqincikin da badiyya ta
sashi,shi ya san ba sonta yake ba, amma
kallonta ma sashi farin ciki yakeyi, ya ce Muje
Rumah, murmushi ta sake, yace me sa idan
nace miki Ruma kike murmushi? Tace saboda
Tsoho kadai ke kirana da sunan, Yayi murmushi
shima yace kice mazajen ki kadai ke kiranki da
sunan, koh? Ta sa hannu ta rufe fuska, ya miqe
tare da riqo hannunta, oya muje Zabin Tsoho,
ta kalleshi tayi murmushi, a ranta tace nakusa
Zama zabinka.
Akan idon badiyya suka fita, hankalin ta ya
tashi, har ynz jikinta a kumbure yake, da sauri
ta lalubo wayar ta ta doka ma Bokanta kira, ya
na dauka ya fashe da daria, dama jiran kiranki
nakeyi don na san dole ki kirani, cikin tashin
hankali tace boka, na gama aiki, aikinm ya
karye, jiya zayd dukan kawo wuqa ya min da
mahaifiyata, ya kuma korata, kuma yanzu kan
idona suna fita da matarshi, ka taimakeni, boka
ya fashe da daria, yace ai ba wani taimakon da
zan miki, ni na karya asirin da na ma Zayd, ke
duk asirin dana yi a rayuwata sai dana karyashi,
sbd mutuwata nake jira, banda lafia kuma
nasan mutuwata na kusa, taimakon da zan miki
be wuce na ce miki ki je Asibiti ki fara neman
magani, dif ya kashe wayarsa Badiyya ta shiga
juya maganganun Boka, abun da ta ka gane shi
ya karya Asirin Zaid amma ba ya ga nan ba ta
gane komai ba.
Duk inda Zaid yayi da Maysah na gefenshi, sunyi

kyau matuqa, kallo daya zaka musu kasan sun
dace da juna, sai tambayanshi akeyi Dr. Zailani,
who is she? Kai tsaye yake ce musu she's my
wife..
Kaduna
Ya na dawowa ta sha gabanshi, tace wai meye
haka? Meyasa kakeson aiko min direba? Mu
kwana gida daya amma ka na baqin cikin yi man
magana? Nidai in har ka na son wani abu daga
gareni ni zaka fada mawa kar ka qara aiko min
direba, bakinta ya matse da karfi,ta sake ihu,
yace ba na hanaki rashin kunya ba? Ni tsaranki
ne? Kika qara min haka sai na lallasa ki cikin
gidan nan, ya jefar da ita kan kujera, ta shiga
murguda baki tana matsa. Kwallah, a ranta kuwa
cewa takeyi na tsani wannan Jawad din.
******
Misalin karfe 12 da rabi na dare, Jawad na
zaune na shan cofee yana rubutu kan dining,
fadila dake bacci a dakinta taji kamar an duro ta
windonta, ta miqe ta leqa, hantar cikinta ta
kada sakamakon wasu da ta gani su 2 zuwa 3 ba
ta tabbatar ba dai, da bindigogi a hannu, cikin
kidima ta wawuro wayarta ta rasa wanda zata
kira, kawai sai ta danna emergency number 911
dukda ba ta da tabaccin yana aiki, cikin saa aka
dauka cikin rudu amma a hankali ta ke sanar
dasu abun da ta gani, wani gari take? Tace
kaduna, ta ba su full address, sukace nan branch
din lagos ne amma ynzu zasuyi alarming kaduna
As soon As possible, kyarma takeyi bata son yin
kwakwaran motsi sujita, tana kallo suka daure
maigadi, suka nufo parlorn.
Ji yayi ansa mai wani abu kamar bindiga akai, ya
dagi da sauri, Inalillahi wa ina ilaihir rajiun
yace, ya daga hanayenshi sama alamar
surrender, yace kar ku kasheni, zan baku kudih
wlh, daria suka fashe dashi, we dont need ur
money rich boy, all we need is ur life, but
before den sai ka dauko mun signed contracts
din da zakayi a Niger Delta, cikin Jawad ya duri
ruwa, yace pls lets talk dis out, buge mai kai
yayi da bindiga, yace zaka dauko min ko sai na
tarwatsa kanka da harsashi na? Jawad yace Aa,
Alamun jiniyar mota na waje yaji, ya leqo cikin
kidima ya ce boss, ga masu bakin kaya, ya dago
da mamki yace ya akai suka san muna nan? Dd
u call anyone? Jawad yace ai bansan da zuwan
ku ba, kai da waye a gidan nan, da sauri yace ni
kadai ne, a zuciyarshi yana me roqon Allah kar
fadila ta fito, yes boss dama oga yace shi kadai
ne be da mata, kawai mu kashe shi mu gudu

kafin su shigo, ji sukayi ance we are advicing u
to put ur guns down, ur hands behind ur heads,
come towards us slowly, u try to make a wrong
move we fire, you are surrounded, i repeat u
are surrounded, a hankali sukayi yadda
polisawan sukace suka fita a hankali, signal
dayan yayi suka arce a guje, babban police din
yace hold ur fire, no one shoots, we need dem
alive nan suka bi su a guje, tuni suka dire,
polisawan suka bisu. Ya jawad ya yu hanyar fita
don ganin meke faruwa, Tana fitowa ta ga wani
ta window yayi saitin bayan Jawad da bindiga,
da sauri ta rugo gunshi da karfi tace
Yajawaddddd, juyowan sa yayi daidai da harbin,
jin harbin bindiga yasa sauran polisawa sukayi
gurin da sukaji harbin, Ganinta yayi kwance jini
ya malale wurin da karfi yace Fadilaaa ya rugo
da gudu ya tsugunna gaganta ya tattaro ta
jikinshi, yana kuka yace stay with me fadila,
dont leave me please, i got u, jini na bulbula
daga bakinta da qyar tace Yaa jaawaadd dif ta
dauke, cikin tashin hankali da karfi Jawad yace
Someone Help!! Ambulance! We need an
Ambulance!
_Bibilicious Biebee_
5⃣2⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by Biebee Isa💕Biebee Isa💕Da gudu wani
polive ya shigo, yana tambayan jawad sir are u
okay? Cikin tsawa yace we need an Ambulance
u stupid idiot, cant u see? Da sauri poloce din
ya kira Ambulance, cikin mintunan da basu
wuce Goma ba sai ga Motar taimakon Gaggawa,
akai akai jawad ya matsa a dauki fadila a sata
cikin mota fir yaqi sai dai shi ya daga abarsa ya
kai mota, a motar ma tana rungune dashi har
suka isa asibitin 44 dake kaduna da sauri akayi
da ita Accidents and Emergencies, aka amsheta,
Dr ya ba Jawad wasu forms yayi signing zaa ma
matarshi operation don ciro bullet din da ke
cikin kafadarta, da sauri ya sa, aka ja gadon
fadila bayan an sa mata oxygen akayi theatre
room da ita, jawad na biye a baya, zai shiga
dakin wani security da ke tsaye bakin kofar yace
sir u cant come in, jawad yace try to stop me,
ya raba ta gefenshi ya shige, nurse na ganinshi
tace sir, u cant be here wani hararan da ya
wurgi nurse din dashi ya sa ta matsa mai, Ganin
haka Dr yace let him, nd lets get to work. Haka
suka duqufa aiki kan fadila, jawad kuwa sai
Addua yakeyi Allah ya tashi kafadun matarshi,
she cant die.
Maiduguri
Isowarsu kenan, straight dakin Mamanshi Aunty

Nuratu yayi da ita, bata tunanin ta taba shigowa
sashen, duk sai taji kunya, Hanifa ta gaishe da
Aunty Nuratu da ke gyaran gadon da zayyad zai
ajiyeta, ta amsa don ba ta tuna ranar da
Hanifab ta gaisheta ba, sannu ya kafan ta amsa,
Zayyad ya shimfideta kan gado ya fita yayi
sassan tsoho, tsoho da kansa ya zo gaida hanifa
a dakin Aunty Nuratu, yayi mamakin yadda
kafar ya kumbure, ya yi umarni da Baba Hassan
da ya kira me dorin kafa. Har gida akaje dauko
me daurin kafan, hajia babba ta riga ta gyara
dakin da Hanifa zata sauka, sai ji tayi ance sun
iso har an kaita dakin Aunty Nuratu, Ashar ta
sake tace ba zai sabu ba, ta fita Aunty Abida
Maman Hanifa ta rufa mata baya sukayi sassan
Baba Hassan, Masifa ta so saukewa ganin tsoho
tsaye ya sa ta yin shiru, Zayyad ya gasiheta ta
kalleshi a gyatsine ta amsa, ya gaida aunty abida
ta amsa, Tsoho yace bari ya koma sassan sa,
tsoho na fita Hajia babba tace kai dan
wulaqanci, ban taba ganin mugu kamar ka ba,
kaje ka aje yarinya chan qasar kabilu ba uwa ba
uba ko leqen gida ba ta zo ba har watanin 8,
don mugunta, ba ka kula da ita, sai da kayi
sanadiyar turgudewarta zaka kawo mana ita
nan? Toh ba zaiyu ka ajiyeta nan ba dakina zan
tafi da ita don ta samu kulawa, ba Zayyad ba har
Hanifa sai da taji ba dadi, yace kiyi hquri hajia,
bari a maidata chan dakin naki ta juya fuuu,
tace da dai ya fi, Aunty Nuratu na zaune ba dai
ta tanka ba, Maman hanifan ma ba ta ji dadi ba,
sumsun tavi bayan mamanta, hanifa ta kalli
mijinta ciki tausayawa, a ranta tace bawan
Allah, haqurin shi yayi yawa, yace hanifa bari
akai ki dakin hajia ko? Batace komai ba, ya
dagata sama, a hankali tace kayi haquri Yaya,
murmushi yayi ya fita da ita. Ko da me gyaran
yazo dakin hajia babba akayi dashi, yace zaa ja
kafan a gyara, zayyad na gaban Matarshi, hajia
babba tace kai dalla mallam zoka fita zaa ja
mata kafa, kayi wani kane kane, hanifa ta kasa
haquri tace haba hajia, me yayan ya tsare miki
ne eyi? Tun dazu na yi shiru na kyaleki? To ba
inda zaije ta qarashe tare da murguda ma
kakan nata baki, bakih bude hajia babba take
kallon hanifa, ita da ta san hanifa ta tsani
Zayyad amma gashi ynz sai kareshi takeyi,
Zayyad yayi murmushi ya shafi kumatun hanifa
yace bari dai na jira a waje, hanifa tace no yaya,
hold me pls, Zayyad ya kalli hajia babba da har
ynz bakinta a hangame yake sbd mamakin
hanifa, yace ma mai gyaran bismillah, mai

gyara ya kama kafan hanifa ta kwallara ihu tare
da janye kafar, har cikin kwakwalwar shi yaji
ihun nan, hajia babba ta kalleshi tace ai sai ka
riqeta kar ka min tsaye a ka. Zayyad ya zauna ya
riqe hanifa, me gyara ya cigaba da jan kafar, shi
ko harda hawaye don jin yadda hanifa ke ihu.
********
Suraj da Bilkisu sunzo Maiduguri don duba
hanifa, hanifa da bilkisu suka kulle a dakih suna
firan yaushe gamo, suna ba juna labarin
rayuwarsu bayan aure, Bilkisu tace lallai hanifa
dole ki sauko ki nuna ma Yaya zayyad so a zahiri
da badini, don ya yi hquri dake ba kadan ba,
idan kuma kikace zaki tsaya jan aji wannan
fatitin zai aura, a maidaki yar kallo, hanifa ta ja
numfashi tace wlh Bilkisu na yi nadama, duk
abubuwan da nake mishi be taba fisho dani ba,
Ni so nake mu koma gidanmu, tunda naga
tsoho da mamana ban marmarin gida, naji
sauki wlh, Bilkisu ta yi daria tace kamr kinsan
for a 2nd bansan yin nesa da Yasuraj, don wlh
Ya suraj ya qware a iya love, suka chafe tare da
kwashewa da daria.
Cambridge England
Shopping tazo ita kadai don zaineema na
lectures, ta gana siyan kayab da suke buqata ta
fito wajen Mall din, ta na tafia da ledojin ta a
hannu tana jiran Cab, Ji tayi ance Islah don
girman Allah ki saurareni da sauri ta juyo ta
kalleshi, kallo daya ta mai ta ga ya rame ya yi
duhu, ganin bata ce komai ba ya sashi fara
magana kamar haka; Dalilin da ya sa na zo
london shine ina so na manta da Hanifa, ina so
cireta a raina, don nayi mata zazzafen so, sbd
son hanifa da nakeyi har pricking fingers din
mu mukayi muka sha jinin juna, its hard for me
to forget her easily, ganinki kuma na bata raina
i dont want to hurt u shisa na bar Gidan don i
dnt knw wat i will do to u idan ina ganinki a
matsayin matata, shisa na bar kasar ba tare da
na gaya ma kowa inda zani ba,don kar a tilasta
min na dawo, i chose to come to London dan
na saba da garin, i chose to be alone just to
forget hanifa nd come back to u, mu fara
rayuwar mu mu biyu, nd wallahi i forgot every
single thing abt her last 3 months, i taught my
self how to love u sincr den, ynz kece nakeso,
kece zuciyata ke tsanannin so,Son da ban taba
ma yi ma wata ya mace, wlh ko son da nayi ma
hanifa be kai kwatan wanda nake miki a yanzu
ba, wlh lokaci daya sonki ya shige ni, kece
nakeso ki zama uwar yayana, i want to spend d

rest of my life with u Islahulkhair. Tun tuni na
siya return ticket to Nigeria, flight ina in d next
two weeks, i wannid to come home to u, i want
us to start a new life, nd unfortunately i saw u
here, Islah pls ina fatan kin fahimceni da
dalilaina, Islah da idanuwanta sukayi ja, ranta a
bace, Mu'ammar din nan ya ma gama raina
mata wayau, tsaki ta buga ta juya ta cigaba da
tafia, ya biyota a baya haba hanifa, kar dai baki
gamsu da maganganu na ba, ya riqota tace let
go off me, ka raina ma kanka hankali, u
Stomped on my pride d moment u left me, i
dont want nythn to do with u jus lemme be pls,
girgiza kai yayi yayi saurin rungumeta ya na
hawyae, i cant leave without u, forgive me pls,
Islah ta ture shi da qarfi, da gudu ta qarasa
gaban motan polisawan dake parke, Mu'ammar
ya bita da ido don ganin me zatayi. Ta ce
officers, someone's bin chasing me, i dont knw
him? He's embarassing me, suka fito suka ce
We'll deal wit him, suka nufa amar suka kama
shi, daya da ga cikin officers din yace, why are u
chasing her? Ya kalleshi cike da takaicin abun da
ta mai yace she's my wife, da sauri tace he's
lying m not, officern ya kalli Amar yace keep
off, yace da Islah wenever he bothers u again u
knw wat to do, ta gyada kai tace i will call u ryt
away. Good u can go, ta kwashi ledojinta ta yi
gaba zuciyarta fal da farin ciki, Amar cike da
bacin rai ya juya beson inda yake jefa kafanshi
ba, ya nufa titi wurin tsallaka titi ne wata mota
tayi gaba dashi, chan gefen titi a kaga Amar
kanshi ya bige da wani qarfe, kan shi na zubar
da jini, da sauri aka kamshi a ka sa shi cikin
mota akan idon Islah akayi komai, taso tayi
tafiarta ganin shi ya miqe da kafarsa, amma
rashin imaninta bekai nan ba, ta tsaida mota ta
ce ya bi bayan motar chan.
Abuja
Shigowarshi kenan, ya ji wayarsa na kara, da
sauri ya ciro wayar daga Aljihu, Jawad ya gani
ya dauka, hello jawad?daga bangarensa ya na
kuka yace brother m scared? Zaid ya ce me ya
faru jawad? Me ya sameka? Yace its fadila, she's
bin shot, took a bullet for me, Inallilahi wa ina
ilaihir rajiun inji zayd, is she dead? I dont knw,
tun qarfe 11 aka fiddota daga theater room,
sunce operation din is successful amma har ynz
bata farka ba, Bro i cant loose her, Zaid cikin
rudu yace Gani nan zuwa, ka kwantar da
hankalinka, she's gonna b fine kajih. Ya shiga
ciki suka ci karo da Maysah ta fito daga kicin

yanda ta ganshi ta san cewa ba lafia,Ya zayd
lafya? Yayi dan tsaki, kana yace matar Jawad ce
a ka harba, maysah ta zaro ido, Fadila? Yazayd
is she alright? Yace shine xanje kadunan ynz,
yazayd m coming with u, ya danyi shiru, kafin
yace yi sauri ki shirya, we are leaving now.
*****
Tana ganin tafiansu ta sakr ajiyar zuciya, ko
sallama be mata ba, dama so take ta samu
damar fita balle ynz da ta quduri zuwa asibit
sbd wasu manyan kurajen da ta gani a gabanta.
Ta shirya ta nufi wani Prvt hospital, bata sha
wahala ba ta shiga ganin likita, bayan yan
tmbyoyin da likita ya mata game da kurajen,
har dai ya nemi ya gani, ya sake mata wasu
tmbyoyi, likita ya kalleta sosai yana son
karantar wani abu a fuskarta, chan kuma ya ciro
wata na'ura ya ce zai dan chaketa da allura a
yatsa, zai mata test, badiyya ta miqa yatsarta
bayan ya sa hand gloves ya dan diba jini tare da
sawa kan strip din injin. Bayan wasu mintuna
machine din yayi qara, Dr ya maida glass dinshi
ya duba machine din ya dago a raxane, ya kalli
Badiyya, ya ce Mrs Zaid Zailani, what m abt to
tell u is - tace cut d crap n tell me wats wrong
wit me, ya tabe baki yace you are HIV
POSITIVE...
Gidan Gandu
5⃣3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕 Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Cikin tashin
hankali diyya tace HIVn Uwarka? Ni fa ban san
iskanci, ta figi jikkarta ta fice daga office din a
fusace, gabanta na dukan 3uku, Dr ya dauko File
dinta ya kara karanta sunanta ya tsaya yana
tunanin. Tashin hankali ya bayyana karakara a
fuskar diyya, ta gaza sukuni, wani asibitin ta
nufa, ta na zuwa tace amata HIV test, gwajin
farko ya nuna tana da cutar HIV, ihu Badiyya ta
kurma tare da daura hannu a kai, sai da ta gama
kururuwarta kafin ta nemi ganin likita, don
neman shawara, haka liktita ya shiga gaya mata
abubuwan da zata kiyaye da abubuwan da
zatayi, ta fita jiki ba kwari, ta biya chemis ta
siya magunguna kafin ta koma gida cike da
damuwa...
Cambridge England
E&A aka kai Mu'ammar don har ynz kanshi na
fitar da jini, Dr Miracle ya kalli wanda ya kawo
shi yace yayi loosing blood sosai and dole zaayi
mai karin jini, yaje ya siyo a blood bank,
Orange Negative (O-)zai siyo, ko da yaje siyo
jinin baa samu O- ba, mutumin yace a aunashi
aga idan jinin yayi daidai da na Amar, ko da aka

Aunashi, kwatakwata ba zaiyuwa a dibi jininshi a
sama Amar ba, Likita yace dole ake samo jinin
da za'ayi transfuse a jikin Amar before he runs
out of blood, if he does, he will die eventually,
Islah da ta gama jin abunda dr din yace ta
qaraso da sauri tace I am (O-) i will b d one to
donate the blood, mutumin da ya buge Amar
yace nd you are? Da sauri tace Relative, Dr yace
ok, d earlier d better, bayan an auna jininta aka
jininsu yayi daidai aka dibi leda biyu na jini
Islah, kafin aka bata kayan marasa lafia aka
kaita dakin da amar ke kwance ya dan samu
bacci, kusa da gadonshi aka kwantar da ita don
ta huta bayan sun bata madara tasha. aka hada
jinin a jikin Amar...
Kaduna
Karfe 5 ta musu a kaduna straight Asibitn da
aka kwantar dasu Fadila suka nufa, Zaid ya kira
Jawad ya musu kwatancen dakin, yace Amenity
Ward room 11. Ba su sha wahala ba suka gano
dakin, Jawad na zaune kan gadon marasa lafiya
yana sanaarsa wato kuka, duk ya tattaro fadila
da ba tasan inda kanta yake ba zuwa jikinsa, ga
rungumeta kamar zaa kwace masa ita, ga drip a
hannunta ga oxygen a hancinta, suna turo kofa
Jawad yayi saurin xame jikinsa tare da fadawa
kan Zaid ta fashe da sabon kuka, ita kuma
Maysah ta ruga gurin da fadila take kwance
itama ta sa kukan, Zaid yace Jawad yi shiru
mana, be a man, ya girgiza kai yace Brother, i
cannot loose fadila, she cannot die, she took a
bullet for me, dat was my bullet, zayd ya
matseshi a jikinshi yana bubbuga bayan kanin
nashi, gudan jininshi, yace shes going to be
fine, InshaAllah, have faith, Allah zai tashi
kafadunta, Jawad ya dago cikin bacin rai yace i
promise u whoever did dis to my wife is going
to pay, Zaid yace ya isa haka jawad, ya sakeshi
ya qarasa gun gadon fadila, tare da yin dube
duben su na likitoci, Zaid yace kar ka damu,
bacci takeyi, kai kawai Jawad ya daga mai,
Maysah ta ce Yaya Jawad Allah xai bata lafia,
zata warke, u two will live to see ur kids, be san
sanda murmushi ya kubuce mai ba, yana
tunanin kalan yaran da wannan ma bakin tsiwan
zata haifa mai. Da sauri ya qarasa kan gadon ya
riqo hanunta yace fadila, i know u can hear us,
wake up, i need u, i miss u, i missed everything
abt u.. Zaid yace i dont think ko lunch kacih,
yace rabona da abinci tun dinner din jiya,
hankali na a tashe yake, Xayd yace yanzu Rumah
ta tsaya a nan, sai na kai ka gida kayi wanka kaci

abinci, kafin mu dawo ta tashi InshaAllah, Jawad
cikin d'oki yace ok bro, Rumah bari muje mu
dawo ko? Tohm yazayd Allah ya kiyaye Amin.
Jawad yace Rumaysa ki kula min da matata, kar
kaji komai Yayanah, zan kula maka da ita toh
ngd suka fice.
Maiduguri
Salatin da Tsoho ya rafka ne yasa duk yan dakin
zuba mai ido, Zaidu tun yaushe hakan ta faru?
Zayd Yace ka kwantar da hankalinka tsoho, jiya
ne da daddare, amma ynz har Anyi mata aiki
kuma an dace bata dai kaiga farfadowa
bane,Nima yau Jawad din ya kirani ya sanar
dani shine muka taho da rumah, Tsoho ya ce
InshaAllah gobe mu na nan tahowa, Zaid yace
tsoho wani tafia zaka iyayi? Duk kuyi zamanku,
ba sai kunzo ba, tsoho yace bazai yuwu ba, yau
ma don marece yayi ne da ka ganmu amma
asubar fari zaku ganmu. Zaid yace toh Allah shi
kaimu. Tsoho na aje waya duk suka hada baki
gun cewa lapya? Yace yan bindiga ne suka je
gidan Jawad jiya har sun harbi fadila, hajia
babba ta aza hannu akai wayyo mun shiga uku,
Allah ya sa ba su halbi Jikana jawad ba. Tsoho
ya galla mata harara. Ya kalli Suraj da Zayyad
yace Fadila ce aka harba amma an mata aiki ynz
haka suna asibiti, Suraj ka shirya gobe zamuje,
kai Zayya ka tsaya da matarka, Bilkisu tace
tsoho nima zanje danAllah, yace aa ki tsaya kiyi
jinyar yaruwarki, ya kalli hajia babba yace ki
shirya ke da Abida da ku zaa tafi goben, Alhaji
baka gaya min ya jawad dina yake ba? Tsoho
Yayi banza da ita ya fita daga sashenta Yayi
sashen Hajia Ama, ya ko ci saa Aunty Hassana
na zaune, yace Hassan ina Aliyu? Tace barka da
maraice baba, tun da ya fita be dawo ba, yace
ina Aishalle? Tace bari na kirata ta miqe ta
kirata tazo ta zauna, wani tsautsauyi ya faru a
kaduna jiya daddare, Dam gaban Aunty hassana
ya fadi, A ranta tace Allah ka sa ba wani abu ya
samu diyata fadila ba, tsoho ya cigaba Yan
bidinga suka shiga gidan Jawadu da niyyar
kasheshi cikin rashin saa suka harbi Fadila a
kafada, Ama da Aunty Hassana suka fashe da
kuka, tsoho yace ku kwantar da hankalinku. Xaid
yace da sauki gobe zamuje daku gabaki daya.
Kar ku tada hankalinku. Sai da ya kwantar musu
da hankula kafin ya miqe ya shige Sassan
Umma hajja..
*****
Asubar fari suka dauko hanya mota biyuu akayi
da babba da karama, karamar motar baba

hassan ce, shike tuqa tsoho, hajia Babba da
hajia Ama sai Umma Hajja, ba yanda basuyi da
tsoho kan yayi zamanshi ba fir ya qih, Babban
motar kuwa bus ce ta Gidan Gandu. Sai da
laasar suka samu suka iso. Zaid ne ya je ya
dauko su a Kawo, suka iso Asibitin. Yau asibitin
44 ta shaida da zuwan Familyn Zailani, Straight
dakin suka nufa suka shiga da Sallama, Maysah
ta ruga da gudu ta rungume tsoho cikin jin dadi
kafin ta shiga gaida kakaninta da uncles and
aunties. Ganin iyayenshi da kakkani be sa ya
xame daga rungumar da ya ma fadila ba kan
gado, Tsoho yace Sannu jawad ya me jiki? Ya
fashe da kuka Yace tsoho ba sauki har ynz bata
farfado ba, baba hassan yace Ai jawad zata
farfado, Allurar ce bata sake ta ba, Zaid yace na
gaya mishi ai, wasu idan aka musu anaesthesia
sai bayan kwanaki 3-4 suke farfadowa. Jawad
yayi saurin cewa Allah ya sa ta tashi ynz suka
amsa da Amin, Tsoho ya umurcesu da suyi mata
addua, nan kowa ya dinga ma fadila addua, suka
shafa, Jawad ya labarta musu abun da ya faru,
ya hada da cewa tsoho wlh ina son matata bana
so ta mutu, ta cece rayuwana, ta mutu wlh nima
sai na bita, karaf hajia babba tace ja chan
sakarai, don me zaka mutu? Alhamdulilah tunda
kalau kake, Ni na bi na tashi hankali na duk
zatona barayin suna maka wani abun ko baka da
lafia, wlh dana san haka ne da nayi zamana,
wani muguwar harara jawad ya wurgi kakarsa
dashi, ran tsoho ya baci ds jin magangannun
hajia babba zai yi magana sai dai yayi shiru,
Jawad ya hade rai tumuk ya kalli Aunty Abida
yace mom get dis woman outta here i dont
want to see her, Aunty Abida ta harari Jawad,
tace shes my mother, mom rwly? Bakiji me
take cewa game da matata ba? Dint u here me
say she took a bullet for me? Mom da yanzu
nine fa a kwance kila na mutu, sakkayar da zaku
yi ma wacce ta ceci raina kenan? Dis shud hav
bin me, she doesnt deserve dia at all,Jikin anty
abida yayi sanyi, ta kalli fadila cike da tausayawa
lokaci daya taji son fadila a ranta, ta ji dadin da
danta ya auri jaruma kamar fadila, Hajia babba
zatayi magana Zaid yayi saurin janta yace muje
daga waje kakus, tace yauwa don na gaji da
tsayuwa, na sha hanya a banza muje ka ban
labarin yar gayu, ya ma sunanta? Dif zaid ya
dauke wuta ya yi kamar be taba daria ba, ya
kalli tsoho yace Tsoho ina jin ya kamata kuje
masauki, don dr yacr patient bata son
hayaniyya, ya'll shud get going, tsoho yace haka

ne, muje masauki Gobe ma dawo, daya bayan
daya suka fita, aunty abida ta matsa kusa da
fadila ta mata kiss a goshi tace Allah miki
Albarka nagode, jawad kadai jita yayi murmushi
Yace thanks mom, ta shafi ganinshi tace take
care of my daughter inlaw, yayi smile sosai yaji
dadi yace i will mom. Ya kalli Aunty hassana da
ta tsaya ta kurawa diyarta fadila ido tana dan
hawaye, yace Mummy m so sorry, wlh bansan
da zuwan fadila gurin ba, duk a zatona tana
dakih, forgive me mummy, aunty Hassana ta
girguza kai tace ba laifinka bane jawad, Allah ya
riga da ya qaddara
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment