Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

ta kai
kanta kasa don kunya, duk sukayi daria, Zaid da
kanshi ya kai kanshi kasa gurin da Jawad ya
ajiye motarsa, don wani karfi yazo mai, dama
fargaba ce ta maida shi haka. Suna isa gidan
Jawad ya zube a parlo, Maysah ta yi hanyan
kicin tace bari ta hada abinci, Zaid ya shige
toilet don ramuwar wankan da baiyi ba na
kwana 4...
Indomie ce ta dafa musu, haduwa sukayi kan
table duka, zuba ma Zaid ba tare da ta kalleshi
ba, tundazun yake son karantar ta, fir taqi yarda
su hada ido, Fira sukeyi Jawad na basu labarin
dawowan Mu'ammar, Xaid yace muma dai gobe
za muje Maiduguri, Maysah ta dago kanta suka
hada ido aikuwa idon zaid akanta, da sauri ta
kawar da kanta tana murmushi. Wayar Jawad
tayi qara, yace ohh god, ya dauka, yace hello
baby, m so sorry, fadila tace shine kaki nemana

koh? Jawad ya shiga bata haquri, yana wani
narkewa yana shagwaba, yana fada mata how
much he missed her, baki bude Zaid da Maysah
suke kallonshi, ji yanda yake magana kamar
mace, Jawad ya kalli zaid da matarshi ya
murguda musu bakih, yace baby bari naje daki,
wannan yayan naki da matarsa sun sa min ido,
Zaid ya kaimai dukkan wasa, yace kato da kai
kana shagwaba, jawad ya sa handsfree yace
baby kinji bros nace min kato koh? Fadila tace
ravu dashi baby,ai kasan ka fi jariri zama baby
koh? Zaid ya bishi da gudu shi kuma ya shige
dakih yana daria. Maysah ma darian ta ke, Zaid
ya tako har gabanta ya na mata wani irin kallo,
da sauri ta tashi ta fara hada kwanonin da suka
bata, Zayd ya riqe hannunta ya juyo shi gareta,
ya hada idanuwansu, Zabin Tsoho kin qi kallo
na, kin ki nuna min farincikin da kike ciki na
rashin samun cutar nan. Yace i am so sorry for
pushing you away, i dint mean to hurt u, but i
want u to understand that its for ur own good.
Maysah tayi murmushi tace na fahimceka va sai
ka min bayannin komai ba, Zaid yace dole na
fahimtar dake, don kar kiyo tunanin wani abun
daban. Yanzu gobe zamuje na kaiki gurin
tsohonki koh? ta gyada kai, tace nagode, Zaid ya
hadeta da jikinshi ya rungumeta tsam, a hankali
ya rada mata a kunne yace thank u for
everything, i pushed u away but u stayed,
kinsan matsala na amma kika yi kasadar zama
dani, u were willing to damn d consequences
nd take d risk, i cannot afford to loose u, Zabin
tsoho i cannot live without u, U are a Blessing
to my life, I love you Rumaysah, Maysah da
hawaye ya gama wanke mata fuska, ta qara
rungumeshi tsam, farinciki take tayi, tana gode
ma Allah.. A rannan ta ga soyayyah a wurin Zaid
har ta na ta mamakin dana Zaid yana magana?
Maiduguri
Motarsu na tsayuwa fadila tazo ta rungume
Jawad shi kuna ya dagata sama, baby i missed
u, Zaid yace ku dai kuka sani, da sauri Fadila
tazo tana dari Yazayd ina wuni ya amsa yace sai
ynz aka ganni? Tayi daria ta rungume Maysah,
tace sannu da zuwa Maysanmu tace yauwa
Eleerhnmu,Baby zo ki cire mun wani abu a ido
da sauri fadila tayi kan Jawad tana sannu muga
idon, Zaid ya kalli Maysah ya girgiza kai yace
Wadannan koh? Tayi daria, Handbag dinta zata
dauka Zaid yayi saurin dauka, ya rataya shi a
hannunshi, Sannan ya juya gun fadila tace ke da
mijinki ku kwaso mana kaya idan kuna gama

love din, ya kama hannun maysah ya riqe, tace
Yazayd ka bani handbag dina, ya kashe mata ido
yace come nd get it, tayi murmushi, sukayi
hanyar Sasshen tsoho hannunsi riqe da juna.
Sukayi Sallama. Tsoho ya tashi ya hade su biyu
ya rungume yana hawayen farinciki, Zaid yace
tsoho naji jikinka da zafih, lafia? Tsoho yace kai
tafi chan, kalaw nake zaka ja min wani zafin jiki.
Zaid dai ya share, suka zube kasa suna kwasar
gaisuwa...
******
Su duka 12 su na zaune gaban Tsoho, Kallo daya
zaka ma Tsoho kasan cewa yana cikin farinciki,
murna, da Annashuwa. Tsoho yace
Alhamdulilah naji dadi, kun bani mamaki, ina
mai Alfahari daku, Ina mai farin cikin ku nawa
ne, Da farko zaku ga kamar tsana ce ya sani
hadin auren ku da waenda kuka ki jini, ko ku ka
tsana, toh ba haka bane, Na yi hadin nan ne don
sama muku dauwamamen farinciki tsakaninku,
Matayenku sune gatan ku, sune abun
Alfaharinku, sune Rufin Asirinku, ya nuna
Mu'ammar yace matar da ka tsana kamar me
itace ta zama me ceton ranka don jinin jikinta
ta baka to Islahulkhair itace GATANKA, kai
kuma Surajo Bilkisu ta tsare maka kanta da
rayuwar aurenta duk da tsanar da take maka
amma hakan be sa ta kauce hanya ba, ka ga
kuwa itace abun ALFAHARINKA, kai Zayyad na
san kai ba ka zafafa abun ba tun farko, ka yi
haquri ka riqe matarka da mutunci, baka ta ba
kawo kararta ba, ka shanye duk wasu bakin cikin
da ta ke dasa maka, ni ina alfahari da kai, sbd
duk cikin zuriyata babu mai sauqin hali
kamarka, ta dalilin haka yasa Allah ya jarrabeta
da sonka, gashi kuwa yanzu son ka kamar ya
haukatar da ita, ya kalli Hanifa duk sukayi daria,
Tsoho yace Hanifa Zayyad ne NISF HAYAT dinki,
ya kalli Amira yace mutane da yawa sun dauke
ki mara lafia, sbd hallaiyarki ta neman magana,
fada, da rashin ta ido, ni nasan ba haka kike ba,
nasan Jikata mai hankali ce, nasan ke me ta ido
ce, na san ke me son a zauna lafia ce, Shi ya sa
na baki Samir, Don nasan shi yafi kowa sonki a
da har ma a yanzu, shi zai kula dake, Samir
shine HABIBI na gaskia. Ya kalli Jawad yace
Bayan aurenku sai na fara tunani anya banyi
gangancin hada abokan fada aure ba? Mata da
zafin kai take, miji da zafin kai yake, tuni na ke
kasa kunne naji an kirani ance daya ya halbe
daya, nan ma akayi daria, amma sai labari ya
sha bambam, wai ashe kawar fada ce ta amsar

ma abokin fada bullet, kuma a lokacin ba sa
shiri, sai ynz na gano cewa bawai shiri ne ba
kwayi tun farko ba, kun kasa gane cewa son
junanku kuke tun farkon haduwan ku da juna,
amma kiyyaya ya hanaku gani, tabbas ku Abin
KWATANCE ne ga Al'umma, ya kalli Zaid, yace
Zaidu na tsoho, aurenka da badiyya rubutaccen
alamari ne, ido na sama ka sabida na san ba a
hayyacinka kake ba, aiki sihiiri ke dauwainiya da
kai, amma sai na ce bari na bari duniya ta koya
ma hankali, na barka ka aureta, ko da ba ka
samu ciwon nan ba, amma ka ji jiki, don
fargaba ya maida ka wani abun. Tun filazal na
san cewa ba wacce ta dace da kai Sai Rumah,
abu daya ya banbamta ta duk sa'ointa, Haquri,
na san cewa ba wacce zatayi haquri da halayyen
Zaid duk cikin saointa sai Ruma, duk da kai baka
damu da ita ba don idon ka na kan Badiyya, ta
zauna da kai, ta yi haquri da halin da ta tsinci
kanta a cikin gidanka, ta ma matarka da
sirikarka bauta, ta tsaya kusa dakai da kake
tunanin lokacin rabuwarku tayi. Zaid, Rumaisa'u
ce _GATANKA_ itace _SIRRINKA_ itace ABUN
_ALFAHARINKA_, itace _RAYUWARKA_. Toh
farinciki nah shine yanxu duk kun gane abun da
nake son cimmawa a farko, kun ga hangen da
nake muku? ku kasance masu rufama juna asiri,
ku dauki juna daya ba bare a cikin ku, banda
nuna wannan ba dan Sashen mu bane to ba
ruwana dashi, duk daya kuke a guriba, dukkanku
nawa ne, inasonku duka, ku kula da junanku, ku
tsaya ma junanku a matsalolinku, a tare suka ce
InshaAllah Zamu zama abunda zakuyi Alfahari
damu, Suraj yace tsoho Allah ya ja da rai, ya
nuna maka jikokin mu, Tsoho yace anya kuwa
surajo? Na tsufa da yawa, Allah ma ya sa naga
yaranku, suka ce zaka Gani InshaAllah, Jawad
yace Tsoho Zabinka Alheri ne wlh,dama ka kara
xaba min wata, ka ga sai na ga Alheri masu
yawa ta kowani gaba, Fadila ta wurga mai
harara, da sauri yace sorry Baby dama Misali
nake badawa. Duk sukayi dariya yace mun gode
da ziyarar da ku ka kawo mana, ina so ko wanne
ya shirya ya koma gidansa da bakin aikinsa zuwa
Ranar Jumaa, Allah ya muku Albarka, suka amsa
da Amin, duk suka tashi, daya bayan daya suke
rungume tsoho, yana sa musu Albarka.
Gidan Gandu
6⃣0⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕fita suka fara
yi, Tsoho ya cire bakih ya kira Maysah, yace
Ruma in ganki mana, tace to tsoho, Zaid ya
tsaya shima, tsoho yace sai a barni da Ruma ko?

Zaid ya shafa kai ya fita yasan maganarshi zaayi,
Tsoho yace Ruma, ya maganar shaye shayen
Zaid? Har ynz yanayi? Ta danyi shiru ta sadda
kanta kasa, Tsoho yace na fahimci kina son boye
sirrin mijinki, hakan na da kyau, amma ki fada
min, Har yanzu Zaid na shan giya? A hankali
Maysah tace, Eh tsoho yana sha, balle idan
ransa ya baci, sai ya sha gwangwani ya Kai 20,
tsoho ya gyada kai yace haka ne, ya ciro wani
garin magani a aljihu, yace ki barbada mai a
lemu, ko abinci, InshaAllah idan har ya sha, toh
InshaAllahu ko kamshin Giya ba zai so ba, balle
yayi marmarin sha. Maysah ta amsa cikin jin
dadi, tace Nagode tsoho Allah ya qara girma,
yace Amin Ruma nah, ya miqo mata jarida yace
ansa ki karanta min, ta ansa tace i miss dis, ta
shiga karanta mai Newspapern.
*******
Hajia Babba ta dura Ashar, tace wallahi ba za ta
sabu ba, rabon da naje Hajj tun shekara biyu da
suka wuce, yanzu kuma yace da Aishalle zai tafi,
ba zai sabu ba, ta miqe kamar zata tashi sama
ta nufi Sasshen Tsoho.
******
Zaid ya kalli Tsoho yace tsoho baka da lafia,
gaya min, jikinka zafi, ka bari na duba ka, tsoho
yace kai zaidu ka bar kira min ciwo, nace ma
kalau nake koh? Tsaya ma ka gani, tsoho ya
miqe ya na gudu a hankali, yace kagani koh?
Zaid dai murmushi yayi ba wai don ya gamsu da
abunda tsoho yace ba, sai kawai don kar ya
matsa mishi da tambaya, ya ce toh nagani, tsaya
muyi hoto, tsoho kuwa ya gyara zaman gilashin
zaid ya kashe musu hotuna yana posting. Hajia
Babba ta shigo ko sallama babu, tace Alhaji me
nakeji haka a cikin gida? Wai Hajj zaku kai da
Aishalle? Wannan wani irin rashin Adalci ne? Ta
rufe ido sai masifa takeyi, Zaid yace kaka kiyi
shiru mana, ki bari zan biya miki Hajj, tace kai
dalla rufawa mutane baki, saura sati 2 su tashi
wuri ya qure, Wannan rashin Adalcin har ina?
Wallahi Alhaji kaji tsoron Allah kar ya
tambayeka, hayagagan da ihun da hajia babba
keyi ya janyo hankalin mutanen gidan, kan kace
wani abu parlorn tsoho ya cika tam, yan cikin
gida suka cika parlon, ganin idon mutane be sa
Hajia Babba daina yayyafa ruwan rashin
mutunci ba, Ran Tsoho ya baci, yace karime
mina miki na rashin Adalci? Allah shaida ne ina
bakin kokari nacewa na ba wa kowa haqqinsa
cikin ku 3, bayan shekaru 2 na ke zuwa hajj,
kuma ina daukar daya daga cikinku, ya kalli yan

dakin yace ku shiga maganar nan, shekaru 6 da
suka wuce da hajjo na tafi, bayan shekara 2 na
tafi da karime, bayan shekara2 da wa ya kamata
na tafi? Duka dakin aka amsa da Hajia Ama,
Tsoho yace madallah, karime gaya min, me
nayi na rashin Adalci? ta manta shaf da ita akaje
last amma da yake masifa na cinta sai ta fara
borin kunya, eh ai dama ka fi sonta, ba tun yau
kake min haka ba,Allah dai na kallon ka, Tsoho
ya miqe tsaye don zuciyarsa na mishi zafih,
gashi be da isashen lafia, ba tu yau ba, daurewa
kawai yakeyi don kar ya tada ma Iyalansa
hankali, tib ya fadi kasa. Gabaki daya suka yo
kanshi, hajia Babba ta sake ihu, zata yo kanshi,
Zaid ya fizgota cikin zafin nama ya fitar da ita
waje, ya dawo ya kullo kofa, baba hassan ya
shiga neman layin Dr Munnir, da sauri Zaid ya
shiga ba Tsoho taimakon gaggawa, masu kuka
nayi, tsam ya dauki tsoho kamar jariri yayi cikin
daki da shi ya shimfideshi kan Gado, ya shiga
shafa mai ruwa a hankali, ya sauke gauron
numfashi yace yana numfashi, duka dakin
sukace Alhamdulilah, Hajia Babba kuka takeyi
daga waje, Alhaji na tuba wlh, kar ka mutu da
bakin cikina, wlh bazan kara tada maka hankali
ba, xan zauna da Aishalle lafia, nayi Alqawari
zan zauna da kowa lafia, ku bude man dan
girman Allah, ku taimaka ku bude man, kar
Alhaji ya mutu, Auren saurayi da budurwa
mukayi, muna son junanmu, mutuwa ki fara
daukeni, kar ki dauke Alhaji, karki dauken
farinciki na, Ta dinga sambatu,duk da suna cikin
tashin hankali, hakan be hanasu murmusa wa
ba, ana haka sai ga Dr Munnir ya nufo sashen,
ganin hajia babba a waje tana ihu ya sa
gabanshi faduwa, badai tsoho Zailani ya mutu
ba, ya qarasa gurinta yace hajia lafia? Hajia
babba da majina ya gama mata facafaca da
fuska ta share hawaye tace kulleni sukayi duk
suna ciki, DonAllah su bude ka ceto min shi, ba
zan iya rayuwa bashi ba, kuran ya mutu sai na
bishi, de munnir ya shiga kwankwasawa, Zayyad
yazo ya bude mai, wuf hajia babba ta shige tana
ina Alhajin, Zayd yace karku bari ta shigo, su
jawad suka tattare ta, ita ko kira take, Alhaji kar
ka mutu wlh ka mutu sai na biyoka ka yafe min,
Dr munnir ya kalle mutan dakin yace he needs
fresh air, Baba Gambo yace duk ku fita, Ya tasa
qeyarsu Hajia Ama yace Mama mu tafi, ya
farfado, ku barshi ya huta pls, duk suka yi
hanyar waje, Maysah na tafia tana waiwayen
tsoho, Zaid ta ma Alamu da ido, tace take care

of him.
*****
Dr Munnir zaune gaban tsoho, yace Alhaji
donAllah ka daina fadar mana da gaba, u cant
be cheating death anymore, ka tsufa, ba ko da
yaushe zaka dinga dacewa idan ka fadi kasa ba,
wata rana idan ka farfado lafia wata rana ba
zaka farfado lafia ba, Wannan ba shine kadai
hanyar da zaka samu Zaman Lafia a cikin Zuri'ar
ka ba, tsoho yayi murmushi yace Dr kenan, ka
yarda dani wannan shine lokaci na karshe da
zanyi karyar mutuwa, nayi na farko na ci nasara,
wannan ma na ci nasara, don na tabbatar maka
da cewa wannan ne hanyar shiryiwar karime, na
tabbatar maka Karime zata zauna da kowa lafia
kamar yanda tayi Alqawari, tana sona fiye da
komai, ganin zata rasani ya sata nadama, Amma
InshaAllah ba zan sake yin haka ba, ko don na
bar tada ma Zuriyata hankali ba, dis is d last, it
will never repeaf itself again. Dr yace
Alhamdulilah Allah ya sa hakan ne Sanadiyar
hadin kansu tsoho yace Amin. Zaid da ya shigo
dakin yanzu ya ji su tsaf, murmushi kawai yayi a
ranshi yace wannan Tsoho da dubara yake, ga
karfin Hali, Allah dai ya ja da rai, Amma komin
banza ya tsoratar da hajia Babba, yayi daria. Su
tsoho na ganin zaid sukayi shiru, ba su san ya ji
su ba. Tsoho ya wayance da cewa Zaidu je ka
kira min kowa, Zaid yace toh Tsoho mai dubara,
Tsoho da Dr suka bi bayanshi da kallo, tsoho
yace likita ko ya ji mu ne? Dr yace anya? Da
kyar ne gaskia..
******
Hajia Babba kulle cikin dakinta taci kuka har
idanuwanta sun kumbura, idon nan yayi luhu
luhu abinka da farar mace, nadamar gaske ta
shigeta, tunani takeyi tun da aka auro Aishalle
da Hajjo ba wacce ta taba ko harararta, ita ke
musu tijara da nuna isa, ita ta adabe su, ba su
taba mata laifin komai, basu taba tankata ba ko
da kuwa zata rufesu da duka, fiye da shekaru 50
suna fama da ita, to meyasa ba zata daina
wannan halaiyarta ta zauna dasu lafia ba? Duk
sun tsufa, ta son Alhaji na sonta, kuma yana
sauke duk haqqoqinta da ke kansa, amma ta
danne gaskia saboda kishi, Nadama ya shigeta
ta fara istighfari da neman yafiyar ubangijinta.
******
Nasiha me ratsa jiki Tsoho ya shiga yi ma
daukacin zuriarshi, na su ji tsoron Allah, su bi
junansu, su hada kansu, su zama tsintsiya
madaurinki daya. Hajia Babba ta doka sallama

a nutse a kofar parlorn, duk hankalinsu ya koma
kanta, ta shigo kanta a kasa kamar wata sabuwar
Amarya, Gaban Hajia Ama da Umma Hajja ta
tsaya ta durqusa gabansu, ta kamo hanayensu
tace Aishalle, Hajjo, na dade ina baqanta muku
rai, na dade ina chuzguna muku, na chusa ma
jinina kiyayyar jininku, na rabasu, na saka tsana
mai karfi tsakanknsu, na dade ina shiga
rayuwarku, ku yafe min, ku gafarta mun, kuka
sukeyi dukkansu, hajia Ama tace kiyi shiru yaya,
na yafe miki, Allah ya yafe min, Umma hajja
tace bakomai yaya dama ban taba riqe ki a
raina ba, kar ki manta ke yar uwa tace, na yafe
miki. Suka rungume juna su 3 suna kuka, duk
parlorn aka hau kabbara, sunji dadin wannan
abu, ba wanda ya kai tsoho farinciki, Hajia
babba ta miqe ta koma gaban tsoho, tace Alhaji
ka yafe min, nasan duk nice sillar shigar ka
damuwa, nice kadai matsalarka, Alhaji ka yafe
min, tsoho baki har kunne, yace Karimeta, ai ba
ki min komai ba, na san duk abun da kikayi
saboda ni ki kayi, kishi na kikeyi, amma kin
wanke kanki, Allah ya yafe mana gaba ki daya,
uwargida ran gida in baki ba gida, karime ta
musbahu mutu ka raba, hajia babba ta rufe
fuska wai ita kunya, aiko su jikoki suka hau tafi
suna sowa don jin kirarin da tsoho ya ma hajia
babba. Nan kowa ya shiga neman yafiyan wanda
suka bata ma wa, duk aka yayyafe juna, Kowa
murna yakeyi barin ma tsoho da ya fi kowa jin
dadi, ko yanzu Allah ya dauki ransa be da
fargaban komai, Burinsa ya cika, ya hada kan
Zuriyarsa kaf, ya maidasu Tsintiysa madaurinki
daya, sai fatan Allah ya basu dauwamamiyar
farinciki, ya kara hada kansu, ya barsu tare cikin
so da kauna. Allah ya bar Zailani Family.
Gidan Gandu
6⃣1⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 A karshe Baba
Hussaini ya rufe taro da addua aka watse, kowa
sai murna da farinciki.
Yau juma'ah duk sunyi shirin komawa
gidajensu, Hajia Babba ta shirya musu kayan
miya, kamar daddawa, kuka, kubewa busasshe
da sauransu, kowa da kullinshi, Amira tace ai su
wlh ba sa so, ai ni da bigbro ba ma shiri da
tuwo, so ba abunda zamuyi da daddawa hajia
babba ta hararesu, tace ai ke ba a muku abun
arziqi, da ke da mijinki kamar ragowan yunwa,
Amira zatayi magana Samir yace yi shiru
lilsismeera, ta ga na fi tsohon mijinta ne, Hajia
babba tace kai yaro, Musbahu ya wuce ka, ka ga
dan saurayi son kowa kin wanda ya rasa, duk

suka sa daria, Zayd yace yauwa Ruma ya ma
sunan abun nan da kike samun a tea? Me
kamshin nan, tace oh kanumfari, yace yauwa shi
hajia ki bamu inaso, Hajia babba tace gaskia
bandashi, sai dai in kakar ka Aishalle na san
tana harka da kayan yajin nan, Hajia Ama da ke
zaune ta na kallonsu tace eh akwai Kanumfari
guri na, bari na je na kullo muku, Zaid yace ba
sai kin tashi ba, a ina kika ajiye muje mu dauko
ni da Ruma, ta musu kwatance ya ja hannun
matarsa suka fita., Fadila tana ta jin dadi don ta
nason tuwo, Jawad yace ina zaaje da wadannan
tarkacen? Fadila tace Baby kaduna mana, yace
wallahi ba zaa sa min mota yayi ta warin
daddawa ba, ta turo bakih tace hajia babba kina
jinshi ko? Hajia tace kai dallah chan ka bar dadi,
ina ma amfanin wannan cimar da ka ke ci,
banda tsotseka ba abunda yake kara ma a jiki,
ka dage da cin abincin gargajiya, irinsu tuwon
masara ko kayi kumari, amma sai wani abu da
sunan ko dadi babu, ya sunan abun ma? Ko
guiza yake? Duk suka fashe da daria, yace haba
hajia sai ki bamu kunya, pizza ake cewa, tace kai
ni rabani da abincin mayu da aljannu, duk suka
fashe da daria. Mu'ammar yace indai ta ni ne to
gaskia ki bar kayan warinki, ba maso koh Khairi?
Islah ta sunkunyar dakai tana daria, Hajia babba
tace yan Ingilan burauba, kun ma kanku, Ta kalli
su Zayyad da suraj tace Wai ku tsaya ma, idan
kunsan ba kwaso ku aje min kayana kar ku je
dashi chan ku ajiye min nayi asara. Suraj yace
mu muna cin tuwo gidan mu gaskia amma ba
sosai ba, sai muna marmari ko honeybunch?
Bilkisu tace eh muna so hajia babba, Zayyad
yace no ni ina cin tuwo, ban son shinkafar nan,
Umma hajja tace ai ni burgeni kakeyi Zayyad ba
ruwanka da zaben abinci, kai dan gargajiya ne,
yace gaskia ni komai aka dafa ci kakeyi, hajia
babba tace kaji dadinka. Nan suka dan taba fira,
sukayi sallama kafin suka nufa Sashen Tsoho
don yi mai Sallama.
Nasihar ce dai ya qara musu, a karshe ya sa
musu Albarka, suka shirya tafia, Mu'ammar da
suraj da jawad da Zaid suka dauki hanya daya.
Samir ya dauki hanyar bauchi, Zayyad kuma aka
kaisu Airport.
*****
Zaria
Tunda ya shigo gidan yake kwala mata kirah, a
parlor suka yi kicibus, tace YaAmar lafiya
wannan kira haka? Yace close ur eyes, ba ta mai
gardama ba, ta rufe idonta, ya sa mata wasu

takardu a hannu yace ta bude idonta, ta bude
Tickets to Cambridge England ne, ta zaro ido
tace yaya? Yace i told u, m ready to sacrifice
everything, akwai time zaki koma skool, nd i
will apply for masters, still kuma i will find a
job, we'll start allover there, we will build our
home, nd i will give u the joy and happiness u
truly deserve. Dadi ya kashe Islah ba ta san
lokavin da ta rungumeshi ba tare da manna mai
kiss a baki, tace i love u yaAmar, yace i love u
more swrhrt.
Abuja
Time din da ya shigo gidan bata nan ta je skul,
ya gaji sosai ya fada dakih, yana si Yayi baccin
rana amma ya kasa, giyyarsa ya ciro cikin fridge
ya bude zai sha kenan ta shigo da sallama, da
sauri ya boye kar ta gani, DonAllah ya daura
mai wani irin kunyarta, ba ya so ta ga yana shan
giya, shiyasa tunda suka dawo daga Maiduguri
yake sha a boye, ta ganshi ta ga me yakeyi.
Amma ba ta nuna mai ta gani ba, sai a sannan
ta tuno da maganin da tsoho ya bata. Ta qudiri a
ranta yaum zatayi amfani da maganin, Allah dai
ya as a dace. Yace Yaxayd ina wuni, duk ya bi ya
daburce yace lafia lau, banji shigowarki ba, tace
ina ta sallama ba amsa ai, ganin ya kasa sakewa
da ita ya sa tace bari taje ta rage kayan jikinta,
ta fita, tana fita ya kwankwade giyyarsa, daki ta
shiga bayan ta cire hijav dinta, ta bude kayan ta,
ta ciro ledan maganin da tsoho ya bata, ta shiga
kichin ta shiga hada musu lunch, cikin jug din
sobo ta juye maganin nan tas, ta kai dinning,
zuwa tayi ta shiga kwankwasa mai, sama sama
ya ke jinta don har ya fara bacci.Tace yazayd ga
lunch na gama, ka fito kaci, cikin magagin bacci
yace ki bari sai anjima, ta marairaice tace plss,
yace ok lemme dressup, sai da ya fads toilet ya
sakar ma kanshi shower kafin ya fito, kan table
ya isketa, ta yi serving dinshi, white rice ne and
sauce, ya ci kadan, ta zuba mai sobo ya sha
sosai sbd yayi dadi, ba a fi 5 mins ba, ya ji
zuciyarshi na tashi, Warin giya yake ji, Amai ya
zo mai da gudu ya fads toilet ya dinga kwarara
Amai ba tsayawa, Maysah sai sannu take mishi,
sai da ya kusan minti 20 kafin aman ya tsaya,
ya bata tausayi sosai, ta bashi roban ruwa ya sha
ya kuskure bakinshi, ta riqoshi ta kaishi daki, ji
yayi dakin na warin giya, yace ki kaini dakinki,
haka ta miqar dashi ta kaishi dakinta, duk ya
galabaita, Sai da yayi kwana 3 kafin Aman ya
tsaya, duk ya rame ya qare, sai da wani
colleague dinshi yazo Gida ya samai drip, randa

Zaid ya warke ya shiga dakinshi ya fiffirto da
dukka kwalayen giyan da na fridge yayi waje
dasu ya cinna musu wuta, Maysah na kallonshi,
dadi ya rufeta, nan take ta kira tsoho ta shaida
mai abun da ya faru, shima yaji dadi, yace ai
Zaid kuma da Giya har Abada, yanzu ko wani ya
gani yana shan giya sai yayi Amai, don kyamar
giyya yakeyi yanxu, Mijinki ya daina shan giya
da Yardar Allah. Maysah tace Nagode Tsoho
Allah ya bar mana kai. Murmushi tsoho Yayi ya
kashe wayar..
(3months later)
Mrs Zaid hurry up, zaki sani latti fah, daga ciki
tace just a minute Mr Zaid, yace ko na tafi? ta
fito tana gyara zaman gyalenta tace ai na ma
fito, Zayd ya matso yace u grw more beautiful
every morning, murmushi tace ai ban kai ka ba,
yace i love everything about u, murmushi tayi
ta ce mu tafi kar Ka amsa query gurin Dr
James, har zata shiga mota ya riqo hannunta,
yace na sa miki ido wato ke ba ki san ido ba ko?
Ta zaro ido tace yazayd me nayih? Oh baki san
me kikayi ba ko? ta marairaice tace kayi haquri
Yazayd, me nayi? Shima ya bi ya marairaice
kamar yadda tayi, ya turo baki yace ban taba jin
kin ce min i love u ba, waiyo Allah, kunya ta
lulluba maysah, ya tsare ta da ido yace ehen ina
jinki, ganin kunyanta ya motso ya saketa ya
bude mata mota yace na lura akwai sauran
kunyana a tare dake, a hankali zan cireshi, da
sauri ta kawar da kai tare da yin murmushi.
Karfe 12 ya gama ganin patients a OPD, ya
kalleta yace Mrs Zaid kin gaji ko? Ta girgiza kai
tace Aa, ina kallon ka ne yanda kake duba
patients cikin kwarewa, kaji dadinka Allah
Girma, yayi murmushi, yace dadi na da Zabin
tsoho akwai Adduoi kamar mutanen da, tayi
daria, yace oya ta shi muje muga patients a
ward, daga chan sai mu wuce gida, ta miqe ds
sauri suka fita daga office hannun su riqe da
juna, suna tafia suna birge mutane, wanda Suka
sansi sai suce MrAndMrs Zaid, sai su daga
musu hannu, a haka har suka isa Ward, Zaid ya
shiga ganin patients dinshi, ita kuma tana basu
kudi sadaka, ana ta musu godia, su ka fito,
daidai wani daki sukaji
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment