Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Yayi smilling back tare da bude booth din
badiyya da uwarta sukayi kiciniyar saka kaya a
booth gogan ko fitowa beyi ba. Suka shiga
motar, ko kallon arziqi be ma uwar Badiyya ba
yace, Ina wuni mama,Ita ko a ranta cewa take
Ashe diyyata bata yi karya ba, Zaidun nata
hadadde ne, ta amsa cikin wani murya sai da
diyya ta juyo ta kalleta. Zaid ya ja mota sai
gidansa dake Maitama.
Ta zage ta dafa Tuwon semo miyan agushi da

yaji ganda, ta kai kan dinning ta ajiye, tun dazu
take zaman jiranshi, har bacci ya dauketa kan
3sitter, Sun iso gidan suka dinga kwankwasawa
shiru, Zaid ya kwala ma maigadi kira yazo
jikinsa na rawa, yace kai wata ta fita daga gidan
nan? Yace auu akwai mutum ciki? Zaid yace ba
tambayar da na maka ba kenan, yace Yallabai
indai ka bar mutum a nan to ta na ciki, don tun
da safe ina nan zaune ba inda naje. Zaid yayi
tsaki ya ciro keys ya kalli su badiyya yace muje
Badiyya da ta gama cika tayi fam kamar ta
pashe ta ja akwatinta uwar na biye da ita a
baya, suka zagaya baya, zaid ya sa mukuli ya
bude wani qofa ashe ta kichin ne, tun daga
kicin din suke jin wani daddadan k'amshi, har
suka iso parlorn, kwance ya ganta tana bacci,
kallo daya ya mata ya dauje kai, idonsa ya sauka
kan dinning yaga kulolin abinci, ya tabe bakih,
Diyyan ta kade ganin tsaruwar gidan, ya kalli
uwar diyya yace feel at home mama, ta sakar
mai murmushi ok son, ya kalli diyya yace bari
na shiga na yi wanka, tace dear, ai da ka barih
kacih abinci yar matarka, ta qarashe tana
zolayarsa, ya dan bata rai yace nahhh, you go
ahead, ya ja briefcase dinsa yayi dakihnsa, suko
nan suka dire kayansu suka nufa kan table,
Diyya na bude kular miya taji wani qamshi, nan
da nan miyonta ya tsinke, sai da ko ta lasa, ta
zuba a plate, ta sam mamanta, nan suka hau ci,
daman mulmula biyar ne, diyya da Maman ta
suka kwashi tuwon nan tassss. Cikin bacci taji
ana buruntu tayi sauri ta tashi, idonta ya sauka
kan Diyya da mamanta, Gabanta ya yanke ya
fadih. Diyya ta juyo ta ganta tsaye, Auu
Rumaisah kin tashi? Zo ki kwashe kayan nan ki
kai kicin, sannan kizo ki shigar min da kayana
dakihna, ki nuna ma mama dakinta, Hantar
cikin Maysah ya bada Kulululu. Meke shirin
faruwa da ni? Ta tambaya kanta.
_Bibilicious Biebee_
2⃣4⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Ji ta yi abun
kamar a mafarki nan ta tsaya kamar robot,
tsawan da badiyya ta mata ne yasa ta dawo
hayyacinta, ko ba kya ji ne? Cewa nayi zo ki
kwashe kayan table din nan, Sannan ki kwashi
kayan chan ki kai dakih, Maysah ta hadiye wani
mugun miyau, jiki ba qwari ta tako ta harhada
kwanukan tayi kichin, Tuwon da ta tuqa domin
ta da mijinta, ga wasu nan sun cinye tas, ita ko
ko a bakinta, gashi wani yunwa takeji, daman
niyyarta sai ya dawo zasu ci tare gashi an cinye,
tuni hawaye suka bi kuncinta, ta dawo parlorn

ta ja Akwatin su tayi hanyar wani dakih,
kasancewar Gidan 3bedrooms ne, Badiyya ta
cire bakinta ta kwala mata kira, jikina barih ta
zo da sauri in kai wannan akwatin dayan dakin,
wanchan akwatin ki kaishi wanchan dakin ta
nuna dakin kusa da Zaid, waiyo Allahnta,
dakinta take nufi zata kai kayan Badiyya, to ita
ina zata kwana? Muryar badiyua ya katseta yace
ke ki min sauri, hakan ko Maysah tayi, Maman
badiyya tayi daria woo diyata baki da wasa,
Badiyya tayi daria tace ai mama Yar aiki muka
samu, tunda tayi qoqarin shiga gonata ga
hukuncinta, ai naso auren nasu ya dore ya dade
da ta mun bauta har sai naga wannan kyaun ya
disashe, amma duk da haka zan moreta na sati
1, tunda lokacin aurensu zaiyi expire. Suka dau
shewa tare da kashewa. Nan suka zauna suna
kallo ba Maghriba balle Ishai, ita ko bayan
sallah ta shiga kichin ta gyara, sai da ta qara
tuqa tuwon don akwai sauran miya. Wuraren
qarfe 11 maman ta ma diyarta sallama ta shiga
daki don huta gajiya, Badiyyan ma ta shige
dakih da watsa ruwa, tun dazu maysah ke kichin
zaune, har ta fara gyangyadi, bacci kawia take
sonyi, jin ta daina jin hayaniyarsu yasa ta
leqowa parlor, ba sa nan, zuwa tayi ta kashe tv
din, ta dauko throwing pillow ta ajiye a kasa ta
kwanta ta re da chusa hannayenta tsakankani
cinyoyinta alamun sanyi. Nan bacci yayi awon
gaba da ita.
Ko da ya fito parlor ya kunne wuta ganin ta yayi
kwance, kallo daya ya mata ya dauke kai, dayan
dakin ya shiga, kwance ya ga Maman Badiyya
daga ita sai Underwear tana waya, bata yi wani
yunqurin suturtace jikinta ba shima be damu
ba, yace mom ina Badiyya, tace tana dayan
dakin, ya rufe yana mamakin dayan dakin
kuma, dakin ya nufa ganinta yayi xaune gaban
dressing mirror tana shafa, ta mirrir ta
hangishi, myzayd ya dai, ya dan bata fuska, yace
kinsan dakin yarinyar nan ce nan ko? Tace toh
me kake nufi? Yace gata chan kwance parlor,
tace y do u care? Yace i dont, but its not fair a
zo gidan ta a fidda ta wajeh, badiyya ta qwale
ido, kar dai Zaid taussyin yarinyar nan yake, in
haka ya faru ita kam ta kade. Ta dai daure tace
ya kake so ayi? Yace ki koma dayan dakin ita
kuma ta dawo dakinta. Tace ni gaskia ba zan iya
kwana da mama ba, kwana take ta na waya, ya
danyi tsaki, tace sai dai ko dakin ka, ya yi hanyar
fita yace ko ina zaki kwana ki kwana, just leave
dis room,. Parlorn ya koma, da qarfi ya dinga

cewa Keh, keh tashi ki koma dakih, cikin bacci
taji kaman muryan shi, da sauri ta miqe tacw
Yazayd ina wuni, ka dawo lpy? Yayi hanyar
dakihnsa yace ki shiga dakinki, nan ta daskare
ganin badiyya ta fito da wata irin shegiar nyt
gown tayi dakin mijinta. Hawaye suka shiga reto
wlh da ma kwanciyarta tayi a parlor ta bar mata
dakin, ds ta bar wata ta shiga dakin mijinta.
Tana gani badiyya ta shige dakin Zaid tare da
kullewa. Maysah ta zube kasa tana kuka. Da ta
ga hakan ba zai fisshe ta ba ta shige dakih ta
dauro Alwala ta hau Sallah.
Kwanciya yayi kan gadonsa, ita ma badiyya ta
haye, nan suka fara iskancinsu, Zaid na ganin
badiyya na qoqarin wuce gona da irih yayi
saurin tunkudeta, idonta ya kada yayi jaaa, cikin
dakusheshen muryarta tace please Zaid, just
once, pls Zaid, ya miqe tsaye yace kinga abunda
ke hadani da ke ko?nace miki bana so, yayi
shigewarsa toilet, Badiyya ta fita hayyacinta ta
shiga murqususu a kan gado, har ya fito kallo
daya ya mata ya kawar da kai, da qyr tace Zaid
pls help me Help ne i need u, ya ce ok,
briefcase dinshi ya dauko, ya ciro wani magani
ya dago fuskanta ya titila mata ko minti 5 ba
tayi ba ta fara bacci. Ba ta farka ba sai 11safe.
Ranta a bace ta waiga ta waiga ba Zaid, ta ha ba
brief case dinshi. Ta jayo wayanta ta kwada mai
kira, A lokacin kuwa ya na zaune a office ya na
duba wani patient, kiranra ya shigo, yaqi dauka
sai da ta mai 3missed calls, a na hudun ne ya
kalli patient din yace excuse me, ya dauki
wayan Hello Diyyana, cikin fada ta fara fadin
Zaid y are u doing dis to me? Isit bcoz i lov u?
Cikin mamaki yace me na miki diyyata? U knw i
wont hurt u knowingly, tace i asked u to help
me not to doze me off, ya danyi murmushi
yace dats d only help i cud give u, I told u na
tsani Zani, ki yi haquri har muyi aure mana,
yanxu dai ina diba patient, sai na dawo ba tare
da ta ce komai ba ya kaahe wayarsa. Baqinciki
ya tokareta Wato ya tafi Aiki ya barta kwance a
nan kamar kayan wanki,Bata taba ganin Dan
iska irin zaid ba, wato baka zina amma kana
shayeshaye? To meye bambancin dambe da
fada? Zaid ka bini a sannu tayi kwafa ta shige
toilet.
Tun da tayi asuba ba ta koma ba, ta na kichin
tana hada musu breakfast don ta san Zaid zaije
office, wurin 7 ta shiga wanka, ashe har zaid
yayi tafian shi, ba ta sani ba, tana ta zama
jiransa ba shi ba alamarsa, duk yan gidan dai

bacci sukeyi. Qarfe 12saura badiyya da uwarta
suka fito suka hau kan table suka kwashi abinci,
Maysah ta zo tana gaidasu ba wanda ya amsa, da
ta gaji ta miqe zata tafi Maman badiyya tace ke
Rumaisa jeki soya mun doya zallah bana son
me qwai din nan, haka maysah taje ta sake wani
soyen. Haka dai Maysah ta yini ta na bautar
Diyya da Mamarta..
5days later.
Haka rayuwan Bayin Allahn nan ya cigaba da
gudana duk gidajen nan ba Zaman Arziki, Ba
me kula kowa, Amira kullum sai ta ma Samir
magana a takiace ya ke bata amsa, Zayyad
kullum sai ya ma Hanifa magana ko tana da
buqatar wani abu ko kallo be isheta ba, Jawad
ko kula fadila ba yayi, trust fadila ita ma harkan
gabanta takeyi, ko abinci daidai cikinta takeyi,
Bilkisu da Suraj kamar mage da bera, kullum
sai ta mai rashin kunya, Islahulkhair bata qara
saka Mu'ammar a idonta ba har ta saba da
zaman kadaici, Maysah kuma na yin bautar
karuwa da uwarta, Zaid ko lasan abincin ta be ta
bayi ba, ita kuma bata taba gajiya da aikinsu ba,
Kullum sai tsoho ya kirata bata taba nuna mai
komai ba nan zai ta mata nasiha yana samata
Albarka....
Bibilicious Biebee
Yau Juma'ah misalin qarfe 11 na safe Ya shigo
gidan tana bacci a parlor taji ana qwanqwasawa
abun har ya dan bata tsoro, ta miqe ta nufa
qofa ta bude, Mu'ammar ne tsaye, tayi
mamakin ganinsa ba tare da yace mata komai
ba ya raba ta gefenta ya shige ciki bayansa ta bi
da kallo, ya shige wani dakih. Zamanta tayi a
parlo ta kunna TV, Wayarta tayi qara fadila ce ta
dauka sis yane? Tace lapya ya gida,? Tace hmn
ga gida nan, ina Ya Jawad? Fadila ta tabe bakih,
yau wurin 10 ya shigo gida naga ya hada
kayansa qila Maiduguri zaije, Islah tace kuma
bakwa magana? Fadila tace ni ko iskar da
deboshi ba sani ba, Islah zata ce wani abu taga
Mu'ammar ya fito da dan jakka a hannu ya na
waya, okay kana qofar Gidan? Gani nan fitowa
ya bar parlorn ba tare da ya tankata ba. Islah ta
fashe da kuka, fadila na tambaynta ta kashe
wayar gabaki daya.
Bayan Jumaa Suraj ya fito da dan akwatinsa ya
kalli bilkisu dake lunch yace Ni na tafi
Maiduguri, tayi tsalle tace wa zaka bari a gidan
nan? Yace ke mana, tace kambu, ai baka isa ka
barni ba, tare zamu tafi ko wallahi ba zaka dawo
ka sameni ba. Yace toh ki yi yanda kikeso, don

ni kam ba inda zaki bini, ya fita tare da rufe
kofar wajeh ya ja motarsa. Ihu bilkisu ta sa ta
dinga tsine tsine.
Maiduguri
Jawad da Mu'ammar sun iso Maid lafiya
kasancewar tare suka taho, Jawad ya biya ya
dauki Mu'ammar straight Sashen Hajia Babba
suka nufa, Ta na ganinsu ta hau murna, ga
mutanen Garin Gwamna, sannunku da zuwa,
daman kuna tafe, Mu'ammar yace ba dole ki
ganmu ba, ai nan Zuwa mukayi don a raba
auren nan, don tun da aka kaita ban kwana
gidana ba, Hajia babba tayi daria tace shege
Ammar, kuzo ku ci abinci sai muje ayi magana.
Suka qarasa ciki, suka ci abinci ko wannensu
yayi sashensa, Aunt Abida ta rungune Jawad,
Son haka kayi baqih? Yace Umma ba dole ba,
ina kwana gida daya da maqiyyana ai dole na ke
chanza kala, tace Ina danuwanka? Yace wai ba
zai samu damar zuwa ba week din nan don
shine Dr on call saturday nd sunday, but yace
idan an raba auren zai sa yarinyar a jirgi, tace
toh shkn, Abunda sai mu jira muji me Hajiar ta
shirya. Mu'ammar ya kira Jawad yace kai mu
hadu Sashen Tsoho kar labari yaje mai mun iso
tun dazu ba muje mun gaida shi ba, yace toh
muje..
Ko da suka isa Sashen Tsoho, Suraj na nan
zaune suna labari da tsoho Sallama sukayi,
Muammar ya daure ya ba Suraj hannu suka
gaisa, banda jawad din da ya dauke kansa ya
maida hankali gurin gaida tsoho, Tsoho yayi
murnar ganinsu, ya dan zolayesu da Angwaye
kun sha qamshi, aiko suka sha kunu dukansu,
suka miqe zasu fita yace ku zauna mana muyi
hira, haka tsoho ya dinga jansu labari, ina
matayenku,? Ince dai ba wata matsala koh?
Shiru suka mai. Sallamar Hajia Babba ta katse
musu hanzari, Anty Abida da Aunty Sadiya na
biye da ita a baya, Bakih har kunne tsoho yace
Karime kinga Angwaye koh? Ta tabe bakih, tace
Alhaji magana nake so yi, ya dan gyara zama
yace wace irin magana kenan?Alhaji Auren da a
aka ma yaran nan nakeso a warware shi gabaki
daya banda na Amira da Samir yanxu, tsoho ya
kalleta sosai. Yace saboda me? Ai idan na daura
aure, ba warwara ba sakih duk rintsi duk wahala
ya qullu kenan sai mutuwa zata raba, Hajia
karime ta harzuqa, Kai Alhaji kar ka raina mana
wayau mana, Auren da aka daura don a sama
maka lapya yaran nan suka amince, ba sa son
junansu amma tunda ka warke yanzu dole za a

raba, ko wannne a bashi wacce yakeso, Tsoho ya
kalle ta sosai, cham ya kwada ma Sarkin Gida
kirah, sai ga Mallam Iro ya shigo jiki na rawa,
Tsoho da idonsa yayi jaaa yace je ka kira min
Kowa. mallam iro ya fita, yaje ya kira duka yan
gidan cikin mintuna kadan kowa ya hallara
parlorn tsoho, parlorn yayi tsit ana jiran aji
abinda tsoho xaice, ya kalli hajia Babba da take
murnan haqanta ya cimma ruwa, yace Karime
maimaita abun da kika fada, ba kunya ta
maimaita, Tsoho ya miqe ya shiga dakih sai
chan ya fito Da Alkurani izzu 60, ya riqe ya ce ni
Musbahu Zailani, nayi rantsuwa da kuranin nan,
duk randa daya daga cikin maauratan nan da
aka daura aurensu jummar da ta gabata, ya saki
matarsa ko da saki days ne, to Na saki Karime
saki 3, kuma na tsine ma mahaifansa, Inallilahi
wa ina ilaihir rajiun kowa ke maimaitawa,
Banda Hajia babba da ta sake Ihu na shigesu,
Alhaji Me yayi zafih haka? Yau na banu, ta fashe
da kuka, ita tasan ba zata iya rayuwa ba tsoho
ba,(lol)shima tsohon ya san karime na sonsa, ta
dinga kururuwa, Hajia Ama da Umma Hajja
suka jinjina kai. Ya kalli su Mu'ammar da jawad
da suka kidime iya kidima yace Ku gaya ma yan
uwanku saqo na, idan har kuna so na tsinewa
iyayenku, na kuna saki kakar ku toh ga takarda
nan ku rubuta wa matan ku saki. Ya ce ku tashi
ku tafi na sallame kowa. Jiki ba qwarih aka fara
watsewa, banda karime da tako kusa da Tsoho,
don Allah Alhaji kai man rai, tun kuriciyar mu
baka saken ba sai ynz? Ka san ina sonka, don
Allah kar kai min haka, yace karime ina sonki,
ba xan sakeki ba , amma da yaran nan sun saki
matansu, to kema a bakin aurenki fah, da sauri
tace wlh ba me sakar kowa, ai auren nan mutu
ka raba, Allah ya basu zaman lapya ya hada
mana kawunannasu, Tsoho yayi murmushi ya
san karime ciki da bai hakan kadai ne
maganinta. Yace Amin karime ta👻
Tafia sukeyi amma ba me ganin gabansa,
Mu'ammar yayi tangartangar zai kife Jawad yayi
saurin taro shi, yace haba mana Mu'ammar,
calm down mana, Mu'ammar cikin fushi yace
Calm down? Ana nufin idan na sake yarinyar
nan za a tsine ma uwata? don na san ko ya tsine
ma baba ba zai bishi ba, don ba shi ya haifeshi
ba, Amma dagaske yake sai ya tsine ma er sa ta
cikinsa, uwata? Wallahi na tsane yarinyar nan,
ba na sonta bana qaunarta, Kamar yanda nima
Bana son Bilkisu kuma bana kaunarta ba, jawad
da Mu'ammar sukayi saurin kallon me furucin

nan, Suraj ne ya nufosu, ashe yana jinsu, Jawad
ya tunzura, yace ance maka ita ta na sonka ne?
Ni jawad ni kadai takeso, zaka qarasa rayuwarka
da matar da ba ta sonka, nd its going to kill you
inside dat she loves me alone, Suraj yayi
murmushi ya juya dubansa ga Mu'ammar yace
let me make one thing straight, Islahulkhair is
my only sister, ina sonta fiye da kaina, Idan na
sake naji ka mata wani abu wlh baza mu kwashe
da kyau ba, dat reminds me, M married to your
sister Bilkisu, Hurt my Sister and i will hurt
yours. Don Er uwa ba ta fi Er Uwa ba. And to
you Dummy ya kalli Jawad, kai ma kasani fadila
ba ta sonka bata kaunarka, ni kadai takeso
nikadai ke zuciyarta, kaga we have one thing in
common. So i can leave wit this. Nd da kake
ikirarin bilkisu ba za ta taba sona ba, yayi dan
daria ka manta ni Architect ne? Toh idan ka
manta bari na tuna ma I am an Architect, i will
do what i do best, I will Redesign, Rebuild and
Reclaim her Heart. Yana kaiwa nan yayi tafiarsa
ya bar su tsaye kamar Robot.
_ Bibilicious Biebee_2⃣6⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by💕Biebee Isa💕 Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Ransu in yayi
dubu ya baci, ko wannensu ya wuce dakinsa
ransa na mai Zafih, Jawad na shiga dakih ya kira
Zaid, ya Zayyane masa komaibda abinda Tsoho
yace, Zayd yayi dan jim, chan kuma sai yace
shidai ya sani, ni banda matsala, tayi ta zama da
igiyar aurena, ba sai na kulataba?
Asubar fari Mu'ammar ya baro borno motar
haya ya hau, ko Jawad be san ya tafi ba, ba zaria
Yayi ba, Abuja ya nufa, sai dai muce Allah ya
tsare.
Badiyya zaune gaban Bokanta, ta muskuta tace
yanzu kai boka ka na nufin na baro Abuja na zo
Maiduguri kuma ba biyan bukata? Wlh na matsu
da Zaid, kamar nayi hauka, Boka yayi daria yace
Diyyan shagali, yanzu ya kike so nayi? Na gaya
miki hakan ba zai taba yuwu ba, Zaid ba zai taba
kusantarki ba indai har ba aure kukayi ba,
Daniska ne amma baya zina, Abu daya zance
miki, ki sashi ya aureki, kar ki bar Garin nan ba
tare da kin samu karbuwa wurin danginsa ba,
tace ta yaya? Yace ki kutsa, ni kuma zan miki
aiki, dukda wannan kakan nasa dan iskan kansa
amma na ga Aure tsakaninku, tayi murmushi
yauwa gatana shisa nake sonka, haka ta cika mai
al aljihu, sukayi sallama bata yi ko ina ba sai
gidan Mubahu Zailani, ko dar ba ta ji ba ta
tambayi sassan Hajia Babba aka nuna mata, ta
shiga dakin da Sallam bayan ta gyrara tsayuwar
gyalenta, Hajia Babba ta amsa daga cikin daki,

Badiyya ta ma kanta masauki kan sani
lafiyayyen kujera, Hajia Babba tace tou ina
muka samo Yar Gayu? Badiyya tayi murmushi
ta risina hajiarmu ina wuni, Waiyo Allah dadi
xai kashe hajia babba ta ji yar gayu tace mata
hajiarsu, nan badiyya ta gaidata cikin barikanci,
ta amsa, sai dai ban shaidaki ba, Allah sarki
hajiarmu Badiyya ce K'awar Zaid ce ni amma ni
a zahiri ni Aurenshi nake so nayi sai dai naji ba
a auren bareh a gidannan Hajia babba ta jinjina
kai tace eh haka ne, Badiyya ta zamo ta riqe
kafat hajia babba ta na roqonta ta taimaka
mata, lokaci daya ta siye zuciyar hajia babba da
zantuttuka masu dadi har hajia babba taji za ta
tsaya ma Badiyya tunda tace zaid din na sonta,
ta shafa kanta tace karki damu Badiyya abun da
wuya, amma zan miki kokari har Allah ya sa a
dace. Da Sauri diyya ta rungume hajia babba
tace kai Amma nagode hajiarmu, Allah ya ja
rai, ya barki da tsoho, ai kamar an tsundumata
a Aljannah taji dadi, Badiyya ta cikata da kudi,
duk da kudi ba matsalar hajia babba bane
amma bata da godian Allah. Har badiyya ta
miqe hajia babba tace yauwa jikata dani da
Hajjo wa yafi kyau da diri? Badiyya a ranta tace
wacece kuma Hajjo? Amma a fili tace wai
daman cewa akayi kyau ne da ita? Ai wlh
hajiarmu kin wuce a hadaki da wata hajjo, Hajia
babba taji dadi matuka, baki na rawa don bata
san kalan amsar da za a bata ba ta ce Aishalle
fah? Badiyya ta tabe bakih ba don ta san waye
Aishalle ba tace wannan me kama farar mayu.
Shewa hajia babba ta sa ta rungumi diyya tana
tafa hannaye, yauwa Yar gari, da wannan
kodawar da badiyya kema hajia babba taji zata
yi yanda tayi don Zaid ya auri Badiyya haka
sukayi sallama cikin jin dadi, Hajia Babba na
zuwa dakih ta Kwalama khalil kira, Autan baba
mudassir, yazo da gudunsa, ta mika mai wayar
tace kira mun Zaidu, khalil yayi daria, wai hajia
ba kya ganewa ne? Har hoton Yazayd a ka
samiki a contact picture don ki ganeshi amma
kullum sai kin kirani, cikin fushi tace zaka kira
minshi ko sai na kwashi buraubaka a hannu?
Daria yayi yace Maida wuqar hajia ya kira mata
Zaid Bacci yakeyi misalin Karfe 2 na rana, hutu
kenan na kwana 2, yanda yaji dadin weekend
dinnan Diyya ba ta nan taje Maiduguri,
Mamanta ma bata gida, kamar a sama yaji
wayarsa na ringining tsaki ya sake, duk zatonsa
wayar asibiti ce ake kiransa, haushi ya cika shi
daya ga personal wayarsa ce, screen din wayar

ya hasko mai Grams, guntun tsaki ya saki ya
dauka,Hello Grams ina wuni?daga bangarenta
kamar tana waya da wanda yake Sama ta
bakwai, da karfi tace Hello Zaidu, Yanzu Yar
Gayu tazo, haushi ya cikashi, wacece yar gayu?
Haba wannan diya me sunan larabawa, fara me
kyau, ni wlh na mance sunanta, tace min kuna
soyayyah, hajia babba ta fara mai kwatamce
don tsakaninta da Allah ta manta sunan diyya,
tuna min sunanta mana? Tsaki Zaid yayi ya
kashe wayan. Tsaf ya gane Badiyya ce, miqewa
yayi ya fita daga dakin. Zaune ya ganta tana
kallon Zee World. Tana ganinshi ta tashi tsaye,
ko kallonta beyi ba ya yi kichin, doya ya dauko
da wuk'a ya fara fira, shigowa kichin din tayi
yace Yazayd ga abinci fa a dining yanzu na gama,
kamar ba zai tanka ta ba yace bana ci, ki daina
abinci da ni kinaji? Bata tanka ba sai cewa tayi
kawo na fere ma doyan toh, shiru yayi sai da ta
kara maimaita mai, yace kije na hutassheki. Jiki
ba kwari ta bar kichin din. Nan zayd ya gama
fera doyanshi ya soya, ya soya Kwai har da
sauce dama zayd ba daga baya ba gun girki.
Tana kallonshi ya xo ya bude fridge ya dauka
fresh Milk yayi dakinsa, miyau ta hade me ciwo
ta na ba kanta tausayi, dukda jiya dayau ba ta
wahala ba, ta wala a cikin gidanta kasancewar
Badiyya da uwarta basa nan..
Bauchi
Bigbro Samir, ya dago ya kalleta kadaran
kadahan, tace mena maka ne? Me sa ka tsaneni
haka? Kamar ba kai ba? Idan ka bar gida sai
dare ka ke dawowa, kamar baka son bude
idanunka ka gannin, Kamar m not ur
lilsismeerah, eyi yasamir? Me nayi maka ne?
My heart cant dmtake dis anymore, ka fada
mun idan da akwai abunda nake ma wanda
bakaso wlh a shirye nake na barih, because i
love u, i can do anything for u, kallonta kawai
yayi ya watsar, zuciyanta ya shiga zafih, cikin
masifa tace is dis because of Islahilkhair? Its
high time da zakayi letting feelings din Islah
flow kayi replacing dinshi da nawa coz m stuck
here with u forever nd u have to deal with dis,
U will never Get Islahulkhair back kadai ji
abunda Tsoho yace, idan ka na tunanin in
anyway she'd get back to u, toh stop dreaming
nd wake up frm ur slumber. Ta tashi ta bar mai
parlorn shi ko kalamanta sun mai zafib har be
san time din da ya fara hawaye bah.
Kaduna
Karfe 5 na yamma fadila ta hade cikin riga da

skirt na atamfa, tana kallon The Vow taji ana
Sallama ta mik'e ta bude tare da Amsar
sallaman, wata kyakyawar Mata da bata wuce
25 years ba riqe da wani kyakyawan yaro me
kama da ita ta gani tsaye tana mata murmushi,
kaman ta santa ta mata iso har parlorn Fadila ta
sa hannu ta amsa yaron ta cillashi sama tace
Bonbon yadai? Shi ko yaro sai kyakyata daria
yakeyi, suka gaisa cikin mutunci, ta ajiye shi ta
shiga kicin ta hado drink da ruwa ta dire gaban
matan, suka Kara gaisawa, Matar tace sunana
Amal, mu 'yan garin Gombe ne, jiya muka
dawo garin nan don anyi ma mijina transfer
zuwa garin nan, gidan mu ne jingine da wannan
idan kin leka zaki hange katangan, Hakkin
Makotaka yasa nace bari na shigo, Fadila tayi
murmushi tace Allah sarki ni ma kwana 12 a
nan gidan Lahhh Amarya ce? Fadila ta tabe
bakih, ta chanza topic din. Ya sunanka Bonbon?
Amal tace Irfaan, nima banyi 2years da aure ba,
ta miqe tace bari na tafi, Fadila tayi murmushi
tace InshaAllah nima zan shigo, toh shkn sai kin
shigo Amarya, fadila ta bata rai nidai sunana
Fadila, Amal tayi daria ta dauki Amal, fadila tayi
cikin daki da sauri ta hada ma Amal kayan
kamshi ta mata rakiya, Suna haraban gidan ne
suka ga Mai gadi ya wangale gate, duk suka bi
motar da ta shigo da ido, Jawad ne fuskar nan
ba annuri, tamk'e tamau, nan da nan kamar an
aiko ma Fadila mutuwa itama ta tsuke fuska,
Amal na lura dasu duka, a ranshi yace wato an
fara yi mishi shigeshige ko? Toh ba zai dauka ba
Ya fito kamar zai tashi sama...
Bibilicious Biebee2⃣7🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕
⃣ Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕 Suna tsaye
har ya karaso, kallon da suka wurga ma junansu
ya sa Amal fahimtar irin zaman da sukeyi lokaci
guda, nan da nan ta fuskanci ba jituwa
tsakaninsu, Amma sai ta basar ds yake itama
waiyayya ce, Amal ta bude bakinta tace ina
wuni? Kwarjininta da Girmanta ya sa ya amsata
da muna lpy?tace lpylao, Amal da bakinta tace
Ashe Sabin Amare ne, Allah Ya bada Zaman
lapya ya kwabe fitina, ya bar ku tare, ya kawo
yara masu Albarka ta qarashe maganan da
zolaya, Hankalin Jawad ya tashi ainun, be son
lokacin da ya ce mata Toufa, wa'annan adduar
sa ki nayi? Ko ce miki nayi ina sonta? Ya kallk
fadila yace keee Ba ki gaya mata yadda akayi
auren nan ba?
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment