Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD

Tace Aa Amma,
Amma tace liar, na ganki kina kuka, kamar jira
take ta fashe da kuka, Amma ta rungumeta sai
da ta yi me isarta, tace Amma Yazayd Dan iska
ne, Mashayi kuma Maz--- Amma ta dakatar da
ita ta hanyar sa mata hannu a bakih, Sai kuma
ta mata murmushi tace Maybe ke xaki kubutar
dashi daga sinful acts dinshi, ki nuna masa
hanya madaidaiciya, Amma how? I cant, Amma
tace shhh, mya Baby i trust u, u can even do
more, Have Faith kinji? Ta gyada mata kai. Tace
Oya tashi tsoho ya aiko A kiraki nace kina
wanka, tashi kijei, jikih ba qwari ta daura
dankwali ta fita. Amma ta bi bayan tillon diyarta
da ido, tausayinta ya mamayeta, Allah ga
Baiwar ka nan, Allah ka shige mata Gaba Amin..
******
Tsoho ya kalleta yace Rumah Nah, ba tare da ta
kalle shi ba tace Naam Tsohona, yayi murmushi
yace yau ko kallona ba zakiyi ba? Ko har ynz
fushin akeyi dani? Ta qaqalo murmushi, haba
Tsoho nah, wani irin fushi a na zaune kalau, ya
girgiza kai yace Rumah kenan, my favourite
among them all. Tayi murmushi, yace A tunanin
ki na shiga tsakaninki da farincikin ki na hadaki
da baki'n ciki, A Ganinki na hadaki da kunama
me zafin Halbi, na san xakice anya Tsoho na
sona? Ya hadani da Mashayi kuma Mazinaci?
Maysah na san abinda nakeyi. Allah yayi yarinya
me hankali, me tunani, me hangen nesa, da
sanin ya kamata uwa uba ga ki da Hakuri, kinyo
gadon kakarki Aishalle, Auren Zaid Jihadi ne, ke
kadai zaki iya hakuri da halayenshi, ke kadai
zaki tsaya tsaye a kansa har Allah ya sa ya bar
halayensa, kuma nayi istihara tun kafin nayi
hadin nan, naga Aurenku Alheri ne, Kece Rufun
asirinsa. Rumah kin fahimce ni? Maysah ta daga
kai tana kuka, tace eh Tsoho, Allah ya bani iko
Allah ya sa hakan yafi zama Alheri tsoho yace
Amin Rumah nah, sannan Abu na gaba, munyi
magana da Mudassir yace Zaid zai fara
housemanship dinshi Nextweek a Abuja a nan

National Hospital, Asibiti ta bashi Gida, Amma
na baku daya daga cikin gidaje na na Maitama,
na yanke hukuncin dake zai tafi, sai ki fara
Shirin tafia, gaban Maysah ya bada Hinqim tace
Allah kaimu. Yace Amin, Gani yayi sai Kyarma
takeyi, hakan yasa yace toh kina iya tafia,
sannan Akwai Taron duka Gida Gobe da Safe
Misalin Karfe 10 na safeh. Tace toh Tsoho Allah
kaimu Goben. Yace Amin Ta miqe guiwa a sake
ta bar Dakin tsoho.
******
Wallahi da an san yanda na tsana ganin Fadila da
ba a yi gigin hada auren nan balle a daura, wlh
na kijininta, Bilkisu tace ni wai ya ma za a aura
mun Azzalumi kamar Suraj, ji dai randa ya
kamamu ya zane, wlh na tsaneshi, Mu'ammar
da yake ganin kamar ya fi su tashin hankali,
babban tashin hankalinsa kuwa shine ganin an
daura auren Hanifa da wanninsa, Zaid kuwa ba
abunda ya damesa, chatting dinsa yake da
Diyyan Shagali. Amira kuwa ta maidasu TV sai
kallo take wannan yace ka za wannan yace kaza.
Aunty Saadiya tace hajiar mu kice wani abu
mana, toh dan ubansu sun ishe mutane da
surutan banza su saman ido mana suga yanda
zan warware alamarin nan, jira nake na ji ta
bakin Alhaji, sai na san abunyi, Amma sun tasa
ni gaba sai babatu suke tayi, ba sai na sa musu
ido ba, Aunty Abida tace ynz dai haquri zamuyi
gabaki daya, Sai mu jira muji me baban zaice
gobe. Kun gane koh? Duk suka gyada kai, Amar
yace hajia me zakiyi ke goben, ni burina a
warware auren nan kawai, hajia tace kai dai ka
bari sai Goben u shud all trust ur Grandma.
Hajia Babba Ta kalli inda zaid ke zaune tace dan
gidana Yaya dai banji kace komi bs? Ya kalleta
ya watsar yace ban da ta cewa, tace wai ni mesa
kake man haka ne? Miqewa yayi yace Jawad ka
kirani idan baba ya dawo ya fice daga parlon,
hajia babba ta hau masifa ina sonka kana gurxa
man, sai wulaqancin tsiya shege me qiran
samudawa, kowanensu sai da ya dara..
Gabaki dayan su sun Hallara parlorn tsoho suna
zama jiranshi, da sallama ya fito daga dakinsa
suka amsa mai, kujerarsa ya zauna aka fara
kwasar gaisuwa, sai da aka gama kafin yayi
gyaran murya tare da gajeruwar Muqadima,
yace Ahhh A jiyan ne aka daura auren Jikokina
su 12, Allah sa Alheri, 'yan dakin hajia Ama da
Umma Hajja kadai sukace Amin, Hajia Babba
kuwa sai hura hanci take tayi, abu na farko, ya
kira Hanifa yace taso nan, ta miqe ta nufeshi ya

ciro wata envelop ya miqa mata kamar ba za ta
amsa ba ta amsa yace dubu 50 ce sadakin ki ne,
jiki ba qwari ta koma mazauninta ta xauna, haka
ya kira Bilkisu, Islahulkhair, Amira Fadila da
Rumaysah ya danka musu sadakin su a hannu,
Sannan yace Ahh gobe lahadi, nasan gobe yan
mazan zasu koma bakin aikinsu, to na yanke
hukuncin kowannensu zai tafi da matarsa,
Jikokin Hajia Babba suka zuba mata ido alamun
zasu yi magana hannu ta daga musu alamun
suyi shiru, bari taga iya gudun ruwanshi, Tsoho
ya cigaba na bada kudadde zaaje Dubai a ma
yanmatan kayan daki da na kitchen, da kuma
lefe kuma na mallaka ma mazajen Gidaje a duk
garin da suke aiki, Sannan kuma na chanza ma
kowa mota nd kuma. Toh ina umurni da matan
su Shirya, gobe zasu bi mazajensu... Hajia
Babba tayi karaf tace kagama? Haba Alhaji? Ran
tsoho a. Bace yace Karime menene haka? Tace
bangane kowa ya bi mijin shi ba? Sbd me? Daga
daurin aure jiya, sai kace an gaji da su,,, ta
cigaba da bambami, Tsoho ya fara tarin karya
kamar xai shife, tarin da karfi, kuma sai Allah
ya kawo mai atishawa me zafi, ai nan hankalin
kowa ya tashi, Hajia karime ta rude, sannu
Ahaji, Baba hassan ya ruga firij ya dauko ruwa
yana fadin Baba sha ruwa, ya ture ya shaqe
murya yace ba ruwan da zansha ai haka take so
ta ga karshe na koh?toh bazan sha ruwan va, ku
barni na mutu kawai tunda ba za a mun yadda
nakeso ba, ai nan ta fita hayyacinta, ta fara cewa
ya haquri Alhaji, danAllah ka sha ruwa, wlh ko
ynz kace su tafi zasu wuce, daman wai naga ba a
shirya ba ne, amma yadda kace hakan zaayi,
Allah ya huci zuciyarka, danAllah ka sha ruwa,
Tsoho ya kurba Ruwan nan taro ya watse bayan
an Tsaida maganan gobe kowa xai wuce da
matarsa..
*****
Mu'ammar kamar zai yi hauka, fadih yake Hajia
wai menene haka? Bangane ba? Ya akayi kika
amince masa? Hajia babba tace dan ubanka so
kake mijina ya mutu, haquri kawai zakuyi ku
tafi dasu din, bayan sati 1ko 2 ku danqara ma
shegu saki 3 3, da dadin bakih da jan magana
suka amince da tafiar
Hajia Ama da Umma Hajja ne zaune parlorn
Umma Hajja su ka tasa Jikokinsu gaba suna
musu nasiha me ratsa jiki da ban haquri, tare
da jadadda musu haqqin zaman tare da na
auratayya, Da kuma ban Haquri, duk wanda yyi
haquri zai ci ribar rayuwa a karshe suka samusu

Albarka, sannan sukayi umarni da yanmatan
suje su hada kayan buqattunsu kafin a aiko
musu da wasu, haka suka miqe suna matsar
Kwallah kowa yayi sashensu don shirya kaya..
RANAN
_Bibilicious Biebee_
2⃣1⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee💕Biebee Isa💕Tsoho ya kalli
Aunty Nuratu da Aunty Zainab yace ku zaku
raka Rumah Abuja dukda shi Zaid din yace sai
Gobe litinin zaiyi reporting so tafianku sai gobe,
ke Abida da Hassana zaku raka Islahulkhair
gidanta da ke Zaria, Hussaina da Sadiya ku zaku
raka Amira gidanta dake Bauchi, Raijana da
Maryam ku xaku raka Fadila gidanta dake
Kaduna, Yusrah da Rafiyyah kuma zasu kai
Bilkisu gidanta dake Kano. Zayyad kuwa zai
dauki matarsa Hanifa su tafi chan gun aikinsa a
lagos... Ban san tashin hankali, Amare kawai
nace a kai gidajensu bance ayi tsegunguma ba,
ku tashi ku tafi, Allah ya tsare hanya. Suka amsa
da Amin, nan fa aka fara bankwana masu kuka
nayih, barin ma Islah, rumah da fadila da suka
rungume juna suna kuka, sun ba kowa tausayi,
don shaquwarsu ya wuce misali, ko tsoho kansa
sai da ya share hawaye. Da qyar aka tura Fadila
motar Ya jawad Aunty maryam da Aunty
Raijana suka shiga baya, jiki Ba qwari ya Jawad
ya zo ya durqusa gaban tsoho Tsoho ya mai
Adduan Allah ya tsare, haka ma akayi da Islah
Aunty Abida na huran hanci ta shiga motar don
bata son tafian nan take ba. Haka Ya Muammar
ya shiga motar bayan tsoho ya mai Addua, Yaya
Yusrah, da Yaya Rafiyya suka ja Bilkisu zuwa
motar Suraj, inda yaje yayi bankwana da
kakaninshi kafin ya shiga motar Tsoho yace to
ku tunda tafiar ku hanya ce kuna iya tafia. Allah
ya bada zaman lafia ya kawo kazantar dakih, ba
wanda ya tanka mai, Suraj ne ya fara jan motar
sanna Mu'amar ya bi bayanshi sai jawad ke
qareshe, Convoy sukayi suka bar gidan mudai
sai dai muce safe journey.
******
Baba usman ne ya kebe da samir inda yake
cewa Samir kaga kai da na ne, sbd Zainab
kanwata ce ita ke bi mun, Akwai shaquwa
tsakanina da Mahaifiyarka, ina so ka riqe min
Amanar diyata Amira, donAllah kayi haquri da
halinta, quruciya ce da sakarci ke dawainiya da
ita A sannu zata dawo daidai, Samir ya hadiye
miyau me dacih, wato kowa yasan Amira bata
da wayau, har ana hada shi da Allah yayi haquri,
wato yayi ta haquri shi yana cutuwa, da qyar

yace ba komai baba, yace yauwa Samir Allah
bada zaman lafia, Anya ba zaku bar tafian nan
gobe ba ku bi jirgi? Yace aa bari mu ta tafia ynz,
ina da abunyi gobe a office yace toh Allah muku
Albarka, Samir yayi bankwana da kakaninshi, ya
kwashi Amira da Aunties dinta biyu da zasuyi
mata rakiya zuwa Bauchi state.
******
Gudu suke ta shatatawa, ba me cewa juna qala.
Balle duk motan ba sa shiri, dama dama motar
Suraj Rafiyya da Yusrah Kawayene su kan taba
hira. Amma tsohon nan akwai hadin doya da
manja. In banda dole me zai hada Aunty Abida
da Aunty hassana a mota guda? Haka dai suka
daure kowa na kai zuciya nesa har Allah ya kawo
su Kano lafiya Unguwar Nassarawa GRA, Gida
ne da ya amsa sunansa Gida, a yau ne Tsoho ya
mallaka ma Ya suraj gidan nan, ko da suka iso
maaikata sun gyara gidan sun kalkale, Fadila da
Islah suka fito don kama ruwa, Aunties ma duk
suka shigo banda Jawad da Ammar, Yaya
Rafiyya tace ku Jawad ba za ku shigo ba? Ya
gimtse fuska ganin An kawo bilkisu gidan
waninsa be ganin zai iya shiga yace no yaya
wadannan ma su fito mu tafi kar maghriba ta
mana, yaya yusrah dai ta tabe bakih, tace ina
kano ina kaduna? Mu'ammar ne ya yi qoqarin
shiga ya dan leqa gidan, auntt tace ku ku muje
ko? Kun san tafia mun da nisa, duk suka
mimiqe, Islah ta kama hannun Bilkisu ta mata
Sallama tace Allah ya hada fuskokin mu da
Alheri, Harara bilki ta jefeta dashi, Fadila ko
kallo bilkin ba ta isheta ba suka bar dakin,
Bilkisu ta rungume Yayanta ta na kuka, Yaya pls
kar ka tafih, bana son nan, Muaamar ya share
mata hawaye a hankali yace dont cry sis, kin
manta abubda Hajia babba tace? Dis is for a
short period of time okay? Jus take care of
urself Ta gyada kai u too, Suraj na kallonsu ya
tabe bakih ya kaufa kai. Mu'ammar ya fita. Haka
suka qara daukan hanyan Zaria, in less dan
3hours suka iso Zaria, Cikin gari sukayi
Kuyambana Lowcost, inda Tsoho ya ba
Mu'ammar gida, haka dai suka shiga gidan suka
firfito har yan motansu Jawad, shima dai ya
fito, suka nufa ciki, Akwai dan Kurah a gidan
suka kakkabe, don shi Mu'ammar ya qiyin waya
a zo a gyara. Bayan sun dan huta ne su Jawad
suka musu Sallama hardasu Aunty Abida da
Hassana don gobe zasu bi flight din maiduguri
kuma ta kaduna zasu tashi, Islah ta sha kuka
sosai, don ba wanda aka bar mata daga ita sai

Muaamar, tana kallonsu suka shige mota suka
nufa Kaduna, suna barin gidan shima
Mu'ammar ya bar gidan don bejin xai iya kwana
under same roof with wata idan ba Hanifa ba.
Nidai Bie nace Islahulkhair u are on ur own oo😉
Gab da Isha'i suka shigo Garin Gwamna, sai da
Jawad ya biya dasu Mr Biggs sukayi take away,
ya kuna tsaya a One Eleven ya siyo musu Kaza
da Masa kafin yayi Unguwar rimi Lowcost dadi
inda Tsoho ya ba Jawad Gida me dan karen
kyau. A gajiye suka shiga gidan, gidan yayi kyau
matuqa. Nan suka zauna a parlo suka huta.
Samir ya kira Jawad yace yadai kun isa? Yace
shigowar mu kenan, shima Samir din yace mu
ma ynz muka shigo bauchi, Allah huta gajia
sukayi bankwana...
WasheGari
Ya Suraj ya kai su Yaya Raffiyya Airport don yau
zasu wuce Maiduguri bayan su mai nasiha
sosai,haka ma Samir ya kaisu Aunties dinsu
Airport, Jawad ma ya yankan musu Tickets din
komawa Maiduguri...
Maiduguri
Haka ma aka kawo Yazayyad da Hanifa Airport
su biyu rak bayan ta sha kuka sosai, suna zaune
suna jiran jirginsu da zai tashi zuwa lagos. Shi
ko Zaid ya kwashi Aunty Nuratu da Aunty
Zainab da Maysah a mota suka bar gidan bayan
Tsoho ya kebe da Rumarsa ya qara jaddada
mata, sun kusa wajen Garih ne ya latso wayarsa
ji kawai sukayi yace Na kusa dags bisani kuma
suka ji ya gangara bakin titi ya parker, ba wanda
ya tanka mishi, ta gilashin mota ya hangota, ya
kalli Maman Samir da ke zaune gaban mota
yace Aunty Zee dan koma baya, mun qara
samun pasinja, tace pasinja kuma? Be tanka ta
ba ya bude murfin kofa duk suka bishi da ido
gurin wata suka ga ya nufa, Ta sha Ado sosai ta
na janye da Akwatin Trolley, Gaban Maysah ya
buga sakamakon wacce ta gani ba kowa vace
illah wannan da suka ga ta na bacci kan Gadon
Yazayd, wacce sukayii fada da Amira, toh
wacece wannan?to ba kowa bace illa Baddiyan
Shagali, Da sauri Maysah ta fara maimaita
inalillahi da ita zaa Abuja? bude booth yayi ya
tura Akwatin Diyyan Shagali, kafin ta zo ta bude
gidan Gaba ta fada tana me karya jiki da feleqe
ta juya baya ta bi su da kallo daya bayan daya ta
watsar, bata da niyyan tankasu, duk irin
tsageranci na Zaid sai yaji be ji dadin hakan da
tayi ba, a hankali yace Dear, My Aunties, ta dan
juya tare ds yin kicinkicin da fuska tace Ina

kwananku? Aunty Nuratu ta kasa haquri dai tace
Zaidu wai Wacece wannan????
_Bibilicious Biebee_
2⃣2🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕
⃣ Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Zaid ya danyi
gajeran tsaki yace Aunty sunanta Badiyya,
Aunty Nuratu ta yi shiru da bakinta haka suka
dauki hanyan Abuja, Gudu suke ta shatatawa,
sun tsaya sun ci abinci a kano kafin suka dauki
hanya kuma.
Lemmie help u wit ur seatbelt, ta galla mai
harara tace i dont need ur Help, Zayyad ya yi
murmushi ya saka nashi belt din, Jirginsu ya
fara tafia Matuqar tsoro ta tsorata, ba yau ta
fara hawan jirgi ba amma ta tsorata da tashin
Jirgin yau, bata san tym din da tayi saurin dafa
YaZayyad ba da jirgin ke niyyan tashi tare da
rintsa ido, Zayyad yayi murmushi yace Ashe
yarinyan na da tsoro, da sauri ta janye
hannunta daga nasa ta galla mai harara, be
tankata ba, illa ya ciro Chalbin shi a aljihu ya
fara Ja. Haka suka daidaitu a sama suna tafia
har bacci dai sai da tayi a kafadun YaZayyad ba
tare da saninta ba, Cikin Awa daya da yan
mintuna suka iso LAGOS, hanifa ta gaji sosai,
Cab ya tsaida musu suka hau, har gidansa da ke
wani unguwan da sai na tambayo sunansa😉 Gida Gida
ne self contained, ya biya me tazi din ya kwashi
kayan shi da nata ita ko handbag ta dauka, Nidai
nace Waiyo Allah Zayyad Bawan Allah, be dau
abun da Zafih ba, idan ta qi bada kai ka zane ta
kawai👻
Zayyad Hussaini Zailani Matashi ne dan kimanin
Shekaru 29, yaro ne kyakyawa wanda be da
matsala ko kadan, hak'urin shi ya wuce misali,
Yana aiki ne a Birnin Lagos A wani Companyn
Oil And Gas. Rokonsa daya Allah ya bashi
Zaman lafia da wannan er Zafin kai ni dai nace
Amin.
Sai dare suka iso Abuja, Straight sai da yaje
Garki ya ajiye Diyya yace mata sai yazo, kafin ya
dauki hanyar Gidan da Tsoho ya mallaka mai
dake Maitama, Gida ne na 'yan mala'u masu
brush da cinyen kaza, gidan ya tsaru iya
tsaruwa, Su Aunty nuratu suka shige dakih da
huta gajia.
Zaid Mudassir Zailani tsaran Zayyad ne amma
Zayyad ya bashi kwana 14, ya na da kwalin
degree na likitanci, A gobe ne zai fara
HouseManship a National Hospital Abuja, Zaid
be da wata matsaala in banda ta shaye shaye da
kuma tsageranci, Toh gashi an hadashi da
Salihar Mace, toh ko ya tafian nan zaiyuwu?🤔

Ko da Jawad ya kai su Aunty Abida Airport
bayan tashin su straight Office dinsu ya nufa,
Jawad Mudassir Zailani Matashi me ji da kanshi
dan kimanin shekaru 27 ya karanta Industrial
Chemistry, ynz haka yana Aiki a NNPC kuma
tauraruwarsa na haskawa don yana da himma
da qwazo, Jawad na da zafih be son raini kwata
kwata, gashi an hada shi da Macen da ba a
tabata ta kyale duk girman mutun. Toh ku
biyoni dai muje.
Samir kuwa tunda ya kaisu Aunty, ya tafianshi
Office, Samir dan kimanin shekara 27 ya
karanta Engineering, samir na da sanyin zucia,
be da matsala, Samir Injiniya ne wanda ake
damawa dashi a garin bauchi, Matashi ne ko
shekara daya be rufa da fara aiki a Bauchi ba,
Amma ko ina damawa ake dashi, balle
gwamnati da ke bashi kwangiloli, Samir Gambo
Zailani kenan Matashi me ji da kudi, Young
Billionaire. Toh ya zaman shi zai kasance da
Psychic lilsismeeranshi?🤔
Hmmm Mu'ammar Labaran Zailani, Matashi me
shekaru 28 a dunia, Ya hadu iya haduwa, Shima
dai Injiya ne amma na jirgi, wanda ake kira da
Air Police Engineers, Mu'ammar na aiki ne a
nan Air force Aviation da ke Zaria, Mu'ammar
dan zafin kai ne, Shi ya sa abu a gaba to sai ya
cimmai, in ko ba haka ba ya shiga damuwa,
Tunda ya iso Zaria ya bar Yar baiwar Allah ita
kadai ciki, ita kadai ta kwana, ya tare gidan wani
Abokinsa Ahmad, don shi gani yake ba zai iya
kwana gida daya da Islahulkhair ba, don ya na
mata tsana me zafih, toh su Amar ga shawara
idan zaka k'i mutum ka k'i shi saisa saisa don ba
a san wanda gari zai waya ba.
Suraj Umar Zailani dan shekara 27 a dunia,
Matashi ne dogo kyakyawan gaske, ya Karanta
Architecture, Yana aiki ne a nan kano mostly
Gwamnatin kwankwaso ta tsaya mai wuri zanen
Tituna masallatai, makarantu d.s, Suraj ya
qware ta fannin zaneh, ko mutum zai zana shi
tsaf, Suraj na da kirki yana da haquri amma abu
kadan ke bata mai rai baya son raini ko kadan,
Arch. Suraj kenan Angon Bilkisu er baba
labaran.
Da Daddare
9:30pm;; Samir ne ya paka motarsa ya fito, da
take away a leda ya yi hanyar parlonsa, zaune
take gaban kofar parlorn, gashi dare ya farayi,
kawai ganinta yayi zaune, sai da ta bashi tsoro,
ita kuwa tana ganinshi ta miqe da sauri, Ta nufo
shi ds niyyar rungumsshi, Ya gimtse fuska tare

da matsawa baya, Bigbrosamir, tunda safe ka
bar gidan nan, ina ta kiran ka ka qi dauka
qarshe ma ka kashe wayanka, ina taji tsoro
nikadai a gida, be tankata ba ya raba ya bude
kofa ya shiga ciki, ledar take away din hannunsa
ya ajiye kan dinning, ya shigewar sa dakih
donyin wanka. Zuwa tayi ta bude ledar taga
kazah ce da Fresh Yoghurt, ta nufa kicin ta
dauko plate tayi dakin samir dashi, tym din ya
fito wanka ya na tsane kansa da dan qara min
hand towel, dagowan da zaiyi ya ganta tsaye,
dan guntun tsaki ya sake, tace bigbrosamir ga
abinci kazo muci, kamar ba zai tankata ba yace
ni na koshi, wannan nakine, Tace Allah ko? Toh
nagode, ta zauna kan kujera kamar zai yi ihu
don takaici, ya daure dai yace Amira i want to
dress up, ba tare da ta kalleshi ba tace go ahead
mana, m ur wife ryt? Ganin idan ya biye mata
ranshi zai baci ya zira jallabiyanshi ya koma
toilet, ta gama cin kazarta ta sha yoghurt ta kai
plate kichin, ta shiva dayan dakin ta yi wanka
tare da sa nughtgown, ta koma dakin Samir, har
ya kashe wutan Dakin ya kwanta yana latsa
waya, Gadon ta haye, da sauri ya miqe tare da
kunna side lamp, ya daure fuska, ke Amira
Lafia?? Tace menene bacci zanyi, Yace ki fita
mana ki koma dayan dakin, tace jar uba, ni
kadai ral cikin dakih, to ba zan iya ba, ka fita ka
barni ni kadai na haqura ynz u expect me to
sleep all alone? Hell No, wlh nan zan kwanta,
samir kamar zaiyi hauka don takaici, a hankali
yace Amira pls ki fita, tace lallai bari ma ka
gani, ta gyara kwanciyarta kan gado, Cikin daga
Murya yace Amiraaaa ta dago sosai dan taji
muryan sa kamar me shirin yin kuka, yace
please leave, tace nifa na gaya ma i aint going
anywhere, ya miqe ya dauki pillow yace Please
Amira dont make me hate you
2⃣3⃣ 🏡GIDAN GANDU🏠by 💕Biebee Isa💕Gidan Gandu🏠by 💕Biebee Isa💕 by 💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Biebee Isa💕Mamaki ya
rufe Amira, Toh me yayi zafih haka? Ya samir
me na maka haka har kana kira min kalmar
Tsana? Be tankata ba ya dauki pillow ya bar
dakin parlo ya nufa ya kwanta kan doguwar
kujera, Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba,
a rayuwarta yau ne a ka taba mata abu ba tare
da ta rama ba, yau ne aka mata abu ta tsaya
tana kuka ba tare da daukar mataki ba, in banda
Yasamir wa ya isa ya takata haka? Waiyo
Allahnta, ya zatayi? Ga wani son samir da ya
shigeta farat daya, haka ta dinga rubzar kuka
har bacci yayi awon ga ba da ita.
Kaduna

Ko da Jawas ya iso gidan karfe 10 da wani abu,
xaune ya iske hakimar wato Fadila a parlor ta
na kallon Series din nan na "Married Again "
Dakinsa ya wuce straight ita kuwa bayan
sallamar da ta amsa mai ko kallonshi ba tayi ba.
Ta cigaba da kallonta tana kada k'afa daga bisani
ta miqe tayi kicin don dafa indomie. kichin din
shaqe yake da kayan Abinci ko mi akwai don
Tsoho sai da ya cika su da komai na abinci kama
daga kayan miya, nama, kaxa, kifi, kai harma da
o
tolotol
o👻
Lagos
Shigowar sa kenan Gidan ya nufa dakih, ka
sancewar gidan 1bed room ne amma dakin me
girma ne, kwance take kan gado tana hawaye,
ya cire bakih ya kirata yace Hanifa, hanifa,
banza tayi dashi kamar bata san yanayi ba, da
yaga ba zata kulashi ba ya shigewarsa toilet din
dakin, ya yayi wankansa ya dauro Alwala yayi
shafa'i da wutr, yazo ya chanza kaya zuwa na
bacci, ya hau gadon ya kwanta, kukan ta takeyi
ba ta fasa ba, Shi filazal baya son kukan mace,
ya daure dai ya ce Hanifa donAllah kiyi shiru,
bana son kukan nan naki, ko me yayi zafih
maganinshi Allah, kiyi haquri mana, cikin tsiwa
ta miqe tace kai mallam saurara min, ina ruwan
ka da kuka na? In kaji zafih ka sakeni, yayi
murmushi yace banji zafih ba Allah ya baki
haquri, have a Sound sleep, yayi kwanciyarsa
tare da juya mata baya, takaici ya sa ta saki
wani kukan da qarfi, shi ko yayi saurin runtse
idanuwansa, da yaga taqi shiru pillow ya dauko
ya fita sitroom, tsoro ya mamayeta kamar tace
ya dawo, Amma taurin kai da irin zuciyar Hanifa
ya sa ba ta nuna komi ba, amma harga Allah
tana tsoron kwana dakin nan ita kadai, haka ta
kwanta rabin ido daya a rufe rabi a bude (lol)
Zaria
Taci kuka har ta qoshi, tayi sallah ba adadi, a
tsoroce take, tun jiya rabon da taga Mu'ammar,
haka ta kwana cikin tamfatsetsen gidan nan ita
kadai, hankalinta ya gama tashi, da qyar ta dafa
Taliya tacih, ta kira Wayan Maysah a kashe, ta
kira fadila ta ci saan wayar ta kunne yake,
amma ba a dauka ba, kasancewar wayar na chan
dakin ita kuma fadilar tana parlor tana kallo,
wani kukan ya subuce mata, gashi ba ta san
kiran Umminta don kar hankalinta ya tashi,
Dare kuma Ya Tsala, haka Islahulkhair ta kwana
tana kuka, da ta ga kanta na neman Bugawa sai
ta dauko Alkurani mai girma ta shiga karatu. Shi
ko Mu'ammar na nan Gidan Abokinsa Ahmad,

ya ma manta da yana da wata mata a Gida.
Kano
Ya shigo da sallama ta na jinsa amma tayi biris
dashi, ya qara doka sallama tayi banza dashi,
qarshe ta hau karkada kafarta, da qarfih yace
keee bilkisu, ba ki jin ana sallama ne? Ko ba ki
iya amsawa ba? Cikin tsiwa ta kalleshi ta
haraeshi, tace naji kana sallama, na iya amsawa,
ban dai ga damar amsaka bane, fuuu ta wuce
dakinta, zuciyarsa tayi k'una, har ya bita dakin
don ya lakada mata na jaki, sai zuciyarsa ta
haneshi, ya danne zuciyarsa, yayi kwafa. Ita
kuwa tana shiga dakin ta dinga murna ta
bakanta ma Suraj, haka ta dinga kullah yanda
zata dinga chuzguna mai har sai ya saketa kafin
Hajia babba tayi na ta aikin.
Abuja
Da Safe, Ya kaisu Aunty Nuratu Airport, bayan
sun dade kan Maysah suna mata nasiha don sun
lura da take taken zaid, tasha kukanta, haka
suka rabu, sai da yaga tashinsu kafin ya wuce
National Hospital, yaje yayi reporting dama
suna expecting dinshi, aka bashi office da tag
dinsa a rubuce an sa Dr. Z.M Zailani Nan take ya
fara ganin patients cikin kwarewa, yanda kasan
bature haka yake tafiar da Alamuransa. Har
misalin karfe hudu, ya tattara yana sa yanasa
yayi signing out ya tafiarsa. Hotel din da ya
sauke Badiyya ya nufa, ya kirata a waya, ringing
daya biyu ta dauka, yace gani na iso,sauko qasa,
a yangance tace ba ni kadai ce ba fa, yayi jim
chan yace ke da waye? Tace ni da mamana,
shirun ya qarayi chan kuma yace yaushe tazo?
Tace yau din nan, to ku fito muyi ta tafia, bayan
mintina 12 sai gashi sun sauko, ta side mirror
ya hangosu, ko wannensu dauke da akwati
trolley, maman baddiyya ta qi amincewa ta
tsufa, irin shegun matsatsun kayan nan ke
jikinta, fuskan nan tasha coiling ga gashin doki a
kai, wannan shine like mother like daughter.
Kwankwasa mai tayi yayi winning glass da
murmushi a fuskanta tace Oga a bude Booth
ko?
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment